Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min fad'a haka muka dawo Allah Dady daidai shigowarmu gidan na farka daga mafarkin sakammakon kiran sallar asuba.”
Shattima idanunsa masu matuqar haske da kwarjini ya firfito da su yana dafe goshinsa tare da lumshe idanunsa lokaci d'aya ya furta.
“Ya Allah! Baby bakiyi addu'a ba da zai kwata koh? Ba hanaki kwanciya ba addu'a ba?”
Khairy ta shagwab'e kamar zatayi kuka tace.
“Kai sweet Dady Allah nayi addu'a kawai tsabar kewarkune ni kawai kazo haka Mamy tace zatazo yau ga shi har 5 ta gota basu zo ba, daman nasan wayo tamun.”
Ta k'arashe mgnar tana fashe masa da kukan zallar shagwab'a har dira qafafunta take.

Shattima yay gyaran murya yana fad'in.
“Ni fa Baby bana son rigima, toh yanzu dai yi shiru kiji wani Abu ko wlh na kashe kiran sai ki huta naga wa zakima kukan fitinar...”

Baki ta turo gaba tana rage kukan zatayi magana
Sallamar Mamynta da Maryam ne ya dakatar da ita daga magana,ta Saki baki tana kallonsu zuciyarta cike da murna, har suka qaraso suka zauna ta kasa motsi tsabar murna.
Auntie Aisha tace.

“Toh Dadyn ne koh?”

Mamy ta kalli Khairy tana murmushi tace“Babyn Shattima ba'a murnar ganin Mamy? Sai fa na juya idan bakya murnan ganina kashe wayan kiji da Mamynki.”
Khairy ta saki ihun murna tana ajiye Qur'anin saman table ta nufi wajan Mamy aguje tana fad'a jikinta ta rungumeta gam, hannunta d'aya manne da wayan tana fad'in.
“Sweet Dady wlh ga Mamy zaune gabana wayyo dadi....”


*YI WA KAI*

Free Novel

_October23/10/2022/ 5:01pm_

*35&36*


“I miss you my sweet Mamy, Dady ga Mamy fa!”
Ta k'arashe mgnar tana zaro wayan daga kunnenta, ta mannawa Mamy a kunnenta, tana murmushi tare da sake mannewa jikinta.
Mamy tace.
“Hello Shattima ina wuni?”
Khairy ta waro matsagaitan fararen kyawawan idanunta waje, tana fad'in.
“Kai! Mamy! Dady karka amsa ni bari kama min sunan Dadynah sweet Dady kana jinta koh?"
Daga can Shattima bai san lokacin da wani irin k'asataccan murmushi ya sub'uce masa ba, yana shafa sumar kansa yace.
“Bana amsawa sweetheart, riqe kayanki, barka da zuwa fatan kun sauka lafiya?”
Mamy tana shafa bayan Khairy da tayi luf ajikinta sai kace mage.
Ta murmusa kad'an tace.
“Wlh lfy lau sai 'yar gajiya, ga Babynka ta hayemin jiki sai naniqata takeyi.”
'Yar dariya Shattima yay yana fad'in.
“Uhmm! Yanzu fa ta gama min kukan ba garai ba dalili wai naqi zuwa, sannan kince zaki je baki jeba, bani Auntie mu gaisa zan kiraki zuwa anjima idan kin huta.”
Mamy tace.
“Ok auntie ga minister. ”
Ta fad'a tana beqawa auntie Aisha wayan.
Amsa tayi tana fad'in.
“Oya Ilham ki kai Mamynku suyi wanka, Ke kuma Khairy maza d'auki Qur'aninki oya karatu, bana hanaki yawan surutu ba? Ina me takaba ina surutu?”
Ta qarashe mgnar tana Kai wayan kunnenta tare da sallama tabar wajan.
Shattima ya amsa sallamar yana fad'in.
“Godiya nake my auntie ai wlh baby sai ke ayanzun, Allah ya biyaki yabar zumunci, ya gida da yaran?”
Auntie Aisha tayi murnushi tana amsa masa ta haye stairs.
Suhal ya miqe yana kallon Khairy yace.
“Mamy! Ta d'agaki ke kam Khairy akwai son jiki yawa mage. Mamy ina kika samo wannan yarinyar ban santa ba?”
Mamy tayi murmushi tace.
“Tabb Suhal da son girma kamar zakafi Maryam kake gani koh? D'iyar Aminin dadynku Ce.”
Dariya yayi yana d'aukan system d'insa yay gaba.
Maryam kuwa ta tsirawa Khairy idanu cike da abubuwa iri-iri, wani b'angaran tausayin Khairyn take matuqa wani b'angaran kishinta, ji take kamar ta auri Shattiman.
Ilham ta miqe tana fad'in.
Mamy muje kuyi wanka.”
Khairy ta janye daga jikin Mamy, tana kallon Maryam zatayi mgna sai taga ita ta qurma idanu, ta hura mata iska tana fad'in.
“Sorry k'anwata Maryam Mamy ta d'auki hankalina barka da zuwa y hanya?”
Maryam tayi murmushin yaqe tace.
“Kai auntie Khairy ai nagani kam.”
Tafiya sukayi Ilham ta kaisu suyi wanka, Khairy kuwa ta koma ta zauna tana karatunta kafin su Mamyn su fito...


*Gumel*
10pm.
Alhaji Mustapah zaune cikin shirin bacci yana amsa waya, hajiya Karima itama cikin shirin baccin take saukowa daga upstairs, ta k'ura masa idanu.
Wannan rusheshan cikin nata ya samu guri sai sama da qasa yake, sai wata irin tafiya take ta taqama.
Kusansa ta zauna tayi kiskirin tana sauraronsa, taji akan businesses d'insa yake magana.
Usman ne ya sauko riqe da cup a hannunsa hannunsa d'aya yana amsa waya yana murmushi.
Sanye yake da jeans da T-shirt, yana wani irin fitinannan k'amshi.
“Godiya nake yallab'ai Allah ya qara girma da d'aukaka, hakan ma yayi sosai kadunar da anan gumel ma zanyi aikina, wlh nida naji shiru nazaci ka manta dani.”
Ya qarashe mgnar yana nufar kitchen.
Shattima da ga can yana zaune gefen bed cikin shirin bacci yana sanye da fararen kayan bacci masu taushi, ya shafi kansa yana fad'in.
“No! Usman! Bana mgna na canza, ko dutse da na canza maka naga kamar a kadunan zai fi shiyasa na tambaya anan, hope duk kuna lfy ya mahaifinka da mamarka da kishiyar mamarka?”
Usman wanda yake tsaye a kitchen yana bud'e flask d'in ruwan zafi, ya amsa da.
“Duk lafiyarsu lau yallab'ai ai auntie Zainab bata nan tin yaushe Dad ya saketa shekaru biyar na tab'a fad'ama ma inajin koh?”
Minister Shattima yace.
“Subahanallahi banji dad'i ba anan Gumel d'in?”
Usman yace.
“A'a tana garinsu katsina kullun sai nayi yinqurin zuwa ganinta sai nafasa Zan daure naje insha Allah.”
Shattima ya lumshe idanunsa yana sauke numfashi tare da hamdala aransa yace.
“Ok Allah baka iko, bari na barka bye.”

Alhaji Mustapah ya kalli Karima tana wani cika tana batsewa ya murmusa yana fad'in.
“D'anki dai a kitchen me ya faru kike wani cikada batsewa uwar gida?”
Baki ta tab'e tace.
“Kuma amarya ba, wlh akan tafiyarmu ne Dubai nanda sati d'aya kuma banda isashan kud'i.”
Zaiyi magana Usman ya shigo falon yana fad'in.
“Mom Dad! Albishirinku Kaduna zanyi aiki minister Abdallah Shattima yamun hanya...”
Hajiya Karima ta firfito da idanu tana fad'in.
“A ina ka sanshi har ya ma hanya Usman? Kai Masha Allah ashe zamu qara shigowa gari.”
Dad Mustapah yace.
“Alhmdllh naji dad'i Allah ya qara masa d'aukaka da bud'i.”
Usman ya amsa da.
“Amin ya ALLAH. ”
ya miqe ya basu waje.
Karima tace.
“Ni fa Alhaji kud'i nakeso na samu?”
“Insha Allah za'a duba muje ciki agajiye nake.”

Sosai Mamy da Auntie Aisha suka Sha fira bayan sunci sun Sha, Maryam dai kallonsu take yadda auntie take nan nan da Mamy da Khairy.
Ko wajan kwanciya Kahiry tana maqale da Mamy kamar zatasha nono, fafur ta hana Mamy babban motsi ta maqaleta.
Washegari ta Kama ladi bayan sallar azuhur su Mamy sukayi shirin tafiya Khairy tace gari da uban wa sai tabi Mamyn ta,sai da auntie Aisha ta mata Jan ido aka bata Shattima a waya ya lallab'ata cewar jibi zai dawo qasar bazaije jigawa ba sai yabiya nan Abujan ya taho da ita, tikun aka samu tabar Mamy suka tafi.

Kamar yadda liman yace zaiyi tsawon kwana uku yana istihara, toh Alhamdulillah yayi, sosai abun ya firgitashi, dan abu d'aya yake nunawa masa tsakain Khairy da Shattima akwai alkhairi tare da babban rabo akwai babban haske cikin al'amarin nasu, amman lamarin nason sirrine ba wai kai tsaye zai fallasa komai ba.
Hakan ya saka washegarin da ya gama istiharan ya yanke shawaran bazai fad'awa kowaba shi ya tsara yadda komai zai gudana wanda hakan zai fi.
Kiran Mamy yayi awaya ya fad'amata yadda ya tsara yace tayi shiru da bakinta ko a fuska karta kuskura tasake nunawa Shattima tana son ya auri Khairyn, bare ta tunkari Khairy da zancan Shattima, tabar komai hannunsa har lokacin hakan yayi.
Mamy taji dad'i sosai tama liman godiya da dogowar addu'a tayi kuma alkawalin bazata sake tayar da mgnar ba sai lokacin da shi ya tayar da mgnar.

Katsina Malali.
Bakinta d'auke da sallamar zuci irin tasu ta kurame ta shigo, tsakar gidan tana d'aga hannayenta alamar sallamar,sosai takejin zafi yau sbd irin ranan da akeyi, ga ciwon kai ga haushin Alhj Nura aranta, bata San me yasa indai zata fita ba sai an tayata.
Inna ADAMA da take zaune tana yanka salad ta d'ago ta kalleta ta amsa mata, tana fad'in.
“Zainabu! Sannu wai yau kin kwaso Rana.”
Murmushi tayi tana ajiye Jakarta akan tabarma tana zama kusan inna ADAMA.
Sosai yau Zainabu tayi kyau
Jamila ta fito cikin shiri tana gyara mayafinta.
“Umma! Sannu da rana kinzo da wuri yau, can wajan makarantarku ne zanje, har ina cewa na biya.”
Zainabu ta kalleta tana, murza goshinta ta nuna mata kanta alamar ciwo yake mata, ta tambayeta da hannu ina zataje?
Jamila ta rusuna tana dafa cinyar Zainabu tace.
“Ayyah! Umma sannu Allah ya baki lafiya, gidansu iqilimah 'yar ajinmu zanje yau fa bikinta, Abbu yace Karna wuce la'asar. Bari na kawo miki paracetamol kisha ummah.”
Ta fad'a tana miqewa ta koma d'aki.
Inna ADAMA tace.
“Toh kiyi sauri kije ki dawo kinga dai yau gidan shiru su Raihana ana gidan Marwan.”
Da kanta ta b'alla mata maganin ta kawo mata ruwa tasha tace.
“Umma! Je ki kwanta ki huta,natafi sai na dawo, inna Bye.“
Zainabu ta miqe tana mata bye ta d'auki Jakarta ta shiga d'aki ta zube saman katifa tana fashewa da wani irin kuka, mai tsuma zuciya.
Jamila da har ta cira qafa ta dawo ita da Inna ADAMA tserere wajan shiga d'akin.
Gabanta suka zube suna kamata tare da tambayarta, lafiya?
Kanta ta girgiza tana rage kukan tana masu kurmanci ba komai.
Innah ta d'ora kan Zainabu acinyarta tace.
“Haquri zakiyi koma meye watarana sai labari, ki yawaita innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Nasan bai wuce wani yau ya ganki yace yana sonki ba shine ya kawo kukan, toh dan Allah zaki zauna jiran wanda baki san ko zai dawo gareki ba? Shekara biyar tinda ya sakeki bai tab'a nemanki ba! Shin tsayama ana aure da saki ukune?”
Kai kawai Zainabu take girgizawa ta lushe kawawan idanunta tana sauke numfashi a kullun k'aunar Mustapah k'aruwa take acikin zuciyarta.
Jamilah tace“Au Umma kukan soyayya kikeyi? Wlh har kin tayarmin da hankali, Allah kawo wanda zai sanya umma farin ciki Amin, sai kinyi kamar kin manta abu sai abu ya dawo, innah sai na dawo.”
Inna Adamaw tace“Karki wuce lokacin da ya baki fa!”
Inna tana zaune kan Zainabu akan cinyarta har bacci ya saceta ta maida mata akan pillow ta miqe ta koma ta qarasa gayaran salad d'in da zasuci d shinkafa.

B'angaran gidansu Aliyah anata shirin biki, yau akayi kamu, ba laifi itama an shirya mata gidanta tsaf sun mata kaya na zamani.
Banda kuka rinda akayi kamu ba abinda Aliyah take,sam bata qaunar Salim,Allah ya had'ata da mahaifiya ta gari, sosai take nusar da ita akan tayi haquri ta amshi k'addarata komai yayi farko yanada k'arshe.

Salim zaune A falonsa ransa a matuqar b'ace, sigari kawai yake zuqa yana fesar da hayaqin.
Ya tsani wannan auren na Aliyah kawai shi yarinyar bata masa ba, duk da ya amshi budurcinta.
Hanyar da zai b'arasa da auren yake nema, sai dai yasan abune mai wahala.
Sheqewa yayi da dariya yana fad'in.
“Yanzu nasan yadda zanyi ta gudu da qafafunta, ci ba dare ba rana zan dinga rufar mata, dan ubanta sai tace bata aurena, na saketa na auri Khairynah.”
Ya fad'a yana miqewa ya shige bedroom d'insa.

Yau akayi wunin biki gidansu Aliyah anyi walima harda dinner wanda Hashim ya matsawa Salim harda marinsa kafin ya akaita abinda yakeso.
Da dare waja 8 aka kawo amarya gidanta bayan tasha doguwar nasiha wajan iyayanta.
Salim daga shi sai Abdulrazaq suka zo dan yace baya gayyatar kowane aboki,shima daga falon aakyi siyan baki ya korasa ya saka ya maida qawayenta yaje ya siyo kaza gudu ya rufe qofa, sabida jarabar da take cinsa dan yayi shaye shayen magugunansa.
11 pm tana zaune saman lafiyayyan gadonta kanta qasa tana famar kuka sabida duk an watse an barta.
Zama yayi kusanta yana janye mayafin yace.
“Amarsu bakya laifi ko kin kashe d'an masu gida, sai dai ni wlh ko kazata kika kashemin sai na d'auki mataki, muje kici kaza naci kaza duk da ragowace...”
Wani irin kuka ta fashe da shi tana kallonsa.
Tsoki yaja yana miqewa yace.
“Illar auren dole kenan, wlh 5 minutes na baki idan baki fito ba ina shigowa zaki ban haqqina.”
Yana fita Aliyah ta d'aga hannayenta tana kuka tana fad'in.
“Ya Allah! Idan laifi na maka mai muni ka jarabeni da auren irin wannan mijin ya Allah ina roqonka ka yafemin laifina, ya Allah ka cireni acikin wannan huqubar kabani mafita.”
Ta qarashe mgnar tana kuka ta miqe ta shiga bathroom ta kimtsa kanta ta fito ta iskeshi falon.
Ba abinda taci shi kuma bai matsa mata ba, tin afalo ya dinga ciremata kayan jikinta.
Wani uban ashar ya lailayo ya afka mata ganin bata sallah, ya tunkud'eta gefe tare da cewa.
“Dan ubanki kinsan bakya sallah kika yarda aka kawoki gidana? Kwana nawa kike? Yaushe kika Fara?”
Ya mata tambayar cikin tsawa.
Tana kuka tace.
“Yau sati nakeyi.”“Aikin banza kawai.”
Ya fad'a yana matsarta ta ko ina sbd abubuwan da yakeji, breast d'inta sunci ubansu yau tayi kuka har ta gaji.

★★★
Yau ta kama weekend satin su Mamy d'aya da suka dawo daga Abuja wajan Ummulkhairi. Maryam tin lokacin da taji labarin Khairy ta saka abun aranta dayawa, kishi yana damunta yanzu abun ya kaita har dasu ciwo, kwanata uku asibitin Mamy, kuma mamynce take dubata, hankalinta yayi mugun tashi sbd yadda taga jinin Maryam ya hau, ta mata tambayar duniya ta fad'a mata me yake damunta taqi, ita kuma ta kasa fad'awa Ammi da commissioner, shiyasa ta buqaci Maryam ta zauna ita har ta warware tace maleria Ce ke damunta.

Yau kuma Shattima yake dawowa Nigeria duk da yace mata Lagos zasu tsaya sai dare zasu shigo.
Tin safe Mamy take famar shirye-shiryen tarbar mijinta, Maryam ta Kama mata sbd ta murmurs ba laifi yanzu burinta Shattima ya iso tayi tozali da shi ko taji abunda ya tokare mata azuciya ya saketa.
Zaune Mamy take saman sofa falon yana ta b'arin k'amshi ga sanyin A.c taci ubansu kwaliya, da d'anyar shaddah golden colour, doguwar riga tasha qananun kitso farin hannunta da farar qafarta sunci Jan lalle tayi wani irin kyau, waya take latsawa tana sakin k'ayataccan murmushi, ta fara tura masa saqo kamar haka.

```“Hello Mi Amor! Kana ina? Nafa ganka online ba dai ka shigo Lagos ba? Wayyo I miss you Ashe bazan ganka ba yau nasan sai gobe.”😿```

Kusan 10 minutes kafin ya bud'e.
Emoji na dariya ya turo mata, tare da rubuto mata.

```“Sweetheart! Ki bari kawai ba a Lagos suka diremu ba Abuja nan da 20 minutes zamu shiga meeting, zuwaira 9 na dare jirginmu zai taso, me kika tanadar min? I love you sai nazo zan amsa waya.”```

Mamy tana bud'e saqon ta danna masa Kira.
Bugu d'aya ya d'aga yana fad'in.
“My Billy! Ki jirana komin dare...”

Saurin katse shi tayi da cewa.
“Please mi amor! Kuna gama meeting ka wuce wajan Baby ka ganta wlh d'azu muna girki ta kirani a wayan Suhal ta gama min kuka kaqi zuwa wajanta kuma tasan ka dawo Nigeria, tana kiranka bata samunka, dak'yar na lallasheta na rantse ma akan baka dawoba kana hanya, dan Allah kaje ta ganka ko hankalinta ya kwanta, bata saba rashinka haka ba, ina ma mgnar kwanaki Ce ai ta wuce kamar kasa komai a ranka Mi Amor please kaje kaga babynka gudalliyar 'yarka.”
Shattima daga can ya yamutsa fuska yana tauna lips d'insa na qasa, yaja sirirn tsaki tare da fad'in.
Sweetheart! Karki sake tashin tashi bana so wlh ni na manta ma kawai yanayin aikine, OK zanje zuwa 6 na yamma nima nayi missing sweet daughter bye zan kiraki idan naje sai hankalinku ya kwanta ba!”
Dariya tayi tana fad'in.
“I love you Mi Amor d'inmu...”
Da sauri yace.
“Keda wa?”
Cike da tank'washe murya tace.
“Ni Billy ni Bilkisu.”
Murmushi yay yana fad'in.
“Me too Kira yafi goma kin Hana na d'auka bye.”
Ya fad'a yana katse kiran.

Dariya Mamy tayi mai sauti tabi wayan da ido, kafin ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya, Allah ya sani tana bala'in son Shattima kamar ranta haka tana bala'in kishinsa, sai dai tana son Khairy ma ta zauna da Shattiman zama na auren sunna na har abadan, su samu zuri'ah mai yawa tana son ta gansu inuwa d'aya matsayin ma'aurata.
Wasu siraran hawaye masu azabar d'umi taji suna gangaro mata akan kumatunta, tai saurin gogewa tana murmushi tare da danna kiran wata lamba.
Maryam da take gefe zaune cikin Riga da skirt na material baqi tayi kyau kanta ba d'ankwali gashinta da yasha gyara sai walqiya yake, ta qurawa Mamy idanu sai kallonta takeyi, tana magana da turanci tana murmushi.
Maryam ji take kamar ta shaqo wuyanta sai ta daina motsi ko ta huta da baqin cikin ganin abinda Mamyn take shirin aikatawa.

*Abuja*


*YI WA KAI*

Free Novel

_October25/10/2022_

*37&38*

*Abuja*
Shattima bai samu kansa ba sai ana dab da Maghreb, wanka kawai yay ya nufi masallaci, bayan sallar isha yana shigowa ya duba yaga lokaci sauran 1 hour flight d'insu ya d'aga zuwa dutse, yaushe zaije yaga Khairy har su wuce airport? Dole ya biya ko atsayene su gaisa sai su wuce airport.

Khairy sanye da jallabi milk colour kanta yasha kalba, ta yane kanta da mayafin jallabiyar, sai uban qamshi take zubawa.
Zaune suke akan dining area, suna dinner.
Auntie Aisha tana kusa da mijinta, yayin da Suhal yana facing da Khairy, Ilham tana kusan Suhailat k'awar Khairy, wacce tazo tin jiya.
Khairy tana kallon Suhailat tace.
“Please kici Betsy sai wani cokalawa kikeyi,wai wa kike kunya anan? Baba ko Mummy? Ko k'annena Suhal da Ilham?”
Suhal ya harareta yace.
“Wlh nine babba tinda nine namiji shekara biyu kawai fa kika ban, kinada 21 inada 19.”
Khairy ta tintsire da dariya, har tana k'waruwa.
Auntie Aisha tace.
“Wato dai bazaki daina yawan surutu ba koh? Suhailat dan Allah kici abinci bar biya shirmen yaran nan...”
Murmushi Suhailat tayi.
Wayan Auntie Aisha ta d'auki ringing.
Ganin me kiran ta d'aga tare da sallama.
Shattima daga can compound d'in gidan yana hakimce a mota, ya amsa sallamar yana fad'in.
“Gamu cikin gidan fa! Kuma dududu bazamu wuce 20 minutes, za'amu wuce airport. ”
“Masha Allah Abdallah barka da zuwa ka shigo kawai.”
Ta katse wayan tana kallon mai gidanta wanda ya miqe yana goge baki da tissue, tace.
“Minister ne ya biyu mu gaisa zai wuce jigawa yanzu.”
“Kai Masha Allah munada baqi ashe, bari atarosa, Khairy! Tashi muje tarban Dady...”
Duk waige-waige suka fara ganin ba Khairy akan dining, basuga fitarta ba, ita ko tin lokacin da taji Auntie Aisha ta ambaci sunan Dadynta tayi jifa da spoon ta toshe bakinta ta miqe ta sulale ta fice.
Shattima yana qoqarin zuro qafafunsa waje daga cikin motar ya hangota aguje tana tahowa sai dariya take.
Idanunsa ya janye daga kanta yana murmushi ahankali ya furta.
“Toh fitinanniya.”
Ya fad'a yana fitowa daga motar.
Da sassarfa ta fad'a jikinsa tana fad'in.
“Oyoyo sweet Dady”
Sai kuma ta fashe da kuka tana qanqameshi.
Shattima yana qoqarin janyeta daga jikinsa, taqi tana sake lafewa cikin kuka tace.
“Dady baka sona yanzu? Dady wata uku ban ganka ba baka ganni ba,sai yau shine ko d'umin mahaifina banji ba zaka janyeni, I miss you so much Dady.”
Ta fad'a cikin kuka tana sake lafewa a jikin Shattima.
Shattima ya buga bayanta ya rankwafo da kansa, tsawonsu ya daidaita, bakinsa dab da kunnenta, cikin kwantar da murya yace.
“Tuba nake sweet daughter, bazan qara bari hakan ta faru ba OK? Ayima Dady afuwa.”
Ya k'arashe mgnar yana janyeta daga jikinsa,ya zaro handkerchief mai shegen k'amshi ya goge mata fuskarta ya Kama hannunta suna tafiya yana mata mgna qasa² tana murmushi.
Da Baban suka had'u ya fito tarbansa, yana murmushi yace.
“Ashe tuni taji ta gudu mu muna nemanta, Kai Khairyn Dady,Abdallah barka da zuwa ya hanya?”

Shattima yay murmushi ya kalli Khairy ta jimqe masa hannu gam kamar za'a k'wace mata shi.
Hannu yabasa sukayi musabaha suka gaisa cikin girmamawa ya masa jagora har cikin falon.
Ilham da Suhal suka tarbesa cike da murna suna gaishesa.
Auntie Aisha tace.
Shattima ya amshi gaisuwar Suhailat yana fad'in.
“Suhailat! Yaushe kika zo wajan k'awar taki? Sannu Allah bar zuminci .”
Khairy ta kwantar da kanta saman kafad'ar Shattima tana fad'in.
“Dady jiya tazo wai gobe zata koma don Allah sweet Dady kace tayimin sati.”
Dogon hancinta yaja yana hararanta. OK ta daina karatun tazo ta sakaki gaba?”
“Toh chingum sai ki sakeshi yaci abinci baida lokaci dayawa.“
Khairy ta matsa tana son sakin kuka jin Shattiman ba kwana zaiyi ba.
Hararenta yay yana lalubo lambar Mamy bugu biyu ta d'aga yace.
“Ga 'yarki.”
Yaba Khairy wayan.
Auntie Aisha tace.
“Toh muje dining area.
Shattima baya son musu ya bita yayi koda spoon d'aya na abinci ne zasuji dad'i.

Mamyt daga can tace.
“Baby! Yau dai hankali ya kwanta Dady yazo koh?”
Khairy ta fara kukan shagwab'a tana fad'in.
“Abinda ba kwana zaiyi ba Mamy kice Dady ya kwana please. ”
Mamy tayi dariya tace.
“Oh! Baby kiyi hqr yanda abubuwa anan d'in zai koma Abujan ai.”
Khairy tace“Mamy kawai dai kun daina sona gwarama ke,jiya Suhailat tazo gobe zata wuce gata Ku gaisa.”
Mamy suka gaisa da Suhailat tana mata godiya da kulawa.
Wajan tafiyar Shattima Khairy kuka kamar zata shid'e, ta riqeshi gam wai sai ta bisa, ganin Auntie Aisha zata mata fad'a, yay saurin tarewa, ya zazzare mata kamar zai doketa da gaske ta fasa kukan ya samu ya lallab'ata, ya bata tsarabasu ita da su Ilham, ya tafi suna d'ago masa hannu.
Auntie Aisha tace.
“Idan kinyi wasa wlh dukama riqeqi zanyi, shagwab'abb'iya, bakya girma Sam.”
Acan kuwa airport an samu 'yar matsala jirgi bazai tashi ba sai 11 pm.
Shattima ko ajikinsa, wayoyinsa ma yake yi tare da duba saqonni a email d'insa, kafin lokaci, suna chart da Mamy, hakan yasa Mamy nishad'i sosai.

Dutse
Aliyah zaune a falo ta rabka tagumi abin duniya ya isheta, amugun tsorace take da Salim, sbd ya kamata tana sallar isha, tasan shirun da ya mata abun ba alkhairi zai biyo baya ba.
Hawayen fuskarta ta share tana fad'in.
Ya ALLAH ka cireni daga wannan baqar rayuwar da nake ciki ka kawomin haske, idan Salim alkahirine agareni ubanagiji ka shiryeshi ka dawo da shi hanya, yabar zalumtata, idan babu alkahiri a zaman mu ka tarwatsa auren nan ka bani miji nagari wanda zai soni tsakani da Allah.”
Ta qarashe mgnar cikin kuka.

Salim zaune agaban Father da Umma Sa'idah, ba kunya ba shakka yake fad'in.
“Ni fa tsakani da Allah Umma idan anga na Saki Aliyah kar wanda ya tuhumeni tinda ba zaman aure tazo ba, idan bataona ba sai ta fad'aba na saketa meye aciki.”
Umma Sa'idah tace.
“Kaga bamason kwana² fito ce ga abinda ta maka ba wai kana mgna me harshen damo ba.”
Salim yace.
“Toh ba rufe² kullun cikin qarya take bata sallah, tinda tazo gidan kullun hakane,yau na kamata tanayi wlh taci sa'a yau inajin mutunci da tuni an wuce wajan na koya mata hankali sai ta kwana ahospital.”
Hashim yace.
“Subahanallhi Salim yaushe zakayi hankali ne wai? Komai d'an haqurine dan ubanka bakaga yadda ka mata afarkoba, ba dole ta dinga gudunka ba, wlh Sa'idah kina shaida idan ka kuskura ka Saki Aliyah sai na maka baki na amshe dukkan dukiyata ka fita kabar min gidana, tinda bakada takaici da hankali ai Kai ba yaro bane kasan baqi kasan fari, kuma naji saqonka wajan uwarka wlh idan ina Raye bazaka auri Ummulkhairi ba, tashi wuce katafi gidanka mutumin banza.”
Salim cikin fushi ya miqe yana tafiya yace.
“Idan kuma Allah yayi matatace ba sai rabo ya kashe ka Father. ”
Ya fad'a da sauri yana barin falon.
Umma Sa'idah tana tafa hannayenta tace.
“Me zanji me Zan gani Salim! Akan mace kakema mahaifinka fatan mutuwa?”
Hashim yace
“barsa dan ubansa zai dai mutu.”

Lokacin da ya dawo gidan har Aliyah ta kwanta, sai da ya gama shirinsa

Please Login or Register in order to submit comment