Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin wani irin k'amshi na tashi, na girke-girke, gefe ga na turaren wuta.
Mamy Bilkisu ta kasa zaune ta kasa tsaye,da kanta take shiryama Shattima abincin tarba wanda suna hanya ayau suke shigowa Nigeria komin dare.
Maryam ma ba'a barta abaya ba, sosai ta jajirce wajan taya Mamy girkin,tana koyon yadda Mamy take had'a lemon fruits, da kunun aya sbd yana masifar son kunun aya, komai da Maryam akeyi, ta wani fannin sai nace azahirance kamar tafi nuna d'aukin son Dady Shattima ya iso gari, sbd tayi masifar kewar ganinsa da salonsa da yake nunawa Mamy,sai ta dingajin wani bala'in sonsa.
Tsaf suka gama girke-girken, Laraba da Harira suka jera akan dining area, suka gyara kitchen d'in ko ina fes.
Mamy ta kalli Maryam tace.
“Daughter je kiyi wanka ki kwanta ki huta, kafin Dadynki ya iso nima zuwa zanyi nayi wanka na huta kaina na d'an min ciwo,ga shi gobe hutuna yake k'arewa Zan koma bakin aiki ya Rabbi!”
Maryam tace.
“Mamy! Ni dai banajin bacci bari nayi wanka sai na sauko nayi kallo,sannu Mamy yoh kisha magani mana.”
Bilkisu ta yamutsa fuska tace.
“Dole koda paracetamol ne.”
Ta k'arashe mgnar ta nufi stairs.
Maryam ta koma ta zauna tana k'urama Tv idanu.

Acan kuwa k'asar Singapore.
Cikin sati da kwana biyu da su Ummulkhairi suka kwashe agarin, sosai Abdoul ya samu kulawa, wajan iyayansa,wanda suke shirin komawa gida su barsa da Khairy sai ya warke.

Matsalarsa baya sakarwa Ummulkhairi fuska idan ba agaban iyayansa bane, idan sun barta sun tafi can gidan har ta k'ara zamanta su dawo baya tanka mata, haka agabanta zai dinga waya da Aziza suna hira soyayya, amman koda wasa bai cemata yana asibiti ba, sbd yasan tabbas sai tazo ko sama zata had'u da k'asa,addu'arsa kar Allah yasa taji labarin aurensa da Khairy baisan ya zaiyi ba yasan wacece Aziza akansa batada mutunci.

Ummulkhairi kuwa duk abinda yake bai dameta ba, dan ita shedace akan son da Abdoul yakema Azizar, duk da ba wata macan burgewa ba,takuma San ita laqamasa akayi ita kuwa _matar shige bata daraja._ (Sadiya Abdul mai zafafa).
Dad'in abun akullun Abba Aminu zai kiramata Mamy Bilkisu su gaisa haka Shattima ma da yake London, wanda yana hanyar koma gida ayau.

Jigawa
Unguwar Yalwawa.

Duk da ta kasance unguwar masu k'aramin k'arfi, amman dole za'a samu gidajan masu akwai, akowace unguwa.
Gidane mai kyau da tsari mai zanen farin fanti da ruwan toka.
Ba laifi compound d'in gidan yanada girma.
Azizah ce zaune a rumfar hutawa kayan ciye-ciye agabanta, tana sanye da jeans da wata ficiciyar riga, duk Rabin surata ana gani, kai ba wani kyan k'ira ba amman baka suturta jikinka, taci kitson attachment.
Waya riqe hannunta, tana chats sai dariya take,idanunta akan pictures d'in Ummulkhairi da Ammi and Abba Aminu acikin jirgi.
Akan picture d'in ta danna wajan Voice ta fara mgna,da murya may sufar ta k'ato.
“Ke! Kam Hamida bakida mutunci me ya kaiki d'aukarmin iyayen mijina, wai Ina ne zasu ma naga fa harda Khairy wacce ta auri Salim Hashim.”

Kai tsaye Hamida ta bud'e saqon ta saurara ta kira video call.
D'agawa Aziza tayi tana dariya.
Hamida tace.
Kinsan Allah dariyarki nan sai ta zama kuka,yau wannan picture d'in wannansa tara wajena,bincike na tsaya nayi,na samu hujja kafin na tura miki,kinsan dai Suhailat d'iyar Alhaji Bukar mai dala k'awar Ummulkhairi ce? Ni kuma Suhailat da mamarta da mamana ubansu d'aya,toh cikin siyaya na dinga mata tambaboyi tin randa na gansu ajirgin da ya kaimu abuja.
Shegiyar sai jiya taban cikakken bayani, Bari kiji toh...”
Dukkan abinda ya faru kakaf t zayyanewa Aziza har karyar Abdoul da zuwa jinyar sa da aka tafi da Khairyn.

Wani mahaukacin ashar Aziza ta kawo ta lailaya had'i miqewa tsaye tayi fatali da tray'n da yake shaqe da kayan motsa baki, ta dannawa Abdoul Kira.

Alokacin da kiran Aziza ya shigo ammi da Abba Aminu da Ummulkhairi na zaune,Abdoul na toilet.
Kira wajan biyar, Abba ya ce.
“Khairy! Ki d'auka kawai kowaye kice yana toilet, kar yaga an wulaqanta shi.”
Ummulkhairi cike da ladabi ta amsa.
“Toh Abba.”
Ta k'araso wajan wayan,tana ganin sunan da yake yawo akan screen wayan gabanta ya fad'i,ta sanya hannu ta d'auki wayan,hannuta har rawa yake tayi picking call d'in ta kai wayan kunnenta tare da sallama...

_YI WA KAI...!_

_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_



*P 13&14*


Aziza jin muryan mace tana mata sallama, ko tantama batayi Ummulkhairi ce.
Wani irin ashar ta lailayo ta afka mata, tare da cewa.
“Ke zakkar mata! Annoba abun b'oye ya fito fili, alhaji Hashim yaqi ki auri d'ansa sbd masifar da take bibiyarki, shine aka liqama mijina? Aure kwana d'aya kacal ya had'u da tsautsayi. Toh wlh bari kiji ki rubuta ki ajiye sunanki sakaka idan baki fita daga rayuwar Abdoul na rantse miki da Allah sai na d'aid'aita rayuwarki, ba shi wayansa bak'ar kadara kawai matar cushe.
Wlh na rantse miki zakuci kazan-kazan abin ubanku Ku dukanku ban ware kowa ba, idan dai na haifu cikin uwata da ubana ni ba shegiya bace, 'yar halak ce, Abdoul da iyayansa dake zaku gani. Hajiya Hajara uwata da ta haifeni ba'a tab'a mata kishiya ba, haka alhaji Ya'u babana bai tab'a jin son yima uwata kishiya ba, amman sbd ni nayo rakiyar mata aduniya, tin kafin ayi maganar aurena an rangad'a min kishiya, kishiyama mai class, kai Ina wallahil azim sai na tarwatsa komai ku zuba idanu ki gani, basa wayarsa dan ubanki baqar annoba.”

Ummulkhairi tinda Aziza ta fara magana, taji duniya na juya mata batasan bala'in da iyayan Salim suka liqa mata ba ya fara gama gari sai yau, tinda ga shi an fara zargin ita ta jazama Abdou tsautsayin karyan.
Wani yawu ta had'iye mai bala'in d'aci tayi k'ok'arin saita kanta, ta danne kukan da yake bala'in taso mata, taji kewar Dadynta da Mamy ta mamayeta.
Cikin maganar da bazaka tab'a cewa ta shiga matsanaiciyar damuwa ba tace.
“Angode sosai da kulawa, ba shi bane yana toilet zai kira daga baya sallamu alaikum.”
Ta k'arashe mgnar tana katse kiran.
Dai-dai lokacin Abdoul ya fito daga toilet, ya tsira mata manyan idanunsa ganin wayansa a hannunta zata ajiye.
Ummulkhairi kallo d'aya tai masa ta kawar da kanta sbd mugun kallon da ya watsa mata afakaice.
Ajiye masa wayansa,tayi ta koma mazauninta, Allah kad'ai yasan me takeji ayau acikin zuciyarta da gangar jikinta.
Zama yay saman gadon ya d'auki wayan, sai ga kiran Azizan.
Picking call d'in yay yakai wayan kunnensa. Daga can Azizah tace.
“Abdoul! Ni zakaci amana ka tozarta? Ni kawa haka? Yarinyar annoba kowa na gudunta kai aka liqa maka tsabar baka k'aunata. Toh wlh kazuba idanu kaga me zai biyo baya, yadda ka tozartani sai na rama, kuma ka dubi hanyar zuwana akowane lokaci...”
Abdoul bai cemata k'alaba ya katse kiran, tare da rufe wayansa dole magana sai su biyu.
Ammi da Abba Aminu idanu suka zuba masa, suna tambayarsa.
“Lfy? Wai wa yake kira bakwa mgna?”
Abdoul yay murmushi yace.
“Abokina ne fad'a yakemin ban fad'a masa ba, ina hospital. ”
Ummulkhairi ta kalleshi jin k'arya da yake laftawa.
Abba Aminu yace.
“Toh tinda jiki da sauqi insha Allah gobe zamu wuce Khairy zata zauna har ka warware tinda kun kusa hutu bai wuce wata uku ba, sai kutafi tare.”
Abdoul ya kalli mahaifinsa da sauri zuciyarsa na bugawa, amman baice uffan ba.
Ammi tace“Kallon lafiya kake masa ko bakason zaman nata ne?”
Ta tambayesa tana had'e fuska.
Abdoul yay murmushi yace.
“Kai Ammi inaso mna...”

*Nigeria*
Jigawa
Aziza lokacin da Abdoul ya kashe wayansa abun ya mata mugun ciwo, hakan ya sakata sake d'aukan zafi, ta kira Hamida bugu biyu ta d'auka tana fad'in.
“K'awata ya kukayi da shi?”
Azizah tace.
“Bamuyi ba zamuyi dai Hamida wlh sai na gyara musu zama,Abdoul bai sanni bane, zai sanni ko nace zasu sanni da ni d'iyar Ya'u da Hajara suke magana, mufa ba'a cikawa zuri'ar Hajara kishiya ba kakaf yayuna wa kikaga me kishiya? Idan sun iskema fita ake abasu waje sabida sun isa bare ace za'a musu, nasan me zanyi ki saka idanu kigani.”
Daga can,
Hamida tace “Bana sonki da wasa k'awata duk wanda ya miki kan kara ki masa na itace.”
Azizah tace.
“Yeah ai cikin satin nan zan musu dirar mikiya k'asar Singapore tinda dai nima ba d'iyar matsiyata bace bare na ciza yatsa, ina daidai da su, tsaf ashirye Zan doshesu...”

_Commissioner Quarters_
Mamy Bilkisu wanka tayi tai sallar azuhur, ta sanya doguwar riga ta shaddah Green colour.
Ta yi sample makeup sosai tayi kyau, abinka da farar mace siririya, ga kyan fuska.
Paracetamol ta sha tayi kwanciyarta.

Maryam kuwa tana hawa wanka tayi tai sallah ta shirya cikin riga da skirt na atamfah, shud'iya d'inkin ya zauna mata d'as duk da itama ba wata mai jikin bace tayi bala'in kyau, abinka chocolate, ita ba baqa ba ita ba fara ba.
D'auri ta murza ta yafa siririn mayafi, ta sauko qasa tana kallon Tv tashar Bollywood, daman sunyi lunch.
Wayanta ta d'auka tai dialing number Ammi.
Hira sukayi sosai da iyayan nata, da Abdoul har da Khairy,Abba Aminu ya sheda mata gobe Duke taso cikin dare.
Suna gama wayan taji k'aran doorbell.
Miqewa tayi ta nufi hanyar falon.
Da Laraba suka had'u ta fito daga kitchen zataje ta bud'e.
“Am Laraba! Ki koma zan bud'e.”
Da “Toh”
Laraba ta amsa.
Tana zuwa hannunta ta d'ora akan handle d'in k'ofar, ta shaqo daddad'an k'amshin turarensa, da zazzaqar muryan shi, yana amsa waya.
Wani irin bala'in sanyi taji yana ratsa dukkan sassan jikinta, ta bud'e k'ofar.
Sanye yake da wani d'ayan boyel milk colour, d'inki mai bala'in kyau ya amshesa sosai, sai ya zama tamkar wani matashi irin 'yan shekaru 37 wanda sukayi latin aure, bazaka ce yakai 48 a haife ba.
Maryam kallo d'aya tai masa lokacin shu'umar k'wayar idonsa ya fad'a nata, taji tamkar anyi mata alluran kasala had'e da ta bacci, ba shiri tai k'asa da kanta, ta rusuna tana masa sannu da zuwa, tare da gaishesa.
Wayan ya katse yana amsawa, yace.
“Daughter na sameku lafiya?”
Asanyaye ta amsa.
“Lfy lau Dady ya gajiya?”
Ta k'arashe mganar tana Jan trolley d'insa ta juya falon.
Kai tsaye stairs ta haye da trolley'n NASA.
Shattima ya zube saman sofa ya zuba wayoyinsa saman glass table d'in da yake saitinsa, bayan ya kashesu baki d'aya sabida yana buqatar hutawa.
Ya cire hular kansa, yana shafa lallausar suman kansa.
Maryam aqofar d'akin Mamy ta ajiye trolley'n tayi knocking k'ofar, har sau biyu taji shiru, sai ta tuna tace kanta na ciwo, k'ila tasha magani ta kwanta.
K'asa ta sauko Shattima ya meqe dogayen qafafunsa saman sofa.
Kallon tsanake tai masa daga nesa.
Kitchen ta nufa ta yanka masa Watermelon da Pineapple,ta jera a tray'n silver ta d'auko jug wanda aka cikasa da lemon fruits, ta d'ora gefe da cup glass biyu ta d'auka ta fito.
Aladabce ta k'araso bakinta d'auke da sallama, ta rusuna ta dire tray'n saman table, murya can k'asa tace.
“Dady! Mamyna na bacci kanta yana ciwo.”
Ta k'arashe mgnar tana tsiyaya masa lemon, ta ajiye ta miqe ta koma sofa mai facing d'insa ta zauna tana maida hankalinta kan Tv.
Kaifafun idanunsa masu lumshewa ya bud'e yana miqewa zaune ya sauke k'afafunsa k'asa, yana gyara zamansa, ya kalleta cikin daddad'ar muryasa mai kashewa mata jiki, ya furta.
“Sannu daughter Ngd,subanallahi tayi aiki ta gaji koh? Bari na dubata.”

Ya k'arashe mgnar yana d'aukan cup d'in yay bismillah ya kurb'i lemon.
Sai da yasha rabi ya ajiye ya dauki yankan Watermelon, ya kai bakinsa ya d'auki pineapple yaci ya miqe yana sake mata godiya, ya nufi hanyar stairs.
Maryam ta bisa da kallo cike da begensa yadda yake sarrafa k'afafunsa wajan tafiya, ita kawai yanayin jikinsa talau ba nauyi burgeta yake, dukirin arzikinsa da hutun da yae samuamman smabaida k'iba iron ta masu kud'i ko tumbi d'an sumul talaulayi da shi.
Idanunta ta janye daga kallonsa ta maida kan Tv.
Sai da ta tabbatar ya haye tai saurin tasowa ta d'auki cup me sauran lemon da yasha, ta kafa bakinta daidai saitin bakinsa ta kurb'i lemon ta lumshe idanunta. Tass ta shanye lemon tai saurin zuba wani daidai Inda ta gani, ta koma ta zauna ranta fes.

Yana bud'e d'akin wani irin sahihin k'amshi da sanyi ya daki hancinsa ya lumshe idanunsa, bakinsa d'auke da sallama ya kutsa kansa, tare da rufo k'ofar.
Bacci take mai cike da mafarkan da suka firgitata, tare da razanata ta d'imauce, sai girgiza kanta take tana kuka tare da fad'in.
“Don Allah kuyi haquri wallahi bazan iyaba,hakan tamkar mutuwatace take dosoni, wannan abun ba Yiwa Kai bane cutar da kai ne...”
Daidai lokacin Shattima ya iso dab da lafiyayan bed d'in nata, ya hauro saman bed d'in yana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Bilkisu! Me ya faru? Me ya sameki? Meye ba yiwa kai ba?”
Ganin bata hayyacinta bata ma san me take ba, sai sambatu take tana kuka tare da fad'in bazata iyaba, ya miqe qafafunsa, ya janyota ya d'orata akan cinyarsa ya rungumeta jikinsa sosai ya fara karanto mata addu'o'i, kusan minti 20 ahakan, cikin ikon Allah yaji tayi shiru ta lab'e ajikinsa, tana baccinta.
“Ya Rabbi! Wannan sabon al'amarin fa! Sweetheart?”
Idanu ya zuba mata ganin yadda ta k'amk'ameshi tana baccinta.
Zufar goshinta ya goge mata, ya sunkuyo da kansa ya sumbaci labb'anta ya kwanta rairan tana samansa ya zagaye hannayensa bayanta yana shafawa ahankali.
Sai ana kiran la'asar ta farka ta ganta shame-shame a saman k'irjin Shattima kwance. Kai ta d'ago bata sauke shi ako inaba sai saman kyakkyawar baqar fuskarshi me zagaye da saja.
Wani kallo mai cike da k'auna ya mata tare da kashe mata ido d'aya, ya sakar mata tattausan murmushi, yana shafa kanta, yana jira yaji ta masa zancan mafarkinta da tayi yaji shiru,sai ya basar k'ilama bata san tayi ba.
“Ya Allah! Mi Amor! Yaushe ka dawo har nayi bacci ajikinki ban saniba?”
Hancinta yaja can k'asan cikin taushin murya ya furta.
“Da jimawa sweetheart. ”
Janye jikinta tai tana miqa tace.
“Sannu da zuwa Mi Amor ya gajiya? Muje kayi wanka lokacin sallah kar ya wuce, idan ka dawo daga masallaci sai na cika maka cikinka da launikan abincin da kafi so.”
Ta fad'a tana sauka daga bed d'in ta shiga bathroom d'inta ta had'a masa ruwan wanka, ta dawo ta kamashi ya miqe suka shige...
Can kuwa Maryam, shiru-shiru bataga iyayan nata sun fito ba, sai taji ta damu hakan ya saka ta miqe ta kashe kayan kallon ta kira Laraba ta kwashe kayan ta maida kitchen ta saka a fridge na kayan ciye-ciye.

*Singapore*
Washegari su AbbaAminu suka tashi da shirye-shiryen dawowa Nigeria. Ummulkhairi hankalinta idan yayi dubu ya tashi,tana bala'in tsoron abarsu itada Abdoul,idan ta shiga toilet batada aiki sai kuka.
Da yamma Johnny ya raka Abba Aminu kamfanin waya ya siyomata Samsung mai bala'in kyau da tsada,ya siya mata layi ya loda lambobin iyayanta da nasu, nan ne kawai taji sanyi ita johnny da Diana mamanta batada lfy bata zoba, suka raka su Abba Ami u suka rakasu airport, duk haqurinta da jirginsu zai tashi sai da tayi kuka.
Koda ta dawo ko d'an lallashi Abdoul bai mata ba kallonta kawai yake tana kukanta.
Abinda ya ishesa ya kira Johnny yace.
“Kazo ka kai wannan gidan karta sakamin ciwon kai naji da kaina.”
Johnny murmushi kawai yayi yace.
“Ok ganinan.”
K'in zuwa yay ya tafi sha'aninsa dan tsaf ya gano baya son yarinyar.


Acan Nigeria kuwa washegarin zuwansu Abba, Maryam ta shirya ta tafi gidansu cike da d'aukin zuwan iyayanta tana son ganinsu.
Shattima nada kwana biyu da zuwa Mamy ta koma bakin aiki hospital d'inta ta kanta,da Shattima ya bud'e mata mai suna *Clinic Khairy hospital*.
Kwanan sa biyar da dawowa ya fara shirin tafiya,ganin Abdoul, ya kira Abdoul d'in ya tura masa address d'insa, Amman dan yayi musu surprise yace sai k'arshen wata zaizo, kenan nanda kwana goma.

Asokoro
Salim zaune ya miqe qafa d'aya kan d'aya, yana k'yalk'yatar dariya, yana busa sigari, sai uban hayaqi yake fesarwa.
Tabbas shi kad'ai yasan me yake shiryawa.
Wayansa ta d'auki ringing.
Kallon wayan yayi yaga baquwar lamba.
Baija ajiba ya d'auka.
Daga can Aziza tace.
“Salim! Kana son Khairy har yanzu ko ka fasa? Idanu ya zaro yana fad'in.
“Da wa nake magana?”
Azizah tace.
Da Azizah budurwa Abdullahi Aminu kazaure.”
Dariya yayi yace.
“A'a bana so.”
Ya katse kiran sabida kawai haka yaji bai yarda da itaba.
Miqewa yayi yaje wanko bakinsa ya b'are sweet ya sanya bakinsa, ya fesa turare,ya fita ya nufi cikin gidan nasu.

Ba kowa a falon sai Umma Sa'idah tana waya.
Da sallama ya shigo.
Rusunawa yayi ya gaisheta.
“Ummata! Ina kwana?”
Baki da hanci ta saki tan kallonsa.
Kusan k'afafunta ya zauna yayi k'asa da kansa,har ta gama wayan.
Cike da mamaki ta kalleshi tana fad'in.
“Kai! Salim! wane munafurcin ka shiryo? Nice kake wani rusunama?”
Salim yace.
“Umma! Shiriyace ta Allah daman kuma ai ni ba d'an iska bane tinda bana miki rashin d'a'a koh?”
“Hummm wlh dole akwai wani abun fad'i ina jinka?”
Salim ganin ta ganosa yace.
“Wlh ba komai kawai lada nake nema, Abba ya fita koh?”
“Eh ya fita sai kaje ka samesa,baka cire yarinyar nan aranka ba ko?”
Salim ya miqe yace.
“Idan akwai abinda natsana bai wuce itaba bar maganar don Allah.”
Ya k'arashe mgnar yana fita daga falon.
Sa'idah tace.
“Allah yasa hakane hummm...”

Bayan kwana biyu.
*Singapore*
Ajiya aka saki Abdoul SBD hannun yayi sauqi sosai ance duk bayan kwana uku yaje adinga duba hannun kafin akwance d'orin.
Ummulkhairi ta rame sai hanci da jan lips daman abinka da ba mai manyan idanu sosai ba wahala ta saka sun firfito sbd Abdoul ko magana ta msa baya amsawa,haka take rakub'e agidan, tayi kuka har ta gaji.
Ajiya ne Aziza ta iso ko kayanta bata ajiyeba ta fara masifa ta hanasu bacci shi kuma Abdoul kamar wani shanyayye ya kwana yana bata haquri wai zai d'auki mataki.

Ummulkhairi tsaye a kitchen tana girki tana kuka idanunta sunyi jajir, sun kumbura ta rasa wa zata kira ta fad'ama damuwarta, ace budurwar miji ta dinga sakata aiki? Tana zaginta ita Sam batasan wani abu rigima ko fad'a ba.
Mari taji fauuuu an d'auketa da shi an shaqo wuyanta.
Kallon Aziza tayi sanye da jeans da Riga mai gajeran hannu ta saki kitson attachment.
Zagi ta lailayawa Ummulkhairi, tana janta tare fad'in.
“Wallahi sai ka saketa yanzu agabana ko na kashe kaina. Na tsani annobar nan.”
Abdoul cikin tsawa yace.
“Wai ke! Azizah! Bakya jin maganata? Tin jiya nake miki magana d'aya ki jira tukun ko so kike iyayena su tsinemin ne?” k'aran danna doorbell yaji ya nufi k'ofar zatonsa cikin mak'wabta ne masu shigowa ganinsa, ya Kama handle d'in k'ofar zai bud'e.

Azizah cikin masifa ta bi bayansa tana fad'in.
“Wallahi sai ka saketa ko najama magana aqasar nan ayau.”
Ta k'arashe magana tana hankad'a Kahiry, ta tafi tagala-tagal zata bugu da bango, dai-dai lokacin Abdoul ya bud'e qofar. idanun Shattima suka sauka akan Khairy zata fad'i...

_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_



*P 15&16*


Cikin wani irin zafin nama Shattima ya kamo hannun Khairy, wanda saura qiris ta buga kanta da bangon, ya rungumeta cike da mungun tausayin 'yarsa, a cikin zuciyarsa yana maimaita kalmar.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Bayan ranan da aka fasa aurenta da yau zai iya rantsuwa da mahaliccinsa, yakai shekaru 20 bai shiga mugun tashin hankali ba, da b'acin rai da damuwa irin na ranan da saqon fasa auren Khairy yazo, sai yau da yaga yadda Ummulkhairi ta koma cikin abinda bai fi kwana 10 ba.
Khairy duk ilahirin jikinta rawa yake,jin irin k'amshin Dadynta,wanda ko amafarki taji shi zata banbance, ta d'ago kanta, tana shasheqar kuka, idanunta ya sauka akansa, sanye da farar shadda idanunsa ya kad'a yayi jajir.
Wata irin qanqamewa tai masa, kamar zata koma cikin cikin sa, ta kira shi.
“Dady! Daman nasan idan kana raye a duniya bazan tab'a mutuwa cikin wahala ko wulaqanci ba, don Allah ka d'aukeni Dady wallahi kashe ni za suyi da baqin ciki, tinda nazo qasar nan banyi farin ciki ba.”
Ta k'arashe maganar cikin matsanaicin kuka, tana qara qanqame Shattima tana kuka mai tsuma zuciya.
Shattima bai san me zai ce ba, akan wannan al'amari, da idanu kawai yake bin Abdoul da kallo yana bubbuga bayan Khairy. Dan Sam koda wasa bai kalli Azizah ba, tin ganin da ya mata ta hankad'o Ummulkhairi, ba suttura arzik'i ajikinta.
Abdoul kuwa mutuwar tsaye yayi awajan, tinda uwarsa ta haifesa bai tab'a jin ya tozarta, ya kunyata irin na yau ba, ji yayi kamar qasa ta tsage ya shige, kansa k'asa ya kasa ko k'wak'waran motsi, tsabar kunya, bakinsa yayi masa masifar nauyi ya kasa koda ma Shattima sannu da zuwa, bare ya gaishe shi.
Aziza ma duk rashin kunyarta,suna had'a idanuwa da Shattima ta daburce, bala'in tsoronsa ya shigeta, gabanta ya shiga fad'uwa,tai saurin juyawa, kamar zata fad'i dan sauri ta nufi bedroom d'in Abdoul dan anan ta sauka, hankalinta atashe tasan minister Shattima zai iya yin komai akan d'ayarsa.
Shattima kukan Khairy nacin zuciyarsa, ya waiga baya babban Guard d'insa wanda shi kad'a yaba umarnin biyosa.
Kallon da yamasa ya fahimci komai.
Cike da girmamawa ya gyara zaman bindigarsa ajikinsa, ya juya bar qofar falon ya nufi farfajiyar gidan.
Shattima ya sake shigar da ita cikin jikinsa, yana buga bayanta murya can k'asa ya saddo kansa bakinsa dab da kunnenta ya furta.
“Sweet daughter! Yi hkr ki kasance mai juriya da tawakali da amsar k'addara ki akoda yaushe, kiyi haquri kina hannun da bazan iya kub'utar dakeba, koda kuwa naman jikinki zanga Abdoul yana yankawa, sabida Aminu yamin halaccin da bazan iya tozarta jininsa ba, Amman zan tayaki da addu'a, kiyi haquri ki kwantar da hankalinki, kici gaba da masa biyayya mijinki ne, watarana sai labari,babu abinda yake d'orewa a duniya sai ikon Allah, dan haka don Allah ko a waya karki kuskura kibari Bilkisu ta Sani, nima nayi nadamar zuwana, amman ba komai.”
Ya k'arashe maganar yana janyeta jikinsa, ya kama hannunta suka tako har cikin falon, ta kasa mgna kuka kawai takeyi.
Zaunar da ita ya yi saman kujara, ya zauna can nesa da ita, ya zurama Abdoul idanu wanda ya kasa ko k'wak'waran motsi.
Shi kuma Abdoul jikinsa ya yi sanyi kunyar duniya yau ya jita, cijewa yayi ya rufe k'ofar ya nufo wajansu, kanshi ak'asa.
Can nesa ya zube k'asa saman carpet, yace.
“Dady! Sannu da hanya don Allah dan darajar Annabi Muhammad kayi haquri da abinda idanunka suka gani, na rantse ma sharrin shed'an ne, bazan kumaba, nayima alqawali zamu zauna lafiya daga yau, alfarmar Annabi da Qur'ani.”
Ya k'arashe maganar yana rushewa da kuka tare da riqe k'afafun Shattima.
Shattima yace.
“Abdullahi! Karka damu kai d'ana ne dukkanku d'iya nake kallonku ba banbanci, ba komai don Allah ku gyara zaman aurenku ku zauna lfy da juna, sai dai wacece wannan da tazo har gida take cutar da Baby kana kallo?”
Abdoul yayi tsuru² da idanu ya kasa magana, yayi k'asa da kansa.
Muryan Shattiman yaji ya jefo masa tambaya.
“Koh ita ce surukar tamu?”
Abdoul cike da kunya ya qara k'asa da kansa yace.
“Eh Dady tazo dubani ne.”
Shattima cike da mamaki yace.
“Daga Nigeria tazo takanas ba tare da akwai aure tsakaninku ba? Har take shigar banza agidanka Abdoul anya kayiwa mahaifinka adalci? Kayiwa kanka adalci? Kaa kuwa tsoron fushin Allah akanka?”
Abdoul har wata zufa take karyo masa cikin rud'ani yace.
“Dady ayi haquri yanzu zan saka ta tafi.”
Shattima ya girgiza kai yace.
“Haba! Abdoul! Ba Ina taya Khairynah kishi bane,amman ka duba anan Ina kaga macan da zata haifama 'ya'ya nagari? Haba! Abdoul yaushe ka rushe tarbiyar mai kyau da aka Gina maka tun kana yaro? Kasan hakan ya sab'awa Allah ya sab'awa maganar manzon Allah, taya zaka zauna gida d'aya d'aki d'aya da macan da ba muharamarka ba?”
Abdoul dai haquri yake ba Shattima ya miqe ya nufi hanyar bedroom d'insa.

Aziza tana tsaye tsakiyar d'akin ta had'a kayan cikin akwatinta, ta canza kaya yanzuma jeans ne ta saka da riga mai tsayi har guiwa, sai kai komo take tsakiyar d'akin,duk hankalinta atashe.
Abdoul ya shigo yana mata wani irin kallo yace.
“Dan ubanki kwashe kayanki ki tafi,sai da nace miki kibi komai asannu Zan gyara komai, ga shi yanzu kin jazamin musiba, idan mahaifina yaji labarin nan wlh tsinemin zaiyi nasani.”
Azizah tace.
”Kobaka ce ba tafiya zanyi amman na rantse maka Abdoul ba macan da zata moreka arayuwar aure sai ni Aziza Ya'u, ka shirya zaman aure dani na har abdan, yanzu ma tsoron minister ne zai saka na tafi tin inada sauran mutunci na ma'asallama sai kunzo maganar aurena.”
Ta k'arashe mgnar tana yafa mayafin hannunta ta janyo akwatinta ta fice.
Cike da kissa ta saki akwatin ta zube k'asa ta kama qafafun Khairy tana kuka tace.
“Don Allah ki yafemin nabi Allah na

Please Login or Register in order to submit comment