Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Mamy da liman harda Hajja Hafasatu.
Waigowa yay yana motsa laɓɓansa yana kiran suna ALLAH, ya juya cikin wani irin sassarfa ya nufi bedroom ɗin nata.
Ƙofar ya murɗa ya shiga daidai ta fito daga bathroom, aguje ɗaure da guntin towel gashin kanta ya bazu ya rufe mata fuskar, ihu take tana neman faɗuwa jikinta yana wani ɓari.
Ganin Shattima ya shigo tayi kansa tana kece masa da kuka.
Yana ƙoƙarin riƙeta karta afka jikinsa, Amman Ina tuntuni ta ɗare jikinsa ta maƙaleshi tana wani irin rawar jiki da kuka tana faɗin.
“Dady ɓoyeni wlh tsoro nake ji.”
Ta faɗa cikin kuka tana rawar jiki tare da sake shigewa jikinsa kamar zasu zama abu ɗaya, tana cusa kanta tsakiyar ƙirjinsa.

Shattima da ƙyarta ya tattaro nutsuwarsa, sabida bai taɓa ganin surata haka ba kaya tin lokacin da ta balaga sai yau ɗin, yaci karo da santala_santalan baƙaƙen cinyoyinta masu taushi tsabar huta da cin me kyau, ga rabin ƙirjinta duk awaje, jikinta amurje ɓul_ɓul sai sheƙi take ga wadatattun cinyoyi masu sheƙi da taushi.
Yalwataccan gashinta baƙi ya zubo ya rufemata fuska.
Shattima yay saurin kauda idanunsa kanta, maƙalewa A jikinsa wajan Khairy ba sabon abu bane, sam baya jin wani abu Amman yau da ta kasance ba kaya jikinta sai guntin towel, yadda manyan albarkatun ƙirjinta suka manne masa suna bashi wata irin kulawa, sai da ya yay da gaske wajan saita kansa, ya tallabo fuskata ya janye gashin da ya rufe mata fuska, anatse cikin bata dukkan kulawarsa yana shigar da manyan fararen kaifafan idanunsa cikin nata idon, cikin kamilar muryasa yace.
"Baby! Menene kinga ki nutsu ki faɗa min me kika gani haka, kalleni faɗan Ok?"
Khairy duk ta gigice tsoro yasa ta fita hayyacinta, tana kulle idanunta da ƙyar take iya fizgo numfashinta wanda yake barazanar ɗaukewa tace.
“Dady! Ƙadangare yana ciki saman window na gansa ka kashesa Please Dady.”
Fuskata cikin tafin hannunsa yana hura mata iskar bakinsa ya ɗan mari fuskan kaɗan dan ta dawo hayyacinta yace.
"OK naji ki nutsu muje na kashe miki shi sai kiyi wankan, bari kukan haka ko kinason kanki ya fara ciwon wata sabuwar rigiman ki ta motsa?...”

Kai ta girgiza tana ƙara cakume shi ta ɓoye kanta ƙirjinsa tana ƙanƙameshi gamgam,.jikinta na rawa, tsakaninta da ALLAH mugun tsoron ƙadangare take.

”Wlh Dady bazan tsaya ba ni tsoro nake ji ƙatone wlh sai kallona yake, Ni nafasa wankan mutafi ka kaini wajan Mamynah hospital wlh bazan zauna ba.”
Shattima ya furzar da iska mai zafi waje daga bakinsa yana kiran sunan ALLAH.
Bai tsaya ɓatawa kansa lokaci ba yasan zatayi ta rikici ne saboda yadda take tsoron ƙadangare tin tana ƙanƙanuwarta.
Cak ya cicciɓeta sama yana rungume ta ƙirjinsa, anitse ya furta.
”Toh kukan na me ye kuma? ya isa haka.”
Ganin yana ƙoƙarin barin ɗanki da ita ya saka tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ta ƙara nitsa kanta ƙirjinsa tana shaƙo ni'imataccan ƙamshinsa, duk ta jiƙa masa gaban riga da hawayenta harda guntuwar majina.
Kai tsaye ɗakin Mamy ya nufa da ita bai yarda ya kalletaba, bai tsaya da ita falo ba ya wuce bedroom, can ma bathroom ya shige.
Direta yay yana faɗin.
”Oya kiyi wanka maza zan kawo maki kayan da zaki saka yanzun.”
Ya ƙasashe mgna ba tare da ya yadda ya kalleta ba, ya juya zai fita ta kamo hannunsa tana faɗin.
"Dady wlh duk atsorace nake Ni nafasa wankan nan fa!”
Juyowa yay yana kallonta adole.
Anitse ya furta.
“Baby! Ki nutsu ba komai anan zanje tarone kina ɓatamin lokaci da rigiman kin nan, ko kina so ni mahaifinki na miki wanka da kaina ne uhmm? Faɗa ina ji?”


Afuwa ba kullun zaku samu update ba, Amman insha ALLAHU zanyi iya ƙoƙarina naga ina baku ba tare da naja ba! Ina ƙaunar duk mai bibiyar labarin nan, saboda kuma ƙaunar ta saka kuke bibiyansa.😍
Rahma Ladingo Omu Farisah +22796515805.

*ALLAH ya jiƙanƙi ya miki rahama,Aishatou nah.😿😥*


_*YI WA KAI!*_

_November 24/11/2022_

_Free Novel_


Maganar mugun nauyi ta mata, ta zaro kyawawan matsagaitan fararen idanunta tana kwaɓe fuska, ta fara masa kukan zallar shagwaɓa tana sake damƙe hannunsa, ta girgiza kanta tana ɗan harba ƙafafunta,shagwaɓe tace.
“No! Dadyna ba haka nake nufi ba ai,ni tsoro nake ji da ka fita cizo na ƙadangaren zaiyi ko yakushina kasan ai ya raina mata, Ni kawai na fasa wankan gaskiya."

“Ya SALAM!”

Ya faɗa aransa yana janyota cikin jikinsa ya maida hannayensa ya kulle, ya ɗan rankwafo saitin kunnenta anutse cikin kamilar muryansa mai taushi ya ce.
“Na zauna na sakaki gaban kina rigima kin nan da bata ƙarewa karna fita ne? Dubi yadda kika cakumemin kayan jikina baby, ai kin kyauta koh?”

Wani baƙon yanayi Khairy taji wanda bata taɓa jina irinsa ba, take taji wani abu ya tsikareta tin daga tafin ƙafarta ta dama har tsakiyar kanta sai dai kasancewar kallon uba da take masa bata kawo komai aranta ba, ta basar tanajin Amman wata irin kasalar da bata san ta meye ba sai ta dauka duk cikin tsoron ne ta girgiza kanta ta ɗago tana kallonsa da matsagaitan lumsassun fararen idanunta da sukayi jajir.
Cikin Sa'a ita yake kalla amma iya ƙwayar idanunta.
Shigar idanunsu waje ɗaya a wannan lokacin wani irin babban al'amari ne Ubangiji ya saukar musu cikin zukatansu, da ya sanya bugun zuciyarsu lokaci ɗaya, wanda ya saka Khairy saurin rintse idanunta, tanajin matsananci faɗuwar gaba.

Baki ta turo masa gaba tana buɗe idanun nata tana rau-rau da idanun ahankali tace.
”Toh Dady kayi haƙura sai ka sake wasu kayan, Ni ban ce ba ka zauna Amman tare zamu fita, kuma ka tsaya ƙofar nayi wankan karka gusa, idan na gama na shirya sai ka kaje ka kashe ƙadangaren sai mutafi ka kaini wajan Mamy pls. Dady yau idanunka tsoro yake bani me ka saka ciki?”
Tai maganar tana rufe idanunta.

Idanunsa ya janye daga kallonta yana sake linka jarumtarsa, cikin taushin murya yace.
“Ok maza haɗa ruwan kiyi wanka.”
Ya faɗa bai tsaya bata amsar shirmen mgnarta ba, yana janyeta daga jikinsa, ya fice ya janyo mata ƙofar yana faɗin.
"Kul naji kinyi wata mgna anan ina tsaye oya yi wankan.”

Jin abinda yace ta cire towel bata tsaya ɓata lokaci ba, ta kunna shower ta ɗauki hadadɗan sabulun Mamy na ruwa da tattausan sosanta ta matse sabulun mai ƙamshi da samtsi ta fara cuɗe jikinta tana faɗin.
”Sweet Dady nah kana kusa koh?”
Zazzaƙara muryasa taji yana faɗin.
“Yeah daughter.”
Jin muryansa yasa ta saki jikinta tana wankata anutse.
A hankali ya fice daga bedroom ɗin, yana fitowa falon ƙofar abuɗe ya fice ya koma sashen Khairy.

Bathroom ɗin ta ya shiga ya nemi ƙadangaren bai gansa ba, ya rufe window ya fito ya janyo ƙofar.
Ƙatuwar wardrobe ɗinta wacce take shaƙe da kayan sawarta ya buɗe kaya kamar banza kala² kowane kala layinsu daban.
Wata abaya black mai shegen kyau taji adon stones buɗaɗɗiya wacce bazata kama jiki ba, sai ƙyalli take.
Zarota yay da mayafinta sai ƙamshi take kamar yanzu aka fesa mata fitinannan turarenta mai Bala'in ƙamshi.
Rufe wardrobe ɗin yay ya koma wajan takalma.
"Oh! Baby wannan takalma kamar za'a buɗe shago?"
Mara tsini ya zabar mata baƙi mai maɗauri.

Yana isowa falon Mamy ya dinga jin ihunta, tana kiransa.
Shigowa bedroom ɗin yay tana tsaye ɗaure da ƙaton towel tana rarraba idanu.
Harara ya watsa mata cike da kamewarsa, muryansa mai taushi da nutsuwa yace.

"Zo nan.”
Wayansa ta ɗauki ringing Wanda shine Kira karo na 4...
Hannunsa dayan wanda baida kaya ya zura cikin aljihunsa ya zaro wayan.
Ganin sunan Usman ya saka shi ɗagawa tare da Kaita kunnensa.

Usman ya masa sallama yana faɗin.
“Yallaɓai na iso dutse yanzu."
Shattima cike da nutsuwarsa tare da kamewa ya furta.
”Masha ALLAH sannu Usman Ngd matuƙa
ka iso gidan ina jiranka."
Usman ya amsa da.
"Ok an gama insha ALLAH."
Sallama sukayi, ya kalli Khairy da take raba idanu.
Yafitota yay da hannu, yana beƙa mata kayanta.

Da sassarfa ta nufosa tana son sakin kuka tace.
"Ga Ni Dady wlh motsi naji a toilet din inata kiranka baka amsaba shi na fito.”

"Ok kina nufin bakiyi wankan ba? Zo nace koh.”
"Nayi Dady kayi hƙr dan Allah karka dakeni kaji?”

“Da ina dukanki ne yanzu da zan dakekin? Zo mana jirana ake fa! Baby”

Ƙwalla shagwaɓa ta matso tana yarfa hannayenta

Bai mata magana ba kallonsa kawai yake yadda jikinta yake wani irin sheƙi yana fitar da ƙamshin sabulun da tai anfani da shi.
Anitse ta ƙaraso wajansa taja tsaya gabansa kamar zata shige jikinsa kanta ƙasa, tana matsar hawaye.
Bai ce mata komai ba ya kamo hannunta yajata, suna tafiya.

A gaban dressing mirror ya tsaya yana janyo stool ya zaunar da ita, anutse cikin kamewarsa yace.
"Yi sauri ki shirya ina mota amshi kayan ki, karki ƙara wani turare ajikin kin nan na rigar ya isa."
Ya faɗa yana juyawa zai bar wajan da wani irin sauri, yana sauke zazzafan numfashi.
Ganin zai fita ta kamo hannunsa da wani irin sauri ta langwaɓar da kanta kalar tausayi cike shagwaɓa tace.
”Dadynah wallahi duk atsorace nake tsaya na shirya mu fita tare dan ALLAH."
Shattima ya shafi sumar kanta mai samtsi ya tattara gashin ya ɗaure mata yace.

"OK Baby sakeni toh."

Sakin hannunsa tai ya koma kan babbar
Turkish chairs wacce take ita ɗaya ƙwal acikin bedroom ɗin Mamyn sauran a falonta, lumewa yay ciki yana sauke ƙaton numfashi, ya lumshe idanunsa yana jingina bayansa, tare da furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa.

Khairy anitse ta shafa manta ganin Dadynta yana nan zata saka kayan taga ba bra da pant ta ɓata fuska amma tasan ba yadda za'ayi Dadynta ya ɗauki mata, ita pant tafi so bra ba damunta yayi ba.
Anitse ta iso wajansa ta zauna tana kwantar da kanta ƙirjinsa ashagwaɓe ta kirasa.

”Sweet Dadyna!"

Kaifafan idanunsa ya buɗe ya kalleta, yana kauda kasan murya can ƙasa yace.

”Baby meke damunki ne yau wai uhmm?”

Tsintar kanta tai da rungume shi tana sakar masa kukan da babu dalili sabida wani shaukinsa da yake ɗibarta ba tare da tasan shaukin bane, da wani abu mai girma da batasan meye ba ya riƙe mata zuciya, idanunta zuciyarta gangar jikinta jininta ɓargonta komai nata ayau Sweet Dadynta ne...

Ƙasa² ya kalleta Tsaf ya gano me take so da bai dauko ba kuma yasan bazata iya faɗa masa ba.
Gaza magana yay kawai ya maida hannayensa duka ya zagaye bayanta ganin kamar jikinta na ɗan rawa, ya shiga buga bayanta idanunsa a lumshe, bakinsa dab da kunnenta ya rada mata.

”Tunda bakya buƙata naje taron da ake buƙatar ganina acan, mu zauna a haka Baby, idan lokacin juma'a ya kusa dole zan fita, muje kiyi breakfast Kisha maganinki.”

Yay mgnar cikin wata kasalalliyar murya mai kashe gaɓɓan jiki, yana jan tsinin hancinta.
Baki ta mele gaba akasalance ta kirasa.
"Dadyna!"
Yatsarsa ya ɗora bakinta ƙasa-ƙasa ya furta.
"Ba dai hakan kike buƙata ba? Yau ko breakfast baki bari munyi ba, tashi ki shirya maza."

Shiru tayi masa tana yin luf abinta ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya, anutse tace.
"Dadyna zanyi breakfast."

“Ikon ALLAH!"

Abinda Shattima ya furta kenan, ya dagota cikin daure fuska yace.
”Wlh zan rufeki aɗakin nan nayi tafiya ta, na baki 2 minute ki shirya.”

Marerece fuska tayi kamar zata fasa kuka tace.
"DADY kayi haƙuri nima yau haka nake jin son zama da mahaifina dan ALLAH Dady karka fita, mu zauna ahaka ka bari sai zuwa 12 katafi masallaci kaji?”

Bai yadda ya kalleta ba, ya janye ta daga jikinsa ya miƙe yana faɗin.
"Ki sameni ƙasa a falo.”

Dole haka ta saka kayan ba bra ba pant dan bazata je ɗakinta ba, atsorace take.
Yana sauka ƙasa ko zama bai gama yi da kyau ba,yaji takun saukowarta.

Kallon hayar stairs yay, ya hangota alamun tsoro ƙarara a fuskarta, tana yarfa hannunta na dama.
Laraba ya kira tana isowa itama tana isowa anutse yace ma Laraban.

"Ki rakata ɗakinta tayi abinda zatayi yanzu ku dawo, fatan kin fahimci rakiyar da za'a miki Baby?”

Baki ta zumɓuro kamar zatayi kuka tana dira ƙafafunta.
Laraba ta kama hannunta suka nufi upstairs.

Shattima ya girgiza kansa yana miƙewa ya nufi kan dining area.
Tea me kauri wanda yaji kananfari da citta, ya haɗa yasha madara ya fara kurɓa baya jin zai iya cin wani abu yanzu.
Kalaman Mamy suka dawo masa lokacin da take roƙonsa yaci wani abu kafin ya fita. Tattausan murmushi ya saɓa e masa, murya marar sauti ya furta.
"My Billy tawa Ina son matar nan yawa dayawa."

Tass ya shanye tea ɗin cikin kuzari da jin daɗin sa abakinsa.

Farfesun kan rago da wainar shinkafa ya zuba, wanda yawun sa ya fara tsinkewa tin kafin ya fara ci, ya sakawa Mamy albarka saboda duk abinda yafi so shi take girka masa, bata taɓa bin son abinda tafi so ba.

Lomar ɗaya ya shaƙo ƙamshinta, kafin yaji tana kiransa kamar zatayi kuka.
Gyaran murya ya yi da ɗan ɗaga murya yadda zata ji shi.
Ai kuwa da saurinta ta nufo kan dining area ɗin.

Kujera kusa da shi taja zata zauna yace.
"No! Baby miƙe maza je ɗauko basket ki saka warmers ɗin abincin da plate da cup da flaks idan kinje can wajan Mamynki sai kiyi breakfast."
Bata musaba tace.

"Tom Dady."

Ta faɗa tana sanya tattausan tafin hannunta ta goge masa miyar da ta taɓa gefen haɓarsa, wato kan kyakkyawan gemonsa.
Kallonta yay yace.
"Oya mana Baby kina akin da ba'a sakaki ba."
Dariya tai ta yago tissue tana tallabo fuskarsa tana goge masa ashagwaɓe tace.
"Allah Dady sai na goge maka bakinka haka kawai ka manta ka fita da miya akan gemun nan mai kyau."

Uffan bai cemata ba ta goge masa tana dariya, har bata san lokacin da kwanto jikinsa ba, tana ciga da kallonsa, yadda yake cin wainar da naman ragon.
Gyara murya yay cikin muguwar dauriya da jarumtarsa, yana watsar da baƙon yanayin da yake kawo masa farmaki gama da ita, ya watsa mata Harara cikin kamewarsa yace.

"Allah zan hanaki fitar nan."

Da suari ta janye daga jikinsa ta tafi tana basa haƙuri...

Sai da Shattima ya canza wani haɗaɗɗan boyel milk colour Wanda yafi wancan kyau da tsada, sabida wancan Khairy ta ɓata masa shi da cakuma da hawayenta, harda majinarta.

Wata baƙar Jeep me maiƙo da sheƙi jibgegiya mai baƙin glass nan aka buɗe musu suka shiga, Shattima ya kame abayan motar yana amsa waya tare da duba wani saƙo ta email.

Khairy gefe zaune tana kallon wayanta tana dubawa taga batada kuɗi aciki.
Lokacin da Maleek yaja motar ya nufi haɗaɗɗan ƙaton gate ɗin.

Shattima yana ajiye wayan, yana danna wacce yake duba saƙonnin email, anutse cikin taushin murya yace.
"Maleek! ka hanzarta guri na ƙuremin."
Ya faɗa yana ɗaukan wayansa da ta fara ringing.
Ganin Usman kai tsaye ya ɗaga yana faɗin.

”Na'am Usman!"

Usman da yake dab da isowa bakin gate yace.
"Yallaɓai na iso."
"Madallah gamunan fitowa ka biyoni baya Ok?"
Usman ya amsa da.
"Ok yallaɓai."

Motar na fitowa Usman yabi bayansu yana santin narkekiyar Jeep ɗin.

Khairy ta kamo hannunsa tana matsar ƙwalla tana kallonsa.
Kallonta yay baiyi yinƙurin janye hannunsa ba, anutse cikin kulawarsa gareta, ahankali ya ɗago haɓarta da hannunsa wanda bata riƙeba yana kallonta wanda dole tai ƙasa da idanunta, sabida wani irin abu da yake shigewa cikin idanunta daga lokacin idanunsa suna bin dukkan illahirin jikinta.
Ta turo baki gaba tana kwaɓe fuska.
Anutse ya ce.

"Me kuma akayi yanzu anan ɗin? Yau duk meke damunki daughter?"

Jin yadda yake mata mgna cike da kulawarsa, yana riƙe da haɓarta kaifafan idanunsa akanta, ga fitinannan ƙamshinsa mai kashe gangar jiki, ta kifa goshinta akan tafin hannunsa, laushin hannunsa da ƙamshin na sakar mata da kasala.
Bai tanka ba, yaci gaba da duba wayansa.
Can yaji akasalance tana faɗin.
"Sweet Dadyna banida kati awayana."

Murmushi mai bala'in kashe garkuwar jiki ya suɓuce masa, baiyi magana ba, ya mata trensper credit mai Yawa.
Jin text ya shigo wayanta ta ɗago kanta tana kallon wayan.
Dariya tayi tana faɗin.
"Wani abun sai Mahaifinka wlh Dady i love U thank u Ubangiji ya ƙarama buɗe da arziƙi na halalinka yabar ka da Mamynah muahhh Dadyna."

Ta ƙarashe mgnar tana basa sumbata akumatunsa.
"Yaji daɗin Addu'arta ya shafi gefen fuskarta, anutse ya amsa da.
"AMEEN ya RAHEEM Baby."

_*Khairy clinic and maternity*_

A bakin gate Maleek yay parking.
Shattima ya kalli Khairy, ya kamo lallausan hannunta, ya saka mata ledar maganinta, anutse cikin bata dukkan kulawarsa ya furta.
"Daughter! kinacin abinci yanzu Mamynki ta baki magungunan kishi wlh idan baki shaba bazan kaiki Abuja wajan Aunt Aisha ba.

Fuskarta ta narkar tana son sakar masa kuka, tana kallonsa tace.
"Dadyna tafiya zaka yi ka barni? Ni zan bika kaji?"
Kallon mamaki yake mata ya girgiza kansa anutse cikin sigar lallashi yace.
"Ok jeki anjima zanzo na daukeku muje yawo bayan sallar juma'a keda Mamynki, oya jeki, ki kama bakinki nan saura kima Mamyn ki wata magana daban ko rikicinki nan na rashin baki mari."
Ya ƙarasa mgnar yana jan kumatunta.
Zata narke jikinsa
Ganin fuskarsa ba Wasa ya saka ta manna masa kiss a kumatunsa tana gyara masa hular kansa har lumfashinsu na gauraya waje ɗaya.

Idanunsa ya ɗan lumshe yana kiran sunan ALLAH, kafin ya sake kame kansa ya kama hannunta yana kallon ƙwayar idanunta, anutse yace.
"Jeki Baby nayi lati dayawa."
Kai ta ɗaga tana ƙoƙarin buɗe motar taga an buɗe mata ta fito, aka rufe motar ta isa wajan booth Maleek ya beƙa mata basket ɗin.
Ta amsa ta ɗagawa Dadynta hannu duk da bata ganinsa shi yana ganinta.

Shigewa tai cike da nutsuwarta take tafiya.
Motar Maleek yaja yabar bakin gate.
Shattima ya ɗan miƙe ƙafafunsa, ƙasan kukeran yana sauke wahaltaccan numfashi, yana lalubo handkerchief cikin aljihunsa ya shiga goge zufar goshinsa da wuyansa yana furzar da zazzafar iska mai ɗumin gaske.
A hankali ya furta.
"Baby dole zaki wuce Abuja wajan Auntie Aisha."
Idanunsa ya buɗe ya ɗauki iphone ɗinsa ya lalubo lambar Aisha ya kirata.
Lokacin cikin Sa'a wayan tana wajanta tana ganin Shattima ta ɗaga tare da sallama cikin sigar tsokana tace.
"Assalamu alaikum ango kasha ƙamshi mijin mace biyu. Ina Bilkisu da Baby luv?"

Shattima ya sake furzar da iskar bakinsa waje, yana ƙara saita nutsuwarsa, anatse ya amsa sallamar yana faɗin.

"Ah Aunt tsokana, hopa kuna lafiya? Yasu Ilham da Suhal? Da labarin su Marfu'ah?"
Cike da kulawa ta amsa masa.
"Duk suna lafiya, yasu Khairyn?"
Shattima ya shafi sajansa yace.
"Duk muna lfy but Auntie abinda nakeso kizo dan Allah ki tafi da Kahiry wajanki, please idan bakida uzuri kuma yayanmu ya aminta kizo dan ALLAH, ba sai kin kwana ba ki shigo jirgi ko zuwa gobe ne kafin kizo zan saka amuku booking tickets na tafiya."
Auntie Aisha bata tsaya bincike ba ta amsa da.
"Ok insha Allahu zanzo gobe sai ku shirya, Amman ka sani ina kawota shiryata zan fara yi."
Shattima bai musaba yace ya amince da duk abinda za'ayi matan, burinsa suyi nesa da juna idan ba haka za'ayi abin kunya...

Khairy lokacin da ta shigo office ɗin Mamy bata nan, tana dakin tiyata.
Zamanta tayi ta baje ta haɗa tea mai kauri ta sha, ta zuba wainar guda uku ta saka wadataccan naman kan ragon taci tayi dam, taƙi shan maganin ta tattare komai ta maida basket taje ta wanko hannunta tazo ta zauna ta kira lambar Suhailat ƙawarta.
Bugu ɗaya na biyu Suhailat ta ɗaga tana sakin ihu tace.
"Besty! Ina kika ɓuya! Inata missing ɗinki? Nagaji da kiran wayanki kullum acemin switch of, har Ina Shirin komawa Abuja jarabawar da muke ta hanani, nace kawai ƙarya kike ranan da kika mukayi charting, kikace kin dawo."

Khairy ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Dallah can kizo yanzun nan na dawo Dutse, da gaske tin ranan kawai banda lafiya ne, gani hospital ɗin Mamynah kizo musha fira, ko kina school?"
Suhailat tace.
"Wayyo daɗi toh ganinan zuwa yanzu, A'a wlh rasuwa akayi sai Monday muda school, zan zo anjima insha ALLAH ya jikin naki?"
Khairy tayi fari da kyawawan matsagaitan idanunta, masu haske, tace.
"Na warke abuna, kizo yanzu kafin Mamy tazo muyi wata fira mai daɗi."
Suhailat tace.
"An gama ganina zuwa."
Khairy ta katse kiran tana ajiye wayan ta miƙe saman kujeran tana buɗe hancinta tana shaƙar ƙamshi Dadynta da ya gauraya da jikinta.
Idanunta ta lumshe tana turo baki gaba ashagwaɓe ta kirasa kamar yana gabanta.
"Sweet Dadynah!"
Ta faɗa har gashin jikinta na mimmiƙewa, hakan yasa ta lafe jikin kujera tayi lamo, ƙamshin jikinta wanda ta kwasa jikin Dadynta ya gauraya da nata ya sakar mata da kasala.
*After 30 minutes*

Kwance take saman kujeran bacci ya saceta, mai cike nutsuwa da nishaɗi, da ganin baccin kasan yana mata daɗi.
Mamy ce ta shigo tana cire ɗan hijabin jikinta tare da rigar aikin, ta ƙura ma Khairy.
"Ah Baby tin yaushe tazo? Harda bacci, oh! Rigimammiya."
Ta faɗa tana isowa wajan ta, ta sunkuya tana gyara mata hannunta da ta tanƙwashe sa.
Ƙamshin Shattima ya daki hancinta, wanda yake tashi jikin Khairyn.
Wani abu taji mai girma ya daketa, azuciya, sai tayi murmushi, tana lakatar hancin Khairy, ƙasa² ta furta.
"Zakuma gama niƙu_nuƙun ku bayyana soyayya gaskiya, Allah ya kaɗe dukkan wata fitina tsakanin mu Amin, oh! Ina kaga Baby da cikin Dadynta."
Ta faɗa tana murmushi hawaye nabin fuskarta, ta nufi kan kujeran zamanta, ta ajiye kayan hannunta ta shiga toilet.

Cikin Baccinta mai daɗi taji ana knocking ɗin ƙofar.
Miƙa tayi cike da jin daɗin baccin ta buɗe kyawawan matsagaitan idanunta, tana yamutsa fuska, ta miƙe zaune akasalance tana miƙa.....


*YI WA KAI!*

_November 25/11/2022_

*Free Novel*

Ina wa kowa Barka da sallar Juma'a🕌, ALLAH ya karɓi ibadun mu AMeen.


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*67&68*


Miƙa take cike da kasala, tana kalmar shahada.
Ta miƙa tsaye tana lumshe matsagaitan fararen idanunta, wanda suke cike bacci, ta nufi ƙofar sam bata ma san Mamy ta shigo ba, zatonta Mamy ce.
Tana buɗe ƙofar sukayi ido huɗu da Suhailat.
Tsalle tai ta afka jikin Suhailat suka rungume juna suna dariya.
Khairy tace.
"Ashe zaki zo akan lokaci besty?"
Suhailat ta kai mata dukan wasa tana hararenta tace.
"Ai na saba maki ƙarya..."
Ƙaran bud'e ƙofar toilet sukaji suka saki juna suna waigowa.
Khairy tace.
"Lah! Mamy! Yaushe kika shigo?"
Ta faɗa tana nufar Mamyn da sassarfa ta rungumeta, tana dariya.
Mamy ta kai mata dukan wasan ta yi murmushi tace.
"Kinata baccinki na shigo, fatan kinsha maganinki Baby?"
Khairy ta shiga rarraba idanunta, tana kame-kame.

Suhailat ta gaishe da Mamy cikin girmamawa.
Mamy ta kamo hannun Khairy'n tana amsawa cikin kulawa, tace.
"Ya mutan gida Suhailat? Kwana biyu kin ɓuya? Ki zauna mana kina tsaye."
Mamy ta faɗa tana ɗaukan ledar maganin da tagani ajiye saman table ɗinta.
Suhailat ta zauna tana dariya mugunta ganin ɗura magani za'a ma Khairy.

Mamy ta zaunar da Khairy ta haɗe face tana ɓallo magungunan tace.
"Haaaa bakinki."
Khairy kamar zata fashe da kuka ta ɗaga bakinta tana rau-rau da idanunta.
"Oya haɗiye wadda bata son shan magani."
Ta ƙarashe maganar tana kafa mata robar ruwa bakinta.
Idanunta ta rufe tana damƙe hannun Mamyn ta haɗiye maganin adole.

Suhailat har ƙyaƙyatawa takeyi tsabar mugunta, ganin yadda Khairy take neman sakin kuka.
Mamy tace.
"Suhailat ki haɗa mata da ihu ma tunda ita kam bata ƙaunar magani, gata bata gama warware wa ba, laifin Mi Amor ne da bai dakeki ba kika sha ta ƙarfi, ya wani kawo min ke. Baby haɗomin tea ɗin idan kin rage."

Mamy ta ƙarashe maganan tana nufar kujeran zamanta ta sanya gilashi ta buɗe wani files tana dubawa.
Khairy ta kwanta saman kujera ashagwaɓe tace.
"Sweet Mamy ki sheda na ɓata da Suhailat."
Tai murmushi tace.
"Ai kam itama dole zata rabu da mai ƙin shan magani Ah toh."
Baki ta turo gaba tana harba ƙafafuwanta.
Suhailat dariya kawai take Mamy tana aikinta.
Khairy ta miƙe ta haɗo Mamy tea ta kawo mata, tana kwantar da kanta kafaɗarta Mamy tana sakin nishin ciwon kan da takeji na saukowa.
Mamy ta kurɓi tea ɗin ta ajiye tana taɓa kan na Khairy tace.
"Oh! My God! Kin gani koh Baby, da kinsha maganinki kan lokaci kanki bazai yi ciwon haka ba, je ki kwanta ajima mugani."
Ta faɗa tana kamata suka nufi kan kujera tana langwaɓe wa.
Mamy tace.
"Yarinya sai ragwantan ciwo haba! Zanga yadda zakiyi idan..."
Sai kuma ta haɗiye maganan bata ƙarasa a.
Hijab ta rufa mata, ta koma ta zauna tana aikinta tace.
"Suhailat kin ga rigimammiya bestynki koh? Ciwon kaine ake zabgewa haka."
Suhailat tace.
"Mamy ba zanyi dariya ba taban tausayi."
Mamy ta kurɓi tea tana murmushi tace.
"Bari na gama da files ɗin nan mutafi gida."


Ɓangaren Shattima.

Kai tsaye wajan taron ya bada umarnin Maleek ya kaisa yana sake sanyawa kansa nutsuwa.
Yayin da Usman yake biye da shi cikin motarsa, yana mugun mamakin kamarsa da yarinyar da yaga ta sauka a motar Shattima ta shiga hospital.
Anatse ya furta.
"Wannan kamar fa? Kamar Nadiya kamar Ni kamar Dad ikon Allah!"
Usman ya faɗa yana tuƙinsa cike mamakin wannan al'amari.

A parking spaces Maleek yay parking, securitie'nsa ƙwallon ɗaya da sukazo ya fito ya buɗewa Shattima ƙofar ya fito anatse acikin kamewarsa, yana nufar wajan motar Usman, yayin da securitie'nsa ya ɗauko masa wayoyinsa da wata zungureriyar envelope, ya rufo motar ya take masa baya.
Usman yana rufe motar ya nufo Shattima tin bai ƙara so ba.
Zai rusuna Shattima ya kamo hannunsa yana sakin tattausan murmushin sa mai tsada anitse cikin kamewarsa yace.

"Barka da isowa Usman haƙiƙa naji daɗin zuwanka gayyatar da na maka, ya hanya?"
Usman ya amsa da.
"Ai Yallaɓai ka wuce komai awajena,

Please Login or Register in order to submit comment