Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata shedar ya sauko.

"Uhmm!"

Mamy tace tana murmushi tare da yagar tsokar cinyar kazar.

Maryam tace.
"Mamy lafiya?"

Mamy tayi ƴar dariya tace.

"Daɗin nama mna daughter."

Gyaran muryasa sukaji yana ƙoƙarin isowa wajan.
Maryam tai saurin waigowa tana sauke idanunta akan kyakkyawar baƙar fuskarsa mai wani irin kyawun saje da gemu mai tsari.
Kallo ɗaya yamata cike da mamaki ya janye idanunsa yana, kallon Mamy da ƙoƙari jan kujera.
Maryam tace.
"Welcome Dady good morning?"
Shattima ya zauna kusan Mamy yana kallon Mamy ya amsa.
"Lafiya lau daughter yasu Abbanki?
Maryam ta amsa.
"Suna lafiya Dady."

Da wata irin kalar nutsuwa da kamewa yace.
"Masha Allah."

Ya faɗa yana amsar cinyar kazar hannun Mamy yana mata wani irin kallo, yakai naman bakinsa ya cira yana taunawa.

Mamy bata yarda ta kallesa ba tace.
"Barka da fitowa Mi Amor, ashe kana gidan nazaci ka fita ina bacci tuntuni?"
Murmushi yay yana amshe cup ɗin hannunta ya fara kurɓar tea ɗin anutse yace.
"No! Ban fita ba! Tun yaushe kika tashi?"
Maryam wani irin yawu ta haɗiye mai ɗaci tana kallon Shattima yake cin naman sauran na Mamy da tea yana mata magana cikin wani irin cool voice, kyawawan idanunsa akanta.
Mamy ta kallesa tana sakin murmushi tace.
"Hope kana lfy? Bari na haɗe maka tea billahi girki ya yi daɗi ALLAH ya ƙara lafiya da wadata, tare da kwanciyar hankali me ɗorewa, kamar yadda nake ganin farin ciki zalla atare da kai yau Mi Amor."
Tsadaddan murmushi ya sakar mata yana riƙo hannunta zaiyi magana, Khairy ta iso kan dining din tana rungume Mamy ta bayanta tana dariya tace.
"Congratulation my sweet Mamy wallahi yau ina farin ciki zan kira Suhailat mu haɗa ƙaramar liyafa, ALLAH ya sauke min ke lafiya Sweet Mamynah."
Ta faɗa tana sake ƙanƙame Mamy tana dariya.
Maryam ta zama kamar mutum butumi, ta koma, da kallo take binsu zuciyarta na mata wani irin zafi yanayin numfashinta ya fara sauyawa, ta runtse idanunta, tana kiran sunan ALLAH.

Shattima yana riƙe da hannun Mamyn ya kalli Khairy yadda take farin ciki, ta maƙalƙale Mamy, wadda take ƙoƙarin juyo da Khairy gabanta.
Gabansa ya faɗi ganin sosai laɓɓanta suka kumbura, tausayinta ya ji ya kamasa sosai, bai san me zatace wa Mamyn ba idan ta tambaye ta me ya sameta.

Ya kauda idanunsa daga kallonta, ya kalli Mamy anutse yace.
"No! Sweetheart ki barsa idan naci sauranki ma ya isheni, sauri nake zan fita."
Mamy ta kamo hannun Khairy ta zaunar tana murmushi tace.
"Ni dai naƙi Mi Amor sai kayi breakfast zaka fita."
Maryam tace.
"Auntie Khairy Ina kwana?"
Khairy tace.
"Lah! Sister Maryam! Sorry wlh ban ganki ba ykk? Ina su Ammi da Abba?"
Maryam ta amsa da.
"Suna lafiya."
"Masha Allah, zaki wunin mana koh?"
"Maryam tace.
"Eh Auntie.

Khairy ta kalli Shattima wanda yake shan tea hankalinsa kwance, suna magana da Mamy ƙasa².

"Dadynah ina tsarabata?"
Kallonta yay yana haɗiye tea anutse, yace.
"Je ɗakina ki buɗe trolleyn ki fito da naki da Mamynki."
Cikin murna tace.
"Thank you sweet Dadynah, toh na sister Maryam fa?"
Idanunsa kan cup yace.
"Sai ki bata cikin naku duka na haɗa waje ɗaya ai."
Ta miƙe cikin murna zata tafi Mamy ta kamota tace.
"Maza zauna kiyi breakfast kafin kwaɗayin kayan zaƙi. Subahanallahi Baby me ya sameki a baki haka? Mugani."
Khairy taji wani irin abu, sai ta langwaɓar da kanta tana kwantar da kanta kafaɗar Mamy ta kasa mata ƙarya kuma bazata iya faɗin gaskiya ba.
Shattima ya dire cup ɗin yana ɗaukan wayansa da take ringing ya miƙe tsaye cikin kamewarsa tamkar baima san abinda suke ba, anutse yace.
"Sweetheart na fita."
Mamy tsabar son ɗaukan magana tace.
"Mi Amor Baby batada lafiya kalli bakinta fa!"
Ko wani alamun razana baiba ya juyo yana zubawa Khairy idanunsa masu firgitata ya ɗan haɗe face kaɗan yace.

"Baby! Faɗuwa kikayi ne?"

Khairy da sauri ta kallesa tana langwaɓar da kai gefe ashagwaɓe tace.
"Ni dai Dady ban wani faɗin ba, zan sha chocolate naci biscuit zan warke."
Ta faɗa tana janye idanunta akansa, sbd yadda wutar sonsa take ruruwa acikin zuciyarta, kar taje ta saki zance.

Murmushi Shattima yay yana shafa sajansa, ya kalli Mamy yace.
"Sweetheart kinji Wai chocolate zai warka da ita, ba dai ke bakya bacci sai gefen bed ba, zakiyi ta faɗuwa ƙasa."

Ya faɗa yana picking call ɗin yana barin wajan.
Mamy da mamaki ta bisa da kallo, sai ta saki murmushi tana zaunar da Khairy tace.
"Maza Baby kiyi breakfast sai na baki maganin da kumburin zai baje Ok?"
Kai Khairy ta jinjina tana ɗaukan cup ɗin tea ɗin da Mamy ta haɗa mata, tace.
"Mamy ki barsa zai sace ban son shan magani, Ni dai banajin zafi"

Mamy ta yi murmushi tace.
"Baby kinada son rigima, ƙila rikicinki ya ja miki hukuncin nan."

Ta faɗa tana barin wajan dan kar Khairy ta tambayeta hukuncin me?

Mamy ta iske Shattima yana waya can kusan ƙofar falon.
Hannunsa ta riƙe tana murmushi.
Yana gama wayan ya rungumeta yana sumbatar kumatunta ya shafa cikinta yana gangaro hannunsa ƙirjinta ya raɗa mata.
"Yane Madam Sweetheart? Ina baby na? Suna motsi?"
Ƙirjinsa ta buga da ƙarfi tana kicin-kicin da fuska.
"Na shiga uku me nayi?"
Ya faɗa yana ɗagata sama yana sumbatar goshinta zai sumbaci bakinta ta goce tana hararen sa, da murguɗa masa bakinta.
Dariya yay ya direta ya kamo hannunta ya buɗe ƙofar yace.
"Sai nadawo i love You."
Cikin turo baki tace.
"ALLAH Ya tsare Dady Babyn Babies."
Dariya yay sosai yana faɗin.
"Yeah yeah nine nan sweetheart zan siyo muku abu me daɗi, ki shafamin kansu."
Ya faɗa yana ficewa.
Ƙofar ta rufe tana juyawa.
A falo ta isko su Khairy suna hira da Maryam wacce baki ɗaya ma hankalinta ya fara gushewa tsabar baƙin cikin abinda ya kawota gidan ma.

Mamy tace.
"Baby bakici komai koh?"
Khairy tace.
"Wlh naci mamy."
Bari naje na kawo chocolates da biscuits."
Ta faɗa tana miƙewa ta nufi Stairs...
Maryam gaza zama tayi da rana tsaka ta tafiyarta Khairy ba yadda batayi ta tsaya zata haɗa walima taƙi, tace zata dawo gobe.
Mamy ta saka aka kaita Khairy ta bata tsaraba cikin tsarabarsu.

Shattima yana shiga mota ya kira Dad Mustapah yace Anjima Khairy Maleek zai kawota Gumel.

Salim bai rufe awa daya ba ya iso gidansu Azizah.

Azizah ta kalleshi tana faɗin.
"Shin ka san wa ya auri Ummulkhairi?"
Salim yace.
"Ya kuwa zan sani idan ba'a faɗa min ba?"
Azizah tace.
"Minister Abdallah Wanda kuke kallonsa matsayin mahaifiyata shine mijinta..."
Wani irin ja da baya yay yace.
"Karki min maganar banza mana, ko agarin arna ai ba'a hakan."
Tsaki taja tace.
"Ok shi kenan kaje kayi binkice idan ka gano gaskiya sai kazo mu ɗauki matakin da zamu ɗauka."
Ta faɗa tana juyawa yay saurin dakatar da ita yace.
"Naji na yarda Amman ina mamaki ki ban iya labarin da kika sani?"
Azizah ta zayyane iya abinda aka faɗa mata.
"Kutumar uba akwai masifa da bala'i, amma ta ina zan fara rigima da Minister ?"
Kafaɗunta ta ɗaga tace.
"'ni dai bazan yafe ba sai na rama."
"Ok ta ina zamu fara?"
Azizah tace.
Zamu fara kama Khairy mu ɓoye muce sai ya kawo kansa ba tare da kowaba idan yazo sai mu ɗauki duk irin fansar da zamu ɗauka daga nan sai ka aure Khairy tunda bazamu bari taga asalin fuskarmu ba.
Amman fa sai bayan salla kasan duk iskancina ina girmama wata me tsarki watan Ramadan."
Salim yace.
"Hakan ma ya yi wata ɗaya kamar gobe ne, daman kuma sacan ce ba sabuwa bare na takura sai ta fito da wuri...."
Suka sheƙe da dariya suna tafa hannayensu....

Khairy ta kira Suhailat tazo suka shirya walimar su uku, Mamy sai dariya take.
Ana haka
Abba Aminu da Ammi sukazo taya murna, suka haɗu su biyar Shattima da yake wajan wani taro yazo suka haɗu su shidda.
Suka ci suka sha suka godema Allah da ya basu wanna kyauta.
Sai ƙarfe uku su Ammi suka tafi, bayan la'asar Shattima ya kira Mamy yace Khairy ta shirya Maleek zai kaita Gumel.
Mamy da yake tasan da magana tun kafin yazo ƙasar bata tambayesa dalili ba yana katse kiran ta haye Stairs ta cika umarni Shattima.
Khairy kamar zatayi kuka ta shirya kayanta, ƙatuwar trolleyn ta cika...
5 pm Khairy suka fita daga gidan tana hawaye tana ɗagawa Mamy hannun wacce ta rakota har bakin mota.

Basuyi nisa ba da fita Maleek yay parking a wani guri me kyau ya fita.
Kanta ƙansa tana kukan rashin sallama da Dadynta.
Anutse ya buɗe motar ya shigo.
Ƙamshin fitinannan turarensa ya baibaye hancinta, ta ɗago da sauri tana kallonsa yana zama kusanta.
Cikin farin cikin ganinsa ta kirasa.
"Sweet Dadynah!"
Rungumeta yay ya rufeta da ƙirjinsa tare sumbatar bakinta ya amsa.
"Na'am my baby nine koh?"
Kai ta ɗaga tana tsiyayar hawaye.
"Ok toh ya isa ba ganiba."
Ya faɗa yana lashe mata hawayen fuskarta, tare buga bayanta.
Ashagwaɓe tace.
"Sweet Dadynah Ina sonka dayawa zanyi kewarka."
Anutse ya riƙo kanta ya ɗora bakinsa akan nata yana lasar laɓɓanta yana hura mata iskar bakinsa, cike da tausayinta.
Ashagwaɓe ta riƙo fuskarshi tana kamo laɓɓansa tana tsotsa.
Ganin yadda laɓɓanta suke kumbure yaƙi tsotsa dan kar su ƙara kumbura, ya gyara mata kwanci jikinsa tana shan bakinsa son ranta.
Ta jima kafin ta zare bakinta tana cusa kanta tsakanin wuyansa tana sauke numfashi.
Raɗa ya mata cikin kunnenta.
"Babyn Shattima kinsha ya isheki hakan?"
Asangarce ta ɗaga kanta tana kallon shi tana matsar hawaye.

"No? Baby karkiyi kukan idan bakya son tafiya muje gida abin mu Ok?"
Wasa ta shiga da sajansa a hankali tace.
"Sweet I love you wlh sonka nakeji har cikin ɓargona zaka soni kaɗan nima?

"Ya Ilahi! Baby Ina sonki Ina ƙaunarki, I love you Okay?"
Wani irin ihun daɗi tayi tana maƙalkaleshi tace.
"Ngd my sweet love Dady Shattima my husband..."
Dole ya kamo bakin ya shiga tsotsa slowly ta shiga tayasa suna sauke wani irin fitinannan numfashi atare.
Gudun kar bakinta ya ƙara kumbura ya zare bakinsa yana matseta cikin jikinsa sosai yana lumshe idanunsa.
Khairy tace.
"My husband my sweet love Dady dan ALLAH karka rabu dani ina sonka."
Shiiit! Baby Khairyn Dady bazamu rabuba sai mutuwa, ki nutsu idan kinje ga wayanki zan kiraki zuwa dare banda rikicin banza, idan Dad ɗinki ko ummanki sun tambayeki me ya sameki a baki kice faɗuwa kikayi Ok?"

Dariya tayi tana shafa fuskarsa tace.
"Ni dai ba zanyi ƙarya ba zance madubin dubawa Nah yasha halaliyarsa."
Idanunsa ya zaro mata yana kama kunnenta yace.
"Da na cire kunnen me surutu, kalleni nan ko na baki mari."

Marerece fuska tai tace.
"My sweet love Dady karka mareni laɓɓana zafi."
Iska ya hura yana sumbatarso da wata kalar murya yace.
"I'm sorry my Baby, toh me yasa da safe Mamynki na tambaya baki faɗa mata ba?"
Narai² tai da idanu tace.
"Ai ita bazan taɓa yi mata abinda zataji kishina ko tsananta ba, ya zan iya cemata Dady Shattima ya shanye min bakina ba, Dadynah ƙamshinka na musamman ne."
Murmushi mai taushi yay yana shafa fuskarta ya sumbata yace.
"I love You my Baby sai nazo ganinki Babyn Minister banda rigima Anjima zan kiraki video call."
Jikinsa ta shige tana rufe idanunta, tace.
"Toh Dady love karka min irin na Katsina kaƙi zauwa, Allah yanzu bazan jure ba."
Ta faɗa tana kallonsa.

Shattima bai san kalar ƙaunar da yakewa Babynsa ba, wani irin tausayi take basa ganin yadda ya kumbura mata laɓɓanta wajan horonta amma taƙi tai masa fushi sai ma sonsa da yake gani tana ƙara faɗawa mararan.
Da
ƙyar ya samu ya lallaɓata ya bata wayan ya fita, Maleek ya shigo security na gefensa riƙe da bindiga ya yin Babyn Minister tana baya zaune tana murmushin zallar farin ciki.
Maleek yaja motar suka kama hanyar gumel tana cike da kewar Dadynta, ya gama kasheta da zazzafan love ɗinsa.
Har sukayi nisa atafiyar Khairy bata ankare ba, sabida tana cikin shaukin Dadynta.
Idanun na kallon waje ta furta.
"Allah Sarki! Mamynah na jinjina wa jarumtarki da kika iya mallaka min Sweet love Dadynah, wayyo Mamynah i Love u kaca-kaca..."

Toh Ummulkhairi ALLAH saukeku lafiya Amin.

Real Ladingo Omu Farisah

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 23/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*94*

Shattima yana shiga mota bayan tafiyar Khairy, ya laɓe cikin kujera yana lumshe kaifafan fararen idanunsa, yana furzar da iskar bakinsa.
Wani irin tsadaddan murmushi ya saki yana shafa sajansa, zuwa gemunsa.
Wayansa ya ɗauka ya shiga ma'adanar lambobi ya kira Auntie Aisha.
Bugu biyu ta ɗaga tare da sallama.
Anutse ya amsa cikin girmamawa da kamewarsa ya gaisheta, tare da tambayata yara da mai gidanta.
Auntie Aisha ɗaga can tana dariya tace.
"Shattima Abdallah baban ƴan biyu inda sha Allah,barka da yamma ya gajiya? Ina Bilkisu da sabon babynmu fatan tana lfy bata jinya? Ya Ummulkhairi? Da su Baffa Inno hope kowa yana lafiya Allah yasa hakan?"
Anutse ya amsa mata.
"Alhamdulillah! Kowa lfy Baby yanzu ta tafi gumel."
"MASHA ALLAH, toh yaushe ne kake ganin ya dace tazo ne Abujan? Ya kamata na fara shiyar ƴata."
Ɗan murmushi ya yi yace.
"Uhmm? Zata zo bayan sallah in sha ALLAH, inaso zamuje umarah da Bilkisu muyi godiya ɗakin Allah, akwai cikin ƴan uwa dayawa da abokanan arziƙi da basu taɓa zuwa ba, zan biyawa waɗanda Allah yasa da rabonsu mutum 6 ko 7 suma suje albarkacin samun cikin Bilkisu, hajji idan tazo za'a duba wasu akai daga baya idan ya amince zan maida wanda zamuje umarah dasu su sauke farali."
Auntie Aisha tace.
"Masha Allah Ubangiji ya biyaka ya sauketa lafiya, ai anan zakuyi sallah ko?"
"A'a can zamuyi in Sha Allah da mun dawo, Baby zata dawo nan wajanki."

"Ok Allah ya amshi dukkan ibadun zakuyi acan, ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, zan taho da abata dan ya kamata bayan sallar layya ayi bikin ko sai Bilkisu tare haihu?"
Shattima ya numfasa yace.
"Duk yadda kukayi banida matsala da matata."
Dariya Auntie Aisha ta yi tace.
"Ok Idan Allah ya kawoku lafiya idan nazo zamuyi magana da Baffa har Bilkisu naji dan ita ya kamata ayi shawara da ita akan komai...."
Hira sukayi sosai yana baya hakimce ana tuƙasa, sun jima suna tattaunawa kafin suyi sallama.

Tafiyar awa ɗaya ta kawosu Gumel daga jigawa cikin ikon ALLAH.
Suna shiga gumel Maleek ya kira Dad Mustapha, ya sheda masa sun iso.
Dad Mustapah ya faɗa masa inda zai tsaya za'a zo tarbansu.
Khairy sai kalle-kallenta take, batasan gumel nada kyau haka ba, ashe babban garine sosai, tana de jin sunanta.

Zainabu da Nadiya sun shiryama Khairy abubuwan tarba.
Da kasan ya tarbesu suka zo gida.
Khairy sosai ta yaba gidan mahaifin nata.
Tana fitowa daga mota aguje ta nufesa ta rungumesa tana dariya.
"Welcome back Khairyn Dady Shattima."
"Thank you Dad Ina wuni?"
Hannunta ya kama suka nufi ciki yana amsawa da.
"Lafiya lau Ummulkhairi yasu Dadyn naki? Fatan kowa lafiya?"
Tana murmushi tace.
"Alhamdulillah! Dad."
Suna shigowa falon Nadiya ta taho aguje ta rungumeta tana faɗin.
"Oyoyo Auntie Khairy."
Rungumeta tai tana faɗin.
"Ngd my Nadiya, Ina Umma?"
Zainabu ce ta sauko daga upstairs tana murmushi.
Khairy ta tafi da gudu ta rungumeta, tana fad'in.
"Kai MASHA ALLAH Umma irin wannan kyau haka sai kace wata budurwa, kinyi mul_mul abunki Umma."
Zainabu tana murmushi ta kai mata duka tana jan kunnenta alamun bata jin magana.
Jan hannunta tai suka zauna tana mata sannun da zuwa.
Mustapha sai murmushi yake zuciyarsa fara fess.
Usman ne ya shigo da ƙatuwar trolleyn Khairy yana faɗin.
"Oyoyo my sister."
Wajansa ta nufa tana rungumesa tace.
"My brother Ina wuni na sameku lfy? Ya jikin Mom Allah bata lafiya."
Nadiya ta amshi trolleyn tana ja tana nufi upstairs.
Usman yace.
"Dad! Maleek yace a faɗa maka zasu koma."
"Au Kenan ba kwana zasuyi ba?"
Ya faɗa yana tafiya.
Zainabu ta kamo hannun Khairy suka nufi upstairs, Khairy tace.
"WoW! Umma gidanku da masha Allah gaskiya."
Zainabu da bebanci tace.
Ke ma ai gidanku ne.
Khairy ta fahimci abinda tace, sbd ɗan zaman da sukayi a Katsina sosai tayi ƙoƙarin gane maganarta watane bata fahimta.
Baki ta turo gaba tace.
"A'a Ni dai gidanmu Dutse."
Zainabu kai ta girgiza tana murmushi.
Ɗakinta na musamman da Dad ya qare mata agidan wanda yake facing da na Nadiya Zainabu ta kaita.
Tsalle tai tana faɗin.
"WoW! Komai ya yi ɗakin Nadiya ne?"
Zainabu ta girgiza tana jan dogon hancinta ta nunata natane.
Baki ta turo tace.
"Ni dai zan ina kwana ɗakin Nadiya."
Zainabu ta jinjina kai ta mata nuni ta shiga bathroom tayi wanka.
Kai ta ɗaga tana cire kayan jikinta...

*Jigawa*
Maryam zaune tayi tagumi tana tunanin abinda ya faru yau gidan Dady Shattima, sam bata ga wata hanya ba da zata samu karɓuwa wajansa, kowace cikin matansa tagane bala'in sonsa take, haka shima taga tsagwaron so da ƙaunar da yake nuna musu.
Hawaye masu zafi suka shiga silalowa kan fuskarta, tana jin zuciyarta na mata zafi sosai, bata san me yasa ba idan ta yi kamar ta haƙura da Shattima sai abun ya dawo mata sabo.
Ammi ta fito daga kitchen hannunta riƙe da cup zata wuce falon Abba Aminu ta hango Maryam zaune tana kuka wanda bata ma san ya kuɓuce mata ba.
Ammi ta wuce falon nasa tana shiga ta basa cup ɗin ta juya zata fita ya kamo hannunta yace.
"Zauna magana zamuyi akan Maryam."
Kallonsa tai tana faɗin.
"Ina zuwa gata can tana kuka tabbas yau sai ta faɗa mana damuwarta, nifa wlh bazan zuba idanuba ƴata ta mutu a banza."
Ta faɗa tana zame hannunta ta fita.
Kusan Maryam ta zauna tana kamo hannayenta ta riƙe da hannunta ɗaya, ɗayan hannun ta kamo fuskarta tana shafa hawayen.
Maryam ta zabura tana kallon Ammi ta tsayar da kukan nata.
Murya ba wasa tace.
"Bakin tika-tika-tikkk, yau sai kin faɗa mun me yake damunki tsawon shekara har wasu kwanaki tun kafin mutuwar Abdoul kike cikin wannan yanayin, yanzu ne abun ya fara ƙarfi, me yasa kwana biyu kina mutum kwana biyu ki rikice, yau me ya faru bayan fitarki da kika shigomin arikice hakan?"
Maryam ta fashe da kuka yau takai iya haƙurinta ya kai ƙarshe koda bazata samu Shattima ba zata faɗawa iyayanta tasan bazasu taɓa faɗawa kowa ba.
Ammi tace.
"Subahanallahi Maryam! Me yayi zafi har haka? Ok tashi muje wajan Abbanki."
Ta faɗa tana kamata ta miƙe suka nufi falon Abba Aminu.
Da kallo ya bisu yana ajiye cup ɗin hannunsa, yace.
"Bani ita nan Abinda."
Ya faɗa yana beƙa mata hannunsa.
Hannun Maryam ta damƙa masa, ya kama ya zaunar da ita kusa da shi, yana riƙe hannunta, anutse yace.
"Maryam! Me ya faru ne? Meƙe damunki mu iyayanki ne bakida waɗanda suka fimu? ko kinada Maryam?"
Kai ta girgiza cikin kuka tace.
"Babu Abba kuyi haƙuri abun ne da nauyi, nayi-nayi na haƙura tun lokacin da Mamy take nemawa Dady Auntie Khairy aurenta, amman na gasa haƙuri Abba! Ammi! kuyi haƙuri, wallahi ciwon son Dady Shattima yake neman kasheni..."
Da wani irin sauri Abba Aminu ya sanya tafin hannunsa ya toshema Maryam baki, yana faɗin.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil La hula wala Quwata illah billah, Maryam!"
Abba Aminu ya faɗa hankalinsa tashe.
Ammi ƙafafuwanta suka gasa ɗaukan ta tana tsaye tun shigowarsu bata zauna ba ta dafe kafaɗar Abba ta zauna kusansa ɗayan gefen tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me zanji me zan gani yau Maryam!?
Daman duk ciwon da kike da zirganiyar zuwa gidansa shi kike so ba ko kunya abokin mahaifinki kike so? Maryam mijin Bilkisu ne fa! Wani irin abu ne wannan kikayi? Toh wlh bana goyen bayanki idan so cutané haƙuri maganine"
Ta faɗa tana share hawayen fuskarta.
Maryam ta fashe da wani irin kuka tana faɗin.
"Kuyi haƙuri iyayena nasani ban kyauta ba, kawai na faɗa muku ne dan na rage raɗaɗin da nakeji acikin zuciyata, nasan ku iyayena bazaku taɓa fitar da magana ba, kuyi min Addu'a Allah ya ciremin sonsa araina bani na sakawa kaina ba."
Abba Aminu ya goge mata hawayen fuskarta, abun ya girmame masa matuƙa, haƙiƙa tausayin ƴarsa ya kama shi sosai, yasan tunda har ta bayyana musu ta gaza riƙewa toh ba ƙaramin so take masa ba.
"Maryam! Kiyi hakuri bansan ta inda zan faroba, abinda nakeso dake kiyi haƙuri, kiyi addu'a Allah ya zaɓa miki abinda yafi zama alkhairi agareki, zan tayaki da addu'a amman har cikin zuciyata bana fatan Allah ya kawo ranan da zaki auri Shattima cin amanar ya yi yawa, me duniya zata kallemu? Shin me ma zakiyi gidan mace uku? Ko Khairy tirsasa shi akayi bare ke da kike soyayyar maso wani, sanin kanki ne Shattima mata ɗaya yake so Bilkisu, ki haƙura dan ALLAH ki cire shi azuciyarki dan ALLAH Maryam."
Rungumesa tai tana kuka tace.
"Kuyi haƙuri in Sha Allah zanci gaba da addu'a kamar yadda na saba kutayi kuma addu'ar iyaye bata faɗuwa ƙasa."
Ammi tace.
"Ai dole zamuyi addu'a ina fatan ba wanda kika taɓa faɗawa wannan maganar?"
Maryam ta jinjina kanta tace.
"Wlh ban taɓa faɗawa kowa ba."
Ammi tace.
"Yawwa Allah miki albarka kiyi haƙuri keda kanki kiyi zaune kiyi tunani ace yau Bilkisu tasan wannan maganan ya zakiji? Akwai kunya don Allah kiyi haƙuri, Maryam duk abinda ka saka aranka zaka iya haƙuri da shi wlh zaka iya, ki kalli son da kikewa minister kamar son da kikewa Abbanki kallon mahaifinki toh zaki zauna lafiya."
Maryam ta jinjina kanta tace.
"Ina sha Allah iyayena zanyi."

Albarka suka saka mata suna mata nasiha da nuna mata illar furtawa Shattima so, duniya su zata zaga bayan haka me zatayi gidan mace uku, ta yi fatan ta samu nata mijin ita ɗaya.
Sosai yadda suka zaunar da ita suna mata nasiha abun ya shigeta sai de son Shattima Allah ne ya sakamata azuciya sai lokacin da yaso zai yaye mata...

Acan Gumel Khairy tana fitowa daga wanka ana kiran sallar Maghreb, ta yi sallah bata tashi daga kan darduma ba, sai da akayi sallar Isha'i, tana idarwa ta shirya cikin riga da zani na atamfa, ta yi kyau sosai, ta kunna wayanta ta kira Mamy, lokacin Mamy na can ƙasa tayi baƙi wayan na falon Shattima ta mantata lokacin da ta shiga ta gyara masa ɗakin ta kunna turaren wuta, bayan Maghreb.
Khairy tace.
"Wayyo Mamy tana ina bata ɗaga ba?"
Ta faɗa tana kiran Shattima.
Tanata ringing bai ɗaga ba, ta katse ta kuma kira, sai da ta kusa katsewa ya ɗaga, yana sauke mata numfashi mai ɗumi cikin kunnenta ta wayan.
Kamar zatayi kuka tana narkar da murya tace.
"Wayyo Sweet Dadynah I miss you kana Ina inata Kira shiru dan ALLAH?"
Shattima ya ɗan furzar iskar anutse cikin kamewarsa, yace.
"Miss You too my Baby, yau ba sallama ne?"
Baki ta turo gaba tace.
"I'm sorry sweetie Dadynah, ASSALAMU ALAIKA."
Wani irin murmushi mai kyau da burgewa ya saki yace.
"Wa'alaiki Salam Babyna, kin isa lafiya?"
Ƴar dariya tai tana lumshe idanunta tace.
"Alhamdulillah! Sweet Dadynah, kana Ina yanzun haka?"
Ƙaramin towel ɗin hannunsa ya ajiye da yake goge sumar kansa, anutse yace.
"Ina gida mana Baby yanzu na fito daga masallaci, ke kina mene yanzun?"
Saman lafiyayyan bed ɗin ta faɗa tana shagwaɓe fuska tace.
"Ina ta tunaninka ko ruwa na kasa sha tunda nazo my sweet Dady love, ka bari na ganka kaji?"
Shattima ya numfasa yanajin gashin jikinsa duka suna mimmiƙewa anutse furta.
"My baby girl please kici abinci ki ƙoshi anjima zan kiraki video call bana son ki zauna da yunwa kinji Babyna?"
Kukan shagwaɓa ta sakar masa tana harba ƙafafuwanta tace.
"ALLAH NI dai sai naga Dadynah zan iya cin wani abun."
"Ya Hayyu Ya Qayyum! Baby kina son na kwanta da damuwa koh? Toh yanzun haka kike so na kiraki ba kaya jikina sai towel?"
Matsagaitan danunta farare masu haske ta zaro tana katse kiran, ta jefar da wayan tana rufe idanunta, alamun kunya, sai ta ƙyalƙyale da dariya tana miƙewa ta fesa turare kenan, sai ga Nadiya ta shigo da sallama.
Khairy ta amsa tana kallonta.
Nadiya tace.
"Auntie muje muyi dinner."
Khairy ta kama hannunta suka fita.
A cikin farin ciki da annushuwa suka haɗu akan dining sukayi dinner Usman Nadiya Zainabu Mustapah, abin gwanin ban sha'awa, kowa na nan da nan da Khairy, ta tsinci kanta da farin ciki da annushuwa...

*Jigawa*
Zaune suke a falo bayan sun gama dinner.
Mamy ta kalli Shattima yana danna laptop waya manne akan kunnensa.
Murmushi tai tana shafa fuskarsa, ta sumbaci tsinin hancinsa, tana sosa sumar kansa.
Kansa ya ɗago yana tsayar da danna laptop ɗin, ya mata wani irin kallo yana kashe mata ido ɗaya.
Ramawa tai tana ɗaukan remote ta canza channel, tana maida hankalinta akan Tv dan ta basa daman yin wayan anutse.
Yana idar da wayan ya damƙo anutse cikin daddaɗar muryasa yace.
"Da kin saka na saki layi a maganata da kin sani."
Ya faɗa yana janye rigarta ya shafi cikinta ya duƙa yana sumbatar cikin nata.
Dariya tai tana fad'in.
"Mi Amor! Tsaya kaji Please mana."
Hannunsa ya ƙara zurawa can gaba yana wani irin shu'umin murmushi, ya raɗa mata.
"No! Nima tsaya zanyi wa my baby magana."
"Mi Amor ɗazu bayan tafiyar su Auntie Madinah munyi waya da Baby tana gaisheka."
Shattima bai fasa yawo da hannunsa inda yaso kaiwaba, ya ɗan murmusa yace.
"Na amsa sosai ya gajiyarta? Sweetheart ɗan dafamin shayi me daɗi."
Da "Toh"
Ta amsa tana murmushi ta miƙe tana nufi kitchen.
Da misalin ƙarfe tara na dare aka fara shelar anga wata, ana ta faɗa gidajan Tv da Radio.
Shattima Liman ya fara kiransa ya faɗa masa, kafin Commissioner Aminu, sai yayansa Munnir.
Dan haka da niyar azumi suka kwanta 30 ko 29, sai da sukayi sallah raka'a biyu suka roƙi Allah subhanahu wata'ala yadda aka ga wata lafiya zasu fara ibada Allah ya gwada masu watan sallah lafiya yasa ibadar da zasuyi acikin wannan wata karɓaɓɓiyace.
Shattima bai samu daman kiran Khairy ba tun tana saka ran kiransa har tayi bacci wayan

Please Login or Register in order to submit comment