Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaina mgnar tamun nauyi bare daughter.”
Ya k'arashe mgnar yana fincikota ta dawo gabansa, ya d'ago da hab'arta ransa amugun b'ace, idanunsa jajir, duk da kasancewarsa namiji marar kiba, talau dashi hakan bai hana k'irjinsa wani irin rawa ba, tsabar b'acin rai sbd shi d'in tsayayyan namijine, kawai yanayin jikinsa ne hakan talaulayi da shi se shegen k'arfi.
Cikin sake k'ufula yace.
“Kinaso dai agano bama haihu duk da bincike ya nanu muna.lafiya lokacine baiba koh? Bilkisu ashe zaki Iya tozartamu a idanun duniya? Toh na binne maganar families d'insu Baby, yadda muka faro haka zamu qarasa har Abadan bata uba sai ni bata Uwa sai ke. ”
Ya idar da mgnar yana had'ata da qofar yana mata kallon da ya k'ara firgita Mamy, dan duk tsawon zaman da sukayi shekaru 23 da aure bata tab'a zaton Shattima yanada zafin zuciya hakan ba, duk da suna samun d'an sab'ani, jifa-jifa, dan tsakanin harshe da haquri ma sab'awa akeyi.
Hannayenta biyun ta rungumeshi qam tana wani irin kuka tace.
“Kayi haquri Mi Amor karkayi fushi dani naji na haqura na janye Allah ya zab'amana abinda yafi alkahiri, ya dubi zuciyata yaba Baby miji nagari wanda zai riqe mana ita da amana, kayi hkr nabar mgnar har abadan.”
Shattima wata irin b'oyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji dad'in batunta atake yaji nutsuwa ta saukar masa, ab'oyen ya amsa da “Amin”.
Amman dan karta ga damansa ya janyeta yace“Je ki kwanta se da safe.”
Kai ta jinjina masa tasan halinsa bai fiye fushi ba,Amman idan yayi baya sauka akai tsaye,shiyasa bata takura masa ba tace.
“Asubah ta gari mi Amor ka kasance cikin tsari da amincin Allah har zuwa wayewar gari, Allah ya kareka da sharrin dukkan abun qi.”
Sosai yaji dad'in addu'ar ya amsa da.
“Ameen kema haka good night. ”
Ya k'arshe mgnar
yana bud'e qofar ya fice cikin sassarfa ya rufo mata k'ofar.
Mamy Bilkisu ta zube saman carpet tana kuka, haka kawai zuciyarta zafi take mata, irin sosai d'in nan.
Sai da tayi mai isarta ta miqe ta shiga toilet ta d'auro alwala ta fito, ta sanya hijab fari qal har qasa ta shmfid'a darduma ta kalli alqibla ta fara sallar nafila don roqon Allah ya musu zabi mafi alkhiri.
Shattima yana zuwa bedroom d'insa ya kwanta, saman tamfatsetsan royal bed d'insa,ya qure gudun A/C'n ya lullub'a da wani lallausan bargo, ya lumshe fararen manyan lumsassun idanunsa, wanda sukayi wani irin bala'in ja.
Tattausan hannunsa ya d'ora saman goshinsa, yana murzawa da sauri², labb'ansa suna motsi ahankali.
“No! Impossible! Sweetheart me yasa zaki had'ani da Baby? Yarinyar da ban tab'a jin wani abu kanta ba, bayan d'iyar da na haifa acikina? Mtswwww!”
Yaja tsaki ya juya ya kwanta gefen damarsa ya bud'e idanunsa yana d'ora hannunsa saman k'irjinsa yana shafa yalwataccan gashin da yake kwance ak'irjinsa.
Wayarsa ta d'auki ringing.
Yanaji bai d'ago kansaba bare ya kalli Inda ya ajiyesu, se da ta gama ringing ya miqe zaune ya matsa kusan bedside ya kashe wayoyin baki d'aya ya koma ya kwanta, bakinsa d'auke da addu'ah.

Washegari Mamy Bilkisu ba ta yarda tabar Shattima ya fita wajan aikinsa cikin b'acin ranta ba, tayi qoqarinta wajan kyautata masa kamar kullun, har wajan breakfast ta nuna masa kulawa, kafin ta temaka masa ya shirya ya fita aiki, itama ta shirya ta fice cikin damuwa, dan har yanzu yaqi sakar mata fuska, shiyasa yau A hospital aikin cikin sanyin jiki take aiwatarwa, dan Shattima shine farin cikinta.

*Gumel*
Karkasara
Zaune suke akan dining area su hud'u, suna breakfast, gwanin sha'awa.
Hajiya Karima sai dannawa cikin lafiyayyan sinasir da miyar taushe taji naman rago, da Naja mai aiki ta girka, sai zuba santi takeyi zakayi mamakin yadda take kwasar garar girkin, dan d'an banza cine da ita, ga k'aton cikin nata runduna guda,sai k'ara bajewa yake.
Nadiya sosai mahaifiyar tata ta bata dariya, ta daure ta had'iye ta kalli mahaifinta, yana sanye da wata bugaggiyar shadda purple yayi kyau matuqa, kallo d'aya zaka yimasa kasan tabbas Usman da Khairy and Nadiya, babu wani abu nasa da suka bari.
Alhaji Mustapah ma ta basa dariya dakewa yay, ya kalli Nadiya da take kallonsa tana danne dariyata.
Da harshen fulatanci yace.
“Ja'irar yarinya Mom d'inki kikewa dariya.”
Usman Wanda yake kurb'ar tea ya kalli mahaifiyar tasa ya bud'e baki da niyar maganar Zainab, ya ji bakinsa ya masa nauyi, dole ya k'yale ya maida hankalinsa wajan breakfast d'insa yana fad'in.
“Baba Nadiya ai bataji mgna.”
Hajiya Karima aqufule ta d'ago cikin masifa zatayi magana wayarta ta d'auki ringing, se ta maida hankalinta akan wayarta ta d'auki kiran tana kai wayar kunnenta, tare d'aukan plate d'in abincin ta nufi stairs.
Usman ya k'yalk'yale da dariya yana kallon mahaifinsa, tare da fad'in.
“Babanmu ya dai?”
Nadiya tayi dariya tace.
“Ana tsoronka d'an maye yace, dagani har uwata.”
Alhaji Mustapah ya girgiza kansa yace.
“Ku ko Allah ya shiryamin Ku, wato agida ana tsoron uban Ku mamarku kuke tsoro, nine sa'anku koh?”
Dariya sukayi suna fad'in.
“Sorry Babanmu.”
Tissue ya yaga ya goge bakinsa, yana kallon Usman can k'asa yake mgna bakajin me yake cewa, ya miqe ya nufi falon yana gyara zaman hularsa.
Karima kuwa tana haye stairs ta nufi bedroom d'inta, tana amsa wayan.
“Hajiya Shahida aiki fa yayi kyau, kinga jiya ne na basa wannan ruwan, amman alamu sun nuna ya fara ci dan baimin wata magana ba, da ta shafi shegiyar kurman nan, cewa fa yayi zaije katsinar kiji zai tonamin asiri, dan kinji ance duk randa d'ansa ko shi Mustapah d'in duk randa suka had'u komai ya lalace nima kuma zan lalace, kinga kuwa ai ba batun na yarda nayi wasa da aikin.”
Daga can hajiya Shahida tace.
“Yawwa ta wajena kin iya ai nasani, ai insha Allah suda had'uwa se alahira yadda boka RAUNATA ya tura aljani yayi sifar Mustapah ya saki Zainab shi kuma ya shigesa ya mantar dashi ita arayuwarsa toh kinga su wannan 'ya'yan naki ai k'aramin alhakine.”
Karima tayi dariya tace.
“Wannan haka yake qawata su qananun alhakine, duk da ni na haifesu acikina wlh bazan yarda su tozartani ba, bazan cutar dasu ba Amman dole zanyi abunda suma zasu manta da Zainabu, kamar yadda ubansu ya manta da ita.”
Dariya hajiya Shahida tayi tace.
“Yawwa hakan yayi yanzu dai Ayuba ya addabeni akan Nadiya nace masa ya qara haquri insha Allah baida mata sai Nadiya...”
Karima tayi dariya tace.
“Idan tana so ba matsala yanzu dai ya qara haquri tana cikin karatu.”
Sun jima suna hira tana lailaya sinasir bakinta duk yawansa sai da ta cinye shi Tass.


A b'angaran Shattima kuwa acan office yanata fama da baqi da suke shige da fici, ga yawan fills agabansa da zai sa hannu, se wajan k'arfe 11 ma, ya d'an nutsu jama'a suka rage masa 11:30 kuma suka shiga meeting.
K'arfe 12:50 cif su Shattima suka fito daga meeting, yana komawa office yayi alwala ya nufi masallaci.
Zaune yake cikin hamshaqin office d'in nasa, wani irin sanyin A.C da k'amshi mai bala'in dad'i, ya cika office d'in.
Wani files yake dubawa.
Sanye yake da wani irin boyel mai shegen kyau, da tsada fari qal d'inkin ya zauna ajikinsa, farin glass manne akan fuskar shi.
D'ago da kansa yayi yana janye files d'in gabansa, ya jinginar da kansa jikin kujerar yana lumshe kaifafan fararen idanunsa, yana sauke wani irin numfashi.
Hular kansa ya cire ya ajiye gefe ya cire glass d'in idanunsa, ya beqa tattausan baqin hannunsa mai yalwar gargasa ya d'auki wayansa wacce iya families d'insa yake waya dasu.
Lambar Auntie Aisha ya lalubo ya danna mata kira, yana son yaji lafiyar Khairy.
A can Abuja kuwa daidai lokacin
Khairy zaune A Falon Auntie Aisha, bata jima da gama salla ba, ta fito falon kamar yadda Mummyn ta matsa mata ta fito.
Casbi ne ahannunta tana ja.
Sanye take da doguwar riga ta atamfa hijab har qasa, falon ba kowa se Auntie Aisha tana can wajan maigidanta wanda yazo daga tafiya.
Ilham kuwa bata taso daga school ba.
Idanunta sun tara kwalla, kewar Abdoul take duk da ba wani zaman lfy ba sukayi, haka tana missing Dady da Mamynta so take taji muryansu, amman ta kasa tambayar Auntie Aishan.
Wayar Auntie Aisha da take ajiye akan center table, ta d'auki ringing.
Khairy ta miqe tana leqawa, aikuwa taga sunan Dad dinta na yawo saman screen in wayan.
Cikin d'auki ta isa wajan wayan ta d'auki wayan cikin d'auki tai picking call d'in, tare da sanya masa kuka tana fad'in.
“Sweet Dady! I miss you so much, ina sweet Mamy? ”
Shattima ya furzar da zazzafar iskar bakinsa waje yana fad'in.
“Assalamu Alaiki sweet daughter tinda ke baki iya sallama ba,kuka da shagwab'a kika saka agaba, toh me akayi yanzu na kukan Baby?”
Ya k'arashe mgnar yana d'aukan cup glass d'in da yake gefensa cike da ruwa yana kafa bakinsa.
Khairy ta rage sautin kukan ta amsa sallamar tare da fad'in.
“Sweet Dady yaushe zakuzo don Allah?” cikin zallar shagwab'a tayi mgnar tana kuka k'asa-k'asa.
Shattima cikin kamewarsa kamar kullun muryasa na fitar da amon sauti me dad'i yace.
“Uhmm! Randa kika fasa kukan shagwab'ar mna, hope kina lfy ya haquri kuma? Ina Auntie naga wayan a hannunki?”
Khairy ta tsayar da kukan tana fad'in.
“Allah Dady na daina daga yau zanci gaba da masa addu'a kuzo don Allah ina begen ganinku, ni banda lfy sai randa na ganku Zan warke Dady.
Mummy tana wajan Baba ya dawo daga tafiya se ni d'aya Ilham tana makaranta.”
Ta fad'a kamar zata sake fashewa da kukan.
D'an murmushi mai sauti Shattima yayi yana shafa sumar kansa yace.
“Ya Allah kaba daughter miji a makka ko China ko Singapore akaro na biyu naga iya sangarta bata ganin Dady and Mamy.”
Khairy ta fashe da kuka harda shasheqa tana fad'in.
“Allah Dady ni dai bazan kuma aure ba shi kenan nayi farko nayi na k'arshe, ni daku muta ka raba ina tare da iyayena ba wanda zai kuma rabani daku.”
Shattima ya dafe kansa yana fad'in.
“Astagfirullh Baby ai dolenki ma ni ba uban banza bane da Zan ajiyeki acikin gida, kice dai bakya son Dady yaga jikokinsa wato kina min baqin ciki koh baby?”
Yanayin da yayi maganar ya saka Khairy batasan lokacin da tayi 'yar siririyar dariya ba, tana rufe fuskarta da tafin hannunta d'aya tana fad'in.
“Allah Dady sai da naji kunya fa!”
Shattima yay murmusa yace.
“So duk ba wannan ba,dan Allah Khairy ki nutsu kiyi tawakali da Allah ki yawaita sallar dare da karatun Qur'ani, ki yawaita istigfari da salatin Annabi karki dinga yawan mgna istigfari da salatin Annabi ya zama shine abun yawan anbatonki,ki daina yawan kukan nan, idan ba haka ba wlh kinji na rantse bazamu tab'a zuwa ba har ki kammala takaba, Amman idan bakya kuka kina abinda na saki duk qarshen wata zamuje muganki idan ina k'asar OK?”
Khairy jikinta yayi sanyi ta amsa da.
“Toh Dady wlh na maka alqawali insha Allahu zanyi duk yadda kace.”
Shattima yace.
“Very good sweet daughter Allah ya miki albarka, idan Auntie ta fito ki gaishemin da ita Zan kirata zuwa yamma, ki fa ci abinci sosai OK?”
Kahiry ta jinjina kanta tace.
“Amin sweet Dad zanci insha Allah idan ka koma gida kace ina gaishe da Mamytah.”
“Ok Bye.”
Shattima ya fad'a yana katse kiran bai jira ta sake mgna ba.
Wayar ya ajiye ya d'auki d'ayan da take famar ringing.
Ganin Commissioner Aminu ne ya saka shi d'aukan kiran tare da sallama...

Wasa² tsawon sati biyu Shattima ya d'auka yana fushi da Mamy hakan ba qaramin nakasu ya mata awajan aiki ba, sbd Sam bata iya aiwatar da komai A asibitin nata, har yakai ta daina ma mutane tiyata sbd gudun kar tayi ba daidai ba.
Shittima sai da yaga yana neman yiwa masoyiyarsa illah ya saddaqo tare da mata dogon warning akan ko amafarki baya son sake jin mgnar tayi masa alqawalin hakan bazata sake faruwa ba, ai kuwa suka dinqulewa suka koma kamar da kowa na qoqarin faranta ran d'an uwansa.
Ta dage da addu'a akan Allah ya musu zab'in abinda yafi alkahiri.
Sai dai fa mafarki bata fasaba haka sallar neman zab'in Allah tsakanin Khairy da Shattima bata fasa ba, sbd haka kawai takejin bala'in son su zama mata da miji sab'anin da amafarkin da takejin bazata iyaba hakan ba, amman tin lokacin da ta furtama Shattima son abun yake k'ara linkuwa acikin zuciyarta duk irin hukuncin da Shattiman ya mata daidai da k'wayar zarra son ta had'asun su zama miji da mata bai raguba a cikin zuciyarta.
Sosai yanzu ta dage da addu'a akan Allah ya sanyawa Shattima mugun son Khairyn yaji yana k'aunarta da niyar aure itama Khairyn Allah yasa mata son Shattiman son aure, sannan ya sanyawa kowa da kowa son abun daga iyayan Shattima har nata da sauran dangi Allah yasa abun yazo da sauqi kar asamu tangard'a ako ina.
Wannan shine abinda Bilkisu take roqo ako wane dare tana kuka tsakaninta da Allah son taga Shattima ya auri Kahiry take, dan ta gaji da mugayen mafarkan nan, ko ba komai ita gani take idan Shattima ya auri Khairy *YI WA KAI* ne ai,kuma ba mamaki rabonsa ajikinta.

A b'angare d'aya kuma suna yawan kiran Auntie Aisha suna jin lafiyar Khairy idan sun fara waya sai auntie Aisha ta amshe wayan tace sun mata yarinya na takaba suna sakata surutu hakkaan ba kyau.
Shatiima da Mamy zasuyi dariya sannan su bada haquri, idan haka ta faru sai sun kwashe kwana uku basu kiraba kafun su kira dan atare suke kira da safe ko da dare lokacin suna tare.
Ana haka har akayi ma Abdoul sadakar kwana 40.
(Kenan A musulumce Khairy ta fita daga takaba).
Amman da yake ba wanda yasan Abdoul bai kusanci Khairy ba, dole take iddah dan sam bazata iya fad'in cewa ga halin da take ba, daga ita sai Allah suka San hakan.
Khairy tayi ta kuka awaya akan rashin zuwan iyayan nata har yanzu da ta cika wata biyu A abujan, har commissioner Aminu da Ammi sunzo ganinta wuni sukayi suka koma Amman ace iyayanta basu zoba, kullun dai Shattima da Mamy haquri suke bata akan suna tafe acikin satin nan murna awajanta kamar zatayi hauka.

B'angaran Salim kamar zaiyi hauka an hanasa ganin Khairy ya mata gaisuwa, yayi alqawalin ruwa da iska sai ya auri Khairy yana jiran ta gama takaba ne, yasan ko awaje sai sun had'u.
Anata shirye² biki har ankai akwatinan kaya masu kyau Hashim ya bada kud'i Sa'idah suka had'u,yau aure sauran sati gudu amman Salim ba wani shirye² da yake akan bikinsa da Aliyah yace ya gama shirinsa tin auren Khairy yanzu jiranta yake ta gama takaba ya koma gareta.
Aliyah kuwa mutuwar Abdoul ta zautata ta zama kamar wata zararriya, bata aiki sai fad'in.
“Yanzu da gaske Abdoul ya rasu ya barni? Shi kenan bazan aureshi ba? Shi kenan yanzu D'iyar minister tayi sanad'in da na rasa Abdoul?”
Wannan shine sambatun da Azizah take yawan yi.

Acan Katsina kuwa Zainabu ta sake Masha Allah tayi kyau ta saki jikinta kamar yadda mutumin yace zai samo mata aikin koyarwar A makarantar kuramen anan Katsina toh bayan ya mata tambayoyi ta rattabo masa bayanai da bebanci tsaf ya gane ya duba takardunta Masha Allah nan take ya Kira principal d'in makarantar kuramen da yake abokinsa ne ya masa bayani tare da d'aukan takardunta ya tura masa ta whatspp, cikin kwana biyu akace ta Fara zuwa murna wajan Inna ADAMA da Abbu abin ba'a cewa komai.
Cikin ikon Allah ta fara zuwa koyarwar Allah ya had'ata da yaran kirki acikin makarantar Bari 'yan ajinta, kafin wata d'aya zuwa biyu Zainab tayi suna A makarantar Yara da manya suna girmamata sabida kamun kanta, da son yaranta ga kirki kowa natane.


Misalin 11 na dare Mamy tsaye gaban madubi tana kallo yadda tayi kyau,farar fatarta take sheqi, ta gama shirinta tsaf cikin kayan bacci, Riga da wondo ta shafe jikinta da humrah mai qamshi, ta sanya hular bacci akanta ta d'auki audiga ta zuba miski aciki ta janye wandonta ta ware qafafunta ta goga sosai ta shiga toilet ta jefa aufigar cikin abun shara, ta dawo ta bud'e drower ta d'auki wata roba ta bud'e ta kafa bakinta sai da tasha kusan rabin-rabin robar ta rufe ta mayar ta ajiye, ta b'are sweet ta jefa bakinta ta d'auki wayanta ta kashe k'wan wutar d'akin ta fice d'aga d'akin.
Anutse take tafe har ta iso qofar falon Shattiman, kad'an² takejin qaran Tv na tashi.
Da sauri ta nufi hanyar da zata sauka qasa, da sassarfa take taka steps.
Tana saukowa kitchen ta nufa ta dafo masa coffee kamar kullun, ta juye a wani had'add'an cup glass ta d'orwa akan madedecin tray'n d'in tankaran ta bud'e fridge ta d'auko tufa d'aya ta yanka masa ta jera gefen cup d'in coffee d'in, ta d'auka ta koma stairs.
A hankali ta bud'e qofar ta shiga bakinta d'auke da sallama.
Wani irin sanyin qamshi ya daki hancinta ta lumshe ido ta bud'e, tana kallonsa, zaune saman sofa ya kafama Tv kyawawan fararen idanusa yana kallon tashar Aljazeera.
Sanye yake da wando iya guiwa da singlet, itama fara kyakyawar baqar fatarsa, jikinsa mai yawan gargasa duk A bayyane, sai sheqi yake haka sumar kansa luf akwance kyakkyawar fuskarshi bazaka gane yanayin da take ciki ba.
Mamy ta ajiye trayn tangaran d'in ta haye saman cinyarsa tana shafa sajansa tana kallonsa.
Kallonta yay yana fad'in.
"Aushhhh! Sweetheart zaki karyani fa! Bani coffeen.”
Ya k'arashe mgnar yana zura hannunsa cikin rigarta yana mata wani fitinannan kallo.
Idanunta ta rintse lokacin da taji yatsunsa biyar sun ratsa tsakiyar fatar k'irjinta.
D'umin labb'ansa taji cikin kunnenta yana hargitsa mata lissafi yana fad'in.
“Sweetheart! Coffee. ”
Dariya ta kub'uce mata tana bud'e idanunta tace.
“Ba wani coffee Mi Amor kayi yadda kakeso sai kasha coffen.”
Ta fad'a tana gyara zamanta sosai ajikinsa yadda zaiyi yadda yakeso dan tasan halinsa da zaran ya fara salonsa baya son akatse masa, take yakejin abun ya fice aransa, shiyasa take taka tsantsan da gujemasa idan ba da qwaqwaran dalili ba.
Kusan 15 minutes yana cakud'ata kafin yace ta basa coffeen yasha.
Da kanta fa basa ya Sha ta basa tufa yaci ta manne jikinsa suna hira abun gwanin ban sha'awa, kafin su koma daga cikin bedroom nan suka qarasa wasan cike da son juna da farantawa juna rai, da asuba yake fad'a mata tafiyarsa Tunisia, Mamy harda k'wallarta ta kewarsa da zatayi.

Bayan kwana 3
_*Khairy clinic and maternity.*_
Mamy tsaye acikin office d'inta tana tana tattara takardu waya manne A kunnenta mgna take cike da nutsuwa,salon yadda take mgnar zaka gane da oga Shattima take mgna da shi wanda yau kwanansa uku baya qasar.
Tana sanye da orange doguwar riga mai bala'in kyau taci adon stones, ta d'ora rigarta ta likitanci tana sanye baqin glass, murmushi take saki anutse fararen haqoranta suna haskawa tana magna tana wani fari da idanu.
“Mi Amor! Please sonake na wuce Galadanci naga su Baffa daga can na wuce *Rafin Sanyi* naga jikin Anna, kaga yamma tayi sosai idan na isa gida zamuyi mgna,please hope kana lfy ya sanyin Tunisia?”
Shattima daga can wanda shigowarsa kenan daga meeting, yana baje saman sofa cikin wani tsararren falo ya amsa da“Uhm! Alhmdllh sweetheart, ya aiki da fama da jama'a? OK bye nima Zan fita anjima bye.”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran.
Mamy ta jefa wayanta ajaka ta jera takardun waje d'aya ta cire rigan aikin ta linke ta ajiyeta wajan ajiya ta Sanya hijab d'inta orange har qasa ta d'auki Jakarta ta fito.
Tana rufe qofar ta zare key tana mana matemakiyarta mgna Maryam ta shigo da sallama.
Mamy tace.
“Kai wa nake gani daughter? ”
Maryam ta qaraso ta rungume Mamy tana murmushi tace.
“Allah Mamy nayi missing d'inku dayawa keda Dady, karatu ya hanani zuwa rabona daku tin arba'in d'in yaya Abdoul, ga shi har yayi wata biyu da kusan kwana 6 aqasa.”
Mamy Bilkisu tayi murmushi ta Kama hannunta tace.

“Ai kuwa naji dad'in ganinki daman Dadynku baya gari muje toh fatan Abida da abbanki sunsa da zuwanki?”
Maryam tayi dariya tace.
“Ai su suka saukeni daga makarantarmu suke anyi taron iyayan Yara, kinga yau juma'a ai na kwanan miki biyu.”
Mamy ta sumbaceta tace.
“Ngd sweet daughter kinga kuwa gobe zanje Abuja wajan auntie ki...”
Tsallen ihu tai tana ruqumqume Mamy tace “Zanje don Allah ki roqamin Abba da Ammi.”
Mamy tace“An gama daughter.”
A wulleliyar motar Mamy Ash Kala mai shegen kyau suka shiga baya direba yaja suka tafi Kai tsaye Galadanci ta sanar da direban ya fara kaisu sbd yanzu daidai lokacin da zata samu Baffa liman ne agida.
Suna zuwa inno ta tarbesu kamar zata goya Bilkisu, A mutunce suka gaisa an cika.musu gabansu da kayan motsa baki.
Inno tace.
“Ya wajan Ummulkhairi? Tana lfy ko? Shekaran jiya Aisha ta Kira mun gaisa wlh se qorafi take akan kunqi zuwa.”
Mamy tace.
“Wlh Umma laifin Shattima ne yace wai idan ta ganmu rigima zatayi yafi son ta qarasa takabanta cikin nutsuwa, Amman gobe inaso natafi, Baffan yana nan kuwa? Ban gansa a rumfar gate ba?”
Inno tace.
“Nima hakan yasa ban matsama Shattima kujeba zatafi yin takaba acan da kyau, babanku na b'angaransa d'azu yayi baqi toh tinda suka tafi bai fito ba, qila lazimi yake muje mana Ku gaisa.”
Mamy cike da murna ta amsa da.
“Toh.”
Ta miqe Maryam ma ta miqe.
Tare suka nufi b'angaran Liman d'in.
Inno ta fara shiga da sallama yana zaune yana Jan casbi.
Amsawa yayi yana kallonta.
Can nesa da shi ta zauna tana fad'in.
“Bilkisu ce tazo.”
Liman yace.
“Masha Allah toh ta shigo mana”
Inno ta d'an daga murya tace.
“Bilkisu! Ku shigo.”
anutse suka shigo bakin Bilkisu d'auke da sallama, ta zube nan qasa saman carpet tana gaishesa cike da ladabi.
Liman ya amsa fuska sake, yana fad'in.
“Ya aiki Bilkisu? Ya wajan matata mai rigima?”
Mamy ta amsa da.
“Lafiya lau Baffa.”
Maryam tayi kamar yadda Mamy tayi ta gaishesa.
Baffa yace.
“Ina kika samu yarinya me hankali haka?”
Mamy tace“Maryam ce d'iyar commissioner Aminu abokin Dadyn Khairy.”
Liman yace.
“Masha Allah na tunata kam yanzu kusan sau biyu ai suna zuwa da iyayan nata tare gaisheni, kice dai kin kuma d'iya?”
Mamy tayi murmushi ta kalli Maryam tace.
“Daughter! Don Allah kije b'angaran umma ki jirani yanzu Zan fito sai mutafi kinji?”
Maryam cike da ladabi tace.
“Toh Mamy sai kin fito.”
Tama su Liman sallama ta miqe ta fice.
Amman sai ta tsaya A qofar falon ta lab'e tana fad'in.
“Meye Mamy bata son naji?”
Mamy Maryam tana fita tayi qasa da kanta cikin ladabi tace.
“Baffa inada magana daku dan Allah inaso ku fahimceni sannan kumin kyakkyawan zato, nasan duk duniya idan ba kai ba wanda zai saka minister ya amince da wannan abun Kai tsaye.”
Baffa yayi murmushin su na manya yace.
“Bilkisu kenan nasnaki tin yarintarki har yau ban tab'a jin ko ganin aibinki ba wajan mijiiki da sauran 'ya'yana koh matata gata zaune, dan haka fad'i duk abinda kikeso na saka Abdallah ya miki matuqar bai sab'awa addini ba na miki alqawalin zan sakashi ya miki SBD baki tab'a zuwa roqon wata alfarma wajenaba Bilkisu dan haka fad'i ko ma meye kanki tsaye kinzo wajan da za'a share miki hawaywmki insha Allahu...”
Mamy cikin k'warin guiwa ta bud'e bakinta tace.
“ Na gode Baffa Allah ya qara girma.
Don Allah don darajar Annabi Muhammad S.A.W Baffa so nakeyi ka saka Shattima ya auri Khairy daga ta idar da takaba...”
Sam Bilkiau bataga lokacin da Liman da inno suka miqe ba, sai salatinsu taji, suna tafa hannayensu.
Daga can kuma qofar falon qaran zubewar Maryam sukaji tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Me zanji me Zan gani? Mamy aure tsakanin uba da 'yarsa?”
Ta qarashe maganar tana fashewa da kuka, tare da miqewa tsaye.

Mamy
amugun kid'ime ta miqe tsaye hankalinta yayi masifar tashi ganin Maryam tsaye taji komai...

*YI WA KAI*

Free Novel

_Alhamdulillah am back🏇🏻 na cika alqawali, yau Alhamis 20/10/2022_


31&32

Ba Mamy ba Baffa liman kansa hankalinsa ya qara tashi, ganin Maryam taji komai, da Mamy ta fad'amusu.
Hakan yana nufin babu maganar suji yadda akayi Ummulkhairi ta halatta Shattima ya aureta, bare su ruqi alfarmar abar maganar iya su kar kowa yaji, Khairy ba 'yarsa bace.
Ganin Maryam ta juya aguje zata bar falon, Baffa yace.
“Don sonki da Annabi Maryama tsaya zan nemi alfarma wajanki, dan darajar Annabi Muhammadu S.A.W.”
Cak Maryam ta tsaya tanajin wani irin mahaukacin kishin Khairy da haushin Mamy tinda har ta furta aure tsakanin Shattima da Khairy tasan basune suka haifeta ba, haka yana nufin idan Khairyn ta auri Dady Shattima ita baza tab'a samunsa ba?
Fashewa tayi da kuka ta juyo ta nufo wajansu, ta zube qasa, cikin kuka tace.
“Baffa ga ni insha Allah zanyi muku ko wace irin alfarmace, insha Allahu.”

Mamy kuka take sosai tayi zaman 'yan bori agaban Inno.
Iya tashin hankali Mamy ta shiga ganin Maryam ta gama sanin komai, gata gaban Baffa zaune har suna neman alfarma, wanda tasan baya wuce su ruqeta ta rufa musu asiri abin mgnar iya su bayan tasan mutum na yanzu zaiyi wuya hakan ta samu...
Wayar Mamyn da take cikin handbag d'inta ta d'auki ruri.
Cikin sauri ta bud'e tana kallon wayan.
Sunan Shattima ne yake yawo saman screen

Please Login or Register in order to submit comment