Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin taushi, sai fitinannan ƙamshi yake zubawa, wanda ya haɗu da sanyin A/c ga turaren wutar da Mamy tayi ɗazu.

System ne agabansa yana dannawa.
Sai ajiyar y yake saukewa yana shafa sumar kansa.
Wulleliyar wayansa Samsung ta ɗauki ringing.
Furzar da numfashi yayi yana ɗago da kansa, ya zuba manyan lumsassun kaifafan idanunsa, akan wayan.
Auntie Aisha sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayan.
Auntie Aisha.
Tattausan hannunsa ya beƙa yana ɗan sakin huci me zafi, ya ɗauki wayan yana ɗaga kiran tare da kai wayan kunnensa, cike da nutsuwarsa, da kamewa muryasa mai taushi ya mata sallama.
Daga can Auntie Aisha ta amsa tana faɗin.
"Ran Minister ya daɗe yana jan ragamarsa."
Shattima yay ɗan ƙaramin murmushi na Dattaku, yace.
"Kai Auntie ai babu wani abu da yake ɗorewa adorom ƙasa, nifa na kusa na nayi ritaya na huta."
Auntie Aisha tace.
"Tabb ai wlh ko zaka fasa hawa kujerar ka ta Ministan ilimi na tabbata sai ka kai shekaru 60 lokacin muma muna buƙatar ka huta, kaga kuwa shekarun da saura yanzu ma12 kafin kayi sittin, ai jama'a ce ke ƙaunarka sabida haka kawai aci gaba da gashi, ALLAH ya maka jagora yasa munada rai da lafiya,Amin . Yawwa daman dan nace maka ne munyi magana da Abban Hamza ya amince gobe zan shigo da safe idan anyi sallar azuhur sai mu biyo flight hakan yayi koh?"

Shattima ya jangina kansa da da allon sofan da yake zaune yana furzar da iskar bakinsa waje.
Kafin ya tattaro dukkan nutsuwarsa anutse yace.
"Aunt an samu akasi..."
Tsaf ya labarata mata halin da ake ciki, ya ɗora da cewa.
"Baffa yace atafi da ita, kinga kuwa ai bazai yiyuba adawo da ita, dole za'a barta ta saba da danginta da mahaifiyarta, idan ta kwana biyu sai ta dawo."
Auntie Aisha tace.
"Kai masha ALLAH naji daɗi sosai, amma yanzu dole za'a bar biki har bayan sallar azumi tunda ya kusa kaga bai fi kwana arba'in da biyu ba, ya kamata ta saba dasu koda ana gobe azumine sai ka kawo min ita na shiga gyara, dan tun haihuwarta kasan nayi alƙawarin Ni zan gyara ɗiyata da kaina."
Shattima ya shafi sajansa kaɗan yana murmushi yace.
"Ok ai kinsan Jigawan ma dole sai ta zauna su saba da mahaifinta, zanga yadda za'ayi insha ALLAHU Auntie Baby zata dawo hannunki."
"Yawwa Ngd Allah ya tabbatar da alkhairi zan kirata gobe..."
Hira sukayi ta ƴan uwa kafin suyi sallama da juna.

Tsintar kansa yay da lalu lambar ta yau dialing, yana ji tana ringing ba'a ɗaga ba.
Alokacin kuwa Khairy tana kwance saman gadon Inno mai rumfa tayi lamo, sai juyi take, tana matsar ƙwalla babu abinda take so da buƙata kamar gata ga Dadyn a irin wannan lokacin, tana zuba masa shagwaɓa, yana lallaɓata.

Wayanta da take rungume a ƙirjinta, wadda ta gwada ta kira Dady yafi sau goma ta kasa tunda yace bakinta baida wayo, idan ta kira me zata cemasa? kuma yanzu ƙilama yana tare da Mamy, ai zata takurasu, sai ta kira Mamyn taji wayan akashe sai ta saki ƙaramin kuka tana jin kewarsu baki ɗaya tana gauraye jinin jikinta da ɓargo.
Daidai lokacin taji wayanta na vibration alaman kiranta ake.
Da sauri ta zabura ta ɗago wayan tana kalla.
Sai da taji wani irin faɗuwar gaba ganin sunan Sweet Dady na kiranta.
Cikin murna tana sakin murmushi can ƙasa² tace.
"Su ma sunata tunani Allah Sarki sweet Dadynah."
Ta faɗa tana ɗora yatsanta wajan ɗaukan kiran, dan ta ɗauka, sai kuma ta fasa ta saka wayan silent, ta miƙe zaune ta sauko ta sanyan wayan charge, ta wuce toilet, tana waiwayen wayan, tana tsuke baki.

Shattima ganin har ta katse bata ɗauka ba sai yayi tunanin tayi bacci, dan haka bai sake kira ba ya kashe wayoyinsa baki ɗaya, yana sauke numfashi ajere-ajere, yana danna system.
Ƙofar falon ta murɗa ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Wani irin lafiyayyan ƙamshi yake tashi ajikinta, tana sanye da kayan bacci, masu samtsi, sun mata kyau sosai, pink colour. Tana ɗauke da cup na glass mai wani irin shegen kyau ruwan zaiba.
Sallamar ya amsa anutse, yana ɗago kansa ya kalleta, yana sakar mata tattausan murmushi.
Kan cinyarsa ta zauna daram tana sumbata tsakiyar kansa, ta tallabo fuskarsa, tana manna masa cup ɗin bakinsa.
Ɗan ƙaramin Ƙugunta ya riƙu yana sakin murmushi ya kurɓi haɗaɗɗan coffee ɗin da ta dafo masa.
"WoW! Sweetheart yayi daɗi sosai."
Fuskarta ta matso dab da tashi tana fito da harshenta ta lashi lallausan lips ɗin san tana sake manna masa cup ɗin.
Anutse yake sha tana basa duk haɗiya ɗaya sai ta lashi lips ɗinsa, shi kuma yana famar sakar mata tsadaddan murmushin sa mai kashe mata gangar jiki.
Ahaka ya shanye tass tana shafa fuskarsa, tace.
"Mi Amor muje ka huta yau duk ka gaji kana bukatar tausa."
Dogon hancinta yaja baice komai ba ya kashe system ɗin ta sauka daga kansa kai tsaye ta shige bedroom ɗinsa.
Daman ya gama shirin baccinsa haka can ƙasa ya rufe ƙofa da kashe ƙwayayen wutar falon wanda suke launi daban².
Key ya murza a ƙofar falon, yana kashe ƙwan wutar falon ya nufi bedroom din.
Nan ma cike da nutsuwarsa ya rufe, ya nufi bathroom yana kallon Mamy da baje saman bed ɗinsa tana zaune ƙafafuwan ta meƙe.
"Hy ƴan matana?"
Hararen so ta Masa tace.
"Hi my samari."
Siririyar dariya yay ya shige bathroom.
Bai jimaba ya fito, yana kashe ƙwan wutar ɗakin ya ƙara so ya kunna ta gefe bed mai wani irin duhu-duhun haske mai bada kala gwanin burgewa.
Bismillah yay ya hauro saman bed ɗin yana kamota suka kwanta yaja duvet ya rufe su yana wani sanyata cikin jikinsa, hannunsa saman marata yana shafawa, can ƙasa² cikin wata tsadaddan murya yace.
"Matata Billy ina bala'in sonki wlh, matso kiji wata magana me tsada daga Ni sai ke abin mu."
Cikin Wata irin kasala da ya sakar mata, tana ƴar shagwaɓarta tace.
"Uhm-uhm Mi Amor Ina zan matso bayan agame muke ko haki bazai iya ratsa tsakanin mu. Ni ka sakeni tausa zan maka."
Ƴar dariya yay yana kai bakinsa kan kunnenta, can ƙasa yace.
"Bana son wata tausa kema kin gaji ni zan miki har sai kinyi bacci, matso kiji hiramun ta sirri."
Sake manne masa tayi tace.
"Toh gani faɗa min Please Mi Amor ɗina."
Bakinsa cikin kunnenta, yana shafa marata, yana ganagrowa ƙirjinta, cikin wani irin salo yake komai, anutse yake mata wasu irin maganganu masu tsada na sirri tana wani irin ƙanƙameshi tana jin ita kam ta gama dacen miji duniya da lahira.
Bata san lokacin da tayi bacci ba, daɗin shauƙin kalamansa, da shafar da yakewa ƙirjinta.
Murmushi yay ganin tana baccin anutse, sake shigar da ita jikinsa yay yana karanto musu addu'o'in bacci idanunsa alumshe, ba wani jimawa shima baccin mai shegen daɗi ya ɗauke shi.

Yalwawa
Azizah zaune gefen bed ɗinta tana girgiza ƙafa ko alamun bacci babu atare da ita, duk da kuwa yadda dare ya tsala.
Juyi take tana tuna soyayyar da suka da Abdoul bai kamata ace bata ɗauki fansar wanda yay sanadin rasuwarsa ba! Dan ya aure matarsa.
Wayanta ta janyo ta kira lambar Suhailat, ƙawar Khairy kasancewar cousin ɗinta ce, duk da basa wata alaƙa halinsu haka ba ɗayaba.

Suhailat cikin bacci taji ƙaran wayanta, da ƙyar ta buɗe idanunta.
Ganin sunan Azizah taƙi ɗagawa tana jan tsaki tare da faɗin.
"Uban me zan bata a tsohon daren nan? Ji take kowa irinta ne?"
Ta idar da mgnan tana saka wayan a silent, ta koma ta kwanta.
Azizah ta gaji da kira Suhailat bata ɗaga ba, dole ta haƙura ta barwa safe...

Washegari bayan sallar asubah su Shattima suka gama shirin tafiya, shi da Mamy sunyi shigar alfarma kayansu iri ɗaya wata dakekiyar shadda mai azababban kyau da tsada, ga maiƙo, Purple colour, kana kallonsu sai ka sake kallonsu, sabida sun haɗu, sai wani sahihin ƙamshi suke zubawa.
Mota ta musamman Shattima ya saka Lawan direba ya fito da ita wadda su Dad suka shiga shida Karima da Usman, sai a parking lot ne Mamy da Karima suka gaisa, yadda take kallon haɗuwar Mamy kamar zata fito da idanunta.
Sosai take farin cikin haɗuwa da mutanan nan alkhairi, nan gaba kaɗan zasu zama wasu suma duk da suma sunada nasu arzikin amman ai duniya bata sansu ba.
Motar da zata ɗauki liman da Nadiya da Khairy daban, direban Liman ne zai tuƙasu.
Maleek direba bayan Shattima da Mamy sun kame bayan motar, mai shegen kyau. Babban Guard ɗin Shattima na kusan Maleek da zungureriyar bindigarsa yana sanye da kakin sojoji Maleek yay bismillah tare da addu'a hawa abin hawa yanama motar key ya nufi ƙaton gate.
Motar su Hajiya Karima na bin bayansu suka nufi Anguwan Galadanci...
Real Ladingo Omu Farisah😘

_Ya ALLAH ka jiƙan A'ishah🤲🏼😢_


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*

*MTN* . *Airtel*
1GB = N300. 1GB = N300
2GB = N600. 2GB = N600
3GB = N900. 3GB = N900
4GB = N1200. 4GB = N1200
5GB = N1500. 5GB = N1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = N500.
2.9GB = N1200. 1.5GB = N1100
4.1GB = N1600. 2.9GB = N1400
5.8GB = N2100. 3GB = N1650
7.7GB = N2700. 4GB = N2100

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
For more information call or whatsapp me
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

🪀08066268951


*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 3/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_




*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*77&78*


Suna isa galadanci, bayan motocin sunyi parking a ƙofar gate, aka budewa Shattima ƙofa ya fito anutse.
Kallon Mamy ya yi cikin kamewarsa anutse yace mata.
"Bari na fito yanzu ko zaki shiga ne?"
Hannunsa ta riƙe tana murmushi tace.
"Eh na gaishe da Inno da Baffa mana."
Anutse cikin taushin murya yace.
"Ok muje."
Ya kama hannunta ta fito, tana zare hannunta, suka nufi cikin gidan.
Karima uwar rawar kai da neman guri ta fara ƙoƙarin buɗe mota Dad yace.
"Ke! Ina zakije? Suma ba zama zasuyi ba, koma zauna."
Baki ta mele tana faɗin.
"Nazata nan ɗin mukazo ko?"
"A'a tafiya ce gaban mu, kawai kisa ido kiyi kallo wajena na babban taro."
Baki ta washe tana faɗin.
Masha ALLAH, toh shi kenan zaka sameni me biyayya insha ALLAHU."
"Uhmm!"
Kaɗai yace saboda haka kawai yaji ya tsaneta, kuma tunda Baffa liman yace a ɓoye mata komai har aje yasan ba banza ba.

Khairy wacce ta gama shirinta Tsaf tinda tayi sallar asuba, ta haɗe cikin atamfa, blue mai ratsin baƙi da fari, mai shegen tsaɗa ɗinkin doguwar riga bai kamata sosai ba irin mai tsokewa daga ƙugu ƙasa ya baje.
Cikin kayanta da suke nan ta zaɓa ta saka.
Ta murza ɗauri ta yafa mayafi daidai misali fari ta saka takalmin shima fari handbag fara, tayi wani irin bala'in kyau, baƙar fatarta da ta gaji da hutu da jin daɗi, sai sheƙi takeyi, lipstick ta shafa a laɓɓanta, masha ALLAH.
Nadiya ma tayi wankan Khairy tace ta zaɓi kayan da zata saka cikin manya.
Ta saka abaya red me kyau.
Tea suke sha mai kauri wanda Inno ta dafashi tin ƙarfe 4 na asubah.

Inno ta shigo ɗakin tana faɗin.
"Ummulkhairi! Ku fito har Dadynki sun shigo mun gaisa suna ɓangaren Malam."
Khairy ta kai cup bakinta, tana kallon Inno batayi magana ba, sai da ta ƙara sa shanye tea ɗin tace.
"Alhamdulillah! Tom Inno gamunan zuwa, Nadiya ƙara sa muje."
Inno ta fice tana murmushi.

Liman na zaune cikin shiri Shattima da Mamy suka shigo falon nasa bakinsu ɗauke da sallama.
Ya amsa suka zube suna gaishesa.
Ya amsa cikin sakin fuska yana saka musu albarka.
Shattima yace.
"Baffa sai muje kar lokacin ya fara ja, tunda yau zamu dawo."
Baffa Liman ya miƙe yana faɗin.
"Toh ai Ni na shirya, amman dole sai mun kwana akwai tafiya sosai.
Gobe sai mu dawo. Ina mutuniyar ko baku ganta ba?"
Shattima ya miƙe yana faɗin.
"A'a bamu ganta ba."
Suna fitowa da ɓangaren liman, su Khairy na fitowa tana riƙe da hannun Inno, tana mata magana ita ko sai dariya take.

Idanunsu bai zame ko ina ba sai cikin na juna ita da Shattima.
Wani iri sukaji atare, dukansu kallon yadda kowanensu yayi wani irin bala'in kyau suke cike da wani irin shauƙin da basu taɓa jiba tsakaninsu ba.
Cikin kamewarsa ya waske yana kallon wani gefe kamar yadda itama ta fara maida kallonta kan Mamy, ta saki hannun Inno ta isa wajan Mamy ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, tace.
"Good morning sweet Mamy ?"
Mamy ta shafi gefen fuskarta tace.
"Morning sweet daughter, kin tashi lafiya? Me kika ci yanzun anan?"
Dariya tayi tana sake lafewa jikin Mamyn tace.
"Tea nasha me daɗi Mamy."
"Ok good Amman baki gaishe da sweet Dady ba, har Nadiya ta rigaki samun ladan."
Khairy ta janye tana dariya tace.
"Ai farin cikin ganin ki ne Mamynah."
Ta faɗa tana waigowa ta hango Shattima rumfar ajiye motar liman shida Yahuza direban liman wanda yake goge motar.
"Toh Mamy bari na gaishesa ina liman da Nadiya?"
Mamy tayi murmushi tace.
"Suna magana da Inno ne, Nadiya ta fita ta gaishe da iyayanta tazo, a motar liman zaku tafi, je ki gaishe da Dadynki."
Khairy ba yadda ta iya ta amsawa Mamy da.

"Toh Mamy."

Ta faɗa tana nufar wajansa, yayin da Mamy ta fita waje bakin gate dan shiga mota.
Anutse yakema Yahuza direba magana, wanda yake aikin goge motar, ta iso wajan.

"Assalamu alaikum. Dady ina kwana?"

Ta faɗa tana tsayawa nesa da shi kaɗan.

Waigowa yay ya mata kallo ɗaya yana kauda kansa, anutse cikin taushin murya ya amsa da.

"Wa'alaiki Salam, lafiya lau daughter kin tashi lfy?"

Murmushi tayi tana faɗin.

"Alhamdulillah Dady."
Cikin wata irin taushi murya mai narka zuciya ya furta.

"MASHA ALLAH, nan motar zaku shiga keda Nadiya, da Baffa Ok?"

Wani yarrrr taji har wani sanyi na shiga ɓargon ƙasusuwanta.
Anutse cikin dakiya tace.

"Tom Dady."

Dab da ita ya matso yana faɗin.
"Kije ki sako hijab akwai sanyi cikin motar idan an fara tafiya."
Ya faɗa yana sanya hannunsa ya ɗago haɓarta, cikin wata rikitacciyar murya yace.
"Jiya kinyi bacci da wuri ne?"
Ƙafafuwanta suka soma rawa, ta kalleshi idanunta har sun kawo ruwa ta ɗaga masa kai.
Hannunta yaja suna tafiya ya shige corridor, ɗin bayan rumfar motocin.
Dab da shi ya tsayar da ita, ba tare da ya riƙe ko hannunta ba, yana kallonta, fuskarsa ba fara'a.
Yaƙi mata magana, sai horata yake da manyan lumsassun kaifafan idanunsa.
Ga fitinannan ƙamshinsa, ya gama cika mata ƙofofin hancinta.

Jikinta ya soma rawa, hakan ta dake tace.
"Dady muje kar ajiramu."
Ta faɗa tana maida ƙwallar da take son zubowa, ta juya da niyar tafiya.
Tattausan hannunsa taji cikin tafin hannunta ya janyota dab da shi, ba tare da jikinsu ya haɗu ba.
Fuskarta ya riko da dukkan hannayensa.
"Nace me aka miki kukan me zakiyi min yanzu anan ɗin? Nace jiya bakiga ina kiran ki ba?"
Sosai ta sakawa kanta jarumta, kar ya kuma kiranta marar wayo.
Anutse tace.
"Kayi haƙuri Dady nayi bacci ne ɗazu na gani."
Yatsarsa taji akan lips ɗinta yana goge lipstick ɗin da ta shafa.
Muryasa mai rikitata dab da fuskarta taji yana faɗin.
"Karki kuma sawa."

Idanunta ta janye daga kallonsa, sabida ji take kamar zata suma, cikin dakiya tace.

"Tom Dady kayi haƙuri muje."

"Me kika ci yanzun?"

Tambayar da ya jefo mata anutse.
Kasa kallonsa tayi sabida ko ina na jikinta vibration yake.
"Dady nasha tea me kauri, kayi haƙuri zanci wani abun ahanya.
"
Bai ce mata komai cike da nutsuwarsa ya kamo hannunta suka fito.
Suna fitowa ta zame hannunta ta jingina da motar da zasu tafi, tana maida numfashi, zuciyarta tana mahaukacin bugawa, tana ƙoƙarin ɓiye halin da take ciki.
yana tafiya cike da nutsuwarsa taji Amin daddaɗan muryasa mai cike da Dattaku da nutsuwa yace.
"Shiga ɗauko hijab Babe."
Ya faɗa kansa tsaye yana tafiya.

Bayansa ta bi da kallo, tana janyo numfashi, taja ƙafafunta, tabi bayansa, shi ya nufi gate ita ta nufi ɓangaren Inno.
Hijab ta ɗauko mai kauri,tare suka fito da liman suka shiga mota ita da Nadiya.
Liman zaune kusan Yahuza direba Khairy da Nadiya suna baya.
Motar ta nufi gate.
Khairy ta lafe jikin kujera tana lumshe idanunta.
Shattima na shiga motar ya kalli Mamy tana kallon gefe.
Kanta ya kamo yana juyo da fuskarta gefensa.
Baki ta zumɓur masa kamar wata ƴar baby.
Yay ɗariya marar sauti yana faɗin.
"Zan cinye bakin fa."
"Aff adaidai nakane Mi Amor."
Hannunta ya damƙe cikin nasa, yana murzawa, yace.
"Tafiyar mu fa sai mun kwana dole."
Kanta ta kwantar kafaɗarsa lokacin da motarsu take barin ƙofar gidan Liman.
Motar su Dad na tsakiya ta liman ce abaya, haka suka jera abin gwanin ban sha'awa.

Misalin ƙarfe goma na safe kasancewar weekend ne, Azizah ta shirya ta tafi gidansu Suhailat.
Suna zaune falo ta shigo.
Umma tace.
"Tabb Azizah yau agidanmu?"
Azizah ya zauna tana murmushi tace.
"Kai umma ai kinsan ina zauwa, idan na samu lokaci, ina kwana umma?"
Suhailat tace.
"Uhm su Auntie Azizah yau agidanmu."
Azizah tace.
"Toh ya ranki ya miki?"
Tace.
"Fais ah toh."
Umma tayi dariya.
Suhailat ta miƙe tana faɗin.
"Bara na shirya na wuce kar rana tayi sosai."
Azizah tace.
"Ina zuwa?"
Suhailat tace.
"Gidan Aunty Barira zanje batada lafiya."
Azizah tace.
"Ayyah! Allah bata lfy ki shirya sai na biya na ajiyeki."
Suhailat bata komai ba ta wuce, dan tasan daman zuwan natane.

Bata jimaba ta shirya ta fito suka wuce.
Anutse take driving tace.
"Dan Allah Suhailat zaj tambayeki idan kin sani ki faɗa min kiyi dan zumunci? Ki tuna Ni ƴar uwaki ta jini, kar ki zaɓi bare ki barni."
Suhailat tace.
"Toh Aunt Azizah me kikeson ki tambayeni ne?"
Suhailat ta tambayata.
"Don Allah dan Annabi kinsan mijin da Khairy ta aure kwanan nan ne? Waye shi ina yake dan ALLAH?"
Suhailat aranta tace.
"Tabb ai bazakiji mutuwar sarki a bakina ba shi toh."
Azahiri sai Suhailat tace.
"Tabb Aunt Azizah kin daddaƙo aiki, ni kam ban saniba, ita kanta bata san mijinta ba har yanzun."
Azizah tace.
"Dan Allah duk ranan da kika ji waye ki sanar dani."
Suhailat dan kar suja maganan ta amsa da.
"Toh ba damuwa."
Sosai taji daɗi tana janta da fira har suka isa gidan Aunty Barirah.

Abba Aminu ya fito cikin shiri yana amsa waya, ya zauna saman lumtsumemiyar kujera yana amsa wayan.
Maryam ta ƙaraso cikin farin cikin ganin mahaifin nata bai fita.
Ammi ta kalla tana zaunawa kusanta, tana ƙasa da murya, tace.
"Ammi! Toh don Allah kima Abba magana zanje gidan Dady Shattima. Kinga har auntie Khairy ta warware ban komaba."
Ammi tace.
"Ai ke kam kin cika ƙwawa, ai ga ke ga shi, bari ya gama wayan."
Maryam ta shagwaɓe fuska tana rau-rau da idanunta.

Abba Aminu ya kammala wayan yana kallon Ammi yace.
"Me take so ne take wani nuƙu-nuƙu?"
Ammi tayi murmushi tace.
"Hamm gidan Dadynta zataje wai ta kwan biyu bataje ba. Har Khairy taji sauƙi."
Murmushi yay yana miƙewa yace.
"Shine take wani nuƙu²? Toh basa garin sun tafi Katsina, sai ki jira har su dawo."
Maryam tana matso ƙwalla tace.
"Allah maidosu lafiya Amin."
Abba Aminu ya mike yana faɗin.
"Amin dai Abidah zan fita, Maryam kenan ke bakije islamiyya ba koh?"
"Abba kuyi haƙuri kaina yake ciwo zan tafi da yamma."
"Hamm Amin amman kika so tafiya gidan Shattima, ki kula bana son rashin karatu da!"
"Zan kiyaye Abba".

Ammi ta rakashi har ƙofar falo ya tafi compound inda Guard ɗinsa ke jiransa a mota su fita.

Maryam ɗaki ta koma ta lafe kam bed tana aikin kallon pictures ɗin Shattima, tanaji kamar ta cinyasa dan so...

A Kano su Shattima sukayi breakfast kafin su ɗauki hanya Katsina.
Hajiya Karima ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba ganin inda zasuje amman da yake ta sakawa ranta aikin YANKAN WUƘA baya faɗuwa aƙasa, sai taji daɗi.

Katsina.
Abbu tun safe ya fita yayin da Zainabu da inna ADAMA suke rumfa zaune, su Jamilah suna islamiyya.
Hira suke yayin da inna ADAMA idan ta magana sai ita ta mayar mata da hannu, suna dariya idan abun dariya ne.
Inna Adama tace.
"Bari dai na ɗauka mana dafa dukan shinkafa, kafin yaran su dawo shaɗaya ta wuce sun kusa wannan uban jin yunwan zai zo ya fara mita."
Zainabu ta miƙe tana mata bebenci tace.
"Zauna Aunty Ni zan dafamana jalof mai daɗi, bari naje bakin titi n'a amso Mana kifi sukumbiya."
Ta faɗa tana murmushi ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab da kuɗi.
Inna ADAMA tace.
"Kai Zainabu bakya gajiya da hidima Allah yayi albarka Ameen."
Zainabu tayi murmushi ta fice.

Tana fitowa daga soron ƙofar taga motoci maka maka guda uku na parking sun jeru ƙofar gidansu.
Bata saka komai arantaba ta fara tafiya anutse, tana kallon gabanta.
Kamar a mafarki taji muryan Dad Mustapha yana ƙwala mata kira.
"Zainabu Nah! Ashe zan sake ganinki?"
Kanta taji yayi wani bala'in sarawa duhu na ƙoƙarin rufe idanunta, cikin juriya, ta juyo sukayi idanu huɗu da Mustapha aguje ya nufota, bayansa Karima ita kuma take binsa da gudu tana faɗin.
"Kawa Allah karka taɓata ta harmata gareka..."
Zainabu da yatsa take nuna Dad Mustapha da Karima kafin tayi luuuu da baya idanunta na rufewa.... ```iya comments iya yawan typing.🫣☺️😊```
*Waɗanda kukayi yimin comments da sharhi, ƴan Yi Wa Kai fan's, da sauran groups da ake sharing jiya, wallahi na gode Ubangiji ya biyaku da alkhairinsa, yabar zumunci i love You tafka-tafka.😘😘😘*


Real Ladingo Omu Farisah


*YI WA KAI!*

_December 5/12/2022_

*Free Novel*

_#MatarɗanAlhaji🫣_

Billahi kyauta nake gaisheku mabiya labarin nan, ina godiya da fatan alkhairin da kuke min.🙏🏽🥰


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*79&80*


Duk yadda Mustapha yaso ya iso wajan Zainabu ya tarota, kar ta faɗi abun yaci tura, har ta kai ƙasa sumammiya.
Hajiya Karima ta YANKAN WUƘA ikon Allah.😂Gudu take tana son riƙe Mustapha kar ya isa wajan Zainabu, tana faɗin.
"Mustapha zaka aikata zina, taɓa matar da ba muharamarka ba..."
Cak bakinta ya tsaya da maganan da yake, sakamakon zama da Mustapha yay gaban Zainabu ya sanya hannunsa ya ɗagota zuwa jikinsa, yana rungumeta tare da girgizata yana kiran sunanta.
"Zainab! Don Allah ki tashi ki faɗa min yaushe na sakeki? Ya akayi kika iya rayuwa Bama tare muda mukayi alƙawalin kasancewar rayuwa tare. Usman Nadiya! Kuzo Dan Allah kuce ta tashi, ku kawomin ruwa na zuba mata"
Usman da Nadiya aguje sukayo wajan mahaifinsu.
Karima wani irin ihu ta kwarara tana gudu, tayi wani irin tuntuɓe ji kake timm tayi wata irin faduwa wanwar ƙasa, rubda ciki, sai da kanta ya bugu da ƙasa, fuskarta tayi fata-fata da ƙasa, har tana shiga idanunta, ta miƙe cikin ɗingisawa tana nufarsu.
Khairy ta iso wajan Mamy tana damƙe hannunta tana kallon ikon ALLAH, wanda suke matsayin mahaifinta.

Shattima ya furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa, yana faɗin.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."
Yana kallon jama'a har sun fara taruwa, wasu nayima Karima dariya yadda fuskarta tayi butu-butu da ƙasa ta riƙe ƙugu tana ɗingisawa.
Ya kalli Baffa liman anutse, cikin kamewarsa ya furta.
"Baffa! Kaje ka masa magana ya ɗauke suka shiga daga ciki a zuba mata ruwa, jama'a har sun fara taruwa ba daɗi, ga wannan matar tasa zata tara masa jama'a"

Liman yace.
"Hakan ne zanyi abun ne baki ɗaya ya gama ɗauremim kai, Allah ya kyauta."

Ya faɗa yana nufar wajansu Mustapha.
Shattima ya kalli Mamy anutse, yace.
"Ku shiga cikin gidan kawai."
Mamy tace.
"Tom muce mu suwaye?"
Shattima ya kalleta anutse ya furta.
"Bilkisu! Ku shiga kawai nace, Please kubar wajan nan."
Ya faɗa yana kallon Khairy tana rau-rau da idanunta, wanda suke kallon iyayanta na asali ganin wacce take jikin Mustapha, ita ce matsayin mahaifiyata, fara mace kyakkyawa, batada wani shekaru ma alamu sun nuna da wurine aka mata auren har ta haifetan.
Shattima yace.
"Baby kuje ciki bana son naji wata rigima ko kuka sam Ok?"
'
Khairy ta kalleshi tana jinjina kanta, cikin sanyin murya tace.
"Dady su shiga cike anata kallonsu awaje ba daɗi."
Ta faɗa tana langwaɓar da kanta, tana kallonsa kamar zata fashe da kuka, tana jiran taji me zai ce.

Idanunsa ya janye daga kanta, yana jinjina kansa, yana kallon Mamy yace.
"Sweetheart kuje ciki."

Mamy ganin yanayin Shattima ya saka ta amsa da.
"Toh, Baby muje."
Khairy ta bita tana jaye da hannunta, idanunta akan Mustapha da Zainabu sai taji hawaye yana gangarawa kan baƙar kyakkyawar fuskarta.

Karima tana zuwa wajan tace.
"Mustapha kafa yi haramun abinda kayi ka matsa daga kusanta.
Wani irin kallo yamata wanda saida taji fitsari na neman zubo mata.
Ga wata azaba da takeji addukan illahirin jikinta, tanajin wasu abubuwa na mata yawo kamar zata zura da gudu, ga idanunta na mata bala'in zogi abinda takeji baida kwatance, dauriya kawai take.

Anutse Liman yace.
Mustapha! Tashi ɗauke ta shiga koda zauren gidan ne azuba mata ruwa don ALLAH."
Mustapha ya miƙe ba musu ya nufi soron ƙofar, wanda lokacin su Mamy suka shige.
Haka yayi daidai da isowar Abbu wanda ya hango Zainabu rungume ajikin Mustapha.
Da gudu ya iso ya tare ƙofar shiga yayi banga-banga, yana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fi musibatihi wakhlifni khairn minha. Me zan gani haka? Kai Mustapha! Ashe bakada kunya bakada mutunci?, sauketa anan, sauketa

Please Login or Register in order to submit comment