Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BoY7L6yHuks8F59z1U4UWd


_YIWA KAI...!_


_Free Novel_

Jumma'ath Mubarak

*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha me sunanki.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 1&2*


_Jigawa dutse._
Yanayi ne na lokacin zafi, yau juma'a an tashi da wani irin zafi sosai, ga rana ga shi ba lokacin damuna ba, bare asaka ran saukan ruwan sama ko za'aji sassaucin zafin.
Hakan yasa sosai jama'a dayawa suke mita akan zafin, ga qaran cin wutar nefa bare wad'anda suke da fanka agidan su su kunna ko sa samu sassauci.
Wasu kuma sun fawwalawa ALLAH ikon sa, basa mita sabida suma abinda suka ga dama suke bare kuma Rabbil samawati.
Amman masu akwai wad'anda sukaci suka tayar da kai, gida A.c mota A.c office A.c basusan anayi ba, sai sun fito.

*Bayan sallar juma'a*

_Central mosque_
Duk inda ka kalla jeran gwanon motoci ne, narka-narka masu tsada da masu rangwamen kud'i, ko ina sai tarin sojoji da 'yan sanda suke yawo, alamun akwai manyan k'uso shin k'asar acikin masallacin.
Dan yau yawan cikar al'ummar da yawan motocin sun qaru alamun sun nuna wani babba ne zai aurar da 'yarsa ko d'ansa, abun sai ya zama biyu, sbd limamin mai bada sallar juma'an masallacin, shine mahaifin uban amarya.
'Yan uwa da abokan arziqi sun hallara, abin sai wanda ya gani.

Zaune suke cikin masallacin suna jiran isowar waliyan ango, aurensu ne za'a fara d'aurawa, amman an d'aura dukkan auren da suke da shi a yau, har yanzu waliyan angon Ummulkhairi basu iso ba.
Mai shela sai fad'i yake.
“Ina waliyin ango na wajan Ummulkhairi Abdallah Umar shattima da fatan sun samu isowa?”
Lokacin da me shela ya idar da shelan hankalin minister Abdallah Shatiima yayi bala'in tashi, ya kalli dubban jama'arsa 'yan uwansa da abokanan sa, manyan k'uso shin k'asar nan, ya maida kallonsa kan governor.
Kaifafan idanunsa ya janye daga kallon kowa, na cikin masallacin dan yasan kowa jiransa yake.

Wayoyinsa har guda 3 ne suka d'auki ruri alokaci d'aya, kamar had'in baki, babban sojan da yake na hannun damarsa ya qaraso wajan minister Abdallah, cikin ladabi yay masa magana k'asa-k'asa, dab da kunnen shi ya beqa masa wuleliyar Samsung d'insa.
Jujjuya wayan yay cikin iliminsa kamar yadda yake minister ilimi, ya kai wayan kunnensa Wanda sai da ya katse kiran cikin ilimi tare da kasheta kafin ya fara magana kamar gaske tare da fad'in.
Ok sai kun iso anata jiranku, No! Ba komai anyi muku uzuri.”
Ya k'arashe maganar ya beqawa sojan wayan.
Sai lokacin na gama k'are musu kallo tsaf.
Sanye dukkan family's d'in suke da wata irin d'ayan farar shadda mai bala'in maiqo, sai k'yalli suke, ba kamar ta jikin minister Abdallah Umar Shattima.
Baqi ne, amman jin dad'i da hutu tare da kwanciyar hankali ya saka baqar fatarsa qara murjewa tana sheqi,sai bala'in taushi.
Dogo ne kyakkyawan baqin bafulatanin asali, mai cikar haiba da zati Uwa uba kwarjini, yanada cikar halitta amman baida jiki talaulayi ne, d'an kimanin shekaru, 48.
Manyan idanunsa masu lumshewa ya lumshe ya motsa k'aramin bakinsa tare da kiran sunan ubangijin shi, gabansa ya shiga fad'uwa tsoro ya cikasa, tabbas yasan ya gama kunyata cikin dubban al'ummar da ya gayyato auran 'yarsa, ya kasa bud'e idanunsa.
Yasan kaf cikin masallacin shi aka zubawa idanu.
Muryan mahaifinsa Malam Umar Shattima ya ji yana fad'in.
“Shattima! Wai lafiya har yanzu tawagarsu Alhaji Hashim bata isoba?”

Cikin jarumtarsa da juriyar shi, da barwa Allah lamarinsa, duk da kuwa yasan tafaru ta qare anyiwa mai dame d'aya sata, Salim d'an amininsa Hashim ya fasa auren 'yarsa, hakan bai saka ya ji ya karaya ba, ya bud'e shanyayyun idanunsa ya zuwaba babban malamin wanda yake mahaifinsa, ya saki sansanyan murmushi cikin kamewar shi da juriyarsa da tawakali kamar kullun cikin zazzaqar muryar shi ya furta.
“ALLAH shi temakeka Baffa! Suna hanya aqara haquri da shi mukayi waya yanzu.”
Ya k'arashe mgnar cikin alhinin abinda zai faru jimawa kad'an.
Hannun da ya ji ya dafa shi ne yay saurin maida idanunsa, akan babban aminnsa commissioner Aminu.
Murmushi ya sakar masa yana fad'in.
“Kuyi haquri sun kusa isowa.”
Aminu ya girgiza kasan ya ce.
“Muje daga waje zamuyi magana.”
Ba musu minister Shattima ya miqe yana zuba hannayensa cikin aljihun babbar rigarsa, wadda taci aikin surfanin zamani irin nasu na manya qyalli kawai yake.
Can gefen suka rab'e gefen masallacin, yayin da security's suke tsare dasu da bindigogi a hannayensu suna shawagi.

Alhaji Aminu ya dafa kafad'ar Shattima ya Ce.
“Banyi zaton zaka iya b'oyemin wani abu da ya shafeka ba! Ai ni dakai wlh na d'auka tamkar Uwa d'aya uba d'aya muke, tin yarinta tare muka tashi haka tare muka zama wasu ak'asar nan, shawaramu d'aya mu kashe mu binne, haka matan mu, shin me akazo aka fad'ama da ya d'agama hankali haka? Ni ina gane damuwarka koda kowa bai ganeba.”
Shattima ya zubama commissioner Aminu kaifafan idanunsa, ya fesar da zazzafar iskar bakinsa waje, kafin ya shafi gefen fuskarshi ya furta.
“Aminu! Salim Hashim ya fasa auren Ummulkhairi nah, kasan k'aunar da take masa, ya zanyi da ita? Wlh zan iya jure komai banda ganinta cikin matsanaicin hali. Ya zanyi da jama'ar da suka cika a mosque nan suna jiran su shaida auren gudan 'yata wacce taci burin aurenta da Salim Hashim? Daman sun shirya hakane domin su tozartani nida 'yata KO me hakan yake nufi?”
Minister Aminu ya Ce.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!
Allahumma ajirni fii musiibatihi wa khalifni khairan minha. Mu Hashim zai wulaqanta? Toh wlh bamu yayima ba kansu suka yiwa, akwai ranan nadama tana zuwa, wallahi Abdallah duk wanda ubangiji ya rufawa asiri ba mai tona masa, muje yanzu a d'aura auren da Abdullahi d'ana wanda na isa da shi.. Kuma kakaf dukiyar da aka kashe ma Ummulkhairi, aka kai gidansu aka shirya komai acan bamaso abarmusu, ni zan mata komai sabo, ayau akawota gidana bayan d'aurin aure tayi zamanta can, kafin Abdullahi ya dawo daga Singapore, an shirya mata komai na 'yar gata.”
Ya k'arashe magnar ransa amugun b'ace tamkar Maryam 'yarsa ce akayiwa cin mutuncin nan.
Ya d'agawa securitynsa hannu, cikin rawar jiki ya beqo masa wata zungureriyar waya mai kyau, ya latsa wata lamba bugu d'aya aka d'aga ya furta.
Kawu Bala yanzu akawomin huhun goro biyar da alewa da dabino central mosque kuzo kamar Ku goma azafafan motoci daman nida jama'ar tawa muna nan kawai inason aga wasu sun qaru ne, abun zaifi bada citta.”
Ya k'arashe maganar yana katse kiran, kawai sai ya zura wayarsa cikin aljihunsa.

Shattima ya zubawa alhaji Aminu idanunsa cike da mamakinsa, yana tunanin wata irin k'auna ce Aminu yake masa da zai fitar dasu kunya, yasan shi d'in mai k'aunarsa ne tin tashinsu,duk da Aminu ya basa wajan shekaru biyar ahaife,kawai amince ne suke wanda Allah ne ya had'a jininsu.
Hannayen Aminu ya riqe cikin dattaku yake magana.
“Haba commissioner! Ya zakama my takwara haka baya k'asar ka d'aura masa aure da k'anwarsa? Bayan kasan akwai wacce yake so shima kamar ransa?”
Fuska commissioner Aminu ya had'e ya ce“Dallah can ni fa kaga abinda yake had'ani da kai fulatancin ka, da kawaicin da bazai anfanemu ba, duk da kana ministan ilimi, har yanzu kana nan da fulatancinka, yanzu sbd Allah har na haifi d'an da zan bashi umarni yaqi binsa? Abdulahi ne zan tsaya sai naji ta bakinsa kafin na aura masa wacce nake so? Har yamutu zai samu mace ne kamar daughter Ummulkhairi? Ai kabar mgnar nan kawai Abokina.”
Shattima kasa mgna yayi sosai farin ciki ya gama lulub'e shi ya rungume Aminu yana godiya.
Dukan wasa ya masa abaya ya Ce.
“Kul na kuma ji tsakanin mu ba godiya komai nayi maka ko kamin _yiwa Kai ne.”_

Cikin masallacin suka koma, ba'a fi mintuna 15 jama'ar da Aminun yayi kira suka hallara cikin masallacin tare da dukkan abinda ya buqata.
Nan aka gabatar da dukkan abinda ya dace na neman aure, nan dubban jama'a suka sheda aure tsakanin Abdullahi Aminu kazaure, da Ummulkhairi Abdallah Umar shattimai,akan sadaki mai daraja naira dubu d'ari uku, lakadan ba ajalan ba.

Bayan d'aurin aure akayi tarin addu'o'i na neman Allah ya basu zaman lafiya,da yiwa k'asa addu'a da neman kwanciyar hankali da arziqi me anfani.
Aka raba goro da alewa da dabino, masha Allah abin sai wanda ya gani.
Haka taron ya watse cikin farin ciki da annushuwa, ba tare da jama'a sun ankare juyin mulkin da akayi ba wajan d'urin auren ba, sai malam Umar da wasu daga cikin 'yan uwansu.

Unguwan (commissioners Quarters).
Wani qerarran gida ne mai kyawun gaske, wanda tin daga dogayen shifkokin da suka zagaye da dogayen katangun gidan, zuwa tamfatsetsan gate d'in gidan zaka san gidan na masu fad'a ajine.
Tin daga layin da zai sadaka da gidan kake jiyo kid'e-kid'e tare da busar sarewa na tashi, zaka rante gidan sarkin dutse ake aure,maroqa da mawaqa natayi, wasu manyan rumfunane da kujero a qofar gidan da cikin gidan ko Ina 'yan sandane suke shawagi da bindigugi.
Jiniyar motocin su Shattima ne sun dawo daga d'aurin aure,jiniyar ta kard'e dukkan layin.
Shattima yana zaune a side d'in baya ya kame, idanunsa akan yawan taron da ya gani tin basu qaraso gate d'in gidan ba.
Hular kansa ya cire ya shafi lallausan sumar kansa mai taushi ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa, ya bud'e ya zubawa wayoyinsa guda 4 wacce Kira ya kuma shigowa ya d'auka wadda bai san adadin yawan jama'ar da suka kira ba, ya dai ga miss calls 30.
Amsa kiran yay 'yan tayasa murnane.
Wata number ya kira bugu d'aya aka d'aga cikin kamewarsa ya furta.
“Please kar a kori kowa ayi musu dukkan wani abu na karrama baqo k'unata ta sanya dukkan bayin Allah'n zuwa wajan auren 'yata, so abarsu kowa ya nuna bajintarsa, sannan asaka idanu sosai akan dukkan masu shigi da fici duk da akwai wadatar CCTV cameras.”
Ya k'arashe maganar yana katse kiran bai jira yaji abinda za'a ce masa ba, tare da lalubo number da akayi saving da sunan.
_(Sweetheart)_ ya danna kira..

Wani hamshaqin falone da d'ud'uma-d'ud'uman kujeru har seats uku, baki d'aya adon maroon ne falon tin daga kan kujeru carpets labulaye komai maroon ne, sai wata tamfatsetsiyar Tv plasma wacceta ta kusa cin rabin bangon gusum, falon ya ji kayan alatu ainun.
Matane cike da falon wanda suka kai da Wanda basu kaiba.
Kowacce ajikinta wani dakeken lace mai shegen kyau Green colour mai tsada.
Wasu kuma suna sanye da abinda ya sawwaqane kasancewar akwai baqi daga gari-gari da danginta da dangin shi.
Hajiya Bilkisu kyakkyawar mace fara bafulatana, siririya 'yar kimanin shekaru 41, amman jin dad'i ya b'oye shekarunta bazaka Ce ta haura shekaru 36 zuwa 37 ba, idan kaga Ummulkhairi bazaka ce ita ta haifeta ba, sabida qaramin jikinta.
Ansha gwala-gwalai wuya da hannu k'unshin nan d'as ya
na baqin lalle da ja.
Tsaye take suna falo na gefen babban falo, suna magana da hajiya Abida mahaifiyar Abdullahi ango😂, akan baqin k'awayensu na kano wanda suke akeb'antaccan waje a b'angaran gidan wajan saukar baqi, suna son suma suyi musu tarba wacce zata saka gobe idan suna safga aguje zasu dawo.
Fauziya k'anwarta ta iso da sassarfa tana fad'in.
“Auntie! Hamma Minister na kira fa!”
Hajiya Bilkisu ta amshi wayan tana sakin murmushi tana fad'in.
“Masha Allah aure ya d'auri Babyn dady hankli zai kwanta,bari na amsa waya Hajiyata nazo.”
Sunan da take fad'awa hajiya Abida kenan sbd amincin da yake tsakaninsu.
Hajiya Abida ta washe baki ta Ce.
“Lallai fa yau zan damqa amanar 'yata hannun Salim Hashim Masha Allah, Allah yasa bad'i warhaka munci rangan d'in twins.”
Bilkisu wacce ta d'aga wayan tana amsa da.

“Ameen Ina kaga Dr Bilkisu Mrs Abdallah da jika d'an Baby khairinmu wow! Abun zai bada citta fa! Hajiyata.”
Ta qarashe mgnar tana kai wayan kunnenta tare sallama.
Hajiya Abida ta k'yalk'yale da dariya ta ce“Ai munyi wajan Azima ko jikana ba naki bane?”
Hannu ta d'aga mata alamar tana zuwa, ta nufi stairs.
Daga can wanda lokacin motarsu ta shige cikin tamfatsetsiyar rumfar Adana motocin gidan, ya amsa sallamar yana fad'in.
“Sweetheart! Ki sameni falon hutawa na, yi sauri zan koma wajan baqina.”
Cike da kulawa tare da tarin soyayyarsa ta amsa da.
“Ok Mi Amor yanzu kuwa.”
Murmushi ya saki yana katse kiran, lokacin da ake bud'e masa motar...

Stairs ta haye sai tabi ta can akwai hanyar da zata sauka zuwa falon hutawarsa, tana tafe tana sakin murmushi.

Matashiya ce 'yar kimanin shekaru 21 baqa, irin baqin nan mai bala'in kyau, cikin wani tsararran falo, wanda ya gaji da had'uwa. Fuskarta na nuna alamun damuwa kad'an.
Tsaleliyar iPhone 13 pro max ahannunta tana famar latsawa,wata number wacce aka rubuta sunan.
_(Nisful Hayat)_
Tai dialing number akaro na biyar bata shiga.
Goshinta ta dafe cikin zazzaqar muryata ta furta.
“Ya Rabbi! Wai nisful Hayat na lfy kuwa ace anyi d'aurin aurenmu shiru bai kiraba ya mun barka kamar yadda muka tsara ni kuma na kirasa bana samunsa?”
Ta k'arashe mgnar cikin zallar shagwab'arta tana mele baki tare da kiran number Abdulrazaq babban abokin angon.
Bugu d'aya ya d'aga tare da sallama.
Ummulkhairi ta miqe cikin nutsuwarta ta fara takawa ta nufi bedroom d'in auntie Balaraba,tana masa sallama.
Amsawa yay tare da fad'in.
“Amarsu ykk?
Ummulkhairi ta Ce.
“Ba yadda nake ina nisful hayat? Inata kiransa bana samunsa fa! Fatan an d'auro?”
Abdulrazaq wanda zufa ta fara karyo masa ya b'oye tashin hankalinsa ya had'iye wani yawu me d'aci da baqin cikin halin da ake ciki ya Ce.
“Eh an d'aura congratulations Ummulkhairi, kiyi hkr jama'a ta ma Salim yawa anjima muna zuwa insha Allah OK?”
Wani fari tayi da matsagaitan lumsassun fararen idanunta, ta saki murmushi wanda wushiryarta ta sama da qasa ta bayyana, tsakankanin fararen jerarrun haqoranta ta ce.
“Alhamdulillahi ko yanzu na mutu burina ya cika na mallaki Salim d'ina, kace masa ina tayasa murnan samun abar son shi bye sai kun zo.”
Ta k'arashe maganar tana katse kiran tai tsalle tana juyi ta nufo qawayenta tana fad'in.
“Alqawalin Allah ya cika k'awayena aure ya d'auru tsakanin Ummulkhairi da Salim d'inta.”
K'awayenta suka zagayeta suna ihu babbar k'awarta Suhailat ta rungumeta tana fad'in.
“Congratulations my dear.”
Maryam ta sumbaci kumatunta ta ce.
“Auntie congratulations. ”
Sauran ma suka zagayeta suna tayata murnan mallakar abin sonta.
Cikin su kowace ka kalla farin ciki take, 'yan matane 'ya'yan masu akwai da akasin hakan, kasancewar Ummulkhairi batada raina mutum akwai son mutane ba ruwanta da abota da sai mai kud'i kowa natane,shiyasa yau gidan Auntie Balaraba k'anwar Shattima wacce ta d'auki wunin amarya anan za'a mata wanka ya cika Tabb da 'yan mata, sunata shagalinsu sai kid'a ke tashi suna raye-rayensu, waqar Umar m Sharif ta amaryar share hawayenkin yau ake d'aura aurenki.

Sai ihu suke suna tsalle Kowace ta taci adonta da ankon lace, purple colour,amman kowace iya aljihunta ta d'inka sabida qarfin ba d'ayaba akwai 'ya'yan talakawa acikinsu.
Wankan su ya zauna ajikinsu ba k'arya.

Ummulkhairi sanye take da wani hamshaqin lafiyayyan lace purple wanda qalla kud'unsa zai kai dubu d'ari da hamsin riga da skirt ne, qafafunta da hannunta sunsha k'unshi na jan lalle duk da tana baqa k'unshin ya fito ya mata kyau, haka kitsonta da k'ananu masu irin wata lank'wasa yayi bala'in kyau, jelar rabi ta sauka har gadon bayanta saura gefen fuskarta ya zubo harwucin k'irjinta, sai sheqi take tayi wani irin mashahurin kyau. tanada hanci me tsayi, da d'an qaramin bakinta wanda jin dad'i ya maidasa kalar pink, tanada idanu matsagaita basuda girma sosai haka basuda k'ananu can, fararene tass idan tana kallon ka zaka zaci kallon raini take maka ita kuma haka yanayin halittar kallonta take sai kun saba zaka fahimceta.
Allah ya mata kyawun diri da sura mai d'aukar hankali, akwai hips uwa uba bom-bom matasa masu cikar lafiya, tanada matsagaicin tsayi da jiki bata sahun ramammu,haka bata sahun masu k'iba wato (tsaka tsakiya).
Cikin zallar farin ciki ta ce.
“Bari na kira Sweet Dady.”
Tai dialing number minister Shattima wanda akayi saving da sunan.
_(Sweet Dady)_

Acan kuwa gidan minister Shattima Bilkisu tana isowa qofar falon hutawar nashi, wani d'an madanni ne manne jikin glass d'in qofar ta latsa wasu lambobin, atake qofar glass d'in ta bud'e ta shige had'add'an falon mai bala'in kyau da tsari, ga wani irin fitinannan k'amshi tare da sanyin A.c ya gauraye falon mai tsarin na turawa.

Tana shiga atake k'ofar ta rufe kanta.
Bakinda d'auke da sallama ta tinkare shi ya lume cikin sofa idanunsa a lumshe amman waya yake amsawa.
Kallonsa take kamar zata cinye shi cike da k'aunarsa.
Dab da shi ta zauna tana sakin murmushi, ta sanya dukkan hannayenta ajikinsa ta fara qoqarin cire mishi babbar rigarsa.
Ba musu ya bata damar yin hakan, lokacin da yake ajiye wayan akan wani had'add'an glass table.
Linke rigan tai ta ajiye gefe ta miqe ta nufi fridge ta d'auko jug wanda yake cike da lemun masoyinsa wato inibi.
A cup ta tsiyaya masa ta zauna kamar zata koma cikinsa, ta tallafo kansa ta manna masa cup d'in abakinsa, tana fad'in.
Barkanmu yau mun sauke haqqin da Allah ya d'ora mana aurar da 'yarmu ga miji nagartacce.”
Kaifafan idanunsa masu lumshewa ya kafa mata, yana had'iyar lemon cike da nutsuwa.
Sai da ya shanye tass ya janye bakinsa tare da rungumeta tsam k'irjinsa, yana shafa kumatunta, bakinsa dab da kunnenta cikin nutsuwar shi da soyayyar shi da hikimarsa ya zayyanewa hajiya Bilkisu kakaf abinda ya faru ayau d'in game da d'aurin auren yadda abin ya juye aka d'aura auren da Abdullahi Aminu.

Bilkisu ta rangad'a gud'a ta Ce.
“Allah na gode maka da hakan ta faru, wlh najima inason had'a zuria da babban amininka, kawai ba yadda na iyane sbd son da Baby take ma Salim ba na wasa bane, wlh tin lokacin da tace min ta kamashi yana shan sigari ya fita araina to kasan baby da kafiya tinda tace shi take so idan bamu bata ba zata kwance mana ciwo, amman alhaji Hashim sunban mamaki shi da zuri'arsa, kuma wani halin ga Allah baiwane, kansu sukayiwa bamu ba, ga shi Allah ya sauya mana da mafi alkhairi.”

Minister ya murmusa yana sakinta yaja hancinta ya ce.
“Kul ki sanar da kowa har sweet daughter ki barni da abata zuwa dare zanji da ita.”
Bilkisu ta murmusa tana sanya yatsarta ramin dimples d'insa ta ce.
“An gama yallab'ai mi Amor, Amman hajiya Abida bata san komai ba ita koh?”
Zaiyi magana
Daidai lokacin ne kiran Ummulkhairi ya shigo wayansa.
Ganin me kiran ya d'auki wayan yana picking call d'in.
Kafin yakai ga magana ya ji tana kyalkyala dariya da tsallen da take daga can yana shigowa cikin dodon kunnensa.
Kallon Bilkisu yay yana girgiza kansa ya saka wayan a speaker, yana jiran ta gama haukan murnan.
Shattima ahankali ya furta.
“ALLAH na gode maka da ka bani wannan d'iya tawa marar kunya.”
Bilkisu tai dariya zatayi magana taji muryan Ummulkhairi tana fad'in.
“Hello sweet Dady! Ngd Allah ya barku da sweet mamytah, ngd da aura min wanda nakeso muahhhhh i love you sweet Dady.”
Shattima dariyar da yake dannewa ta kub'uce masa, yay kad'an ya tsagaita jin ta biye masa daga can.
“Sweet daughter na dakatar da dinner d'inku da duk wani shagali walima kawai na yarda ta zallar mata kuyi shima dan a wa'azintar dakune, na Kira Balaraba nace maza ta koma wajanku, kashe wayarki yanzu bana son ki kunnata sai bayan an kawoki gida OK?”
Kai ta langwab'e tana mele d'an qaramin pink d'in bakinta,asakalce ta ce.
“Kai! Sweet Dady! Anata fa kirana kuma anjima su nisful Hayat zasu shigo.”
Cike da umarni ya ce“Na ce ki kashe wayanki karki kunna sai an kawoki daga gidan Balaraba, karki kuma ari wayan kowa ki kira kowa Ku dakatar da dinner, kinaji KO bakya jina?”
Tsaf ta nutsu ta nemi waje ta zauna ta fara rarraba idanu jin Dadyn ya dawo asalin halinsa, cike da tsoron shi ta amsa.“Ok toh Dady kayi hkr zanyi dukkan abinda ka ce yanzu, Ina sweet Mamy?”
Ba wasa ya ce“Tana jinki oya kashe wayan yanzu.”
Da
“Toh”
ta amsa ta kashe wayan baki d'aya tana tutturo baki gaba tana diddira k'afafunta.
Banda dariya babu abinda k'awayenta suke mata, nan ta Samar dasu walima kawai za'ayi bayan la'asar.

Haka kuwa akayi wajansu Ummulkhairi walima kawai akayi, haka wajansu hajiya Bilkisu ma ita akayi ta manyan mata, ayau almajiran da suke jigawa sun san anyima d'iyar gata aure sunci sun Sha.

Quarter
*ASOKORO*
Matashine d’an kimanin shekaru 27 wankan tarwad'a ne, ba laifi yanada kyau da dirin maza mai kyau daidai shi, dogone kana kallonsa kasan d'an hutune.
Kwance yake saman lafiyayyan bed d'insa, yana d'aure da drip ajikinsa.
Cike da wata irin muguwar kasala ya fara bud'e k'ananun idanunsa masu kyau, wanda,sukayi masa nauyi bai sauke kallonsa a ko ina ba sai akan drip d'in jikinsa.
“Subanallahi me kuma ya sameni?”
Yay mgnar yana waigowa ya kalli Abdulrazaq babban amininsa yana riqe hannunsa ya ce.
Abdulrazaq ya ce.
“Wlh idan nace ga abinda ya sameka nayi qarya, na gama shiri zan taho lokacin da ka gama kirani nayi sauri nida Najib mu kaima su Ummulkhairi saqonsu, na shiga mota kenan naga kiran Father yace nazo gida sun ganka ka zube ba rai amman an kira Dr families naku yana dubaka agida...”
Daga nan ya basa labarin dukkan abinda ya faru kakaf da fasa aurensa da akayi da Ummulkhairi wanda umarnin Father ne, amman bai fad'a masa labarin d'aya ba.

Ahaukace Salim ya fasa ihu ya fizge drip d'in jikinsa, atake jini ya fara fita daga hannunsa,wani irin ashar ya lailaya, yana fad'in.
“Wallahi ko uban waye ya auri Jewel sai ya saketa ko na kashesa na rantse da Allah ba wanda ya isa ya zauna min da matata afad'in duniyar nan.”
Ya k'arashe mgnar ya dirowa daga saman bed d'in.

Abdulrazaq ya riqeshi da niyar kwantar masa da hankali, ya fizge da k'arfi yana hankad'e shi ya nufi qofar fita.

A haukace ya shigo babban falon nasu ko ganin baqin da suke cika falon 'yan zauwa biki baiyi ba.
Cike da masifa da bala'i Salim yake kiran mahaifiyarsa.
“Umma! Umma!! Umma!!!

Please Login or Register in order to submit comment