Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kira.
Kira biyar tai masa bai samu daman ɗagawa ba, ta kira Mamy kamar zatayi kuka tace.
"Mamy! Kinga Dadynah dan ma kar muyi maganan yaƙi ɗaukan kirana koh"
Mamy tace.
"Yi haƙuri dole zai ɗauki kiranki kimasa uzuri Ok?"
Baki turo gaba tace.
"Toh Mamy..."

Auntie lokacin da kira Khairy dan sanar da ita tuntuni taji, tace ta bari tare zasu tafi sai ana jibi sunah.
Kuka ne bata mata tace toh badan zata yarda takai lokacin ba...

Shattima bai samu kansa ba, sabida jama'ar da suke kiransa da masu zuwa har gida yi masa Barka da samun kyawawan Twins ɗinsa, sai misalin 10 na dare, jama'a suka ɗauke ƙafafuwansu, ya samu ya yi wanka, ya yi shirin kwanciya bacci, yaje ya gano Mamy da yaransa ya shige ɓangarensa.
Kwance yake akan katafareren gadonsa, AC na ratsa shi ta ko ina ga wani fitinannan ƙamshi da ya gauraye ɗakin.
Kiran Khairy ya yi yana murmushi yasan rigima zata masa yanzun.
Tana ringing bata ɗaga ba, sai da ya mata kira uku, ta ɗaga cikin bacci ta mishi sallama, tana faɗin.
"Dady dan kar muyi maganan zuwana shine ka ka ƙi ɗaukan kirana koh? Dady Barka nayi ƙanne biyu rana ɗaya."
Murmushi ya saki yana faɗin.
"Babyn Ruhinta inata fama da jama'a shiyasa ya barki sai yanzu anutse muyi magana, ykk my Baby?"
Ashagwaɓe tace.
"Dadynah gani na lalace da kwaɗayi wlh, komai idan ba na yaji naci bana jin daɗinsa. My Ruhi zaka bani Baby ɗaya koh?"
Dariya ya yi yace.
"Kin fini kusa da Bilkisun ai my Baby."
"Yawwa Sweet Dadynah nace ba gobe sai tahowa Jigawa koh?"
"No! Baby keda Auntie Aisha zaku taho..."
Ta sakar masa kuka tace.
"Ni dai gobe nake so Dady love don Allah kaji Mijina Dadynah Ruhina madubin dubawana."
Ƙirjinsa ya shafa yana murmushi yace.
"Naji jibi Maleek zai ɗaukanki Ok?"
Cikin murna tace.
"I love You Ruhin Baby Ngd muahhhh."
Gyaran murya ya yi yace.
"Kika ce bakya iya cin abu sai me yaji? Please Babyn Ruhinta ki rage cin yajin nan bana so Ok?"
Kamar zatayi kuka tace.
"Sweet Dadynah bakina lami."
Anutse yace.
"Zai daina idan kinzo zaki samu lips ɗin Dadynki kina shan abunki."
Ɗan kukan sangarta ta saki tace.
"Sweet Dadynah Ni yanzu nakeso nasha kaji ina missing Please angona."
Shattima ya yi dariya yace.
"Oya Babyn Ruhinta ta koma bacci ta daina rikicin nan..."
Daƙyar ya samu ya lallaɓata da kalaman soyayya masu sanyaya zuciya har ta koma baccin, yana jin saukar numfashinta ya katse kiran yana murmushi...


Washegari da misalin goma na safe Ammi ta fito cikin shirin tafiya gidan Mamy, Kausar na zaune a falon tana kallon Tv.
Ammi tace.
"Kausar na tafi gidan haihuwa sai nadawo."
Kausar tace.
"Ammi zanje Abba ya faɗa min nima idan zakije na biki, maman Khairy koh?"
Ammi tace.
"Ok tashi ki shirya mutafi tunda da yawunsa."
Kausar ta miƙe masha ALLAH ta yi mulmul abunta.
Cikin shiri ta fito.
Sai ga Abba Aminu kamar an jefosa falon,ya kallesu yana washe baki yace.
"Ah Matana Commissioner Aminu ina zuwa?"
Ammi tana murmushi tace.
"Inda ka aikemu mana."
Kausar ta yi dariya tace.
"Kai Ammi kin iya bada amsa. Abba sannu da zuwa."
Abba Aminu yace.
"Au magana aka faɗa min?"
Ammi ta yi gaba tana cewa.
"Ni kam na fita sai kinzo ina wajen mota."
Kausar ta riga Ammi fita gudun kar Babyn nata ya damƙota, idan Ammi ta rigata fita.
Dariya ya yi yana kallon yadda ta zuba da gudu.
Ammi ta kalleshi ta watsar tace.
"Ko buƙata ta kawoka amaidota?"
Kallonta ya yi yace.
"Abidahtah bakida dama, ai da buƙatace ke zan turmushe tunda aikin ne wasu takardu nazo ɗauka."
"Kai jama'a Ni Abidah Abban Abdoul adinga tauna magana sai anjima."
Ta faɗa tana wucewa...

Mamy suna zazzaune masha ALLAH ɗakin sunada yawa, hira ake sai ga Ammi da Kausar.
Mamy sosai ta yi farin cikin ganinsu tare, tana washe baki tace.
"MASHA ALLAH Hajiyata keda ƙanwarmu?"
Ammi ta ɗauki Neehal tace.
"Masha Allah munyi haihuwa nan fa, Hajiyata barka da arziƙi."
Mamy ta yi murmushi tana kallon Kausar, tace.
"Barka Hajiyata ya ciwon kan?"
Ammi tana sumbatar Neehal tace.
"Naji sauƙi."
Kausar ta amshi Baffa a hannun Aunty Madinah tana rungumesa tace.
"Mamy barka Sannu Allah ya raya mana, ina Khairy ko bata zoba?"
Mamy ta yi murmushi tace.
"Sai gobe zata iso in Sha ALLAHU.
Gaskiya naji daɗin ganinku haka Allah ƙara muku zaman lafiya da fahimtar junanku Allah ya rabaku da ƴan tsirku."
Ammi ta yi murmushi Kausar ta amsa da.
"Ameen Mamy...."

Mamy tanada kwana biyu da haihuwa Khairy ta iso Jigawa da dare suka shigo.
Da ihun murna ta nufi ɗakin Mamy.
Mamy da take shayar da Baffa tabi Khairy da kallo, tana murmushi.
Ruƙunƙume Mamy ta yi da Baffa ta haɗa da Neehal ta saki kukan shagwaɓa haɗe da murna tace.
"Mamynah Barka Allah ya rayamun ƙanne na, sannu kinji Mamynah."
Mamy tayi dariya tana dukanta abaya tace.
"Shi mutum dai sai shagwaɓa, sakeni toh ki amshesu."
Sumbata kumatun Mamy ta yi tana janye jikinta ta amshi yaran tace.
"Bari muje sutayani canza kaya."
Ta faɗa tana ficewa yaran.

A ƙofar falon Shattima suka haɗu ya fito yana amsa waya.
"Oyoyo Dadynah kalli kyawawan ƙannena masu kama dakai."
Ta faɗa tana nufo wajansa.
Dole ya yi sallama da wanda suke wayan ya zura wayan aljihunsa, yana kallonta fuskarshi ɗauke da murmushi.
Tana isowa ya amshi Baffa ya kamo hannunta suka nufi falon sa.
Zaunar da ita ya yi yana shafa fuskarta yace.
"Baby bakiyi kewan Dady ba?"
Tanawa Neehal wasa tace.
"Ni banyi ba ga ƙanwata na samu ma."
Dariya ya yi yana kallonta cike da so da ƙauna, yaga yau bata wani damu da shi ba...

Har dare ya yi sosai Khairy na wajan Mamy ba yadda Mamy batayi ba taje ta kwanta taƙi tace nan wajenta zata kwana, dole ta haƙura ta barta taso ta taya Dadynta kwana amman fafur taƙi sam bata wani ɗaukinsa irin nada ita ƙamshinsa ma yanzun baya burgeta.

Tun zuwa Khairy Mamy ta ankare da akwai shigar ciki ajikinta, wani irin farin ciki marar misaltuwa ta shiga ta yi gum da bakinta ne, sai bayan sunah ta sanar da Shattima.

Wasa² har gobe suna Khairy taƙi yarda da Shattima, batason ko rungumeta ya yi sai taji kanta na juyawa, baki ɗaya ta tare ɗakin Mamy har kayan sawarta, da Mamy da tace taje wajansa sai kuka bata son raɓarsa...

An shirya komai na sunah cikin tsari da ilima, Mamy tasha ƙunshi da kitso, baƙi sun cika gida su Auntie Aisha Zainabu Maryam ga ƴan uwan Mamy harda na nesa sun zo haka na Shattima, kowa na tayasu murna, zuwan Zainabun da Maryam yasa yau Khairy ta koma ɗakinta wajansu, tare suka kwana.

Washegari da safe akayi fatihar sunah Twins sunci suna. Umar Faruk, da Aminatu.
Kusan dai sunan nan basai na fito na zayyane dukkan abinda akayi ba, suna ya kwashi dubban al'umma anci ansha anyi kyaututtuka daban daban Khairy yau anyi kwaliya kala-kala ansha hotuna kowa ya yabawa Khairy da Mamy a taron sunan Twins ɗin nan.
Ammi da Kausar daman sauran mata su ƙara ɗaukan ilimin zama da kishiya ayau, wanda zai ce Mamy da Khairy basu burgesu ba, toh bayada tsoron Allah.
Zainabu sai da ta yi kukan farin ciki aɓoye yau kam ƴarta ta burgeta haka Mamy.
Shattima manyan-manyan ƙusoshin Nigeria wanda basu samu sami halattar gayyatar zuwa taron murnan da ya yi ba na sunah basuda yawa dan sama da mutum ashirin baƙi daga ƙasashe suka zo, bayan manyan ƙusoshin Najeriya ya yi kuka harda hawaye lokacin da ya yi sujada dan miƙawa Allah godiyarsa baisan shi wani bane sai yau baisan yanada jama'a masu ƙaunars har haka ba sai yau...
Mamy lokacin da Shattima ya leƙo dan mata ban gajiya tayi bacci.
Khairy tana can maƙale da Babies ɗakinta.
Zainabu ta matsa mata sai ta kawosu harda su kuka ta tarkatosu ta kawosu ta isko Mamy tana bacci ta kwanta kusanta ta rungume yaran...
Shattima sai juyi yake iskancin Khairy ya ishesa fafur taƙi ko Romance ɗin ta ya yi.
Tsaki yaja yana lumshe idanunsa anutse yace.
"Wlh Baby idan kin shiga hannuna sai kinyi bayani..."
Washegari sunah su Maryam suka koma, da Zainabu Khairy harda kukanta, ga Auntie Aisha ta koma Galadanci tun ran sunah da dare.

Da asubah bayan sallah Khairy ta fito zuwa ɗakinta ta ɗauko wayanta da bari dan kiran Ummanta taji sun isa lafiya juya basuyi wayaba.
Tana shiga Shattima ya rufa mata baya.
Kamota ya yi ya rungumeta yace.
"Wa na kama?"
Kuka ta saki tana tureshi tace.
"Ni dai sakeni Dady bana so kana taɓa ni..."
Cak ya ɗauketa yana murzawa ƙofar key ya nufi bed da ita.
Wani irin sahihin romance ya fara mata yana jujjuyata akan bed ƴan cakuɗata tare wani irin sansanyan kissing tare da kalaman ƙauna.
Ashagwaɓe tace.
"Ni bana so Dady."
Cikin raɗa yace.
"Ni inaso Babyn Ruhinta barni nayi kiɗana da rawata.".
Ya faɗa yana sumbatarta.
Khairy tana kuka tana tureshi haka ya samu ya yi sex da ita cikin wata irin fitinanniyar soyayyarta yake haƙarta yana sambatu tare da tambayarta me ta ƙara jikinta take irin wannan zaƙin da garɗin tafi zuma da komai na duniya zaƙi. Yana aiki yana mata surutu ita kuma tana famar masa kuka tana tureshi har zuciyata bata so...

Ai yana gamawa tun bai cireba ta dinga kelaya masa amai ajikinsa.
Hankalinsa atashe ya cire ya cicciɓeta sai toilet, Yana mata sannu.
Kafin ya gama mata wanka zazzaɓi me zafi ya rufeta.
Hankalinsa atashe ya mata wankan tsarki shima ya yi.
Agurgune ya shiryata shima ya shirya, ya ɗauke ta suka fice, tana famar masa kuka tana kiran Mamy.

Nan clinic din kusan gidansa ya kaita, aka amsheta cikin kulawa.
Bayan anyi gwaji aka bata gado tare da ɗaura mata drip sabida sai amai take tana kuka tana kiran Mamy. Shattima sai lallashinta yake.
Sakamako na fitowa Shattima yaga ciki kwana 42 abin Khairy.
Hawaye kawai yaji suna sauka akan fuskarshi, ya gaza koda motsi kusan minti biyar kafin ma ya iya furta kalmar .
"Alhamdulillah!"
Kai ɗai.
Goshinsa ya kai ƙasa yafi tsayin minti 20 kafin ya ɗago ya sanya takardar result ɗin aljihunsa. Shi kaɗai yasan gudummawar da zai ƙara wa mai asibitin nan dan ta ƙara haɓaka.
Bayan Dr ya basa rubuta masa duk wani magani da zai siya tare da masa kashedin yabar yawan sex da ita har cikinta ya yi ƙwari,
ya koma wajan Khairyn tana bacci ya rungumeta yana famar saumbatarta, tare da kissing bakinta...

Lokacin da suka dawo gida goma na safe, kuma lokacin ya gama shelar cikin Khairy wa ƴan uwansa.
Murna karkaso ka gani, bai matsa mata ba ya barta ta tafi ɗakin Mamy ta kwanta, Mamy dai kallonta take ganin yau kamar rigima takeji.
Shattima ya kira Mamy tazo falonsa yana son ganinta.
Yaran ta ɗauka ta tafi.
Rungumesu ya yi da yaran yana sumbatar su yana shirin faɗa mata sai yaji nauyi bazai iyaba gwara har ya fahimci haka da kanta.
Mamy ta kalleshi tace.
"Albishirinka Mi Amor."
Yana shafa kanta yace.
"Goro amaryar jego."
Dariya ta yi tace.
"Wlh Baby nada ciki tun zuwanta na fahimta..."
Gaza magana ya yi ya rungumeta yana sauke numfashi tare da ɗago kanta yana tallabe fuskarta ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta...
Washegari Mamy ta matsawa Shattima ya ɗauki Khairy su koma Abuja amman cikinta da ya yi wata takwas za'a dawo wajanta shi kenan kuma ita da Abuja sai hutu.
Shi dai baida bakin magana umarninta yabi yayin da Khairy ta kafe bazata ba, sai da taga Mamy ta yi fushi tabi Shattima suka tafi.
Bayan tafiyarsu Mamy taci gaba da wanka da kulawa da yaranta mai tayata zama ƙanwar Anne tana kulawa dasu sosai ga mai reno da aka kawo mata.
Shattima ba ƙaramin fama da Babynsa yasha ba kafin ya samu ta saki jiki da shi dan tana samun kulawa sosai wajansa.
Satinsa biyu yazo ganin Mamy da Babies daƙyar ta barsa ya yi kwana uku ta maidasa tace ta yafe akula da Baby.

Ahaka har Mamy sukayi arba'in masha ALLAH yaransu masu girma kyansu da kamarsu da Shattima na ƙara bayyana.
Shattima da yazo sai da ya yi sati suna kwasar amarci da Mamy sunci soyayya kamar ba gobe kafin ya koma Abuja yana santin Mamy dan baƙaramin gyara ta sha ba.
Bayan haihuwar Mamy da wata huɗu Zainabu ta haihu ɗanta kyakkyawa mai kama da ita har farin natane karkuso kuga murna wajan Dad Mustapha.
Lokacin sai yazo ɗaya da auren Nadiya Wanda ta samu miji a Yobe.
Lokacin cikin Khairy ya shiga wata shidda haka tazo sunah da auren ƙanwarta har Mamy tazo masha kamar karta koma, Abujan taji a lokacin.

Cikin Khairy nada wata bakwai akayi auren Suhailat ƙawarta aka kaita Kano harda kukanta sabida Shattima ya hanata ya bata haƙuri, yama Suhailat abun alkhairi sosai.
Salim daƙyar Umma da Hisham suka basa Aliyah da ƴarsa sabida sunga ya musu ya tuna da gasken gaske, ya riƙe Aliyah da ƴarsa amana tabar ma da yake sha ya daina, Himsha ya tuba ya daina duk wani bin malamai ya koma ga Allah ya kuma amshi ƙaddara sa ta ƙasa da akayi da shi wajan aiki, Shattima ya ɗan sauka daga fushin da ya yi da shi tun daga haihuwan Mamy da ya tsaya kaida fata akayi komai da shi duk da bai nemesa ba...
Cikin Khairy na cika wata 8 Shattima ya kawota wajan Mamynta, lokacin Neeehal da Baffa suna rarrafe suna kama abu ma su tsaya masha Allah yana masu shiga rai kayawawa manyan dasu, Allah ya ɗorawa Shattima tsammanin ƙaunarsu wataran dasu yake zuwa office wajan aiki Allah ya musu shegiyar ɓarna kuwa kamar Muhammad Al'amin ɗin Asma'u ta cikin Ƙaddara muce auren miji ɗaya.🤣

Komai na haihuwar Khairy an tanada ɗakinta bakiɗaya an canza komai, sabo.
Har kuka ta yi ta rasa wace irin ƙauna Mamy take mata.

Tunda Khairy tazo ta tattara ƙannenta wajanta wani lokacin suke raba dare sai sunyi bacci Mamy take zuwa ta ɗauke su yaran sun shaƙu da Khairy matuƙa.
Wata ranan asabar Khairy ta tashi da ciwon naƙuɗa hauka ihu tana faɗin.
"Dady zan mutu Mamy Neehal Baffa ku riƙe ƙaninku ko ƙanwarku amana Ni tawa ta ƙare..."
Mamy Abun ya bata dariya ga tausayi ta rufe mata baki Shattima hankalinsa atashe ya ɗauketa Mamy ta barwa Baraka me reno su Neehal suka tafi asibitin.

Cikin ikon ALLAH bata jima da zuwaba ta haifo ƙaton ɗanta mai tsannain kama da ƴan uwansa shi wanka tarwaɗa ne baida baƙi kuma ba fari bane, chocolate kenan.
Mamy karkaso kaga murna, suna kiran ƴan uwa da abokan arziƙi tana fadamasu.
Lokacin da Mamy taba Shattima kyakkyawan Babynsa naɗa cikin kayan sanyi sabida irin sanyin da ake tsulawa, yaron sai lasar ma baki yake yana harba ƙafafuwansa, yana lasar baki sai ya tuno ranan da suka tsinci Khairy cikin kwali haka ta dinga yi, addu'a ya masa ya masa kiran sallah ya tura masa lips ɗinsa bakinsa ya fara tsotsa.
Zarewa ya yi yana murmushi shi kuma yaron ya fashe da kuka.
Mamy tace.
"Tarihi ya maimaita kansa wannan yaron rikicin Baby zaiyi wlh."

Shattima ya yi dariya yana sake maƙale yaron a ƙirjinsa yaba Mamy waya ta musu fito...
Kafin awa daya ƴan uwan Mamy dana Shattima kusan mutum goma sun halarci Khairy clinic and maternity.

Bayan an sako Khairy Mamy tama Khairy wanka, ta matsa taci farfesun kaza tasha romon tasha kunnun gyaɗa mai zafi ta matsa mata ta shayar da yaron zafi takeji sosai.
Ta kalli Shattima da ya sakasu gaba, yana murmushi, Neehal da Baffa sai wasnsu suke ajikinsa.
Ido ya kashe mata ta zumɓuro baki gaba tace.
"Ni dai bazan sake haihuwaba."
Ta faɗa tana Rungume Mamy tace.
"Ngd Mamynah ina roƙon ALLAH yabani abinda zan saka miki ya haneni dukkan wani abunda zanyi wanda zai ƙuntata miki ko cutar dake ina sonki ina ƙaunarki Mamynah, ga Babyn na baki ki haɗa kinji?"
Shattima ya ƙyalƙyale da dariya ya ɗuko ya sumbaci kumatunta yana jan hancinta, ya shafi kan Babyn ya mata gwalo Mamy tana musu dariya.
Khairy ta cika da haushi ta saki kuka tace.
"Mamynah kina ganin abinda Dadynah yake min koh? Bazaki masa magana ba ya daina?"
Mamy ta daki ƙirjin Shattima tace.
"Tashi Mi Amor ka fita kana sanye min Baby kuka, yi shiru Baby barni da shi, ka tashi katafi mutane ƙasa yanzu zasu fara hayowa barka."
Khairy ta zare nononta bakin Baby ya tsala kuka yana harba ƙafafuwansa.
Shattima ya zauna yana zungurin Khairy akai, ya gyara Babyn yana kamo maman ya saka ma yaron abakinsa ya cafke yana tsotsa, ta riƙe damtsen hannunsa tana shagwaɓe fuska tace.
"Dadynah zafi wallahi shiyasa nace Mamy ta haɗa ta shayar dasu."

Shattima ya yi murmushi yace.
"Ai ke ya biyo haka kikayi dan haka shayar min da ɗana, koh Neehal Baffa ashayar muku da ƙaninku koh?"
Neehal ta rarrafo ta kama ƙafar Shattima tana dariya, Baffa ya riƙe Mamy yana sanya kuka.

Mamy ta yi dariya tanajin wata irin nutsuwa tana kallon Khairy na shayar da Babynta, Shattima yana rungume da Neehal tana wasa da gemunsa.
Baffa ta ɗauka ta zauna tana shayar da shi, tace.
"Ni kam Mi Amor bazaka fita ka bamu wajeba ne sai jama'a sun rutsaka?"
Khairy tace.
"Mamy ki amshi jikinki ya takurani."

Shattima yana rungume da Neehal, ya amshi Baffa da yake daga hannunsa yana ɓare bakinsa dan yin kuka ya sunkaya ya ɗauke sa ya haɗasu yana kallon Khairy yace.
"Bataso ke zaki shayarmin da ɗana kaji me wayo koh"
Ya faɗa yana ficewa da yaran.
Khairy tace.
"Mamy kice ni ba ruwana da shi fah!"
Mamy dariya take sosai tana faɗin.
"Baby haihuwar bata saka kika shiryu ba? Yi haƙuri ki shayar mana ɗanmu jikinmu ke kuma ƙaninki ɗanki, daga yaye idan na amshe shi, shi kenan Ok?"
Kai Khairy ta ɗaga.

Zainabu koda taji Khairy ta haihu ba ƙaramin farin ciki ta yi ba, kullun tana tunanin ƴarta.
Tana faɗa wa Dad Mustapha yace zasuje su gano jikinsu, Nadiya ma tanajin haihuwa tace ana jibi suna zata taho daga Yobe.
Suhailat ma sai murna take ta kira mijinta yana wajan aiki ta faɗa masa ya kuwa ce zataje suna in Sha ALLAHU.
Kausar ma da take fama da laulayi ta yamma ta biyo Ammi sukazo barka sai yabon Babyn Khairy take.
Maryam da take ɗauke da cikin wata huɗu ta yi murnan haihuwar Khairy hankalinta ya kwanta Usman yace zasu zo sunah.
Washegari

Da dare bayan jama'a sun watse, Mamy ta sallami Khairy har tayi bacci Inna ADAMA ce mai zaman biƙi.

Mamy taje ta samu Shattima yana falonsa yaran na jikinsa suna wasansu.
Ta zauna gefensa tana shafa fuskarshi tace.
"Mi Amor wannan yaran sun koyi rashin bacci da wuri har Auntiensu Baby ta yi bacci."
Shattima yace.
"Barmin yarana wannan rikitacciyar Khairyn taki, tashi dafo min coffee."

Mamy tace.
"Ok an gama Mi Amor."
Ta faɗa tana sumbatar lips ɗinsa ta miƙe dan zuwa dafo masa coffee.
Neehal ta ɗaga mata hannu tana furzo mata yawu irin wasan yaran.
Mamy ta ɗauketa tana faɗin.
"My Neehal kin fiye shegantaka."
Goyata tayi ta sauka ƙasa ta dafo masa coffeen.
Sai yasha ya nutsu, lokacin Yaren sunyi bacci takai ta shimfiɗesu akan gadajensu ta dawo ta hau kan cinyarsa, tace.

"Mi Amor meye sunan da ka sakawa Babynmu?"
Hannunsa ya zura cikin rigarta yana ɗaukan magana, anutse ƙasa² yace.
"Ki zaɓa na baki gari, naso ace macace na saka mata sunanki."
Cikin farin ciki tace.
"Ngd Mi Amor, Amman kaba Baby zaɓi."
"No! Keda ita duk ɗaya."
Jikinsa ta Kwanto tana hawaye tace.
"Ngd Mi Amor da yadda kuke bani daraja da mutuntawa har yau banga wani abinda kuka min na kaicona ba, Allah yasa mu ɗora ahaka, na zaɓi sunanka asakawa ɗana jikana mijina, na zaɓi Abdullahi, in Sha Allah Baby zata haifo mai sunana nan kusa."
Shattima ya kalleta yana sake shigar da cikin jikinsa, ya sumbaceta yace.
"Ngd Sweetheart sunan Mijinki ya miki?"
Kai ta ɗaga tana hawaye.
Harshensa ya saka yana lashe hawayen yace.
"An gama daman nasan shi zaki zaɓa shi na saka masa tun jiyan, daga ke har Babyn wlh naji ajikina sunan zaku zaɓa, Allah yasa nan kusa ki haifomin me sunanki tunda Su Baffa an girma anyi ƙani."
Cikin farin ciki ta jefa bakinta cikin nasa tana kissing ɗinsa...
Toh Alhamdulillah jama'aaaa anan zan ajiye alƙalamina, sai nace Ayi sunah lafiya, Allah yasa daga Baby Khairy ta zubar da wanka ta sake samun ciki Allah kuma yasa ta haifo ma Mamy takwara Mamy kuma Allah yasa ta sake haifo mana Twins Amin.
Kausar Allah saukeki lafiya Maryam Allah saukeki lafiya, Nadiya Allah saukeki lafiya Suhailat Allah saukeki lafiya, Amin.

Abinda na rubuta na lada Allah kabamu ladan nida masu karatu, na zunubi ALLAH ka yafe mana dan alfarmar Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama Ameen ya Hayyu Qayyum.
Ma'assalam sai Mun haɗu a sabon labarina Happy Ramadan, lbrn baida tsayi in Sha ALLAHU zaku dinga samun update akai-akai kudai kubani haɗin kai wajen comments, and sharhi, littafin yana cike da tausayawa da wata irin fitinanniyar soyayya me sanyi, da wata irin sarƙarƙiya, akwai abubuwa dayawa da bazan iya fayyace muku ba, sai mun haɗu kar na cikaku da surutu ku dai ku jirayi wannan zazzafan labarin wanda ya faru da gaske sai ɗan abinda da ba'a rasaba na ƙara. Zan fara sakar muku labarin nan February 15/2/2023 in Sha ALLAHU.
Dan haka duk me son kasancewa cikin group ɗinmu inda zaku fara cin karo da wannan littafin nawa sabo 15/2/2023 zaku iya tuntuɓar wannan lambobin dan sakaku cikin group, sabida idan an fitar da link maza na shiga, hakan bai dace ba shiyasa na zaɓi hakan, idan kiyi magana za'a tura miki dokokin group idan ya muku sai a sakaku, karku manta littafin free book, sabida ku anfana yadda duniya ta rikice da rashin kuɗin nan muna sane daku, ku dai kuyi ƙoƙari wajan comments and sharhi kun biyani. mungode masoya sai mun jiku.😍 *+22796515805*. *+22798792126*. *07032817477*

Dan haka s
😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment