Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta samu horon girki daga Mamynta masha ALLAH.."

Maryam da Nadiya atare sukace.
"Kai Mummy tare da mukayi fa!"
Dariya suka musu Khairy da bata gane komai sosai sabida azababban ciwon da kanta yake, ta ɗan yi murmushi tana musu gwalo...
Har suka kammala cin abincinsu suka dawo falon su Mamy basu sauko ba.
Abinka da wayayyun mutane babu wanda jimawarsu ta dama sai sukayi tunanin sunyi hakan ne dan su, su sake suci abincin sosai.

Khairy tana kwance tayi matashi da cinyar Auntie Aisha suka sauko.
Ƙamshinsu ya shaida mata suna saukowa.
Idanunta ta lumshe tana ƙara laɓewa jikin Auntie Aisha.

Shattima ya ƙara so da sallama, cikin kamewarsa yana sake ba Dad hannu da Usman.
Ya zauna, yana ya zubawa Khairy idanunsa.
"Auntie Aisha ya gajiya?"
Ya yi maganar cikin siririya murya.

"Wlh Alhamdulillah! Ya gajiyarku? Ai banyi tunanin ayau zaka iya fita ba, amman dan ƙokari ka fita."
Murmushi ya yi yace.
"Toh ya za'ayi sai haƙuri, idan kana jan ragarma mutane dole lokacin da ake buƙatar ka a ganka awajen."

Mamy tace.
"Auntie Aisha barka da zuwa, ya hanya? Zainabu sannunku da zuwa afuwan kunga sai yanzu banajin daɗine amman yanzun Alhamdulillah! Usman sannunku Dad ina wuni ya gajiya?"

Mustapha da Usman suka gaisa cikin girmama juna, Zainabu ma haka ta hannu.
Mamy ta gyara zamanta tana faɗin.
"Baby! Allah yasa kowa yaci abinci ba'a jiramu?"
Khairy ta ɗago tana dariya bata yarda ta kalli Shattima ba, ta kalli Mamy tace.
"Mamy ai mu kam abincinmu yanzu ai ya fara zama kashi, aciiinmu sauran ku Mamy dan ALLAH kici abinci dayawa, har kunun gyaɗa na miki."

Mamy ta miƙe tana faɗin.
"Allah ya miki Albarka Mi Amor muje kaci wani abun."
Wayoyinsa ya zuba cikin aljihunsa, yana miƙewa idanunsa akan Khairy wadda ta ɗago kenan da niyar satar kallon sa suka haɗa idanu.
Baki ta zumɓuro gaba, da sauri ta ɗauke kanta, tana kallon Usman wanda yake kallon Maryam ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Lah! Wlh Dad kayi suruka akusa ku kalli Ya Usman ya kafe Maryam da idanu kamar zai cinyeta..."
Real Ladingo Omu Farisah

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = ₦500. 500Mb ₦500
2.9GB = ₦1200. 1.5GB ₦8000
4.1GB = ₦1600. 2GB ₦1600
5.8GB = ₦2100. 3GB ₦2000
7.7GB = ₦2700. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 31/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*100*

Bayan Shattima da Mamy sunyi lunch, Shattima ya zauna suna hira da Dad Mustapah.
Auntie Aisha ta fuskanci Mamy,
tana kallonta tace.

"Bilkisu! Daman magana nake so muyi akan ƴarki."

Mamy tana murmushi kwalin juice na coconut a hannunta tana tsiyaya cikin cup tace.

"Ok Auntie ina jinki."

Zamanta ta gyara tace
.
"Akan maganan bikine ya kika gani wane lokaci ya kamata asaka?"

Mamy ta yi murmushi tana kurɓar juice ɗin, tace.

"Alhamdulillah! Gaskiya faɗuwa tazo daidai da zama, daman yau nake cewa nayima Mi Amor mgna.
Ni dai anawa zaɓin ayi bikin kafin sallar layya, don ALLAH kar asaka nesa har na fara nauyi, tunda kinga yanzu bana ciwo bacci ne kawai bare ace ina jinya baza'ayi biki ba, ko ya kika gani Auntie?"

Auntie Aisha ta sauke ajiyar zuciya tace.

"Ya yi hakan Bilkisu kenan zanyi ma Baffa maganan yanzu idan muje can koh?"
Mamy ta jinjina kanta tace.
"Ok har naji daɗi wlh."

Can ɓangaren su Khairy suna garden ita da Nadiya da Usman da Maryam, suna hirasu cikin nishaɗi.
Usman ya keɓe da Khairy yace.

"Ƙanwata! Dan Allah ki shige min gaba, ina son yarinyar nan dayawa daga kallo ɗaya na mace akanta, wlh ina sonta."

Khairy ta ƙyalƙyale da dariya suna tafa hannu da Usman tace.
"ALLAH daman nace sonta kake da gangan na janyoku nan, dan ku samu wata dama, ta musamman.
Maryam! zo zan baki saƙo."

Maryam suna hira da Nadiya ta waigo tana kallon Khairy tace.
"Toh Aunt."
Ta faɗa tana miƙewa tace.
"Sister Nadiya Bari nazo yanzu."
Nadiya ta yi dariya tace.
"Ok aje ajiyo adawo my Aunt."

Maryam ta zaro idanunta batace komai ba, ta nufi wajansu.
Sallama tayi ta zauna kusan Khairy tace.
"Ga Ni Aunt."
Khairy ta yi murmushi tace.
"Yaya gata ka faɗa mata da bakinta, dan ance waƙa abakin me ita yafi wanda zai kwaikwaya."
Ta faɗa tana miƙewa tabar wajan.

Maryam kamar ruwa ya cita awajan, ta sadda kanta bata iya ɗago kanta ba.

Usman ya yi gyaran murya yana kallon Maryam yace.
"Maryam! Bazan ɓoye miki saƙo naba ƙanwata Khairy ta faɗa miki tace na faɗa da kaina.
So magana gaskiya tunda na ganki naji duk duniya ba macan da nake so da ƙauna, da son mallakarki, ki zama uwar ƴaƴana, ALLAH yasa ba wanda ya rigani furta wannan kalmar agareki?"

Ya ƙarashe maganar yana leƙen fuskarta yana murmushi.
Maryam hawaye taji na son zubo mata, sai de ta dake ta mayar da hawayen dan ganinta wannan shine wanda Allah ya zaɓa mata bazatayi wasa da damar da Allah ya bata ba, dole zata amsa masa koda ba yanzu kai tsaye ba.

Ta ƙara ƙasa da kanta, ta rufe fuskarta da tafin hannunta, batace uffan ba.
Wayarta ya zare A hannunta ya loda lambarsa, ya kira kansa yana ganin lambar ta yace.
"Zan kira gimbiyar zuciyata nasan daman yanzu da wuya na samu amsa."

Miƙewa ta yi cike da kunya tabar garden ɗin ta nufi cikin gida...
Khairy da Nadiya suna masa dariya.
Khairy tace.
"Ya Usman! An dace koh? Dan kam so da alamun kunya yakeji farawa."

Murmushi ya yi yana sosa kansa yace.
"In Sha ALLAHU za'a dace ku tayani da addu'a a haɗa da bikina da naki."
Khairy ta rufe idanunta tana dariya batace komai ba.

Bayan sallar La'asar su Mustapha sukayi shirin komawa Gumel, zasu biya gidan Liman su gaishesa daga can zasu wuce.
Da Mamy da Auntie Aisha har Shattima tare sukayi rakiya.
Khairy harda ƙwallar shagwaɓa sai da Shattima ya zare mata idanu ta haƙura ta saki Zainabu, da Nadiya sai ita da Maryam aka bari agidan, wanda so take ta fece yanzu kan su dawo, dan tana son nisanta kanta da duk abinda zai haɗata da Shattima.

Suna zuwa bayan gaishe-gaishe, Auntie Aisha tace.
"Toh Baffah maganan tsayar da bikin, ga Bilkisu nan na mata maganan tace kafin layya ayi bikin tunda tana lafiya kafin ta yi nauyi."
Liman ya kalli Mamy yace.
"Bilkisu! Haka ne?"
Mamy aladabce tace.
"Eh Baffa haka ne dan ALLAH asaka kusa tunda gasu Dad Mustapha nan."
Baffa yace.
"Toh shi kenan daman kece uwa hakan ya yi sai asaka, kamar wane lokaci ya miki kafin sallar layya?"
Mamy tace.
"Baffa asaka kwana 40 ya yi koh?"
Baffa ya jinjina kansa, yana kallon Shattima da Dad Mustapha yace.
"Toh kunji yadda Bilkisu uwa amarya tace hakan ya yi koh?"

Shattima baice komai ba, kallon Mamy yake cike da tsantsar soyayyarta, ya rasa wace irin mace Allah ya basa mai farar zuciya.
Dad Mustapah yace.
"Ya yi mana har abadan bazamu ja da duk hukuncin da Bilkisun ta yanke ba, hakan ya yi, Allah ya tabbatar da alkhairi, Ubangiji ya biyaki da mafi alkhairinsa."
Auntie Aisha tace.
"Ameen ya Allah, Bilkisu mutum ce ai."
Baffa yace.
"Ameen, Abdallah! Baka ce komai ba, ko hukuncin da muka yanke bai maka ba?"

Shattima kansa ƙasa yace.
"Baffa ya yi Allah ya nuna mana da ran da lafiya."
Baki ɗaya suka amsa da.
"Ameen ya ALLAH."
Liman ya musu addu'a aka taɓa hira su Mustapha sukayi ma liman sallama, suka tafi, cike da farin cikin ɗakinsu Shattima arayuwarsu.
Usman ma zuciyarsa cike take da zallar farin ciki, shiyasa yake driving cikin wani irin yanayi me burgewa.

Auntie Aisha suna zaune falon Inno sumbar Shattima wajan liman zasuyi magana.
Tana kallo Mamy tace.
"Toh Ni dai ina nan da safe zanje gidan."
Mamy ta ɓata fuska tace.
"Haba! Don Allah Auntie Aisha tashi muje kawai tunda dai mu akazo yima sannu da zuwa."
Auntie Aisha tace.
"Naƙi kam sai da safen, kefa daga nan gidansu Anne zakije koh?"
Mamy tace.
"Eh ba sai muje tare ba."
Inno tace.
"Aa Bilkisu kije ku gaisa dasu Anne anutse."
Mamy dai murmushi take.
Kiranta Shattima ya yi awaya ta fito suka wuce.

Har ciki Shattima ya shiga suka gaisa da surukansa, ya barta ya tafi tace bayan Maghrib zata dawo.
Daga can Shattima ya saka Maleek ya wuce da shi wajan Commissioner Aminu.
Azizah tunda taga Shattima take famar kuka, kwana ɗaya tak tayi wani irin baƙin bakinta ya bushe.
Salim kansan bai san rayuwa zata juya masa haka lokaci ɗaya haka ba.

Cikin ƙarfin hali, da azabar da takeji a dukkan jikinta, Azizah tace.
"Don Allah Minister kayi haƙuri, wlh ban saba shan wuya ba haka, Allah na haƙura da ɗaukan fansar Abdoul ɗin na gane ƙaryace ake muku baku kukayi sanadin mutuwar Abdoul ba, na cuci kaina canfin banza ya janyo min, na shiga halaka, dan Allah karku shigar dani kotu, wlh zan shiryu na zauna waje ɗaya na samu miji nayi aure.."

Shattima cike da mamaki yace.
"Oh! Daman fansar Ɗana zaku ɗauka kuna tunanin Ni zan kashesa ko Khairy? Na yarda bakuda hankali."

Salim cikin mawuyacin hali yace.
"Wlh na haƙura kuyi haƙuri don Allah karku shigar dani ƙara kotu don Allah wlh nayi alƙawarin bazaku sake samuna da wani laifi ba kowane irine, bare shiga sabgar Ummulkhairi don ALLAH Dady ku yafemin zan rungumi matata na gyara halina."
Tasi'u yana kuka yace.
"Daman Ni sabon shigane wlh na gyaru bazan sakeba."

Shattima ya kallesu fuska ba wasa yace.
"Tsaianinku da ALLAH kunyi alkawarin shiryuwa kusan abinda kukeyi?"
Atare sukace.
"Wallahil azim munyi alƙawali."

Shattima baice musu komai ba ya juya.
Abba Aminu yace.
"Ka barni dasu fa nace ko ka manta? Wai shine ma dalilin dawowar taka?"
Shattima ya ɗan saki murmushi yace.
"Ayi haƙuri nayi shiru naga kamar nadama ƙarara afuskarsu shiyasa..."

Sai yamma sosai ya nufi gida, dan shirin sallar Maghrib.
Khairy sai ita ɗaya zaune falonsu tana shan ruwan zamzam, tana kallon Tv, Maryam ta tafi gida tun bayan tafiyar su Mamy, kunyar Khairyn takeji haka kawai.
Ƙaran Doorbell ta ji ta ajiye robar zamzam ɗin ta miƙe zatonta Mamy ce ta dawo.
Tana buɗe ƙofar idanunta suka shiga cikin lumsassun fararen idanunsa masu bala'in kwarjini, wanda suka nuna gajiyarsa ƙarara.
Idanunta ta janye daga cikin nasa, cikin sanyin murya tace.

"Dadynah sannu ina Mamy Nah?"
Shigowa ya yi yana kamo hannayenta, ya maida ƙofar ya rufe, yana jinginata da ƙofar, anutse ya haɗe jikinsa da nata, yana kamo kyakkyawar fuskarta da tafukan hannunsa, ya sumbaci goshinta da kumatunta, ya lashi laɓɓanta, ya hura mata iskar bakinsa, yana zura hannunsa ta bayan ƙofar ya rungumeta ƙamƙam, yana sauke numfashi, yana manna bakinsa kunnenta ahankali ya kirata.
"My Baby! Bakya missing Dadynki uhm?"
Da wata kalar shagwaɓa ta sanya hannunta tana rungumesa gam, tana kifa fuskarta tsakiyar ƙrjinsa, tana sauke ajiyar zuciya, tana shaƙar ni'imataccen ƙamshinsa.

Kiss ya sakar mata tsakiyar kunnenta yana kiranta.
"Babyn Shattima ba magana me kuma Dady ya yi ne uhm?"

Kukan shagwaɓa ta sakar masa tana sake manna fuskarta ƙrjinsa.
"Ya Rabbi! Baby Khairy menene kuma zo naji meye nayi."
Ya faɗa yana ɗago kanta, ya zuba mata idanunsa masu tasiri akanta, yana wasa da gazar² ɗin gashin idanunta.
Ahankali dab da ƙofar hancinta yake mata magana yana yawo da harshensa saman idanunta.
"My Baby me Dady ya yi ake rigima?"

Sake laɓewa ta yi ajikinsa, tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ashagwaɓe tace.
"Toh Dady ba kai bane ka hanani na biku rakiyar su Umma, ka hanani zuwa can gidan Baffa kuma kake ta hararata kana zaro min idanu."
Ta ƙarashe maganan tana ƙara fashe masa da kuka.

Wata irin runguma ya mata, yana buga bayanta, ya raɗa mata a kunnenta.
"Oh! My Baby haka zaki dinga rikici ga shi kin kusa yin ƙanne uhm? Ok naji zo muje zan faɗa miki dalili, ki daina ma Dady rikice kin mata gobe Abuja zaki uhm Baby?"

Baki ta turo gaba, tana ƙara shigewa jikinsa tana jin nutsuwa na saukar mata, ashagwaɓe tace.
"Dadynah goyani."

Handkerchief ya zaro ya goge mata fuskarta tass, ya sumbaci lips ɗinta ya duƙa ta hau bayansa, ya miƙe da ita tana murmushi ta zagaye hannayenta ƙirjinsa, ta kwantar da kanta, ahankali tace.
"Sweet Dadynah Ina sonka kaji?"

Murmushi ya yi ya nufi hanyar da zata sada shi da falon, yana faɗin.
"Na sani Baby nima irin dayawa ɗin nan nake son Baby Khairy nah Ok?"

Cikin murna ta sumbaci ƙeyarsa ta beƙo kanta ta sumbaci kumatunsa, tana dariya tace.
"Dadynmu dagani sai Mamy koh?"
Ƴar ƙaramar dariya ya yi yace.
"Bakwason na ƙaro muku abokiyar zama ne?"
Ƙanƙameshi ta yi tana faɗin.
"Wlh bamaso tabbb wlh yarinyar da ta shiga uku dukan safe daban na rana daban, na yamma daban, ba mai raɓar mana mijinmu."

Shattima murmushi yake yana girgiza kansa, jin ta dage tana zata daki ƴar mutane.
Yana hawa upstairs ya nufi ɓangaren sa da ita.
A falonsa ya direta kan sofa, yana zama kusanta tare da faɗin.
"Washhh ALLAH."
Khairy ta kalleshi ganin idanunsa lumshe.
Ahankali ta kwantar da kanta ƙirjinsa tana shafa gashin da yake kewaye akan kyakkyawar fuskarsa, ahankali bakinta dab da hancinsa tace.
"My Dady me ya sameka?"
Ahankali ya buɗu kaifafan lumsassun idanunsa da suka nuna tsantsar gajiya, yana sauke su akan kyakkyawar fuskarta, ya furzar iskar bakinsa, ya sanya hannunsa yana ƙarasa janyota jikinsa, yana shafa kanta ya sumbaci lips ɗinta, anutse cikin wata irin fitinanniyar murya mai taushi, ya furta.
"My Baby duk nagaji ga bacci idanuna zafi."

"Ayyah! Sannu Sweet Dadynah bari na haɗa maka ruwan zafi kayi wanka koh?"
Fuskarta ya kamo ya haɗe da tasa, ahankali yace.
"Haaaa bakinki Babyna."
Anutse tana kallonsa jikinta na ƙara mutuwa ta buɗe bakinta.

Iskar bakinsa ya hura mata ya zura harshensa cikin bakinta yana yawo da harshensa cikin bakin nata, yana laso ko ina tare da sauke mata zafafan sumbata, wadda take sakata ƙanƙameshi tana jin wani irin bala'in sanyi na gauraya dukkan jikinta, dukkan gashin jikinta na mimmiƙewa.
Kissing ɗinta ya fara anutse yana tallabe da fuskarta idanunsu cikin juna.

Lumshe idanunta ta yi tana narkewa ajikinsa tare kamo harshensa tana tsotsa tana sauke numfashi.
Sannu hankali suke shayar da junansu wani irin yawu mai zaƙin gaske suna fitar da wani irin fitinannan numfashi.

Khairy yadda Dadyn nata yake koyar da ita kissing ɗin bakinsa sai ta ji duk duniya ba abinda ya fi mata bakinsa daɗi da ɗanɗano.

Ahankali ta zare bakinta anasa tana kallonsa idanunta tab hawaye tana lashe yawunsa can ƙasa muryata bata fita sosai tace.
"Dadynah me yasa nakejin yawunka yafi min komai daɗi da ɗanɗano a duniya?"
Bakin nata ya laso yana murmushi ya raɗa mata.
"So ne Ƙauna ce my Baby inajin fiye da yadda kikeji Ok?"
Idanunta ta lumshe tana laɓewa jikinsa tace.
"Ina sonka Dady love Kaine farin cikina."
Akunnenta ya raɗa mata.
"Nima haka fiye da ke Babyn Dady Oya je ki haɗa min ruwan kar a fara kiran sallah."
Kai ta jinjina tana lashe masa yawunta da ya ɓata masa gefen bakinsa, tana kallonsa kamar zatayi kuka, azababbiyar ƙaunarsa take wujijjiga mata zuciya, ji take kamar ta hadiyesa dan ƙaunarsa.
Haɓarta ya ɗago yana lasar idanunta, hannunsa ɗayan ya ɗora akan ƙugunta ƙasa_ƙasa yake mata magana suna kallon junnasu.
"Ina sonka Khairynah ina jin ƙaunarki har cikin jinin jikina ɓargon ƙashi Ok my Baby?"
Idanunsa ta laso tana sake ƙanƙameshi ta ɗora bakinta akan nasa tana kamo laɓɓansa ta shiga sha kamar ta samu lollipop, ta lumshe idanunta.
Shattima ya sake tallabota yana shafa bayanta ya zuba mata idanunsa yanajin jikinsa na ɗaukan vibration, ƙaunarta na wujijjiga zuciyarsa.

Da sauri ta zare bakinta anashi tana kwaɓe fuska, ta sauka daga jikinsa ta nufi Bedroom ɗinsa.
Lumsassun kaifafan fararen idanunsa ya zuba mata yana sauke fitinannan numfashi.

Idanunsa lumshe ta dawo ta kamo hannayensa tana faɗin.
"Sweet Dadynah tashi na haɗama ruwan."
Idanunsa ya buɗe yana kallonta ya riƙe yana ɗaukanta sama yace.
"Ok muje ki tayani ba!"
Idanunta ta zaro tana wutsil-wutsil da ƙafafuwanta tace.
"A'a wlh naƙi Ni saukeni Dady bazan jeba, Ni dai Dady love saukeni ko nayi maka kuka."

Ta idar da maganan tana shirin saka masa kuka.
Sauketa ya yi yana dariya daman tsokanarta yake.
Aguje tabar falon nasa.
Shattima yace.
"Babyna kwana nawa ya rage kiyi bayani."

Khairy ƙasa ta sauka nan tayi alwala tana jiran kiran sallah, ta kira Mamy awaya bugu ɗaya ta ɗaga tana faɗin.
"Mamynah ina kika shiga ne?"
Daga can Mamy tace.

"Ga ni gidan Anne tana tambaya dake kam, anjima idan nayi sallar Isha'i zan taho Ok?"
Khairy zatiyi magana taji Shattima ya rungumeta jikinsa yana jan dogon hancinta.
Narkewa ta yi jikinsa ashagwaɓe tace.
"Toh Mamynta duk ba laifinki bane kina kallo Dady ya hanani binku, ai da kinsa baki zai barni koh?"
Mamy ta yi dariya tana faɗin.
"Naji nayi laifi Baby ai zakizo goben kafin ku wuce Abujan."
Khairy tayi dariya, tace.
"Yawwa Mamynah shiyasa nake bala'in sonki bye sai kinzo."

Ta faɗa tana katse kiran tana turoma Shattima bakinta tana kwaɓe fuskarta.
Sumba ya kai mata yana sakinta ya miƙe yace.
"Baby kinji an fara kiran sallah, na fita Maryam ta tafi ne?"
Khairy ta miƙe tana kamo hannun Shattima suka jera tana dariya.
"Wai Dadynah kasan yaya Usman yagani yana so wlh..."
Ta zayyane masa komai.
Shattima ya yi murmushi yace.
"Ai nasan za'azo wajan, nayi farin cikin hakan Allah ya tabbatar da alkhairi."
Khairy tace.
"Ameen Dady my love I love you, yawwa Dadynah ya maganar yarinyar nan da nace zan taimawa Please?"

Yana damƙe da hannunta har can ƙofar falon, ya sumbaci hancinta yace.
"Oya koma Babyn Shattima rakiyar ta isa haka koh? Wannan bakida matsala tunda tafiya zakuyi gobe, ki faɗa Lawan unguwar ki basa lambar ta za'a taimaka mata in Sha ALLAHU."

Kai ta ɗaga ashagwaɓe tana kallonsa.
Kusansa ya ƙara matso da ita, ya rankwafo ya sumbaci laɓɓanta yana lasarsu ahankali anutse yace.
"Babyna kice musu Dadynki na sonsu."
Cikin murna ta rungumesa tana murmushi.
Hannunsa ya zagaye bayanta yace.
"Baby Ana kiran sallah koma bari na tafi."
Kai ta ɗaga tana janyewa daga jikinsa tace.
"Bye sweetie Dadynah na gode Allah yasa ka gama da duniya lafiya."
Ta faɗa tana juyawa ta tafi.
Yana murmushi yace.
"Allahumma Ameen Babyna kema haka..."


Aliyah ta fito daga kitchen ta zauna tana kallon Umma na magana ta waya.
"Lallai kuwa tunda har kaga commissioner Aminu ya saka an shigar dasu ƙara kotu, toh babbar matsalace, ba dai Salim bayada hankali ba bayajin maganarmu ba, ai komai zai faru dasu."
Daga can Lagos Hashim yace.
"Lallai duniya ta juyamin baya dayawa, Sa'idah har ke, ɗan mu kikewa mugun baki koh? Ai addu'a zakiya Allah yasa hakan ya zama silar shiriya garesa nasan waye Aminu nasan waye Shattima wlh duk abinda zasuyi zasubi hanyar da zata saka ɗan mu ya dawo hanyane ba wai dan atozarta sa ba."
Umma tace.
"Aff ka dawo hanya ashe nima haka nake nufi baka fini son Salim ba, halinsa ne bana so."
Tsaki ya yi yana katse kiran.
"Hummm Allah shi kyauta."
Ta faɗa tana ajiye wayan, dan ba inda zataje neman belinsa ta fi son yaci ubansa da kyau yasan Allah ɗaya ne lokacin zaiyi hankali.

Aliyah da alamun damuwa tace.
"Umma lafiya? Me ya samu yaya Salim ɗin?"
Kallonta tayi tace.
"Ke kam bakisan ciwon kanki ba, toh bazan faɗa ba, idan zaki nutsu ki nutsu ki kama kanki ki fita sabgarsa kija jikinki ki nuna masa ke ayanzu bakya ra'ayinsa rabuwa kikeso kuyi wlh na tabbatar miki zai dawo hayyacinsa."
Aliyah tace.
"Toh Umma shi kenan..."

Dad Mustapah suna isowa bayan sallar Isha'i, ya tafi wajan Karima.
Lokacin da taji shine yazo nemanta jikinta har rawa yake ta fito.
Tun kafin ta ƙara so kusansa ya toshe hanci cikin tsawa yace.

Dan ubanki karki ismun nan, tsaya anan.
Ashe Karima ke karyace ban saniba? Bayan shirka har maza kike bi? Ni zaki munafunta kije waje ki kwaso cikinki ki aikamin ɗanki da takardar shedar kinada ciki? Yaushe rabona dake? Ko kin ɗauka Ni jahiline?
Toh wlh idan kika kuskura kika sake dangantani da haramtaccan cikinki nan sai na ɗaureki ɗauri me tsauri wlh kinji na rantse, asarariya."

Ya faɗa yana jefe mata mata takardar result ɗinta, ya buɗe mota zai shiga ta riƙe ƙafafuwansa tana kuka, ya hankaɗata ta faɗi yaja motarsa ya tafi.
Karima wani irin kuka take me tsuma zuciya baki ɗaya taji ta tsani duniya da abinda yake cikinta.
Kiran YANKAN WUƘA tayi tana kuka tace.
"Bazan taɓa yafe maka ba, ka cutar dani ka barmin abun kunya ka saka nayi ba, ban taɓa zina aduniya ba sai akanka akuma ranan da nayita tabarmin abun faɗa aduniya, ƴaƴana nagari masu tarbiyya ina baƙin cikin barmusu abun kunya da ace na haifi cikin shege da boka gwara na mutu na mutu na huta, na ragewa ƴaƴana takaicin ganima aduniya..."

Ta ƙarashe maganar tana katse kiran ta nufi bakin titi tana kuka da jin tsanar kanta ji take ta aikata abinda ko Ubangiji bazai dubeta ba.

(Batasan Allah shi gafuru rahim bane, matuƙar ka tabu da kyakkyawar niya.)

YANKAN WUƘA jin abinda Karima ta faɗa ya saka shi zabura yana faɗin.
"Alo kinajina karki zubarmun da ciki banda kowa sai cikin ban taɓa samun haihuwa ba sai akanki."
Sam bai ma san ta katse kiran ba kamo hanyar zuwa wajanta.
Bisa tsautsayi saida ya kusa shigowa gari kan mashin ɗin sa, ya gamu da karen hauka, tunda YANAKN WUƘA ya hango karen yasan karen haukane.
Ya ƙara gudun mashin ɗinsa hankalinsa tashe daman ancemasa bayan dutsen nan ana zargin akwai karen hauka.

Ai duk gudunsa a mashin sai ga karen nan yasha gabansa yana wani irin haushina hauka, ya yi wani irin tsalle ya nufi YANKAN WUƘA.
Cikin saddabarun da YANKAN WUƘA ya iya ya fara ƙoƙarin yi dan ceton kansa amman ina dama da ALLAH ya basa ta lokaci ƙalilan har ta ƙare atake karen nan ya ruƙunƙumi YANKAN WUƘA suka zube ƙasa ya dinga yagonsa da cizonsa, yana yaga masa kayansa saida ya masa zigidir haihuwar uwarsa ƙarshen karen nan ya kama ƴaƴan marenan YANKAN WUƘA duk ya fashesu da haƙoransa ya shanye ruwan, cikin, ya taune kan uwar gayyar.
Atake anan YANKAN WUƘA, ya dinga wani irin haushin kare yana fuzgar naman fatar hannunsa yanaci yana son ya miƙe ya kasa ko ɗaga ƙafafunsa sabida karen nan ya cinyemasa gabansa kawai ALLAH ne baiga damar kashesa ayanzun ba.

Karima tana isowa bakin titin wata mota Toyota Corolla ta taho da wani irin mugun gudu, kawai ta tareta aguje, motar tayi ciki da ita, tayi sama ta faɗo ƙasa motar tabi ta kanta tayi mata murza gyaɗa idan za'a cire manta.

Daidai lokacin Yalwa ta iso wajan ta ɗora hannunta akai tana kururuwa kafin a ankara me motar ya gudu kamar walƙiya ba wanda ya gansa.
Jama'a suka baibaye Karima da ƙafarta ta dama tana can wani gefe hannunta na hagum shima ya fita, fuskarta baka ganeta jini kace-kaca, sai lokacin Yalwa ta lura ƴan hanjinta awaje alamar dai ta mutu, cikin mawuyacin hali.
Kuka take tana faɗin.
"Jama'a ku taimaka min na shiga uku..."

Usman suna zaune a falo sun idar da cin abinci kenan, Nadiya na Masa hirar Maryam Zainabu na jinsu tana murmushi sai ga kiran, Yalwa.
Cikin kuka tace.
"Usman kazo yanzu."
Gabansa ya faɗa yana faɗin.
"Yalwa lafiya koh Mom ce ba lafiya?"
Katse kiran tayi, ya miƙe hankalinsa tashe.
Zainabu tana tamabyarsa da hannunta lafiya?
Arikice yace.
"Yalwa ta kirani kamar ba lafiya ba.*
Dad ya kallesa baice komai ba ya maida hankalinsu akan takardun gabansa.
Nadiya ta miƙe tace.
"Yaya Zan bika."
Da hannun ya yafito yana faɗin.
"Dad zan fita can gidansu Mom."
"Ok sai kun dawo kayi tuƙi cikin nutsuwa fa?!"

Zainabu ta kalleshi batayi magana ba dai.
"My Zeey kinada magana ne?"
Kusansa ta matso tana kwantar da kanta kafaɗarsa.
Kanta ya shafa yace.
"Ki nutsu ba komai karki damarmin kanki, Ok?"
Kai ta jinjina.

Lokacin da su Usman suka isa asibitin da aka kai Karima dan ajiye gawar kafin gobe agama binceke abasu, Nadiya suma tayi Usman kamar ƙaramin yaro yake kuka, yana jin tausayin mahaifiyarsa, ga ciwon jin an nemi wanda ya kadeta an rasa.
Dad lokacin da Usman ya dawo da Nadiya gida, bayan ta farfaɗo tana kuka, ya faɗa masa mutuwar Karima sai da ya jijjiga, ya tausayama mutuwarta cikin wannan halin da take, sai ya fara zargin ko abinda yaje ya matane yasa ta kashe kanta? Toh zai amshi ɗan da ba nashi ba?
Zainabu kuka sosai take da hawaye taki tausayin Nadiya da Usman ba kaɗan ba.
Washegari da misalin ƙarfe 10 aka tattara Karima aka kaita gidanta na gaskiya daga ita sai halinta, Dad ana dawowa daga jana'za baifi awa ɗaya ba ya tafi sabida yanada uzuri har yanzu Nadiya kuka take.
Zainabu

Please Login or Register in order to submit comment