Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halin da ake ciki. Na san kuma shima zai sanarwa gwamna abin da ya faru, tunda dai wannan (case) ne da ya shafi qasa. wadannan ma'danai da 6arawon ya sata tun shekaru talatin da suka wuce (resourcces) ne na qasa baki daya. Kuma kowa yana da labarinsu. Dole ne gwamna shima ya shaidawa ministan albarkatun qasa labarin sace Nalamma, Tunda a jiharsa abin ya faru, kuma a nan ake tsammanin 6arawon ya 6oye ma'adanan tun a wancan zamanin. Kan zo mu tattauna akan (case) din, wannan bahagon al'amari ne....! Dole ne muyi taka-tsan-tsan don kada wata matsalar ta faru a wajen bincike da bin diddigin yadda aka yi har aka sace Nalamma."
.
Kwantirola musa sabo yayi masa gdy, ya ce zai zo a minti goma masu xuwa. Suna gama wayar ya dauki mabudin motarsa dake akan kujera. Ya zo zai fita kenan daga falon, matarsa ta shigo dauke da tiren abinci da tambulan din ruwa da kofi a gefe.
.
"ba zan iya cinye abincin nan ba,ya mayar dashi kawai."
.
Ya ce da ita lkcn da yake qoqarin bi ta gefenta ya wuce. Matar tasa ta tsare qofar cikin damuwa, in har akwai abin da yafi komai 6ata mata rai a duniya, bai wuce ta gama abinci ta sha wahalar shiryawa mijin nata abinci, sai ta kawo masa Kuma ya ce ba zai ci ba." da yake shima ya san bata son hakan, Kuma duk da yawan shekarunsu irin wannan ya sha hadasu rigima a tsawon lkc da suka yi tare. Tun kafin tayi magana sai ya ce da ita.
.
"ki yi haquri maman faruq, wani aikin gaggawa ne ya taso ynxn nan, shi yasa ba zan sami tsayawa in ci abincin ba,ya ynx haka Eriya kwamanda yana can yana jirana a ofis."
.
'yar gajeriyar matar tasa, wacce zata kai shekaru arba'in, ta ce dashi cikin damuwa.
.
.
Yau ma rahmert khaleel zazzau zata shigo "TASKAR GIDAN LITTAFI" dauke da shirin "filin raha" misalin qarfe takwas na dare.
Lp=18}~~~~~~{ Gobe jar kasa 2}~~~~~~{
page 18
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
'yar gajeriyar matar tasa, wacce zata kai shekaru arba'in ta ce dashi cikin damuwa.
.
"komai ya taso ai dai ka tsaya ka sanya wani abu a cikinka. Tun daxun nake ta sauri in gama abincin nan, don na san halin ka, kana iya cewa zaka fita wani wuri..."
.
Kwantirola musa ya dakatar da ita cikin sauri ganin zata 6ata masa lkc, ya ce da ita kai tsaye.
.
"ke ba lfy! Nalamma aka sace ynx-ynxn nan, Kuma 6arayin sun gudu dashi."
.
Maman faruq ta bude baki a tsorace, bata san lkcn da tiren abincin ya su6uce daga hannunta ya kife a qasa ba." mijin nata ya fice ya barta a falon, bai yi mamakin tsoratar da tayi ba." don kuwa ya sha bata labarin Nalamma Tsohon 6arawo mai taurin kai. Kuma ya ta6a sanar da ita cewar, idan har aka sace Nalamma a hannunsu, Akwai yiwuwar zai iya rasa muqaminsa baki daya.
.
Dole ne kuwa maman faruq ta rikice a sakamakon jin wannan labarin.
.
.
*** ***
.
.
Sun kai minti talatin motar tana kwarara gudu dasu, kamar zasu tashi sama. Tun lkcn da suka tabbatar sun 6acewa motocin Jami'an tsaron dake biye dasu, sai sadi ya baiwa Shago umarnin ya canza hanya, don gudun kada 'yansandan suyi waya a kamasu a gaba.
.
Shago ya kada kan motar ya hau titin wani qauye mai kilo mita arba'in, suka ci gaba da tafiya. Duk abin da yake faruwa mai ankwa na kishingide a gaban motar kusa da Shago, yana dafe da qafarshi yana numfashi daqyar, yana cije baki sbd tsananin azabar harsashin dake sukar cinyarsa. Jinin da yake xubowa daga cinyarsa ya jiqa qafar wandonsa sharkaf, yana taruwa a qasan motar.
.
Duk da sadi yana sane da Jami'an tsaron sun harbi mai ankwa a qafa bai sa hankalinsa ya tashi ba." yana a Bayan motar a zaune ya qanqame Nalamma, wanda idanunsa ke a rufe kamar ya suma. Lkc zuwa lkc sadi ya kan kai hannu xuwa qirjin Tsohon, don ya ji ko xuciyarsa tana bugawa. Ya fi xullumin rayuwar Tsohon fiye da rayuwar yaran nasa biyu, mai ankwa da Shago.
.
Lkcn da suka zo wani qauye ne da misalin qarfe takwas na dare, sai sadi ya daga murya ya ce da Shago
.
"samu wuri ka tsaya Shago ina son muyi magana.-
.
Shago ya ragewa motar gudu, ya yo fakin a kusa da wani kwatami, inda ruwa ya ke taruwa. A saman ruwan kainuwa ce ta yaryadu, wanda hakan ke nuna alamar idan rana ta yi a nan agwagin qauyen suke xuwa su baje kolinsu. Suyi wanka su tsattsagi qananun kwadi su fito waje su sha iska.
.
Sadi ya ce da Shago
.
"sun harbi mai ankwa a qafa, sannan Kuma wannan Tsohon yana buqatar hutawa na wani lkc, kafin ya gama farfadowa ya kamata mu samu inda zamu 6oye na wani lkc."
.
Shago ya dubi mai ankwa wanda ya kwantar da kanshi a gefe guda idanunsa a rufe. Ya juya baya ya ce.
.
"to ina kake gani zamu je oga? Ka san fa ynx an baza Jami'an tsaro a ko ina su nemo mu. Bai kamata mu tsaya a kusa ba."
.
Sadi ya ce.
.
"dole ne mu rabu do motar nan Shago. Sbd ita ce abu na farko da za a fara amfani da ita wajenn gano mu, sun riga sun ga motar, dolene mu rabu da ita, mu samu wata motar, idan kuma har muna son wannan Tsohon ya samu damar yin magana, ya zama wajibi mu kaishi inda zai huta, amma ba zai iya jure kwaramniyar tafiya a mota ba, kada mu zo muyi wahalar banza yazo ya mutu a qarshe, ba tare da ya fada mana abin da muke so ba.
.
Shago ya tambayeshi cikin ladabi.
.
"to ynx ya zamu yi kenan oga?"
.
Sadi qare-garke yayi tunani na wani qanqanin lkc. Ya dubi Nalamma wanda ke kwance magashiyan akan cinyarsa. Kamar an jera masa qasusuwa. Ya ce da Shago.
.
"mu fara rabuwa da motar tukuna. Mu qara yin gaba inda Babu kowa sai mu fito mu sawa motar wuta ta qone. Daga nan sai mu taka a qasa. Ni zan dauki wannan Tsohon. Kai kuma sai ka dauki mai ankwa mu samu inda zamu 6oye kanmu. Idan muka samu mafaka duk abubuwan da zasu biyo baya zasu zo mana da sauqi."
.
Shago ya tuqa motar suka qara gaba, a wannan karon baiwa yi gudu ba." suka wuce qauyen a hankali. Sadi ya kai ganinsa inda wasu gungun matasa suke zaune akan wadansu guma-guman itatuwa, da kuma wani qwan
Lantarki shi daya qwal a jikin wani gida inda qananun yara suka yi dandazo wanda ke nuna alamar gidan bidiyo ne....! Ya kawar da kansa, a haka har suka yi nisa suka bar qauyen.
.
Sun yi tafiyar kilomita uku basu qarisa wani qauye ba." a daidai lkcn da suka zo wajen wasu kwazazzabai. Sadi ya ba Shago umarnin tsayawa. Da tsayawarsa sadi ya bude qofa, ya fito dauke da Nalamma a hannunshi ya kaishi gindin wata doguwar giginya dake nesa kadan da wajen, ya shimfidar dashi a qasa. Kafin ya juyo ne ya koma wajen motar, Shago ya fito da mai ankwa ta hanyar dora hannuwanshi a wuyansa, da kuma daukar qafarsa wacce aka harba. mai ankwa yana ta qaraji, a yayin da Shago yake tsayawa suna hutawa, a haka har ya kaishi inda sadi ya kwantar da Nalamma. Ya ajiyeshi a kusa da tsohon, suka jeru kamar wadanda suka yi hadarin mota.
.
Shago ya koma wajen sadi wanda yake tsaye yana jiransa a wajen motar.
.
"oga mai ankwa fada yana jin jiki. Ya kamata muyi wani abu da sauri, kada jininsa ya qare, har ynxn xuba yake yi baiwa tsaya ba."
.
"bani ashanar dake a wajenka."
.
Shago yayi saurin lalubo ashanar ya miqawa ogan nasu. Da sadi ya amshi ashanar ne ya bude ya zaro tsinke daya, kafin ya qyasta ne ya bude murfin tankin man motar ya jefa ashanar dake ci da wuta a cikin tankin man motar. Kafin wutar ta shiga cikin tankin ne ta kama bakin tankin da ci.
.
Shago ya Jami'an baya a lkcn da yaga wutar tana ci. Sadi ya bi shi suka sake nisanta daga wajen motar, suna tsaye har xuwa lkc da wutar tayi bindiga a cikin motar. Motar ta kama ko ina da ci bal-bal kamar ta samu karmami, sadi ya kawar da kanshi daga kan motar ya dubious Shago.
.
"mu hanzarta mu tafi kada dare ya yi mana, bamu samu ma6oya ba."
.
.
Lp=19}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 19
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"mu hanzarta mu tafi kada dare yayi mana, bamu samu ma6oya ba."
.
Shago ya ce cikin ladabi.
.
"daga nan ina zamu nufa oga? Ka san wani gari ne dake a kusa, wanda zamu je mu 6oye a can?"
.
sadi ya ce dashi cikin qwarin guiwa.
.
"shi yasa nace da kai ka biyo wannan hanyar dama. Akwai qananun qauyuka da rigagen fulani a gaba kadan, amma kafin nan akwai wani bahauwan kogi da zamu qetara. Shi nake xullumi, don kuwa ba lallai bane mu samu kwale-kwalen da zamu yi amfani dashi. Amma dai can din zamu je dole, babu inda zamu je mu samu ma6oya mai kyau, inda hankalin Jami'an tsaro ba zai karkata xuwa wajen ba fiye da can."
.
Shago ya ce dashi.
.
Kome ka ce haka za a yi oga."
.
Sadi ya shige gaba, Shago yabi bayansa. Da xuwansu inda giginyar take sadi ya tattaro motsattsen Tsohon ya xubashi a bayansa kamar ya debi kayan wanki. Shago ya dubi mai ankwa, wanda ya fita hayyacinsa. yana a kwance magashiyan yana fitar da numfashi daqyar, kamar ranshi zai fita. Ya sunkuya ya daukeshi daqyar don kuwa a halin ynx ba zai iya tafiya ba."
.
Bayan sun dauki mutanen biyu ne, sai sadi ya sake shiga gaba, Shago ya bi bayansa yana dauke da mai ankwa wanda jikinsa yayi nauyi ko motsawa ba ya iyawa. Suka bi wata hanya wacce tayi hannun riga da titin. Suka tafi ba tare da sun sake waiggowa baya ba sun kalli motar dake ci da wuta rigi-rigi. Hayaqi yana tashi sama yana sajewa da manya-manyan giza-gizan da suka tsare harabar sararin samaniyar tun wani lkc.
.
Wasu maharba biyu dake a nesa kilomita daya daga inda motar take ci da wuta, suka fara zantawa akan qona daji da mutane suke yi da daycare. Daya ya ce masu neman zuma ne a saman bishiya. Dayan ya qaryatashi ya ce, masu fadamun rake ne suke sharar gona, don kuwa qone-qone da daddare ya fi dadi idan Babu rana.
.
Abin da maharban biyu basu sani ba shine, wata sabuwar mota mai rai da lfy wasu 6arayi suka qona don kada a gane inda suke. Kuma basu damu da asarar ba,ya don kuwa suna san rai da samun wani bayani ne, wanda zai kaisu inda zasu gino wata gagarumar dukiya, wacce zata iya mallaka masu motoci fiye da dubu a tashi daya.
.
.
.
***
.
.
"laifin me nayi maka nura...? Don allah me nayi maka?"
.
Hauwa ta tambayi nura tana kuka da qarfi, a lkc guda itama tana kallonshi cikin tsoro da fargaba. Nura ya ce da ita.
.
"na fada maki ni kadai nake son in mallaki wadannan gwala-gwalan ba tare da kowa ya sani ba." na dade ina son in mallaki dukiya mai tarin yawa a duniya Hauwa. Kullum da wannan burin nake kwana, dashi nake tashi a rayuwata. Sai yau burina ya cika, gashi na mallaki gagarumar dukiya mai tarin yawa."
.
Hauwa ta ci gaba da Ja baya tana yi masa magiya.
.
"kayi haquri kada ka kashe ni nura, na bar maka gwala-gwalan ka riqe su kai kadai, bana son ko daya. Don allah ka barni da raina nura, na barmaka su."
.
Nura ya yi murmushi. Gabza-gabzan hoqoranshi suka bayyana a hasken farin watan.
.
"dukiya irin wannan ba dukiya bace da mutum zai yarda da wani akanta. Ba zai yiwa in yi sakacin barin ki da rai alhalin kin san ina tare da wadannan gwala-gwalan ba." me zai hana ki garzaya wajen 'yansanda ki fadi masu cewar gwala-gwalan Suna a wajena? Me zai hana ki fadiwa mahafiyarki da qawayenki? Idan har na kuskura na barki a raye Hauwa, dolene asirina ya tonu komin dadewa. Kuma duk inda na shiga a duniyar nan indai har Jami'an tsaro sun sami labarin ina tare da wannan dukiya, na tabbatar zasu bini su kamani.
.
Don haka kashe ki shi ne rufin asirina. Babu wanda ya san wannan sirri, daga ni sai ke. Hankalina ba zai ta6a kwanciya ba idan kina a raye Hauwa. Zan kashe ki ynxn nan, in gina rami in binneki. Babu wanda zai ji kukanki a dajin nan, mu biyu ne, daga ni sai ke. Ki daina ba kanki wahala."
.
Hauwa ta ci gaba da kuka tana matsawa baya, nura yana binta a hankali riqe da qatuwar digar haka rami, wacce yake shirin kwada mata.
.
ina fuskantar matsalar network, jiya Sau biyu ina typing amma idan zan yi post sai yaqi loading. Don haka kada kada ku damu, zan riqa yin kadan-kadan, don alkinta wanda ya samu.
.
Kuma inshaa allah yau ina tare daku matsawar wuni. Zan riqa yin post akai-akai. Idan kin yi nisa ko kayi nisa za a wuce ka, ko a wuce ki.
.
.
Hauwa ta waiga ko ina hagu da dama, babu wani mutum a kusa.
.
.
Lp=20}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 21
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Hauwa ta waiga ko ina hagu da dama, Babu wani mutum a kusa. Gashi Kuma dare ne, ballantana wani ya hangota daga nesa ya fahimci abin dake faruwa, a zo a ceci rayuwar ta daga hannun azzalumin masoyinta nura aljan. Wanda ya sha alwashin sai ya kasheta.
.
"ki tsaya a waje daya, babu inda zaki je ko kin gudu Hauwa."
.
Nura ya gargadeta a wannan karon ya murtuke fuskarsa, kuma ya fara qosawa ya kasheta, ga alama ya gaji da surutin da suke yi.
.
"ba zaki iya tsere mani ba, ke kanki kin san haka. Kuma ihunki banza ne, ko kinyi Babu wanda zai ji ki, saboda Akwai nisa a tsakanin mu da gari."
.
Hauwa ta waiga baya ta hango titin dake a nesa, motoci Suna wucewa lkc-lkc. Daga saman tsaunin tana iya hango danjojinsu idan sun bada baya. Idan har zata iya guduwa ta kai bakin titi, ba tare da nura ya cimmata ba,ya tana sa ran zata tsira. Don kuwa ba zai yiwu ya bita titin ba motocin suna wucewa Suna haskesu da fitilinsu.
.
Wannan tunanin da Hauw tayi shi ya dan qarfafa mata guiwarta. ta sake waigawa cikin sauri ta hango titin. To amma Kuma a lkc guda nura shima ya gano tunanin da take yi, Kuma shi kanshi nura ya fahimci idan har ta tsere masa ta kai bakin titin, dolene ya rabu da ita,
.
Don haka tun kafin ta sake yin wani tunanin sai ya taso mata aguje riqe da digar a hannunsa na dama. Hauwa tayi kururuwa ta juya aguje ta gangara xuwa qasan tsaunin, bata san lkcn da ta watsar da takalmanta da gyalenta ba."
.
A tsakanin ta da nura Akwai tazarar taku biyar, Kuma ga mamakinshi Hauwa tana da gudu fiye da yadda yayi tsammanin zata iya. To amma wannan gudun tana yin shi ne don ta ceci rayuwarta. Ya biyota aguje suka gangaro daga saman tsaunin, itatuwan da aka sare da tsittsige, suka fara ji mata ciwo a qafa, amma hakan bai sa ta fadi ba, ta mayar da hankalinta wajen gudun da take yi, tana kuka tana waigowa baya, tana kallon nura, wanda yake biye da ita a fusace, riqe da mugun makamin da idan har ya cimmata, ya kwada mata, Babu shakka kwananta ya qare.
.
Lkcn da Hauwa ta gama saukowa daga saman tsaunin, ta ba nura tazarar qafa takwas, ta fishi gudu, kuma indai har suka ci gaba a haka, da wahala ya kamata, har ta kai bakinn titin. Wannan tunanin shi ya tsorata nura, domin idan har Hauwa ta tsere mashi bai cimmata ya kasheta ba,ya rayuwasa tana a cikin hadari. Bayan rasa wadannan gwala-gwalan da zai yi, ya tabbatar a gidan yari zai qarisa rayuwarsa a matsayin wanda za a kama da laifin yunqurin kisan kai.
.
Da nura yaga haka sai ya tsaya a wurin da suka kafe babur din da suka zo dashi dajin, ya hau ya tayar ya sagala digar a kafadarshi, ya murza babur din a lkc guda ya juya shi ya fuskanci hanyar da Hauwa ta bi tana gudu wacce zata kaita bakin titin.
.
Nura ya biyota da babur din.
.
.
Lp=21
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 22
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Nura ya biyota da babur din, hasken fitilar babur gami da hasken farin wata suka dauko masa Hauwa wacce tayi nisa akan hanyar tana gudu sanye da fararen kaya. Duk da ta fara gajiya, Kuma qafafuwanta sun farfashe suna jini, sbd tsinin itatuwa da take takawa a hanyar, wannan bai sa ta saurara ba, ta san idan har tayi sa'ar kaiwa bakin titi, nura bai kamata ba,ya komai zai wuce ya zama tarihi.
.
Nura ya ci gaba da bin Hauwa akan babur din, tana gudu tana kuka. Shi kuma yana qarawa babur din wuta. Basu dade ba a haka, ya cimmata ya tureta da tayar babur din ta gaba. Qafafuwanta suka harde ta fadi akan ciyayin dake a hanyar, a daidai lkcn ne tayi doguwar kururuwa har sai da tsaunin ya amsa kuwwar da razananniyar muryarta tayi. Tsuntsaye da kururuwa ta tsorata su suka fara nuna damuwarsu ta hanyar yin nasu kukan, da fuffuka, wadansu suka tashi daga bishiyoyin da suke 6oye, tare da jariran 'ya'yansu, suka canza makwanci.
.
Nura ya wuce Hauwa, wacce ta fadi qasa. Bai yi nisa ba ya juyo da fuskar babur din ya dawo inda ta fadin, fitilar babur din ya haske fuskar Hauwa, wacce tayi sharkaf da hawaye, nura ya murza babur din ya sake rinqaqowa ya nufota aguje, Hauwa ta tar6e fuskar ta a sakamakon hasken da ya kashe mata idanu. Kafin nura ya qariso inda take a xube a cikin ciyayin ne, ta tashi cikin sauri ta fada cikin gonar gyadar dake a kusa da ita. Ta fara gudu a cikin gonar tana tsallake kunyakai, a rude! Ba tare da ta san inda zata nufa ba a halin ynxn.
.
Nura ya san ba zai iya binta da babur din ba a halin ynx, tunda dai cikin gonar akwai kunyakai, don haka sai ya kashe babur din ya jefar dashi, ya sake tashi dauke da digar ya bita cikin gonar suka sake rufawa a qasa. Bai yi zaton Hauwa zata Bashi wahala baka ba. ya dauka tsoro zai hanata guduwa ya kasheta cikin sauqi ba tare da 6ata masa lkc ba." ya qosa ya kaasheta yayi sauri ya koma wajen gwala-gwalan, don kuwa sun yi nisa daga kan tsaunin, yana tsoron kada wani abu ya same su."
.
Hauwa ta rude ta riqa gudu Babu saurarawa. Nura yana bin ta, a haka har suka yi nisa, suka fita daga cikin gonar gyadar suka fada cikin wata gonar, sun yi ta wuce gonakin masara da na dauro, da kuma gonakin waken suya da dawa, nura ya kasa kamota, gashi sun yi nisa, shi kanshi ba zai iya gane inda suka dosa ba. Don kuwa ynx ba a kusa da titi suke ba, Kuma sun ba tsaunin baya tuntuni.
.
Shima nura ya gaji daqyar yake gudun, ga kuma nauyin qatuwar digar dake a hannunsa. Sun xo inda wani kangon daki yake ne, a wata tsohuwar rigar fulani da suka dade da tashi babu kowa a wajen. Sai wani firdeden kare ya taso ya fara haushi.
.
Mahaukacin kare ne, wanda ya zare tun wata uku da suka wuce, fulanin dake a yankin sun dade Suna neman karen don su harbeshi, tunda dai sun ga ya haukace sun san ynx Bashi da amfani, sai dai illa don kuwa yana iya cizon wani. Amma Kuma karen baya zama a kusa, sai dare yake dawowa kangon rigar yayi kwanciyarsa yana gurnani shi kadai, yana fada da itatuwa yana cizon qasa.
.
Kukan da Hauwa take yi tana gudu da Kuma sautin qafafuwansu da suke ratso shuke-shuke shi ne abin da ya tsorata mahaukacin karen ya taso a guje ya nufo inda ya ji motsinsu.
.
Lkcn da qaton karen ya fito yana haushi, Hauwa ta wuce, don haka sai suka yi arba shi da nura...ba zato ba tsammani. Mahaukacin karen yayi tsalle ya dirar masa, suka fadi qasa tare. Nura ya saki digar ba tare da ya sani ba, karen ya hayes kan ruwan cikinsa ya fara kokuwa dashi, yana kekketa masa riga da dogayen faratansa masu kaifi dA dafi.
.
Hauwa tayi nisa tana ta sheqa gudu ba tare da ta san abin da ya faru da nura ba a baya. Karen ya fara danna masa haqora, yana cizonshi. nura yayi ihu, ya fara yunqurin ture Mahaukacin karen. Amma Kuma karen yafi qarfinsa nesa ba kusa ba." kafin wani lkc karen ya 6ata masa jiki, yayi masa jina-jina a fuska da qirjinsa. Nura ya ci gaba da ihu yana neman wanda zai zo ya taimakeshi ya rabashi da Mahaukacin karen, kada ya hakashi a cikin dajin. To amma babu kowa, gashi Kuma Hauw tayi nisa, ba zata biyo sautin kukanshi ba, balle ta juyo ta ceceshi daga hannun mafadacin karen.
.
Haqoran karen suka riqa farka jikinsa kamar algarara. Jini yayi faca-faca a ko ina a jikin nura wanda ke ta qoqarin ture karen daga jikinsa, yana kuka a yayin da karen yake qara danna masa haqoransa yana farke jikinsa, tuni har ya cire masa fatar fuskarsa da farcensa, ya 6ata ko ina a jikin nura, wanda ya galabaita ya a kare kansa.
.
Sai da Mahaukacin karen ya kafa haqoranshi a wuyan nura, sannan azzalumin saurayin ya fara tunanin lkcn mutuwarsa ce ta zo. karen ya huda maqoshin saurayin, a daidai lkcn ne hankalin nura ya fita, ya fara kakarin mutuwa. Duk da haka bai mance da gwala-gwalan sa ba da ya barsu a saman tsaunin da ya biyo Hauwa zai kasheta.
.
Minti goma bayan haka karen ya tashi daga kan nura, wanda ya mutum idanuwansa a bude yana kallon Mahaukacin karen da ya canza mA kamanni. Da wahala mahaifiyarsa ta ga gawar ta gane gawar nura ce.
.
Karen yayi haushi na kusan minti uku, ya garzaya aguje ya koma makwancinsa.
.
.
Lp=22}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 23
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
Karen yayi haushi na kusan minti uku, ys garzaya aguje ya koma makwancinsa, kafin wani mai tsautsayin ya sake biyo hanyar ya tsorarta shi.
.
Wata shamuwa dake a kwance a saman wata bishiyar dorawa dake a kusa da gurin, ta gyara kwanciyarta bayan ta gama ganewa idanunta zaluncin da halittun duniya suke yi na ba gaira ba dalili, ita ma daxu nan wani maharbi ya zo dajin ya kashe mata mijinta da suka dade tare, tana kallon maharbin ya danne mijin nata ya darza masa wuqa ya yankashi, ya saka a jakarsa ta farauta. Wuni tayi tana kuka da hawaye kamar yadda mutane suke yi.
.
Ko ynx Akwai ragowar hawaye a idanunta. To amma Kuma ynx ba nura take wa kuka ba." mijinta take bege, wanda aka rabasu ta hanyar kisan cilla.
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi na bakwai
Da misalin qarfe tara na dare sadi qare-garke da yaronsa Shago suka kai bakin kogin dake a wasu qauyuka jefi-jefi wadanda rufin gidajensu na kwano ne dake haske daga nesa, musamman idan lullumi ya kauce haske ya bayyana.
.
Sun yi doguwar tafiya ta kusan away daya a qasa, Kuma a duk wannan lkcn basu tsaya sun huta ba, duk kuwa da wahalar da suke Shago na dakon mutanen da suke dauke dasu. Lkcn da suka zo bakin ruwan ne, sadi ya ce da Shago.
.
"gamu mun xo kogin, ynx sai batun samun kwale-kwalen da zamu shiga, mu tsallaka xuwa daya 6angaren,"
.
Shago wanda yafi sadi gajiya, ya sauke mai ankwa ya shimfidar dashi akan korayen ciyayi dake a malale a harabar kogin dake kama da filin qwallo.
.
Babu wani sautin dake tasowa a wajen, sai Kukan kwaduna manya da qanana, da kuma motsin kifaye wadanda suke ta wasa a cikin ruwa cikin annashuwa, tunda dai dare ne, duk masunta masu koma da fatsa sun koma makwancinsu, Babu wani hatsari a tare dasu.
.
Sadi ya ajiye Nalamma akan ciyayin, yayi

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment