Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu."
Hannunsa ta riƙo tace.
"Please Mi Amor ka kwanta ka huta ina zaka je ne? Kai da kake tare da gajiyar tafiya"
Zama yay gefen bed ya zura hannunsa cikin rigarta yana shafa cikinta da marata, yana murmushi anutse cikin zazzaƙar muryansa yace.
"Bazanje ko ina ba kiyi bacci ina zuwa bana buƙatar kiyi girkin safe, ki huta umarni na baki Ok?"
Idanunta ta rufe tana jin yadda hannunsa yake yawo cikinta zuwa ƙirjinta.
Murmushi yay yana zare hannun nasa ya miƙe yana zura hannunsa ɗaya cikin aljihun jallabiyarsa.
Waya ɗaya ya ɗauka yana kunnata ya buɗe ƙofar ya wuce, yana rufe mata ƙofar.
A falonsa ya zauna yana kiran Liman.
Bugu biyu ya ɗaga tare da sallama.
Shattima ya amsa yana gaishesa cike da farin ciki yace.
"Baffa! ALLAH ya amshi addu'a Bilkisu ALLAH ya bata ƙaruwa sati huɗu."
Liman yace.
"ALLAHU AKBAR MASHA ALLAH Godiya ta tabbata ga ALLAH Alhamdulillah! ALLAH Ubangiji ya buɗe ido lafiya, ya baku zuri'a ta gari. Kai yau dole mu kasance cikin farin ciki, lokaci ya ya, mahaƙurci mawadaci."
Shattima ya amsa da.
"Ameen Baffa, sai zuwa yamma zan shigo, bari na kira Inno."
Ya faɗa yana katse kiran ya kira Inno yana faɗa mata.
Kusan tafi liman farin ciki, harda guɗa take Shattima yana dariya.
Munnir ya kira ya faɗa masa ya kira Balaraba, kaf ƴaƴansu da ƙanninsa sai da ya kirasu ya sanar dasu da ƴan uwan nesa da kusa, kowa yau ya farka da labarin da ya faranta ransa cikin Mamy Bilkisu.
Sai da ya idar da ƴan uwansa ya kira Commissaire Aminu ya faɗa masa kusan rabin farin cikin Shattiman suka kasance da Ammi dan ba ƙaramin tausayinsu sukeji ba, rashin haihuwa babban giɓine arayuwar ɗan Adam.

Bayan ya idar da wayar ya sauko ƙasa, su Laraba na ta aikinsu na gyaran falon.
Anutse ya amsa gaisuwar da suke masa, ba tare da ya kalli inda suke ba, ya fara magana, idanunsa akan wani babban hotonsu, shi da Mamy da Khairy tana tsakiyar su ta rungumesu tana dariya.
Hoton ba ƙaramin kyau sukayi ba.

"Yawwa Laraba idan kun idar da wannan aikin ki fere dankalin turawa mai ɗan yawa, ki fasa kwai ki zuba komai ki sulala kaza, sai ku ɗora abinda zakuyi breakfast, acan kitchen ɗin su Lami, kuje wajanta kuyi tare sai ki fitar da naku."
Cikin ladabi ta amsa da.

"Toh Yallaɓai."

Ya juya ya nufi Stairs anutse.
Mamy tana bacci koda ya shiga ya cire jallabiya ya sanya ƙananun kaya, ya ɗauko ɗayar wayan ya kunna yana daukan ta Khairy ya kunna ya ajiye ta falonsa, ya zauna yana waya yafi 30 minutes kafin ya koma.

Lokacin da ya fito sun idar da komai, da ya sakata sun tafi.
Kitchen ya shiga ya dafa tea yaji kananfari da citta ya juya a ƙaton Flask, ya soya dankalin turawan da kazar ya soya biredi.
Masha Allah Tsaf kamar ba namiji ya yi ba, sabida Shattima ya iya girki tun lokacin yana saurayi, shi yakewa kansa girki da yake karatu a ƙasar waje.
Tsaf ya jare komai akan dining area.
Wanka yay ya canza kaya, farare na shan iska yana wani irin fitinannan ƙamshi, ya yi kyau na musamman, yau cikin farin ciki yake marar misaltuwa.
Ganin Momy na baccinta baya son tashinta ya fito yana latsa wayansa.

Dai dai lokacin Maryam ta shigo gidan, saboda ita kai tsaye take shiga gidan batada shamaki, security basa hanata.
Ta jima tana danna Doorbell kafin Laraba yazo ta buɗe, sabida sun dawo suna kitchen suna gyara wajan da Shattima ya ɓata, zatonsu ma Khairy ce ko Mamy sukayi soye-soyen.
Laraba na buɗe wa Maryam ta shigo tana murmushi.
"Su Mamy na nan ko taje aiki?"
Laraba tana rufe ƙofar tace.
"A'a ta nan, suna sama."
Maryam tace.
"Ok Ngd."
Ta faɗa tana shiga falon ta zube akan sofa tana ƙura ma hoton Shattima idanunta...

Shattima Bedroom ɗin Khairy ya shiga dan ta fito ta yi breakfast.

Ta baje saman ƙaton Italiyan bed ɗinta tana sharara baccinta hankali kwance, rabin jikinta rufe da Duvet, daga ƙirjinta zuwa wuyanta fuskarta a buɗe, ko hijab ɗin da tayi sallah bata cire ba, take ta kwasar Baccinta.

Anutse ya ƙarasa wajanta ya zauna gefen bed ɗin, yana kallonta murmushi akan fuskarsa.
Ganin yadda baccin yamata daɗi ya ji bazai iya tashinta ba.
Ya sanya tattausan hannayensa ya ɗagota kaɗan ya zare mata hijab ɗin jikinta, ya ajiye yana kwantar da ita, ta fara motsi, tana ƙoƙarin buɗe idanunta tana laluba hannunta ta kamo tattausan hannunsa, tana buɗe idanunta.
Idanunsu suka sarƙe waje ɗaya.
Ta maida idanunta ta lumshe tana kifa fuskarta cikin tafin hannunsa, kunyarsa taji ba kaɗan ba.
A hankali tace.
"Dadynah ina kwana?"

Hannunsa yake ƙoƙarin janyewa yana wani irin kalar murmushi ya amsa gaisuwar yana ɗago fuskarta, taƙi yarda ta rintse idanunta.
Da wata tsadaddiyar murya ya yi anfani da ita wajan mata magana anutse.
"Oh! Baby kunyar Dady kuma yau?"

Yana juyeta yana kwantar da ita, tai wani irin riƙesa tana tutturo bakinta gaba.
Binta yay, tare da jan Duvet ya rufesu har kansu, can ƙasa ya furta.
"Ok ya isa rigimar, faɗa min me akayi bakya son na tafi?"

Khairy ta ɗaga kanta tana wani irin lafewa ƙirjinsa,tana jin wani irin sanyi da nutsuwa na ratsata.
Shattima yay murmushi ya furzar da iskar bakinsa, yaja hancinta anutse cikin wata irin fitinanniyar murya yace.
"Kin gama baccin Babyn Dady ko akwai saura ne?"
Ya faɗa idanunsa cikin nata.
"Wayyo Dadynah ka daina min wannan kallon ƙirjina."
Ta faɗa tana kamo hannunsa tana ɗorawa saitin zuciyarta, wanda hannunsa ya ratsa lafiyayyan tattausan breast ɗinta.
"Ya Hayyu Ya Qayyum!"
Ya faɗa yana janye hannunsa tare da zareta daga jikinsa, yana fita daga Duvet ɗin, ya zauna yana faɗin.
"Naji Babyna me yasamu zuciyarki haka take bugawa?"
Ashagwaɓe ta mirguno wajansa tana kwanciya saman cinyarsa kanta akan ƙirjinsa tace.
"Dady ban saniba ba ALLAH."
Ta faɗa tana ɗago kanta ta kalleshi tana sanya yatsarta cikin ramin dimple ɗinsa, tana taɓawa, tace.
"Dadynah kayi kyau sweet Dady Ina chocolates ɗina da biscuits?"

Jelar gashinta yaja yana tattarawa ya ɗaure mata, yana shigar da ita ƙirjinsa, hannunta ɗaya cikin hannunsa, ya manna bakinsa akan kunnenta yana mata raɗa cikin wata kalar murya, still yana murza tafin hannunta cikin nasa.
"Baby ta afka tarkon ƙauna koh?"
Khairy idanunta lumshe tanajin yadda Dadyn yake mata magana a kunne hannunsa cikin nata yana murzawa.
Ajiyar zuciya ta sauke tana ɗaga masa kanta, dan bata wani fahimci inda maganar ta dosa ba.
Kiss mai tsada ya sauke mata akunnenta, yana ɗago da fuskarta yana ƙasaitaccan murmushi yace.
"Baby bud'e idanunki na baki labari me daɗi."
A hankali ta buɗe idanunta, ta kalleshi.
Da sauri tai ƙasa da kanta tana rau-rau da idanunta, zuciyarta nata wata irin fitinanniyar bugawa, wani shegen shaukinsa da begensa ya gama kasheta, kawai sai ta kirasa kamar zatayi kuka.
"Sweet Dadynah!"
"Na'am Babyn Dady, albishirinki kin kusa ƙani Mamynki tanada ciki..."

Wani irin zazzaro idanunta tai tana kallon Shattima, take taji mutuwar jikin ta kau, tai wani irin rungumesa tana ihun murna, duk ta cukuikuiye shi, ta cika masa kunne da ihu.
Kafaɗunta ya riƙe yana hura mata iskar bakinsa, Anutse yace.
"Ya isa ya isa Baby kar kanki ya yi ciwo mana, idan murna zaki nuna je kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ki ma ALLAH godiya da kyautar da ya baku, ki roƙesa ya sauki Mamynki lafiya, ya baki ƙanne masu albarka irinki, kiyi kyautar duk abinda kika fi ƙarfinsa yau ranan murna ce.
Oya je kiyi alwala kiyi sallah, sai kizo muje kiyi breakfast, ko muje restaurant mu siyo idan wancan baiyi daɗi ba. Tashi Baby kar Mamy ta tashi ta nemi abinci."

Kallonsa take cike da burgewa tana murmushi, ta ɗora tafin hannunta akan kyakkyawar fuskarsa, tana taɓa kwantaccan gashin sajansa.
Gaza magana ta yi kallonsa kawai take tana murmushi hawaye sun cika mata idanunta, tace.
"Dadynah kai na daban ne a rayuwa, haka kayi arayuwa Mamy ta dace da mijin kere Sa'a, ni kuma na dace da uba nagari, nayi ma mata dayawa zarrar uba."
Ta ƙarashe maganan tana sakar masa kukan zallar farin cikin samun cikin Mamy.
Fuskar ya shafa taee da tallabo fuskar yana kallon yadda take kukan tsakaninta da ALLAH.
Harshensa ya zaro ya shiga ɗauke hawayen da yake tsiyaya akan fuskarta, idanunsa lumshe yana buga bayanta da hannun ɗaya.
Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi, tana kallon yadda yake lashe hawayen fuskarta, cikin wata irin kalar kamewa tamakar yana shan coffee.
Dole ta dakarta da hawayen tana sauke ajiyar zuciya, tace.
"Sweet Dady baka tsantsani ne?"

Ya maida harshensa bakinsa yana furzar da iska mai ɗan ɗumi, ya yi kissing idanunta da goshinta, ya kamata ta miƙa tsaye, akan bed din, da wata kalar murya mai taushi yana sake riƙe kansa daga abinda yake fizgarsa ya furta.
"Baby je mana kiyi abinda na sakaki, ina ƙasa ina jiranki maza jeki Please."

Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Hannayenta ta béka masa kamar zatayi kuka tace.
"Sweet Dadynah please kaji da Ni kaga har yanzu nice Babynku kafin nayi ƙani, Ni ka goyani ka kaini bathroom Allah yau shagwaɓa nakeji sosai kaji Dadynah."
Ta faɗa tana tsalle saman bed ɗin tana beƙa masa hannayenta.
Kai ya girgiza yana sake sakawa zuciyarsa juriya tare da ƙoƙarin riƙe kansa ya iso dab da ita yana zungurinta akai, ya kamo kafaɗunta yana fito mata da kaifafan lumsassun idanunsa, can ƙasa yace.
"Kina son kasheni ne Baby?"
Kai ta langwaɓar kamar zata fashe da kuka, idanunta cikin nasa da kalar wata irin shagwaɓa can ƙasa² tace.
"No! Dadynah ya zan kashe madubin dubawata, please Ni dai goyani bayanka Dady nutsuwa nake samu."
Ta faɗa tana saƙala hannayenta wuyansa, tana murmushi.
Shattima ya fara kai ƙarshen haƙurinsa zuciyarsa har wani bala'in bugawa take, da wani irin sauti ya furta.
"Ya Rabbi! Baby."
Ya fad'a ya ɗagata cak Idanunsa akan fuskarta, sakata tsakiyar gadon bayansa ya yi ya goyata, ya nufi bathroom ɗin da ita.
Dariya tai tana leƙensa ta sumbaci gefen kumcinsa tana masa raɗa a kunnensa.
"Sweet Dadynah madubin dubawana ninkainna dubawa...."
Da wani kalar sauri ya saukota yana mannata da ƙofar bathroom ya sakar mata ƙirjinsa, ya riko ƙugunta da hannunsa ɗaya, yana tallabo fuskarta da ɗayan hannu, yana wani irin hura mata iskar bakinsa, ya haɗe face ɗin su ya fara magana cancan ƙasan maƙoshi da wani irin kalar salo atausashe idanunsa cikin nata yace.
"Idan kin sake magana zanyi maganin bakin nan Baby, Oya kije kiyi alwalan kiyi abinda na sakaki ki daina ɗaukan maganan da baki shirya ba..."
Ya faɗa yana mata wani irin kallo tare da sanya mata yatsarsa ƙarama bakinta, yana murmushi. Baki ɗaya yamata ƙawanya, ƙamshinsa kawai ya isa rikita mace, bare shegen salonsa da Allah ya basa fannin iya SOYAYYA mai ratsa zuciya.

Baki ɗaya ya gama rikitata da salon maganansa, da riƙon da yamata tare da hura mata numfashinsa, da wasa da yatsarsa cikin bakinta.
Sai taji ta manta wani kamewarta dan kar yace bata wayo, ita fa Allah yana gani bazata jure wani basar da Dadynta ba.

Cikin shegen shaukin da ya kwasheta, baki ɗaya ta manta kowa da komai adaidai wannan lokaci sai Sweet Dadynta.
Ta shiga lasar yatsar tana sanya hannayenta ta zagaye bayansa cike da shagwaɓa ta ciza yatsan kaɗan tana ƴar dariya tace.
"Madubin dubawata Dadynah kamin duk hukuncin da ya dace Ni dai bazanyi shiru da bakina ba..."
Ɗumin damshin lallausan lips ɗinsa taji akan laɓbanta, ya wani irin kamosu cikin bakinsa yana zura harshensa Tsakiyar bakinta yana yawo kamar yana neman Abu aciki, ya lumshe idanunsa tare da sauke numfashi kamar yadda tai tana ƙankamshi tana jiran taji ya fara kissing ɗinta, duk da ƙafafuwanta sun fara rawa, bazata jiri kissing ɗinsa ba...
Da wani irin nutsuwarsa ya kamo lips ɗinta ya fara tsotsa da wani kalar salon da numfashinta ya kusa tsayawa cak.
Ta buɗe idanunta tana kallonsa, abinda bata taɓa jiba agame da shi yau takeji.
Ta fara ƙoƙarin janye bakinta idanunta tabb da ruwan hawaye.
Ji tai ya kamo harshen ya gama da laɓɓanta ya fara sha.
Asma'u ta tsinci kanta da kamo nasa harshen ta fara sha slowly zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa, idanunta akan kyakkyawar fuskarsa idanunsa lumshe.
Dai dai lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, ana magana...
Rahmatullahi ce😂🤣

Kai jama'aaaa kuka soyayya da safiyar ALLAH.🤔😜

Ina muku read more dayawane sabida bana baku update kullun, da na cirasa guntu-guntu gwara me ɗan yawa yafi koda ba kullun zaku samuba, masu comments da sharhi group ɗina da ba group ɗina ba, wallahi na gode hakan yasa ma nake ƙoƙarin typing kwana ɗaya zuwa biyu, sabida ina littafin kuɗi dole sai anyi haƙuri, zan ƙoƙarta na gama muku labarin da wuri ku huta nima na huta, ALLAH yabar ƙauna abadan.🫱🏽‍🫲🏽🫶🏽

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 21/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_

``` BREAKFAST```

*DEDICATED To*
👇🏽
Masu min Sharing, kusani inajin daɗi sosai.

*MumSayyed&Noor.*
*Maman Sultan. Shamsiyya Mrs Sadauki.*
*Bingel* *Nanne.*
*Muhammad Karim.*
*Nazifi na* *yarima.*
*Abubakar Ak* *saraki.*
*Sdeendtm.*
*Da sauran da nake gani groups-groups ban sankunba ƙauna ta sa* *kuke min Sharing billahi Ngd sosai, Allah ya rabaku da duniya lafiya, jazakallahu khairan.🙏🏽🫶🏽*

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*93*

"Baby! Kina Ina? Kema baccin ne har goma ta wuce? Ga Maryam tazo, miki sannu da zuwa, ke...."
Bakin Mamy ne ya tsaya cak sakamakon ganin Shattima da Khairy tsaye ƙofar bathroom, suna tallabe da fuskokin junnasu, idanunsu lumshe bakinsu haɗe suna kissing ɗin juna, cikin yanayin da kallo ɗaya zaka musu kasan ƙaunar da suke wa junnasu baki bazai iya faɗa ba.
Da sauri ta toshe bakinta idanunta akansu, yadda kowa yake shayar da ɗan uwansa yawunsa, Tsaf take jin sautin ƙaran kissing ɗin da suke wa junansu.
Da mamaki take kallonsu yadda basuji maganan da ta yi ba, basu ma san ta shigo ba.
Da wani irin sauri ta juya ta fice tana janyo musu ƙofar a hankali.

Abinda ya saka Mamy shigowa ɗakin Khairy, yanzun shine.

Lokacin da ta farka daga bacci ta ga Shattima baya nan,ta kalli agogon da yake manne jikin bango taga goma ta gota, sai ta yi murmushi ta shiga bathroom ɗinsa tai wanka tana ɗaure da towel, ta fito falonsa taga wayoyinsa biyu ajiye akan Centre table, har da ta Khairy ajiye, sai tayi tunanin ko ta shigo ne ta fita.
Ɓangarenta ta tafi ta shirya ta sauka domin breakfast, dan yunwa takeji sosai.
Tana dab isa matattakala Maryam tana hayowa.
Mamy ta tsaya cike da mamaki tana kallonta, da mamakin inda zataje.
Tana shirin magana Maryam tai saurin tarar numfashinta, ta hanyar rungumeta tana dariya tace.
"Good morning my Mamy? Nazo taya murna ashe zamuyi ƙani ko ƙanwa, Congratulation Mamy, tun ɗazu ina ƙasa ba kowa Laraba mai aiki tace min keda Auntie Khairy kuna sama shine nace bari hayo naganku."
Mamy tai murmushi tace.
"Daughter ykk? Sorry bamu san kinzo ba ai, ni ina bacci Baby naga wayanta falon Dadynta da alama ta tashi bari na fito da ita yanzu."
Maryam tace.
"Tom Mamy a fito lafiya bari na koma falon
"Ta faɗa tana juyawa.
Mamy tana murmushi ta nufi ɗakin Khairy, tana shiga ne tayi Tozali da abinda bata zata ba ayanzun zai iya shiga tsakanin Khairy da Shattiman.

Da ƙyar ta kai kanta bedroom ɗinta.
Ta zube ƙasa saman tattausan carpet ta rintse idanunta hawayen masu zafi suna sauka akan kyakkyawar fuskarta.
Wani irin fitinannan kishi mai azabtar da zuciya takeji.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!
Hasbunallahu wa ni'imal wakil.
A'uzubillahi minan shaitanir rajin."
Ta faɗa tana sakin kuka, bata taɓa zaton haka take kishin mijinta ba sai yau da ta gansa da Ummulkhairi, bakinsu cikin juna suna kissing cikin fitar hayyaci wanda har ta shiga ta fita basu ma san tazo ba.
Wani irin nauyi taji zuciyarta ta yi, amman son da takewa Khairy bazata bari ba, shaiɗan ya samu wajan zama azuciyarta har ya saka mata matsanaicin kishin Khairy har su koma suna ganin rashin darajar juna bata fatan hakan, dole zata cije ta daure tasa haƙuri tinda ita ce tayi abun nan ba wanda ya matsa mata.
Addu'a kawai take kowace iri tazo bakinta yi take.
miƙewa ta yi ta shiga bathroom, kayan jikinta ta cire ta kunna shower ruwa masu sanyi ta sakarwa kanta, sabida azabar zafin da takeji ajikinta, kamar ba yanzu tayi wanka ba. Ashe haka kishi yake idan kaga mijinka da kakeso da wata macan da ban?
Haka ta yi ta saƙe² azuciyarta.

Sosai ta tsaya ruwan shiga jikinta, tana maimaita kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Har taji zuciyar ta yi sanyi, ta ɗaura towel ta fito.
Riga marar nauyi ta saka mai ƙaramin hannu ta yane kanta da mayafi baƙi wanda ya karawa farar fuskata kyau, ta shafa humrah mai shegen dad'i ta ɗauki wayanta ta fito.
Koda wasa bata kalli ƙofar falon Shattima ba bare ta Khairy ta tafiyarta abunta.
Anutsu ta sauko Maryam na zaune ta kunna Tv tana kallo.
Mamy ta nufi kan dining area tana faɗin.
"Daughter! Zo muyi breakfast."
Maryam bata musaba ta miƙe tana tunanin ko ina Dady Shattima shi take mararin gani.

Mamyn tana haɗa tea Maryam ta iso ta amsa tace.
"Mamy bari na haɗa miki."
Mamy ta yi murmushi tace.
"Thank you."
Kurɓar farko da ta yi ta gane wannan tea ɗin haɗin Shattima ne.
Idanunta ta lumshe tana jin tsananin ƙaunar mijinta na ratsa ko ina na jikinta.

Tsawon 20 minutes suka ɗauka suna kissing bakin junansu, ba tare sun gaji ba, cikin wani irin yanayi na shauki da ƙaunar junansu da ta musu mugun kamu, tuntuni ba tare da sun ankare ba.

Khairy ce ƙafafunta suka gaza ɗauka ta, suna rawa amman ta gaza sakin bakin Dadyn nata, saboda zaƙi da garɗi da wani irin kalar ɗanɗano da takeji.

Shattima ne ya buɗe idanunsa, yana zare bakinsa anata, tare da rungumeta sosai ƙirjinsa yana sauke numfashi da wani irin sauri, yana kallon fuskarta da shafa kumatunta.
Khairy ta laɓe ƙirjinsa tana maida numfashi idanunta a lumshe tana lashe yawunsa da ya biyu laɓɓanta.
Har yanzu ƙafafunta rawa suke.
Ɗan murmushi yay yana ɗaukanta kamar ƴar jaririya, ya nufi bed da ita.
Kallonsa tai cikin bala'in sanyin da jikinta yay, ahankali ta buɗe bakinta wanda yake cike da ƙamshin bakin Shattima tace.
"Sweet Dadynah zan shiga bathroom ai nayi abinda ka sakani."
Ta ƙarashe maganar tana ɓoye fuskarta ƙasan wuyansa.
Iskar bakinsa ya furzar yana zaunar da ita gefen bed, ya tsugunna gabanta ya kamo ƙafafuwanta masu taushi yana matsawa anutse, idanunsa akanta yana sakin murmushin da ya saka zuciyarta wata irin karaya, ta sanya hannunta ta shafi fuskarsa tana wasa da gemunsa, cikin wata irin kalar shagwaɓa tace.
"Madubin dubawata wallahi abinda nakeji akanka irinsa naji fiyema da shi nakeji lokacin da naso Salim..."
Wani irin mugun kallo ya watsa mata yana sakin ƙafafunta da yake matsawa sabida su daina mata sanyin da sukayi suka gaza ɗaukanta, ya juya zai fita cikin matsanancin ɓacin rai.

Khairy ganin Shattima ya miƙe ya juya zai fita ta fashe da kuka tace.
"Don Allah Sweet Dadynah kayi haƙuri na tuba, wlh ba laifi na bane haka kawai naji kamar na fara sonka ne da gasken gaske, amman zanyi haƙuri da wani idanun zan kalli Mamynah.
Kawai na faɗa ne saboda lokacin da na fara son Salim inajin hakan...."
Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata wadda ta kusa suman wucin gadi sabida tsoro, ta haɗa kanta da guiwowinta.
Bata dawo hayyacinta ba taji ya damƙota ya mata wata irin runguma ya ɗago kanta yana sanya bakinsa cikin nata ya shiga mata wani irin kissing na Azabar so da kishi mai zafi, yanayi yana ciza lips ɗinta da harshenta.
Khairy sosai takejin azaba kamar zata saki fitsari amman ta kasa kuka idanunta kawai ta zuba masa tana ƙara rungumesa gam-gam.
Alamu jini yaji acikin bakinsa, haka yake so daman yajima bakin ciwo jinin ya fita ko zata kiyaye harshenta, duk da yafita jin azabar acikin zuciyarsa ciwon da ya jimatan, sai dai bazai nuna mata ba a gabanta.
Zare bakinsa ya yi anata yana ɗaukanta yaje gaban ƙaton madubinta ya tsayar da ita yana juyata tana kallon madubin yana shafa bakinta da ya fara kumbura ga jini nan gefe.
Idanunta ta zaro tana kallonsa ta madubin ta saki marayan kuka tana juyowa suna facing juna, ta rungumesa, tana faɗin.
"Sweet Dadynah kalli ciwon da ka jimin me zance wa Mamynah idan taga bakina a kumbure?"
Anutse ya kamo fuskarta ya sumbata yana lashe idanunta.
Cikin kamewarsa kamar ma bai damuba, ya fara mata magana.
"Idan kika sake kamanta son da kike min da wani, Baby zan baki mamaki, bance dole kice kina sona ba, bare ki haɗa sona da wani banza kin gane ai abinda nake nufi koh?"
Ya ƙarashe maganar yana lashe mata jinin da ya taɓa gefen bakinta yana lasar dukkan fuskarta tare sauke mata kisses yana mannata ƙirjinsa tare da sauke ajiyar zuciya.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."
Khairy ta faɗa cikin zuciyarta lokacin da taji ta gama haukacewa da son Dadyn nata.
Wani irin marayan kuka ta sake sakar masa cikin shasheƙar kukan tace.
"Wallahi bazan kuma ba kayi haƙuri Dadynah wallahi naji ina sonka fiye da komai idan aka cire Mamynah Bana iya haɗa sonta da kowa kaine na biyu sai Umma da Dad Mustapah ban girma da su ba, ban rayu da su ba bazan iya musu son da nake muku ba, duk da kuwa babu abinda yafi iyaye aduniya, toh ai Ni ku nasani iyayena, Wlh kaine mutum na biyu a duniya dana fi sonsa da ƙaunarsa i love You Sweet Dadynah Ina ƙaunarka kaima kasoni kaji?"
Ta faɗa tana sake ƙanƙameshi tare da sumbatar ƙirjinsa dan nan ne daidai tsayinta.
Shattima tsayuwan take neman gagarasa ya gaza magana ma, kawai ya ɗauketa ya kaita bathroom ya haɗa mata ruwan wanka mai ɗumi yana kallonta cike matsanancin sonta da ƙaunarta yace.
"Baby ki nutsu naji bazayin fushi dake ba, yi wanka ki fito muje kiyi breakfast zan fita bari na taso Mamynki tayi breakfast Ok?"
Kai ta jinjina ahankali tace.
"Sweet Dadynah ya zanyi da Mamynah ina son mijinta?"
Wani irin murmushi mai shegen kyau ya saɓace masa yana kamo fuskarta da dukkan tafin hannunsa ya sumbaci laɓɓanta da suka ƙara kumbura anutse cikin wata irin murya yace.
"Ba yadda zakiyi ai Mamy ta baki Dadynki, kiso abunki Kawai abinda nakeso ki dinga ɓoye son Dady gaban Mamy OK ?"
Narai-narai ta yi da idanunta tace.
"Toh zanyi ai daman bazan so ran Mamynah ya ɓaci ba, Dadynah ai zaka soni nima kaɗan ko rabin na Mamynah koh?"
Ta faɗa tana ɗora hannunta akan fuskarshi tana shafawa.
Shattima yace.
"Sosai zan so Babyna mana."
Dariya tayi tace.
"Madubin dubawata ka ɗagani kaɗan."
Ƙugunta ya kama ya ɗagota kaɗan.
Bakinsa ta kamo ta tsotsa kaɗan ta lashi idanunsa ta sumbaci dogon karan hancinsa ta masa raɗa a kunnensa tace.
"Sweetie Dadynah Ina sonka zanyi zaman aure da kai na har abadan, wlh bazan iya barinka ba ALLAH inajin sonka dayawa bansan kuma yaushe ne ba, kamar tun akatsina."
Shattima ganin Khairy zata iya sakashi ya haƙe mata bai shirya ba, sabida baki ɗaya yarinyar ta gama da zuciyarsa da gangar jikinsa da ruhinsa, ƙaunarta yake ji babu algus acikinta.

Cikin Ruwan ya sakata yana juyawa anutse.
"Babyn Shattima kiyi sauri kizo kiyi breakfast sai naga kinci wani abun zan fita Ok?"
Ya ƙarashe maganan yana ficewa daga bathroom ɗin ya rufe mata ƙofar.

Kai tsaye ɓangaren sa ya nufa sabida awannan halin da yake ciki bai isa ya shiga wajan Mamy zata gane komai Tsaf.
Ruwa ya watsa ya canza kaya, zuwa kayan fita wani mahaukacin boyel fari mai tsada ya saka, ya yi wani irin fitinannan kyau yana baza ƙamshinsa mai kashe jiki da kasala, ya manna glass fari.
Agogon da yake ɗaure atsintsiyar hannunsa da rufaffan tsadaddan takalmin ƙafarsa kawai abin burgewane da kallo.
Yana fitowa falonsa ya ɗauki wayoyinsa da ta Khairy ya kasheta ya sanya cikin aljihunsa, ya fito ya rufo ƙofar ya nufi bedroom ɗin Mamy.
Wayam bata ciki yagani.
Murmushi yay yana zura hannayensa cikin aljihunsa, yace.
"Yunwa ta tashi Sweetheart."
Yana fitowa ya sauka bai yarda ya koma wajan Khairy ba!

Khairy kuwa kwance tai cikin ruwan bayan fitar Shattima, ta jima kafin ta yi wanka ta fito ɗaure da alwalan.
Rigarta ta sallah ta saka ta sanya hijabi tayi sallar nafila raka'a biyu tama ALLAH godiya da kyautar da yama Mamy da Dady, ta jima tana addu'a Allah ya sauki Mamy lafiya kafin ta miƙe tana sakin murmushi, ta shafe jikinta da body lotoin me ƙanshi ta ƙura ma laɓɓanta idanu da gaske sun kumbura saboda azabar da Dady Shattima ya musu kawai dan ta anbaci Salim.
Murmushi tai tana shafa laɓɓanta wajan da ya ɗan fashe.
Tsalle tai tana dariya tace.
"I love You sweet Dadynah kayi haƙuri bazan kuma cewa ina son waniba kaji?"
Ta ƙarashe maganan ashagwaɓe tana kama kunnenta, kamar yana gabanta.

Riga da skirt ta saka na atamfa, ta murza ɗaurin zahra buhari, ta fesa turare mai shegen sanyin daɗi, ta shafa lipstick, a kumburaren laɓɓanta shiga neman wayanta bata ganiba ta tuna jiya Shattima ya amsasheta ya fita da ita.
Murmushi tai ta nufi ƙofar fita.

Mamy da Maryam suna tsaka cin soyayyar kaza da dankalin turawa suka korawa da tea, suna hira jifa².

Mamy ta shaƙo fitinannan ƙamshi turarensa hakan ya

Please Login or Register in order to submit comment