Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nashi, ya samu ya zare hannunsa yanajin kansa ya fara juyawa, da sauri ya sauka daga saman bed d'in, ya shige bathroom, yana kiran sunan Allah.

Mamy kuwa tana fita d'akinta taje taci kukanta ta wanke fuskarta, ta sake simple makeup ta fesa turare ta had'a musu kayan arziqi a babbar leda,ta sauka ta kira Laraba ta amshi ledar suka tafi wajansu.
B'angaran su Hajiya Karima kuwa Mamy tana fita suka samu gamun daddad'an girki sukaci sunyi haniqan suka sha lemo mur suka murje idanu suna jiran Mamy.
Hajiya Karima ta gyara zama tana fad'in.
“Yau shigar dare inaga zamuyi, tunda gidan kawu ba kai tsaye zai barmu mu fita ba, ita kuma taje ta tisa miji agaba sai kace ita d'aya ta iya soyayya”.
Hajiya Shahida tace.
“Kwarai kuwa ga Nadiya ta addabeki da Kira, mu k'ara jira kad'an mugani.”

Karima zatayi magana Mamy ta shigo da sallama tana fad'in.
“Afuwa na barku koh?”
Karima ta washe baki tana fad'in.
“Lah! Ba komai wlh muna godiya da karramawa.”
Mamy ta zauna tana murmushi tace.
“Ba komai ai baqon ka Annabin ka ne, Laraba ajiye ledar sai ki tafi da kayan abincin, fatan dai kunci?”
Shahida tace“Munci an gode wlh.”
dire musu ledar Laraba tayi akusan Shahida ta kwashe kayan abincin ta fice.
Karima ta miqe tace.
“Toh Hajiya Dr Bilkisu mun gode sai gani na biyu a beqa mana godiya wajan minister Allah ya qara girma.”
Mamy tace“Insha Allahu zai ji yana gaisheku agajiye yake yaso ma Ku gaisa ga shi yace Ku zuba mai sauran direba yasha ruwa ahanya.”
Ta beqa ma Shahida bandir d'in 'yan dubu² na dubu hamsin.
Shahida tace.
“Aa wlh bazamu amsaba mun gode da karramawar ma.”
Mamy ta nuna rashin jin dad'inta, tace.
“Sai dai idan rainawa kukayi.”
Shahida ta amsa tana fad'in.
“Toh mun gode Allah ya qara arziqi.”
Mamy ta amsa da.
“Amin.”
Ta d'aukar musu ledar da ta shaqe musu tsadaddun turaruka da maiyukan gyaran jiki da sabulu da kayan makeup, suka fito.
Har compound d'in gidan ta rakasu parking lot suka shiga mota taba direba ledar ya saka a booth.
Sosai ta nuna musu karramawa suka rabu lafiya suna mata godiya tana tsaye sai da motar su tabar gidan ta koma ciki.

Zaune yake da farar jallabiya yana wani irin fitinannaan k'amshi, yana danna system, farin glass manne akan fuskarshi, ta shigo falon.
Kallonsa tai ganinsa da wasu kayan ba na d'azu ba, ta zauna kusansa tana lumshe idanunta, tace.
“Wlh bacci nakeji.”
Kai tsaye ya kashe system d'in ya miqe ya yana d'aukarta kamar baby yace.
“Nima baccin nakeji but Amman bana cikin moment mai dad'i.”
Mamy langwab'ewa ajikinsa tana sauke numfashi tana jin wani irin d'aci azuciyarta, ta kasa magana har ya haye upstairs da ita.
Bedroom d'inta ya nufa da ita ya direta kan tamfatsetsan bed d'in.
Mirginawa tayi samansa tana kwanci kan k'irjinsa tace.
“Mi Amor ka Kira Baffa ka fad'a masa halin da ake ciki tin kafin Khairy ta rigamu idan yaso sai muyi bayani yadda kowa zai fahimcemu sannan Baffa yama Khairy bayanin auren da ya mata.
Sai lokacin Shattima ya tuna Ashe fa Khairy an mata aure bata ma saniba.
Wata irin iska mai zafi ya firzar yana lumshe idanunsa yana shafa bayanta ya furta.
“Ok..OK! Amman bansan wane irin kallo dangina da naki zasu mana ba! Bana son atakuraki Sam ko mgnar nayi miki kishiya shine bazan jureba Sam wlh, Amman kuma ayanzu bayyana gaskiya tinda wacce ba'aso ta Sani ta Sani dole Ce, zuwa yamma za'a had'a meeting .
Bari idan ta tashi sai muje wajan Baffan OK? Yanzu muyi bacci koda na k'uncine.”
Mamy zatayi magana idanunta na fitar da hawaye ya hanata Sam wajan manna bakinsa kan nata ya ja musu blanket ya k'ank'ameta qam yana bata wani irin kisses mai zafi tare da yamutsata lokaci d'aya ya cirema damuwarta kaso 60% cikin 100%, take ta sakar masa jikinta yana bata sabon salon darasinsa mai bala'in mantar mace a Inda take.
Yasan sarai bata sallah, sabida sanin lokacinta, duk da wani lokacin wata yana canzawa mutum Amman yana qoqarin ankarewa.
Sosai sukasha romantic d'insu kafin baccin yayi gaba dasu.

Da misalin qarfe 8 na dare....

*YI WA KAI*

Free Novel

_November 7/11/2022_



*55&56*

Misalin k'arfe 8 na dare motocinsu Zainabu suka shigo dutse, yayin kai tsaye suka nufi masaukinsu, yayin da suka samu tarba ta musamman

B'angaransu hajiya Karima kuwa 7:40 na dare suka shiga Gumel. Tinda suka zo tayi wanka tayi sallah kwanta ta huta tinda melai gidan baya gari, ta kasan cin komai tana buqatar hutu sabida fuskar Khairy ta kasa barin idanunta, tanajin matsanaiciyar fad'uwar gaba. Zaune ta miqe, da wani irin sauri kamar an mintsineta tace. “Ni dai nasan da kaina na shaqema jaririyar wuya tabar numfashi, bayan haka sabida bansan yadda Zan binneta ba cikin qurarran lokaci shiyasa na yanke shawaran nasata a kogi wanda inada yaqinin koda ace bata mutuba toh ruwan zai kasheta naman ruwa ya cinyeta. Ina sam ba ita ba ce d'iyarsu ce kawai kama ce mistswwww! Na wani damu kaina da abunda bazai yuba har abdan me had'in ma kifi da kaska, bari naje naci na qoshi ba wata shegiyar uwa ko 'ya da zasu rab'i mijina Mustapah na Karimatu ne har gaban abdan.” Ta fad'a tana saukowa falon, dan cika tunbinta. Makoh?m zaune tana cin dabino ta kalli Ammi tace. “Ammi! Gobe zanje nama Khairy sannu da zuwa, sai Nagano Mamy kwana biyu nayi missing nata.” Abida tace. “Wannan Maryama koh humm kinji wato d'azu Abbanki na waya da Dadyn Khairy koh?” D'an guntin murmushi tayi tana kallon Nafisa tace. “Zakije koh?” Nafisa tace“Eh idan Abba ya barni.” Maryam tace“Zai barmu qilama can yatafi shi.” Ammo tace“A'a baije ba.”

Asokoro

Aliyah zaune hankalinta kwance tanacin faten wake yaji attaruhu da albasada alayyahu, umma Sa'idah ta kalli k'ofar shigowa falon jin ana tab'a k'ofar. Salim ne cikin shigar manyan kaya. Aliyah gabanta ya fad'i ta dake tak'i kallon b'amgaran da yake. Aladabce ya gaishe da umman yana kallon Aliyan yadda tai wani irin cikowa tayi qiba, kamanin masu sabon cikin sun bayyana ajikinta. “Wai kallon uban me kake matane? Ince dai lafiya?” Salim ya had'e face yace. “Umma ita bata iya gaisar da miji bane? Ko ni sa'antane?” Sa'idah ra miqe fuskarta ba wasa tace. “Tashi wuce uban naka bai shigoba jeka can compound ka zauna idan yazo ka gaishesa, wlh Kar na sake ganin tsohuwar qafarka falona, sau nawa zanma kashe.” Bai Ce komai ba yana ciza baki ya miqe yana kallon Aliyu har yawu yake had'iya tsabar jaraba da ta taso masa, ita kuma ganin idanun umman akansa ta dinga banqaro k'irji da gangan tana gyara zama har cinyarta na bayyana... Kusan fad'uwa yayi, har Aneesa k'anwarsa na dariya ta toshe bakinta. Yana fita umma ta murza key k'ofar tana fad'in. “Wlh keko Aneesa zaici ubanki ne, Aliyah ki Kama kanki wlh idan ya miki dad'in baki kin zubar da cikin nan bazan sake Shiga lamarinki ba, ba ruwanki da shi sai kin haihu.” A ladabce ta amsa tana cin fatenta.

Galadanci Madedrcin d'akin taron da yake gidan Baffa liman cike yake da jama'a. Liman zaune saman kujeran da yake zama idan an had'a meeting. 'Ya'yansa kaf sun hallara sai wanda basa gari irinsu Auntie Aisha, amma idan an fara bayanin za'a kirata taji komai ta waya har an fad'a mata sai zumud'in taji me za'a tattauna take. Shattima na gefen mahaifinsa. Mamy zaune kusan inno yayin da Khairy take maqale da Mamy'n. Alhaji Bilal da Hajja Hafsatu iyayan Mamy sai Adam babban yayanta. Liman yayi gyaran murya ya bud'e taro da addu'a, kafin ya kalli Shattima yace. “Abdallah! Kai muke jira kace a had'a families meeting harda iyayan Bilkisu toh gamu kai muke saurare?” Shattima ya muskuta yana gyara zamansa, ya fara magana cikin kamewarsa kamar ko yaushe cikin sautin amon muryasa mai dad'in sauraro. “Da farko muna mai baku haquri iyayenmu, akan kuskuren da muka tafka abaya, duk da anamu ganin ba kuskure mukayi ba YI WA KAI mukayi nida Bilkisu, sbd duk wanda ya jiqan wani ya taimakesa kaima Allah zai taimakeka, idan kayiwa wani abun k'warai kanka ka yi wa... Abun farin cikin shine nago mahaifin Khairy ta sauqi mgnar da make muku wacce ta jefar da ita yau tazo gidana godiya sabida samawa d'anta aiki da nayi a Kaduna, sanadin hakane Ummulkhairi taji muna mgnar har ta tashi hankalinta.” Kakaf abinda ya faru tin ranan da suka tsinci Khairy Shattima bai rage komai tsaf ya zayyane komai kamar yadda Mamy ta fad'awa Liman da inno da Maryam kwanakin baya. Baki d'aya 'yan falon dikira suka fara tare da salallami masu tafa hannun nayi banda inno da Liman. Khairy kuwa wani irin kuka ta fashe da shi tana qanqame Mamy tana fad'in. “Don Allah Mamy karku rabu dani wlh ni dai bana son kowa zaman iyayena sai ke da Dady.”

Shattima yace. “Ok yi shiru daughter anji bar kukan kar kanki yayi ciwo OK?” D'ago da kanta tayi ta kalleshi ya janjina mata kai, kai ta d'aga tana lumshe idanunta ta kwantar da kanta kafad'ar Mamy hawayen sun kasa tsayawa daga idanunta, Mamy na famar buga bayanta. Hajja Hafsatu kallon Mamy da Khairy kawai take ta gasa furta komai sabida mamakin 'yar tata wacce bata San wane suna zata kirata ba. Alhaji Bilal ne yace. “Abdallah! Ai wannan tabbas Yi wa Kai ne kun kyauta kun riqe amana Bilkisu haqiqa kinyi qoqarin riqe wannan amana da hannu bibbiyu har kuka mata auren farko yanzu kuka sake mata na biyu, har Abadan Ummulkhairi jikar muce halak malak, liman ya kake ganin za'ayi wajan dosar mahaifinta da yake Gumel sabida muguwar matarsa nan?” Liman yay gyaran murya yana fad'in. Abdallah! Munji komai da ka fad'a Allah yamaka albarka ni wlh bakumin wani laifi ba taimako kukayi kanku kuka taimaka tabbas wannan abun Yi Wa Kai ne. Alhaji Bilal! Dole zamuje nida kai har Gumel zamuyi magana da mahaifin Khairyn.” Shattima yaji wani banbarkwai, ya kasa haquri yace. “Baffa Khairy fa batada wani mahaifi da ya wuceni kace wanda dai yay sanadin zuwanta duniya, Koh Baby?” Khairy ta d'ago tana kallonsa fuska kwab'e tace. “Eh Dady dana Allah kar arabani daku kaji? Ni Ku nakeso kune iyayena...” Idanunsa cikin nata yace.“Yeah Baby fatana ki nutsu ki daina wannan kukan kanki yana ciwo, OK?” Tana kallonsa tayi narai-narai da idanu, tace. “Dady! Na daina tinda bakaso.” Ta k'arashe mgnar tana lumshe idanunta, ta maida kanta jikin Mamy tana sauke lumfashi.

Sosai jama'ar falon suka tausaya musu ganin wata irin matsanaiciyar shaqu mai k'arfin gaske atsakaninsu. Mamy sai famar hawaye take tana buga bayan Khairy. Shattim yace. “Bilkisu! Please ki daina hawayen nan bana so don Allah, bakya ganin kanki ciwo zaiyi?” Kallonsa tai cike da k'aunarsa mai tarin yawa, tana jin fad'uwar gaba batasan matakin da zai d'auka ba idan yaji labarin Khairy matarsa Ce. “Na daina kayi haquri.” Shine abinda ta iya fad'a masa tana janye idanunta akansa.

Liman ya sake gyaran murya ya kalli Bilkisu yace. “Bilkisu! Kina buqatar na bayyana wancan sirrin ayanzu ayi zama d'aya ko sai nan gaba?”

Baki d'ayan falon kallon Mamy suke suji me zatace. Mamy ta kalli Shattima taga kaifafan idanunsa akanta tayi qasa da kanta tace. “Eh Baffa kawai a bayyana sai suyi jinya d'aya kawai a wuce wajan.”

Liman yace “Masha Allah, Allah ya miki albarka, haqiqa iyayanki Allah ya bazu 'yar da bakowa ake ba irinta ba.”

Ya fad'a yana yafito Khairy da hannunsa. Miqewa tayi jiki asake ta zauna gefensa suka saka shi tsakiya itada Shattima. “Yawwa Abdallah! Dakai Zan fara Kaine babba, nasan dai kasan babu wanda yake wuce k'addarasa idan Allah ya k'addarama abu baka isa ka tsallake k'addaraka ba, ko ka kuje mata kuma kasan dai tin ran gini ran zane koh?

Kai Shattima ya jinjina gabansa yana wani irin fad'uwa, ya d'ago narkakkun idanunsa yana kallon mahaifinsa sbd baisan me yake nufi ba. Liman yace. “Yawwa Allah maka albarka. Ummulkhairi inaso akoda yaushe ki kasance macace mai tawakali da amsar k'addaraki hannu bibbiyu kamar yadda yanzu kika amshi wannan k'addara naji dad'i, haka akeson cikakken mummuni ya kasance mai amsar k'addarasa, kamar yadda Bilkisu mace ta gari ta amsa. Dan haka abinda nakeso daku kuyi haquri Ku amshi k'addaraku kuyi min biyayya matuqar kuna ganina da daraja.” Shattima kallon mahaifinsa yake bakinsa kamar an rufe masa yana son yaji me zai masa biyayya bama shi ba harda Khairy. Ba Shattima da Khairy ba kowa na falon ya matsu yaji me liman yake nema wajan Shattima da Khairy. Ganin irin kallon da kowa yake masa yay murmushi yace. “Nasan duk na barku cikin duhu koh? Nan wato dagani sai Bilkisu da innar yara suka San komai, toh Ku kwantar da hankalinku yanzu zakuji komai.” Ya k'arashe mgnar yana kamo hannun Khairy ya kamo hannu Shattima ya had'e waje, ya jimqe. Khairy da Shattima suka kalli juna suna ma Kansu kallon mufa bamu San meke faruwa damu ba. Khairy ta langwab'ar da kanta tana sake jimqe hannun Shattiman cikin nata wani irin taushi biyu ne suka had'u, ga wani irin d'umi da sukeji atare cikin tafukan hannun nasu. Muryan liman ta dawo dasu daga kallon tambayar junansu da suke da ido. “Shattima! Ga Khairy amana na baka matarka ce halak malak idan dai nine mahaifinka inaso ka riqeta amana ka amshi aurenta bana son naji ko na gani ka quntata mata,Bilkisu matarka ita ce ta nemi hakan da amincewarta na d'aura muku aure sama da wata biyu sabida istiharan da nayi naga akwai alkahirin, na bayyana gaakiyane sabida bana son aga ko nayi son kai ra'ayinane na aura muku juna A'a zab'in Bilkisu ne, nawa tayaku roqon Allah ne idan da akwai alkahiry Allah tabbatar ga shi ubangiji ya tabbatar...”

A lokaci d'aya jinsu da ganinsu ya d'auke na wucin gani jin abinda liman ya fad'a, tin farkon fara bayaninsa suka zama kamar mutum butumi azaune ba mai iya k'wak'waran motsi, sabida yadda maganar ta daki zuciyoyinsu.

Wani irin zare hannunsa Shattiam yay wanda yake had'e dana Khairyn, tamkar saman wuta haka yaji hannun nasa, yay wata irin miqe tsaye yana kallon Mamy wani irin matsiyacin kallo, yake watsa mata. ya manta kowa da komai da yake cikin d'akin taro ya iso wajanta, har zai damqo wuyanta ya miqar da ita, sai kuma ya fasa ya Kamo hannunta ya miqar da ita yajata yana tafiya da ita, ya nufi hanyar fita daga d'akin taron. Cikin kuka ta d'aga murya tana fad'in. “Baffa wallahi sakina zaiyi don Allah ka dakatar da shi muna keb'ewa sakina zaiyi ina son mijina bazan Iya rayuwa babu shiba.

Don altlah kuyi haquri Baba Anne kuna gani fa zai fita Dani ya sakeni wlh gaskiya nake gayamuku zakina zaiyi daman yamun kashedin hakan duk Randa na sake maganar aurensa da Khairy zai rabu Dani yabar qasar kowa ya huta,dan Allah Ku ceceni Baffa...” Baffa liman idanunsa ya sauke k'asa tabbas yaga tashin hankalin da bai tab'a ganiba a idanun d'ansa ba lokacin da ya miqe....


*YI WA KAI*

Free Novel

_November 8/11/2022_


*57&58*


“Abdallah! Dakata! Komo zauna inason magana dakai akaro na biyu.”
Cak Shattima ya tsaya yana riqe da hannun Mamy, shi bai juyo ba shi bai tafi ba.
Shi mutum ne mai bala'in biyayya wajan mahaifinsa, bayajin zai iya qin ciki umarnin mahaifinsa ba, ya koma ya zauna d'in.
Juyowa yay yana sakin hannunta ya koma wajan mahaifin nasa ya zauna kamar wani mutum butumi, ya kasa kallon kowa ya kasa mgna, aransa dai yanaji tabbas sai yama Khairy saki d'ai d'ai har uku wanda bazama ayi batun gyara ba, Sam bazai iya zaman aure da khairy ba yayi yaya da ita? Ko ya mata wani kallo 'ya ko mata? Sam bazai iyaba mace d'aya yake buqata acikin rayuwarsa ita Ce Bilkisu Bilal, Khairy 'yarsa Ce ta har abdan.
Ko da wasa bai kalli gefen da Khairy take zaune ba, wacce ta jima da suma azauna amman ba wanda ya ankare da hakan.

Dukkan wanda yake cikin falon hankalinsa yayi bala'in tashi lokacin da sukaji Mamy na fad'in Shattima zai fita da ita ne dan ya saketa, shiyasa suka zabawa liman idanu dan suji abinda zai Ce, sosai hankalin Hajja Hafsatu ya tashi jin 'yarta na batun za'a saketa daga taimako. sai lokacin da sukaji liman ya basa umarnin ya dawo duk hankalinsu ya dawo jikinsu.

Gyaran murya Liman yayi yana kallon Shattima ya kirasa.

“Abdallah!”

Kansa ya d'ago narkakkun fararen idanunsa sun rikid'e sunyi jajir, ya kalli mahaifin nasa dak'yar ya iya bud'e baki ya amsa da.

“Na'am Baffah!”

Liman yace.
“Gaskiya ne abinda Bilkisu ta fad'i janta da kake qoqarin yi waje dan ka saketa ne, akan kawai ta had'a alkahiri tsakaninka da Ummulkhairi? Inaso ka amsa min?”
Shattima yay k'asa da kansa ya saki wani irin zazzafan numfashi, kansa tsaye sabida shi mutum ne kaifi d'aya bai iya wani niqu-niqu ba, yace.
“Eh Baffa gaskiya ne, sbd na mata kashedin hakan munyi mgnan ba yau ba an wuce wajan ni har Abadan Ummulkhairi matsayin 'yar da na haifa take awajena ba mgnar aure, shine tazo ta had'a. Baffah don Allah kuyi hkr Ku yafemin zan saketa taci gaba da zama matsayinta na 'yar cikina....”

Tsawa Liman ya daka masa yace.
“Baka isaba Abdallah! Kana nufin ni zanyi abinda zai cuceka? Kasan adadin kwanakin da nayi ina istihara akan lamarinka da Khairy? Kana nufin zamu cutar da kai? Wato baka amshi auren ba sakinta zakayi?”

Shattima kansa aqasa zuciyarsa zafi kawai take.
“Toh Bari kaji wlh wlh wlh idan ka kuskura ka ma Bilkusu ko kallon banza bare akai ga saki ban yafe maka ba.”

Shattima ya d'ago yana kallon mahaifinsa cike da mamakinsa, yanajin wani irin k'una azuciyar tasa.

“Eh kalleni dakyau, kuma duk Randa ka furtawa Khairy saki ko ab'oye kaje ka auramata wani bamu saniba wlh tallahi ban yafe maka ba, zaman aure ya zama dole da ita rabon da ubangiji ya k'addara tsakaninku ina zaku kaishi? Duk Inda kakaita sai ta dawo gareka wlh ina fad'a maka dan haka ni Umar mahaifinka nake umartarka ka janye dukkan k'udirinka akan matanka.”

Ya k'arashe mgnar aransa yana fad'in.
“Abdallah Allah maka albarka na yafemaka duniya da lahura dukkan yadda zaka nunawa matanka fushinka, nasan kana yanayi dan dole sai ka nuna fushinka azahiri, kawai na furta azahirance ne dan kaji tsorin bakina karka d'auki mataki mai tsauri ne, Allah ya karemin kai da dukkan sharrin abun qi.”

Shattima kansa k'asa ya matso kusan mahaifinsa yace.
“Dan Allah Baffah! Ka yafemin tinda nake da kai kullun albarka kake sakamin da addu'o'i na neman tsarin sharrin mutum ko aljan, amman me yasaka yau akan mace zakamin baki?”

Baffa ya had'e fuska yana fad'in.
“Ni ban maka baki ba ai sai kayi abinda na haneka tukun.”
Alhaji Bilal yace.
“A'a liman baza'ayi haka ba ka dai yafe masa nasan Abdallah da biyayya insha Allahu bazai qetare maganarka ba, yanzu yaushe ne zamuje can Gumel d'in? Dan nafison ayi agama komai, kowa ya huta.”

Liman yace“Zamuje insha Allah kasan irin mugayen matan nan ba'a tinkarasu haka kai tsaye gaba da gaba, dole sai nayi mana 'yan addu'o'i koda na sati d'ayane yadda Allah zai jib'anci lamarin mu komai yazo da sauqi.”

“Eh toh hakan ma yayi Allah ya karemu da sharrin dukkan masu sharri.”

Falon baki d'aya jama'an suka amsa da.
“Allahumma Amin.”

Liman ya kalli Khairy yace.
“Ummulkhairi! Allah miki albarka wlh kinyi matuqar burgeni yadda baki nuna damuwa ko neman bijirema umarnin mu ba, zo nan d'iyata.”
Ya faad'a yana beqa mata hannun da nufin sake had'e hannunsu akaro na biyu.
Idanunsa ya zaro ganin kamar bata ko motsi jini na bin qofofin hancinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Abdallah tab'amin yarinyar nan.”

Wani irin damm k'irjin Shattima yayi wai ya tab'ata, shifa yanzu Sam baya buqatar wata alaqa da Khairy, wacce zata had'a jikinsu sabida yadda lamarin ya juye mugun nauyi abun yake masa.
Ba yadda ya iya ya waigo yana kallonta, jinin da yagani yana kwararowa daga hancinta ne ya razana shi, ya kai hannunsa kanta yana kiranta.

“Daughter!”

Ya kirata sai kawai sukaga ta fad'o jikinsa bata motsi, jinin na zubowa daga hancinta.
Mamy wani irin kuka ta fashe da shi ta nufo wajan aguje ta zube gabanta ta d'agota daga jikin Shattima,wanda ya dasqare, ta shiga girgizawa tana fad'in.
“Shattima muje asibiti karta mutum dan manzon Allah. ”
Liman yace.
“Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil LA Haula Wala Qauwwata Illah Billah.

Abdallah tashi mana d'auketa ko sai jininta ya qare?”
Shattima ganin halin da Khairyn take ciki ya firgitasa sai ya mance waccan batun na mata yana kiranta “Baby! Daughter! Me ya sameki?”
Ya fad'a yana sanya tattausan hannayensa ya ciccib'eta ya nufi hanyar waje yana fad'in.
“Bilkisu muje ki dubata da kanki yi sauri.”

Mamy ta d'aga kai tana share hawayen fuskarta taji dad'in yadda Shattiman ya nuna damuwarsa ga Khairyn sabida ta sarema lamarin nasa.

Dole taron ya watse inno liman Alhaji Bilal Hajja Hafsatu Munnir Balaraba Adam, da sauran jama'a haka suka dinguma hospital sukabi bayan su shattima duk hankalinsu atashe.
Masha Allah Khairy ba abinda zatace sai godiyar Allah sabida har yanzu kakaf wajan families Shattima Dana Mamy ba wanda yaji ya tsaneta sai qarin k'aunarta da sukaji aransu.

Daga can Abuja kuwa dukkan abinda ya faru tanaji ta waya wacce Balaraba take riqe da ita, har aka kammala zuwa lokacin da Shattima ya d'auki Khairy zuwa asibiti.
Zaune take cikin bedroom d'inta tama rasa abun cewa jin hankalin Balaraba atashe bata katse kiran ba, suka fita zuwa asibitin, sai ita ta katse kiran.
Wayan ta ajiye saman table, tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hasbunallahi Wa Ni'imal Wakil, kenan dai nice silar komai sabida uzurama Bilkisu da nayi bata haihuwa duk da ba wani jimawa sukayi da aure ba alokacin? Allah sarki Bilkisu ashe Khairy ba 'yarki bace? Ki yafeni nima lokacin bansan me ya hau kainaba, Sam ban kyauta ba ki yafemin, kaji k'udirar ubangiji ya raineta ya aureta, haqiqa Bilkisu macace jaruma wadda samun irinta ayanzu zaiyi wuya matuqa, ki yafemin Bilkisu, ba'a samun mata irinki ayanzu.”
Auntie Aisha ta k'arashe mgnar tana zubar da hawaye.
“Tabbas ni zan fuskacin Wannan shegiyar muguwar matar insha Allahu zataga yadda wazan zai kaya...”

Suna zuwa asibitin Mamy da kanta ta shiga taimaka Khairyn cikin wata irin jarumta, take dubata suka had'u da Dr Lawee abinka da asibiti mai wadatattun kayan aiki, cikin 1 hour suka gama ganon matsalar tayi mugun razana ne da jin labarin da ya daki k'irjinta har zuciyarta ta kusa bugawa wanda hakan yay sanadin tsayuwar numfashinta.

Dak'yar suka shayo kan ciwon na Khairy wanda suka samu ta farfad'o sai dai bata hayyacinta fizge-fizge take tana sambatu marasa kan gado ba abinda yafi d'agawa Mamy hankali sai furucinta.
“Wayyo Allah da na zauna da Dady matsayin mijina wlh tallahi gwara na mutu nasan bana duniya, a ina d'iya ta tab'a auren ubanta? Wlh kaina Zan kashe ko na shiga duniya kowa ya huta...”
Wannan kalaman suka razana Mamy hakan yasa ta banka mata allurai na bacci na tsawon 24.
Mamy tana fitowa tamata liman da iyayanta harma da shattiman bayanin komai akan Khairy da abinda take fad'in da ciwon da saura k'iris ta rasa ranta sabida yadda maganar ta shige ba zato.
Shattima uffan bai ceba liman ne yace.
“Insha Allahu komai zaiyi daidai shi zamu gayama zata haqura Allah ya bata lafiya, ke Bilkisu kije gida kuje kawai inno zata zauna wajanta sabida ganinku ma idan ta farka wani tashin hankalin ne.”
Mamy tace“an mata alluran bacci sai gobe wannan lokacin zata farka daman zamu tafi akwai masu dubata idan qarin ruwan ya qare a d'aura mata wani.”
Liman albarka ya sakawa Mamy kowa yayi haramar tafiya gida.

Misalin 12 na dare Zainabu kwance idanunta arufe ba bacci take ba, nazarin rayuwa kawai takeyi.
Zaune ta miqe tana kallon abokanan tafiyarta kowa baccinsa yake.
Tsaye ta miqe taje ta d'auro alwala ta dawo daman da dogon hijab ajikin, ta d'auki darduma d'aya cikin darduma ukun da suke ajiye ad'akin.
Sallah tayi raka'a hud'u ta gayama Allah buqatunta tana kuka kafin ta shafa addu'a ta miqe ta linke darduman ta komanta kwanta lokacin 2 na dare.

*Commissioners Quarter's*
_K'arfe uku na dare_
Shattima zaune yake tsakiyar qatuwar bedroom d'insa, saman wata tattausar darduma sanye da jallabiya sabuwa dal milk colour, sai wani irin bala'in qamshi yake, acikin awannin da suka wuce tashin hankalin da ya gabata har fuskarshi ta d'an yi rama duk da bazaka tab'a gane b'acin ransa ko zallar damuwarsa ko tashin hankalinsa ta fuskarsa ba, amma kallo d'aya zaka masa kasan baida wata nutsuwa.
Hannayensa sama addu'a yake yana kukan zuciya akan wannan lamari sabida Sam baiji ya amshi Khairy matsayin mata ba, abun akwai mugun

Please Login or Register in order to submit comment