Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tokare mata ƙahon zuciyarta.
A hankali ta buɗe baki tace.
"Ya ALLAH ka mallaka min Dady Shattima ina sonsa wallahi."
Ta faɗa tana goge hawayen da yake silalowa kan fuskarta.
Ma'adanar lambobi ta shiga, lambar Shattima da tayi saving da.
( *MURADIN ZUCIYATA*)
ta saki murmushi ta fara ƙoƙarin kiransa taji motsin mutum, da sauri ta fita daga ma'adanar lambobi, ta ajiye wayan gefenta, tana rarraba idanu.

Ammi ta shigo ɗakin tana kallonta tace.
"Wai ke kam Maryam! Wani mugun haline kika koya, zaman ɗaki? Me kike da wayan da kika ganin kika ajiye? Mugani."
Ammi tace tana beƙa mata hannunta fuskarta ba wasa.
Maryam ta langwaɓar da kanta gefe tace.
"Wallahi Ammi ba komai, kawai ina tunanin Ya Abdoul ne."
Sai hawaye shar suka gangaro mata.
Ammi ta zauna gefen bed ɗin tana girgiza kanta ta kamo hannunta, tana ƙura mata idanu, tana kallon yadda yarinyar take ramewa, bakinta duk ya bushe,Maryam batada lafiya kana mata kallon farko zaka san akwai abinda yake damunta tana ɓoyewa ne.

"Maryam! Ni fa mahaifiyarki ce, kinada waɗanda suka fini ne aduniya?"

Maryam ta girgiza kanta.

"Ok toh me yake damunki dan ALLAH ki faɗa min idan dai kin yarda duk duniya bakida waɗanda suka fi mahaifiyar ki, zan kuma share miki hawayen ki."

Maryam sai taji kwaɗayin son sanar da Ammi gaskiya, amman idan ta tuna kyakkyawar alaƙar da take tsakanin Mamy da Ammi tasan bazata taɓa yarda ta goyi da bayanta ba!
Tabbas ɓoye mata shine mafi a'ala, dan tasan halin mahaifiyarta, bazata bata goyon baya ba.
Ƙasa tayi da kanta tace.
"Wlh Ammi iya gaskiyata na faɗa miki mutuwar Ya Abdoul tana taɓani fiye da zatonku, na kasa ciresa araina bayan shi banida wata damuwa Ammi ki tuna kafin rasuwar sa baya ba haka nake ba."
Ammi ta jinjina kanta azahiri ta nuna mata ta yarda,amma acan ƙasan zuciyarta bataji ta yardaba dole sai ta ɗana mata tarkon da zata gano gaskiya kar taje tayi sake ƴarta ta mace abanza a hofi.
"Toh Maryam ya zamuyi dole haƙuri zamuyi, muci gaba da masa addu'a, kalli fa yadda kike rama, kinsan kuma Mamynki Bilkisu tace a kiyaye ɓacin ranki, zuciyarki ta samu matsala, shiyasa bana son kina keɓance kanki ke ɗaya kina tunani tashi muje falo."
Ta faɗa tana kama hannunta.
Maryam ta miƙe tana faɗin.
"Toh Ammi bari na shiga bathroom na fito zan fito wallahi kuwa."
Ta faɗa tana murmushi.
Ammi tace.
"Ok maza kizo ina jiranki."
Kai ta jinjina ta nufi bathroom.
Ammi tana fita ta fito ta ɗauki wayanta ta shiga ma'adanar lambobi tana ƙoƙarin sake kiran Shattima.

Can kuwa Katsina Khairy
Dakewa ta yi ta ƙaraso kusansa ta tsogunnna, ta ajiye tray'n gabansa, anutse tace.
"Dady barka da yamma ina wuni?"
Ta faɗa tana serving ɗinsa.
Muryasa mai cike da daɗin sauraro cike da bata kulawansa, anutse yace.

"Lfy lau Baby, kinyi bacci dayawa koh?
Hope kina lfy? baki tash da mura ba?"

Ya ƙarashe maganar, yana kafeta da kaifafan idanunsa masu karya mata garkuwa jiki, sosai yake kallon kyakkyawar baƙar fuskarta.
Bata yarda ta kalleshi ba ta jinjina kanta, tana haɗiye wani guntun yawu sbd jin maƙoshinta ya bushe lokaci ɗaya.
"Alhamdulillah Dady normal nake. Ina Mamynah?"
Ta tambayesa tana miƙewa tsaye, da niyar ficewa.
Tattausan tafin hannunsa taji cikin nata tattausan hannun, anutse ya janyota ta dawo baya ya zaunar da ita saman katifar dab da shi, yana sakin hannun nata.
Kallonsa ta yi tana ƙif-ƙif da idanunta, ta sadda kanta ƙasa, tana wasa da zoben hannunta na diamond mai ɗauke da Harafin (U K)

Hannun da take wasa da shi ya kamo ya riƙe yana murza zoben, sai da ta ɗago ta kalleshi, tai ƙasa da kanta ƙarya take ta jure kallon Dadyn awannan lokacin, sabida idanunsa sun gama kashe mata sanssan jiki, haka kawai taji zuciyarta na wani irin bala'in bugawa.
Gudun karta kwabsa ya sake cemata marar wayo, yasa ta fara ƙoƙarin sai ta nutsuwarta, tana ƙoƙarin zame hannunta daga cikin nasa, tace.
"Dady! Bara na koma, zan haɗiyi maganin ciwon kai."

Shattima yay murmushi yana murza zoben hannunta, yay ƙasa da kansa, yana taɓa goshinta, yaji ba zafi.
Kusan sumar da ita yay lokacin da taji zazzaƙar muryasa dab da hancinta, ya kirata.
"Baby! Kanki babu zafi fa, kiba Dady abinci yaci, wai me yake damunki duk kin canzawa Dadynki uhm daughter? Kalle mugani amshi Baby."

Ya ƙarashe maganan yana ɗago fuskarta da tafin hannunsa, ya shiga hura mata iskar bakinsa mai ɗumi tana fitar da wani irin azababban ƙamshin da bata isa ta tantance kalarsa ba.
Wani irin yanayi ta tsinci kanta, wanda ta rantse batasan kalar yanayin ba.
Abu ɗaya ta sani adaidai lokacin nan bazata jure ƙin masa shagwaɓa ba.
Kallonsa tai tana shaƙar iskar bakinsa me ƙamshin daɗi da yake huramata akan fuskarta, ta damƙe tafin hannunsa cikin nata, wani irin ɗumi da taushi sukaji lokaci guda.

Tai wani irin narkar da fuska tana kallon tsakiyar idanunsa, da wani kalar shagwaɓa ta kirasa.
"Sweet Dadynah!"
Goshinta ya mannawa kiss yana murmushi anutse da amon muryasa mai daɗi ya amsa.
"Na'am Sweet daughter menene? Faɗamin naji, bakida lfy?"
Fuskarta tai kalar tausayi tana ƙasa da kanta, ahankali tace.
"Dady kaci abincin."
Ta faɗa tana sake tura tafin hannunta cikin nasan.
Janyota yay baki ɗaya ya shigar da ita cikin jikinsa.
Atare suka sauke ajiyar zuciya mai sauti da wani irin wahaltaccan numfashi suka ja tare, suna kallon junansu.
Idanunta tai saurin lumshewa, tana cinno masa baki gaba, ta tura kanta ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Shattima yay murmushi yana manna bakinsa akan kunnenta
Anutse yace.
"Baby me Dady ya yi ne?"
Ƙanƙameshi tayi, tana murmushi ta buɗe idanunta tana kallon kyakkyawar bak'ar fuskarshi me cike da wani irin kwarjini, hannayenta ta saƙalo wuyansa, suna kallon juna.
Ashagwaɓe tace.
"Sweet Dady yau kayi wani irin kyau, Allah yasa Mamy ta haifo min ƙani me irin fuskar ka, har Black fatarka WoW zai sha lele wajena ALLAH Dadynah."
Ta faɗa tana ƴar dariya taja dogon hancinsa, tana taɓa sajansa zuwa gemunsa, ta shafa gazar-gazar in gashin idanunsa.
Shattima ya yi wani kakan murmushi mai narkar da zuciya, yana jan karan hancinta yace.
"Ameen Baby ke zakiyi renon ai."

"Yeah Dadynah Ina son ƙanne nayi girma dayawa, bari kaji na zanama kalar gatan da zan yi ma ƙannina Sweet Dady."
Ta faɗa tana juyi ajikinsa, tana dariya jin daɗin abinda Shattiman ya faɗa.
Ta fara lissafo masa.
Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska mai zafin gaske, yana kiran sunan ALLAH.
Ganin fa ita ko jikinta, tana cukuikuiye shi tana masa surutu, sai goga masa ƙirjinta take cikin hira batama san tanayin ba.
Da wani irin cool voice ya furta.
"Baby kiban abinci mana Please."

Ta janye jikinta ta ɗauko plate ɗin abincin ta tsakuro a spoon tana matsowa kusansa tace.
"Sweet Dady haaaaa na baka abincin kar ya wuce, kayi haƙuri Ni fa na manta ma wlh."
Ta faɗa tana marerece fuska.
Numfasawa yay, Hannunsa ya ɗora saman nata ya zare spoon ɗin yana mata wani irin kallo, ya janyota kan cinyarsa, ƙasa² ya furta.
"Baby tafi Dadynta jin yunwa haaaaa."
Ƴar dariya tayi tana buɗe bakin ya bata, ta shiga taunawa tana kallon abincin tace.
"Sweet Dady akwai dad'i."
Kai ya jinjina ya ƙara ɗebowa yakai bakinta ta amsa tana ci, ta sanya hannunta ta ɗebo abincin takai bakinsa.
Amsa ya yi dole ya haɗa da yatsunta ya ciza kaɗan.
"Aushhhh! Dady ka cijeni wayyo ni yatsana zafi."
Ta faɗa tana kwaɓe fuskarta kamar zatayi kuka.
"Oh! Sorry Baby ban kulaba muga yatsun."
Hannun ta beƙa masa tana son sakar masa kuka.
"Iska ya hura mata yana ɗora harshensa akan yatsun yana lasa anutse.
Khairy tai saurin kwantar da kanta ƙirjinsa tana sauke numfashi, tace.
"Sweet Dady wani..."
Sai tai saurin jan burki tayi shiru bata ƙara saba.
Tsotsar yatsunta taji yana yi hankalinsa kwance, ɗumi da sanyi na ratsa yatsunta, gashin jikinta na wani irin miƙewa.
Shattima ko ajikinsa yatsunta yake tsotsar su kamar Sweet.
Khairy kuwa baki ɗaya jikinta ya ɗauki vibration, tanajin wani baƙon yanayi, ta kasa janye hannunta, kamar an tsikare shi ya zare yatsun abakinsa, yana ɗagota, da fuskarta.
Idanu suka hada yaga idanunta sunyi ja harda ƴar ƙwalla.
Hura mata iska yay cikin idanunta, ya tsakuro abincin yakai bakinta.
Kuka ta sanya masa tana maida kanta ƙirjinsa.
"YA RAHMAN! Baby me kuma akayi?"
"Dady Ni dai bazan zauna ba anan babu kai ba tare zamu koma."
Ta ƙarashe maganar cikin shasheƙar kuka.
A kunnenta ya mata raɗa cikin kamewarsa ya fara magana anutse, murya mai taushi.
"Ok naji bari kukan idan naji kukan ki bana jin nutsuwata ajikina, ya isa haka, zakije yawo mutafi a mota? Idan anyi Maghreb?"
Ya ƙarashe maganan yana goge mata hawayen da tafin hannunsa.
Kallonsa tayi tana ɗaga masa kanta alamar "Eh zataje."
Anutse ya furta.
"Ok ki kasance da wayanki akusa zan kira ki."
Kai ta ɗaga tana wasa da zobunan hannunsa, ta lafe cikin jikinsa, tana shaƙar ƙamshinsa, tanajin nutsuwa na dawo mata sannu².
Anutse tace "Sweet Dady kasha lemon toh idan bazakaci abincin ba!"
"No! Baby na ƙoshi Mamynki ta ban abinci naci ɗazu."
Kallonsa tayi zatayi magana wayansa ta ɗauki ruri.
Sai da ya ɗan janyeta kaɗan ya zaro wayan cikin aljihunsa.
Ganin ba suna ya saka bai ɗauka ba, yana kallon Khairy ta janye jikinta tana miƙewa tsaye.
Shima miƙewa yay yana gyara rigarsa yadda ta tumurmushesa duk ta yaƙune.
Har zata ɗauki tryan kayan abincin taga yadda riga Dadynta tayi, ta fasa ta matso gabansa, tana tana ɗora hannunta akan rigan tana tayasa gyarawa ta marerece fuska tace.
"I'm sorry Sweetie Dady bansan nayi hakan ba kaji?"
Murmushi yay yace.
"Ok naji ɗauki kayan ki tafi."
Ƙiyawa tai taci gaba da tayasa, anutse tana masa surutu.
Wayan ta sake ɗaukan ruri akaro na biyar.
Khairy tace.
"Dadynah ka ɗauka mana Please."
Ta faɗa kanta tsaye tana zura hannunta aljihunsa tana ƙoƙarin zaro wayan.
Hannun ya riƙe yace.
"Baby ba suna bana ɗaukan lamba ba suna idan mutum ya matsu zaiyi min text."
Ƙafafuwanta ta fara diddirawa tana janyo wayan tace.
"Ni dai sai ka ɗauka Dady."
Ta faɗa tana zaro wayan ta beƙa masa tana rungumesa.
Picking call ɗin yay ya kai wayan kunnensa ba tare da ya yi magana ba.
Yaja hannun Khairy'n suka zauna yana kwantar da ita jikinsa ita kuma ta laɓe abunta tana kallonsa, tana murmushi tace.
"Sweetie Dady bakayi magana ba!"
Kai ya girgiza, yana lakatar hancinta.

Maryam daga can taji muryan Khairy da duk abinda ta faɗa, sai taji gabanta ya faɗa, wani irin kishin Khairy ya turniƙeta, amman ta dake tana saita nutsuwata tai ƙasa da muryanta.
"Assalamu alaikum Dady ina wuni? Maryam ce."
Shattima yay gyaran murya yana amsa sallamar tare da amsa gaisuwar cikin kamewarsa anutse yace.
"Ah Maryam! Kina lfy? Yasu Abbanki da Amminki?"
Cikin wani bala'in farin cikin ta ƙara lanƙwasa murya tace.
"Lafiya ƙalau Dadyna, ya Mamy?"
Shattima ya amsa.
"Lafiyarta lau."
Maryam ta sake narkar da murya tace.
'Dadyna zanzo nan gida wajankun Abba yace min kunyi tafiya, amma dai dan ALLAH Dady bazaku daɗe ba koh?"
Tayi tambayar kalar zatayi kuka."
Shattima ya amsa.
"Eh bama nan bazamu jimaba dota mungode da kulawa ki gaishemin da Amminki da Abbanki."
Maryam ta amsa da.
"Tom Dady idan ka dawo zanje gidan nayi muku kwana biyu."
Kansa ya ɗan shafa ya numfasa anutse yace.
"Ok sai mun zo."
Daga can Maryam tace.
"Thank you Dadyna Allah ya Kara maka lafiya bye ka huta lafiya."
Ta faɗa cikin farin ciki tana katse kiran.

Khairy tana turo baki tace.
"Wai Dady wacece wannan ɗin da kuka sha hira haka ne?"
Sumbatar hancinta yay yace.
"Maryam ƙanwarki ɗiyar Aminu fa!"
Murmushi tayi tace.
"Lah! Maryam ce Dady bari na saka kati zan kirata ai."
Anutse ya janyeta yana miƙewa ya furta
"Yawwa toh ya yi Baby muje."
Trayn ta ɗauka tana gaba yana biye da ita suka fito.

Zainabu na zaune ita da Inna ADAMA da su Jamilah, Nadiya na gefen Zainabu. Shattima ya musu sallama ya nufi ƙofa, Khairy ta rakasa da kallo, tana murmushi.
Kusan Zainabu ta zauna tana murmushi ita ɗaya.
Jamilah tace.
"Auntie Ummulkhairi ya dai sai murmushi kike ke ɗaya?"
Rungume Zainabu tayi tana mata raɗa akunnenta.
Zainabu ta zaro idanu tana dukanta abaya, ta ɗago fuskarta tana hararenta.
Khairy ta ƙyalƙyale da dariya tana ɓoye kanta kafaɗar Zaianbun.
Nadiya ta ƙura musu idanu cike da burgewa, ji take daman ita ce ahakan.
Hannun Khairy'n taji tana share mata hawayen da bata san ma tana yiba.
"Haba! Nadiya dan ALLAH ki daina kuka, bana jin daɗin hakan ki daina Please."
Kai Nadiya ta jinjina tace.
"Auntie bazaki gane halin da nake ciki bane."
Khairy tace.
"Nasan komai, bawa bai isa ya canza ƙaddara sa ba..."
Zainabu ta haɗasu ta rungumesu tana buga bayan Nadiya.

Kusan Liman Shattima ya zauna yana ƙasa da kansa,cike nutsuwarsa murya A kame yace.
"Baffa za'a kai ka masauki ne ko anan zaku kwana?"

Baffa liman yace.
"A'a kwana ɗaya kawai Abdallah, zan kwana ana amman Mustapha da Usman za'a kaisu su huta koh?"

Shattima ya gyara zamansa yace.
"Eh na kama musu ɗakuna har dasu Maleek ma, Anjima zamu tafi.
goben insha ALLAH, zamu biyo mu wuce, ku kasance cikin shiri."
Liman yace.
"Masha Allah, Allah yay albarka."
Shattima ya amsa da.
"Ameen ya Allah Baffa."
Liman nan ya labartawa Shattima abinda ya faru akan auren Zainabu da Mustapha, da sakin Karima da haukan da take tuburan.
Shattima ya girgiza kansa yace.
"Allah yasa mufi ƙarfin zukantanmu, ya tsaremana imaninmu."

Hira sukayi sosai sai da lokacin sallar Maghreb ta kusa suka fara ƙoƙarin alwala.
Bayan sallar Maghreb Shattima ya faɗawa Usman su shirya Maleek zai kaisu masaukin da zasu kwana.
Abbu ya sake raka Usman asibitin suka kai abincin dare, lokacin shegen YANKAN WUƘA ya saka an maido Karima kamar ba'a ɗauke ta ba.
Yanzu kam bakinta bata iya magana sai soshe-soshe na jikinta, baki ɗaya kamanninta sun fara canzawa.
Usman kuka kawai yake kamar yaro ƙarami yana faɗin.
"Mom kin cutar damu dayawa ki diba kiga halin da kike ciki ayanzun wa gari ya waya?"
Dariya kawai take tana kiran Mustapha da Zainabu.
Abbu ya jaza suka tafi.

Khairy tunda tayi sallar Maghreb take jiran kiran Shattima shiru bai kirata ba har akayi kiran isha'i nan ma shiru, taji kuma Abbu yana faɗin ya tafi.
Kasa cin komai tayi ta kwanta tanata duba wayanta ta kasa kiransa.
Sai tayi kamar zata kirasa ta kasa.

Ɓangaren Mamy Ana kiran sallar Maghreb ta farka da ƙyar ta sauko daga bed tana mike taje tayi wanka ta ɗauro alwala, tazo ta sanya kaya tayi sallar Maghreb tayi azkhar, ta miƙe ta fito falon ta buɗe sauran abincinsu ta fara ci tana korawa da lemon kwakwa.
Ƙaran buɗe ƙofar taji ta waigo da sauri tana kallon ƙofar.
Shattima ne riƙe da babbar leda alamaun shopping ya musu, anutse ya mata sallama.
Murmushi ta sakar masa tana kai spoon bakinta, tana masa wani sahihin kallon so ta amsa sallamar, tana faɗin.
"Welcome Mi Amor."
Kusanta ya zauna yana ajiye ledar akan table ya sumbaci kumatunta ya kamo hannunta me spoon, anutse cikin kamewarsa yace.
"My sweetheart wannan abinci ya yi sanyi bari akawo mai zafi."
Langwaɓar da kai tayi tana kamo hannunsa takai spoon ɗin bakinta tace.
"Yunwa nakeji Mi Amor. Wai Ina katafi yanzu fa na tashi sai wanka da salla da nayi."
Matsota jikinsa yay yana kallon kyakkyawar fuskarta, anutse yake bata abinci yace.
"Naje can gida wajansu Baffa da Baby kar suce mun ɓata."
Murmushi tayi tana kai masa sumba bakinsa, tace.
"Uhmm! Su Mi Amor bah!"
"Me ne nayi Sweetheart?"
Ƴar dariya tayi tana ɗaukan lemon ta sha sosai ta ajiye tana, faɗin.
"Alhamdulillah."
Shattima ya buɗe ledar kayan yace.
"Oya Sweetheart je ki sauya kaya kiji daɗi wannan sun ta kuraki."
Amsa tayi tana hamma tace.
"Yanzu ma baccin nakeji wlh bari nayi sallar Isha'i."
Shattima ya kamota ta zauna kan cinyarsa ya shiga ciremata kayan jikinta ya saka mata figigiyat rigar baccin, yana sumbatar ƙirjinta, yace.
"Oya je ki saka hijab kiyi sallar sai ki kwanta."
Kiss ta masa tace.
"Thank you Mi Amor."
Ta faɗa tana nufar bedroom.
Bayanta yabi ya sake kaya jallabiya fara ƙal ya saka ya fesa turare, ya fito falon, dan shi yayi sallar Isha'i tun can gida.
Tv ya kunna ya zauna yana lalubo lambar Khairy ya kirata.
Bacci ya fara fizgarta taji ƙaran wayanta, ta buɗe idanunta ta kalli wayan, ganin Dadynta ne ta ɗauka tana kiransa.
"Sweetie Dadynah! Na fara bacci ka zo ne na fito? Please Dady karka cemin A'A zanyi kuka ALLAH kuwa."
Yadda tai maganar sai da ya sauke wani ƙaton numfashi yana furzar da iska mai ɗan ɗumi daga bakinsa, anutse cikin kamewarsa yace.
"No! Baby kar kiyi kuka Please, kiyi bacci zanzo da safe kinji?"
Kukan ta sakar masa tana faɗin.
"A'A Dadynah kai fa ka sakamin arai ni ni sai kazo."
Shattima yace.
"Ok naji bar kukan bana sonsa, zanzo tunda bakya son naba Mamy kulawa."
Da sauri ta haɗiye kukan tace.
"A'a Dady ka bata kulawa kace tayi haƙuri dan ALLAH NI wasa nake maka, ban ita na bata haƙuri Dady."
Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa yace.
"Bazata taɓa fushi dake ba, kiyi addu'a kiyi bacci kinji?"
Kai Khairy ta jinjina tana amsawa da.
"Tom Dadynah insha ALLAH."
"Thank you Baby muahhh sai da safe."
Ya faɗa yana katse kiran.
Khairy ta ajiye wayan tana gyara kwanciyarta, tana sauke ajiyar zuciya tanajin hirasu su inna ADAMA harda Nadiya, daga waje.
Ƙwalla ta matso daga idanunta tana rufe idanu, bakinta na motsi alamar addu'a, take ba jimawa bacci ya kwasheta dan maganin bai gama sakinta ba.
Shattima wayan ya ajiye yana murza goshinsa yana sakin wani irin tattausan murmushi nutsuwa na shigarsa.
iPad ɗinsa ya ɗauka yana wani aiki da shi.
Mamy tana gama salla sai bacci.
10 pm yay Kiran ma'aikatan hotel aka kawo masa pizza da coffee yaci sosai yasha coffee ya miƙe ya shige bedroom.
Wanka yay ya saka kayan bacci, ya haye bed yaja duvet ya shige ciki yana rungumota jikinsa tsam, yana shafa cikinta yana faɗin.
"Sweetheart zakiji yunwa cikin dare maybe."
Ya fad'a yana kissing lips ɗinta.
Juyi tai tana ƙara mannewa da shi.
Addu'a bacci ya karanto musu idanunsa alumshe...
★★★
Washegari daƙyar Shattima ya samu Mamy tayi sallah ta shirya, ya kira Maleek awaya sun shirya, yazo ya ɗauke su.
Lawan ya ɗauki Usman da Mustapha.
Dole suka biya asibiti aka ɗauki Karima wacce aka dirkawa alluran bacci dan kar ta basu matsala amota.
Mustapha yana kusan direba Usman da Karima baya wacce take ta bacci.

Shattima suka shiga da Mamy sukayi ma Zainabu da inna ADAMA sallama.
Khairy tana bacci yace kar atashe, zai kirata awaya. Zainabu da Abbu sunyi godiya sosai wajan Mamy da Shattima.

Nadiya ta fito suka tafi tana motar liman .
Ko daga gari basu fita ba, Mamy sai bacci, kanta A ƙirjin Shattima.
Gyara mata kanta yay yana shafa fuskarta, yana leƙen fuskarta, cike da damuwa, shi kam abin mamaki yake basa wannan bacci na Mamy ya fara damunsa, ya yi yawa...

Real Ladingo Omu Farisah

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 14/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_



*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*87&88*

Khairy koda ta farka ta samu labarin su Shattima sun tafi, bata nuna damuwa sosai ba, tasan sun hana a tasheta dan kar tayi kukan rabuwa dasu.
Amman taji babu daɗi kewarsu ta dameta, taso abar Nadiya da ta ɗebe mata kewa.
Shattima suna isa Jigawa wanka kawai ya yi suka ci abinci ya fita sabida yanada meeting.

A can Gumel suna isa Mustapha yace, Karima bazata shiga gidansa ba akaita gidansu.
Ba kalar roƙonsa da Usman da Nadiya basuyi ba, ya rufe idanunsa ya ƙi amincewa, dole gidansu aka nufa da ita sabida hauka tuburan take yau ɗin, dole aka nufi asibitin mahaukata da ita.
Irin zantukan da take abun baya faɗuwa, duk wani nata ya ji takai cin ta, da dana sanin saninta arayuwa.
YANKAN WUƘA kuwa ya koma gefe yana dariya, dan ya gama tsara komai lokaci yake jira, yadda baza'a gane nufinsa ba, yasan yanzu kam Hajiya Karima dole sai auren irinsu.

Mustapha ko hutawa bai ba ya saka aka kwashema Karima kayanta, ko tsinkenta bai bari ba.
Ya kira masu gyaran gida aka fara sabon gyara, dan komai sabo yake buƙata, kafin Zainabu ta tare dan kafin azumi zata tare.
Irin kukan da Nadiya ta Sha ɓata bakine faɗin sa, amma tasan bata isa ta sauya ƙaddara ta ba, komai Karima ta zamandainita ce mahaifiyarta.
Dole Usman ya zauna ya lallasheta, yana bata haƙuri akan addu'a kawai zasu yima mahaifiyarsu idan da rabon sauran shiriya ko hankali toh.

A Dutse sai yamma bayan La'asar Shattima ya samu kansa.
Can Galadanci ya nufa, dan yi wa Liman ban gajiyar tafiyar da suka yi.

Salim tsaye abakin gate ɗin gidansu, suna magana da Abdurrazaq abokinsa.
"Salim ka gane wlh iya ƙoƙarina nayi akan gano wanda Khairy ta aura ban gano ba, shin wai me ruwanka ma da ita ne? Kana son sanya kakan cikin matsala abanza, tunda da zaran ansan kana bincike akan mijinta, baka ganin za'a iya cewa kai ka kashe na farko?"
Salim da ƙarfi yace.
"Stupid so what's? Idan ance nine tunda nasan bani bane? Kuma ai inada niyar hakan daman Allah ya amshi abinsa. Kaje kawai Abokina yau za'a iya samun matsala tsakaninmu, tunda gaskiya kazo faɗamin."
Ya ƙarashe maganan yana shigewa cikin gidansu.
Abdurrazaq ya girgiza kansa yace.
"ALLAH ya ganar dakai Salim."
Ya faɗa yana shiga motarsa.

Aliyah tana zaune tana kallon Tv tashar Tozali Tv, hannun Apple take ci falon ba kowa sai ita ɗaya.
Bataji buɗe ƙofar sa da shigowarsa ba, sai da taji hucin numfashin mutum kusa da ita.
Da wani irin sauri ta ɗago tayi idanu 4 da shi.
Gabanta ya yanke ya faɗa tana ƙoƙarin miƙewa ya kama hannunta ya toshe bakinta yace.
"Ai daman na faɗa miki zan samu Sa'a akanki, muga ƙarya iskanci."
Ya faɗa yana cirata sama da niyar tafiya da ta.
Umma Sa'idah tace.
"Ajiye ta ɗan ubanka, marar kunya, wallahi Salim ka fita a idona, ai tunda ka nuna baka son haihuwa kaida Aliyah sai gani sai hange, sai ta haife mana abun cikinta dan iskan yaro."
Ta faɗa tana kamo hannunta Suka nufi kitchen ɗin tare suka barsa nan tsaye.
Salim ya bugi iska yace.
"Wato kuna nufin kun haramta min matata ko? Zan canza taku ai, idan na ɗauke ta munbar gari ina shi kenan."
Ya faɗa yana barin falon.
"Wlh Aliyah idan baki kiyaye ba ya miki wayo ya kaiki gidansa yasan dubara da yayi ya rabaki da cikin nan ke kika sani, dan zaki iya mutuwa kinga cikin yayi girma sosai."
Hawaye ta share tace.
"Umma kiyi haƙuri zan kiyaye insha ALLAH."


Mamy zaune a falo bata jima da tashi daga bacci ba, sai wanka da sallar La'asar da ta yi.
Sanye take da skirt da riga na wani tattausan yadin Senegal na mata, Ash colour, ɗinkin yabi ƙaramin jikinta ya zauna ɗas abinka da farar mace.
Sai ka rantse irin ƴan matan nan ne da suka jima karatu basuyi aure ba, suma irin masu kyan jiki, bazaka taɓa yardaba idan ance Mamy ta kai shekaru arba'in ahaife har da ƴan kai.
Ta tsafe kanta A zuwansu ta wanke ta kameshi Tsaf sabida tanada gashi, jelar ta sauka har kusan tsakiyar bayanta, wata siririya sarƙa ta saka da ƴan kunnayenta.

Idanunta akan Tv anutse cikin mutuwar da jikinta yay ta kira Laraba.
Anutse ta amsa ta fito daga kitchen.
Gabanta ta zube tana faɗin.
"Ga Ni Hajiya."
Mamy tace.
"Ki ciro kaza a fridge ki sakamin aruwa ki gyaramin kayamin miya ki markaɗa, ki jiƙamin shinkafa, sai ki kwaɓamin fulawa kwanko biyu Ina zuwa, fatan Lami ta ɗora girkin ma'aikata?"
Laraba tace"Eh an ɗora acan kitchen ɗin baya ."
"Ok kije toh."
Mamy ta fad'a tana ɗaukan wani blue cup glass ta kai bakinta tana shan lemon kwakwan da takejin duk yafi mata daɗi ayanzun da komai.
Tana gamawa ta miƙe ta nufi Stairs.
Bata fi minti goma ba ta sauko ta nufi kitchen.

Dab da Maghreb motar Shattima ta shigo cikin gidan.
Ana danna Doorbell ɗin falo, Mamy ta gane shine.
Laraba zata fita tace.
"Laraba! Tsaya kina dubamin bari naje,.da kinga na ɓata lokaci ban dawo a ki ƙara sa min"
Ta faɗa tana wanke hannunta a fanfo ta fice.

Tana buɗe wa ta kalle shi tana sakar masa murmushi, ta matsa ya shigo, tana karemasa kallo.
Wasu narkakkun suit ne ajikinsa Wanda suka amsa sunan su, masha ALLAH sai ya zame mata wani matashin sauriya.
Takalmin ƙafafunsa ta kalla ta dawo kan agogon da yake ɗaure akan tsintsiyar hannunsa.
Rungumeta yay ƙirjinsa yana cusa fuskarsa ƙasan wuyanta ya shaƙo ƙamshi, ya sumbaci ƙasan wuyan nata, yana wani irin ƙanƙameta, cikin kamular muryasa mai fitar da amon sauti mai ratsa zuciya, ya raɗa mata a kunnenta.
"I miss You Sweetheart, ya baccin ya sakar min ke koh."
Ya ƙarasa magana yana sumbatar kunnen nata.
Wani irin ƙanƙameshi tayi tare da jin wani ɗan banzan feeling marar misali.
Hannayenta ta maida wuyansa ta saƙalo tana kallon kyakkyawar fuskarsa, tana murmushi haɗi da lumshe idanunta, tace.
"Mi Amor sannu da zuwa, ya gajiya?"
Murmushi yay sumbaci laɓɓanta haɗi da tsotsar su yana ɗaukanta sama kamar baby cikin raɗa yake mata magana yana tafiya.
"Sweetheart kwalliya tamin kyau zan biya idan na dawo daga masallaci."
Bakinsa ta kamo tana sumbata ta lalle shi tace.
"I love You Mi Amor ka kasance dani iya wuya Please."
Bai ce mata komai ba, ya haura stairs da ita yana murmushi.
Falonsa da bedroom ɗinsa ya tsaya kallo yadda ta gyarata sai ƙamshi ko ina yake.
Ita ta cire masa kayansa ta haɗa masa ruwan wanka.
Wajan wankan ne Mamy ta kasa jurewa ta shiga masa salon da ya fizgota cikin ruwan ya fara rikitata da salonsa, sai ga ma'auratan an shiga

Please Login or Register in order to submit comment