Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qasashen duniya da suke zuwa sarin kaya zata rantse bai fi hotel uku ba da taga zasu Goga da wannan tamfatsetsan ginin larabawan, wanda larabawan ma sai wanda suka amsa sunansu larabawa. Mamy ta Kira laraba ta bata umarnin ta kunna burner ta zuba turaren wuta falon baqi , taje ta tarbosu a compound ta kaisu can,Saliha kambacin mai aikinsu d'aya da akayi aure satin da ya wuce ita kuma aka bata umarni takai abin motsa baki da ruwa tace musu tana zuwa. Motarsu na tsayawa wasu narka narkan motoci gudu uku suka shigo gidan kai tsaye suka nufi parking lot. Hajiya Karima tabi motocin da kallo tana had'iye miyau, wani qaton soja d'auke da bindiga taga ya bud'e baqar jibgegiyar motar ya koma gefe. Rufaffan takalminsa wanda ya zauna aqafafunsa ya Fara zuro waje kusan second 10 kafin taga ya fito baki d'ayansa kyakkyawar fuskarshi d'auke da qawataccan murmushi,taga ya beqa hannunsa motar sai taga hannun mace sanye da awarwaron da ko kaffara bazatayi ba zinare ne. Tana gama fitowa, Baki da'ayanta ta turo baki tana magana tana riqe da hannunsa. Zame hannunsa yay yana amshe wayanta ya tura aljihunsa yana mata mgna, ya fara tafiya anutse, PA d'insa na jido masa wayoyinsa. ta ko ina gaishesa ma'aikatan gidan suke suna masa barka da zuwa. Da d'an gudunta ta biyosa kamar zatayi kuka, tsabar shagwab'a, ta cinmasa. Sai lokacin Hajiya Karima ta qarema fuskar Khairy kallo,atake gabanta yayi wani rin mahaukacin fad'uwa, taji k'irjinta na wani irin bala'in dukan uku-uku ta zazzaro idanunta tana b'alle murfin motar ta fito tana sake k'urama Khairy idanunta baki d'aya....


*YI WA KAI*

Free Novel

_November 4/11/2022_



*51&52*

Hajiya Karima hankalinta yayi mummunan tashi ba kad'an ba, ganin tsagwaron kamar da Khairy take da Usman, kuma Mustapah, shin me hakan yake nufi? Wata irin wawar ajiyar zuciya ta sauke sabida tuna da hannunta ta shaqe jaririyar Zainabu, ta sakata akwali takai ruwa ta jefa, tanada yaqinin da dorunar ruwa ta cinye gawar namanta. Hajiya Shahida kanta ta girgiza da ganin kamar Khairy da Mustapah kamar an tsaga kara,batada banbanci Amman Sam bata kawo komai akanta ba,ta fito tana riqe Karima tace. “Ke! Nutsu kar a ankare damu mana kinsan irin gidajan nan,cike yake da CCTV cameras, kamace kawai Allah ya saka musu,Nima na girgiza da ganin kamar,Amman aciki karki kuskura ki nuna irin yadda kika nuna anan Sam baiyi ba sai azargi wani ba fa!” Hajiya Karima ta sauke ajiyar zuciya,tama Khairy k'ur da idanu tana tafiya cike da nutsuwa, ta iso wajan minister ta kamo hannunsa tana masa magana ashagwab'e, shi kuma yana murmushi tare da girgiza kansa. Hajiya Shahida ta sake girgiza Karima tana fad'in. “Karima idan bazaki nutsuba kisan ta ko ina Allah ya saka Kama a fuskokin bayinsa zaki jazamana a tuhumemu idan bazamu shigaba mu koma mota mu wuce kawai.” Karima ta saita nutsuwarta ta kasa daina kallon Khairy, har suka mata nisa, tace. “Ok muje ina mamakin kamane da Usman d'ina, ashe Allah yana saka Kama har haka a fuskokin da bai saniba, yanzu na gano dalilin da ya saka minister ya taimakawa Usman Kama take da 'yarsa.” Daidai lokacin Laraba ta iso ta gaishesu cikin girmamawa tace. “Hajiya tace ashar daku ciki.” “Ok” Kawai Shahida ta amsa sabida Karima tension d'in take neman tashi, sabida tana wani zargi akan Khairy. Hannunta ta Kama tana magana qasa² sukabi bayan Laraba. B'angaran Shattima kuwa tin lokacin da ya sauko idnunsa suka sauka akan baquwar motar da take cikin parking lot, tabi layin jeran motocinsa, haka kawai yaji motar hankalinsa bai kwanta da ita ba, bai gama sarewaba sai kallon da yaga hajiya Karima tanama Khairy, yana ankare da su ta tsinin idanu sabida yadda yake jan tafiyar anutse ahankali cikin iliminsa da Allah ya basa, wayansa ya kira Okasha sojan k'ofa, bugu d'aya ya d'aga batare da yakai wayan kunnensa yake mgana sbd akwai Bluetooth a kunnensa. “Okasha! Da izinin wa baqin nan suka shigo gidan nan?” Okasha yace. “Yallab'ai na hanasu jin ba sanin Madam, toh sun roqeni akan na kirata idan ta amince sai su shiga, toh ta amince Amman lokaci kad'an ta basu sabida zuwanka.” Shattima bai ce komai ba ya katse kiran yana Jan hannun Khairy. Lafiyayyan falon sauqar baqin mai d'auke da manyan kujeru da wani tamfatsetsan carpet mai laushin Laraba ta kaisu suka zauna suna shaqar k'amshin daddad'an turaren da yake tashi,ga sanyin A.c. Saliha ta zuba musu ruwa da lemo ta ajiye kan table kowa kusansa ta ajiye tray'n apple da Watermelon atsakiyarsu ta gaishesu ta miqe ta fice. Hajiya Karima ta d'auki cup d'in ruwan ta shanye, ta k'ara tsiyaya wani ta shanye, ta d'auki lemonta shaye, tana sauke ajiyar zuciya. Hajiya Shahida ta tsira mata idanu cike da tuhuma tace. “Karimatu! Anya kinada gaskiya kuwa? Me kikeyi hakane? Kodai akwai b'oyayyan sirrin da ban saniba da kike b'oyemin?” Karima da qarfin tsiya ta tattaro nutsuwarta ta dawo hayyacinta, ta sauke qatuwar ajiyar zuciya tace. “Wlh ba komi kawai ina mamakine tsabar kamar da take da yarana da miji, Amman ba komai bayan shi na bar mamaki kam sha'anin Allah. ” Shahida tace, “Yawwa ko ke fa! Amman haka kawai ki saka ayi zarginmu.” Murmushin qarfin hali tayi tana d'aukan apple tana kaiwa bakinta.

Mamy upstairs ta haye ta koma ta d'auko babban mayafi mai bala'in kyau ta sauko, tana zaune 5 minutes taji ana danna doorbell d'in falo ta miqe dan ta sallami su Laraba sun tafi part d'insu. Cike da shaukin son ganin Shattima ta nufi hanyar da zata sadata da qofar falon. Tana bud'e qofar ta zuba musu idanu cike da farin cikin ganinsu. Hannayensa ya ware mata yana na sakar mata tattausan murmushi, kanta ta kauda daga kallonsa sabida yadda shauqin sonsa yake fizgarta idan ta afaka jikinsa zata Iya masa komai ba, hakan kuma ba tarbiyar da suka ba Khairy bace, iya hugging kawai idan yazo daga tafiya sukewa juna shima dukansu su biyun suke rungumesa shiyasa hug d'insa bai zama wuya wajan Khairy. Khairy tayi tsalle ta d'are jikin Mamyn tana dariya tare da fad'in. “Mamy I miss you, wayyo Mamy kinyi kyau wlh sosai.”. Ta fad'a tana qanqameta har tana shirin kayar da ita, sai da Shattima cikin sauri ya taro Mamyn ya riqota sosai yana fad'in. “Baby wai bakya ganin kinfi Uwa taki kauri Masha Allah ai zaki jimata ciwo irin wannan chakumar haka.” Khairy ta zumb'uro baki tace. “Mamy! KingaDady koh? Bayaso naji d'umin uwata.” Mamy ta janye daga jikin Shattima tana 'yar dariya tace. “Yanzu dai sannunku da zuwa ya hanya? Baby kinyi kyau abinki, lallai Auntie Aisha ta iya kiyo.” Kallon da Shattima yamata yasa ta kamo hannun Khairy tana tafiya da ita, tace. “Baby wanka koh abinci? Inada baqi.” Khairy tace. “Sweet Mamy wanka dai, amman Dady wlh yunwa yakeji.” Mamy ta Ce. “Oya toh je kiyi an had'a miki ruwa.” Tsalle Khairy tayi ta janye hannunta ta nufi tsakiyar falon, tana ware hancinta dan shaqar daddad'an turaren wutar da baibaye ko ina. Gyaran murya Shattima yama Mamy. Ta juyo tana marerece fuska ta masa nuni da hannu Khairy. Harara ya zabga mata yana yafitota da hannu. Ganin Khairy ta nufi upstairs. Hannunsa ya hard'e ak'irjinsa yana kallon Mamyn. Anutse ta iso wajansa ta masa wata irin runguma,tana qanqameshi gam. Ajiyar zuciya suka atare, yana sanya dukkan hannayensa yana matseta jikinsa, ya rankwafo yana cusa fuskarshi mai kyawan saja lungun wuyanta,yana juyawa tare da sumbatar fatar wuyan Nata yana lasa anutse still yana shafa bayanta ahankali. Mamy ta sakar masa jikinta tana sake ruqumqumeshi, ahankali ta furta. “Mi Amor! I miss you barka da zuwa fatan kazo lafiya?” D'ago kansa ya yi yana mata wani shu'umin fitinannan kallonsa, wanda ya sakar mata da dukkan jijiyoyin da suke gudanar da gudun ruwanda jininta, ta murmusa tana aika masa kiss na baki irin na muahhhh ba tare da kai fuskar mutum ba. K'ugunta ya riqo da hannunsa d'aya yana murzawa, yana lumshe idanunsa ya d'ago fuskarta da hannunsa d'ayan, anutse ya sake rankwafo da kansa tsawuonsu yazo d'aya, ya had'e face d'insu idanunsa arufe yana had'e fuskarsu yana hura mata iskar bakinsa kafin ya d'ora bakinsa akan anata, cikin wata irin dashashiyar murya mai dad'in sauraro ya furta. “Sweetheart! Oya kiss me ina bala'in missing d'in sweet lips naki.” Wata lafiyayyar Sumba ta basa tsakitar bakinsa tare da kamo lallausan harshensa, mai bala'in k'amshi sweet na Pineapple, ta fara tsotsa ahankali tana shafa sumar kansa. Jin ya kamo tattausan labb'anta zai fara tai saurin zare bakinta tana murmushi ta masa rad'a akunnensa. “Mi Amor kayi haquri zuwa anjima Zan sameka b'angaranka, nayi baqi ban San su waye ba na dai Ce akaisu falon baqi, kar suga na wulaqantasu, muje na had'ama ruwan wanka kafin ka kimtsa Zan sallame su OK my Shattima nah?” Ta k'arashe mgnar tana Kama hannunsa tare da sakar masa lafiyayyan murmushi. Gira d'aya ya d'age mata, muryasa can qasa yace. “amman kinsan zanzo meye na tarbar wasu baqin?” Rungume shi tayi tana buga bayansa tace. “Hi haquri Mijina na tuba kaji?” “Naaji ai kinsan bakya laifi, yafa mayafinki je ki dawo zan had'a da kaina 20 minutes kawai Sweetheart. ” “Kai amman na gode My minister muahhh.” Harara so ya mata, yana tafiyarsa mai nagarta. Bata tsaya komai ba yana hayewa upstairs ta yafa mayafinta ta fice.

Hajiya Karima cikin k'osawa tace. “Idan matarnan bazata fito ba ko mutafi sabida Allah an wani shanyamu...” K'aran bud'e qofa sukaji tare da sallama cikin nagartacciyar muryata mai taushi. Shahida da Karima suka amsa suna kallon tsantsar kyawun Mamy da kamewarta, gata da jikin yara, dan sun zaci wata babbar mace zasu gani irin uwar nan ashe ba haka abun yake ba, koda yake koda sukaga minister yau azahiri ba Tv ba, sun Sha mamaki ashe yafi kyau da yarinta a waje gashi D'an gayu, dole matarsa zata zama 'yar gayu.

Lace d'inta kawai suka kalla suka raina Kansu sunajin sun k'ure adaka. Cikin sakin fuska ta iso tana fad'in. “Sannunku da zuwa dan Allah kuyi haquri na barku Ogan ne ya shigo gari yanzu.” Ta fad'a tana zama. Tare suka had'a baki wajan cewa. “Lah! Wlh ba komai wlh haka ma mungode.” Mamy ta murmusa tace. “Masha Allah Ngd da uzurinku.” Shahida tace. “Hajiya Bilkisu mu baqine da mukayi tattaki tinda daga Gumel, mune iyayan Usman wanda minister ya samoma aiki a Kaduna mun gode sosai Allah qara girma, amiqa mana godiya wajan yallab'ai.” Bilkisu kallon mamaki take musu, dan ita Sam batasan wani Usman ba, da minister ya taimakawa. Gabanta ya fad'i tuna Kodak yaron da Shattima ya bata labari sun had'u a airport d'in Abuja suna Kama da Khairy? Idan hakane cikin dole d'ayace uwar yaron wato kishiyar uwar Khairyn kenan. Wani yawu mai d'aci ta had'iye muqutt, tana sake saita nutsuwarta. Tayi murmushi tace. “Ai yiwa Kaine ba komai nima ngd sosai da yin tattaki tun daga Gumel, Allah ya saka da alkahiry.” Su Karima suka amsa da. “Amin ya Allah.” Waya ta d'aga ta Kira Laraba ta had'o music lafiyayyan girkin da Mamyn tayi ta kawo musu Mamyn tace. “Toh bismillah kuci abunci bara naje Zan dawo kafin ku gama.” Karima tace. “Wlh mun qoshi Hajiya mun gode zamu juya sabida akwai Inda zamu biya gidan kawuna, daga can sai mu d'auki hanya.” Mamy ta canza fuska tace. “A'a gaskiya bazanji dad'iba idan bakuci abincin nan ba kawai kuci shine zanyi farin ciki, please. ” Ta fad'a tana miqewa. Shahida tace. “Zamuci insha Allahu mun gode da karramawa.” Mamy tayi murmushi tace. “Ngd ina zuwa.” Ta fad'a tana ficewa.

Tafiya take ji take qafafunta basa saud'aukarta amman kuma ta wani fannin k'ulla alaqa dasu zai saka asiri yayi saurin tonowa wanda hakan takeso komai ya qare ko Khairy ta tare gidan Shattima duk da tasan za'asha gwarma.

Khairy tana hayewa sama ta shige d'akinta wanda Saliha ta gyara tsaf ko ina sai qamshi yake, kayanta ta core ta shige toilet tayi wanka, ta fito ta Sanya jallabi ta shimfid'a darduma tayi sallar azuhur, tajima tanama Abdoul Addu'a harda kuka, kafin ta miqe ta cire rigar ta shafe jikinta da lotions masu taushi da qamshi, ta tupqe gashinta gida biyu ta sanya ribbons, ta saka Riga da skirt na atamfa, shud'iya d'inkin yaso mataeta kad'an, ganin irin yadda ya kamata ta d'ora after dress milk colour, tana baza qamshinta, ta zauna tana chat da Suhailat akan sun iso tazo gobe dan sufita Tasha iska idan ita d'ayace Dady bazai barta ba.

Shattima bayan ya fito daga wanka ya shirya kansa cikin qananun kayan da yake sakawa agida dan ya huta yayi sallar azuhur. Zaune yake a falonsa hankalinsa kwance yana amsa waya, anutse Bilkisun tayi knocking qofar ta bud'e ta shigo, ganinsa afalon zaune bata tsaya rufe qofar ba,ta iso wajansa ta zauna kusansa tana kwantowa jikinsa hawaye na qoqarin zubo mata. Ganin yanayinta yayi sallama da wanda suke wayan, ya katse yana ajiye wayan saman table ya riqota yace. “Sweetheart! Ya dai? Me ya faru?” Daidai lokacin Khairy ta shigo falon ta bud'e baki da niyar kiran Dadynta taga Mamy jikinsa tana fad'in. “Sweetheart! Kasan suwaye sukazo gidan nan? Ba kowa bane sai muguwar matar nan da ta jefar da Baby akwali muka tsinta mahaifiyar Usman yayan Kahiryn, wai sunzo min godiya, ka samama d'ansu aiki a kaduna, matar nan idan fa taga Khairy akwai matsala, zatayi bincike idan ta gano yarinyar da jefar Ce wlh sai tabi duk hanyar da zatabi taga ta kasheta... Baki Shattima ya rufewa Mamy yana fad'in. “Babu mahalukin da ya isa a duniya ya tab'a min Khairy ko shi wanene naganta tin lokacin da muka shigo tabi Khairy da kallo hankalinta atashe, babu abinda ta isa...” Bakinsa ne ya kafe waje d'aya sabida ihun da Khairh tayi tana shirin zubewa take fad'in. “No! No!! No!!! Dady ba gaskiya bane no banda uba sai kai,banda Uwa sai Mamy wallahi mafarki nakeyi Ku tasheni don Allah...” Ta fad'a idanunta na lumshe ta yanke jiki ta sulale zata fad'o saman qofar. Shattima da wani irin bala'in zafin nama ya Saki Mamy ya nufo wajanta da mugun gudu yana kamo tsintsiyar hannunta, ya janyota jiknsa yana jijjigata, tare da kiran sunanta wanda tuni kanta ya bugi handle d'in k'ofar goshinta ya fashe. Mamy kamar mutum butumi ta koma wajan ta dasqare bata ko iya motsa yatsarta tsabar tashin hankali...


*YI WA KAI*

Free Novel

_November 6/11/2022_



*53&54*

Cak Shattima ya cira Khairy sama yana nufo kan sofa cikin wani irin sauri yana fad'in.
“Bilkisu! Yi sauri kawo ruwa a zuba mata.”
Ya fad'a yana kwantar da ita saman sofa, yana murza hannunta tare da kiran sunanta, amman ko motsi batayi.
Mamy ta kalleshi tana zubar da hawaye tace.
“Idan mun zuba mata ruwa ta farfad'o ayanzu kanada hujojin da zamu bata ta gamsu damu kai tsaye? Kanada k'warin guiwar da zakayi iyamata byani anutse har ta gamsu?”
Shattima yace.
“Ok kinaso mubarta ahaka karta farfad'o? Bilkisu kusani aikin gama ya gama fa! Khairy taji komai babu wata hanya da zamu iya juya mata magana, har gobe har jibi Khairy d'iyarmu ce, karki sakawa kanki damuwa ko sarewa al'amarin kiga kamar zata gujemu, nasani har abadan Khairy bazata gujemu ba, zuba mata ruwan idan bata farfad'oba sai ki bata taimakon gaggawa agida idan kuma asibitin zamuje toh.”

Mamy kasa tashi tayi sabida mutuwar jiki da kasala ta beqawa Shattima hannun, ya kamata ta miqe ta nufi fridge tana hawaye.
Ruwan ta sheqa mata yadda zai ratsa jikinta tayi saurin farfad'owa.
Ai kuwa ruwan na ratsa jikinta wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana wani irin tari tare da fashewa da kuka, tana fizge-fizge tare da fad'in.
“Don Allah dan Annabi Dady and Mamy kuce bacci nake mafarki nayi ba gaskiya bane abinda naji dan Allah kunji?”
Mamy ta rungumeta qam tana fashewa da kuka, yayin da Shattima ya rufe mata baki da tafin hannunsa, d'aya d'ayan yana d'ora mata handkerchief a goshinta, sabida yana fitar da jini kad'an.
Kuka suke sosai Mamy da Khairy, Shattima, yayi gyaran murya yana fad'in.
“Bilkisu tashi kima baby dressing d'in goshinta yana fitar da jini.”
Khairy ta janye daga jikin Mamy tana musu wani irin kallo, ta miqe tana girgiza kanta cikin wani irin kuka, tace.
“Ba kune kuka haifeni ba koh? Dady ni ba 'yarku bace koh? Innalillahiwa'innailaihirraji'un! Allahumma ajirni fii musibatihi wakhlifni khairan minha...”
Ta k'arashe maganar tana yanke jiki zata sake fad'uwa, Shattima ya daka mata tsawa yana tarota ta fad'o jikinsa, ya riqe kafad'unta, yana girgizata yace.
“Ki dawo hayyacinki baby shin ke bakisan k'addara ba? Bawa fa baya wuce k'addarasa, shin ko kina ganin duk duniya akwai wanda ya isa ya rabamu dake matuqar ba kece kika qimu ba? Inaso kima zuciyarki haquri ki amshi k'addaraki duk da nasan akwai zafin da kikeji aqasan zuciyarki, idan kika ajiye hankalinki kika amshi k'addaraki zan tsaya na miki bayani yadda zaki fahimci komai nine nan zanyi miki jagora zuwa naiman wacce tayi sanadin zuwanki duniya, domin muji komai daga bakinta, ki nitsu bana son abinda kikeyi nan matuqar nine matsayin mahaifikin Bilkisu mahaifiyarki, kin kuma d'aukemu iyayan naki.”

Khairy ta k'urama Shattima idanu tana wani irin kuka, jikinta sai b'ari yake ta riqe damtsan hannunsa tana fad'in.
“Dady! Taya Zan iya nutsuwa? Ya zan iya rayuwa inaji ina gani dakai da Mamy amatsayin mariqana ba iyayena ba? Taya Zan iya rayuwa mai inganci bana tare daku wallahi tallahi Dady bazan iyaba, bazan iyaba Dady.
Mamy! Don Allah don Annabi Ku rufe zancan nan idan ba wanda ya Sani, sai Ku d'in shi ni me nama wacce tayi sanadin zuwana duniya ta yadani? Wlh bazan karb'i kowa akan dangina ba sai Ku.”
Ta k'arashe mgnar cikin matsanaicin kuka, tana sakin Shattima ta zauna k'asa zaman 'yan bori.
Shattima ya dafe kansa yay ya matso kusan Mamy wacce baki d'aya jikin ya mutu batada wani kuzarin yima Khairy magana saboda tasan a wannan gab'ar bazata iya shayo kan Khairy ba, sabida itama tayi rauni sosai, tana cikin tashin hankali.
Miqar da Mamy tsaye yay yana goge mata hawayen fuskarta, k'asa-k'asa yace.
“Baby fa inaga sai kinyi mata allura tayi bacci ta samu nutsuwa ayanzu Sam bazata fuskance mu ba, sabida ta shiga tension dayawa, je had'o allura ki mata, akwai agidan ko sai kin kiran daga hospital an kawo? Sannan ki fito da kayan da zaki mata dressing goshinta.”
Mamy ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in.
“Akwai.”
Hannunta yaja suka fice yana mata magana qasa-qasa.
Khairy ta bisu da kallo tana sake qara sautin kukan nata.
Shattima yaja ya tsaya yana sakin hannun Mamy yace.
“Je ki had'o kizo bari na lallab'ata.”
Kai ta gyad'a tana masa wani kallo ta fice, tare da bala'in tausayin kanta, sai yanzu takejin me ma yasa ta had'a auren nan, haka kawai takejin kishi mai zafi ayau d'in yadda Shattima yansan Khairy ayau ta fashe ba 'yarsa bace Amman sai wani irin tattalinta yake yi.

Tsugunnawa yay gabanta yana kamo hannayenta, ya had'e fuska yace.
“Baby! Kalleni.”
Kallonsa tayi tana wani irin kuka harda majina, dak'yar take janyo numfashinta wanda yake sama da qasa, yana k'ok'arin tsayawa. Ta d'ora hannunta saman na Shattima, tana fitar da numfashi dak'yar, tace.
“Dady! Wlh bazan Iya jure ganinku amatsayin mariqana ba iyayena ba, Dady ka tasheni abaccin da nakeyi kace min mafarki nake dan darajar Annabi Dady...”
Ta qarashe mgnar cikin kukan da dak'yar take yinsa tana janyo numfashi.

Idanunsa ya lumshe tare da furta.
“Ya Rabbi! Baby zaki halaka kanki koh?”

Ya fad'a yana miqewa tare da miqar da ita tsaye, ya zaunar da ita akan sofa, yaje fridge ya d'auko sansanyan ruwa, yazo ya zauna ya bud'e ya kafa mata abaki, yace“Oya Sha dayawa ki nutsu muyi magana.”
Dak'yar take shan ruwan sabida numfashinta da bai fita da kirki.
Sosai tasha ruwan, ta janye kanta tana shashek'ar kuka.

“Oh! My God! Baby! Shin ke ba musulma bace? Bakisan k'addara ba? Shin ya kike da 'ya'yan da iyayansu suka haifa ta hanyar zina wato karuwanci, suka jefasu a bola, wasu kuma suka riqe abinsu wasu ta hanyar fyade ake samun cikinsu ba'asan Inda za'a samo uban ba haka zasu girma su tashi da uwarsu wasu gidan marayu wasu gidan karuwai wasu ma basusan dangisu ba aduniya ta dalilin jefar dasu, wasu su zama karuwan idan namijine yazama d'an fashi ko wani riqaqqen d'an daba, wasu kuma zama manyan mutane duk ba yadda Allah baya yin ikonsa, wasu sunaji ana zaginsu ana aibatasu ana kiransu 'yayan zina 'ya'yan karuwai, 'ya'yan fyad'e, ana jifansu da mugayen kalamai ana k'yamatarsu cikin jama'a, acikinsu amman masu imani da *Tauhidi* me suke cewa?
“Muma bamu mukayi kanmu ba! Allah ne yaso ya ganmu ahaka, shiyasa ya haliccemu ta wannan hanyoyin, dan haka mun amshi k'addaramu da hannun bibbiyu.
Wad'anda kuma Allah baiso da rahama ba acikinsu zasuji zafin ta yadda sukazo duniya suyita sab'on Allah sua izgilanci a doron duniya.
Baby ke bazaki godema Allah ba da kika fito ta hanyar auren suunan sannan gidan dattaku 'yar asali bafulatanar usuli kika fito ta tsatso mai kyau uhmmm baby?”
Khairy idanu ta k'urama Shattima cikin shasheqar kuka tace.
“Dady! Ka tabbata ni ba 'yar zina bace?”
Mamy da take shigowa tace.
“Tabbas baby 'yar halak ce kum d'iyar Asali da dangi, kinason sanin kowa naki acikin siyasa mu kaiki gidan naku da yake a Gumel?”
Kahiry ta d'ago kanta tana kallon Mamy wacce ta zauna kusanta, tana lalubar damtsen hannunta, kafin ta tantance ta tsira mata allura da ta had'a wajan kalla uku.
Wani irin ihu ta Saki tana fashewa da kuka ta qamqame Mamyn tana kiran.
“Dady! Mamy tamin allura wayyo zafi Dady.”
Shattima yace.
“Yi shiru k'yaleta zan rama miki.”
Idanunta suka lumshe bakinta na musmus hawaye na kwaranya saman baqar kyakkyawar fuskarta nan take bacci ya d'auketa tana rungume da Mamy.
Zamewa tayi ta mata dressing goshinta, miqe tana kallon Shattima tace.
“Daukarta kaita bedroom d'orata saman bed zatafi jin dad'in bacci.”

Shattima ya kalli Mamy yace.
“Ban gane ba saman bed d'ina ba?”
Mamy batace komai ba, ta gyara mata kwanciyarta ta nufi k'ofa zata fita. Shattima ya kamota ya rungume cikin taushin murya, yana shafa fuskarta bakinsa dab da hancinta yace.
“Sweetheart me ya faru kuma?”

Mamy girgiza kanta tayi tace“Ba komai, sakeni zanje na duba baqin kar suga an sharesu yanzu zasu juya Gumel.”

Murmushin fatar baki yayi yana fad'in.
“Kinyi fushi sbd naqi kai 'yarki bedroom d'ina ta kwanta? Kinsan fa halin da ake ciki ayanzu, ko abaya bamu bata wannan tarbiyar hawa saman bed d'ina bare yanzu.”
Mamy ta rufe masa bakinsa da tafin hannunta, tana zubar da hawaye tace.
“Ni ba jahila ba Ce nasan haramci nasan halak ci, idan dai har ka d'auki Ummulkhairi d'iyarka har baya kuma ta halatacciya kawai kaita saman bed ka kwantar ai larura Ce can nake d'azu ma kai ka d'aukota da ta suma? Tsakaninka da Khairy wlh ba haramci dan ka tab'ata dan Allah d'auketa karta fad'o kasanta da mugun bacci.”
Shattima yace.
“Ni ban tab'a jin Khairy ba halak d'ina bace har gobe 'yata Ce ta cikina.”
“Good.”
Mamy fad'a tana sumbatar k'irjinsa ta janye tana fad'in.
“Zasu samu damar ganinka ko kawai naji dasu su wuce abinsu?”

Shattima wanda ya isa wajan Khairy ya sunkuyo yana ciccib'arta baki d'ayanta yay sama da ita ya nufi hanyar bedroom d'insa yace.
“No! Bana k'aunar mgna ta had'ani da azzalumar Matar nan sai ta zama dole toh yanzu lokacin titseta bai qaraso ba, bana buqatar magna da ita, suyi su wuce min daga gidana.”
Ya qarashe mgnar yana tura qofar bedroom d'in da k'afarsa ya shige.
Mamy taji wani irin bala'in kuka yazo mata, ganin yadda Khairy cikin bacci ta saqala hannayenta wuyan Shattiman fuskarta dab da tashi tana baccinta anutse.
Wani Abu taji ya tokare mata aqahon zuciya, yadda Shattima yake nuna mata madarar k'auna haka zai nunawa Khairy nan kusa zasu fara sharing d'insa ita da Khairyn kenan? Da Sauri ta fice kuka na kub'uce mata.

Saman tamftsetsan Royal bed d'insa wanda yaji lallausan zanin gadon d'an Saudiya,ya kwantar da ita tare da lullub'ata da tattausan bargonsa mai shegen taushi da qamshi, ya kunna mata Ac.
Ya juya zai fice yaji ta damqe hannunsa.
Da wani irin Sauri ya juyo yana tsaida idanunsa akanta, bai tantanceba yaji ta fizgosa ya fad'o samanta, yaji ta fashe da kuja tana kiransu.
“Dady! Mamy!”
Shattima da wani irin sauri ya zabura ya sauka daga samanta ya mirgina gefe yana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Ya fad'a yana rufe mata baki had'i da buga bayanta yana duba goshin nata.
Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya,tana bacci amman hannunta maqale

Please Login or Register in order to submit comment