Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kina ina..? Wallahi yau akwai masifa da bala'i agarin dutse.....”

Rahma real Ladingo Ce😍

_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha me sunanki.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭



_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 3&4*


“Akan me kika shirya dukkan tuggun nan Ko ince kuka shirya keda Father, dan ku rabani da muradin raina? Me namuku, anya kune iyayena...”
Fauuu kakeji hajiya Sa'idah ta d'auke shi da gigitattun maruka har guda 3.
Kumatunsa ya dafew yana kallonta ya ce.
“Umma! Ni kika mara sabida gaskiyata, ina tambayar meyasa kuka tauyemin haqqina,na hanani abar sona?”
Ya k'arashe mgnar hawaye na zarya akan fuskarshi.
Cikin b'acin rai take magana.
“Toh maras kunya, nace maras kunya nunawa duniya kai bakada kunya bare tarbiya dan babanka, naji na qara tsanar Ummulkhairin, ka tab'a ganin iyaye sun cutar da d'nsu? Kasan irin gatan da muka maka kasan taimakon da muka maka, kasan yadda muka kauda Sani da nunawa namu namune dan mu tsiratar da kai daga wannan k'addararan auren? Kasan yadda akayi aka tsiratar da kai da mukayi, akan k'in amincewa ka auri Ummulkhairi? Yarinyar masifa ce annoba ce, da acan baya kafin ta shigo rayuwarka haka kake? Nace haka kake? Jibeka ka zama wani sakarai mahaukaci zautacce.”

Ta k'arashe maganar cikin zafi tana fizgar hannunsa suna tafiya.
Baki d'ayan falon kallonsu akeyi cike da mamakin kalaman umma Sa'idah.
Salim kasa magana yayi zuciyarsa na tafarfasa, binta kawai yake har suka shiga b'angaren alhaji Hashim, wanda shigowarsa kenan yana amsa waya.
Kusansa ta saki hannun Salim wanda yake d'igar da jini.
alhaji Hashim ya katse wayan yana miqewa tare da fad'in.
“Subanallahi my son hannunka na fitar da jini, sannu ka farka?”
Salim ya matsa gefe yaqi yarda Hashim ya tab'asa.
Cikin tashin hankali yake fad'in.
“Karku tab'ani sai kun fad'amin akan me zaku rabani da farin cikina? Me na muku kuka rabani da abinda nafi so?”
Alhaji Hashim yay murmushi yana fad'in.
“Yaro man kaza.”
Ya kamosa ya nad'e hannun da yake fitar da jini, da handkerchief, ya zaunar da shi saman 3 seater, ya zauna kusan shi, ya ce.
“Sa'idah! Zauna mu masa bayani ko zai dawo hayyacinsa.”
Ba musu ta zauna suka sanyasa tsakiyarsu.
Idanu ya zuba musu yana jiran abinda zasu fad'a.
Alhaji Hashim yay gyaran murya ya ce.
“Inaso kaje kayi nazari da kanka tin lokacin kuka k'ula alqa ta soyayya da 'yar gidan minister Shattima, asara nawa kayi, accident nawa kayi rashin lafiya nawa kayi, na rantse ma da Allah ayau babu abinda muka baka sbd ka fita daga hayyacinka dan kar ka auri Ummulkhairi.
Ranar da kayi gobara motarka ana sauran sati d'aurin aurenku motar ta k'one qurmus, bazan manta ba ranan ai naje k'auyen zakirai wajan Malam ILU mai taimakamin, nake masa bayanin irin yawan tsautsayin da yake samunka.
Ya cemin zai min istiharah ta kwana washegari zai min bayani, washegari da safe ya kirani awaya yake fad'in wacece Ummulkhairi da so samu ne ka yanke aqa da ita.
Ranan hankalina ya tashi nayi juyin duniya ya fad'amin meke faruwa ya dai ce nayi qoqari na rabaku idan zaka hanu, shi bazai zayyano min komai ba, nan gaba akwai gagarumar matala, zamanku ba alkhairi.
Wlh tin ranan har zuwa yau ban kuma barcin kirki ba, na rasa ta inda zan b'illowa al'amarin, inajin matuqar nauyin minister Shattima, amman yau lokacin da naganka akwance babu rai na cire kunya da jin nauyi na aika musu saqon suyi haquri aure ya fasu duk da nasan zan sha zagi tinda bazan fito na fad'i gsky ba, taron da mukayi dan zuwa d'aurin aurenka da Ummulkhairi sai ya juye muka d'aura maka aure da Aliyah d'iyar yayana Basiru wacce take karatu a A.B.U Zaria sabida kar mutane su ankare, ita kuma acan an d'aurawa mai tsautsayi, Abdullahi Aminu kazaure.”
Salim da idanu kawai yake binsu da kallo ba ko k'iftawa,mamaki fal zuciyarsa, kawai dan k'addara ta haushi sai ad'aurawa Ummulkhairi? Jin da wanda aka d'aura mata auren hanklinsa ba qaramin tashi yay ba.

Miqewa ya yi bai ce uffan ba ya fice daga falon yana tangad'i hawaye tab sun cika masa idanu, shi kad'ai yasan me yake ji me kuma zaiyi.
Hajiya Sadi'ah ta ce.
“Ya Allah ka kawo mana k'arshen musibar nan.”
Alhaji Hashim ya ce.
“Amin kuma dan ubansa sai ya zauna da Aliyah ya gama jimamin rashin annobar ta sa...”


Misalin qarfe shidda na yamma commissioner Aminu ya bar gidan minister shattima, ya nufi gidansa da yake cikin nan unguwar commissioners Quarters, titi biyune ya shiga tsakanin su da Shattima.
Yana isa gida wanka yayi ya d'auro alwalan Maghreb sbd ta kusa, ya nufi cikin lambu ya zauna, ya lalubi number d'ansa Abdullahi ya danna masa kira, yana so sai ya gama magana da shi kafin ya tara iyalinsa ya musu bayani.

_*'Kasar*_
(Singapore)

Matashine d'an kimanin shekaru 28 sanye da kayan motsa jiki, yana tsaye ad'akin motsa jiki, ya had'a uban gumi daga ganinsa yanzu ya gama motsa jikinsa, sbd uban gumin da yake yana famar goge zufar.
Farine dogo ingarman namiji tsayayye mai murd'add'an jiki, kyakkyawa ma'abucin fara'a, yanada manyan idanu farare da dogon hanci bakinsa mai fad'ine jajir da shi, yanada gashin gira da na idanu akwai yawan sumar kai bai fiye askewaba sosai, kallo d'aya zaka masa kasan shi d'in bafulatanin asaline fararen fulani.
K'aramin towel d'in hannunsa wanda ya gama goge zufa ya rayata saman dogon wuyansa, ya fara takunsa mai burgewa ya bud'e qofar ya fito ya nufi tsararran d'ank'aramin falonsa.
Fridge'n ya bud'e ya d'auko gorar ruwa mai sanyi ya bud'e tare da bismillah ya kafa bakinsa.
Sai da yasha sama da rabi ya rufe ya maida fridge'n ya qaraso ya zauna saman sofa ya zuba dogayen k'afafunsa saman center table, ya lumshe idanunsa cikin daddad'ar muryashi yake fad'i.
“Ya Allah! Ni kam yau fad'uwar gaban me nakeyi ne?”
Ya k'arashe maganar yana bud'e idanunsa, wanda bai sauke su ako Ina ba sai kan wayasa da take ajiye saman table d'in tin kafin ya shiga motsa jikinsa ya barta anan kuma a silent take.
Hannunsa ya beqa yana fad'in.
Abby! ”
Yay picking call d'in ya nufi kunnensa da wayan, yana miqewa tsaye ya fara takawa zuwa bedroom da nufin idan sun gama magana yayi wanka.
Kamar an kwab'e wayan ta sulale tafad'i k'asa saman tayis tayi wani irin fashewa glass d'inta yay raga-raga.
Abdoul ya dafe kansa yana fad'in.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil.”
Ya duk'a ya d'auki tsadaddiyar wayan ta shi da ta canza kamanni, ya danna ba'a ganin komai ta tashi a aiki, yakai wayan kunnensa ya ji ko zaiji magana mahaifin nasa.
Cikin sa'a kuwa ya ji muryasa yana fad'in.
“Abdoul! Lfy kuwa? Me ya farune?”
Falon ya dawo ya zauna yana murmushi ya gaishe da mahaifin nasa, yana fad'in.
“Wlh Abby wayana ne ta fad'i kaga fashewan da tayi komai bana gani taci screen, glass d'in ya farfashe sai wata.”
Daga can commissioner Aminu ya ce.
“Subahanallahi sannu Abdoul, yauwa nace kuwa ka Kira k'anwar taka Ummulkhairi ka mata barka yaune aurenta fa!”
Kansa ya shafa yana murmushi ya ce.
“Wlh na manta Abby amman zuwa gobe insha Allahu zan kirata.”
Daga can Aminu yay gyaran murya ya Kira sunansa.
“Abdullahi! Kasan dai Ina sonka bazan tab'a abinda zai cutar da Kai ba koh?”
Abdoul ya amsa da.
“K'warai kuwa Abby ni shaidane me ya faru?”
Abby ya ce.
“Allah ya maka albarka yasa ka gama da duniya lfy.”
Ya amsa da.
“Amin Abby fad'amin me ya farune?”
Gyaran murya yay ya ce.
“Alhaji Hashim da d'ansa suke son raina mana hankali cikin taron baina nasi, mu kunyata ni kuma sai nayi abinda da nasan insha Allah alkhairine...”
Tass ya labarta masa komai akan aurensa da Ummulkhairi..
Abdoul ya miqe tsaye yana firfito da manyan idanunsa waje, jikinsa har tsuma yake bakinsa na rawa dak'yar ya iya furta.
“Abby! Aure kuma nida Ummulkhairi? Ya zanyi da Azizah?”
“Ok saki Ummulkhairi da na aura maka tinda ban isa da Kai ba Abdoul. ”
Hankalinsa atashe ya ce.
“Duk ba haka bane kayi hkr Allah ya sanya alkhairi.”
Aminu ya amsa da.
“Amin Allah ya maka albarka daman nasan bazaka kunyatani ba.”
Abdoul hannunsa dafe da kansa ya amsa da.
“Amin Ngd Abby Allah ya k'ara girma...”
Suna sallama ya buga wayar da bango ya fara Kai komo daga tsakanin bedroom zuwa falo, yana dunk'ule hannayensa, shi kad'ai yasan azabar da yake ji azuciyarsa, akan me za'a aura masa wata Ummulkhairi?
“Shin wai su ansan dalilin da yasa suka fasa aurenta ni Abby ya liqamin? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Abinda yake fad'a kenan ya nufi bedroom.

Acan kuwa Nigeria.
Bayan sallar isha'i commissioner Aminu ya Kira hajiya Abida ta dawo gida, dan har lokacin tana can gidan minister Shattima sai ta kai amarya d'akinta daga can zata wuce gida.
Zazzaune suke a falon hajiya Abida na gefensa sai yaransu guda uku sun zagayesu Habib Nafisa Auta Sabir, Maryam na can wajan amarya.
Gyaran murya yay ya kirata.
“Abida! Akwai al'amarin da ya faru yau wanda daman can ubangiji ya k'addara zai farun, ni nawa cikawane akan umarnin da ubangiji ya bani, dan nasan komai da umarninsa muke aiwatarwa...”
Kakaf ya zayyane mata abinda ya faru ayau d'in ya d'ora da cewa.
“Bana son kice komai ki sanya musu albarka kawai da fatan alkahiri, sai ki tura masu aiki da Nafisa su gyara b'angaran Abdoul na nan, anjima nida ke zamuje mu d'aukota ta zauna wajanmu kafin yazo dan gagarumin biki za'ayi insha Allahu idan ya dawo.”
Hajiya Abida ta rangad'a gud'a ta ce.
“Alhamdulillahi wlh naji dad'i sosai da wannan abun, najima inama Abdoul kwad'ayin samun Ummulkhairi Amman ganin ga inda hankalinta ya karkata shima hankalinsa wajan Azizah take ko wa? Wlh shiyasa naja bakina nayi shiru, ashe duk wannan hidimar da nayi yau d'ana nayiwa, Kai Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi.”
Commissioner Aminu ba qaramin dad'i ya ji ba ganin matarsa tayi na'am da auren.
Habib ya ce“Gsky naji dad'i bro Abdoul yayi sa'ar mata, dan wlh Ummulkhairi tafi Aziza komai har tarbiya farar fata kawai Aziza ta fita.”
Nafisa mai bin Maryam ta ce“Kwarai Yaya Habib, ai kuwa ranan tarewarsu akwai shagali, sai mun sake anko.”
Auta Sabir ya ce.
“Ni kuma zan koma gidan auntie Ummulkhairi.”
Dariya dukaninsu suka sanya zuciyoyinsu fari k'al.
Abidah ta kira Lantana da Kulu masu aiki ta ba Nafisa key tace suje su gyara part d'in Abdoul a saka turarukan d'aki na wuta da ruwa.
Ai kuwa kafin 40 minutes sun gyara tsararren falonsa da bedroom d'insa da toilet, wanda ka rantse d'akin amaryane, amaryama 'yar gata babu abunda babu aciki ko ina sai k'alli yake.

Misalin 8 pm Auntie Balaraba da auntie Madina yayar Bilikisu suka shigar da Ummulkhairi toilet suka Fara gurjeta, da ruwan lalle wanda yasha maguguna da turaruka,sai mita take.
Auntie Balaraba tana mata dariya.
Tsaf aka shiryata cikin wani had'add'an material pink, wanda tsaya fad'in tsadarsa bata lokaci, anyi mata makeup na kece raini turaren wuta na jiki ya kamata, da na ruwa dole idan ka kalli baqar yarinyar nan ka kuma kallonta sabida bala'in kyau d'in da tayi.

K'arfe 8:40 pm cif motocin su auntie Balaraba suka iso qofar gidan minister, tamfatsetsan gate d'in aka bud'e musu suka shige motar amarya bata tsaya ko ina ba sai dab da qofar sashen minister falonsa na hutawa dan nan yace ma Balaraba su kawota.

Falon shiru kakeji sai qaran A.c da TV wanda qaran sautin TV ahankali yake fitowa, tashar CNN ana gabatar da labarun harshen turanci.
Dogayen baqaqen k'afafunsa meqe suke saman sofa, ya jingina bayansa da pillow, hannunsa d'auke da wani farin cup glass fura ce yake k'urba taji nonon shanu mai lunk'um asaman cup d'in.
Sanye yake da wani yadi fari k'al mai taushin gaske, d'inkin shan iskane na hutawa agida, fararen manyan idanusa kafe akan TV, yana girgiza k'afafunsa.

Suna isowa Balarba password d'in da minister ya fad'a mata ta saka, qofar glass d'in ta bud'e suka shige bakinsu d'auke da sallama.
Kansa ya juyo ya zuba musu idanu bakinsa na motsawa alamar sallama yake amsawa.
Kusan shi Balaraba ta zaunar da Ummulkhairi tana fad'in.
“My brother ga Baby Ku gama bari muje falon auntie Billy mujiraku kafin 'yan d'aukan amarya su zo.”
Minister ya saki sansanyar murmushi ya ce“Ok ba damuwa ki turomin Bilkisu, ah Maryam! Kina nan baki koma gidaba? Sannunku da qoqari, Suhailat Allah ya muku albarka.”
Ya k'arashe mgnar yan kauda kansa sbd kallon da Maryam take yi masa kamar zata cinyeshi, idan da sabo ya saba da kallon yarinyar abun na bashi tsoro wani lokacin.
Su Sulahilat suka amsa da “Amin.”
Suna ficewa.
Maryam kuwa bata tafi ba, aladabce tai k'asa da kanta ta ce.
“Eh Dady sai munkai auntie khairy daga can sai na wuce gida ai Ammi tana nan, tare zamu tafi.”
Ta k'arashe mgnar tana juya anutse tana tafiya cikin nutsuwarta.
“Ok.”
Shattima ya amsa yana kamo hannayen Ummulkhairi yana murmushi ya ce.
“Masha Allah,sweet daughter yau za'a bar Dady koh?”
Ya k'arashe mgnar yana leqa fuskarta ta cikin mayafin.
Kuka Khairy ta fashe da shi ta fad'a jikin Shattima tana shasheqa.
D'agota yay cikin nutsuwarshi yana fad'in.
“Lah! Haba My sweet kar muyi haka mana, kuka kuma sabida Allah? Toh bari nima nayi kukan sai arasa mai rarrashi wani tsakanin uba da 'yarsa koh?”
Ya k'arashe mgnar ya d'ago fuskarta da tafukan hannunsa ya mele baki irin zaiyi kukan nan yayi narai-narai da idanu, yana kallonta, ya fara kukan gangan harda shan majina.
K'urr ta masa da idanu tana shasheqar kuka, amman ganin abinda yake ya saka ta had'iye nata kukan sai kawai ta k'yalk'yale da dariya tana maqalqaleshi ta sak'ala hannayenta wuyansa tana tab'a dimples d'insa da yake lob'awa.
Cikin dariya hawaye na zarya akan kuncinta, da zazzaqar muryata ta ce.
“Wallahi sweet Dady! Kukan ya maka kyau daman kayi na gaske na tab'a ganin hawayen sweet Dady na farin ciki ya aurar da babynsa.”
Ta k'arashe maganar a shagwab'e tana Jan gemusa da gashin sajansa.
Baki da hanci ya Saki yana kallon ikon Allah.
Bilkisu ce ta shigo falon tana kallonsu ta ce.
“Ya dai? Duk kallon k'arshen ne akeyewa baby haka ba k'iftawa?”
Murmushi yay ya ce.
“Sweetheart! Baby ta ce kukana take son gani yau, zo ki zama sheda.”
Ya fad'a yana Jan dogon hancin Ummulkhairi,tare da zungurinta akai cikin sigar wasa.
Zama tayi kusan Shattima tana dafa cinyarsa tayi dariya ta ce.
“A'a ni wannan mgna bana shiga tsakanin uba da 'yarsa ba ruwana, ai sai ka mata kukan mugani musha dariya.”
Ta fad'a tana Jan dogon karan hancinsa.
Shattima ya murmusa ya janye Ummulkhairi daga jikinsa ya zaunar da ita akan cinyar Bilkisu.
“Aushhhh! Mi Amor kafa San baby da nauyi ai sai ta karya maka ni sauke min ita gaskiya, yadinya taykusa biyuna.”
Shattima ya zaro mata idanu tare da murd'e mata baki ya sumbaci bakin ya ce“Tubarkallah bazaki cinyemin 'yata ba, idan ta karyaki ba sai ta zabomin k'aramar yarinya sabon jini cikin k'awayenta ba na aure mubarki da jinya can da tsaminki.”
Ya k'arashe maganar cikin kamewarsa kamar gaske yana mata gwalo.
Dariya Ummulkhairi tayi ta sake shigewa jikin Bilkisu tana fad'in.
“Wlh wannan salon love d'in naku yake burgeni tin ina k'arama shiyasa nakeda burin nunawa nisful Hayat ba wani sai shi, kamar yadda nake kyautata zaton nima ba kishiya irin na sweet Mamy ko sweet Dady?”
“Yeah Baby, yanzu dai sweet daughter ban hankalinki nan.”
Ya k'arashe maganar ba wasa yana kamo hannunta, ya ce.
“Sweet daughter! Kinsan dai bazan tab'a cutar dake ba koh?”
Kai ta jinjina ta ce.
“Eh Dady nasani.”
“Good Baby abinda nakeso dake akoda yaushe ki amshi k'addaraki mai kyau da akasin hakan, kisani ni bazan tab'a cutar dakeba...”
Nasiha yay mata mai kashe jiki akan tama mijinta biyayya da iyayansa taso 'yan uwansa da duk wanda ta gani tare dasu,sannan ta kasance mace me sakin hannu kar abun hannunta ya gamata da kowa, ta kyautatawa makotanta koda ba musulmai bane,ta zauna da kowa lafiya, ta tsayar da sallah, ta kasance kamar baya kullun cikin karatun Qur'ani, ta kasance kamar baya azikhar na safe da yamma.
Bayan ya gamata nasiha mai ratsa jiki, ya umarci Bilkisu ma ta mata nasiha sosai amatsayinta na mahaifiyarta sosai suka kashe mata jiki da nasihar su, ta fara kuka ta rungumesu jikinta yayi sanyi wata irin kewarsu take ratsa dukkan sanssan jikinta.
Shattima ya shiga buga bayanta ya ce.
“Daughter! Bar kukan haka kar kanki yayi ciwo, kuma kinga kwaliyarki zata b'aci fa! ina mai baki haquri sweet daughter ki amshi k'addaraki ki mana biyayya zakiga sakammako mai kyau...”

Tsaf ya zayyane mata dukkan abunda ya faru wajan d'aurin aurenta da Salim Allah yayi ikonsa aka d'aura mata aure da Abdulllahi d'an aminsa commissioner Aminu.
Ummulkhairi tayi wata irin zabura jikinta ya fara rawa gab-gab, dak'yar cikin wani irin matsanaicin kuka mai tsuma zuciya take fad'in.
“Dady! Salim bai aureni ba? Me na masa? Yanzu na rasa muradin raina? Meye aibuna da ya gujeni? Dady! Meyasa Salim zaimin haka? Ya zanyi da tarin k'aunarsa da nakeyi? Yanzu ban samu Salim ba amtsayin abokin rayuwata? Dad Abdoul na aura..?”
Ta k'arashe maganar cikin fitar hayyaci idanunta na lumshewa kawai sai gani sukayi ta zube jikin Shattima babu alamar rai atare da ita...
Bilkisu ta kamata tana fashewa da kuka tana fad'in.
“Na shiga uku! Dadyn Khairy kaga abinda nake gudu koh? Yanzu Allah kad'ai yasan ranan tashinta....”
Shattima ya rufe mata baki yana fad'in.
“Please kayi hkr karki saka damuwa tamin yawa, insha Allahu zata farka ayau d'in nan, d'auki wayana kira Dr yazo yanzu please kafin Aminu su iso d'aukarta.”
Ya k'arashe maganar yana kwantar da Ummulkhairi, ya shiga muraza tafin hannunta da sauri-sauri yana kiran sunanta.
Bilkisu cikin rawar jiki cikin wayoyinsa ta d'auki gudu ta kunna sabida ya kashesu.
Tana kunuwa ta cire password d'in ta lalubo number Dr Safwan ta kirasa.
Cikin sa'a bugu d'aya d'aga.
Beqawa Shattima wayan tayi, ya amsa bayan sun gaisa ya ce.
“Dr Baby ba lfy tayi suman nata please kayi sauri kazo ajaraba agida muga ko za'ayi sa'a ta farfad'o yanzu.”
Dr Safwan ya amsa cikin mutuntaka sukayi sallama ya katse kiran, ko ajiye wayan baiyi ba kiran commissioner Aminu ya shigo.
Idanunsa ya k'urama wayan ya kasa d'aga kiran...
_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha me sunanki.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 5&6*


Hannunsa mai riqe da wayan, Bilkisu ta riqe tana d'ora yatsarta akan setin inda za'ayi piking call d'in.
Cikin kwantar da murya ta ce.
“Mi amor don Allah ka amsa su da kansu sun san dole idan taji labarin abinda ya faru, sai ta shiga wannan halin.”
Ta k'arashe maganar tana picking call d'in, tare da kai masa wayan kunnen shi.
Anutse yama Aminu sallama.
Daga can commissioner Aminu ya amsa tare da fad'in.
Gamu nan ahanya ashirya mana 'yar mu.”
Murmushi Shattima ya yi ya ce.
“Please nima tinda d'ana ne za'a Kai wa ita, toh abarni na kawota, gata kwance ba rai tinda taji abinda yake faruwa, Dr muke jira ya dubata.”
Aminu ya ce.
“Subahanalahi wlh daman nasan hakan sai ta faru, tayi haquri haka Allah ya k'addara, OK toh bari mukoma sai kunzo, Allah ya bata lfy dan Allah idan yau d'in tace bazata zoba, karku takura ta, abarta zuwa goben ta huta ko zuwa dare ne please.”
Sosai minister Shattima ya ji dad'in maganar aminin nasa ya amsa da.
“Ok insha Allah.”
Sallama sukayi ya kalli Bilkisu wacce take famar zubar da hawaye, ya girgiza mata kai, yana cigaba da murza hannun Khairy, tare da kiran sunanta.
15 minutes Dr Safwan ya iso Shattima ya masa iso har falon.
Cikin gaggawa ya fito da kayan da zai bata taimakon gaggawa.
Cikin ikon Allah kuwa, ba jimawa ta farfad'o tare fashewa da kuka tana kiran Salim.
Shattima ya ce.
“Dr! Abu mafi sauqi had'a alluran bacci banka mata, bazan jure wannan tashin hankalin ba...”
Qafafun Shattima ta riqe tana wani irin kuka tare da roqon shi.
“Dady! Don Sonka da ma'aikin Allah ka raba auren nan na auri Salim, wlh yana sona shima...”
Bakinta ya rufe mata yana rungumeta yama Dr nuni ya mata alluran.
Ai kuwa take cikin dubara ya tsira mata allurar.
Tana ji amman yanayin tashin hankalin da take ciki, ya hanata nuna taji zafin allura, kanta kawai take bugawa a k'irjin Shattima tana kiran Salim.
Bata rufe minti biyar ba sai bacci.
Bayan Dr ya tafi ya gyara mata kwanciya saman sofa, yana kallon Bilkisu ya ce.
“Kije ki sallami 'yan rakiyar amarya kice na kaita da kaina suyi haquri, zan kai miki ita yanzu b'angaranki.”
Bilkisu ta amsa da.
“Toh.”
Tana share hawayen tausayin tilon 'yarta.
Can a falon kuwa cike da jama'a anata hira su auntie Balaraba, Maryam Suhailat babbar k'awa.
Bilkisu na shigowa auntie Balaraba ta miqe ta ce.
“Toh ku tashi muje Dady amarya ya gama da ita, ko auntie Billy? ”
Murmushi Bilkisu tayi ta ce
“Ai kuwa dai 'yan rakiyar amarya Dadynta dai ya tafi da ita, ya barku da jira, sai kuyi haquri Suhailat! Maryam! Bari na saka amaryar daku gida da sauran k'awayenku.”
Ta k'arashe maganar tana latsa wayanta, bugu biyu aka d'aga, ta ce.
“Yawwa dan Allah amayar da k'awayen amarya, kowace akaita har gate d'in gidansu.”
Balaraba ta ce.
“Kai amman brother ya gama damu kawai ya tafi yakai 'yarsa muna nan zaune, ai kam sai ku tashi mu fece.”
Ta fad'a tana yafa mayafinta.
Maryam ta maqale kafad'a ta ce.
“Mamy ni dai ki kira Ammi kice mata nan zan kwana please. ”
Bilkisu ta ce.
“Ok daughter shi kenan kuwa na riqe ki sai kinmin kwana biyu.”
Dariya 'yan falon sukayi, nan masu tafiya sukayi haramar tafiya baqi na 'yan zuwa wajan biki kuma kowa ya nufi makwancin sa, Bilkisu taja Maryam suka haye stairs, ta kaita d'akin Ummulkhairi.
Sai da minster Shattima ya ji gidan tsit kowa ya Kama makwancin sa, ya ciccib'i Ummulkhairi ya nufi b'angaran Bilkisu da ita.
Bilkisu na kwance cikin shirin bacci taji sallamarsa, daman k'ofar karota ne tayi sbd zuwansa.
Sallamar ta amsa tana miqewa zaune tana kallonsa tana gyara hular kanta.
Dab da ita ya kwantar da Khairy, yana fad'in.
“Sweetheart kiyi dubara ki cire mata kanyan jikinta, sai ki saka mata na barci marasa nauyi, dan wannan ko ta farka sai zuwa safe, good night Allah bamu alkhiari sweetheart. ”
Ya k'arashe maganar yana kamo fuskarta ya sumbaci labb'anta ya shafi gefen fuskarta ya juya ya nufi k'ofa yana zura hannayensa cikin aljihun wandonsa.
“Ok night mi amor ka kularmin da kanka, I miss you. ”
Murmushi yay ya janyo musu qofar.

*Asokoro*
Salim tinda ya dawo d'akinsa bayan tafiyar Abdulrazaq ya rufe k'ofarsa, bugun duniya alhaji Hashim yayi yaqi bud'ewa kuka kawai yake kamar qaramin yaro yana kiran Ummulkhairi.
Tsaye yake yana kai komo ya saqa wannan ya kwance wannan, ya rasa hanyar da zaibi ya samu ganin Ummulkhairi sabida kaf wayoyinsa an b'oye shi kuma zuciya ta hana shi tambayar su.
K'ofar ya ji ana tab'awa, ya kalli wajan ya kauda idanunsa, ya koma kan kujera ya zauna, ya d'auki sigari ya kunna ya zuqa ya fesar da hayaqin ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya, yana girgizawa ya zubama k'ofar idanu jin ana yanke qofar.
Alhaji Hashim ya iso ransa b'ace ya d'auke shi da mari ya rufeshi da masifa.
“Dan ubanka ni zaka d'auka d'an iska? Sbd inason ginama rayuwarka, shine kake shamin taba agida?”
Murmushi yay ya ce.
“Wai kana son ginamin rayuwa humm kuna son lalatamin rayuwa dai, tinda kun haramtamin abinda nakeso, ina wayoyina?”
Alhaji Hashim ya saki baki yana kallon Salim,tsabar takaici kasa magana yayi ya wurga masa wayoyinsa biyu ya wuce yabar d'akin.
Cikin rawar jiki ya d'auki wayan ya shiga ma'adanar lambobinsa, amman wayam yaga ba sunan kowa sai na Umma da Father da Aliyah layinma sabone.
Allah yasa yanada number Ummulkhairi akansa.
Loda number yay ya danna mata kira.
Wayan na wajan Shattima.
Ganin number ba suna ya d'aga yana jin muryan mai kiran, ba b'ata lokaci bai ko tsaya kashe wayan ba, ya ciro layin daman da Sim d'aya take anfani ya jefasa bakinsa ya taune ya shafe komai na kan wayan.
Salim kamar zaiyi hauka ya loda number Abdurrazaq.
Bugu biyu ya d'aga ko magana baiyi ba,Salim ya ce.
“Don Allah Salim ka samomin number Abdoul Aminu.”
Abdulrazaq dan kar aja magana ya ce.
“Ok ba damuwa za'a samo,ka canza layine?”
Katse kiran yayi bai tanka ba, yayi jifa da wayan, ya kunna sigari ya zuqa.

Misalin qarfe biyu na dare.
Unguwar _(Galadanci)._
Gida ne mai kyau da tsari Masha Allah.
Liman Umar zaune a bedroom d'insa, saman darduma sanye cikin fararen kaya,sai k'amshi yake casbi ne k'ato ahannunsa yanata ja.
Har yanzu lamarin auren Ummulkhairi na d'aure masa kai, ya jira Shattima ko zai kirasa ya masa bayani shiru bai kirasa ba, haka ya jira ya ji ko inno matarsa zata ce wani abun tinda can suka wuni amman shiru.
“Allah ya kyauta, bari na Kira

Please Login or Register in order to submit comment