Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace.
”Ok tinda bakya son sanin yadda Abdoul ya rasu bare ki ɗaukar
masa fansa sai an jima...”

Da sauri ta beƙa hannunta ta damƙo hannunsa tana faɗin.
”Tsaya da ALLAH muyi magana.”
Salim ya fizge hannunsa yace.
Idan kina buƙata biyoni.”
Ya faɗa yana nufar matarsa.
Yana shiga ya tayar ya fizgeta yabar wajan.
Azizah wutar ɗaukan fansar da take ruruwa acikin zuciyarta ya sakata fizgar motar ta tabi bayan Salim aguje.

_*Khairy clinic and maternity*_

Yana shigowa bayan yay parking a parking lot ya fito ya kulle motar ya nufi ciki anitse, yana karkaɗa makullin motar hannunsa.
Duk suna zaune a receptions ya isko su kusan su 10 harda liman da kansa Inno Munnir Alhaji Bilal Hajja Hafasatu Fauziyya, Balaraba da sauransu.
Anitse cike da girmamawa ya gaishsu, suna amsa wa cike da kulawa, banda Liman da ya tsuke fuska yana faɗin.

”Kayi sauri ka shiga baiwar Allah Bilkisu sai ita ɗaya take fama, ta rikice tace mufito zata shawo kanta, nasan bakinta bazai mutu ba sai ka shiga lamarin.”
Shattima cike da kuwala yace.
”Allah bata lfy bari naduba.”
Ya faɗa yana nufar hanyar da zata kaishi room ɗin da Khairy'n take.

Tsaye suke tana riƙe da ita ita kuma tana famar rusa kuka, tana faɗin.
”Wallahi Mamy bazan zaunaba idan baku raba wannan auren ba,gwara kawai na shiga duniya ko na kashe kaina akan na zauna matsayin matar Dady kishiyar Mamy, duk da kuwa irin ƙaunar da nake muku keda Dady wlh da na zauna matsayin matarsa gwara nabar duniyar, wlh ciwon zuciya zaiyi kasheni, dame zanci rana zafi inuwa ƙuna...”
Mamy ta saketa tana kuka tace.
”Shi kenan Baby tunda ban isaba dake ni ce yau na nemi alfarma kika ƙi yi min koh? Da ki zauna damu gwara ki kashe kanki ko shiga duniya sabida kawai Shattima ya zama mijinki...?”

Bango Khairy ta dafe tana faɗin.
”Eh Mamy kuyi haƙuri wallahi ƙaramar ƙwaƙwaluwata bazata ɗauki wannan tashin hankalin da rikicin ba, idan kina sona kina ƙaunata kawai ki saka Dady ya sakeni, ki aura min ko kuturo ne ko makaho, kai ko mayene ki auramin zan zauna akan dai na zauna da Dady matsayin mijina, dan Allah Mamy ku tausaya min, ku raba auren nan...”
Juyowo tayi jin azababban ƙamshinsa me sanyaya zuciya, ya gama cika ɗakin, wanda duk halin da take ciki ƙamshinsa baya taɓa ɓacewa hancinta ba.

Da wani irin sauri ta toshe bakinta tare da runtse idanunta tana kauda kanta, jikinta na wani irin ɓari ta shiga bin bango tana son guduwa daga ɗakin sakamakon 4 eyes da sukayi da
Shattima wanda ya shigo kusan 2 minutes tsaye yana kallon su.
Ƙafafuwanta ne suke neman gaza ɗaukan ta sabida wani fitinannan kallo da Shattima yake watsa mata hannayensa zube cikin aljihun jallabiyarsa.
Daƙyar take ɗaga ƙafafuwan nata tana ƙoƙarin isa ƙofar, da taimakon dafa bangon ta iso wani irin jiri ya kwasheta sabida karkarwar da ƙafafunta suke yi, sabida wani irin fitinannan kallon da Shattiman ya mata kafin ta janye idanunta, tana ƙoƙarin fizgo numfashita wanda yake ƙoƙarin tsayawa cak, zuciyata wani irin bugu take, ta fashe da wani irin kuka tana girgiza kanta idanunta A rintse.
Tai saurin dafe handle ɗin ƙofar cikin ɗan sauran kuzarin da yay mata saura ta murɗa da niyar buɗewa.
Da wani irin taku ya ƙara so wajanta bai cemata uffan ba ya ɗora tattausan saman
Key ɗin da yake jikin ƙofar ya murza cikin kamewarsa yay magana ”Karki yi kuskure ki buɗe ƙofar nan”.
Ya faɗa yana ƙoƙarin janye hannunsa daga ƙofar wanda wajan rufewar dole sai da hannunsa ya taɓa nata, yay saurin janyewa ya juya yabar wajan.

Cike da nutsuwarsa yake takawa ya nufi wajan Mamy da ta durƙushe tana kuka.
Sunkuyawa yay ya kama kafaɗunta ya miƙar da ita tsaye, yaja hannunta suka isa bakin gadon, yaja kujera ya zaunar da ita, ya tsugunna gabanta yana goge mata hawayen fuskarta idanunsa acikin nata yana mata wani sahihin kallo mai karya garkuwar jiki, anitse cike da kulawa cikin muryansa mai taushi ahankali ya furta.
”Ya isa haka, bana son sake ji ko ganin wani kuka anan kuma, yanzu me kikeso ayi?”
Bilkisu dole ta haɗiye kukanta, tana kallonsa cike da damuwa tace.

”Mi Amor Baby ka kamota tazo kusana muyi magana na tsani kallamar sakin nan da take faɗa, ko tafiya ta barmu, Please kayi wani abu karta samu wata matsalan ta kasa gane bayanin kowa dole fa kaine zaka yi maganin rigimar nan, Please Mi Amor.”

Anitse ya buɗe bakinsa ya furta.
”I know.”
Ya faɗa yana shafa gefen fuskanta, ya janye
Idanunsa daga kallonta ya maida kan Khairy wacce take ƙoƙarin buɗe ƙofar ta fice.

Kalaman Auntie Aisha suka dawo masa yay saurin rintse idanunsa, ya buɗe cikin kakkausar murya yace.

”Ummulkhiari! Zo nan.”

Key ɗin da ta riƙe tai saurin janye hannunta jikinta na karkarwa tsabar ruɗewa da tashin hankalin jin yadda Dadynta ya kirata, shima baya ƙaunarta yanzun? Duk borin da take batajin zata jure rashin Dady matsayin uba tabi duniya, tana razanasu ne dan suji tsoro su kashe auren.
Ƙafafunta gaza ɗaukan ta sukayi ta sulale jikin ƙofar tana rintse idanunta ta fashe da kuka tana haɗe hannayenta tace.
”Don ALLAH Dadyna karka tsaneni saboda wannan mummunan ƙaddara auren wallahi nima bana so kai kafi cancanta ka zauna matsayin ubana Mamy uwata, wallahi idan na rasaku matsayin iyayen na mutuwa zanyi saboda zuciyata bugawa zata yi, don Allah Dady ka taimaka ka rabani da wannan auren nasan zaka tausaya min na kasance matsayin ƴarku ta har abdan.”
Ta ƙarashe maganar cikin wani irin matsanancin kuka.

Manyan fararen idanunsa ya lumshe ya buɗe sabida yadda yake jin zafin kukan nata, ba wasa cikin muryansa anitse yace.
”Yeah haka ne taso zo daughter.”
Cikin wani irin farin ciki da taji yana ratsata, jin ya kirata daughter ta buɗe idanunta wanda suka kumbura ta miƙe daƙyar ƙafafunta suke ɗaukanta tana tangaɗi ta nufi wajansa tana kuka mai tsuma zuciya.
Mamy tayi ɗanyi murmushin farin ciki, ta miƙa ta nufi ƙofar dan ta basu dama su tattauna.
Hannayensa ya ware mata tare da faɗin.

”Welcome daughter.”

Wani irin shigewa jikinsa tai tana sake sakin sabon kuka mai sauti.
Ƙofar ta buɗe ta fice ta rufo daga waje, ta jingina jikin ƙofar tana rufe idanunta, kafin tai saurin saitai nitsuwarta ta nufi office ɗinta.

Hannayensa ya kulle bayanta ya shiga bugawa ahankali cikin sigar lallashi, cikin kamewarsa yana faɗin.
”Ya isa kukan daughter, bana son wani kuka anan kuma, me kikeso ayi yanzu?”

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana lafewa jikinsa, muryanta a shaƙe kalar tausayi tace.
”Dady! Araba auren ni ƴarka ce idan bana matsayin ƴarka zuciyata bugawa zata yi, haka jama'ar gari da sauran ƙasashen duniya zasu tsine mana suce na auri ubana, Mamy kishiyata wallahi bazan iyaba ka auramin kowaye na aminci Dady.”
Ta faɗa tana sake ƙanƙameshi, tana sakin kuka mara sauti.
Shattima ya fesar da zazzafan numfashi ya janyeta daga jikinsa yana riƙe da hannunta ya nufi gadon yana cewa.

”I know”

Zaunar da ita yay saman gadon ya zauna kusanta riƙe da hannunta ɗaya, ɗayan yana share mata hawayen cikin kamewarsa anitse yace.
”Za'ayi yadda kikeso daughter, amma sai kin nutsu, bana son sake jin wani kukan kuma, ko bori akan batun,kar kuma naji ko ganin kin ambaci batun wani aure tsakaninmu nna ki share maganar, kamar ma ba'ayi ba, kici gaba da min kallon Dady bana son ki canza komai na baya haka zai saka liman ya raba auren tinda daman shi ya ɗaura, karki kuskura na kama Mamy tana kuka akanki Ok kin ɗaga mata hankali akan auren, kiyi shiru karki sake tayar da maganar zakiga abinda zanyi kin fahimci maganata?”

Idanunta masu haske da sheƙi wanda suka kumbura sukayi jajir ta kafa masa.
Hiramin kansa wanda yay bala'in Masa kyau ta sanya hannun ta gyara masa tana kallon ƙwayar idanunsa, ashagwaɓe tana langwaɓar da kanta gefe tace.
ALLAH Dady da gaske kake?”
Cikin basarwarsa ya saki hannunta ya miƙe tsaye cikin kamilar muryansa mai sautin daɗi ya furta.
”But mubar maganar tunda ina miki ƙarya Baby.”

Ganin yanayinsa ba wasa zai miƙe ta cakumo shi tana mannewa ƙ'irjinsa ta sakar masa kuka.
Shattima ya rintse idanunsa cikin ransa yana faɗin.
”Ya RAHMAN!”
Ƙoƙarin janyeta yake taƙi tana kukan.
Fizgota yay yana riƙe kafaɗunta cikin sigar lallashi yace.
”Baby! Ki nutsu kuka-kuka yayi yawa meye ne wai Khairy? Meke damunki ne? Bayan fitinar rigimar auren sai me kuma wai? Kina buƙatan sakamin damuwa da kukan kin nan?”

Ya mata tambayar yana tsareta da kaifafan idanunsa. Abinda zai baka mamaki baka isa ka gano asalin meye a fuskar ta shi ba, sbd babu wani alamun ɓacin rai yay maganar.

Ƙasa jure kallonsa tai tana sadda kanta ta tura kanta ƙirjinsa tana girgiza kanta,

tare da cewa.
”Please Dady kayi haƙuri na amince zanyi yadda kace wlh bazan kuma tayar da hankalina ba, ka auramin kowaye da kaga ya dace dani, na daina kuka ko surutun ni na warkema sai goshina da yake min zafi mutafi gida kayi haƙuri Dadyna karka shiga damuwa, kalla ka ga kamar ya kumbura goshina Dady zafi nake ji ka cire min zafin kaji.”

Ta faɗa cikin son ta saki kukan amman ta jure sabida bazata yi abinda Dadynta zai shiga damuwa ba.

Ta kamo hannunsa ta ɗora agoshinta.

”Ya SALAM! ”

ya furta ya janyeta ya zaunar da ita, yaja kujera ya zauna yana riƙe kanta yana taɓa goshin wajan da aka liƙa mata bandeji, ya shiga hura mata iskar bakinsa yace.

”Akwai zafi ne daughter?”

Ashagwaɓe ta ɗaga kanta tana kallon ƙaramin bakinsa yana hura mata iskar bakinsa mai fito da sansanyan ƙamshin Mint.
Kwantar da ita yay yana lulluɓeta cike da kulawarsa a kanta anitse Yace.
”Bari na kira Mamynki ta dubaki Ok?”

Hannunsa ta riƙo idanunta lumshe ta cinno baki gaba, tsabar daɗin ya kira Mamy mamarta ne taji sabuwar shagwaɓa tazo mata.

Anitse yace.
”Me kuma?”
Kai tsaye tace.
”Dady shagwaɓa nake ji sosai ALLAH ya saka na zauna matsayina na ƴarku.”

Kanta ya shafa ya zare hannunsa da yake cikin nata,yana gyara mata kanta, cikin kamewarsa da kulawa akanta yace.
”Oya kimin shiru da bakinki nan idan Mamynki ta shigo, ki sakama bakin ki linzami bana son naji bakinki anan idan Mamynki ta shigo ko su Baffa wallahi zan ɓata miki rai Ok?”

Kai ta jinjina tana rufe idanunta.
Anitse ya nufi ƙofan ya buɗe ya fice.

Khairy ta miƙa zaune tana mai jin farin cikin da nitsuwa akan Dady na matsayin mahaifinta Mamy mahaifiyarta.
Kai tsaye office ɗinta ya nufa.
Murɗawa yay ya shige bai tsaya knocking ba.
Tana zauna saman darduma ta gama sallar isha'i.
Kallon ta yake cike da ƙauna ya iso ya zauna saman darduman yana matseta jikinsa.
Lafewa tai tana sakar masa kyakkyawan murmushi ta shafi gefen fuskarshi, ta saita nutsuwarta murya mai taushi ta manna bakinta kan kunnensa tace.
”Ya Babynmu fatan ka samu ka lallasheta ta amince zata zauna da mijina matsayin mijinta...?”

Shattima wani yarrrr yaji, yay saurin janyo kanta ya rufe mata baki yana faɗin.
”Oh! My God!
Sweetheart! Kiyi shiru kinga na lallaɓata ina nan matsayin Dadynta, Please karki wani mata maganar shareta Ok?”

Mamy idanunta ta lumshe tana goga tsinin hancinta saman tsinin hancinsa, ta zagaye bayansa da hannayenta, ta zaro harshenta tana lasar lips ɗisa tana sauke wani irin lumfashi.
Kallon ta yay yana son ya mata maganar Khairy suje ta dabuta sai kawai yaji shakkar mata maganar ya rasa dalili.
Gyara mata kanta yay yadda zata ji daɗin yin duk abinda takeso, yana mai rungume ƙaramin ƙugunta.
Anitse yaji ta kamo laɓɓansa biyun ta riƙe cikin bakinta, ta tura masa harshen ta.
Yana shirin tsotsa sukaji an turo ƙofar an shigo....

Rahma Oum Farisah


_*YI WA KAI!*_

_November 22/11/2022_

_Free Novel_

_Wallahi kowa ya rasa masoyi yayi kuka.😭Jama'a Rahama ce, haƙiƙa naga ƙaunarku da kulawa ƴan social media, masu kirana da masu min magana ta whatspp da masu turamin sakon messages Nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi, duk wacce taga ban buɗe saƙonta ba tayi haƙuri don ALLAH🙏🏽 Allah ya jiƙanki Aishatou, yasa halinki nagari ya biki, ALLAH ya amshi shahadarki Amin, Allah ya raya mana Nana A'isha me sunanki.🤲🏼😭_



*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*63&64*


Da sauri Shattima ya zare bakinsa daga na Mamy, ya waigo dan ganin waye haka ba tarbiyya, kai tsaye zai shigo musu ba neman izini.?
Da Maryam suka haɗa idanuwa, wadda ta gama gigecewa da tsoron abinda da ta gani, ga kunya ta baibayeta, sai kuma kishin sa da taji har cikin ranta, ganin Shattima da Mamy a yanayi na soyayya.
Da sauri ta kauda kanta ta juya cikin inda-inda tace.
”I'm sorry Dady and Mamy, nayi kuskuren shigowa ba tare da neman izini ba.”
Ta faɗa tana buɗe ƙofar da sauri ta fice.

Mamy ta sauke numfashi mai ɗumi tare da lumshe idanunta, ta buɗe tana janye jikinta ta miƙe tsaya tana kallonsa tana lumshe idanunta, ba tare da ta iya cewa uffan ba.
Miƙewa yay anitse yana gyara hiramin kansa, ya matso dab da ita, ya sanya hannunsa ya riƙo ƙugunta ya matsota jakinsa, yana mata wani irin kallo ƙasa-ƙasa, tare da hura mata iskar bakinsa, saman idanunta da ƙofofin hancinta.
”Uhmmm! Mi Amor muje koh?”
Bakinsa saitin kunnenta ya hura mata iska anitse cikin kamewarsa ya furta.
”Ba fa kiyi abinda kike muradin ba zamu tafi uhmm?”
Mamy ta kalleshi cike da ƙaunarsa tana mamakin sauyawar tashi lokaci ƙanƙane.
Murmushi tai ahankali ƙasa² tace ɗan duƙo kaji Mi Amor.”
Yana rankwafowa daidai tsayinta ta manna masa kiss kan tattausan lips ɗinsa tace.
”I love you Khatir.”
Kaifafan fararen manyan danunsa ya jujjuya, mata wanda hakan yakusa makantar da ta ita sai da ta runtse idanunta.
A tsakiyar kunnenta ya raɗa mata.
”love U too sweetheart.”
Ajiyar zuciya ta sauke tana janye jikinta ta ɗauke darduman ta linke ta ajiye ya kamo hannunta suka fito ta rufe office ɗin suka nufi wajan Khairy.

Maryam kuwa tana fitowa daƙyar ta maido kanta, wajan Khairy'n daman ita ce ta aike ta kiran Mamyn wai goshinta na mata zafi.
Kahiry zaune tana shagwagwaɓe fuska, Nafisa na mata sannu da Auntie Balaraba wacce ta beƙe mata tea mai kauri wanda Mamy ta kawo mata tace.
”Maza ki sha mana kafin Auntie Billyn ta shigo.”
Ashagwaɓe tace.
”Ni bana sha baki ɗaci goshina ciwo yake min bari Mamy tazo ta dubamin.”
Ta faɗa kamar zatayi kuka tana kallon hanya.
Maryam ce ta buɗe ƙofar arikice ta shigo tana maida numfashi.
Auntie Balaraba tace.
”Maryam! Lafiya? Ya dai naganki arikice?”
Saurin sakawa kanta nutsuwa tai, tana ƙirƙiro ƙarya tana takawa wajansu tace.
”Wlh Auntie wani mutum ne ya biyoni yana min mgna sai naji kawai zuciyata bata aminta da shi ba, shine fa na taho da gudu.”
Dariya Balaraba tayi Nafisa na tayata..
Khairy ta ɓata fuska tana faɗin.
”Kenan baki kiramin Mamy ɗin ba?”
Maryam tace.
”Na kirata mana suna zauwa Nafisa mutafi gida Aunt Khairy gobe zamu dawo Ammi tace karmu daɗe..”
Khairy tace.
”Ok Ngd amman kuje gida yanzu tafiya zamuyi, Amman ki jira Dady da Mamy su zo ku gaisa mna.”
Maryam ta daburce dan bata son Mamy da Shattiman su ritsa su.
”Aunt ai mun gaisa fa acan ai goben zamuje gidan insha ALLAH.”

Khairy tana dafe goshinta sabida ciwon da kanta yake mata tace.
”Ok Allah kaimu ki gaishemin dasu Abba.”
Maryam tana ficewa tace.
”Tom zasuji.”
Balaraba tace.
”Toh kici dambun naman da suka kawo miki kafin Auntie ta shigo ta dubaki.”
Fuska ta yamutsa kamar zatayi kuka ta buɗe baki zatayi magana Shattima da Mamy suka shigo.
Kallonta ta maida kansu tana karya wuya hawaye sun cika mata idanu, tana kallon Shattima.
Shattima ya zuba hannayensa cikin aljihu,yana hararenta da idanu yana hanata fito da hawayen.
Hawayen ta maida tana sadda kanta tana sake dafe goshinta.
Ashagwaɓe tace.
”Mamy kaina ciwo Maryam sun tafi gida wai gobe zasu je can gida.”
Mamy ta girgiza kanta, tasan kunya ta hana Maryam zama.
Basar da zancan tayi tace
”Sannu Baby mugani akwai zafi sosai?”
Ta faɗa tana isowa ta shiga dubata.
Shattima ficewa yay ya nufi wajansu Liman.
Dressing ɗin goshin ta sake mata tare da mata allura cikin dubara daƙyar.
Dole Mamy taje tama su Liman bayanin Khairy sai ta sake kwana sabida ciwon kanta.
Dole kowa ya tafiyarsa daga Shattima sai Mamy da Inno tace ita zata kwana Khairy da wuri tayi bacci.
Kusan 12 na dare Shattima da Mamy suka tafi gida.

Lafiyayyan wajan shaƙatawa Salim ya nufa, yana zuwa yay parking ya fito wajan da ba hayaniya ya nufa, ya zauna abun sha kawai ya buƙata.

Azizah ta iso wajansa taja kujera ta zauna, tana kallonsa tace.
”Sabida zaka faɗa min wani abu shi Kenan sai ka raina min hankali? Toh gani na biyoka faɗa min me kasani agame da mutuwar Abdoul ?”

Salim ya tura mata sansanyan ruwan yana murmushi yace.
“Jiƙa maƙoshin ki muyi magana,kibi asannu ba'a ɗaga min murya nafiki iya duk abinda kikeji, but ba wannan ba muyi abinda ya kawo mu, inaso sanar dake akan wanda ya kashe saurayinki ba kowa bane sai mijin da ta aura yanzun, dan haka ya rage naki kiyi ƙwaƙwaran bincike ki san wanene ki ɗauki fansa, ni nan zan kama miki da zaran kin gano waye ki kirani .” mu haɗu mu yaƙe shi tare."
Azizah ta share hawayen da ya wanke mata fuska tana miƙewa tace.
“Nayi maka alƙawarin samosa duk inda yake, ko mu dakata har lokacin da zasu tare gidan aure su.”
Salim yace.
”Shi kenan Ni dai duk lokacin da zaki ɗauki fansa ki ɗagamin hannu.”
Wayanta ta beƙa masa tace.

”Sakamin lambar ka faƙat.”

Lambar ya loda mata ya bata wayanta ta tafi abinta, ranta a ɓace...

Washegari sai lokacin tashin Mamy daga aiki suka taho da Khairy, taji sauƙi sosai, ta cire mata bandage, goshin ya Dan kame.
Liman yaso sutafi gidansa da Khairy taƙi tace tana wajan Dady da Mamy, dan tahau kan huɗubar Shattima ta zauna har yanzu zaman ƴarsu take tama manta batun wata matarsa take har ranta kwatakwata ta shafe babin.

Ajiya Maryam bacci sai ɓarawo ya ɗauke ta da zaran ta rufe idanunta bakin Shattima take gani, wanda yake cikin na Mamy, suna rungume da junansu, abun sai ya zama kaman mai kamun aljannu haka ta dinga zabura tana rintse idanunta, tana jin wani irin abu mai tsananin girma acikin zuciyarta, tayi kuka sosai har sai da kanta yayi ciwo, batasan yadda zatayi da ciwon son Shattima ba, abun sai ya lafa sai ya dawo ta yarda soyayyarsa tayi mata mugun kamu.
★★★

Yau ta kama juma'a
*Kaduna*
6 am.
Usman cikin shiri ya fito sanye da wani boyel Green colour, ɗinkin ya masa kyau, sosai yau zallar kamar su ta fito da Khairy.
Falonsa ya rufe ya zare key ɗin hannunsa riƙe da darduma, ɗayann kuma yana amsa waya anatse.
Sai da yaje ya buɗe gate yazo ya shiga mota ya fito waje ya fita ya kulle gidan ya shiga motar yana karanto addu'ar bulaguro, yaja motarsa ya harba bakin titi.
Wayasa ya ɗauka yana tuƙinsa an natse, ya lalubi number mahaifinsa ya danna masa kira.
Alokacin acan Gumel shigowar Mustapha kenan gidan daga masallaci.
Zama yay gefen bed ɗinsa ya ɗauki wayan tare amsa kiran, yana dafe kansa saboda wani irin sarawa da yake masa ayau ɗin, ga wani yanayi da yake ciki baima san wane yanayi bane ba. Sallamar Usman ya amsa yana saita nutsuwarsa yana tambayar sa.
”Usman! Ya Kaduna? Fatan kana lfy?”
Usman ya amsa.
“Alhmdulillah Dad ya gajiya kazo lafiya? ”
“Alhamdulillah Usman fatan komai lfy?”
“Lafiya lau Dad, yau insha ALLAH ina shigowa komin dare, ina Mom da Nadiya?”
Mustapha ya amsa da.
“Masha Allah, sai kazo Allah ya tsare ya kawo ka lfy, duk suna lfy.”

Hira sukayi kaɗan bayan sunyi sallama Mustapha ya kwanta kaɗan sabida azababban ciwon kan da yake damunsa...

Hajiya Karima kamar an tsikareta ta miƙa daga baccin da take tana haɗa uban gumi.
Dirowa tayi daga kan bed ɗin arikice ta nufi wajan da ta saka wayanta change ta cirota, hannunta yana rawa ta shiga ma'adanar lambobi ta lalubo wata lamba wacce akayi saving da YANKAN WUƘA.
bugu ɗaya biyu uku sai ana huɗu aka ɗaga ana kecewa da dariya tare da faɗin.
"Saura ƙiris ki makara kin makara Karima wane ganganci ya kaiki wannan gidan ɗanki yana hanyar zuwa gidan shima sannan ayau idan baki gaggawar kawomin baƙar jaka mai tsohon ciki da baƙar tumkiya mai sabon ciki, sai maniyin kuturwa wacce bata fi shekaru 27 ba a haife, ki gaggauta cikin awanni 3 komai zai runcaɓe, aljani KASUBU ASAKA zai gudu yabar jikin Mustapha matukar ayau Usman yaga Zainabu, daga nan kuma kinsan me zai biyu baya...."
Karima ta fasa wani irin ihu jikinta na rawa tace.
"Faɗi min nawa zan biya asamo komai cikin gaggawa taimaka min kar zuciyata ta buga ayau?"
Dariya yay yana faɗin.
"Kin manta ranan da na faɗa miki sharaɗina? Dole wannan abubuwan kece zaki samosu cikin awanni 3 kacal ki hanzarta."
Kashe wayan tayi kai tsaye ta kira wata lamba bugu ɗaya aka ɗaga cikin tashin hankali tace.
"Asamomin baƙar jaka mai tsohon ciki da baƙar tumkiya mai sabon ciki da maniyin kuturwa nan da awa biyu ga Naira miliyan ɗaya kash."
Wani irin ihu akayi daga can mai ihun ya amsa da.
"An gama bani awa ɗaya da rabi Amman aikomin kuɗin kash yanzu."
"Ajiyar zuciya ta sauke tace.
"Ok yanzu zan fito da kaina na kawomaka da kaina ba saƙo ba."
Ta katse kiran jikanta na rawa ta buɗe dirowa kuɗin da ta amsa jiya hannun Alhaji Mustapha kash Naira miliyan ɗaya ne da dubu ɗari biyu da hamsin.
Dubu ɗari biyu da hamsin ɗin ta cire ta zura hijab ta ɗauki key ɗin mota jikinta na rawa ta fice.

*Dutse*
Commissioner quarters.
Mamy tin 7 ta kammala musu breakfast su Laraba sun shirya komai a dining room, sun gyara kitchen, suka shiga gyaran falo.
8 Mamy ta kammala shirin zuwa wajan aiki saboda yau da wuri take saukowa kuma tanada operations 3 wanda ita ce zatayi su, Khairy nacan ɗakinta tana bacci.
Tsaye take a bedroom ɗinsa, dab da kasan tana sakin murmushi ganin yadda yake baccinsa anatse, kamar ba wajan aiki zai fita ba.
Idanunta ta lumshe ta buɗe ta zauna gefen bed ɗin, ta shafi gefen fuskarsa, ta sunkuya ta sumbaci lips ɗinsa, ta kwantar da kanta saman ƙirjinsa.
Batasan idanunsa biyu ba, tinda ya fito daga ɗakin motsa jiki bai koma bacci ba.

Sanye take da doguwar riga ta shaddah blue ɗinki baida hayaniya ya zauna mata daram a siririn jikinta mai mutaƙar kyau, ta murza ɗauri ta yafa babban mayafi blue takalmi blue jakarta ma haka, abinka da farar mace, MASHA ALLAH tayi bala'in kyau, sai ƙamshi takeyi bazawa.

Sumbatar tsakiyar ƙirjinsa ta yi, tana ƙoƙarin janye jikinta daga nasa taji ya ƙanƙameta, yana mata wani irin sihirtaccan kallon ƙauna da lumsassun kaifafan idanunsa.
Ƴar dariya tai mai ɗan sauti akasalance tace.
”Good morning Mi Amor na kammala maku komai nayi lati, bara na wuce, akulamin da my Baby idan ta farka kafin ka fita, Please ka mata da gaske ta sha magungunan ta.”
Shattima ya kamo lallausan laɓenta ya ɗan ciza kaɗan, can ƙasan maƙoshi cike da kulawa ya mata magana.
”Kiyi aiki cikin nasara ALLAH ya biya ki da taimakon da kikeyi, ki kular min da kanki, i love You, fatan kiyi breakfast?”
Sansanyan ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi tace.
”Ameen mi Amor please kaci abinci sosai Baby ma haka Ok?”
Bai ce mata uffan ba, sai kissing mai saka nishaɗi da kasala ya sakar mata tsakiyar bakinta, ya ɗaga mata gira ɗaya, ya lumshe idanunsa, anitse ya furta.
”Allah dawo dake lafiya ya miki albarka.”
Gefen fuskarsa ta shafa tana amsawa da.
”Ameen mi Amor...”

Sai da ta biya ɗakin Khairy taga tana baccinta A natse, ta fice.
Agurguje tayi breakfast, ta fice a gidan cikin motar ta.

10am, Shattima ya fito falonsa anitse cikin shirinsa na juma'a, yana zuba wayoyinsa cikin aljihun babbar rigarsa.
Sanye da wani farin boyel mai shegen kyau da tsada, kana kallon boyel ɗin da ɗinkin wanda ya zauna jikinsa, kasan Naira tasha kashi awajan.

Sosai yay kyau, ɗinkin ya masa kyau duk manyan ɗinki ne irin nasu na Ministers, kansa sanye da haɗaɗɗiyar hula wacce saƙarta ta saƙu ta amsa sunanta hula, wacce kana gani kasan an kashe kuɗi wajan mallakarta.
Dogayen ƙafafunsa sanye da rufaffan tsaddan takalmi baƙi, sai wani ƙyalli yake, hannunsa ɗaure da agogon zallar fata mai tsada sai yatsunsa sanye da zubuna gold da azurfa guda uku a jere.
Wani fitinannan ƙamshi yake tashi ajikinsa mai sanya nutsuwa da kwanciyar hankali.
Tafiya yake cikin nagarta da kamewarsa da ta zauna ajikinsa.

Dole awannan lokaci Shattima ya burgeka sabida irin yadda shigar tai masa kyau, ta ƙara fito da tsananin kyawunsa da kwarjinin sa da nagartarsa.
Yana zuwa dab ƙofar ɗakin Khairy bai wani waigoba ya wuce abunsa, anitse.
Ihun yaji har tsakiyar kansa, tana kiransa tare

Please Login or Register in order to submit comment