Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nauyi babba.

Mamy da take can d'akinta itama sallar tayi sabida tsarkin da ta samu kusan 12 na dare, shiyasa tayi sallah tana roqon Allahn, ta gama taji tana buqatar kwanciya jikin mijinta ko ba komai taji sanyi a ranta.
Hijab d'in ta cire ta cire rigan sallan ta mayar da rigan baccinta ta shafa humram mai shegen dad'i ta sanya hula akanta, ta fice zuwa sashen Shattiman.
Bata tsaya knocking d'in k'ofa ba dan tasan yanzu baya falon ta bud'e ta shiga ta murza key daga ciki, ta nufi bedroom d'in.
Ya miqe ya nufi bed kenan yaji qaran tab'a qofa.
Tsaye yayi fuskarsa ba walwala ya kafawa qofar bedroom idanu, bai fi second 10 ba ta murd'a k'ofar ta shigo bakinta da sallama.
Idanunsu suka manne waje d'aya tai k'asa da kanta sabida bala'in kwarjinin da ya mata.
Juyawa yay ba tare da ya cire jallabiyan ba ya haye tamfatsetsan royal bed d'insa, yana shigewa cikin wani tattausan pink d'in bargo mai fitar da azababban k'amshinsa, ya lumshe idanunsa.

Key Mamy ta murzawa qofar bedroom d'in.
Ta nufo gadon kanta qasa.
Kyawawan k'wayayen wutar d'akin ta kashe, ta kunna ta gefen gadon, tana qoqarin hawa bed d'in taji sautin daddad'ar amon muryasa mai sakamata qara sonsa anitse yana fad'in.
“Karki hau je d'akinki ina buqatar keb'ewa ni d'aya...”
Wani irin dam dam k'irjin Mamy ya buga, taji wani bala'in tashin hankali.
Kuka taji yazo mata sabida zafin abinda yace matan, gadon ta haye kai tsaye ta janye bargon ta fad'a k'irjinsa tana qanqameshi cikin kuka tace.
“Wlh bazan iyaba kamin hukunci ko wane iri amman banda hukuncin hanani rab'arka Wai Shattima kasheni kakeso kayi? da wannan zanji dan Allah meye laifina cikin wannan lamarin alkahiri fa na had'a...”
A hassale ya kamo kafad'unta cikin d'acin zuciya yana girgizawa yace...


*YI WA KAI*

Free Novel

_November 10/11/2022_



*59&60*

“Ni ai kin kasheni Bilkisu kin gama dani, ya zanyi da halin da kika sakani aciki? Ni baki tausaya min ba? Ashe ni ban isa dake ba? Me nace miki wancan lokacin akan maganan Khairy? Shi ne kika rufe idanunki kikaje kuka had'u da Baffa kuka liqamin auren Khairy, shin ke aganin ki kin kyauta? Da wane idanu Zan iya kallonta na kuma kalli duniya nace 'yar ciki ita ce matata ayanzu? Wlh kinci sa'ar Baffa da dakatar dani a k'udirina na sakinki na saketa itama nabar muku k'asar, sabida sam bazan iya da abin kunyar nan ba, wai shin ma da wani idanu zan kalli Babban aminina Aminu? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kun sakani tsa...”
Mamy tai saurin rufe masa bakinsa da tafin hannunta, tana kuka tace.
“Don Allah kayi haquri Mi Amor kayi shiru da bakinka idan bazaka fad'i kalma mai dad'i akan wannan auren ba, ni na tabbata nan gaba kad'an sai kayi alfahari da wannan auren, kasani ina Sonka ina k'aunarka ina bala'in kishinka, duk duniya idan ba Ummulkhairin mu ba, babu macan da zanyi wannan kasadar na sadaukar da mijina wanda nakeda yaqinin acikin maza 50 bai fi asamu irinsa 2 ko 3 zanyi kasadar bama wata shi.
Hutawa tayi kad'an taci gaba da fad'in. “Da ita kawai na amince azamanin wannan har na had'aku aure, wlh banyi zaton zaka gujema auren Baby ba, mu muka raini abinmu ga shi ubangiji yayi nufinsa ta dawo hannunmu, ayanzu ta lafiyarta muke da fuskantar ta yadda zata amshi aurenka dan tafika rikicewa da al'amarin...”
Wani irin kallo Shattima ya watsa mata tare da zameta daga jikinsa, ya juya mata baya yana rufe jikinsa tare da lumshe kaifafan fararen idanunsa, yana anbaton sunan ALLAH acikin zuciyarsa.
Mamy gabansa ta dawo ta shige cikin bargo tare rungumeshi qanqam, fuskokinsu suka manne waje d'aya suna shaqar numfashin juna.
Hannunta ta tura cikin rigarsa tana shafa k'irjinsa mai yalwar gashi zuwa nipples d'insa, ta zaro harshenta tana lasar fuskar shi, tare kaimasa sumbata dukkan fuskar shi .
Qala bai ce mata ba, kamar yadda baiyi yinqurin hanata ba, yanajin yadda ta zage tana shafarsa wajan da yafi buqata, tana masa salon da baya jurewa komai yanayin da yake ciki, amman yau al'amarin yasha banban baya cikin moment mai dad'i baya wani jin feeling, haka ta gama yamutsashi har bacci ya kwasheta bakinta manne da nashi.
Zare bakinsa yay ahankali yana me sake shigar da ita cikin jikinsa ya lumshe idanunsa ba wai dan zai iya baccin ba.

Washrgari Mamy tayi iya qoqarinta wajan ganin ta tsareshi yayi breakfast kafin ya fita, sai wani ciccije mata yake.
Yana fita itama ta wuce zuwa asibiti.
Tin bayan sallar asubah liman ya koma asibitin ya dubu Khairy ya kira Shattima akan yaje ya dubata kafin ya wuce wajan aikinsa.
Haka kuwa akayi dole asibitin ya fara zuwa kafin ya wuce aikinsa.

Alhaji Bilal da Hajja Hafsatu da Adamu sunje suma sun dubo Khairy'n.
Mamy bayan ta duba Khairy haka ta jure ta wuce, ta duba patients ta wuce office d'inta.
Tana zama ko umarni wad'anda zata duba su fara shigowa bata bada ba, wayanta ta d'auki ruri.
Kyawawan idanunta wanda suka gaji da kuka har sun tasa sosai dan tana sanye da glass ne bazaka gane haka ba, ta zubawa wayan.
Ganin sunan Abidah yana yawo saman screen d'in wayan.
Tattausan farin hannunta ta beqa ta d'auki wayan tai picking call d'in tana sake saita nutsuwarta tayi sallama cikin kamilar muryata.
Daga can Ammi ta amsa tana fad'in.
“Bokan turai! Barka da safiya fatan kin tashi lfy! Ya fama da jama'a ya daughter da Dadynta?”
Mamy ta amsa da.
“Lafiya k'alau hajiyata ya yarana? Khairy gata hospital batajin dad'i, Amman da sauqi ta samu bacci.”
Ammi ta gyara zamanta tana fad'in.
“Subahanallahi tin yaushe? amman wlh baku kyauta mana ba, yanzu fa mun gama shirin da abbansu zamuje sannu da zuwa,su Maryam kuwa sai sun dawo daga school zasu je yanzu gamunan zuwa yanzu da Abbansu.”
Mamy ta sauke numfashi tace.
“Ayi haquri jiya da dare ne wlh kaina ya d'auki charge dayawa, OK sai kunzo.”
Ammi tace.
“Ok gamunan.”
Ta fad'a tana katse wayan, tana kallon commissioner Aminu wanda yayi shirin fita aiki, tana fad'in.
“Abban Abdoul! Wai Khairy ce ba lafiya tin jiya da dare tana asibiti.”
Idanunsa ya kafa mata cike da mamaki, ya samu kamar second 20 kafin yayi magana.
“Ashaaaa! Me ya sameta? Ni kam me yake faruwane tsakanina da minister yanzu da yake son b'oyemin wasu al'amuransa? da a baya ne tin ajiya zai kirani yace 'yata batada lfy, bansan meyasa minister yake son canza alaqar mu ba! Duba mgnar auren Khairy har yau bai min ba...”
Ammi ta rufe masa baki da tafin hannunta, tana fad'in.
“Haba! Abban Abdoul kayi masa kyakkyawan zato, kasan Shattima bayada haka kawai ina zaton abubuwa suka Sha kansa, shiyasa bai maka mgnar ba! Rashin lafiyar Khairy'n kuwa k'ila jiya Kansu ya fasu ne shiyasa bai kiraka ba yi haquri yanzu dai mutafi mudubata sai ka wuce wajan aikin please karkace komai OK!?”
Hannunta ya janye yana jinjina kansa yace.
“Ok.”
Bai sake magana ba, suka fito zuwa farfajiyar gidan, dan shiga mota.

Suna zuwa hospital Ammi ta Kira Mamy ta fad'a mata, Mamy da kanta ta fito.
Cikin girmamawa suka gaisa da commissioner, ta musu jagora zuwa room d'in da Khairy'n take kwance.
Bacci take kamar matacciya, drip d'aure ahannunta sai shiga jikinta yake anitse, fuskarta tayi fayau har wani farin wahala tayi kad'an, tare da Rama kamar tayi sati biyu akwance.
Commissioner yana kallonta cike da tausayinta yace.
“Dr Bilkisu! Wai tin yaushe ne Ummulkhairi batada lafiya har tayi rama haka?”
Mamy tace.
“Wlh jiyane buguwa kawai tayi, Amman yanzu da sauqi.”
Ajiyar zuciya ya sauke yace.
“Allah ya bata lfy, yanzu kenan ba wata matsala baccin ne?”
Mamy ta lumfasa tace.
“Toh Alhmdllh! Muna sa ran idan ta farka komai yazo da sauqi.”
Addu'ar neman sauqi yamata wajan Allah yace Ammi ta zauna har ajima shi zai wuce wajan aiki...

Zaune Shattima yake cikin tsararran office d'insa, wanda yake bada wani irin sayi had'e da qamshi mai bala'in dad'i.
Sanye yake da wani lallausan yadi fari qal mai bala'in kyau, d'inki ya masa kyau matuqa. Waya yake anitse cikin kamewarsa bazaka tab'a cewa yana cikin damuwaba, sabida shi mutum ne mai b'oye abu azuciyarsa sai idan abun yaci tura kake gane b'acin ransa azahiri.
Hannunsa saman goshinsa yana murzawa, tare da sakin zazzafan numfashi, yana fesar da d'umammiyar iskar bakinsa waje, ya lumshe idanunsa cike da kamewarsa yana k'ok'arin b'oye asalin damuwarsa anitse yake fad'in.
“No! Auntie babu abinda zai faru, ba sai kinban haquri ba, babu wanda ya tab'a tsallake k'addaransa, haka Allah ya k'addaramana, duk mummuni dole zai amshi k'addarasa mai kyau ko akasin hakan.. Kawai abunne ki auna shi da kanki kiga akwai yauni sosai... Lumfasawa yay yana lumshe narkakkun idanunsa, masu haske wanda sunyi dan duhu kad'an, yaci gaba da cewa.
“Uhmm! Wlh bansan randa zan iya kallon Khairy matsayin mata ba! Duk da na amshi k'addarata amman.....”
Daga can Abuja auntie Aisha tace.
“Dakata! Abdallah! Kayi istigfari, matuqar ka amshi k'addaraka dole ka amshi Ummulkhairi amatsayin matarka, tinda an rigada an d'aura ba yadda fa ka iya, kayi haquri ka ajiye komai ka rungumi matanka fa! Yanzu ka tausayama halin da take ciki, Kaine zakayi haquri ka runtse tare da cijewa ka janyota jikinka sabida kasan ayanzu dole guje maka zatayi sabida yadda lamarin ya kasance, tana ganinka matsayin mahaifinta, yau an wayi gari ance bakai ka haifeta ba, qarshe kuma ace Kaine mijinta, Bilkisu kishiyarta. Haba dole sai kayi haquri Kaine kawai zaka saka ta dawo hayyacinta, matuqar kanason ta zauna lfy kamar baya sai ka jata ajikinka kamar baya karka nuna mata baka sonta da aure duk da nasan akwai nauyi zamanku haka zaka jure duk da nasan zaka sauko bazaka jure ganin Khairy cikin tashin hankali ba! Karka kuskara kace zaka biyema rigimarta idan ta nemi Saki ka mata. Kayi qoqarin nan kusa komai ya kammala awuce wajan, abunda nakeso da kai ka kawota nan Abuja gidanka sabida nasan bazata tab'a sakewa da kai ba matuqar tana ganin idanun Bilkisu har abadan bazaku fahimci junaba gabanta sabida nauyinta, amman kuna keb'ewa insha Allahu nasan k'aunar da take tsakanin 'ya da ubanta zata rikid'e ne, ka maidota da zunmar taci gaba da karatunta, Allah yasa ka fahimci duk irin abinda na fad'ama Shattima?”
Shattima runtse narkakkun idanunsa yay, yana jingina bayansa saman kujera, tare da sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, yana shafa suman kansa, cikin kamewarsa da basar da abu komai ya maidasa ba komai ba, ya furta.
“Uhmm! Auntie kawai dakata idan su Baffa sun gama da wanda yay sanadin zuwanta duniya duk yadda suka yanke bass sai kizo ki tafi da ita d'in wajanki inaga zatafi sakewa, damuwarta dai bana so kar ciwo ya sarqeta, daughter bazan fasa kallonta a 'yar cikina ba! Nima nasani bazata jure sauyi daga gareniba.”
Ya k'arashe mgnar yana d'aukan cup d'in gabansa mai cike da madaran shanu mai d'umi ya kafa baki.
Auntie Aisha tace.
“Yawwa Ngd da bani wannan damar zan zo insha Allahu da zaran an gama komai...”
Sallama sukayi ta yanke wayan daman ita Ce ta kirasa, dan su tattauna, ta kuma samu yadda take so.

Knocking k'ofar akayi idanunsa a lumshe yana sauke lumfashi ya bada umarnin shigowa.
Sallamar commissioner Aminu da ta daki dodon kunnensa ya saka shi bud'e narkakkun idanun nasa wanda suke cike da gajiyar tashin hankali da yake ciki, ya amsa sallamar yana me jin d'an fad'uwar gaba, yace.
“Haqiqa ni mai laifine ayafemin. Kwana biyu bana samun zama waya ma rabon da muyi yau kwana 2 I'm sorry...”
Aminu ya zauna kan kujaran da take facing d'insa, yana qanqance fuska tare da nuna tsantsar b'acin ransa yaqi amsa hannun da Shattima yake beqa masa yace.
“No! Ai ni baka buqatar aminci dani, wlh Abdallah kaban mamaki mukashe mu binne tin k'uruciya amman cikin watannin nan ka tsiro da halayyar da ba taka ba, wlh naso na shareka n kasa nace sai nazo namaka Tass wai a d'aurawa Khairy aure tsawon kusan wata biyu ko uku ka gasa fad'amin, yanzu tazo daga abuja tin jiya ba lafiya ka kasa fad'amin haka kirana ma ka daina akan lokaci sai idan nine Zan kiraka bare neman shawarata akan wani abun hummm!”

Shattima ya runtse idanuna yana jin wani irin yanayi cike da kamewarsa tare da danne duk wata irin damuwarsa muryasan mai taushi ya furta.
“Ya RAHMAN! dan Allah kayi haquri, wlh commissioner ban sauyaba ina nan kamar baya, haka k'aunarka tana nan fiye da baya ma d'in, jiya wlh kaina ya fasu ne haka yau shiyasa ban maka zancan Baby ba lafiya ba, mgnar auren baby kuwa don Allah kaje wajan Baffa yau nafison ya fad'ama komai da kansa, wlh tallahi bakina bai isa furtama wannan nauyayyar mgnar ba Sam Sam.”Abba Aminu kallon Shattima yay yana fad'in.
“Zanje ai kuwa da yamma daman shi ya Neman wajan d'aura auren, duk da bansan me ya saka bakaje ba.”
Fararen idanun nasa masu haske ya kafa ma Abba Aminu ya kasa cewa uffan, duk da shi ba miskili bane watara magana tana masa bala'in nauyi.
“Bara na k'arasa wajan aiki daman cewa nayi sai na wanke ka zan wuce.”
Ya fad'a yana miqewa.
Shattima ya miqe yana furzar da iskan bakinsa me zafi waje ya zagayo yana Kama hannun Abba Aminu suka nufi qofar ba tare da ya iya furta komai ba....

Bayan sallar lasar liman zaune acikin tsararrar rumfarsa ta qofar gida suna zaune da muqarabansa, anata hira.
Motocine jibga-jibga guda biyu suka faka,bakin gate.
Commissioner Aminu ne Aka bud'ewa k'ofa ya fito sanye cikin shigar kamala.
Da sallama ya iso wajan tare da risinawa yana gaishesu.
Cikin sakin fuska liman yake amsa gaisuwar shida jama'ar da suke wajan.
Limaan yace.
“Aminu! Kaine tafe da yammar nan?”
A ladabce ya amsa.
“Eh wlh Baffa ni da kaina, ashe Ummulkhairy bataji dad'i ba?”
Liman ya miqe yace.
Eh jiya ba! Bismillahi mushiga daga ciki.”
Liman yana gaba commissioner na binsa har ciki.
Sai da ya biya ya gaishe da Inno kafin su wuce b'angaran Liman.
Zaune suke kansa k'asa.
Liman yace.
“Ina fatan kaji abubuwan da suka kasance Aminu?”
Kai ya girgiza yace.
“Banjiba Baffa Shattima yace nazo wajanka zanfi fahimtar mgnar bansan me yake nufi ba, yanzu na samu sauqin aiki nace akawoni naji daga gareka Baffah.”
Liman ya jinjina kansa yace.
“Tabbas haka ne Abdallah yana jin nauyinka bazai iyamaka bayani ba nasani,wato abubuwan da suka faru shi ne....”

Tass Liman ya zayyanewa Aminu komai.
Ba qaramar girgiza labarin yama Aminu ba da mamakin Shattima irin kyan halinsa da dattakunsa, ya jima yana mamakin Shattima, da Bilkisu samun irinta a duniyar nan akwai wahala.
Ajiyar zuciya ya sauke yace.
“Tabbas hakan yayi aure taskaninsu ba k'aramin alkahiri bane,wannan k'aunar da sukewa juna ta uba da 'ya zataci gaba da wanzuwa ko fiye da hakan, Allah yasa uwar 'ya'yansa ce yabawa Bilkisu ma rabonta, dan ta cika jaruma mai sadaukar da abinda take so wa wani, tabbas wannan mgna tama Sahttima nauyi bazai iya gayamun ba Baffa kuma Allah ya Baku ladan wannan had'in sukuma ya basu juriya da haqurin zama da junansu, ita kuma wannan matar ya kuke ganin za'ayi da ita?”
Liman ya gyara zamansa yace.
“Munyi magana da Aisha d'iyata alaqa zasu qulla da ita yadda asirinta zai fito fili sabida yanzu bamuda hujja cewar itace ta yadata zargi mukeyi kuma ba lallai mijinta ya yardaba, dan haka zamubi ahankali ne har mucinma birinmu.”
Abba Aminu yaja lumfashi yace.

“Ai irin wannan basa wuyar kamuwa fa! Amman ayi yanda aka tsaran yayi Baffa....”
Sun tattauna sosai akan batun kafin suyi sallama ya tafi...

Alhamdulillah ayau su Zainabu sun gudanar da taronsu yau, da misalin 9 na safe,har zuwa 12 na rana, taron da ya samu halartar manya manyan mutane harda minister Shattima, amatsayinsa na minister ilimi. Tare da mai girma gwamna jaha, da sauran Jama'a haka kawai tinda yaga Zainabu lokacin da akirata tana jawabi nasu na kurame yake kallonta, sabida tana yanayin Khairy'nsa, akwai jini sosai duk da ba kama, hankalinsa ya qara bashi wani abu sabida sanin baqin kuramen da sukazo wannan taron daga katsina ne suke, idan bazai manta ba Usman yace masa 'yar Katsina Ce, ba mamaki tanada alaqa da mahaifiyar Khairyn dan baiyi tunanin zata haifeta ba, sabida kwatakwata shekarunta idan za'a kiyastasu basu fi 37 koh 38 ba!

6pm.
Shattima ya sauko cikin shirin zuwa masallaci, yana wani sahihin k'amshi fuskarshi bazaka gane wani yanayi take ciki ba.
Mamy wacce take zaune cikin shigar riga da skirt na shadda maroon color, tayi kyau sosai sai rama da ta k'ara, tana amsa waya ta d'ago kanta suka had'a idanu.
Kansa ya kauda yana qoqarin wuceta ya doshi hanyar falon, tace.
“Sorry Hajja Zan sake kiranki bani 5 minutes. ”
Ta fad'a tana katse kiran, ta miqe tana ajiye wayan da sauri ta tare gabansa tana kamo hannayensa ashagwab'e ta Kira shi.
“Mi Amor!”
Ta rungumeshi ta sakar masa kuka mai cike da tausayi...
Narkakkun idanunsa ya lumshe aqasan maqoshi yana fad'in.
“Ya Allah!”
Idanunsa ya bud'e yana d'ago da fara kyakkyawar fuskarta ya kafa mata idanunsa masu qara tsumata a k'aunarsa.
Cikin yanayin kamewarsa yay magana da taushin murya k'asa-k'asa.
“What happened? Kina kukan dad'ine? Right.”
Mamy ta sake shigewa jikinsa kamar zata koma cikinsa, qasa² tace.
“Don Allah Mi Amor karka dad'e kazo mu tafi hospital d'in please... ”
Idanunsa ya kafa mata yana danne yanayin b'acin ransa ya rankwafo yana had'e fuskarsu ya busa mata hucin numfashinsa mai d'umin gaske, ya sake tallabo fuskarta ya zaro harshensa, fuskarta ya shiga lashe hawayenta tana sakin wasu tare da sake qanqameshi.
Anitse cikin kunnenta ya furta.
“Ya isa haka bana son kukan nan kanki zai iya yin ciwo, kije idan kinyi sallah zanzo nima OK?”
Ya fad'a yana d'ago fuskar tata.
Yadda ya zuba mata idanunsa masu bala'in dafi da kwarjini ya sakata d'aga kanta tare da cewa.
“Ok mi amor.”
Kissing d'in bakinta yay na seconds 10 yana sake goge mata fuskarta da tafin hannunsa, ya janyeta ajikinsa ya Kama hannunta ya zaunar da ita saman sofa ya shafi gefen fuskarta batare da yace mata uffan ba yajuya ya nufi hanyar falo.
Da kallo ta rakasa har ya karya kwanar.
Numfashi taja tana lumshe idanunta tana shaqar k'amshinsa da ya gama baibyeta tana lasar bakinta jin qamshi bakinsa anatan.
Wani qaramin murmushi ya sub'uce mata na jin dad'in Shattiman baiyi dogon fushi da ita ba, tana saka ran fitinar Khairy'n kawai data saka shi ya manta komai ya jata ajikinsa har su zama abu d'aya...

Tunda ya shiga masallaci kafin kiran Maghreb d'in, bai fito ba sai bayan sallar isha'i kamar kullun.

Mamy tinda tayi sallar Maghreb ta koma hospital sabid lokacin tashin Khairy ya kusa.

Sanye yake da jallabiya ruwan k'asa sabuwa dall sai k'amshin da ya gama kama jikinsa yake yi, anitse yake takawa shiga cikin gidan nasa daga fitowa da masallacin da yake manne agidansa wanda yake mallakinsa.
Dogon tattausan hannunsa ya zura cikin aljihun wandon jallabiyan,ya zaro wayan da ya fito da ita.
Kai tsaye bayan ya shiga ma'adanar lambobi, ya dannawa Usman Kira.
Daga can Kaduna kuwa Usman na zaune a falo zaman kenan shima, kiran ya shigo, ganin Minister ne kai tsaye ya d'auki wayan ya d'aga kiran tare da sallama.
Shattima wanda yake isa k'atuwar rumfar gidan nasa ta shan iska ya zube saman kujera yana maida numfashi, tare da amsa sallamar anitse cikin kamewa.
Usman ya gaishesa cikin girmamawa.
Shattima yana lumshe kaifafan gajiyayyun idanunsa yace.
“Usman kana lfy? Ya aiki?”
Usman ya gyara zamansa yace.
“Lfy lau Yallab'ai ya haquri da jama'a kwana biyu kuna gida koh?”
Shattima kamar agaban Usman ya jinjina kansa yana laso busassan lips d'insa da ya rasa yawun kirki tun A jiya.
“Am nace ba! Ka daure zuwa gobe ko jibi ka zo dutse ina son ganinka, ba sai ka kwana ba, zaka iya juyawa OK?”
Usman yace.
“Ok Yallab'ai insha Allahu zanzo jibin daman jibin Zan leqa Gumel na kwana biyu, tinda nazo banje ba sai waya.”
Shattima ya jinjina kansa ya ce.
“Ok ba damuwa sai ka shigo amman jibin ya kasance ka iso zuwa 9 ko 10 na safe OK?”
Amsawa Usman yayi da.
“I.sha Allah Yallab'ai....”
Bayan sunyi sallama ya miqe dogayen qafafunsa, saman kujaran da take facing d'insa, yana latsa wayansa sai ga kiran Liman Baffa.
Idanunsa ya runtse yana furta.
“Ya HAYYU ya QAYYUM!”
ya qarasa fad'a yana bud'e narkakkun gajiyayyaun idanunsa, yay picking call d'in, yana kai wayan kunnensa tare da sallama anitse.
Muryan Liman yaji cikin fad'a yana fad'in.
“Kana son ganin fushina azahiri Abdullahi? Shattima cikin kamewarsa da ta zame masa jinin jikinsa yace.
“A'a Baffa ayi haquri me nayi?”

“Ban saniba tambayata kake me kayi? Toh wlh minti goma na baka kayi sauri kazo asibiti gamu Ummulkhairi ta farfado banda rikici ba abinda take, na Hana asake mata allura tinda ba ahaka zata dawwama ba, nasan ganinka kawai zai sakata ta dawo hayyacinta kaine zaka lallasheta ta dawo daidai Kaine zaka tsawatar mata, bazai yuba ayi ta mata alluran bacci, ruwanka kazo yanzu.”
K'ittt ya katse kiran.
Shattima tinda Liman ya fara balbala masa fad'a idanunsa rufe suke yana jin yadda zuciayarsa take bala'in bugawa.
Idanunsa wanda sukayi wani irin rikid'ewa ya bud'e yanajin bala'in tashin hankalin kukan da Khairyn take,an rasa mai shawo kanta ta daina sai shi.
Lips d'insa duka biyun ya shiga lasa sabida yadda suke bushe masa.

Lamba Maleek ya Kira.
Bugu d'aya aka d'aga cikin bada umarni Ana d'aga da kamamiyar muryasa ya furta.
“Maleek! Afito da mota bakin gate zan fita ni d'aya.”
Yana fad'in hakan ya katse kiran tare da miqewa tsaye...


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BoY7L6yHuks8F59z1U4UWd

*YI WA KAI*

Free Novel

_November 12/11/2022_



*61&62*

Bai canza kaya ba, hirama kawai ya shiga ya ɗauko ya yafa, zaka rantse Shattima baƙin Balarabe ne, sabida kyan da ya yi matuƙa, ga wani sahihin ƙamshi da yake tashi ajikinsa.
Ƙafafunsa sanye da Italian slippers anitse yake takawa, zuwa babbar farfajiyar gidan, yayin da yake amsa waya da wani babban mutum, cike da kamewa da fitar da lafazi akan tsari da sanin darajar ɗan adam.
Tun kafin ya ƙara so Maleek ya buɗe masa ƙofar kungiyar baƙar mota mai lumfashi.
Shiga yay lokacin da yake sallama da mutumin da suke waya, ya amshi key ɗin motar ya kunna ya yaja ya nufi gate, Wanda tin kafin ya iso gate an wangame masa ƙaton gate ɗin anitse ya danna hancin motar waje, security's suna ta ɗaga masa hannu.
Anitse ya harba motar kan titi cike nutsuwa da ƙwarewa yake driving ɗin.

Maryam ta fito cikin shirin tafiya hospital, sai zumuɗi take tasan ko banza zataga Dady Shattima acan, tunda takasa ciresa aranta batasan me Allah ya shiryaba tsakanin su.
Ammi ta kalleta tana faɗin.
”Maryam! Duk shirin zuwa asibitin ne kamar zakije wajan biki?”
Maryam tai murmushi tace.
”Kai Ammi da Abba yana kusa ki saka yace naje na goge kwalliya fuskana koh? Nafisa muje yi sauri ki ɗauko kulan mai dambun naman.”
Nafisa ta nufi kitchen da saurinta.
Ammi tace.
”Ki gaishemin da Khairy ɗazu tanata baccinta har nagaji na dawo, da safe zamu koma da Abbanku, karfa ki zauna kinga dare ne da direba ya ajiye ku kun gaisheta sai ki juyo.”
Maryam ta amsa da.
”Toh Ammi wai Yaya Habib bazai kenan ne?”
Habib yace.
”Da safe zan biya sai na wuce school ki gaisheta.”
Nafisa na fitowa suka wuce zuwa farfajiyar gidan.

Yalwawa. Azizah sanye da riga da skirt na atamfa shud'iya d'inkin ya dameta sosai, wani shegen shara² mayafine guntu agefen kafad'arta.
Tana zaune cikin motarta ta murza key, tana nufar gate ta Saki music, sai zuba uban horn take, megadi ya bud'e mata gate aguje ta fice daga gidan. Wani irin burki ta take ganin mota dab da gate d'insu ana mata horn. Parking tayi acan gefen gate d'insu bata fito ba tana jiran ganin waye. Salim ya fito sanye cikin shigar k'ananun kaya, ya nufi motar. Idanuta d'an zaro tace. “Wannan ba saurayin Khairy ba ne?”
Glass ɗin motar ya ƙwanƙwasa.
Aziza ta janye glass ɗin tana leƙo da kanta, ƴan iskan akanta sai kawai ta nuna bata sanshi ba, ta haɗe face tana faɗin.
Lafiya malam?”
Salim cikin mamaki yace.
”Azizah Ya'u! Nine fa Salim Hisham saurayin Khairy Abdallah, Wanda mukayi haɗaka wajan cikin burinmu Allah baiyi ba Abdoul ya rasu.”
Fuska ta sake haɗawa tace.
”Toh ya kace kaima? Ya rasu kace ai kuwa kaga banda case da ku ayanzun...”
Murmushi yay

Please Login or Register in order to submit comment