Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akusanta.
Washegari jama'ar duniya ta tashi da azumin watan Ramadan, cikin harda ummulkhairi, ta kira Mamy sunsha fira ta kira Baffa Liman da
Inno da su Anne har can Katsina ta kira, Shattima kawai taƙi kiransa wai ta masa fushi.😂
Da dare bayan shan ruwa kafin ya koma masallaci ya kirata, lokacin tana can ƙasa falo suna ɗan lashe-lashemsu da Nadiya, tana faɗawa Nadiya yau azumin baiyi wuya ba."
Nadiya tayi dariya tace.
"Auntie ya zakiji wuya muna kwance sai ɗan aikin da muka kamama Umma saboda Allah muna cikin sanyi."
Khairy zatayi magana kiran Shattima ya shigo wayanta.
Miƙewa tai tsam ta ɗauki wayan ta nufi Stairs.
Ashagwaɓe ta Masa sallama.
Daga can Shattima ya amsa yana murmushi yace.
"My baby fushi kuma?"
Ɗan ƙaramin kuka ta sakar masa ma shagwaɓa tace.
"Yo Dady ba kai bane ba?"
Anutse cike da ƙaunarta yace.
"Nayi me Babyna?"
"Tun jiya kaƙi kirana mana."
Ɗan murmushi ya yi yace.
"Rigima Babu koh? Ykk ya azumin kinyi?"
Ƴar dariya ta yi tana saita muryata tace.
"Ni Sweet Dadynah sai ka sakani ma na fasa yima shagwaɓar, kamar Ni idan bana azumi watan Ramadan ai zaka dakeni. Dady love ina Mamy da ƙanina ko ƙanwata?"
Anutse yace.
"Duk muna lafiya Baby Ina Nadiya da Usman?"
"Ai yau da safe ya tafi Kaduna, Nadiya gata can, toh Dadynah muyi video call please."
Numfasawa ya yi yace.
"An gama baby bari na kira kafin na wuce masallaci."
Ya faɗa yana katse kiran ya kirata video call.
Cikin murna ta ɗaga tana kallon screen ɗin wayan.
Idanu suka zubawa junansu.
Murmushi ya saki yana ɗaga mata gira.
Ashagwaɓe tace.
"I love You so much my Dady love."
Anutse cikin siririya murya yace.
"Me too my baby girl, fad'a min yau kinji ƙishi sosai?"
Khairy ta yi dariya tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta shiga zayyano masa yadda azumin yau ya kasance yana murmushi yana kallonta....

Toh fah haka abun ya kasance sannu-sannu akwana atashi anata ibada azumi ya yi nisa yau har ashirin ba biyu.
Shattima ya biyama daga cikin dangin babansa mutum uku, dangin Lima mutum biyu na Inno mutum biyu sai wani maƙwabcimsu liman mutumin kirki, insha Allahu gobe Jirginsu yake tashi zuwa ƙasa me tsarki domin Umarah da samun sallatar daren goma na ta ƙarshe me albarka.
Khairy batada labarin duk abinda ake sabida sunsan rigima zatayi, sai anje da ita dan rabon da su tafi Makka da ita tun tanada shekaru 18.
Amman Mamy ta matsa yau sai sunje sun dubota da mata sallama koda bazasu fada mata ba, su ganta dai satinkusan Uku basa tare.', da ita sosai suke kewarta.

Maryam dai Alhamdulillah za'ace a fuska ta ɓoye damuwarta amma daidai da rana daya son Shattima yaƙi raguwa a cikin zuciyarta, iyayanta sosai suke mata addu'a, cikin wannan wata mai tsarki haka ita kanta tana addu'a.
Ɓangaren Karima babu wani abunda ya canza sai ma rikicewa da ta yi, ƙaiƙayi ya ƙaru tare wasu irin ƙuraje masu wari, ga YANKAN WUƘA bai fasa saka aljaninsa na satota ahakan yana alfasha da ita ba sabida ciwon da yake jikin Karima Wanda shine Ya goga mata toh nasa ma ya fara bayyana shiyasa ya matso kwanakin da ya basu na magani su ciki ayita ta ƙare...

Khairy yau bata azumi, tun asuba bayan sahur azuminta ya karye, marata na mata ciwo haka cikinta kaɗan² tasha maganinta wanda yake lafawa hakan ya sakata kasala take damunta tea kawai ta Sha ta koma baccin wuya dan sosai wannan karon takejin ciwon marar, daɗin abun ma da zaran tayi kwana ɗaya tana ciwon yana bari har ta gama bata sakewa.
Misalin ƙarfe 11 na safe su Shattima suka shigo Gumel.
Dad Mustapah da kansa ya tarbosu.

Mamy sanye take da shadda Ash colour anko sukayi ita da Shattima, sunyi wani irin fitinannan kyau, ƙamshinsu mai sanyi da nutsuwa yake tashi ajikinsu.
Anutse Shattima ya fito daga motar, yana kamo hannun Mamy ta fito anutse.
Dad Mustapah yana washe bakinsa ya musu jagora har falonsu wanda yake fitar da lafiyayyan ƙamshi ga sanyin Ac.
Khairy tana kwance akan 3 seater, tana ɗan lumlumshe idanunta, tana yamutsa fuska. Sanye take da rigar atamfa doguwa kanta ba ɗankwali ta tufƙe gashinta wanda tunda tazo batayi kitso ba, tun ɗazu take famar turo baki, tana turmusa Zainabu da ta gaji ta mata wayo ta canza wajan zama.

Zainabu ta kalleta tana murmushi aranta tace.
"Za'ayi wa yarinya surprise.
Kamar a mafarki taji sallamar Dady Shattima da Mamy, sai Dad ɗin ta.
Da sauri ta buɗe idanunta tana waigowa idanunta suka sauka akan Shattima da Mamy, tai wani irin narkar da fuska kamar zata fashe da kuka.
Da wani irin sauri ta wuntso tana mai tsannainn farin cikin ganinsu, har ƙwallar kewarsu tana dafe cikinta ta nufi wajansu da ɗan gudunta tana faɗin.
"Oyoyo Mamynah Oyoyo Dadynah."
Real Ladingo Omu Farisah

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 24/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*95*


Idanunsa ya ɗan runtse na second 4, ya buɗesu a kanta yana kiran sunan ALLAH, tsoronsa ɗaya karta afka masa.
Ɓoyayyar zuciya ya sauke lokacin da yaga.
Khairy tana isowa ta rungume Mamy cike da farin ciki, tana faɗin.
"Welcome back my Mamy, ya gajiya? Ina ƙanne na?"
Mamy cikin farin ciki ta sumbaci gefen kumatunta, tace.
"Duk muna lafiya Baby, ya azumin? Me yake damunki naga fuskarki ta faɗa?"
Shagwaɓewa ta yi tana laɓewa jikin Mamy ta saci kallon Shattima, suka haɗa idanu lokacin da yake amsa gaisuwar Nadiya, Idanunsa masu tasiri akanta, ya ɗan zaro mata yana girgiza mata kai, ya janye idanunsa daga kanta.

Lumshe idanunta tai tana buɗe ta e.
Mamy tun safe kwance nake banajin daɗi, amman yanzu da sauƙi, Mamy zauna ki huta."
Ta faɗa tana janye jikinta, tana kamo hannun Mamy.
Shattima zaune suna gaisawa da Zainabu ta bebenci.
Khairy tana zaune kusan Mamy tace.
"Dady ina kwana? Ya ibada?"

Bai yarda ya kalleta ba anutse yace.
"Lfy lau Alhamdulillah daughter, fatan kina lfy?"
Khairy tana riƙe da hannun Mamy tana murmushi tace.
"Alhamdulillah! Dady."
Ta kalli Mamy tace.
"Mamy! ga shi azumi ne bare na kawo maki ruwa ko lemo, ko abinci, Mamy muje ɗakina ki huta ai zaku kwana koh?'
Mamy ta yi murmushi tana faɗin.
"Tambayi Dadynki muji me zai faɗa."
Khairy ta langwaɓar da kanta tana kallon Shattima, tace.
"Dadynah zaku kwana dan ALLAH?"
Akaikaice ya kalleta yana sake kame kansa cike da nutsuwa da bata kulawa yace.
"A'a anjima idan anyi sallah azuhur zamu wuce."
Mamy ta kalla tana rau-rau da idanunta tace.
"Kai dan ALLAH yanzu bazaku kwana ba?"
Dad Mustapah yace.
"Khairy kuje mana ki kaita ta samu ta huta kafin su tashi tafiya."
Kai ta jinjina tana kama hannun Mamy, ta miƙe suka nufi Stairs tana kallon Shattima wanda koda wasa bai kalleta ba.
Suna shiga Mamy ta kwanta saman lafiyayyan bed ɗin Khairy tana faɗin.
"Baby zo zauna muyi magana bana son rigimar kin nan."
Khairy cikin farin ciki, ta haye bed ɗin tana zaune tana matsawa Mamy ƙafafunta sai kace wata mai tsowon ciki
.
"Yawwa Baby gobe Jirginmu zai tashi zuwa ƙasa mai tsarki, zamuje muyi godiya ga Allah subhanahu wata'ala, da ya bamu wannan kyautar, zamu masa bauta ta tsawon kwana goma ta ƙarshen da kowane musulmin ƙwarai yake burin samun rabauta da kusanci ga ALLAH, dan ALLAH baby ɗaga gobe ki haƙura da bacci ki daure ki raye dararen nan domin neman samun kusanci ga Ubangiji."
Khairy sai taji wani Mamy ta bata tausayin da bata san kalarsa ba, da taso mata kukan rikicin Amman sai ta fasa, ta rungumeta tana faɗin.
"Ina sha Allah Mamy bazanyi bacci, ai daman inayi sosai ba sai Ramadan ba, zan dage nayita muku addu'a keda Dady ina sha Allah, Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya."
Cikin farin cikin Mamy tace.
"Ameen ya ALLAH Baby ALLAH ya miki albarka."
"Ameen Mamynah."
Mamy ta gyara kwanciyarta tace.
"Baby jamin Duvet nayi bacci kafin mu wuce, idanuna zafi suke min sosai."
Khairy cike da tausayinta ta rufeta tana kwanci kusanta.

Sosai Shattima da Dad Mustapha suke hira kamar sunyi sabo da juna shekaru dayawa.
Nadiya ta miƙe ta haye wajansu Khairy, Zainabu ma ta basu waje ta tafi can wajansu Mamy ta isko Mamy na bacci Khairy na jikinta tana matse idanu, riƙe da cikinta.
Kamota tai tana mata nuna suje tasha tea.
Saukowa tai daga kan bed ɗin suka fito.
Khairy suna saukowa taga falon ba kowa, ta shiga dube-dube.
Kamar zatayi kuka tace.
"Umma! Toh ina Dadynah?"
Nuni ta mata yana falon Dad ɗinta.
Kai ta jinjina.
Zainabu ta dafo mata tea ɗin me kauri ya ji madara ta matsa mata tasha, sosai da biscuits.
Tana idarwa ta koma wajan Mamy tana bacci.
Wayanta ta ɗauka ta kira Shattima.
Bugu biyu ya ɗaga matsawa tai dan karta tashi Mamy.
"Dadynah yanzu bazan gaisa da kai ba wlh banida ma lafiya fa!"

Anutse ya furta.
"Baby ni dai gaisuwar ki na yafe yau da rana tsaka nan, me yake damunki yanzu bakida lafiya?"

Ɗan ƙaramin kuka ta sakar masa harda shasheƙa tace.
"Eh wlh ko azumi banyi ba."
Cike da kulawa yace.
"Subahanallahi Baby Ok fito muje asibiti adubamin ke, ina Mamynki?"
Ashagwaɓe tace.
"Tayi bacci Ni bazan tasheta ba."
Cikin kulawa muryasa mai taushi da daɗi, anutse ya furta.

"Ok zo mugani ki sameni Ah mota."

Cikin farin ciki ta ɗauki mayafi kalar atamfarta ta yafa, sai kuma ta cire ta ɗauki hijab mai kyau ya wuce guiwarta kaɗan, ta saka ta fice.
Falon Nadiya na zaune tana waya da Usman, Khairy ta wuce ta nufi ƙofar falon.
Shattima na zaune cikin narkekiyar motarsa baƙa wulik, ya hangota tana tafe kamar wata tarwaɗa.

Sosai ya yi kicin² da fuska sanin halinta Tsaf zata haye kansa, da azuminsa ta jiƙa masa aiki.
Anutse ta buɗe ƙofar ta shigo da sallama tana rufewa ta kalleshi kamar zata fashe da kuka, tayi wani kalar tausayi.
Anutse ya kalleta yana faɗin.

"Baby me ya sameki?"

Kanta ta kwantar kafaɗarsa dan bazata iya faɗin gaskiya ba, ta kamo hannunsa tana faɗin.
"Sweet Dadynah ashe gobe zaku tafi umarah? Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah yasa ibadar da zakuyi karɓaɓɓiya ce wajan Ubangiji, Allah ya sauke Mamynah lafiya, yasa ta haifomin Twins."
Ta faɗa tana kifa kanta tafukan hannun Shattima.
"Dady Shattima nayi kewarka da yawa ALLAH." Tace tana kokarin shige masa.

"Ahhhhh Baby tsaya kin manta azumi nake kika cakumeni haka? Ko kinaso azumin Dadynki ya zama rabi ne?"
Khairy tai saurin sakinsa tana matsawa wajan zamanta tace.
"Don Allah kayi haƙuri Dadynah missing ɗinka ke damuna."
Murmushi mai kyau ya sakar mata yana kamo hannayenta duka biyu yana kallonta anutse cikin bata dukkan kulawarsa yace.
"No karki damu, Babyn Dady Shattima yanzu dai faɗa min ina yake miki ciwon?"
Rau-rau tai da idanunta, tace.
"Ni daman lafiyata lau wayo na maka dan na ganka ne."
"WoW! Toh Allah miki albarka Baby, fad'a min azuminki nawa?"
Ƴar dariya tai tana riƙe hannunsa da yake riƙe da nata, tana wasa zobunan hannunsa tace.
"Dadynah irin na kowa tunda ba yafe min za'ayi ba, idan na ajiye."
Goshinta ya sumbata da hannunta ya lakaci hancinta yace.
"Allah miki albarka sannan ki dage ki raye daren goma ta ƙarshen nan Baby kinji?"
Kai ta jinjina tace.
"In Sha Allah Dadynah, Dady bari na koma wajan Mamy kar ta farka."
Ta faɗa tana zare hannunta cikin masa ta kai masa sumba kumatunsa tana kallonsa ashagwaɓe tace.
"Sweet Dadynah na faɗa sau ɗaya don ALLAH kaji?"
Murmushi akan fuskarshi anutse can ƙasa ya matso da fuskarsa dab da Tata ya furta.

"I love U my baby."

Dariya tai tana lumshe idanunta tace.
"I love You too sweet Dady love."
Ta faɗa tana shafo sajansa ta buɗe motar ta fice da ɗan gudunta."

Ɗan murmushi ya saki yana sauke numfashi tare da furzar da iskar bakinsa, ya ɗauki wayansa da take famar ringing.

Khairy ranta fess ta koma wajan Mamynta ta kwanta tana jiran tashinta.

Sai bayan sallar La'asar suka su Mamy suka bar gumel sabida azabar jirin da Mamy ta farka da shi daga bacci.
Khairy kamar wata ƴar baby ta riƙe Mamy tana kuka da zasu tafi, da ƙyar Dad Mustapah ya kamota suka koma ciki Zainabu dariya take dan lamarin Khairy yanzu yafi gaban bata mamaki, saboda ganin Mamyn ma tana zubar da hawaye,sai da Shattima ya sakata mota da kansa.
Har sukayi nisa hawaye take famar masa, ya rungumota jikinsa sosai yana lallashinta.
"Haba! Sweetheart yanzu halin Khairy ne baki saniba? Tana hakane fa dan mutaho da ita, da azuminki ki tsaya kina koke-koke, kina ɓatawa my babies ɗina rai, suma suyita kukan."
Ya faɗa yana sumbatar goshinta tare goge mata hawayen.
"Mi Amor itama ba tana azumin ba take famar kukan, wlh taban tausayi kasan dai Khairy bata jure rashin mu."
Cikinta wanda yake ashafe kamar ba ƙwayar halitta aciki ya shafa yana faɗin.
"Oya yi baccinki ki more kafin Mu isa kinga zakije can gida wajansu Anne ya kamata ki huta yanzun. Ita Baby tace miki tana azumi? Yau ɗin bayan na kamata ɗazu a falo tana cin cake."
Baki ta turo masa gaba tana ɓata ranta.
Murmushi kawai ya saki baice komai ba...

Suna isa Jigawa sai da Mamy ta shiryawa Shattima kayan shan ruwa, Tsaf kamar yadda ta saba, bayan sunsha ruwa sunyi sallah suka tafi gidan Liman daga can suka wuce gidansu Mamy.
A ƙarshe suka yada zango a gidan Abba Aminu.
Maryam tana gaishe da Shattima da Mamy ta Gudu ta killace kanta, sabida akoda yaushe idan ta gansa sonsa yake ƙara hauhawa.

Washegari Jirginsu Shattima ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki, sai muce ayi ibada lafiya.

Ɓangaren Alhaji Hashim mahaifin Salim abubuwa sun fara cakule masa, ta kowane ɓangaren, kadarorinsa sunja baya, haka yanzu wajan aiki yana fuskantar babbar matsala.
Zaune yake ya yi tagumi yana tuna rayuwarsa ta farko kafin ya koyi shiga yawon bin malamai, lokacin da suke tare da Shattima, wanda akullun yake ɗorasa akan turbar gaskiya,.duk.da ya girme masa suke abunta Amman ya fisa hangen nesa.
Umma Sa'idah ce ta iso tana zama kusansa tace.
"Wai kana lafiya kuwa tun shekaran jiya nake ganinka cikin damuwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ɓoye mata gaskiyar yace.
"Kawai ina mamakin mutum irin Minister Abdullahi samunsa zaiyi wuya, ki duba yarinyar ashe tsintarta sukayi duk yadda muke da shi ba wanda ya taɓa, amman ji da karshe matarsa ta aura masa ita duk kuwa yanajin ana raɗe-raɗin yarinyar nada farar ƙafa, amma ji cikin ikon ALLAH arziƙinsa bai rageba sai ma abinda yake bunƙasa ga aikinsa ga business ɗinsa, kinga kuwa yadda Company sa na Abuja yake bunƙasa?"
Umma tace.
"Kaga kabi asannu kar azuminki ya gurgunce, ai wlh Ni dai tun lokacin da naji wannan labarin jikina ya yi sanyi ga shi mun ɓata goma biyar bata gyaruba, ni dai wallahi na fasa wannan canfe-canfen banga amfaninsa ba, yiwa Allah shishigi cikin lamarinsa, yanzu shi me ya samesa da yake aure da ita? Ko Salim ma na zauna nayi tunani dukkan ƙaddarorin da suka samesa daga Allah ne, da bamu tozarta su Bama tunda ba rabon aure atsakaninsu wlh bazai aurenta ba, haka shi kansa Abdoul Allah ya jiƙansa koda bai aureta ba zai mutu, wlh Ni nagane gaskiya bazan sake yarda da canfi ba, banga inda mukajeba sai raguwa ga shi abanza zumumcimmu ya ɓaci dasu sun fita daga rayuwarmu, bayan mune muke anfana dasu..."

Cikin tsawar borin kunya yace.
"Tashi kiban waje munafukar banza kina nufin nine Banda gaskiya cikin lamarin? Saboda komai ya cansa kike kikeson goyen bayansu koh? Ai laifinki ne, lokacin da na fara bibiyar malaman da kin zaunar dani kin nunamin illar hakan zanyi ne? Amman kema lokacin idanunki sun rufe sai yanzu zaki wani zo kina nuna min ALLAH ɗaya ne."
Da kallon mamaki ta bisa batace komai ba ta fice ta basa waje sabida kar su raba hali Aliyah zata jiyosu.

Tana shigowa falon ta isko Salim ya matse Aliyah saman kujera yana matse mata nanna, yana ƙoƙarin kai hannunsa bujenta.😂
Duka ta kaimasa tana turesa tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Cikin watan Ramadan wata mai tsarki wannan yaron anyi ɗan iska wlh tallahi."
Idanunsa ya zaro yana faɗin.
"Toh abani matata mana tunda nace na tuba, ai wlh ina azumi bansa komai araina ba, kawai dan na razanata ne..."

Mari ta daukesa da shi tana fad'in.
"Ni ba Sa'idah da bace wannan special Sa'idah ce dan ubanka anƙi abaka matar taka sai lokacin da ka amsheta matsayin matar da amsar abinda zata haifa matsayin ɗa, wuce bani waje tun ban sauke haushina akanka ba tantiri kawai."

Salim cikin ɓacin rai ya nuna Aliyah da yatsa yace.
"Zamu gauraya sai na sauke miki ɓacin ran da aka dinga sakani akanki."
Aliyah tana kuka ta riƙe umma.
"Ai kinji matslarki kin bari ya rainaki dayawa ta haka kina kukan zaki ƙwaci ƴancinki?"
Aliyah cikin kuka tace.
"Umma bana son tashin hankali ne."
Hannunta Umma ta kama suka nufi ɗakinta tace.
"Kwanta ki huta sai da nace karki ɗauki azumin nan kika ce zaki iya..."

Ɓangaren Shattima da Mamy da jama'ar da suka tafi ƙasa mai tsarki, tunda sukaje sun maida hankalinsu wajan bautawa ALLAH.
Mamy da Shattima sun maida soyayya gefe sun jingineta sai sun dawo gida dan ko waje ɗaya basa kwanciya tunda sukeje kowa neman kusanci yake ga Allah subhanahu wata'ala.
Kowane dare basa bacci sai bayan sunyi sallar asubah suke kwanciya...

Can wajan Khairy tunda ta yi wankan ta maida hankalinta wajan bautar Ubangijin ta, ba wasa, sau biyu kawai ta samu hira da Shattima da Mamy sabida su wayoyinsu ma basa gabansu yanzu keɓewa da ALLAH suke buƙata ayanzun.

Usman da Nadiya haka suka kasance suma cikin masu raya daren suna nema wa kansu alkhairi wajan mahaliccin su, tare da nema wa mahaifiyarsu lafiya da shiriya idan tanada rabon hakan.

Haka ɓangaren Maryam da iyayenta suka kasance, Maryam tana roƙon ALLAH ya cire mata son Shattima ta dinga masa kallon mahaifinta.
Toh sai muce Allah ya amsawa wannan bayi nasa dukkan addu'o'in su na alkhairi,.har yanzu dai Maryam son Shattima daram a zuciyarta, amman muna miki fatan canji na alkhairi.

Kwance tashi ba wuya, yau har ankai azumi 29, ba wanda ya ji ance anga wata, dan haka yauma jama'a duniya musulmi, sun sallaci daren.
Washegari aka tashi da azumi.

Misalin 8 na dare aka fara shelar anga wata, nan jama'a dayawa suka fara kuka na bankwana da watan ni'ima watan daraja watan falala watan ƙara kusancin da Ubangiji.
Acikin masu kuka harda Shattima da Mamy.

Nigeria ma anata shirye² gobe sallah.
Khairy ansha kitso da ƙunshi ita da Nadiya.
Jamilah da Rayhana Dad Mustapah ya tura aka ɗaukosu, suyi sallah a gumel Abbu ya hana Khabir yacematan sun tafi.
Sosai Zainabu taji daɗin hakan.
Washegari Musulmin Duniya suka tashi da sallah, anyi dafe² anci ansha bayan an fito daga sallar idi.
Haka can Mamy anyi sallah ƙasa me tsarki, sunyi waya da kowa na gida ansha hira sunyiwa juna barka da sallah da neman gafara juna da zaman tare.

Da rana suka shirya su Dukansu suka tafiya yawan ziyara inda basuje ba.
Washegari kuma suka shiga siyayya tsaraba.
Khairy sai tunawa Mamy take tsabar abaya masu zafi take so.
Ai kuwa ta siya mata kala biyar masu shegen kyau da kayan bacci da wani Takalmi da ya burgeta zaima Khairy kyau.

Bayan sallah da kwana uku su Mamy Jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria.

Khairy yau cikin farin ciki take, tun safe ta gama shirinta na tafiya jigawa, dan tace ita zataje ta tarbosu a airport.
Su Zainabu sai gobe zasu zonsannu da zuwa, lokacin sun huta Nadiya kuwa tace zatabi Khairy, su Jamilah Zainabu ta hanasu subi ace Khairy tace goben zasuje tare.
Ƙarfe 10 na safe Khairy har Nazir direba ya kawosu Jigawa.
Ko ina Tsaf ta isko su Laraba sun gyara gida ko ina na ƙamshi.
Suna hawa upstairs, bayan ta buɗi ɗakinta sun shiga mayafinta kaɗai ta cire, ta ɗaukin makullin ɓangaren Mamy da n'a Dadynta, tunda duk tana makullansu.
Ita da Nadiya cikin awa ɗaya suka gyara ma Mamy komai Tsaf suka saka turaren wuta Khairy ta wanke bathroom Tsaf ta fesa turaren toilet, ta rufe ƙofar, suka nufi ɓangaren Shattima.
Nadiya ta barma falon ita ta nufi Bedroom.
Dariya tai tana faɗawa saman ƙaton lafiyayyan bed ɗin Shattima tana ƙanƙame pillow tana murmushi tace.
"Dadynah ƙamshinka baya barin duk abinda kake anfani da shi."
Ta faɗa tana jan lafiyayyan wani ƙaton bargonsa mai taushi ta shige ciki tana sanya yatsarta ɗaya bakinta tana ɗan ciccizawa.
Miƙewa ta yi ta sauka ta shiga gyaran Bedroom ɗin cikin awa ɗaya ta gyara masa ƙatuwar bedroom ɗinsa, ta canza zanin gado wani mai shegen kyau ɗan Saudiya fari ƙal mai wani irin taushi, ta sanya rigunan pillows, ta feshe ko ina da turare ma bed ɗin da turare ta shiga bathroom ta wanke daman ko ina tass ta fesa turare, ta fito.
Falon ta isko Nadiya ta gama goge ko ina tass.
Khairy tace.
"WoW! Sannu My Nadi muje yanzu sai girki."
Nadiya tayi dariya tace.
"Kai Auntie baki gajiba? Toh muje."
Khairy ta fito da kyawawan matsagaitan idanunta masu haske tace.
"Tabb aikin Mamy da Dadynah bana gajiya ko zan kwana inaya, muje."
Nadiya ta yi dariya tana yaba son Auntie ta takewa su Mamy.

Kowa da kalar girkin da yafi so tsakanin Mamy da Shattima Khairy ta masa, itada Laraba da Nadiya suka shirya musu girki_girke me daɗi, kowa da kalar nasa da yafi so, ƙarfe biyu sun idar da komai sun jera akan ƙatun dining area.
Khairy ta yi wanka ta yi sallah ta tsantsara kwalliya, wani lafiyayyan lace ta saka mai taushi doguwar riga ta naɗa lafaya tai wani irin shegen fitinannan kyau na ban mamaki ta saka takalmi me tsini, tana wani irin sahihin ƙamshi.
Key ɗin motar ta wadda Shattima ya siya mata, ana gobe aurenta da Salim, bata taɓa shigarta ba.
Lawan ta kira ta faɗa masa ya cire rigar motarta ya goge yau zata shiga.
Ana sallar La'asar Khairy ta kama hannun Nadiya suka fita.
Ni kaina na haɗawa motar Khairy yawu ba dai kyau ba, fara tass wata dakekiyar Benz ce mai baƙin Glass.

Khairy ta yi bismillah ta shige motar tana sakin wani irin fitinannan murmushi, Addu'a ta yi tana kunnata tana nufi tafkeken ƙaton gate ɗin.

Suna fitowa kiran Liman ya shigo wayan Khairy.
Nadiya ta picking call ɗin ta manna wayan akunnenta anutse ta yi sallama tana faɗin.
"Baffa ina wuni?"
Liman ya amsa sallamar yana amsa gaisuwar yace.
"Ya Gumel ɗin?"
Khairy tace.
"Lah! Baffa nazo tun safe, girki na tsaya nama su Dady, yanzu gani hanya zanje tarbar su airport."
Liman yace.
"Masha Allah toh ya yi su Balaraba ma sun tafi inaga ita da su Fauziyya.
Sai kun dawo Khairiya."
Ya faɗa yana katse kiran.
Khairy cikin murna ta ƙara gudun tana fad'in.
"My Nadi ki dubo lambar Mamynah zakiga sweet Mamy ki kiramin ita."
Nadiya ta duba lambar ta kira switch of.
"Auntie arufe wayan."
Khairy tana murza stiyarin motar tace.
"Oh! My God! Ok kiramin Dadynah toh, shima Sweet Dady zaki gani."
Nadiya ta amsa da.
"Toh."
Ta la lalubo lambar ta danna masa kira.
Shima switch of.
Nadiya tace.
"Sorry Auntie switch of shima."
Khairy tai rau-rau da idanunta, tace.
"Ke kam Nadiya bakinki Nan baya faɗin alkhairi ne? Duk ba'a samun su."
Nadiya tace.
"Yi haƙuri yayata ya zanyi toh."
Baki ta turo gaba tana driving ɗinta.

Azizah da take biye da bayansu Khairy a mota ta ƙyalƙyale da dariya, tana kiran wata lamba. Ana ɗagawa tace.
"Kusha gabansu ga sunan ina biye da su, kuyi yadda na tsara muku yadda zamu kamata cikin sauƙi..."

Khairy tana cikin gudu kasancewar sun kusa shigowa airport, sai ta ɗan rage tana tuƙi ahankali, mace da namiji ta hango dab da bakin hanya yana zuba mata mari ya shaƙeta, tana neman ƙwatar kanta, ga tsohon ciki ajikinta.

Wani irin burki Khairy ta taka tana gangarawa daidai kusansu tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kuga azzalumi mace ɗa tsohon ciki kana dukanta."
Ta faɗa ranta a ɓace ta buɗe motar ta fice, Nadiya na mata magana bata saurareta ba....
Real Ladingo Omu Farisah

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 26/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*96*

Hannunta ta sanya tana gyara lafayar jikinta, ta iso wajansu tana beƙa hannu ta fizgo matar, tana riƙe da hannunta, ta ɗauke mutumin da mari, tana matsar da matar baya.
Cikin masifar da kana kallonta kasan arota ta yi, tace.
"Kai wane irin mahaukacine? Mata da ciki tsoho haka kake dukanta akan titi saboda rashin imani, da rashin sanin darajar mace koh?"

Cikin harzuƙa ya zaburo ya ɗaga hannunsa zai mari Khairy.
Ƙiran Azizah ya shigo cikin wayansa, sauke hannunsa ya yi yana ɗaga kiran.
"Kai Tasi'u! Kana haukane zaka mareta nan ka ɓata amna aiki? Ai kawai kayi haƙuri ka haɗiye haushinka idan mun ƙwamusota duk ma abinda kakeso kayi da ita, kayi mana ba matsala sabida na ƙona zuciyar Minister inaso kamata kaca kaca.
Ga Ni bayanku ina kallon komai, zan juya zuwa can, kawai ka cika aiki kamar gaske, yadda zata ƙara tausayinta ta ɗauke ta a motarta kaga zata ƙarasa aikin Ok? Sai kai kuma ka iskoni mota mubi bayansu."
Kai ya jinjina yace.
"An gama."
Ya katse kiran, yana kallon matar me cikin ƙarya yace.
"Wuce muje dan ubanki."

Khairy tace.
"Ka kusa kuskure mai girma arayuwarka, ai da ka mareni wallahi zakayi nadama marar anfani, tabbas."

Ta ƙarashe maganar tana kallon matar tace.
"Baiwar Allah me nanki ne wannan? Ki faɗa min gaskiya?"
Nadiya ta iso tana kamo hannun Khairy tace.
"Auntie don Allah

Please Login or Register in order to submit comment