Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaunawa fuskarsa a murtuke, yana matuqar jin yunwa, to amma baya son ya kashe kudinsa ya sayi abinci, ya san rabi tana nan xuwa, kuma indai ta xo shi take fara yiwa damu, da ta sauke zata kawo masa tasa furar rufe da faifai.
.
Ba a jima ba ya fara gyangyadi akan kujerar, hayaniyar mutane baya hanashi barci a kasuwa. In ya bushi iska sai ya wuni yana sharar barcinsa idan kwastomomi sun zo sai dai su shiga wani shagon, sbd a qa'ida idan Mu'azzam yana barci ba wanda zai tashe shi su kwashe lfy koda kuwa ciniki mutum yaxo zai yi masa a shagon.
.
Bai dade da fara gyangyadin ba ya ji ana ce masa.
.
"kai mai barci ka tashi, ba a barci a kasuwa."
.
Mu'azzam ya farka da sauri cikin fushi, har zai fara zagi kenan sai yaga rabi 'yar fulani a gabansa tana yi masa dariya. Mu'azzam ya mutsittsike idanunsa ya ce da ita.
.
"haba rabi! Sai yunwa ta kashe mutane sannan zaki xo kasuwar? Tun daxu ana ta jiranki shiru-shiru?"
.
Rabi ta dafa kantarsa da yake dora kalkuleta ta ce.
.
"yaushe zan zo da wuri hanya babu kyau duk an yi ruwa daqyar ma na samu babur din da ya kawo ni."
.
Ta mayar da hankalinta akan 'yan kunnaye da sarqoqin dake a cikin kwalaye katan-katan a shagon. Mu'azzam ya ce cikin qosawa.
."ina furar take? Jeki ki damo tun daxun ke nake ta jira ki zo."
.
Rabi tayi dariya
.
"fura...? Ai yau ban zo da fura ba Mu'azzam yadda ka ganni din nan haka nazo."
.
Mu'azzam ya hade fuskarshi ya tambayeta.
.
"kamar yaya baki zo da fura ba, me kika zo yi kasuwar to?"
.
Rabi ta ce dashi...?wannan
.
"yau amsar bashin da nake bi kawai nazo yi kasuwar, fara bani naka jiya muka yi lissafi dubu daya da dari biyu da talatin nake bin ka."
.
Mu'azzam ya dubeta a fusace.
.
"wa zai biya ki bashi baki damo masa fura ba? Ki bari sai ranar da kika zo da fura sai ki samu kudi, amma in ba rainin hankali ba, ki zo kasuwar ba fura mutane suna jin yunwa ki ce a yi maki biyan bashi? Sai ko zo ki qwata."
.
Rabi itama ta dan 6ata ranta, ta kai hannu inda kalkuletarsa take akan kantar, tana cewa.
.
"ai kai dama haka ka ke, baka son ka biya bashi, kuma kana da kudin ba baka dasu ba." biya ne kawai ba aka yi ba."
.
Mu'azzam ya fara tunanin korarta don ta tafi ta bashi wuri, ya ture hannunta ya ce.
.
"ya kike yi mani wasa da kalkuleta? Wannan fa sai ta sayi garken shanunku dukansu ba abar wasa ba ce."
.
Rabi ta harari Mu'azzam
.
"to ai sai ka raina mani wayo malam. An ce maka ban san abin lissafi bane? Ko a rugarmu akwai qanin baffanmu wanda yake da ita. Lallai ma wannan Mu'azzam din...."
.
Da rabi ta fahimci ya gaji da tsayuwarta tunda ba fura ta kawo masa ba,, sai ta ce dashi.
.
"abin da yasa kaga yau ban zo da fura ba, wasu duwatsu na tsinta yau a daji masu kyau mu'azzam. Irin wadanda ake hudasu ne anan yin tsakiya. Na san suna tsada a nan gari shi ne nazo maka dasu in zaka siya ka bani kudina in dauko maka, idan kuma ba zaka siya ba zan kaiwa wani, dama don kada kace na sayarwa wani ban fada maka ba shi yasa."
.
Mu'azzam ya dubeta sosai cikin mamaki, ya ga ba alamar wasa a fuskarta ya ce da ita.
.
"wadanne irin duwatsu ki ke nufi? Ban gane irin su ba rabi?"
.
Rabi ta ce dashi.
.
"bari in dauko qwaryata ka gansu, nima ban san sunan su ba." ganin su kawai nayi na kwashe su a tsaman tsauni."
.
Rabi ta fita daga shagon Mu'azzam ta je inda ta ajiye qwaryarta a kusa da wata bishiyar tsamiya. Ta dauko qwaryar mutanen dake a zazzaune a bakin shagunansu suka fara tambayarta ina kuma zata kai furar yau, ko ba zata sayar masu bane?"
.
Rabi ta ce dasu tana dariya.
.
"yau ba fura, qwan zabi na kawo da man shanu kuma na sayar dasu tun daxu."
.
Rabi ta dawo shagon Mu'azzam ta shiga kai tsaye, bayan ta cire takalminta a waje kamar yadda ta saba yi kullum. Ta sauke qwaryar a gaban Mu'azzam kafin ta bude ta ne yace da ita.
.
"kada fa ki zo mani da kayan surqulle cikin shago rabi, naji kina zancen duwatsu. Ana sayar da duwatsu ne a qauyenku?"
.
Rabi ta ce dashi.
.
"ai wadannan duwatsun na kwalliya ne, har kashe ido suke yi, bari dai kaga irin su."
.
Ta bude qwaryar ta cire faffadan faifan dake a sama. A lkcn ne kyawawan gwala-gwaln dake kama da duwatsu guda goma suka dauke idanun Mu'azzam , ya ji xuciyarsa ta buga da sauri.
.
Ya dade yana jin labarin gwal, amma bai ta6a ganin shi tsirararshi ba a fili, sai dai in an sarrafashi ya zama sarqa ko zobe ko 'yan kunnaye. Wadannan ba baqin idanunsa bane, ko ynx yana da su a shagon sa. To amma danyen gwal idan aka ginoshi a qarqashin qasa wannan sai dai ya ji labarinsu wajen mutanen duniya.
.
Mu'azzam ya sauka daga kan kujerar hannunsa yana kyarma, ya matso kusa da qwaryar nonon kamar zai bude baki ya hadiye ta duka. Rabi tana riqe da faifai a tsugunne tana kallon shi. Ya miqa hannu cikin qwaryar ya shafa abin da ya gani a ciki. Mu'azzam ya ji xufa ta fara keto mashi a goshi nan take. Ya tabbatar wadann gwala-gwalan dukiya ce mai yawa ta zo hannunshi. Kafin mu'azzam ya cire hannunsa daga cikin qwaryar tuni har ya fara lissafa kamfanonin da zai gina da kuma qasashen da zai je ya gina gidaje na alfarma, a dalilin wannan dukiya da rabi 'yar fulani ta kawo masa har shagonsa.
.

.
.
*** ***
.
.
Tafiyar minti arba'in sadi da tawagarsa suka yi a cikin motar kafin su kai tsaunin tudun kudi. Duk da mahaukacin gudun da Shago ke yi da motar, wani lkcn dale sai ya saurara, idan suka xoxoxoxo inda ruwa yake kwanciya akan hanyar. Hauwa tana a zaune tare da Shago a gaba tana nuna masa hanyar da zai bi, sadi yana tare da dan tsoho Nalamma a baya, su duka hudun kowa Akwai tunanin dake a xuciyarsa, babu wanda yake cewa kowa komai, in aka dauke Hauwa wacce ke ta nunawa Shago hanya da yatsanta.
.
Siririyar hanyar da ta hau har saman tsaunin ta yiwa motar kadan, don haka tun kafin su kai jikin tsaunin sai Shago ya tsayar da motar ya kasheta. Ya juyo inda Hauwa take ya tambayeta.
.
"wannan shi ne tsaunin da ku ka xo ku ka haqo gwala-gwalain?"
.
"eh, a wannan tsaunin ne, a can sama inda wata marmara take."
.
.
Lp=42}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 42
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Eh a wannan tsaunin ne, a can sama inda wata marmara take."
.
Sadi yayi saurin cewa.
.
"mene ne na tsayawa wahalar tambayarta Shago? Ba gamut tare da ita ba, ai ita zata kaimu wajen qafarta qafarmu."
.
Sadi yana gama fadar haka, ya bude qofar mota ya fito, bai damu da Nalamma ba wanda yake kashingide da kujerar motar kamar karyayyen dokin kara. Shago ya bude motar shima ya fito waje, ganin haka Hauwa itama tayi saurin bude qofar ta fito.
.
Rana ta fara dagowa a daidai lkcn ta fara zafi. Daga inda suke tsaye a kusa da tsaunin, suna iya hango manoman dake ta aiki a gonakinsu, wadansu suna furi a gonakin masara da dawa, a yayin da wadansu kuma suke duqe suna cire bagyazama a gonakin su na shinkafa.
.
Babu wanda ya mayar da hankalinsa akansu sadi. Don kuwa yawancin manoman dake aiki a gonakin kusa da tsaunin sun yi tsammanin malaman daji ne suka zo yin aikinsu da suka saba. Basu san cewar wadansu riqaqqun 6arayi bane suka zo neman wata gagarumar dukiya wacce aka 6oye shekara da shekaru akan tsaunin.
.
Hauwa ta shiga gaba, Shago da sadi suka bi ta a baya ta jagorancesu suka fara hawa kan tsaunin, daga nesa idan mutum ya hangosu kamar qananun yara zasu shiga daki. A haka har suka kai qololuwar tsaunin inda kututturen itatuwa suke, da Kuma qananun halittun dake kaiwa da komowa suna koke-koke a cikin ramuka da koguna.
.
Hauwa ta kai su inda ta tabbatar a nan suka tsaya ita da nura jiya, inda ya sa diga ya haqo gwala-gwalan. da xuwansu ta yi ajiyar xuciya a kidime da taga babu komai a bakin ramin, gwala-gwalan da nura ya gino ya barsu a wajen babu su babu dalilin su." wa ya zo ya kwashe su? Nura ne ya dawo ya debe su da ya bita ya kasa kama ta? Ko kuwa wani ne ya kwashe su a sanda nura ya bi ta zai kashe ta? Tambayar da Hauwa ta riqa jerowa kanta kenan da ta tsaya a wajen da nura ya gina ramin. Ta nunawa sadi wajen ta ce.
.
"kaga ramin da ya gino su, a nan muka tsaya jiya da daddare.
.
Sadi ya matsa jikin ramin ya durqusa a wajen yana zare idanuwa kamar wanda yake shakkar abin da yake gani ba gsky bane. Ya tambayi Hauwa cikin fushi.
.
"to ina gwala-gwalan suke? Kin ce a nan kuka barsu ke da saurayinki sanda ya bi ki zai kashe ki? Suna ina ynx?"
.
Hauwa ta ce dashi a kidime.
.
"nima ban sani ba, ni dai a nan muka barsu. Ban sani ba ko nura ne ya dawo ya kwashe su."
.
Sadi ya sa hannunsa biyu yana shafa bakin ramin. Shi kansa ya san babu gwala-gwalan, tabbas wani ya zo yayi gaba dasu, to amma duk da haka ya dan ji sanyi a ranshi a qalla hannunshi sun fara dafa inda gwala-gwalan suka ta6a zama a duniya.
.
Sadi ya tashi daga bakin ramin, ya dawo inda Hauwa take tsaye ya kalleta sosai. Hauwa ta dubeshi sau daya ta duqar da kanta, xuciyarta cike da fargaban abin da zai yi mata. Hauwa tayi zaton marinta zai yi sbd fushin rashin samun gwala-gwalan a wajen. har ta rufe idanunta ta sadaqar tana jiran ta ji fadowar hannu akan kuncinta. Maimakon haka sai ta ji sadi ya kwantar da muryarsa cikin rarrashi ya ce da ita.
.
"Hauwa ina so zan yi magana dake, ki kwantar da hankalinki magana zamuyi ta fahimta, ynx kin zama mataimakiyarmu, na qara maki matsayi tunda dai na fahimci ba yaudara ta kike son yi ba. Na san duk abubuwan da kika fada mani gsky ne. Daga ynx zan fara yin shawara dake ne maimakon tilastawa. Na daukeki aiki daga ynx, kome zaki yi zan biyaki ba kyauta zaki yi mani ba." idan har na cimma burina na samu wannan dukiyar, dake zamu yi kasafi zan baki naki kason, ina fatan zaki kwantar da hankalinki ki saki jikinki damu."
.
Hauwa tayi ajiyar xuciya. Ba albishir din sadi ne na kasafta dukiya da ita ya kwantar mata da hankali ba, 'yancin da ya fara bata ya dadada mata rai, ko ba komai dai ba zasu qara zaluntarta.
.
Sadi ya sake duban ramin da a ka haqo gwala-gwalan, ya qurawa kiyasan dake ta sintiri a wajen idanu, wadanda danshin qasar da aka gino da kuma hasken ranar dake sauka ya jawo su daga cikin qananun ramukansu, suka fito waje shan iska. Sadi ya ce da Hauwa.
.
"zai iya kasancewa saurayinki nura ya dawo ya kwashe gwala-gwalan, zai iya kasancewa kuma wani ne ya zo ya kwashe su ba nura ba. Amma kafin in yanke wannan hukuncin ina so in ji ra'ayinki Hauwa likita. Kina ga nura ne ya kwashe su, ko kuwa bayan tafiyarku ne a sanda ya biki zai kashe ki kafin ya dawo wani ya kwashe su?"
.
Hauwa ta rasa abin da zata ce da sadi qare-garke. ta fara dabircewa da taga ya bita da kallo yana jiran ya ji abinda zata ce. A qarshe sai ta tattara hankalinta waje guda ta yi masa magana.
.
"to zai iya zama nura ne ya dawo ya kwashe su." ni dai tunda ya bi ni da muka yi nisa ban san yadda akayi na gudu masa ba, na dai rasa inda ya nufa ne....! Ni kuma na ci gaba da gudu har nazo inda ku ke."
.
Sadi ya yi shiru yana juya maganarta a qwaqwalwarsa. A karo na farko ya fara jin wahalar wannan aiki da suke yi. Duk da a qa'idarsa baya yin shawara da Shago, a wannan karon sai ya kalli yaron nasa wanda yake tsaye yana jiran umarnin oganshi. Sadi ya ce dashi.
.
"Shago daga yadda aiki yake ta bamu wahala, ynx dole mu tattara hankalinmu akan nura, to amma bana so ne sai mun gama wahalar nemansa daga baya kuma ya kasance babu dukiyar a wajensa. Nafi so ynx duk inda muka sa gaba muyi nasara."
.
Shago ya ce dashi.
.
"oga to ya za'ayi yi ynx? Ina ya dace mu karkata akalar aiki?"
.
Sadi shi kanshi bashi da amsar wannan tambayar, don haka sai yayi shiru yana tunani. Ya matsa gaba kadan ya koma wajen ramin da nura ya haqo gwala-gwalan, ya tsaya a bakin ramin ya cci gaba da nazarin duk wani abu dake tattare da wajen, kama tun daga qwari da ciyayi da kuma sawun qafafuwan da suka zo suka samu.
.
Sadi yayi fito a hankali a sanda ya dubi sawun qafaffuwan mutanen da suka xo suka samu, a cikin nazarin da yayi na kimanin minti biyu, ya fahimci wani abu wanda ya fara yi masa caji a qwaqwalwarsa. A labarin da Hauwa ta basu ta ce ita da nura kawai suka zo wajen da daddare, to amma kuma indai abin da yake gani a halin ynx gsky ne, sawun mutane uku ya laqanta wadanda suke da zane daban-daban akan qasar dake harabar ramin da aka gino gwala-gwalan, babu shakka sawun mutane uku ya fahimta sun zo wajen.
.
Sawun qafafuwan mutum biyu sun yi zurga-zurgarsu ne a 6angaren yamma xuwa qasan tsaunin. A yayin da wani sawun kuma ya kasance daga 6angaren gabas xuwa qasan tsaunin, kuma a yadda sawun qafafuwan suka bayar da alamomin dukansu sun tsaya a bakin ramin sun yi wani abu a wajen.
.
Sadi ya tambayi Hauwa ba tare da juya baya ya dubeta ba."
.
"kin ce ku biyu kawai kuka zo nan jiya da daddare ke da nura. Kin tabbatar wani bai biyoku a baya ba, bayan kun taho?"
.
Hauwa ta ce dashi.
.
"gsky babu wani wanda yasan mun zo nan ni da nura. Don ko mama ban fadiwa inda zan je ba. Ba wanda ya biyo mu a baya."
.
Sadi ya numfasa cikin gamsuwa da abin da ta ce. Ya sake tambayarta yana kallon sawun qafafuwan.
.
"ta wanke 6angare kuka hawo nan? Kuma ta ina kuka sauka a sanda nura ya biki zai kashe ki?"
.
Hauwa ta ce dashi.
.
"ta nan 6angaren yamma muka hawo da zamu zo, kuma a sanda nura ya bini da gudu ta nan muka sauka."
.
Sadi ya juya a lkcn da ta nuna masa wajen da suka bi da hannu ya gani da idanunsa. Bata yi masa qarya ba, inda ta nuna masa nan ne yaga sawun qafar mutum biyu da suka banbanta da juna wanda ke nuna alamar sawun qafafuwan Hauwa ne wanda ya gangara ya nufi yamma xuwa qasa.
.
Ya dan yi murmushi kadan sannan ya ce.
.
"wannan sawun shi ne wanda ya zo daga baya. A nan sawun ya tsaya bai wuce gaba ba. Idan har abin da nake tsammani gsky ne, to ko wane ne yake da wannan sawun shi ne wanda ya kwashe wadannan gwala-gwalan ba nura bane,"
.
Shago da Hauwa suka kalli juna a karo na farko tun xuwansu wajen. Su duka biyun sun kadu da maganar da sadi ya fada.... Da yaga mmakin dake a fuskokinsu, sai ya dawo baya ya tsaya a inda suke ya ce dasu cikin qwarin guiwa.
.
"ku duba ku gani, ga sawun qafarki Hauwa, ga sawun qafar nura, ga inda kuka tsaya sanda kuka zo, ga inda kuka bi da kuka ganganara xuwa qasa sanda ya biki zai kashe ki."
.
Sadi qare-garke ya rriqa nuna masu da hannunsa. Hauwa da Shago suna kallo, kamar daliban da suke sauraren malami a wajenikin gwaji.
.
Amma wannan sawun qafarda yazo a nan ya tsaya a bakin wannan ramin, kuma a ddi nake tsammani ba a dade da xuwa ba, da safiyar nan aka zo aka kwashe gwala-gwalan idan ba haka ba, idan ba hakaba me zaisa da sawun ya zo ya tsaya a nan ya koma baa bai wuce gaba ba?"
.
Sadi ya ci gabaa murmushi jin dadi, ya kalli Shago sannan ya juya ya kal hauwa. Kodayaus yana soyaga yayi wani qoqari wanda kowa ya kasa yi.
.
.
Lp=43
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 44
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"bamu da man shanu a wannan rugar, muma sayo nono da mai muke yi a waje."
.
A sanda sadi yake magana hankalinsa na akan sawun qafar da ya biyo cikin rugar. Ya bi sawun da kallon ya ganshi da6a-da6a a ko'ina a tsakar gidan, wanda hakan ke nuna alamar kowanene ke da wannan sawun to a gidan yake zaune. Sadi ya lura da sawun qafar yafi yawa a kusa da wani daki dake a 6angaren kudu, a nan sawun yayi ta shige da fice, daga cikin dakin xuwa waje. Sadi ya tambayi Yaron, ba tare da shakkar mara lfyr dake a kwance yana saurarensu ba."
.
"ina mai wannan dakin yake?"
.
Yaron ya ce dashi.
.
"wannan dakin rabi ce, ta tafi tallar nono gari."
.
Sadi ya kalli mutumin dake kwance a rumfar ya ga ya rufe idonsa, ga alama maganar da yayi ta motsa ciwonsa dake kwankwaso, shi yasa ba a son ana xuwa ana damunsa. Ganin mara lfyr baya sauraren maganar da yake yi da yaron, ta kashi yake yi, sai ya saki jikin ya sake tambayar yaron.
.
"yaushe zata dawo?"
.
Yaron wanda a tsammanin sa sadi dan uwan rabi ne tunda dai yana jin fulatanci, bai 6oye masa komai ba ya ce dashi.
.
"sai da yamma take dawowa."
.
Sadi bai damu da dadewar da zata yi ba' a qalla dai ya gano wacce yake nema. Don ya qara tabbatarwa kanshi sai ya matsa kusa da yaron, yadda mutumin dake a kwance yana jinyar ba zai ji abin da ya fada ba." ya rage murya ya tambayi yaron, a lkc guda ya nuna daya daga cikin sawun qafar dake a ko'ina a cikin rugar.
.
"wannan sawun naga kamar na takalminta ne da ta sa daxu da safe ko?"
.
Yaron wanda bai san Mugun nufin dake a xuciyar sadi ba ya gyada kanshi ya ce.
.
"eh, takalmin rabi ne, ko da zata tafi kasuwa ma shi tasa."
.
Sadi yayi murmushin jin dadi, ya yiwa Yaron gdy, ya ce dashi zai je wata rugar ya nemo man shanu zai kai gida ne a yi masa dambu. Yaron ya nuna masa hanyar wata rugar ya ce a can zai samu man shanu suma a can suke xuwa su saya idan suna buqata.
.
Sadi ya juyo xuciyarsa cike da jin dadin gano wacce ta kwashe gwala-gwalan. bai sake waiwayar marar lfy dake a rugar ba yana jinya. Bai san cewar shine iro mijin rabi 'yar fulani ba, don kuwa bashi yazo nema ba."
.
Sadi ya koma inda Shago da Hauwa suke raku6e a kusa da rugar, tunda suka ga yana dariya shi kadai a hanya suka fahimci yayi nasarar gano abin da ya je nema. Da xuwanshi yace dasu yana fara'a.
.
"na gano wacce ta kwashe mani dukiyar da nake nema, wata matace da take a wannan rugar, amma ynx ta tafi gari tallar nono sai yamma zata dawo. Ku muje mu samu wuri mu zauna mu jira ta akan hanyar da zata dawo, ance sunanta rabi."
.
.
.
Babi na goma-sha biyu.
.
Rabi ta fara yiwa mu'azzam magana ya dawo hayyacinsa da tagar yayi zugum yana kallon abin da ta nuna masa a cikin qwaryar nononta.
.
"ya ka gansa mu'azzam? na fada maka suna da kyau, da irin su ake yin tsakiya da tatuna."
.
Mu'azzam yayi ajiyar xuciya ya numfasa ya ce da rabi 'yar fulani.
.
"na gansu rabi, rufe qwaryar da faifan, na gansu."
.
Ya cire hannunsa daga cikin qwaryar rabi ta rufe ta, mu'azzam yayi haka ne don kada tsautsayi ya jeho wani shagon, yaga abin da rabi take nuna masa ya kai labari. Mu'azzam ya tabbatar rabi bata san wadannan abubuwan da ta tsinta ko mene ba." da ace ta san darajarsu ba zata ta6a kwasosu tazo kasuwa dasu tana neman kai dasu ba. Mu'azzam duk da ya san darajarsu sai ya nemi rangwame ya nuna kamar baiwa san gwala-gwalan ne ba." ya ce da rabi.
.
"irin wadannan duwatsun an daina yayinsu tuntuni rabi. Dama mutanen qauye ne suke daurasu a zamanin da, to suma ynx sun waye sun watsar dasu. Ke ce baki ganin wadannan duwatsun gasu can a kudu ana takasu ba mai so?"
.
Rabi ta rage fara'a da taji abin da mu'azzam ya fada mata, ta sa ran zata samu ko dubu biyar ne don ta dan sayi atamfa guda biyu a kasuwa, to amma wannan maganar da mu'azzam ya fada ynx, ta san cewar dolene farashin da take so ya karye, mu'azzam ba zai sayesu da daraja ba, ta ce dashi.
.
"ai kai dama akwai son banza, in basu yi maka ba in kai wa wani in nuna masa, in baka so wani yana so."
.
Mu'azzam ya ce da ita.
.
"to ai kece naji kina ta faman yi masu kirari kamar wasu kayan gabas, ni ko sayensu nayi a gida zan ajiye su maganin tambaya. Qila a samu wanda zaice yana so wata rana. Amma ynx wake son wadannan abubuwan?"
.
Rabi ta ce cikin qosawa.
.
"to ni dai ynx fadi abin da zaka saya in ji idan yayi mani in sayar."
.
Mu'azzam ya gyara zama akan kujerarsa ya ce.
.
"to bari in baki dari uku rabi. Don ma ke ce, ama da wani ne ya zo dasu daga fan dari ko taro ba zan qara ba."
.
Rabi ta turo baki gaba, sannan tayi tsaki da ta ji irin tayin wulaqancin da mu'azzam ya yi mata. Da yaga alamar tana shirin daukar qwaryar ta fice daga shagon nasa, sai yayi saurin tsayar da ita don kada yayi wa kansa sagegeduwa' ya gyara cinikinsa ya ce da ita.
.
"to ynx dai duk a ture zancen wasa rabi, zan baki dubu daya, na fada maki nima ajiyesu zan yi sai an samu wanda yake so." ajiyar kudi zanyi ba ynx-ynx za a samu mai sayesu ba."
.
Da rabi ta ji ya dan fara kama hanyar gsky ne a cikin cinikin nasu sai ta ce dashi.
.
"gsky albarka. Indai kana sonsu sai ka bani dubu uku, na cire maka dubu biyu in basu yi maka ba in tafi in kaiwa wani ya saya."
.
Mu'azzam ya fahimci da gaske take yi, yayi saurin cewa da ita bakinsa na rawa.
.
"naji na saya a hakan, amma kin san yau ba ciniki, ba kudin zan baki ba, sai kin dawo gobe sai in ga abin da zaki samu."
.
Rabi ta ji ba zata shiga kasuwa ta sayi atamfa ba, sai ta hade rai ta ce da mu'azzam.
.
"ba zan iya ba, in kana so ka dire mani kudina ynx, yaushe zan biyoka kudi muyi ta kai ruwa rana kai da baka son ka biya mutane bashi."
.
Mu'azzam ya bude dirowar da yake xuba kudi a qalla za a samu dubu biyu da dari hudu a ciki, ya jawo dubu daya a fusace ya mayar da dirowar ya miqawa rabi ya ce a cikin qorafi.
.
"amshi, ga dubu daya zan cika maki sauran, ke baki da yarda, ana tare dake kullum amma kamar baki ta6a ganin mutane ba."
.
Da rabi taga qyallin dubu daya ne sai ta dan ji sanyi a ranta.
.
.
Lp=45}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 45
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
Bata amince da daukar shafin ba."
.
Da rabi ta ga qyallin dubu daya ne ta dan ji sanyi a ranta ta sa hannu ta fizgeta ta ce.
.
"zan yi saye-saye a kasuwa yau mu'azzam, don allah ka qaro mani dubu daya, idan nazo goben sai ka cika min sauran,"
.
Mu'azzam ya kai hannu .zai ture faifan dake lulli6e da qwaryar ya kwashe gwala-gwalan ya ce.
.
"ko fuccika ba zan qara maki ba, ai Wataqila guduwa zan yi in bar garin sbd kina bina dubu daya."
.
Rabi ta bi shi da kallo a

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

4 months ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment