Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shigo d'ankita, sabida ya mata kashen rufe qofa tsoronsa yasa bata murza key ba.
Yana riqe da kazarsa aleda.
Zabura tayi ta zauna lokacin da da kunna k'wan wutar d'akinta.
Zabura tayi tana zama ta shiga rarraba idanu.
Bushewa yayi da dariya yace.
“Matsoraciya, ga kaza yau fa sam banajin mugunta ki godewa Allah, tashi kawai kici kaza muyi sallah yau kam harda nafila zamuyi banajin fitina ayau bansan abinda goben zatayi ba.”
Aliyah gabanta na tsananin fad'uwa ta sauko tana goge hawaye ta amshi kazar ta zauna ta fara ci kamar mad'aci haka takeji sau uku ta yaga ta miqe ta shiga bathroom ta wanke bakinta ta d'auro alwala ta fito.
Dariya Salim yayi ya d'auki kazar ya fita. Bai jimaba ya dawo sanye da jallabiya.
Raka'a biyu yajasu.
Aliyah kamar gumki ta zame masa sai yadda yayi da ita, tana jin zafi haka ta daure tana kukan zuciya,Salim kuwa jin wajan yasha gyara Salim sai aka nutsu Ana kwasar gara yana saqe-saqe aransa Anya ma zai saketa ko ya auri Khairyn???😂😂
★★★

*Katsina*
Dare mahutar bawa, kowane d'an Adam a irin wannan lokacin, ya kwanta haqarqarinsa domin hutawa, wasu bacci wasu lazimi daga kwance, wasu kuma charts sukeyi awaya, wasu kuma suna tsaye suna ibada domin neman kusanci ga Allah SWT.
Zainabu tsaye take a adaidai wannan lokacin tana ganawa da ubangijinta,tana kuka.

```'Yar uwa idan kinada buqata ki jaraba wannan addu'ar ki gani.
Idan kin kammala duk binda kike kinzo kwanciya bacci, ki tsaya tsaye ki kalli gabas Ki karanta Qulhuwallahu Ahad qafa Tara Sai Ki fad'i buqatarki.
Sai ki juya ki kalli yamma ki karanta qafa tara sai ki fad'i buqatarki sannaan ki kuma juyawa kudu kiyi haka ki koma Arewa kiyi hakan.
Sai ki kwanta ta b'angaren dama Sai Ki rufe ido Ki karanta qafa goma.
Amma Wannan qafa goman anaso duk qafa d'aya ka fad'i buqatarka.
Sannan anaso idan ka rufe idanunka ba'aso ka bud'e har bacci ya d'auke insha Allahu idan dai zuciyarka A tsarkake, bazakayi wata kana addu'ar nan ba ubangiji bai biya maka buqatunka ba, na alkahiri, koda baka samu wannan abun ba, da izinin Allah zai baka mafiyin wada ka nema.```

Zainabu sai da ta gama kakaf bayan tayi addu'ar bacci idanunta arufe, fuskar Mustapha kawai take gani, hawaye suka taru mata meyasa ta kasa manta shi duk irin cin mutuncin da ya mata? Tasan dai tsakaninsu ba aure saki uku ba mgnar komawa.

Adaidai wannan lokacin shima Alhaji Mustapah, ya kasa bacci yana juyi saman makeken gadonsa yana jin kamar akwai wani abu mai mahimmanci da ya rasa arayuwarsa, sai yaji abun kamar b'arin jikinsa ne.
Hajiya Karima bata qasar sai yakejin kamar ko rashinta ne, amman idan yayi tsai sai yaji Sam ba ita bace.
Tsaki yaja yana juyi tare da fad'in.
“Ya Allah! Ko meye wannan abun ka bayyana min shi dan alfarmar Nabiyi Rahamati.”
Amman ya kasa tashi yayi nafila, sabida an shashantar dashi wajan maida hankali yin ibadun nafila ta farillah ma sai yayi da gaske.

Mamy tana zaune a falo Maryam ta jima da yin bacci, bazata iya bacci ba sai taga zuwan mijinta.
Tv ta qurawa idanu CCTV camera.
Kamar amafarki ta hango megadi ya fito aguje, ya bud'e qaton gate d'in.
Lumtsumemiyar mota baqa wulik ta danno fara tana biye da ita.
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana kallo an bud'ema Shattima motar.
Dogayen baqaqen k'afafunsa masu taushi kamar na jarirai ya fara zarowa suna cikin rufaffan baqin takalmi mai shegen kyau da tsada.
Idanu ta kafa masa, lokacin da ya fito baki d'ayansa.
Sanye yake da shaddah fara qal mai wani irin walqiya, taci uban zubin zare blue, d'ikin tazarce ne.
“Tsarki ya tabbata ga Allah Minister Allah ya maka kyau da tsari ga kyan jiki, wa zai ce ya haifi Khairy...”
Baki ta rufe tana murmushi.
Kallon yadda yake takunsa mai nutsuwa take wani soja na biye da shi d'auke da qaraman trolley'n d'insa.
Tv'n ta kashe ta cire mayafin da ta d'aure kanta, kitsonta mai kyau qananu suka bayyana, riga da wando na bacci mai gashin mage pink colour.
Tanajin qarin door bell, ta nufi hanyar falon.
Tana bud'ewa ta fad'a jikinsa ta qanqameshi, cikin murnan ganinsa tace.
“Welcome back Mi Amor I miss u.”
Ta fad'a tana d'add'age ta hau qafafunsa tanason tsawonsu yazo d'aya.
Gane hakan ya riqo k'ugunta ya rankwafo daidai tsawonta yana sakar mata wani irin tsadaddan murmushi, yana mata kallon tsantsar k'auna.
Ji yayi ta manne bakinsu waje d'aya tana riqe kansa, ta fara kissing d'insa cike da iyawa cikin shaukinsa, take shan bakin NASA lungu da saqo.
Sosai ya riqo k'ugunta yana taimaka mata, idanunsa alumshe.
Bakinta ta zare bayan shud'ewar mintuna 5 tana maida numfashi tana kallon kyakkyawar fuskar shi.
Sama ya cirata ya shige falon.
Wani sansanyen qamshi da sanyin Ac ya shaqa take farin cikinsa ya qaru shiyasa yake bala'in son Bilkisu akwai tsafta da baiwa qamshi haqqinsa.
Akunne ta rad'a masa.
“Mi Amor! Akwatinka ban d'auko ba.”
Murmushi yay yana direta yay gaba bai cemata komai ba.
Kallonsa take har yamata nisa kafin ta juya ta janyo 'yar qaramar trolleyn ta rufe qofar.
Stairs ta haye, d'aure da towel ta isko shi, a tsararren bedroom d'insa.
Cikin sauri tashiga ta had'a masa ruwan wanka me d'umi.
Da taimakonta yayi wanka ta shiryasa cikin kayan baccin da yafi so riga da wando, wandon gajere mai taushi farare Tass.
Dakyar ta samu yaci abinci kad'an, ta had'oma coffee mai dad'i.
2 na dare suka kwanta.
Bai yarda yayi bacci ba sai da ya saukewa Mamy haqqinta cikin tsantsar soyayya ya sarrafata cike k'warewa da salonsa ya bida ita, har ta kusa zauce masa, sabida yadda yake nuna mata ita d'aya ce aduniyarsa, bai barta ba sai da ya tabbatar ta gamsu d'ari bisa d'ari ya barta,sabida yasan kowace mace mai lafiya tsawon kwana 11 zata buqaci d'a namiji.
Bayan sun tsaftace jikinsu suna manne da juna lullub'e cikin blanket, Mamy ta masa rad'a akunnensa.
“Mijina! Bani labarin Babynmu tama rigima koh?”
Shattima ya sumbaci goshinta, ahankali ya furta.
“Dole ai sweetheart uba ai ba wasa ba 3 months bataga Dady ba.”
Mamy shafi k'irjinsa mai yalwar gashi tace.
“I love you Mi Amor muyi bacci.”
Marata ya shafo yana lumshe idanu sbd baccin da yake ji tare da tsantsar gajiyar da ya kwaso yau....
★★★
Kwance tashi yau Kahiry ta fita daga takaba anasu lissafin.😂
Ashee Liman na lissafi k'udirinsa na nan manne aransa, dan tin ranan da Mamy ta basa labarin komai bai tab'a fashin sallar tsakiyar dare ba akan batun auren idan da alkahiri Allah ya tabbatar,ya sakawa kowa son abun azuciaya,har shi Allah yasa komai ya kasance cikin sauqi ya bayyana iyayan Khairy, Allah bata jure d'aukan k'addarata.

Yau ta Kama juma'a.

_*Khairy clinic and maternity*_

Mamy yau bata samu tafiya gida A 12 kamar kullun yadda ta Saba ran juma'a, sabida tarin jama'ar da ita ce take dubasu amatsayinta na babbar doctor na asibitin ta, sam batason katse wasu tace sai Monday, sabida batasan irin yadda mutum yake ji ba.
Sai da ta gama duba kakaf jama'ar da suke jiranta, ta sallami kowa wajan mutum 5 taba gado wasu kuma magani ta d'orasu akai idan baiyi ba amusu operations.
Da sassarfa ta fito daga toilet tana sharce ruwan fukarta.
Ta d'aga kyawawan idanunta wanda suka nuna tsantsar gajiya da yunwa, ta kalli agogon da yake manne jikin bangon office d'in nata taga 2:20pm.
“Ya Rabbi! Astagafirullah ya Allah.”
Ta fad'a tana tana d'aukan darduma ta shimfid'a tana saka hijib.
Tana shirin gyara tsayuwar sallah wayanta ta d'auko ringing.
K'in kallonta tayi ta tayar da salla.
Koda ta idar sai da tayi addu'o'inta tsaf ta shaf, ta miqe wanda kiran shine na 6.
Idanunta suka sauka akan lambar Baffa Liman.
Haka kawai taji gabanta yayi masifar fad'uwa.
Da sauri ta d'auki wayan da take akan table.
Sallama tayi cikin sanyin murya.
Liman ya amsa yana fad'in.
“Bilkisu! Lfy inata Kira bana samunki?”
Mamy ta saita nutauwarta sabida yadda zuciyarta take bugun tara-tara, tace.
“Ina Sallah Baffa a hospital nake ban samu komawa gida ba jama'a sukayi yawa, sai yanzu na samu kaina.”
Liman yace.
“Masha Allah, sannu Allah ya k'ara dafa miki ya miki albarka. Bilkisu na ciki miki burinki d'azu bayan sallar juma an d'aura auren Shattima da Ummulkhairi cikin yarda Allah da shaidar dubban al'ummah...”

*YI WA KAI*

Free Novel

_October27/10/2022_

Afuwa jiya kun jini hiru mura😪🤧


*39&40*


“Ga sadakin Khairy awajena, kizo ki karba na cika miki burin ki had'a Shattima da Khairy aure, Bilkisu kiyi haquri ki qara haquri nasan ke kika matsa ayi auren nan,ko qaqa nan gaba akwai lokacin da zakiji kishi, sabida kishi halittane kuma dole zakiyi kishin mijinki tinda kina son shi.
Ina so ki riqe wannan sirrin har yakai lokacin da ya dace na had'a taro na bayyana shi, Aminu yarda Ce ta saka na amince ya zama alwalin Khairy shi d'in ubane gareta, sai dai ban fad'a masa Shattim ne mijin ba, sai nan gaba idan na kammala dukkan abinda ya dace na bayyana.
yanzu Zan Kira Aisha na fad'a mata karta kuskura tabar Ummulkhairi ta tsaya da saurayi, sannan idan fita ta kamasu tare taci gaba da sakata shiga irin ta Matar aure, kafin lokacin ta dawo hannunku yayi, Allah ya miki albarka Bilkisu.”
Mamy tinda Baffa ya fara rattabo mata bayanai, akan auren Khairy da Sahttima, ta dafe table ta runtse idanunta zuciyarta na matsanaicin bugawa, atake taji wata irin zufa tana tsattsafo mata agoshinta, baki d'aya duniyar taji tana juya mata.
Ji tyi yawun bakinta ya qam lokaci d'aya, ga maqoshinta na mata zafi, dak'yar ta saita nutsuwarta wajan fizgo numfashinta ta dake tace.
“Alhamdulillah Baffa mungode Allah ya saka da alkhairi ya qara muku lafiya da tsawon rai, mai anfani.”
Baffa ya amsa da.
“Amin Allah kema ya miki albarka ki riqe sirrin har lokacin da naga ya dace na fallashi, zanyi magana da Aisha da Shattiman akan nawa Khairy miji...”
Sallama sukayi liman yana katse kiran Mamy ta sulale nan qasa, tanajin wani irin kuka yana taso mata, ta dake ta Saki murmushi hawaye na tsiyaya saman fuskarta.
Miqewa tayi, ta d'auki Jakarta ta saka wayanta aciki, ta d'auki makullin motarta ta fito ta rufe office d'inta.
Duk Inda ta wuce gaisheta ake cikin girmamawa, tana amsawa fuskarta asake kamar ba ita bace yanzu ta shiga rud'ani.
Lafiyayyar motarta 'yar wulwula fara sal ta shige ta mata key ta nufi gate tana zuba horn, bata jira kiran direbanta ba.

Shattima wanda sam baisan abinda yake faruwa ba, yana zaune anan falon qasa, sanye da qananun kaya farare qal na shan iska, sai wani bala'in k'amshi yake, sanyin Ac da k'amshinsa and k'amshin falon suka had'e suka bada wani irin kalar k'amshi.
Waya yake anutse, da gani babban mutum yake magana da shi sabida yadda ya bada gaskiyarsa wajan mgnar kana gani kasan tanada mahimmanci.
Bai jima da shigowaba, yau baiyi sallar juma'a a Central Mosque ba, shiyasa bai san wainar da aka toya agame da aurensu shi da Khairyn.

Qaran doorbell da yaji ne ya miqe sanin idan yana nan, masu aikin basa fitowa ya miqe anutse yana amsa wayan yabi doguwar hanyar da zata sada shia da qofar falon.
Yana bud'e k'ofar ya kafa mata idanu yana karantar wani yanayi akan fuskarta.
Tattausan murmushi ta sakar masa tana shigewa jikinsa ta rungumeshi qam, tana cusa fuskarta tsakiyar k'irjinsa.
Hannunsa d'aya ya d'ora tsakiyar bayanta, ya matsota jikinsa sosai, ya rufe k'ofar yana murmushi, yace.
“Ok thank you so much sai jibin insha Allah, idan mun had'u wajan meeting. ”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran, ya zura wayan cikin aljihun wandonsa, ya d'ago da kanta ya riqe fuskarta da tafin hannunsa, ya zuba mata narkakkun idanunsa masu tsuma mata zuciya da gangar jiki.
Fuskar shi ya matso dab da tata yana shaqa mata numfashinsa, murya can qasa ya furta.
“Sweetheart! Ina kika biya? Ya dai? Me ya faru?”
Ya Kai k'arshen tambayar yana lasar fatar idanunta tare da sakar mata kiss agoshi.
Mamy ta sake shigewa jikinsa tana sauke wani irin numfashi.
“Uhmm! Yau kam sarauta akeji ne sweetheart? ”
Ya fad'a yana d'aukarta cak kamar baby damman abinka da siririyar mace ba wani nauyi, ya nufi falon, yana kallon yadda ta laf'e jikinsa idanunta a lumshe.
Kai tsaye kan dining area ya nufa da ita.
Zaunar da ita yay saman kujera.
Ya shiga bud'e warmes zaiyi serving d'inta, ta miqe tana 'yar siririyar dariya cike da so da k'auna ta rungume shi ta baya, ta riqe hannayensa tace.
“Mi Amor! Kawai tsokanarka nayi niya fa! Bari nayi serving d'inmu a plate d'aya. Gaskiya Mi Amor kayi kyau cikin k'ananun farin kayan nan, kamar na had'iyeka sabida sonka.”
Ta fad'a tana shafa k'irjinsa.
Ajiyar zuciya ya sauke yana juyo da ita suna facing juna.
Wani irin kallo yake mata hanayensa na shafa k'ugunta, yana nazartar ta tsaf ya gane tana cikin damuwa, b'oye masa take.
Tambayar taji kai tsaye ya jefo mata cikin sautin amon muryasa mai fitar sautin dad'i, yana tsattsareta da narkakkun idanunsa.
“My Billy! Me ke damunki? Me ya faru?”
Mamy tana murmushi ta shafi fuskarshi tace.
Allah ba komai Mi Amor sai alkhairi.”
Ta fad'a tana jansa ya zauna, ta d'auki spoon ta fara basa abaki, shima ya shiga bata. Haka suka ciyar da juna, cikin so da k'aunar juna, Shattima ya gama sanin Mamy nada damuwa ta b'oye masa ne.

Baffa liman yama inno bayanin komai akan auren Khairy da Shattima, yace taja bakinta tayi shiru har lokacin bayyanawa yayi.


Azizah zaune a rumfar shan iska ta gidansu, tayi tagumi tunanin Abdoul yaqi barin ruhinta $a gangar jikinta, da gaske tunaninsa yaqi barinta ta huta.
Hawayen da suke sintira akan fuskarta ta goge tana fad'in.
“Yanzu yaushe zan sake samun namiji kamar Abdoul? Wlh ina sonsa, mutuwa ta rabamu, Allah ya isa tsakanina da iyayansa da iyayan Ummulkhairi da ita Ummulkhairi kanta, duk mai hannu acikin wannan had'in auren da ya janyo nayi rashin masoyi babba. Wlh Khairy yadda kika hanani kwanciyar hankali nima sai na hanaki kwanciyar hankali..”
Ta fad'a tana miqewa ta nufi cikin gidan nasu...


*Abuja 9pm*
Auntie Aisha zaune cikin falo tana amsa waya, yayin da Ilham take tsefema Khairy kanta zasuje salon gobe.
Khairy idanu ta zubama Auntie Aishar jin da Baffa take magana.
Asanyaye tace.
“Mummy please kice ina gaishe da mai gidana da kishiyata inno.”
Auntie Aisha tace.
“Toh Baffa bari na keb'e d'in, ga amaryaka na gaisheka Baffa da inno ma.”
Baffa daga can yace.
“Toh ina amsawa agaisheta, Aisha! Inaso ki saurareni da kunnen basira, yau na d'aurawa Khairy aure da wanda ya dace idan lokacin kusan mijin yayi zaku sani ko Shattima ban fad'awa ba, yanzu ne na kirasa zan fad'a masa, dan haka karki barta tayi shigar da bata dace ba ta fita, ko ta tsaya zance da wani kina jina?”
Auntie Aisha da ta miqe ta koma ta zauna dab'as tana fad'in.
“Aure kuma Baffa? Toh da wa? Ita fa zawara ce sai nake ganin kamar ita ya kamata ta zab'i mijinta...”
Liman yay murmushi yace.
“Ni bazan tab'a cutar da jinina ba, ko Shattima bazai musamin ba bare ke wlh kika kuskura kika fad'a mata ko kika zugeta Zan baki mamaki mijinta kuma bazan fad'a ayanzun ba...”
Ganin Baffa ya fara fad'a ta Inda yake shiga batanan yake fita ba ta shiga basa haquri suka rabu lafiya.

Khairy tinda taji mgnar aure gabanta ya yanke ya fad'i, ta kafe Aisha da idanu har ta gamar wayan.
Kusanta ta dawo ta zauna cikin fad'uwar gaba tace.
“Mummy! Wai wacece aka d'aurawa aure?”
Auntie Aisha tace.
“Kai baki santaba cikin dangin Baffa ne na Garin Malam yace sunje d'aurin aure bayan juma'a.”
Khairy ta sauke ajiyar zuciya tace.
“Wlh gabana naji ya fad'i...”
Dariya auntie Aisha tayi tana fad'in.
“Matsoraciya kawai.”
Khairy tace.
“Mummy! Dan Allah ban waya na Kira Dady da Mamy nayi missing d'insu.”
Wayan ta beqa mata.
Cikin murna ta amsa ta nufi bedroom dan tayi hirata yadda take so.
Saman bed ta baje tayi dialing lambar Mamy.
Lokacin Mamy na zaune A falo cikin shirin fita tana jiran Shattima ya sauko.
Ganin lambar Auntie Aisha ce ta d'aga da sallama.
Khairy ta sakar mata ihu tana fad'in.
“I miss you sweet Mamy tah, ina yini?”
Mamy ta murmusa tace.
“Me too sweet daughter habibty, hope kina lfy?”
Khairy tace.
“Lfy lau Mamy sai kewarku ni dai kuzo ko d'aukeni Allah gida nakeso, ina Dadynah?”
Mamy tayi murmushi tace.
“Ok zamuzo ki kwantar da hankalinki dadynki yana sama shiri yake zamuje gidan Baffa.”
“Toh bari na kirasa Mamy goben zakuzo koh tinda weekend ne dan Allah kuzo Ku d'aukeni kafin Dady ya lula wata k'asar.”
Mamy tace.
“Wlh nidai ba ruwa da auntie Aisha fad'awa Dadynki, ki kirasa yanzu kiji naji yace sai bayan azumi zamuje mu kawoki ko auntie ta kawoki...”
Khairy ta sakar mata kukan shagwab'a tana fad'in.
“Bari na kira Dady na fad'a masa.”
Ta fad'a tana katse kiran.
Mamy tayi murmushi tana share hawayen fuskarta tayi saurin saita nutsuwarta.
Shattima tsaye a bedroom d'insa yana d'aura tsadaddan agogon silver, yayi bala'in kyau, sanye yake cikin wata lallausan farin boyel d'inki kamar dan shi aka qirqire shi a duniya, k'afafunsa sanye cikin takalmi na zallar fata,sai wani bala'in k'amshi yake hular ta zauna d'as akansa, idan ka kalleshi bazaka tab'a cewa yakai shekaru 40 bare 47 na haihuwarsa.
Yana gama d'aura agogon wayansa na d'aukan ruri.
Kallon wajan da ajiyeta yayi yana sosa sajansa ganin sunan Auntie Aisha ya saka shi d'auka ya d'aga wayan ba jinkirtawa, tare da sallama.
Yana manna wayan akunnensa kukanta ya bayyana cike da zallar shagwab'a, harda shasheqa.
Sajansa ya kuma shafa yana zama saman sofa ya d'ora dogayen k'afafunsa saman table ya jigina da bayansa da kujera ya lumshe idanunsa yana murmushi qasa-qasa.
Jin murmushin sa ya qara tinzira Khairy ta sake b'arkewa da kuka tana kiransa.
“Dady! Bazaka lallasheni ba?”
Shattima ya kyalkyale da dariya marar sauti mai bada wani irin sauti ahankali yana shafa sajansa, cikin sautin amon muryasa mai dad'i cike da nutsuwa da kamewarsa ya furta.
“Baby wai kiyi kukan kad'an sai na lallashi abata koh?”
Yadda yayi maganar yasa taji wani bala'in nutsuwa da sanyi azuciayrta batasan daliliba, Amman azhiri ta sake sakar masa kukan shagwab'ar tana harba k'afafunta har yana jiyo sautin harbawan.
“Sorry daughter tuba Dady yake, Oya fad'amin wanda ya saka min ke kuka?”
Cak ta tsayar da kukan tana lafewa ajikin katifar gadon ta cinno baki gaba asakalce tace.
“Yo ba Maamy bace tace wai sai bayan azumi Zan dawo wajanku, dan Allah Dady da gaske?”
Shattima ya bud'e idanunsa ya sauke qafafunsa ya miqe tsaye yana d'aukan sauran wayoyinsa ya zura cikin aljihu, cikin kamewarsa yace.
“No! Wasa takemi Baby yanzu dai kinga dare ya fara Baffa yake kirana zuwa gobe zan kiraki na fad'a miki randa zamuzo d'aukarki ki fara shiri OK...?”
Ihun murna Khairy tayi tana fad'in.
“Ngd sweet Dady I love you so much sweet Dadynah.”
Shattima da ya fara takowa zuwa k'ofa yace.
“Love u too na kuma jin kukan ki kiga yadda Zan hukuntaki mai rigimar ba dalili kawai, oya bani auntie mu gaisa.”
Khairy ta sake lafewa ajikin katifar tana murmushi tace.
“Toh na daina Dadynah Mummy fa tana falo ni ina bedroom nazo nayi sirri da iyayena.”
Murmushi yay yana bata sumba ta wayan yace.
“Ok good night Allah miki albarka bye.”
Bai jira me zatace ba ya katse kiran ya lalubi lambar direba bugu d'aya aka d'aga cikin kamewarsa yace.
“Afito da mota zamuje Galadanci.”
Ya k'arashe mgnar yana zura wayansa aljihu.
Tana zaune ya iso yana beqa mata hannu ta kama ya miqar da ita yana hararanta yace.
“Ki kuma sakamin Baby kuka kiga yadda zan cijeki ta ko ina.”
Ya fad'a yana d'aukan mata wayanta ya damqa mata yajata suka nufi hanyar falon, ta kafeshi da idanu.

Wata baqar Jeep ce jibgegiya mai shegen kyau mai baqin glass aka bud'e musu suka shige, aka rufe direba ya shiga da wani soja d'auke da bindiga ya zauna kusan direba, direba yama motar key ya nufi tamqameman gate d'in yana zuba horn, aka bud'e gate d'in ya silala motar waje.
Mamy ta kalleshi tana murmushi jin yana mintsininta awuya da ya zura hannunsa cikin hijab d'inta.
Ido ya kashe mata, murya k'asa² yace.
“Wlh gabana fad'uwa yake.”
Sumbatarsa tayi a bakinsa tace.
“Ka yawaita innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”


Maryam kwance saman 3 seatar a falonsu idanunta k'ura akan Tv amman azahirin gaskiy batama San menene suka haskawa ba atashar MBC 2 ba.
Ammi da ta fito daga kitchen ta d'orama Abba Aminu shayi, ta zauna hannun kujeran da Maryam take ta dafa kanta taji akwai zafi kad'an, tace.
“Oya tashi maza kici abinci kisha magani wlh kona fad'awa Abbanki yana ciki kinsan halinsa sarai, Nafisa je d'akina d'auko mata magani tasha.”
Maryam ta miqe zaune tana matsalar k'walla tace.
“Ni dai wlh Ammi lafiyata lau, banajin ciwon komai.”
“K'arya kike wlh kinaji magani ne bakya son Sha...”
Commissioner Aminu da yake isowa falon yace.
“Maryam maza tashi kisha magani ni narasa meke damun yarinyar nan wlh.”
Ya k'arashe mgnar yana d'agota ta miqe zaune ya zauna yana tab'a goshin nata.
Lamo tayi jikin mahaifin nata tana matsar k'walla.
Ammi tace.
“Nafisa ba cewanayi ki kawomin magani ba?”
Miqewa tayi ta tafi Maryam kuwa ta zame ta miqe tsaye dan ta gudu d'akinsu.
Abba Aminu ya riqo hannunta yana fad'in.
“Maza muje kici abinci kafin kisha maganin d'azu ba'ayi dinner dake ba. Abidah! Na manta ba fad'a miki ba anfa d'aurawa Ummulkhairi aure yau a Central Mosque, amman nayi mamaki da Shattima bai fad'amin ba, kuma ban gansa awajan ba, Baffa ne ya kirani yace ni yakeso na zama alwalin Khairyn sannan kar nama minister mgnar idan ba shi yamin ba, nayi mamaki sosai wlh nace ko Khairyn takeson yaron shi baya so shiyasa yaqi halarta d'aurin auren? yanzu ma dawani Abdullahi akan d'aura Allah ya sanya alkahiri zamu jira muga koza'a mana mgnar....”
Bakinsa ya tsaya cak ne lokacin da Maryam ta saki wani razanannan ihu tana fad'in.
“Wallahi da shine aka....”

Bata qarasa ba ta yanke jiki zata fad'i Aminun ya tarota lokacin har ta suma...

Karku manta kuyima 'Yar uwata addu'a.

*YI WA KAI*

Free Novel

_October28/10/2022_


*41&42*

Idanunta da suka mata nauyi suna mata bala'in zafi ta bud'e, tana bin d'akinta da kallo, kafin ta kalli hannunta wanda yake d'aure da qarin ruwa. Idanunta ta maida kan Ammi da Abbanta, suna famar mata sannu. Idanu ta runtse hawaye masu zafi suna zubo mata, Allah yana gani tanama Shattima wani irin so mai miyar fad'a ko bayyanawa, ita kanta abin tsoro yake bata. Ammi ta share mata hawayen tana fad'in. “Ya isa haka wai me ya faru da Abbanki yayi maganar Khairy tayi aure kika fasa ihu kika suma? Me yake faruwa da kika Sani mu bamu saniba Maryam?” Maryam ta fashe

Please Login or Register in order to submit comment