Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanda yasa hannuwansa bbiyu ya fara kwaso ma'adanan yana xubasu a cikin dirowar da yake tara kudi, wacce ya dan bude ta kadan ya jawo ta don kada rabi ta yi sa'ar hango abin dake ciki. A haka har ya gama kwashe su daga cikin qwaryar rabi tana zaune sororo, ita kanta duk da bata san darajar wadannan abubuwan ba da ta sayar masa, wani abu yana raya mata a xuciyarta cewar mu'azzam ya cuceta. Ta ce dashi cikin karaya.
.
"ai kai dai Wlh halinka sai dai allah ya sauwaqe, ga ka da kudi kamar su kasheka amma sai bala'in maqo."
.
Duk da mu'azzam ya fara gajiya da ganin ta a shagon, sai da ya yi dariya da ya ji abin da ta ce.
.
"rabi kenan."
.
Ya ce da ita.
.
"wa ya fada maki cewar kudi suna kashe mutum? Ai su kudi rayawa suke yi, basu kashewa. Rashinsu yake kawo mutuwa, rashin kudi yake sa mutum ki ga ya tsufa tun kafin lkcn tsufan ya yi, ynx kin ga a yadda kike yarinyar nan sharaf dake ga ki kyakkyawa, da ace mijinki yana da kudi nan da shekara sittin a haka zaki tsaya, ba zaki taba sukurkucewa ba, ba ki da kudi ynx shi yasa da zaki duba madubi nan da shekara goma zaki yi mamakin tsufan da zaki yi, zaki ga kin yi esfaya, kin tashi aiki."
.
Da yake itama rabi 'yar fulani tana da irin wannan falyafin a xuciyarta, sai maganar ta burgeta tayi dariya itama ta ce da mu'azzam
.
"to a haka zaku bar mutum yayi kudin? Kullum ana dama maku fura baku son ku biya mutum kudinsa?"
.
Mu'azzam ya ce da ita
.
"ba ki san sirrin kudi ba rabi. Idan kaga ana bin mutum kudi a duniyar nan to shine mai arziqi. talaka shi yake tsoron ace ana binsa kudi. In kina sauraren rediyo zaki ji irin maqudan bashin da ake bin manyan qasashen duniyar nan.... Sun fi kowa kudi a duniya, amma an fi binsu bashi fiye da kowa. To haka muma a cikin mutane zaki gani, yanayin girman mutum yanayin bashin da ake binshi. Wani a ynx haka ana binshi kudi sun kai million dari. Kuma bai ta6a kwana bai yi barci ya more ba, amma ke yau da za ace ana binki bashin milyan daya Wataqila ke da sake cin abinci har abada sbd xullumi."
.
Rabi ta dafe qirjinta a tsorace ta ce da mu'azzam.
.
"milyan? tafdijan, ai ni kwarankwatsa ko dubu guda aka biyoni bashi bana iya barci, sai na biya nake jin dadi a raina."
.
Mu'azzam ya kwashe da dariya, ba halinsa bane yin raha, amma ga al'adarsa duk sanda yayi wata gagarumar cuta ya more, dolene ya ji nishadi a ga dariyarsa. In ban da yaga irin zaluncin da ya yi wa rabi 'yar fulani, da bata isa ta shigo masa har cikin shago ta rashe, ta dade haka suna xuba surutu ba. Itama ba zata ga wannan fuskar ba a wajensa.
.
Rabi ta dauki qwaryarta ta ce da mu'azzam
.
"ka ji ba biye maka zan yi ba, gara kai kana nan, ni ko komin dare sai na gane hanyar garinmu."
.
Ta fito daga cikin shagon ba tare da mu'azzam ya sake cewa uffan ba. Da ya tabbatar ta shiga cikin kasuwa ta bar layin, sai ya sake jawo dirowar teburinsa, ya sake dora idanunsa akan wadann ma'adanai masu daraja. Mu'azzam ya san cewar wannan dukiya ce mai yawa, kuma koma daga ina ta fito, mutanen da suka haqota basu san ko mece ba, kamar yadda rabi 'yar fulani itama ta tsincesu ccikin rash sani ta zo ta same shi dasu.
.
Mu'azzam ya san ba qaramin hadari bane idan aka zo aka sameshi tare da wadann dukiya, ko ba a gano wanda yake dasu ba indai an san suna wajensa, 6arayi wadanda suka fishi hadama zasu iya kawo masa farmaki, sannan Kuma Jami'an tsaro ma ba za'a barsu a baya ba, dolene su qwace su ce ba nashi bane. Ba kuma don zasu mayarwa da mai su din ba.
.
A cikin wani tunani na hanzari da mu'azzam ya yi na minti daya, ya gano cewar hanyar farko da zai fara bi wajen mallakar wadann gwala-gwalai, bai wuce ya je ya 6oye su a wani ke6antaccen wuri na sirri ba, inda babu wani mutum da tunaninsa zai kai wajen har abada. Idan yayi masu mugun 6oyo, to duk sauran abubuwan da zai yi daga baya masu sauqi ne....! Ko'ina zai je ya nemo manyan dillalan gwala-gwalai, ko qasar waje zai je, hankalinsa a kwance yake, ya san zai dawo ya samesu a inda ya 6oye su komin dadewar da yayi a can.
.
Mu'azzam ya yanke shawarar tashi ya koma gida, abinda ya tasa a rayuwarsa a ynx yafi wannan shagon muhimmanci nesa ba kusa ba. Ya dauko wata baqar leda ya warwareta, ya ajiyeta a qasa, ya kaqaici idanun mutanen dake wucewa ta gaban shagon nasa, ya fara ciro gwala-gwalan daga cikin dirowar yana xubasu a cikin ledar.
.
Bayan ya gama xubasu ne, sai ya daure bakin ledar ya sake dauko wata ya saka wacce ya daure a ciki, ya tattara kudin dake a shagon, cinikin da yayi na wannan satin, ya cusasu a cikin aljihunsa, mu'azzam ya dauki ledar gwala-gwalai ya fito waje ya jawo qofofin shagon biyu ya rufesu, ya sa qaton kwadon da ake datse qofofin ya zare mabudansa, suma ya sa su a cikin aljihu.
.
Mu'azzam ya dauki baqar ledar ba tare da yayi wa kowa magana ba a cikin maqwabtansa yayi tafiyarsa yana cin daci da rai kamar an aiko masa da sammaci. wa zai tsayar dashi ya tambayeshi dalilin da yasa ya rufe shagonsa ya tafi gida da rana tsaka? Ba wanda yake irin wannan maganar da mu'azzam a duk fadin kasuwar. Don haka ba wanda ya tambayeshi dalilin tashinsa a ynxn. Ballantana ma har wani ya zargi abin da yake faruwa.
.
Mu'azzam ya je ya dauki motarsa a filin da suke yin fakin a kasuwar ya tuqa aguje kamar zai tashi sama ya nufi gida. Shudiyar motar tasa qirar (camry) tana ta wuce ababen hawa akan titin, bai saurara ba sai da yazo unguwarsu, ya sauka daga kan babban titin ya karya kwana ya shiga layin su.
.
Gidan alh madugu sananne ne, kamar yadda sunan hamshaqin mutumin ya kasance sananne. farin bene ne hawa biyu wanda ya mori tagogi da qofofin gilas baqaqe, tun daga nesa abin da mutum zai fara hangowa kenan a gidan ya burgeshi.
.
Doguwar katangar dake zagaye da babban gidan, itama an qawata ta da aikin hannu tun zamanin da aka ginata a kusan kodayaushe qofar shiga gidan a bude take, in ba da daddare ba, da wahala a samu qofar a bude.
.
Hakan ya samo asaline a dalilin rashin haqurin alh. Madugu, idan ya dawo ya samu qopar a rufe yana ganin jinkirin tsayawa yayi ta hon ba a zo an bude masa ba, shi yasa ake barin qopar a bude, tunda ba a san sanda zai dawo ba." dalili na biyu kuma shine, gidan baya yankewa da mutane musamman Idan aka ce lkcn siyasa ya zo. Alh. Madugu ya kan wuni a gida, matasan jam'iyya da 'yan jagaliya suyi ta shigowa suna fita.
.
Mu'azzam ya qariso gidan, ya wuce ta gaban wani mahauci dake gasa naman rago akan kwanar da tayi iyaka da katangar gidan alh. Madugu. Mahaucin ya dagowa mu'azzam hannu, shi kuma yayi masa hon sau daya. Duk da fadin ran mu'azzam, suna matuqar dasawa shi da idi mai naman rago. Sau da yawa idan mu'azzam yazo da matansa na bariki da daddare, idi mahauci ke da alhakin gasa nama mai kyau ya kawo masa. Da yake kuma kasuwancin dake tsakaninsu ya shafi hulda ne da qadangarun bariki, inda mu'azzam baya ganin asarar ya kashe ko nawa ne....! Nan take mu'azzam ya kan duntso dubu biyar ya damqawa idi idan ya kawo masa naman har cikin daki cikin ladabi. Mu'azzam yana jin dadin hakan ko don ya dda ake fasa masa kai a gaban baquwarsa. Wacce ita kuma take yiwa mahaucin kallon wulaqnci sb ganin saurayinta yana da kudi, kuma dan birni ne.
.
A wannan daren dai idi mai naman rago ya san bashi da rabo a wujen mu'azzam, amma dai ya san idan dare yayi to za'ayi baqi. to amma da ace idi ya san abin dake faruwa da mu'azzam a halin ynxn' da bai sake sa ran samun wani ciniki daga mu ba, domin kuwa a yadda mu'azzam ya dawo gida tare da wannan gagarumar dukiya da ya samu kamar tsintuwa, yana burin in har sa' a ta hadu ya samu tsallakewa da wannan dukiyar, to ya gama kaiwa a qololuwar arziqi, me zai zauna yana yi a garin yana cin gasasshen naman ragon da ake gasawa akan layi? Sai dai naman dawisu na gwangwani a otal-otal din dake a qasashen duniya.
.
Cikin sauri yayi fakin bayan ya shiga harabar da suke ajiye motoci hudu.
.
.
Lp=46}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 46
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Cikin sauri yayi fakin bayan ya shiga harabar da suke ajiye motoci hudu dake a gidan. mu'azzam ya samu ragowar mota daya qaramar (KIA) mai ruwan toka, ita ce motar haj. Maimuna matar alh. Madugu. Rashin ganin baqar (Jeep) da farar (Civic) a harabar katafaren gidan yasa mu'azzam ya fahimci Alhaji da Larai basu a gidan, ddukkansu sun fita. Ya san a halin ynx alh. Madugu yana can a wajen hada-hadarsa ta siyasa wacce bata qarewa Kullum, ita kuma larai wacce basa jituwa shi da ita a gidan. wa ya san inda ta je? Ba dai alhaji ya bata lasisin yin abin da take so ba?" da gama karatunta na sakandire kwana-kwanan nan ya wani sai mata sabuwar mota tana dagawa mutane kai, ita ga 'yar mai kudi. Mu'azzam yayi tsaki da ya tuno irin adawar dake tsakanin sa da budurwa larai 'yar yayarsa. Yana jin haushin yadda itama ynx ta fara kawo qarfi, alhaji ya fara kashe mata kudi, itama larai a nata 6angaren tana jin haushin yadda mahaifinta alh. Madugu yake kashewa mu'azzam kudi, ta san qanin mahaifiyarta ne, to amma ba ruwanta dashi tunda ta san ba mutumin arziqi bane.
.
Mu'azzam ya fito daga cikin motar, hannunsa na dama ruqunqume da ledar da ya xubo gwala-gwalai kamar yana zaton wani abu zai fado ya qwace masa su ya tashi sama. A haka ya shiga cikin gidan da sauri. A 6angaren tsakiya mu'azzam yake. alh. Madugu da iyalinsa sune a can sama hawa na biyu, gidan qasa Kuma yawancci a nan mutane suke taruwa idan maganar siyasa ta taso.
.
Mu'azzam ya je inda qofar falon sa take bayan ya hau hawa na biyu, ya ciro mabudi ya bude qofar ya shiga, da shigarsa ya rufe qofar ta ciki don kada ma wani ya leqo cikin dakin ya ga abin da ya shigo dashi.
.
Ya kunna wuta, qwayaye biyu dake cikin falon suka haske ko'ina. Abubuwan da mu'azzam yake dasu a falon sa da dakin kwanansa dake ciki, wanda Kodayaushe yake lulli6e da labule, ba wasu baqin kayayyaki bane wadanda ido bai saba ganin su ba." qaton talabijin dinsa ke fara yiwa mutum sallama, wanda yake jone da qaramar na'urar tauraron dan adam qirar (Strong'). a qasan falon da can cikin dakin tattausar dadduma ce kalar ciyawa. Sai manyan kujeru saiti daya da aka shiryasu a falon, an bar hanyar wucewa daga jikin bango, sai kuma hotunan bango na cikin katako da gilasai barkatai a kowanne 6angare na dakin, wadanda suka hada da hotunan 'yanmatan mu'azzam na da da na ynx' yawancinsu ya dade da 6atawa dasu, yana dai kwalliya da hotunan ne kawai a dakinsa yana tuna baya.
.
Sai kuma hotunan qadangarun 'yanmata da samarin mawaqan turanci wadanda suke alfahari da tsaraicinsu a idon duniya. Da kuma hotunan tsuntsaye da na motoci kala-kala. A saman falon akwai fanka mai ruwan zuma wacce kodayaushe take a kunne tana cinye gudu komin sanyi komin zafi.
.
Mu'azzam ya tsaya a cikin falon yana waige-waigen inda zai 6oye wadann gwala-gwalai, ya fi so yayi sauri ya 6oye wadann gwala-gwalai, don kuwa so yake yi adana su tukuna' daga baya koma zai yi sai ya yi? A qalla dai ya 6oyesu. Ko'ina ya duba a cikin dakin bai ga inda hankalinsa yafi kwanciya inda zai 6oyesu ba wani xullumi. Ba zai yiwu ya daga tuntun kujera ya saka su a ciki ba, sbd abokansa da 'yanmatansa suna shigowa dakin, wani yana iya zama akai ya ji tudunsu ya bincciki ko akan me ya zauna, ya cire tuntun ya ga gwala-gwalan.
.
Mu'azzam yayi saurin shiga dakinsa na barci inda ya ajiye turqeqiyar katifa ita kadai kawai a qasa, sai matasan kai guda uku. A gefe guda kuma a jingine da bango, lokarsa ce mai murfi biyu wacce yake xuba kayan sawarsa da takalmansa a ciki.
.
A nan din ma bai ga wani sahihin wuri na ajiya ba, yana iya xubasu a cikin lokar, wani ya shigo ya yi masa bincike, kwanakin baya sun xo dakin tare da wani abokinsa, mu'azzam ya shiga wanka kenan sai abokin nasa ya bude lokar ya daukar masa wata sabuwar (T-shirt) ya tura ta a aljihunsa ya tafi da ita. Ba wani wurin sirri inda 'yanmatansa da abokansa basu kai hannunsu. Akwai matsala babba ya yi irin wannan ajiya a cikin dakin.
.
To amma kuma ina zai kai su? Mu'azzam ya tambayi kansa cikin damuwa shi kadai a tsaye a cikin dakin, faffadar fuskarsa a halin ynx nashe take da xufa, kamar gurasa a tukuba. Ba dai zai yiwu ya kaisu wani wuri ba, dole a nan zai 6oyesu a dakinsa. In ba dakinsa ba kuwa to sai dai dakin yayarsa haj. Maimuna. To amma a nan din ma ita bata yi bincike ta gano ko mene ne ba, larai ce abin tsoro. Bata da shamaki a dakin mahaifiyarta, ko'ina ta samu sai ta kai hannunta, mu'azzam bai yarda da larai ba. Yayi saurin cire wannan tunanin daga xuciyarsa. Ba zai yiwu ba ya kai gwala-gwalan dakin yayarsa. Ya dawo da hankalinsa kan dakinsa ya ci gaba da tunanin inda zai 6oyesu.
.
Ba a jima ba ya gano cewar indai a dakinsa zai 6oyesu, to ba inda yafi cancanta sai dai ya fasa bango ya xxubasu a ciki ya mayar ya rufe da siminti, duk duniyar nan wane mahaluqi ne zai xo dakin yaga inda suke, indai ba duba mutum zai sa malamai suyi masa ba?" ba yadda za'ayi a gano inda suke matuqar suna cikin ginin.
.
Wannan saqon tunanine da mu'azzam ya yi shi faranta xuciyarsa, ya dawo ya saki fuskarsa ta rage muni. Bai tsaya 6ata lkc ba, ya ajiye ledar gwala-gwalan, ya fito ya sake bude qopa, don ya je ya dauko kayan aiki. A can qasa inda hanyar ruwa take daga bayan gidan. Akwai wani aiki da mu'azzam yaga alhaji ya sa ana yi. Ko jiya sai da wani burkila yazo da yaransa suka hada siminti suka yi aiki, kuma a nan suke barin kayayyakin aikin nasu kafin su sake dawowa.
.
Mu'azzam ya sauko qasa a gurguje yau ko nauyin jikinsa ba ya ji. Ya zagaya baya inda aka xuba yashi da suminti buhu uku a gefe guda, da kwangiri da wuqar filista, masu aikin basu xo ba yau, kodayake dama suna tsallaken kwana daya dukan sanda suka zo sai aikin da suka yi ya sha iska, sannan suke sake dawowa suyi wani.
.
Da xuwan mu'azzam bai tsaya jiran komai ba, ya dauki wuqar filistar, ya farke buhu daya ya debo sumuntin ya zuba a kwangirin. Ya sake duba harabar wurin ya samu qaramin maginin da masu aikin sukw qwaqula qasa dashi suna fitar da hanyar ruwan.
.
Mu'azzam ya kwashi kayayyakin a cikin kwangiri, ya koma cikin gidan da sauri, da xuwanshi dakinsa ya fara tunanin inda zai fasa a jikin bango. Baya so ya 6ata dakin kwanansa, don haka sai ya yanke shawarar ya fasa daya daga cikin bangwaye hudu na falon.
.
Ya ajiye kwangirin ya dauki maginin ya fara nazarin ko'ina a cikin falon, a qarshe sai hankalinsa ya tsaya ga bangon shiga dakin barcinsa. Babu wani abu a jikin bangon, sai faskeken hoton wata baturiya, wacce ta dafa kwankwasonta tana dariya. Hoton ya tsare haraba mai yawa a cikin bangon. Daga gefe kuma wani farin katako ne da aka kafw shi a goshin qofar, don ajiye 'yan qananun abubuwan da za'a iya nemansu cikin gaggawa a kowanne lkc.
.
Mu'azzam ya sa hannu ya cire hoton baturiyar wanda ke a cikin gilashi, ya ajiyeshi a gefe guda. Ya shata inda yake so ya fasa, sannan ya fara dukan bangon da magginin. Ba kowa zai ji sautin fasa bangon ba, kowa a gidan sai haj. Maimuna dake sama, koda ta ji dukan bangon zata dauka masu aiki ne suka zo. Mu'azzam ya fara fasa bangon, a qwararan sakwan shida da yayi, simunti da 6aragusan bulo suka fara yankowa suna fadowa qasa, ya 6ata daddumar falon da qura cikin qanqanin lkc.
.
Mu'azzam ya sake fadada ramin da yayi a bangon. Da ya tabbatar yayi fadin zai iya saka ledar a ciki sai ya saurara da fasa bangon haka nan, ya ja baya ya kalli inda ya qirqira a bangon daga qasan katakon, wajen da ya fasa ba qaramin cikasa ya kawowa bangon falon ba." to amma wannan bai 6atawa Mu'azzam rai ba, ynx shi ba bangon yafi damunsa ba, babu sauran wani abu da yake bugeshi a cikin dakin tun sanda ya samu wannan gagarumar dukiya, wacce ya tabbatar in har ta zama tsabar kudi a wani da lkc mai xuwa, to zata iya gina masa manyan gidajen alfarma bila-adadin fiye da wannan gidan na alh. Madugu sbd haka fasa bangon ba wani abu bane, bari dai ya 6oye dukiyar ta zama kudi.
.
.
Lp=47}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 47
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba
.
Sbd haka fasa bango ba wani abu bane, bari dai ya 6oye dukiyar ta zama kudi.
.
Mu'azzam ya shiga dakin kwanansa ya dauko baqar ledar da ya zuba gwala-gwalan a ciki, da dawowarsa cikin falon ya tsaya a gaban ramin da ya gina a bangon ya nannade ledar ya hade gwala-gwalan a waje daya, ya cusa su a cikin bangon, rabi ya shiga, rabinsu kuma ya tokare bai shiga ba." Mu'azzam ya sa qarfinsa ya tura su, suka fada ciki bayan wani 6ungari ya sake fadowa qasa na bulon da ya fasa.
.
Baqar ledar ta tsaya a ciki, kamar dama can nan ne muhallinta, Mu'azzam ya sa hannu cikin ramin ya gyara zaman gwala-gwalan yadda ba zasu yi doro a bangon ba, idan ya mayar da siminti ya shafe. Bayan ya saka su a ciki ne sai ya debo ruwa ya kwa6a siminti da yashi ya sa askar filistar ya fara dibar kwa6a66en simintin yana toshe ramin da ya gina. A haka sannu a hankali yana sa hannu yana gyara zaman simintin a cikin minti ashirin da biyar ya toshe ramin ya tayar da 6annar da ya yi.
.
Bayan ya gama yiwa bangon garambawul ne, sai ya dauko faskeken hoton baturiyar, ya cire qaramar qusar dake saman ramin da ya gina, ya matso da ita daidai inda hoton zai rufe ko'ina na filistar da ya yi, ya kafa hoton a wajen, ya sagale hoton wanda ya 6oye ramin da harabarsa. Mu'azzam ya ja baya ya kalli wajen, yayi murmushin jin dadi, da yaga babu wata alama da ta fito waje ta yadda za a gani a fahimci wani abu ya faru a jikin bangon har abada.
.
Mu'azzam ya kwashe kayayyakin da yayi amfani dasu, ya fita ya mayar dasu inda ya daukosu, ya dawo dakinsa ya dauko tsintsiya ya share 6aragusan simintin da ya xuba a qasa, ya fita dashi waje ya zubar, ya tsaftace dakin ya koma yadda yake da farko, kamar bai yi aikin komai ba a ciki.
.
A qarshe Mu'azzam ya yanke shawarar barin garin, sbd a yadda wannan lamari ya faru tsakanin sa da rabi 'yar fulani, Wataqila wani abu daga baya ya-ka-iya xuwa ya dawo a nemeshi. Ba zai dawo garin ba sai ya tabbatar ba abin da ya faru, sannan sai ya nemo wanda zai sayi gwala-gwalan hankalinsa a kwance. Amma ynx ba zai iya sakin jikinsa ba, ya san da wahala idan ba a dawo da baqo ya sha qwai ba." don haka barin garin zai yi, koma me zai faru dai shi baya nan, kuma in za a yi binciken duniyar nan babu wanda ya isa ya gano inda ya 6oye wadann gwala-gwalai, wata rana idan aka mance zai zo ya kwashe abinsa ya tafi dasu inda ya ke so.
.
Mu'azzam yayi wanka ya fito da sauri ya dauko jakarsa ya zuba kayan da ya ke buqata a ciki, ya tattara duk kudin da yake dasu na cinikin da ya yi, ya zubasu a aljihu ya fito daga dakin riqe da jakarsa ta bulaguro. Mu'azzam ya kulle dakin, ya hau sama inda haj. Maimuna take, da shigarsa babban falon dake tsakiyar gidan nasu, ya sameta ta shigo tana waya, a yadda ya ji irin maganar da take yi ne, ya fahimci da 'yarta larai take waya, Mu'azzam ya katse mata wayar ba tare da ya jira ta ba, ya ce da ita cikin sauri.
.
"haj. Zan yi tafiya sai na dawo."
.
Haj. Maimuna tayi saurin katse maganar da take yi a wayar, ta dawo da hankalinta akan qaninta.
.
"ina kuma zaka je Mu'azzam?"
.
Ta tambayeshi cikin mamaki da rashin amincewa, faffadar fuskarta wacce ke kama da fuskar qanin nata ta daskare babu alamar fara'a. Mu'azzam ya duba agogon dake a hannunsa ya ce.
.
"zan je kudu ne yayata, ba zan dade ba kwana biyu kawai zan yi a can."
.
Haj. Maimuna tace dashi.
.
"sai ka jira alhaji ya dawo ka fada masa da kanka. Haka kake irin wannan tafiyar ka sa qafa ka bar gidan nan, bai sani ba ya dawo ya hau ni da masifa, ya ce ni nake daure maka gindi.....
.
.
.
Lp=48}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 48
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Wannan shafin kacokan sadaukarwa ne ga Dan uwa kuma aminina Sadeeq Shehu Shareef tare da masoyiyarsa Nafeesat. Allah ya kaimu ranar bikin su cikin qoshin lfy.
.
Haka kake irin wannan tafiyar, ka sa qafa ka fita ka bar gidan nan bai sani ba, ya dawo ya hauni da masifa ya ce ni nake daure maka gindi kake abin da kake so a gidan nan. To ba zan dauka ba, ka jira shi ya dawo in shi ya ce ya amince ka tafi duk inda ka ke so sai ka tafi, amma ni ba ruwana."
.
Irin wannan sa'insarar ta sha faruwa a tsakanin Mu'azzam da yayarsa haj. Maimuna. Ta san ba jin maganarta yake yi ba, amma Kuma sbd qarfin hali irin na dan'adam, Kullum tana iya qoqarin ta na fadan gaskiya, duk da yake bai ta6a dauka ba." Mu'azzam ya yi dariya ya ce.
.
"ba zan dade ba, in ya dawo ki fada masa kwana biyu kawai zan yi, nima ban tashi da tafiyar ba, ynx ya taso mani cikin gaggawa
.
Haj. Maimuna ta ce dashi.
.
"tunda baka jin maganata ya zan yi da kai' haka dai kake so ka riqa ganina Kullum cikin 6acin rai ko Mu'azzam? ka je kayi abin da kaga yafi maka tunda ni ban isa in ce ga abin da bana so ka bari ba."
.
Mu'azzam ya juya ya yi tafiyarsa yana dariyar da ya saba ta shaqiyanci, idan ana yi masa fada. Ya fice daga gidan ya bar haj. Maimuna tana ta banbaminta ita kadai a falon tsawon lkc. A sannan tuni Mu'azzam ya yi nisa a tafiyarsa, ya kama hanyar legas yana gudu ba ji ba gani. Ba zai dawo ba sai ya ji kome zai faru, Mu'azzam ya sake yin dariya shi kadai a cikin motar, da ya tuno cewar a halin ynx gwala-gwalansa suna can a 6oye a cikin bango, ba wanda zai gano inda suke har abada.
.
.
.
*** *** ***
.
.
Babi na sha-uku.
.
Tun sanda Kwamishinan 'yan sanda ya gama ganawa da manyan Jami'an tsaronsa hudu dake a shiyyoyin tsaro na jiha, da tafiyarsu A.c Tanko

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment