Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙaramin tables ɗin glass da yake gefe ya, duƙa ya sumbaci bakinta ya janye Duvet ɗin ya shafi cikinta, ya sunkaya kansa ya sumbaci cikin, ya karanto addu'a ya tofa a cikin ya shafe cikin zuwa marata, ya lulluɓeta ya juya ya fita yana rufo mata ƙofar.

Ƙofar falonsa ya murza key, ya kashe ƙwan wutar falon ya nufi Bedroom.
Tana naɗe cikin tattasan bargon da ta zabo masa cikin tarin kalolin bargunan.
Murmushi ya yi yana shiga bathroom.
Wanka ya sake ya fito ɗaure da towel, yana goge jikinsa.
Khairy batasan wainar da yake toyawa ba, sabida bacci ya ɗauketa.
Anutse ya shirya cikin shirin bacci ya ɗora jallabiya saman kayansa, ya gabatar da sallah nafila raka'a biyu yau bacci yakeji da gajiya yasan bazai iya tashin cikin dareba.
Koda ya idar ya jima yana addu'a kafin ya miƙe ya cire jallabiyar ya rage hasken ɗakin ya hauro saman bed ɗin.

Cikin tattasan bargon ya shige tare da tattarota cikin jikinsa, yana mata kyakkyawar runguma tare da sauke ajiyar zuciya.
Sake shige jikinsa ta yi tana sanya hannunta ƙugunsa, cikin baccin.
Anutse yake shafa bayanta bakinsa kan kunnenta, cikin wata irin murya ya kirata.
"My Baby! Oya buɗe idanunki faɗa min me ya sakaki kuka kafin mu iso Jigawa?"
Ya faɗa yana kissing kunnenta tare da ɓoyeta cikin ƙirjinsa.
Cikin bacci ta turo baki tana faɗin.
"Wayyo Dadynah bacci da safe zan faɗa maka.."
Hannunsa ya zura cikin rigarta iya cikinta yana shafawa, yana lasar fatar kunnenta, yana hura mata iska yace.
"No! My Baby sai kin faɗa min."
Kukan shagwaɓa ta sakar masa tana ƙara laɓewa jikinsa tace.
"My Dady love, i love U kai sai ka hanani bacci Don Allah. Toh daman basu Azizah wannan budurwa ta Abdoul, da Salim wai suka siyi wata ta saceni ta kaina can wajansu dan su cutar dani...."

Kakaf ta zayyane masa komai, cikin baccin da yake cinta, har taimakon da take son tama Kausar.
Da wani irin sauri ya janye bargon ya ɗagota ya rungume yana kallonta yace.
"Baby ba abinda suka miki kin tabbatar ko yatsarki basu cutar min ba?"
Wartsakewa ta yi tana kama kafaɗunsa tace.
"Allah Dady love ka tambayi Abba Aminu, ai suna wajansa ana gana musu azaba, da farko banso ka saniba bana son ka sani daga zuwanka shine nace Abba kar ya faɗa ma."
Shattima yana shafa fuskarta ya sumbata yace.
"My baby naji daɗi da wani abun bai sameki ba, da wani abun ya sameki da bazan yafewa kaina ba, muahhhh i love You ƴar yarinyata."
Kanta ta kwantar ƙirjinsa tana murmushi tana jin wata kalar irin nutsuwa na saukar mata, ashagwaɓe tace.
"Dadynah madubin dubawata Ni kai nayi dubawa, ALLAH my Dady Ina sonka dayawa kamar ma na koma cikinka."
Ta faɗa ashagwaɓe tana ƙanƙameshi fuskarta na gugar sajansa.
Shattima ya lashi bakinta yana wani kanainayeta tare da bata dukkan kulawarsa, ya ɗora bakinsa akan nata can ƙasa yace.
"ALLAH nima ina son Ummulkhairi nah, Babytah, kamar na haɗiye abata na huta, kin shirya zama da Dadynki matsayin miji a fara shirin biki uhm my Baby?"
Lips ɗinsa take lasa tana murmushi ta ɗaga masa kanta, sau uku alamar ta shirya zama da shi.
Murmushi mai bala'in narka zuciya ya saki bakinsa kan nata, ya hura mata iskar bakinsa.
Ta sauke numfashi ashagwaɓe tace.
"Dadynah!"
Bai amsa ba, ya watsa mata zazzafar sumbata tsakiyar bakinta, yana laso gefe² bakinta, ya janye bakinsa anata yana rungumeta gam ya lulluɓesu da tattausan bargo, yana shafa kanta.
Lamo tayi jikinsa zuciyarta nata matsanancin bugawa, sai ƙanƙameshi take kamar me jin sanyi, can ƙasa kamar zata fashe da kuka tace.
Sweet Dadynah please ka barni na tafi ɗakina wlh hankalina bai kwanta ba anan."
Murmushi ya yi yana janyeta jikinsa dan shima yana gudun zuwa Anjima ya gaza jurewa ya fara kai hannunsa manyan gurare ajikinta, hakan ya saka,, ya sauka ya beƙa mata hannayensa ta kama ya ɗauketa yana goyata sai kace Baby ta saki dariya tana shafa kansa tace.
"Dady love masoyina abun alfahari Nah."
"My baby kiyi shiru Please karki ja magana yanzun Ok?"

Shiru tayi tana kwantar da kanta gadon bayansa, tana shafa sumar kansa tana murmushi, duk duniya yau ji take tafi mata Sa'a da gata Dadynta abin sonta mijinta mai sonta.
Ahankali akunnensa ta raɗa masa.
"Wayyo Dadynah kwanaki inata haukan banza sai ka sakeni da na cuci kaina, ashe Mamy gata ta min taban miji me tsada, i love You Mamynah."

Ta faɗa tana sanyawa Shattima yatsa a kunnensa tana dariya.
Da sauri ya janye hannunta, yace.
"Wlh My Baby idan na koma bed dake da kuka zaki bar ɗakin nan fa kija bakinki nan me barazana ya zauna lafiya, Ok?"

Baki ta turo tana faɗin.
"Ni Ni toh ba abinda yake raina na faɗa tunda dai kai mijina ne ba wani ɓoye-ɓoye tunda muna son junanmu, kuma ai kai ka horeni kar nayi munafurci a komai na rayuwa na tsaya iya gaskiyata koh?"

Shattima ya furzar da iskar bakinsa me ɗaumi, yace.
"Yeah Baby hakane, Amman kiyi shiru kinji Babyn Dady."
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya tana wasa da sumar kansa.
Shiru ya mata ya buɗe ƙofar Bedroom ya fito
A falonsa taso ya sauketa ta tafi da ƙafafunta ya ƙi sai da ya kaita ƙofar Bedroom ɗinta ya ajiyeta, yana sumbatar bakinta da kumatunta, anutse yace.
"Ki fara shirin tafiya Abuja gobe Auntie Aisha zatazo jibi zaku wuce Ok Baby?"

Kai ta ɗaga tana shigewa ɗakinta tana turo masa baki tace.
"Good night sweet dreams my Dady bye I love you."
Ta faɗa tana rau-rau da idanunta, ta rufo ƙofar.
Murmushi ya saki yana juyawa ya nufi falonsa.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Aminu sun jima suna magana, kafin ya kashe wayoyinsa ya kwanta ɗakinsa dan yana son yabar Mamy ta huta sosai, sai dai abinda su Salim suka Khairynsa ya tsaye masa azuciya...
Maryam tanajin zuwan Khairy bacci bai ɗauke ta ba sai ta yi likimo kamar tana bacci.
Khairy ma bata bi ta kantaba ta shige bathroom, bata jimaba ta fito ta sauka downstairs, ta kira Nadiya suka kwanta suna hira, ba jimawa bacci ya ɗauke su har lokacin Maryam idanunta biyu, tana ba kanta ƙwarin guiwar zata iya haƙuri da Dady Shattima tunda baima san tana yiba, ga taga Khairy ba sauƙi...

★★★
Washegari
Mamy tun asuba da tayi sallah, ta sauka ta shiga kitchen dan girka musu abinda zasuyi breakfast.
Shattima yana dawowa daga masallaci, kitchen ya nufa sanin halinta.

Ai kuwa ita ɗaya tana fama ɗore_ɗore.
Ta bayanta ya rungumeta, yana shafa cikinta, ya sumbaci ƙasan wuyanta akunnenta ya furta.
"Good morning my sweetheart, ykk? Y bbyna? Hope kun tashi lfy? Jiya sai kika gudu ɗakinki kika kwanta koh?"
Ya ƙarashe maganar yana lasar cikin kunnenta.
"Aushhhh! Mi Amor ka bari, tsaya mu gaisa don ALLAH."
Ta faɗa tana zame wa daga jikinsa.
Sake rungumeta ya yi yana shafa kyakkyawar fuskarta, yace.
"Naƙi ahaka zamu gaisa, kuma wuce muje ba zakiyi girki ba."
Fuska ta ɓata tace.
"Ni dai se nayi Mi Amor, please ka barni, ina kwana? Ya gajiya?"
Ta faɗa tana shafa gemunsa, tare da tura yatsarta cikin ƙofar hancinsa guda, tana ɗaga masa gira ɗaya.
"Sweetheart harda mugunta Ngd, Ok bari na kama miki."
"Kai Mi Amor! Please kaje ka huta..."
Baki ya rufe mata yace.
"Matata zan taya aiki Oya mu fara, dame za'a mu fara?"
Ya tambayeta yana kafa mata kaifafan lumsassun fararen idanunsa."
Ƴar dariya ta yi tace.
"Toh fara da tea na Sanka da iya tea."
Hannun jallabiyarsa ya naɗe anutse yace.
"Ok gimbiyar mata an gama."
Murmushi ta yi tana kusansa atsaye tana kallonsa, ya ɗauraye tukunya ya tara ruwa ya kunna gas ya ɗora ya shiga haɗa kayan tea.
Mami ta shiga nata aikin tana kallonsa tana jin nutsuwa na saukar mata...


Usman da wuri ya iso Gumel wajan 10 na safe, saboda har da shi za'aje Jigawa sannu da zuwan Dady Shattima, yana zuwa kai tsaye gidan Yalwa ya tafi duba Karima.
Karima tunda sassafe taji mutuwar Shahida ba abinda ta fara kuka sai dukiyarta da take wajan Shahida dan haka ko sallah batayi ba ta tafi can gidan Shahida gidan akwai jama'a sosai.
Yadda taji ana faɗin mutuwarta taji tsoro sai ta kasa tambayar kuɗin taja bakinta ta yi gum tace har ayi sadakar uku.
Bayan anyi jana'izar Shahida Karima ta tafiyarta gida, sabida yanayin jikinta da yake saɓa ga wani wari da take wanda ita bata jinsa.
Bata jima da zuwa ba Usman ya iso.
Tunda ya shigo take surfa masa masifa, kansa ƙasa baice uffan.
"Ashe Usman haka ka zama ɗan iska ban saniba? Nadiyar ce aka turata wajan shegiyar yarinyar can koh? Toh wlh ka wuce ayau kaje ka kawota nan wajena zaka kawo idan ka wuce da ita gidanku ban yafe ba..."

Idanunsa ya zaro yana kallonta cike da mamaki ya Nadiya zata iya zama anan?
Dan su rabu lafiya, yace.
"Ok za'a kawota.
Usman yana shirin miƙewa ya ajiyema Karima kuɗi masu yawa, ƙoƙarin ɓoye aman da yake taso masa yake, sabida warin da Karima take.
Maganar YANKAN WUƘA sukaji tare da shigowa yana faɗin.
"Gafaraku dai masu gida..."

Karima ta miƙe tsaye tana zazzaro idanunta tace.
"Uban me kake nema anan gidan da baza bari Ni najeba idan ina buƙatar wani abun, sai ka min tonon silili? Me kake nema nace?"
Kai tsaye yace.
"Aurenki na rufa miki asiri, kai yaro yimata bayani, ko yanzu ta yi abinda yafi nada muni, ba'a ja dani..."

Real Ladingo Omu Farisah

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 30/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*99*


Usman hankalinsa tashe ya kalli YANKAN WUƘA, yace.
A'a don Allah duk abin bai kai nan ba, kayi haƙuri yanzu zan mata bayanin komai, ita ma in sha Allah bazata ƙi amincewa ba! Mom! Wannan shine wanda ya temakeki, ya bada magungunan gargajiya har kika warke da ga mummunan ciwon da ya kamaki..."
Tsaf ya zayyane mata komai duk irin abubuwan da ya faru da ita, da taimakon da ya mata, ya ɗora cewa.

"Mom kinji abunda ya faru, toh alokacin yace bazai faɗi ladan aikin ba, sai kin warke zai faɗa, sabida munga kina mawuyacin hali, muka amince duk da bamu san meye zai nema ba daga baya, don ALLAH Mom ki amincewa aurensa dan tsira da lafiyarki."
Ya ƙarashe maganan yana kallon YANKAN WUƘA, yace.
"Don Allah kayi haƙuri kar wani abun ya sameta, zata amince in Sha ALLAHU.."

Karima cikin ɓacin rai ta wanke Usman da mari tana faɗin.
"Dan ubanka kasan waye shi ɗin zaka ce na auresa? Har nayi lalacewar da zan auri la'anannan ALLAH, ƙasurgumin boka? Allah ya kiyaye ya sawwaƙa da na auresa gwara na ƙarasa rayuwata haka wlh..."
YANKAN WUƘA ya sheƙe da dariya yana tafa hannayensa, yace.
"La'anannu dai koh Karima, toh shi kenan tunda kince haka zaki gani kuwa.."

Ya ƙarashe maganan yana juyawa zai tafi.
Usman yay wani irin tsalle ya riƙo rigarsa yace.
"Kayi haƙuri zan saka ta amince ka bani kwana biyu na maka alƙawarin hakan, kayi hkr ɓacin raine yasa ta kiraka boka, zatonta kai boka ne."
YANKAN WUƘA yace.
"Kai Kanada hankali kaje na baka kwana uku, idan ba amsa me kyau na rantse maka sai mujiya ta fita daraja cikin al'umma.."

Karima ta lailayo wani irin ɗanyan zagi irin na maguzawa ta afkawa YANKAN WUƘA, tana huci tare da ɗaukan Buta cike da ruwa, ta jefa masa tana masa zagi tana faɗin.
"Ina baka maidani angulu ba Allah ya tsinewa uwar da ta haifi uwarka albarka, kai Usman idan YANKAN WUƘA ba boka bane ubanka be..?"

Yalwa ta rufe mata baki tana janta ɗakin da suka ware mata, tana jin tashin zuciya.
Usman yaja YANKAN WUƘA waje yana basa haƙuri akan abinda Karima ta masa.
Dariya ya yi yace.
"Ka barta daga yanzu ta gama ƙin auren dani take magana, Nizata yiwa butulci."
Usman yace.

"A'a baza'ayi haka ba, kaban kwana uku in Sha Allah zata amince."
YANKAN WUƘA baice komai ba, yasa kai ya tafi.
Usman yana shigowa gidan ya yi tiris ya tsaya yana kallon Karima Yalwa ta riƙe ya tana kelaya amai.
Cikin damuwa yace.
"Yalwa me ya sameta, yanzu²?"
Yalwa tace.
"Wlh kaga yanzu tace tanajin jiri kanta na juyawa kaga sai amai take jikinta ya ɗauki zafi sosai."
Usman ya bata ruwa ta wanke fuskarta yace.
"Muje hospital a dubaki, abaki magani."
Karima yadda lokaci ɗaya take ji ajikinta bata musaba, Yalwa ta bata mayafi ta yafa Usman ya kama hannunta suka fita.

Suna zuwa asibiti aka amsheta, likita ta fara mata tambayoyi tana amsawa, ɗaya bayan ɗaya.
Gwaji kala uku suka mata, aka mata allurai guda biyu.
Bayan 45 minutes result ya fito.
Karima sosai ta shiga tashin hankali matuƙa, da karfi tace.
"Na shiga uku! ciki kuma?"
Likita tace.
"Abun alkhairi harda shiga uku? Meye na damuwar dan kinada ciki? Ai baki wuce haihuwa ba, idan Allah yaso hakan, kamar yadda yanzun ta faru."

Usman tunda ya karanta yaga Karima nada shigar ciki wata biyu ba kwana biyu cif.
Bai de ce komai ba, ya siyi duk magungunan da aka rubuta masa suka taho.
Ahanya yace.
"Mom! Banji daɗin cikin nan ba sam wlh, ai yanzu kin wuce ma haihuwan ana ganin, amman bawa baya wuce ƙaddarasa, Allah ya saukeki lafiya Amin."
Karima kuka take cike da tashin hankali tsoro ya cika ta tasan watan tonon asirinta ya kama.
Wata irin nadama ta shigeta tsofai-tsofai da ita da ciki, bayan haka ma Mustapha ya kusa wata bai kusanceta ba suka rabu ya za'ace ciki wata biyu ba kwana biyu, kenan sau ɗayan da ta yarda da YANKAN WUƘA har ciki ya shiga? Duk duniya ba wanda zai yarda sau ɗaya tak tayi zina arayuwarta amman ga shi ciki ya shiga.

(Dan kusantarta da YANKAN WUƘA yake na baya bata hayyacinta bata saniba lokacin tana haukan aljani na kai masa ita yana abinda yake so da ita.)

Fashewa ta yi da kuka tana faice majina.
Usman da yake baisan matsalar ba, lallaɓata ya yi, ya tsaya hanya ya siya mata Lemo da su Ayba Tufa, ya ajiyeta agida yana ƙara kwantar mata da hankali, kafin ya wuce can gidansu, sam ta manta da result ɗin cikinta ya tafi da ita.

Usman yana zuwa ya isko Dad Mustapah da Zainabu sun shirya, shi suke jira sabida ba kwana zasuyi ba.
Bayan ya gaishesu cikin girmamawa, Zainabu ta kawoma kayan breakfast yaci kaɗan, ya fuskanci Dad Mustapah yace.
"Dad albishirinki?"
Zainabu wacce ta haɗe cikin wata tsadaddiyar atamfa, bazaka taɓa cewa ita ta haifi Khairy ba, ta kalleshi tana murmushi aranta tana faɗin.
"ALLAH yasa yace ya samu matar aure nayi suruka."

Mustapha ya gyara zamansa yana ajiye wayansa tare da kallon ɗan nasa yana murmushi yace.
"Goro fari Usman suruka nayi ne?"
Usman yace.
"A'a Dad ƙaruwa dai aka samu, amshi ka duba kagani."
Ya ƙarashe maganan yana beƙa masa result ɗin hannunsa.
Dad Mustapah yana washe baki yace.
"Muga alkhairi."
Idanu ya ƙurama pepper, da farko wani irin faɗuwar gaba ya ji zai sake haɗa zuriya da Karima, amman ganin kwanakin cikin ai kusan sati biyu bai kusanceta ba, sabida tafiyar da ya yi koda ya dawo tana period, Koda ta idar kuma bai kai ga kusantarta ba, wannan matsalar ta Zainabu ta ɓullo.
Aransa yace.
"Allah tsinewa me irin halin Karima, ashe dai da gaske take tana bin maza ba hauka bane yasa ta faɗa ranan? Badan ƴaƴana dani suke kamaba da nasaka zargi akansu, sai dai Allah ya tufamin asiri, nawane wannan."
Azahiri kuma sai ya yi ƙoƙarin ɓuye ɓacin ransa da tsantsar tsanar Karima,
Cikin tausayin ɗan sa yace.
"Naga komai kaga yanzu tafiya gabanmu, zanje wajanta da kaina muyi magana idan mun dawo Ok?"
Usman yace.
"Tom Dad ba damuwa Allah ya ƙara girma na gode ban zaci zaka nuna farin cikin ka ba, sbd matsalar da ta gifta."
Kai ya girgiza yana kallon Zainabu yace.
"My Zeey kin shirya mu wuce?"
Kai ta jinjina tana murmushi.
Usman na fitowa, ya tura takardar aljihunsa, yana kama hannun matarsa suka biyo bayansa.

Suna baya shi ne ya musu direba, a motarsa suka tafi...

Acan Jigawa kuwa ko breakfast Maryam bata fito ba, saboda tana son nisanta kanta da Shattima daga yau, ta yi alkawarin hakan.
Khairy da Nadiya da Mamy Shattima sukayi breakfast ɗinsu anutse.
Ko kusa Khairy bata yarda ta kalli Shattima akan dining ba, da gudun kar shaukin sa ya kamata.
Shattima suna gama breakfast, bayan zuwan Abba Aminu da Ammi, ya shirya ya fita sabida yana meeting ba maganan zama da safen.
Maryam kuwa Tsaf cikin siyasa ta shirya zatabi iyayenta, Mamy ta hanata tace sai yamma zata saka akaita, dole ba yadda ta iya ta haƙura ta zauna.
Tunda garin Allah ya waye kuwa jama'a ƴan uwa da abokan arziƙi suke zuwa musu sannu da zuwa, dayawa sun samu ganin Shattima dayawa koda sukazo ya fita.
Shattima sun gama magana da Abba Aminu akan case ɗin su Azizah, Aminun yace ba ruwansa ya saka musu idanu, shi zai magance komai.
Shattima ba karamin farin ciki Commissioner Aminu ya saka shi ba.

Khairy da kanta take shirya girkin tarbar Auntie Aisha dasu Zainabu, ta hana Mamy taɓa komai, haka ya saka Mamy ta haye saman beni tana baccinta ɓangaren Shattima.


Misalin 12:30 na rana su Usman suka shigo Jigawa.
Khairy lokacin basu kammala girki ba ita da Laraba da Nadiya, da Maryam wadda ta dake ta saki jikinta, suna aikin tare.
Tana jin ƙaran doorbell ta wanke hannunta ta fito daga kitchen sanye take da riga da zani na tamafa tayi ɗaurin yoroba, rigar ta ɗaureta cikin zanin, kanta ba ɗankwali tayi wani kyau duk da ba kwalliya fuskarta, sai lisp ɗinta ta shafa lipstick.
Tana buɗe wa tayi ido huɗu da Zainabu.
Cikin farin ciki tayi tsalle ta rungume Zainabu tana faɗin.
"Oyoyo Umma, ina yaya Usman da Dad?"
Zainabu ta rungume ƴarta cikin farin cikin ganinta tana buga bayanta.
Khairy ashagwaɓe tace.
"Umma! Ina su Dad Wai?"
Zainabu tana murmushi taja dogon hancin Khairy, tana kama hannun Khairy suka nufi compound ɗin gidan.
Khairy taja ta tsaya jikin wasu shukar flowers masu kyau, tace.
"Umma kin manta inada aure gidan cike da ma'aikata ko mayafi babu ajikina wlh idan Dad ya gani faɗa zai min?"
Zainabu ta dafe kanta tana mata nuni da hannun sam ta manta farin cikin ganinta ya mantar da ita.
Khairy ta gane abinda take faɗa tace.
"Lah! Wai suka tsaya ƙofa? Dadynah yace kar a sauke ku falon baƙi a saukeku nan babban falonmu fa! Umma! Kije kice su shigo."

Zainabu ta jinjina kanta.
Khairy tana tsaye anan tana jiransu.
Tana hangosu da gudu ta nufi wajansu tana faɗin.
"Oyoyo Dad Yaya Usman."
Dad ɗinta ta rungume tana dariya.
Dad Mustapah yace.
"Oh! Ni kam karki kayar dani wannan ɗiyar ta Shattima."
Khairy ta sake shi tana dariya ta kamo hannun Usman tana faɗin.
"Ya Usman sannu da zuwa ya gajiya?"
Murmushi ya yi yana jan hancinta yace.
"Ba gajiya Khairy, hope kina lfy?'
Dariya ta yi tace.
"Wlh Alhamdulillah Ya Usman..."
Har cikin falon ta kawosu suka zauna ta nufi kitchen tana mai farin ciki.

Ta kalli Nadiya da Maryam tace.
"Gasu Dad can sun shigo, kunga wlh Tsaf sunyi kyau abinsu."
Nadiya cikin farin ciki ta wanke hannunta ta fita.
Maryam ta amshi tryan da Khairy ta jera lemo da ruwa tace.
"Toh kawo na kai musu sai na gaishesu daga can."
Khairy ta bata tana murmushi tace.
"Yawwa Ni sai na ƙarasa aikin."
Maryam tace.
"A'a zan dawo Auntie."

Nadiya tana kusan Zainabu zaune cikin farin cikin ganinsu, Dad Mustapah yana waya da Shattima akan sun iso.
Maryam da sansanyan muryata ta yi sallama tun daga nesa.
Usman da yakewa Nadiya magana ya ɗago da kansa yana kallon ɓangaren da yaji zazzaƙar murya na fitowa.
Cikin Sa'a anyi katari tana kallon, tana mamakin kamarsa da Nadiya da Khairy, wani irin faɗuwar gaba Usman yaji, ya tsira mata idanunsa, bai taɓa ganin yarinyar da ta shiga ransa farat ɗaya ba irin wannan yarinyar, daga kallo ɗaya sonta ya shigesa.
Maryam kuwa kunya taji ganin ya kamata tana kallonsa, sai ta sadda kanta.
Dad da Nadiya suka amsa sallamar shi kam Usman an tafi duniyar masoya yana hasasota har ya sameta suna lambu soyayya suna baza ƙauna.

Dire tray akan Centre table, tana gaishesu tare da sannu da zuwa anutse ɗauki cup tana tsiyaya musu lemo da ruwa ta ajiyema kowa gabansa.
Zainabu ta yaba da hankalin yarinyar sosai.
Nadiya ta kalli Usman ta bushe da dariya tace.
"Umma dan ALLAH kalli yaya Usman."
Maryam da Zainabu atare suka kalleshi.
Maryam taji gabanta ya faɗi ganin irin kallon da yake mata yana murmushi.
Idanunta ta zaro tana miƙewa jikinta har wani ƴar rawa yake ta gudu kitchen.

Dad Mustapah yana shan lemon yace.
"Nadiya! Wannan yarinyar fa? Alamun dai yarona ya gani yana so."
Nadiya ta bugi cinyar Usman firgigit ya dawo hayyacinsa.
Zainabu da Nadiya dariya suke cike da farin cikin yau Usman yaga wacce tai masa.
Khairy ƙin taso Mamy ta yi tace ta huta.
Ƙarfe ɗaya da rabi Auntie Aisha ta iso Jigawa, sai da ta tsaya can gidansu ta yi sallah, suka ɗan taɓa jira da liman da Inno kafin ta nufo gidan Shattima.
Khairy lokacin ta tashi Mamy ta yi wanka ta yi sallah, tana cikin shirya ne Auntie Aisha ta iso gidan.

Shattima shima lokacin ya samu isowa gaisawa sukayi da Auntie Aisha dasu Dad ya haye sama domin watsa ruwa, zafi yakeji duk sanyin Ac'n falon.

Yana hawa Mamy na fitowa zata sauka.
Kallonta ya yi fuskar shi ɗauke da tsadaddan murmushi yana beƙa mata hannunsa.
Isowa ta yi tana shigewa jikinsa.
Rungumeta ya yi yana mata raɗa akunnenta yace.
"Please muje Sweetheart sharf-sharf da safe tausayi kawai kika ban bance miki komai ba, kinyin girki kin gaji yanzu kuma atakure nake marana ta ɗaure dayawa..."
Lisp ɗin sa ta shafa tana ƙara shigewa jikinsa tana jin gimbiyar na taɓota alamun ta fara haniniya.
Ɗan murmushi ta yi ƙasa² tana faɗin."
"Kai Mi Amor har kasa naji kunya kaida abunka meye na tambayar don ALLAH? toh muje ai nasan bazaka jimaba kodan baƙin da suke jiranmu."

Dariya Khairy sukaji tana sauka daga steps ɗin ƙarashe ganinsu manne da juna suna cikin raɗa, tace.
"Kai Allah su Sweet Dadynah da Mamynah an iya soyayya Ni kam da Maryam ko Nadiya ta ganemin ku fa?"

Ta faɗa tana zumɓuro baki gaba.

Shattima ya kalleta yana hararenta tare da sake rungume Mamy cikin zazzaƙar muryansa anutse yace.
"Baby! Kinata yawo kai ba ko ɗankwali ko hula bakya jin sanyi? yau kuma shigar yarabawa kikayi Baby?"
Ya ƙarashe maganan yana mata wani irin fitinannan kallo, wanda ya kusa sakata towana kanta asiri wajan Mamy har gashin jikinta yake mimmiƙewa, tayi dariya tana kallon Mamy da take mata murmushi tana yafitota da hannunta tazo wajansu.
Kafaɗa ta maƙale tana faɗin.

"Mamy kinji yadda nake ƙamshin girki wanka zanje nayi, nazo na ciki tumbina, yunwa nakeji sosai."
Ta faɗa tana nufar hanyar ɗakinta da wani irin sauri tana haɗawa da ɗan gudu tace.
"Mamy na miki kunun gyaɗa."
Mamy tace.
"WOW! Allah miki Albarka Baby."
Shattima ya kama hannunta suka nufi sashensa.
Tun a falon bayan ya murza key ya shiga cire mata kayan jikinta, ya ɗauke ta suka shige bedroom.
Itama kayansa ta cire masa suka yada zango akan tafkeken Italian bed ɗinsa, ya fara aika mata zafafan saƙonni, yana cakuɗata cikin wani irin ƙwarewa tana taimaka masa, kafin su tafi babban birnin inda yau abun ba'a magana abinka da me sabon ciki da baiwa ga irin gyaran da Mamy ta yiwa kanta, a Makka duk da bata yarda tasha abinda me ciki bata sha wanda zai iya cutar da ita.
Shattima kamar zai mata, yau har ta gaji da tambayoyinsa da saka mata albarka dole ta haɗe bakinsu tana shan harshensa, har zuwa lokacin da suka gamsar da junansu ɗari bisa ɗari.
Basu saniba abun ya ɗauke su lokaci sosai.
Bayan sunyi wanka sun shirya Mamy kunya ta cikata kamar zatayi kuka tace.

"Mi Amor! Munyi abun kunya, gida cike da baƙi munzo muna raya sunna.."
Bakinta ya sumbata, yana shafa cikinta yanajin wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali, tare da wani irin sanyi na ratsa sassan jikinsa, ya kama hannunta, anutse yace.
"Muje Sweetheart aikin lada mukayi, Saudiya ibada ta hana mu ganawa har muka dawo, jiya kin gaji na miki uzuri"
Ƴar dariya ta yi tana shafa fuskar shi.

Ɓangaren Khairy kuwa tana shiga Bedroom ɗinta ta cire kayan jikinta ta shige bathroom.
Shower ta sakar kanta tana sauke numfashi, idanunta sai hasko mata Dadynah da Mamynta yake, sai ta sauke numfashi ta yi murmushi can ƙasan zuciyarta tana jin wani abu sai tayi saurin faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Sai tayi murmushi tana goge ƙwallar idanunta.
Tana fitowa ta shafe jikinta da lotoin me taushi da ƙamshi, ta zaɓi cikin dogayen rigunan da Mamy ta kawo mata ta saka wata red mai masifar kyau, taji adon stones kamar hauka, ɗauka ɗan kwalin rigar ba karamin kyau ta yi ba.
Tana saukowa ƙasa taga basa nan basu fito ba.
Kusan Auntie Aisha ta zauna tana murmushi tace.
"Kai Mummy ai da sai azo da Ilham koh?"
Auntie Aisha tace.
"Ai gobe kuna tare acan Abujan dan da wuri zamu tafi, yau kam za'a tsayar da rana, bari zuwa dare zanga Mamynki, kafin ayi magana, ina ce shi kenan rigimar ta ƙare?"
Kai ta jinjina tace.
"Toh ni dai barimin zancan wani sa rana, Mummy bismillahrku abincin ya kammala."
Dukkansu suka hallara akan dining area.
Usman harda santi suna masa dariya, Zainabu ta yaba ma ƴarta, girkin ya yi daɗi.
Auntie Aisha tace.
"Ai in dai Ummulkhairi

Please Login or Register in order to submit comment