Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inaso ganinta yanzu-yanzu."
Usman cike da mamaki yake faɗin.
"Dad! Aure kuma? Ka manta irin abubuwan da suka faru ne? Ka fa saketa saki uku, tare da koran kare..."
Tsawa ya daka masa da ƙarfi, wanda ya saka Nadiya kusan fita daga motar bata shirya ba.
"Nace muku Ni wallahi tallahi ban saketa ba! Kana ina?"
Usman yace.
"Ina commissaire quarters."
Ya kwatanta masa ta ɓangaren.
Yace.
"Ok gamunan yanzu."
Ya faɗa yana katse kiran.
Usman kansa ya dafe yana sauke numfashi mai zafi.
Doorbell ya danna yana saita nutsuwansa.
Kusan mintina 2 kafin Laraba ta buɗe masa ƙofar tana gaishesa, ta matsa ya wuce.
Har duk yadda yake tunanin Dad ɗin su ya tsara musu falo da yaga wannan yasan gaba da gabanta, wai aljani da ya taka wuta.

Baki ɗaya ta shagwaɓe tana narkar da fuska, hawaye har sun fara saukowa kan kumatun ta.
bata motsa daga inda take ba, amman ta kafesa da matsagaitan fararen lumsassun idanunta, da suka fara Ja.
Kanta da ko hula babu gashinta duk ya barbazu saman kafaɗarta, dalilan yadda ta langwaɓar da kanta gefe, tana son sakin kukan da yake cin zuciyata.
Kansa ya kawar daga kallonta, ya haɗe face, ya fara takawa anutse cikin kamilar muryansa mai taushi da fitar da sauti amon daɗi, ya furta.
"Karma ki kuskura kiyi min kuka anan wajan, me na miki? Ɓace min anan maza kije ki ɗaure kanki, ko ki saka hula bana hanaki zama kanki buɗe ba? Ko bakinsa sheɗanu na samun mafaka ta haka ba?
Maza wuce ki saka hula ko ki ɗaura mayafi"
Ya ƙarashe maganar yana tafiyarsa anutse, ya wuce ta gefenta ya fara taka steps.
Da wani irin gudu ta nufesa cikin wata irin sangarta, ashagwaɓe tana kiransa.
"Sweet Dadynah! Please ka tsaya wlh banida lfy, kaina ciwo, harda zazzaɓi."
Ta ƙarashe maganan cikin kukan shagwaɓa.
Cak ya tsaya yana rintse manyan fararen kaifafan idanunsa, ya furta.
"Ya SALAM! Wai meke faruwa ne haka?"

Ya juyo da saurinsa yana nufo wajanta ganin rikici ya rufe mata idanu, kar taje wajan taka steps ta sulale ta faɗo.
"Sai kin jima kanki ciwo abanza, tunda bakya jin maganata ai. Tun yaushe kike ciwon kan? Baki sha maganin ba koh?"
Ya faɗa yana riƙe ƙarfen, steps ɗin da hannunsa ɗaya, sanin ba tsayawa zatayi ba, kansa zata afka.
Wani irin shigewa jikinsa tai tana maƙaleshi ta zagaye hannayenta tsakiyar bayansa, tana ɓoye kanta tsakiyar ƙirjinsa, tana rage kukan, ƙasa² yake fitowa, tare da sauke ajiyar zuciya ajere-ajere.
Wani irin wahaltaccan numfashi yake tare da furzar da zazzafar iska daga bakinsa, ya fara ƙoƙarin janyeta ta maƙale kafaɗa, tana diddira ƙafafuwanta.
Janta yay suka fara taka steps, tana maƙale da shi, sai da ya kai tsakiya ya janyeta tare da zaunar da ita kan step, ya zauna nesa da ita ta matso ta kwantar da kanta kafaɗarsa, tana rera masa kukan ƙarya da shagwaɓa.
Gyaran murya yay yana kallonta, cikin bata dukkan kulawarsa, muryasa mai taushi da daɗi, anutse yace.
"Yanzu menene matsalan rigiman da kikeyi ne? Muga ina yake miki ciwo yanzun ko kawai dan ki hanani zama cikin nutsuwa daughter?"
Ya mata tambayar yana ɗago fuskarta, yana kallon yadda ta wani narke tana kuka ƙasa², hawaye wani na bin wani, idanunta rufe taƙi ta buɗe, baki ɗaya tana shige jikinsa tayi luf.
"Ya ALLAH!"
Ya furta yana taɓa wuyanta yaji da ɗan zafi kaɗan.
Gashinta ya tattara ya daure mata, anutse ya furta.
"Tashi muje, ina maganin naki?"

Kai ta girgiza tana buɗe idanun nata ta sauke kan kyakkyawar fuskarsa, ta ɗora hannunta saman sajansa tana faɗin.
"Dadynah nasha magani don Allah karka bani magani Mamy taban ɗazu. Yanzu kasala ce take damuna. Dady ina kaje yau tun safe? Dady zaka kaini gidan Baffa yau juma'a kaji?"

"Wayyo Allah nah!"
Abinda Shattima Yake faɗa kenan acikin zuciyar sa, kafin ya tamke fuska, ganin idan ya biye mata za'a iya samun babbar matsala ko Mamy ta gansu ahakan ko Suhailat ƙawarta.

Tsaye ya miƙe ya kamota ta miƙe, yana janye da hannunta ya juya suka koma, suka fara tafiya tana famar kukan shagwaɓar.
Ɗakinta ya shiga da ita.
Riƙesa tayi gam tana ƙara sautin kukan tace.
"Dadynah tsoro nakeji daga ɗakin Mamy na fito zanje ɗaukan fura can ƙasa a fridge, ni bazan zauna nan ba, akwai ƙadangare."
Ta faɗa tana cukuikuiye shi, tana diddira ƙafafunta.
Jarumta da ya saba cikin kwanakin nan ita yanzu ma ya aro ya sakawa kansa tare da basar da komai, ya ɗago kanta.
Anutse murya me taushi, yana kallonta tare da goge mata hawayen fuskarta, da tafin hannunsa yace.
"Ok Baby naji kije ɗakin Mamy ɗin zan turo Laraba ta kawo miki furan yanzu Ok?"
Kai ta jinjina, tana damƙe hannunsa cikin nata, tana kallon sa ahankali tace.
"Sweet Dady! Idan kamin aure zaku dinga zuwa kullun gidana kaida sweet Mamy Dan Allah? Kaji? wlh wannan karon Ni zan zaɓi miji ɗan gaye mai wanka irin na Dadynah, amman kuma yaro kamar dai Abdoul ɗina, tunda Ni bazawara ce sai nazaba darje saurayi zan...."
DA wani irin sauri Shattiman ya janyota ta matso dab da shi, har ƙirjinsu na gamuwa yaja baya, da sauri yana ɗora yatsarsa saman bakinta, fuskarsa ba wasa, cikin kamilar muryasa, ya furta.
"Wallahi idan na kuma jin irin zancan shirmankin nan ko awani wajan, zan ɓata miki rai, wai ke bakisan kin girma bane? Wuce min anan tun ban ɓata miki rai ba. Kije maza ki nemi guri kiyi bacci. Kuka ko hawayen ki suka zuba zan gane zakiyi sati baki ganin da idanunkin nan, da basa kunyata ba!"
Ya faɗa yana jan hannunta ya fito da ita.
Ƙanƙame hannunsa tayi hankalin ta tashe, murya na rawa tace.
"Don Allah Dady kayi haƙuri wlh bazan sakeba kuma ba zanyi kukan ba, kaji?"
Kai ya ɗaga yana zare hannunsa daga nata, yace.
"Shige maza ki kwanta za'a kawo maki furan marar jin magana, idan kin kuskura gaban Mamynki kin ganni kina langwaɓe wa ko shigemin duka zan miki."

Khairy tai rau-rau da idanunta, sai tai saurin maida ruwan ƙwallan tace.
"Toh Dady, kayi haƙuri na tafi."

Tana tafe tana waiwayensa har ta shige, ta rufo ƙofar kafin ya sauke numfashi mai zafi ya juya ya nufi stairs, yana gyara rigar jikinsa da Khairy ta gama hargitsa masa ita.

Anutse ya sauko tsararren falon, da Mamy ta turaresa da turaren wuta mai shegen daɗi.
Usman yana hango Shattima ya miƙe yana faɗin.
"Yallaɓai sannu da fitowa."
Shattima ya basa hannun sukayi musabaha, anutse yace.
"Afuwan na barka ban fito da wuri ba, Bismillah muje muyi abinci."
Usman ya sosa kansa yace.
"Yallaɓai daman Dad ɗina sun iso suna bakin gate, kayi haƙuri na tsallake umarni ka."
Shattima ya ƙura ma Usman lumsassun idanunsa, anutse ya furta.
"No! Ba komai karka damu."
Ya faɗa yana zaro wayansa daga aljihu ya kira wata lamba bugu ɗaya aka ɗaga anutse ya bada umarnin a shigo da baƙin da suke bakin gate har ƙofar babban falon gidan.

Yana katse kiran, ya kira Laraba.
Anutse tazo ta zube can nesa tana gaishesa.
Ba tare da ya kalletaba ya amsa yana faɗin.
"Yawwa ki ɗauki fura a fridge ki kaiwa Baby tana ɗakin Mamynta."
Cike da girmamawa ta amsa da.
"Toh."
Ta miƙe dan cika umarnin mai gidan.

Minti huɗu ba'a rufe ba aka danna door bell ɗin falon.
Shattima ya miƙe da kansa yaje ya buɗe ƙofan.
Dad Mustapha da Nadiya tsaye, copy Khairy sak baiga wani banbancin su ba!
Fuskarsa ya faɗaɗa fara'asa, ya baƙi wa Dad hannu sukayi musabaha, anutse yace.
"Barkan ku da zuwa bismillah."
Nadiya ta gaishesa yana rusuna cikin girmamawa, aranta tana faɗin.
"Wow! Kuji dattijo da kyawu ga iya saka kaya masha ALLAH."
Shattima ya amsa gaisuwarta cikin sakin fuska ya basu hanya suka shigo.
Dad Mustapha na faɗin.
"Nan kenan Usman da Zainabu suke?"
Shattima sai da furzar da iska mai ɗumi waje a tausashe yace.
"Eh Usman na nan ita kuma za'a kaika wajanta."

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah shine abin Godiya."
Usman ya miƙe rungume mahaifinsa yana masa sannu da zuwa.
Ya kalli Nadiya yace.
"Ke kuma meye na biyo Dad?"
Dariya tayi lokacin da idanunta suke sauka akan wani tafkeken hoton Khairy tana sanye kayan sanyi tana dariya.
Sai wani su uku Shattima da Mamy sun sanyata tsakiya ta rungumesu tana faman dariya su kuma sun kafa mata idanu.
"Lah Dad! Yaya Usman! Ku kalli wata me kama damu wlh."
Dad kansa sai da gabansa ya faɗi, ganin Khairy.
Yace.
"Ikon Allah! Kaji kama ba haɗi."
Shattima yay murmushi yace.
"Ɗiyata ce kunga tayi kamanku koh? Toh bismillah ku muje dining muyi abinci sai mu kaiku wajan Zainab."
Dad jin abinda Shattima yace, bai musaba suka ɗunguma kan ƙaton dining area ɗin.

Khairy kuwa tana kwance lamo tayi wani iri da ita, furan ma bata sha da kirki ba, bacci yayi awon gaba da ita.

Mamy bacci takeyi sosai abunta hankali kwance ta shige tattausan bargon Shattima mai wani irin taushi da ƙamshinsa.

Suhailat kuwa kallon film take abunta na ƴan Ghana.

Can ƙasa bayan sunyi lunch sun gama suka dawo falon, Shattima ya saka Laraba ta kawo musu abubuwan motsa baki, ya miƙe ya haye upstairs, sabida Kiran La'asar da ake.
Mamy na Baccinta anutse, yay alwala ya fito ya canza kayan jikinsa, zuwa wani yadi mai taushi da tsada, shima fari ƙal ya zauna gefen bed, ya shafi fuskarta ya sunkuya kanta ya zaro harshensa ya zura ƙofar kunnenta.
Wata irin zabura tayi tana riƙe kansa.
Ya sakar mata tattausan murmushi, yana ɗaga mata gira, anutse cikin taushi murya ya furta.
"Ana kiran sallah baccin ya isa haka Sweetheart, mahaifin Usman da ƙanwarsa suna ƙasa zamuje can wajan Zainab, a shirya girki me kyau na dare zamuzo har Zainab ɗin, bye sai na dawo."
Ya faɗa yana sumbatar kumatunta bai jira tace komai ba, ya fice.
Ta miƙa akasalance ta sauka ta shiga bathroom.

Nadiya nan ƙasa Shattima ya nuna mata wani tsararran ɗaki ta shiga ta ɗauro alwala tayi sallah.
Suna fitowa daga masallaci Shattima yazo ya kirata suka shiga mota sai tafiya wajan Zainab.

Mamy da ƙyar ta tashi Khairy tayi sallah saboda baccin da yake idanunta, Suhailat ba irin tashin da bata mataba taƙi tashi.
Suhailat da take zaune gefen bed ɗin Mamy dan bazata iya kwanciya bisa best ɗin Mamy ba.
Tana kallon Khairy wacce ta koma ta kwanta tace.
"Besty baki faɗa min abinda zaki faɗa min ba? Ba fa zankai Maghreb ba, zan wuce fa! Dan haka tashi muyi magana."

Khairy ta sake narkewa tana ƙara shigewa cikin tattasan zanin rufan tana jin wata irin kasalar da ƙamshin Dadynta ya saukar mata.
A hankali ta furta.
"Kinsan da an sake ɗaura min aure, amman inaga an rabasa, ko ana shirin rabawa, dan abin bai wani dace ba Ni bazawara nake jina fa."

Suhailat ta dafe ƙirjinta tace.
"Kai! Haba dai? Da wa kuma?"
Khairy ta miƙe zaune tana rau-rau da idanunta, ta karya wuyanta tace.
Wani ne yakai sa'an Dadynah har kamewarsa tsaftarsa gayunsa kyansa ƙaramin jikinsa ba ƙiba tsayinsa MASHA ALLAH, kwatancen sajansa yawan suman mai taushi, rashin son damuwa,.da rashin hayaniya,ke komai da kika sani kaman Dadynah yake har muƙamin su da baƙar fatarsa mai kyau da hutu duk ɗaya ne, ya zanyi araba auren koh...?"
Baki taji Suhailat ta buge mata da ƙarfi, sai da ta saki ƙara, tana riƙe wajan.
"Ashe ke kam bakida hankali? Awannan zamanin ne zaka samu miji me irin halayyar Dadynki kice bakyaso araba auren? Toh ki auri uban wa? Kul wlh karki kuskura ma ki fara hakan babban kuskure zakiyi wlh, tabb idan nice ma tuni zance a tare wlh ina so kan uba irin Dad Shattima fa kikace?"

Khairy ta ɗaga kanta tana son sakin kuka tace.
"Besty kina nufin na so shi muyi SOYAYYA irin yadda kowasu masoya suke yi, me cike da kulawa? Kina nufin na basa zuciyata kamar yadda Naba Salim, abaya kafin nasan asalin haliinsa na tsane shi? nayi zaman aure da shi irin na kowasu ma'aurata? Wayyo Ni bazan iyaba akwai kunya sosai fa! Dan bakisan asalin waye mijin nawa ba, wayyo matarsa mamana ce fa!"
Suhailat tace.
"Don Allah besty karki zauna da shi ɗin ki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, Ni wallahi idan yanada dukkan abinda kika lissafa irin na Dady Allah idan bakya sonsa haɗani da shi zan auresa...."
Khairy da sauri ta rufe bakin Suhailat tana girgiza kanta, tace.
"Besty ki sakawa bakinki linzami, ya isa haka, bazan iya zaman aure da shi ba, kuma wallahi ba shegiyar da zata aurenmin ubana a barsa da Mmayna ta ishesa rayuwa Ah toh."

Suhailat ta buge mata baki tace.
"Bakida hankali ne? Ni fa Ba Dady nake nufi ba, ai wlh Mamy ta wuce naci amanarta da anjima da wuce wajan, Ni ina nufin shi mijin naki idan bakyaso ki ba masu so.,"
Khairy tace.
"Besty mubar maganan haka tashi mu sauka ƙasa wajan Mamy."
Dariya Suhailat tayi tace.
"Wlh ko waye kina sonsa besty ki gama munafurcin ki dai."

Khairy batayi magana ba ta ɗauki wayanta ta lalubo lambar Shattima wacce tayi saving da Sweet Dady da manyan harufa.

Acan kuwa ɓangaren su Shattima,
Ƙarfe huɗu da rabi da minti shidda suka isa masaukin su Zainabu, wanda suke cikin shirya kayansu gobe da asuba zasu wuce, yanzu an abinda yasa bazasuyi tafiyar yamma ba saboda ance masu hanyar yau akwai haɗari binta da dare nan, sai dai sun iske tashin hankali an nemi Zaunab an rasa sama da ƙasa.
Nan megadi ya faɗa ya ganta ta fice kamar da wani abu ahijabinta tun tashi daga sallar juma'a.
Ai kuwa Dad Mustapha ya rikice yace yanzu kai tsaye Usman ya shiga suka kama hanyar Katsina, daƙyar Shattima ya sa kansa ya amince zuwa asubah har da shi zasu tafi, kafin ya samu ya amince.
Da faɗin.
"Wlh ganin kimarka Minister yasa zan haƙura har goben da asuba da ayau ko gawata ce sai ta shiga garin Katsina."

Shattima da kansa ya buɗe masa mota, yana sakin ƙayataccen murmushi, anutse ya furta.
"Na gode sosai."
Ya faɗa yana ganin zallar rikicinsa ashe Khairy wajan Dadynta ta kwaso daru sai dai ita batada faɗa, asalima tsoron faɗa take,barta da rikicin rigiman sangarta.
Wani irin murmushi ya kuma suɓucewa Shattima har yana shafo gefen sajansa.
Daidai zai shiga mota kiran Khairy ya shigo wayansa.

Ganin ita ce ya kasa basarwa ya shiga motar kansa tsaye yana ɗaga kiran.
"Na'am Baby."
Da wani irin shagwaɓa tace.
"Dadynah! Wai mijina idan irinka ne abin sone karna rabu da shi inji Suhailat, wai ka haɗu ta ko ina, na so abuna mu zauna tare, idan bana so naba masu so, don Allah kaji da Dady, Ni kuma nace mata..."
Da sauri Shattima ya rintse idanunsa tare da furzar da iska me ɗumi, yana faɗin.
"Please ya isa hakan ki nutsu ki kame bakinki, tun ban ɓata miki rai ba, na ƙune bakin da wuta kowa ya huta, ina tare da baƙi bari idan na dawo zan kiraki, ki keɓe zamuyi magana, kul naji kin kuma yin wata mgna akaina zan fahimta da zaran na kalli bakin ki da baida wayo..."
Bai jira me zata ceba ya katse kiran, tare da ba direba umarni.
"Maleek! Galadanci zaka kaimu."
Maleek ya amsa cikin girmamawa yana ma motar key yaja anutse.
Yayin da motar da take bin bayansu masu tsaron sa ne...
Real Ladingo Omu Farisah


*YI WA KAI!*


*Free Novel*

_#MatarɗanAlhaji🫣_
_December 2/12/2022_



*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*75&76*


Cikin hukuncin Allah Zainabu suka sauka lafiya garin Katsina, ana sallar isha'i, mota na sauke su ta shige keke napep ta rubuta masa inda zai Kaita.
Har ƙofar gidansu ya kawota, ta dalilin yadda ta dinga kwatanta masa da hannunta, lokacin da suka shigo layin anguwarsu.
Zaune suke tsakar gida, su dukkansu suna, cin abinci a babban tray'n silver, cike da son junansu.
Basuyi magana ba, har suka kammala, Jamila ta ɗauke tryan da kwana du suka wanke hannu, ta kai kitchen, ta dawo ta zauna suna hira da iyayansu gwanin burgewa.
Jamila tace.
"Allah Sarki! Umma ana can Jigawa, Allah ya kawota lafiya."
Inna ADAMA da Abbu suka amsa da.
"Ameen."
Atare.
Raihana tace.
"Umma tace zata siyomun tsaraba Khabir zan baka, ke kuma Aunty Jamila bazan baki ba ɗazu kinci zalina."
Abbu yace.
"ALLAH na godema da ka bani wannan yaran masu surutun tsiya."

Kamar daga sama suka ga Zainabu tsakar gidan.
Ai kuwa yaran aguje suka tarbeta kamar zasu kayar da ita suna murna.
Murmushin dole take musu taja su kan tabarma suka zauna.

Inna ADAMA cikin farin ciki takema Zainabu sannu da zuwa tana faɗin.
"Ya hanya Zainabu? Ni har ca nake sai gobe zasu taso Barka fatan anyi taro lafiya?"
Zainabu ta jinjina kanta tana murmushi.
Abbu yace.
"Masha Allah sannu Zainabu Abu me tagwayen suna, ya gajiya?"
Kai ta jinjina tana haɗe hannayenta.
Jakarta ta buɗe miƙe ta isa gaban Abu ta zube ƙasa tana nuna masa kyaututtukan da ta samu amman gobe zata raba abiyu taba shugaban tafiyarsu su ƙara da na wajansu su rabawa jama.

Abbu cikin farin ciki yace.
"Masha Allah, sannu Zainabu Allah yayi albarka, harda kuɗi haka? Masha Allah."
Inna ADAMA da kanta ta kawo mata abinci da ruwa ta wanke hannunta Tsaf taci abincinta ta ƙoshi, ta miƙe taje tayi wanka, ko kusa bata yarda ta faɗawa su Abbu gudowa tayi ba, ko hira da ta shafi Usman...

*Dutse*
Mamy cike da karrama wa ta amshi su Dad Mustapha, suka baje sukaci daddaɗan girkinta, suka sha lemon inibi da Khairy, tayi.
Lokacin da suka Karima suka shigo gidan, sabida umarnin barinsu da Shattima ya bayar, Dad suna tsaka da cin abincinsu, yace ta jira za'a shigo da ita.
Sai da suka kammala Tsaf, kafin su fito ya tura Usman ya shigo da ita.

Karima ta kalli Usman tace.
"Wai me yake faruwa ne Ni ban ganeba? Ina Nadiya?"
Usman yace.
"Mom ni bansan me zance miki ba akan wannan magana, dole sai kin keɓe da Dad."
Batace komai ba sabida Allah ya haneta ta ce ɗin.
Ɓanngaren baƙi ta sauka inda su Dad Mustapha suke da Usman.
Naziru direba ma an kaishi inda zai kwana.
Bayan tayi wanka taci abincin da Laraba ta kawo mata, tayi dam wannan ƙaton tumbin ya baje.
Karima ta ƙura ma Dad Mustapha idanu, wanda kallonsa yake Tv tashar CNN, Usman ya fita compound ɗin gidan dan yasha iska abunsa.

"Dadyn Usman nace wai lafiya kuka tare anan? Ina Nadiya take? Sai kumin bayani kun barni a duhu?"
Murmushi ya saki yace.
"Kwantar da hankalinki uwar gidana, lafiya lau, Nadiya sun fita da ɗiyar me gidan zuwa gidan iyayansa, da safe zamuyi magana insha ALLAHU."
Ajiyar zuciya ta sauke azuciyarta tana faɗin.
"Shege YANKAN WUƘA, yafa yi tsiyar ji yadda yake kirana uwar gidansa kai tsaye, tabb ashe na kusa murza kambuna wajan matar Minister Abdallah, wlh sakawa zanyi yamin aiki na mallaketa ina juyata komai nata ya kasance dani aciki."

Azahiri kuma tace.
"Toh Allah ya kaimu goben, bari naje na kwanta nagaji dayawa."
Ta faɗa tana miƙewa, ta shige cikin ɗaki, ta rufo ta kira Hajiya Shahida tana bata labarin abinda yake faruwa suna gidan Minister Jigawa ya gayyace su...

Maleek na parking a ƙofar gate ɗin gidan Liman ta buɗe ta shige cikin gidan, Nadiya na biye da ita.
Maleek ya ɗauko musu kular abincin wanda Khairy tama manta da ita tsabar bata hayyacinta.
A falo ta samu Inno da Amal zaune suna kallo.
Inno tana tafa hannayenta tace.
"Lale da makwaɗaiciyar fura da dambu tazo, yau ba'ayi ko ɗaya daga cikin ba."

Tsalle tayi ta afka jikin Inno tana sakin dariya har ta manta damuwarta sabida ba ƙaramin nishaɗi Inno take saka ba matuƙar suna waje guda.
A ɗan sakalce tace.
"Kai innota ai nasan bazaki ƙi ajiye min ba, shiyasa nataho fa! Kinga kuma harda baƙuwa zataso taci irin dambunkin nan da yasha zogale da gyaɗa."
Amal tayi dariya tace.
"Uhmm! Aunt Khairy ba dai wayoba."
Dariya Khairy tayi tana gyara zamanta ta kalli Nadiya da ta ajiye kular abincin da Maleek ya bata.
Gaishe da Inno tayi tana zama kusan Khairy'n.
Khairy tace.
"Amal! Please ɗauko mata plate taci abinci Ni dambu zanci nasha fura."
Nadiya tace.
"Auntie nima su zanci."
Inno tace.
"da kyau Nadiya kema su zakici
,sakeni toh na ɗauko muku."
Amal tace.
"Ni kam bari nazo na kwashi girkin Mamy nayi bacci me daɗi."
Ta faɗa tana miƙewa zuwa ɗaukan plate.

Khairy ta miƙe ta nufi ɓangaren Baffa Liman dan gaishesa.
Cikin Sa'a ba kowa sai shi ɗaya ta shiga da sallama.
Liman ya amsa, yana faɗin.
"Au ƙin iso ummulkhairi?"
Yau sosai taji wani nauyinsa ta kasa masa wasan jika da kakan da take masa, ta zauna kanta ƙasa tace.
"Baffa ina wuni?"
Murmushi yay da mamakin hankali na Khairy.
"Lafiya lau, ya ƙarfin jikin naki? Sannu Khairiya, Dadynki ya faɗa miki gobe zamuyi tafiya zuwa Katsina mu duka koh?"
Da sauri ta ɗago kanta tana kallon Liman, sai tai ƙasa da kanta, tace.
"A'a Baffa bai faɗamin ba."

"Toh tare zamu dake wajan mahaifiyarki Mahaifinki nan gidanku da ɗan uwanki da ƙanwarki, duk zamuje insha ALLAHU, ko bazaki zauna ba na wani lokaci dasu zamuje sai mu dawo idan yaso daga baya dai kitafi kafin bikinki. Karki ƙyamaci ƴan uwanki Khairiya, sabida basuda laifi, laifi na wacce ta ƴar dake ke amman da yake Ubangiji yayi rayuwarki me tsayine sai Dadynki da Mamynki suka tsinceki suka raineki sai Ubangiji ya juyar da lamarinsa har kika zama matar dadyn naki bayan wasu gwagwarmaya rayuwa da aka sha, Bilkisu da Abdallah bakida kamarsu aduniya idan aka cire iyayan da suka haifeni..."

Khairy idanunta lumshe tanajin wani irin bala'in mugun yanayi, cikin shasheƙar kuka tace.
"Baffa su Dady sun fimin kowa aduniyar nan ina sonsu, ina ƙaunar suci gaba da zama matsayin iyayena, Ni wanda kuke magana ban wani sansu ba amman zanje Katsina inason ganin baiwar Allah nan da aka zalumceta daga haifo ƴarta ko ganinta batayi ba aka rataba da ita aka jefar mata, tsaban ɗaukan alhaki.

Allah Sarki Mamy uwa tagari, ta raineni bata taɓa nunamin wani abu ko sau ɗaya ba, ma ba ita ce ta haifeni ba, duk abinda nake so shi take so.m, ƙarshe ta auramin mijinta da tafi so.

Allah Sarki Dadynah uba nagari, komai nakeso shi yakeso ya shagwaɓani ya riritani kamar ƙwai haka ya ɗaukeni baya son duk abinda bana so, Dadynah mutum nagari abun so ga kowa ga nutsuwa ga kamala ga son mutane, komai nasa na daban ne,Ni Ko me zanso aduniya bayan Dadynah da Mamy, Baffa Dadynah bawan Allah ne shi sam..."
Liman ganin Khairy na sakin layi batama san tanayin ba, sai kuka take ya katse sambatun ta hanyar cewa.
"Ya isa ummulkhairi ai daman keda Dadynki mutu ka raba da Mamyn ki, yanzu dai ki nutsu idan munje ki saki jiki da maman ki da ƴan uwanta karki nuna musu ƙyama."
Khairy ta jinjina kanta tana share hawayenta tace.
"Insha ALLAHU Baffa zanyi duk yadda kace, bari na shiga Inno na jirana."

Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Liman cikin farin ciki samun suruka ta biyu akaro nabiyu wanda sukafi kwanta amsa addukan surukansa na ƴaƴansa maza, kodan ƙaunar shattima ajininsa take yana bala'in son abinda yakeso.
"Toh shi kenan Khairiya, ayita haƙuri kinji? Kowane bawa akwai jarabtar da Allah yake ɗora masa."
Kai ta jinjina ta ficewa.

Bajewa sukayi ita da Nadiya sukaci dambun, tare da shan fura da tasha nonon shanu, bayan sun kammala suka baje suna hira, duk da wani ɓangaren na zuciyar Khairy na tunanin Dadynta kawai jurewa ne take.


Aliyah zaune, tana cin kwaɗon ƙanzon tuwon, da taji tana marmari, Umma Sa'idah na zaune gefenta, tana kallonta.
Kamar an jefosa ya shigo falon hannayensa cikin aljihun wandonsa, yana wani haɗe fuska.
Umma tace.
"Kai bana son rashin arziki meye haka zaka shigo mana ba sallama, ko an faɗa maka nan gidan kafirai ne?"
Salim ya zauna ya sanya Aliyah gaba zuru da idanu, yana faɗin.
"Umma Ni bance gidan arna bane, amman ai wani abinda kuke sai a slow, da kun yarda da kaɗɗara me kyau da mara kyau, bazaku je wajan wani gardi yace muku Khairy na ba alkhairi bace ku yarda ku rabani da ita, ku haɗani da wannan abun."
Ya nuna Aliyah yana miƙewa tsaye.
Marinsa tayi tana faɗin.
"Zakaci ubanka, maras kunyan banza, wuce bani waje."
Ficewa yay yana nuna Aliya da yatsa yace.
"Idan na kamaki akoraran guri zaki yabawa aya zaƙinta."
Umma Sa'idah tace.
"Allah ka shirya wannan yaron."
Aliyah ita kam ko ajikinta, dan tayi alƙawali tana haihuwa ta gama auren bazata zauna da wanda baya sonta ba, duk yadda taso su zauna yana wani tojewa toh na me???


Maryam kwance saman bed ɗinsu, Nafisa tuntuni tayi bacci, ita kam sai juyi take, bata san inda zata kai son Shattima ba.
Wayanta ta buɗe tana kallon picture ɗinsa, Wanda ta sata awayan Mamy wancan zuwan da tayi.
Hawayen da suka gangarawa kan fuskarta ta goge tana kallonsa yadda yay wani bala'in kyau, cikin suit Ash kala, yana murmushi fararen haƙoransa sun bayyana, kumatunsa sun loɓa.
Cikin murya kuka ƙasa² ta furta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Ya ALLAH ka dubeni ba dan halina ba ka mallaka min Dady Shattima, ya Allah kasa inada rabon zama da shi."
Ta faɗa tana sumbatar fuskarsa a hoton ta rungume wayan a kan ƙirjinta har bacci ɓarawo ya saceta.

Zaune Shattima yake cikin tsararran falonsa, cikin shirin bacci, fararen kayane ajikinsa na bacci masu

Please Login or Register in order to submit comment