Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har suka buɗe ƙofa suka fice.
Ajiyar zuciya ta sauke, tana bin ƙaton ɗakin nata da kallo yadda ya tsaru iya tsaruwa.

Auntie Aisha koda ta sauko ta fito sai da ta biya wajan Shattima sukayi magana kafin ta tafi.

Anutse ya fito yana sanye da wani farin yadi me shegen kyau da tsada, yana zuba uban ƙamshi, yana karkaɗa makullan hannunsa na mota, ya nufi compound ɗin gidan.
Tun daga nesa kafin ya iso, babban Guard ɗinsa ya buɗe masa mota side din baya, Maleek ya shiga yana jiransa.
Isowa yay wajansu da sallama, anutse yace.
"A'a zan fita ni ɗaya, Maleek! Ya gajiyar hanyar? Yanzu kuka shigo ne?"
Cike da ladabi ya amsa.
"Eh Yallaɓai sai sallah da muka rama."

Kai ya jinjina ya shiga parking lot ya janye rigar motar da makullan suke hannunsa, ya buɗe ya yi bismillah ya shiga ya mata key yaja nufi babban haɗaɗɗan gate ɗin yana horn ahankali.

Yana hawa kan titi ya lalubo lambar Mamy ya kirata.
Tana famar ringing ba'a ɗaga ba.
Numfashi ya janyo da ƙarfi yana furzar da iskar waje.

Acan Jigawa Mamy bayan ta yi kukanta ta gaji, ta miƙe jin ana kiran sallar Maghrib, ta sauka ta kunna ƙwan wutar ɗakin, ta shiga ta yi alwala ta fito ta sanya hijabi na sallah, tayi sallah.
Tana idarwa bayan tayi azkhar, ta ɗauki Qur'ani me girma ta fara karatu bata dainaba se da taji anyi kiran sallar Isha'i, ta miƙe ta yi sallah, ta koma taci gaba da karatunta se da taji zuciyarta ta yi sanyi sosai wannan nauyin da ya danne mata ƙirjinta babu, ta rufe Qur'anin tayiwa Annabi salati ta ɗaga hannunta sama tana addu'a tana roƙon ALLAH subhanahu wata'ala, akan Allah ya basu zaman lafiya da Khairy yaba mijinsu ikon yin adalci atsakaninsu, ya hane tauye haƙƙin kowace acikinsu, ya kare shi daga sharrin maƙiyansa, ALLAH ya ƙara masa buɗe'i dukiya ta halali yaci gaba da ciyar dasu da dukiyar halali.

Ta jima tana roƙon ALLAH sarki alkhairi, da roƙawa iyayanta lafiya da nisan kwana, da fatan cikawa da imani, kafin ta shafa addu'a ta miƙe ta cire hijabi ta linke, ta ɗauki wayanta taga ƙarfe tara na dare ta wuce.

Manyan fararen idanunta Wanda sukayi ja suka kumɓura ta zaro ganin lokacin ya shige dayawa.
Sai taji gabanta ya faɗa ta lumshe idanunta tana jin ƙananun hawaye suna gangaro mata akan fuskarta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
Ta faɗa tana sakin murmushi tana kallon hoton Shattima da yake mata murmushi wanda shine akan screen ɗin wayata.
Kamar zai kirata ta amsa yana sanye da fararen Armani's jikinsa yana kallonta yana murmushi damples ɗinsa sun loɓa, ta masa hoton.
Kiss tama hoton tana murmushi tace.
"Mi Amor na Bilkisu da Ummulkhairi."
Ta faɗa tanajin zuciyarta wasai babu wani zafi ko nauyi sai ɗan abinda baza'a rasa ba.
Fitowa ta yi anutse.
Ƙofar falonsa ta tsaya ta buɗe ta shiga falon ƙamshinsa ta shaƙa ta lumshe idanunta,ta buɗe, ta kalli hanyar bedroom ɗinsa ta yi ɗan murmushi tana kallon picture ɗinsu manne da bango shi da ita, ɗayan da Khairy.
Juyawa tayi ta fita daga falonsa ta murza key ta rufe ta zare key ɗin, tana karkaɗawa ta sauka downstairs.

Tv ta kunna ta koma ta zauna tana kallon Arewa 24 an saka film ɗin abarwa Rai.
Cikinta taji yana murɗawa ta ɗauki wayanta ta kira lambar Laraba.
Bugu ɗaya ta ɗaga.
Anutse tace.
"Laraba! Yanzu kun tafi ɓangaren ku, me kuka girka ne?"
Laraba tace.
"Mamy tuwon shinkafa ne da miyar ƙuɓewa da bisashen kifi, naga na ranama ba'a ciba oga ne ke bakya gari shi kuma baya cin abincin masu aiki shiyasa bamu masa da dare ba."
Mamy tace.
"Haka ne ki zubemin malmala guda ki kawomin zanci, bari nazo ta ƙofar kitchen ɗina na buɗe miki ƙofar."

Ta faɗa tana katse kiran ta ajiye wayan akan Centre table, tana miƙewa ta tafi.
Toh lokacin ne Shattima ya yi ta kiranta bata ɗauka.
Can Shattima hankalinsa yaji ya tashi, sai kiranta yake.
Laraba yadda Mamy ta nema ta zuba mata a plate ta rufe, suka haɗu ta kitchen ɗinta ta bata ta juya, ita kuma ta rufe ƙofar.
Lemon coconut ta dauko da tufa ta jera akan tray ta dawo falon.
Tana ajiye trayn wani kiran ya shigo.
Zama ta yi, ta ɗauki wayan, tana picking call ɗin, ta sake seta nutsuwata ta yi masa sallama.
Ajiyar zuciya Shattima ya yi yana amsa sallaman anutse yace.
"My sweetheart Ina kika shiga? Kinji yadda naji kuwa? Amman ya naji muryan matata kamar ta canza don ALLAH me ya sameki Sweetheart?"

Mamy gabanta ya faɗi tasan halin Shattimanta Tsaf ya gama saninta ciki da wajanta.
Ƙyalƙyalewa ta yi da dariya tace.

Mi Amor! Ka zaci ina kusa ban ɗauki kiran ka ba? Toh da ka min me? Babynka ne yakejin yunwa shine na samo masa abinda zai ci, kirani video call nasan zaka fi yarda yanzu nacema, banda wata damuwa bazaka yarda ba, kirani kaga zuciyarka tana yadda ka barta My Love."

Ta faɗa tana dariya hawaye na zubowa akan fuskarta.
Shattima yana murza stiyarin mota da hannunsa ɗaya, ya sauke numfashi yace.
"Wlh haka kawai nakeji ajikina matata tayi kuka sam wannan ba muryata bane, my sweetheart ya kike so nayi don ALLAH?"
Mamy kukan gaske yake son ƙwace mata tace.
"Mi Amor nace muyi video call ka ganni zakafi nutsuwa kaji?
Ni yanzu ba wannan ba, sannu da isa ya gajiya? Fatan ka sauka lfy? Ina Baby? Fatan batayi rigima ba, tana nemana?"
Ta faɗa tana dariya.

Shattima ya furzar iskar bakinsa, yana murmushi yace.
"Wlh Sweetheart kamar kin sani tayi, amman ban ganta ba munyi waya dai Auntie Aisha ta bani ita wai bazata tafi ba, sai an kawoki yanzu dai ahalin da ake aciki yanzu kina nan Abujan, wajena tana can tana jiranmu."

Mamy sosai hira ta bata dariya tace.
"Au wai tanama gidan Aunty Aisha?"
Shattima ya kasa cemata A'a yauninta yakeji, sai kawai yace mata.
"Eh, yanzu meye zakici Sweetheart ki barni uhm?"
Mamy tace.
"Mi Amor tuwon shinkafa, zo muci toh."
Murmushi ya yi yace.
"Ok ganinan muahhh I love you kici da rabona Please, ki gaishemin da Baby kice nace masa/mata I love you, bye zan kiraki anjima idan bakiyi bacci ba."
Mamy tace.
"A'a Ni kam yanzu ina gama cin abincin kwanci zanyi mun haɗu da safe i love You too bye."
Murmushi ya yi ya katse kiran, yana driving ɗinsa anutse.

Mamy ta ajiye wayan tana murmushi tace.
"Bawan Allah baya son nasan Baby tana gidansa Ko, Auntie Aisha sakara ce zata sauke masa mata gidanta, ita da take rawan jikin suyi su tafi da amaryar Hamm."
Ta ƙarasa maganan tana murmushi tana goge ƙwallar idanunta.
Ta ɗauki plate ɗin abincin ta fara ci.
Loma biyu kaɗai ta iya ta ajiye plate ɗin ta ɗauki kwalin lemon coconut, tasha fiye da rabi tayi hamdala, ta ɗauki wayanta ta kira, ƴaƴanta Adam.

Bata jima tana ringing ba ya ɗauka.
Sallama ta masa tana gaishesa ta ɗora da cewa.
"My brother Dan Allah zan turo Lawan direba ya ɗauko min me sunan Anne tamun kwana biyu, ta ɗauko kayan zuwa makaranta, sai adinga kaita daga nan."
Adam yace.
"Toh shi kenan kin ganta nan dama gidan Anne zan kaita ita dasu Ayman tunda weekend ne. Kibari zan biyo na ajiyeta in Sha ALLAHU."
Mamy tace.
"Thank you so much my brother sai kunzo bye.'
Ta faɗa tana katse kiran.

Lambar Abidah ta kira, bugu biyu ta ɗaga tare da sallama Mamy ta amsa suka gaisa tace.
"Daman dan nayi wa Hajiyata ban gajiya ne, ya gida? Don Allah a fadawa Abban Maryam idan ba damuwa tazo mu zauna kwana biyu."
Abidah tace.
"Ai ga shi zaune yana jinki yanzu kuwa in Sha ALLAHU direba zai kawo miki ita, ai dole wlh yau kina buƙatar abokin hira, Maryam ke tashi maza ki shirya gidan Bilkisu zaki koma kafin uban naki ya gama cin amarcinsa, ya dawo."

Ta ƙarashe maganan tana kallo Abba Aminu da yamata zuru da idanu yana kallon yadda take haƙiƙancewa tsakaninta da ALLAH.
Mamy murmushi ta yi tace.
"Ngd Hajiyata ina duba hanyarta."
Ta katse kiran.
Tana ajiye wayan ta ɗauki tufa tana ci bata wani jin ɗanɗanonsa ci kawai take.

Abba Aminu yana murmushi yace.
"Maryam! Yi sauri ki shiyar kizo zan saukeki tunda ba nisa."
Maryam ta miƙe ta wuce.
Ammi tace.
"Ikon ALLAH! Kai kuma ina zakaje adaren nan?"
Kallon Nafisa da Habibi da autansu Sabir ya yi sun musu zuru fuska ya haɗe yace.
"Nafisa bana son shashanci, kunada jarabawa kina zaune koh? Sabir! Oya je ɗauko books ɗinka Ammi ta duba maka."
Habib tun kafin azo kansa ya sulale yabar falon.

Ammi tace.
"Ina zakaje Abban Abdoul?"
Murmushi ya yi yana matsowa ganin ba kowa falon, ya sumbaci bakinta ya miƙe tsaye yace.
"Wai da zanje zance ne ko kar naje?"
Dariya ta yi tana tafa hannayenta tace.
"Kama fara? Tsofai-tsofai dakai hakan gemu ya fara furfura shekaru hamsin da ɗoriya zaka zance? Ko kaima an gogama haukan tsufan, auren zakayi? Duk da Shattima bai kaika shekaru ba kuma ba yin kansa bane, matarsa ta aura masa, ai ga shi nan tana kukan zuci."

Kansa ya shafa yace.
"Ni har na tsufa Abidah? Ai ke kika tsufar dani. Kuma haka tagani take so.."
Tsaye ta miƙe cikin ɓacin rai tace.
"Wlh karka saka nayi abinda ranmu zai ɓaci mu duka."
Da sauri yabar wajan yana murmushi, yace.
"Kenan duk randa na shirya aure na ɗaure ƙugu?"
Ya faɗa yana barin wajan da sauri, yace.
"Maryam ta sameni a mota."

Ammi tace.
"Wannan wlh akwai abinda yake ransa tabɗijam! Bari dai na saka masa ido naga me zai biyo baya, daga wasa ake wucewa gaske idan anga fuska."

Sabir ya zauna kusanta yace.
"Ammi ga book ɗin ki dubamin."
"Kaga jeka wajan Habib har nagama yaƙin gabana."

Maryam ta fito da ƙaramar trolley tace.
"Ammi ina Abban?"
"Yana waje yana jiranki."
"Toh Ammi bye natafi."
Ammi tace.
"Nima zanje goben mukwana lfy."

A mota Maryam ta samu Abbanta yana baya, zata shiga kusan direba yace.
"Maryam! Dawo magana zamuyi."
Baya ta shiga ta zauna, tana rufe motar.

Se da motar ta hau kan titi Abba Aminu
Ya kirata.
"Maryam!"
Ta kalleshi ta amsa.
"Na'am Abba."
Kansa ya ɗan girgiza aransa yana faɗin.
"Kai bazan faɗa mata ba, ta kwashe ta faɗa wa Abidah, gwara har na karasa shirina na kama Baby a hannuna kafin hakan."
Murmushi ya yi yace.
"Idan kinje kiyi ƙoƙarin saka Mamunku farin da hira me daɗi, ki kula da zuwa makaranta fa!"
"Toh Abba in Sha ALLAHU..."

Suna zuwa bakin gate aka sauke Maryam.
Sai da ta shiga yace direba yaja sutafi.

Mamy sosai tayi farin cikin zuwan Maryam ta rungumeta, tana mata sannu da zuwa.
Ba'a jima
Hafasat ɗiyar Adam ta iso.
Mamy tace.
"Kai yau Ni ƴar gata ce na haɗa ƴaƴana biyu, tare zamu kwana muna hira."
Dariya Hafsah tayi tace.
"Ai kam Mamy, naji daɗin dawawo nan kwana biyu, gidan Mamy kayi abinda kakeso ba kwaɓa ba hantara."
Maryam tace.
"Wlh kuwa."
Mamy tana murmushi tace.
"Idan abun kirki kake ba! Idan kayi ba daidai ba dole zan kwaɓeka."
Dariya sukayi suka miƙe suka haye sama da kayansu, ɗakin Khairy suka kai, suka dawo suna hirasu hakan ya saka Mamy nishaɗi...

Acan Abuja Shattima bai dawo gidaba se dare sosai.
Lokacin su Suhailat sun manta da sunyi bacci, a ɗakin da Auntie ta basu a ƙasa.
Khairy kuwa tana can tana raba idanu ga wayanta ta nema kaf ta rasa, tafi tunanin Auntie Aisha ta tafi da ita.
Ta yi kuka ta gaji, yanzu tafi zargin wayo aka mata Mamy bata zo Abuja ba!

Shattima yana shigowa ya rufe ko ina, ya kashe ƙwayayen fitilun falon, ya kashe makekeiyar Tv da take manne abango, ya nufi hanyar upstairs.

Ɓangarensa ya tsaya ya yi shirin bacci cikin wasu irin fitinannun kayan bacci farare masu taushi, yana wani irin fitinannan ƙamshi kansa ya kalla a ƙaton dressing mirror ɗinsa, yana lumshe Idanunsa, shi da kansa yasan Allah ya masa kyau duk baida jiki talaulayin jikinsa ya masa bala'in kyau, ga baiwar gargaza, iska ya furzar ya na kashe dukkan wayoyinsa ɗaya bayan ɗaya ya kashe, ya barsu anan jera kan dressing mirror ya juya ya fita.

Falon nasa ya kara kallon yadda aka sake ƙawatasa, ledojin da ajiye kan table ya kalla da plete da ya ajiye,hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon baccinsa ya fice.
Tana kwance lamo zuwa yanzu tsoro ya fara cikata, sai rarraba idanunta take.

Anutse ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, yana sauke kaifafan lumsassun fararen idanunsa akanta, ya ji wani irin Damm gabansa ya buga da ƙarfin gaske.

Matsagaitan kyawawan idanunta ta zuba masa, tanajin fitinanniyar kewarsar na ratsa dukkan illahirin jikinta. Sosai tayi ƙoƙari wajan danne zuciyarta, bata nuna masa kewarsaba ƙarara duk da idanuwanta sun fallasa sirrin zuciyarta.
Anutse ta amsa sallamar tana tambayarsa.
"Dadynah ina Mamy take."
Ta ƙarashe tambayar shi tana janye idanunta daga kallonsa sabida raunin da zuciyarta ta fara.

Tunda idanun Shattima suka sauka akan Khairy, ya kusa gigicewa da yadda ta koma cikin wata ɗaya da ƴan kwanaki da bai sakata idanunsa ba.

Idanunsa ya ɗan lumshe, fitinannan ƙamshin da ya shaƙa cikin dakin nata, wani irin yawu ya haɗiya, yana ƙoƙarin ɓoye rikicewarsa, cike da kamewarsa anutse cikin taushin murya ya furta.

"Babyn Ruhi bakiga Dady bane? Ta Mamynki kike kenan yanzun?
Oya zo nan naji me nene Baby taso Ok?"
Kallonsa ta yi akaro nabiyu tana langwaɓar da kanta, ta kwantar da kanta kan pillow ashagwaɓe tace.

"A'a Ni dai idan babu Mamy atare da kai kaje kawai."
Ta faɗa cikin shasheƙar kuka.

"Ya SALAM! Baby?"
Ya faɗa yana nufu wajanta.
Zama ya yi gefen bed ya sanya tattausan hannayensa, ya warware mata lafayarta jikinta, ta fara sauka, ya kamo kafaɗunta yana faɗin.
"Yi shiru Baby ba gani ba me yasa sai Mamynki tazo uhm?"

Ya faɗa yana kallon tsararren kitson kanta da ƙunshinta, har baisan lokacin da ya kamo hannunta ba yana murzawa ahankali.
Fitinannan ƙamshi da taushin fatarta ya saka shi lumshe Idanunsa yana tattarota baki ɗaya ya mannata ƙirjinsa, yana sauke numfashi.
Cikin kukan zallar shagwaɓa ta fara ƙoƙarin janyewa tace.
"Ni dai babu ruwana daku daga Mamy har kai, tunda kuka min wayo, ashe bata zo ba."
Lafayar jikinta ya ƙarasa warware wa, yana kwantar da ita ya mata rumfa da wadataccan ƙirjinsa mai Yalwar gashi ya tallabe bayanta fuskarsa dab da ta ta ya raɗa mata.
"Kiyi haƙuri kinji Babyn Ruhinta taso muje na baki abinci kici muzo kiyi bacci akwai gajiya atattare dake bari kukan haka, muga hawayen shagwaɓa."

Ya faɗa yana tallabo fuskarta ya zaro harshensa yana tsotse hawayen yana lumshe Idanunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
Baki ta turo gaba tace.
"Dadynah na daina kukan."
Harshensa ya ɗora akan laɓbanta yana lasa, hannuns sanya ya kamota ta zauna.
Sauka ya yi ya kamota ya ɗagota, ya cirata sama kamar Baby ya rungumeta yana mata magana ƙasa².
"Bbyna wannan ƙamshi da taushin bema Dady yawa ba, bamu kaɗai bane agidan uhm?"

Kanta ta ɓoye ƙirjinsa bata iya cewa komai ba, dan bata manta kashan su Auntie Aisha ba.
Falonsa ya direta saman sofa.
Kusanta ya zauna jikinsu baya haɗe, matsawa ta yi tana turo baki.
Kai ya girgiza yana buɗe ledar manya kajini gashi na musamman, ya ciro guda ya cira yana kai bakinta.
Kai ta girgiza.
Fuska ya haɗe yace.
"Wannan sadaka zakici Baby nasan kina jin yinwa, haaaaa."
Bakinta ta buɗe ahankali ya saka mata tsoka mai kyau, ya sumbaci bakin nata.
Anutse take cin abunta hankalinta kwance.
Sosai ya ciyar da ita, ya cika mata cup da fresh milk ya bata abaki ta sha.
Bakin ya lashe yana kwantota jikinsa.
Ahaka shima yaci kaɗan yasha lemon coconut da Mamy ta koya masa Shansa, tun samun cikinta.
Hannunsa ya wanko ya kamata suka shiga Bedroom ɗinsa a toilet ɗin sa ya mata brsh, ya kama hannunta suka fito ya maida sauran abinda suka rage fridge.
Suna shigowa ɗakinta ta zame hannunta tace.
"Dadynah mukwana lfy, se da safe..."
Hannunta ya ɗamƙo yajata toilet.
Tana ga niyarsa ta fashe da kuka tace.
"Ni dai zanyi da kaina, Please kaje."
Bai musaba ya fita ta rufo ƙofar harda mirza key.
Tafkekiyar wardrobe ɗinta ya buɗe ya ciro rigar bacci ƙaɗan tafi guiwa pink colour mai taushi ya ajiye mata akan stool ya haye bed abinda ya shige Duvet.
Bata wani jimaba ta sanye kayan jikinta, tana zazzaro idanunta har ga Allah a tsorace take.
Kallon gadon tayi tana turo baki.
Anutse yace.
"Ki ɗauki rigar nan ki saka.
Rigar ta kalla kamar zatayi kuka tace.
"Wannan tayi ƙarama gaskiya, kuma Dadynah ka tashi ka tafi ɗakinka idan kuma nan zaka kwana bari Ni ta tafi ɗakinka ko wajansu Suhailat ƙasa."
Ta faɗa tana ɗaukan rigar.
"Eh kije ɗakina zan kwana anan tunda haka Auntie Aisha ta koya miki tsayin wata da kwanaki."
Da
"Toh"
Ta amsa ta tafiyar ta.
Murmushi ya saki ya gyara kwanciyarsa.
Tana zuwa ta cire kayan jikinta ta goge jikinta da towel ɗinsa sabo, ta shafa mansa ta saka rigar, ta fito dan kulle falon, tana isa bakin ƙofar yana buɗe ƙofar.
Idanunta ta zaro tana sakin ihu tana duƙewa ƙasa tace.
"Don Allah Dady ka fita ai ba haka mukayi d kai ba."
Key ya murza ya isa wajan kashe wutar falon ya kashe ya iso wajanta ya ɗauke ta.
Kukan shagwaɓa ta saki tana dukan ƙirjinsa tace.
"Ni dai bana so saukeni."
Wutar bedroom ɗin ya kashe yana kwantar da ita saman makeken Italian bed ɗinsa, ya haye bed ɗin cikin taushin murya cikin raɗa yace.
"Babyna ya isa rikicin haka ke ba yarinya bace, ba karatun da baki saniba tishine zanyi, kuma ba yau ba, ki nutsu bari rikicin bacci me daɗi zamuyi abinmu yau, Ok? Ya isa kukan kar kanki ya yi ciwo, Babyn Ruhi bana son canjin nan naki, Dady ne fa! Ko an daina son Ruhi shi kaɗai yake haukansa uhm?"

Ya ƙarshe magana yana kunna fitilar gefen gadon, ya tattarota jikin jikinsa ya rungumeta gam, ya jamusu Duvet, ya raɗa mata akunnenta.
"Maza yi addu'a bacci."
Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara lafewa jikin Dadyn nata tana shaƙar ni'imataccen ƙamshinsa.
Anutse yake shafa santala-santalan cinyoyinta, yana haɗiya yawu, yana mata magana acikin kunnenta, wadda duk ƙwaƙwarka bazaka ji me yake faɗa mata ba, tayi lamo abinta, tana sauke numfashi.
Hannunsa ya gangaro zuwa ƙirjinta ya sauke tsakiya daidai nipples ɗinta, ɗan shafo, tsikar jikinsa na mimmiƙewa.
Ya furta.
"Ya Rabbi!"
Ya yi saurin janye hannunsa, sanin ba lallai ya jureba, tunda bai tashi shiga daga ciki ba.
Ƙanƙameshi ta yi tana sakin kuka tace.
"Dadynah ka bari Please kaji."
Kissing kunnenta ya yi can ƙasa yake mata raɗa yana lasar fatan kunnenta.

"Dole zan bari Babyn Ruhinta.
Baby me Auntie Aisha ta miki kika ƙara wani irin bala'in taushi, ga ƙamshi me tsuma zuciya uhm?"
Ya faɗa yana lasar fatar wuyanta, tare da tsotsar fatar wunya nata.

Hannunsa da yake shafa cikinta zuwa marata ta riƙe tace.
"Ruhina ka bari don ALLAH kaji Dady love?"
Wata irin runguma ya mata, ya sumbaci bakin roƙon, daman baida niyar zurfafawa iya kissing kawai ze tsaya, yace.
"Toh Babyn Ruhinta na bari oya kiss me."
Ya faɗa yana shafa fuskarta ya haɗe face ɗinsu anutse ya haɗe bakinsu yana bata kisses mai tsadar gaske, ya fara mata wasa da harshenta.
Wani irin yawo ya fara mata da harshensa cikin bakinta, wanda ba tama san lokacin da take shanye ruwan yawunsa ba, tare da tsotsar harshensa.

Ita kam tunda taji baya taɓata iya kissing ne ta biye masa suka sha yawun juna, daga ƙarshe bacci me bala'in daɗi ya ɗaukesu suna ƙanƙame da junansu cikin so da ƙaunar junansu me girma.
Ko motsi Khairy ta yi cikin bacci tana mutsu² jikinsa, se ya farka ya sumbaci goshinta ya shafo wuyanta, ya tambayeta.
"Babyn Ruhi menene uhm?"
Cikin baccin cike da shagwaɓa take basa amsa.
"Babu komi Ruhina."
Haka daren ya kasance musu cikin bacci me daɗin gaske da nutsuwa, suna manne kowane ya ƙanƙame ɗan uwansa, cikin kulawa.

Asuba tagari Ruhin Ruhi.🤣


😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_


*YI WA KAI!*

10/1/2023

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*105*

Acan ɓangaren Bilkisu cikin hukuncin Allah, ta samu ta yi baccinta sosai sabida sauƙaƙawa kanta da tayi.
Bata bari tunanin Shattima da Khairy sun dameta ba, yanzu suna ina? Me suke? Sam taƙi bawa zuciyarta daman hakan, sbd duk lokacin da taji faɗuwar gaba ko ta tunasu zatayi saurin faɗin kalmar. (Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!).
Washegari cikin kuzari ta farka, tana sallar asubah ta sauka take ta haɗa musu breakfast, tana kammalawa ta koma tayi wanka Kasancewar weekend ne, ta koma ta tayi kwanciyarta, sai 10 pm ta farka ta sake wanka, lokacin su Maryam suna can ƙasa zaune suna kallonsu.

A ɓangaren Ammi ba ƙaramin tashin hankali taji ta shiga ba, tunda Abba Aminu ya mata zancan zeje wurin fira, duk da bai jima ba ya dawo, fitarsu da Maryam amman haka ta dinga jin damuwa, har wajan kwanciya rikici sosai ta dinga masa tace se ya faɗa mata gaskiya, yana son yin aure ne?
A'a ya ce mata dan ta barsa ya yi bacci, bai shirya rikicin ba...

Can Abuja Ruhin Ruhi, bayan sallar asubah bacci suka koma, maƙale da juna.

Ƙarfe tara Auntie Aisha ta aiko Ilham da manyan kuloli da ƙaton flaks ɗin tea.
Su Nadiya suna cikin ɗakinsu sukaji ana danna Doorbell, Suhailat taje ta buɗe.
Gaisawa sukayi Ilham tace.
"Auntie Suhailat, Auntie Khairy fa?"
Suhailat tace.
Bata tashi ba, da ta tashi da ta sakko."
"Ok kamamun kayan mu shiga."
Ta kama mata kayan suka shiga.
Akan tsararren ƙaton dining room ɗin suka jera komai.
Ilham tace.
"Mummy tace kar na zauna na koma, Ina Nadiya? Ku zubi abincinku kuci, inji Mummy, tace idan Auntie Khairy bata tashi ba karku jirata."
Suhailat tace.
"Ai daman yaushe zamu jirata."
Nadiya ta fito tana dariya tace.
"Ke dai faɗi gaskiya yunwa kikeji."
"Ai sosai ma wlh, muje Nadiya mu lodawa cikinmu abinci tazo mu fice dan yau komin dare Jigawa zan kwana."
Ilham tace.
"Na tafi direba na jirana kwa gaishe da Auntie Khairy bye."

Suhailat da ta nufi hanyar dining room ɗin tace.
"Ok bye ki gaishe da Mummy, Nadiya muje mu take cikin mu."
Nadiya ta yi dariya tabi bayanta, tana faɗin.
"Su Auntie Khairy anata bacci, koda yaushe ta hkr da rigima Mamy ?"
Suhailat tace.
"Hahaha rigima Mamy zatayi tana wajan mijinta, shiru muje ke take cikinki."
Dariya sukayi suka tafi dan ciki tumbinsu....

Jigawa
Salim tsakaninsa da Allah ya ayanzu ko sigari baya sha, haka kawai nadama tazo masa, ya dage yanata azumin da Umma ta saka shi ya yi, wanda ayanzu ya cinye kwana arba'in yana yi, ya yin da.
Aliyah cikinta ya shiga watan haihuwa Father da Umma sun tanadi mata komai, lokaci ake jira.
Aliyah kusa bata shiga sabgar Salim tunda Umma ta mata kashedin karta shiga sabgarsa hakan ze saka ta samu daraja da kima idanunsa, ai kuwa yanzu neman magana yake da ita taƙi.

Hashim zaune a falonsa ya yi tagumi, umma Sa'idah ta iskoshi, ta zauna kusansa, ta janye hannunsa daga tagumin, tace.
"Wai lafiya? Duk kabi ka ɗorawa kanka damuwa? Tuba ɗaya ne idan har kasa azucikarka, ka tuban Allah gafurul rahim ne, don Allah ka rage damuwa."
Hisham yace.
"Wlh na tuba ba malamin da nake zuwa wajanza ayanzun, kawai yanayin wajan aikina ne, matsaloli sun min yawa, anba wani matsayina, nida nakeson nayi sama nayi ƙasa, ga Shattima kiran duniya na masa dan na basa haƙuri wlh baya ɗaukan kirana, ya fita daga sabgata baki ɗaya, Ni kuma wlh yanzu amincinmu nakeso ya dawo..."
Sa'idah, ta riƙe haɓa tace.
"Kaji ƙarfin hali ɓarawo da sallama, kaga don ALLAH ka kama kanka, munyi musu abinda mawuyaci ne su sake karɓar mu nima na gwada da Bilkisu nagani, amma ita tana ɗaukan kirana, ka de yanzu mu tsaya matsayinmu, idan sun yafe mana ma mun gode, Allah ya ƙara shiryamana zukatanmu, munyi babban kuskure wajan fara bin malamai har muka yadda da canfi, ga abubuwan da suka faru marasa daɗi damu, yanzu da bai aureta asara nawa mukayi? Ƙarshe ga shi an saukeka amatsayinka an ɗora wani."
Hisham bai sake magana ba, ya kishingiɗe zuciyarsa cinkushe da damuwa, kwantar masa da hankali ta shiga yi har tasamu ya tashi yaci abinci.

11 AM, Khairy ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta tana mimmiƙewa, saman ƙirjin Shattima.
Kallonta yake cike da zallar ƙaunarta, yana sakin murmushi, yafi 10 minutes da tashi, dan kar ya tasheta ne yaƙi motsawa, yana ƙare mata kallo.

Idanunta ta sauke akan kyakkyawar fuskarshi.
Gira ya ɗaga mata, yana shafa kanta ya sumbaci idanunta, anutse ya furta.
"Good morning my Babyn Ruhinta, ya kk tashi? Oya wanka muje kiyi abinci."

Fuskarta ta kifa ƙasan wuyansa ahankali tace.
"Dadynah ai na gaisheka da asubah toh ina kwana?"
Ta faɗa cikin wata irin kalar shagwaɓa.
Murmushi ya yi yana yawo da hannunsa bayanta, ya furzar da iskar bakinsa, ya mirginata ta koma ƙasa, ya mata rumfa, yana ɗago kanta, yana kallon kyakkyawar fuskarta, wani fitinannan kallo yake mata, me tsuma zuci yana murmushi.
Fuska ta kwaɓe tana rufe idanunta, ashagwaɓe tace.
"Ruhina!"

Laɓɓanta ya kamo ya tsotsa kaɗan ya saki, yana amsawa.
"Na'am Babyn Ruhinta, ya akayi?"
Ya ƙarashe mgnan, yana janye jikinsa ya sauka daga kan bed ɗin, yana murmushi yace.
"Wanka Baby."
Kafaɗa ta maƙale tace.
"Uhmm-uhmm!"
Kusanta ya matso yana kamo kafaɗunta, yana wasa da jelar kitsonta, ya duƙo da kansa ya sumbaci kitson, ya kamo hannunta ya sumbata, ya tsugunna ya shafi tafin ƙafafuwan nata, ya sumbacesu, yana mata wani irin kallo, tare da mata tafiyar tsotsa cikin tafin ƙafafunta, yana shafawa.
Anutse

Please Login or Register in order to submit comment