Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Liza suka biyo bayansu aka dakatar dasu basu shiga ba.
Suna shiga Khairy kallo d'aya tama Abdoul ta zube gaban gadon ta kece da kuka tana riqo hannunsa tare da cewa.
“Don girman Allah Yaya Abdoul ka tashi wlh namaka alqawalin zan tsaya tsayin daka sai ka auri wacce kakeso kaji?”
Kansa ya girgiza yana tari tare da damqe hannayenta hawaye sun cika idanunsa yana so yayi magana ya kasa dak'yar ya iya furta.
“Ummulkhairi Allah ya miki albarka don Allah ki yafemin kicema su Abba su yafemin ki sakani cikin addu'arki sannan don Allah karki...”
Daga nan Allah bai basa ikon sake magana ba bare ya fad'a mata abun na gaba,ransa ya fita fat har Abadan.

Khairy ta sake damqe hannayensa tana kuka tace.
“Yaya sannan me fad'amin don Allah wlh komai kakeso zanyi namaka alqawali.”
Dr Kimo zaiyi magana yaji qaran bud'e qofar ya waiga.
Minster Shattima da Mamy se commissioner Aminu da Ammi, dukkan aguje sukayo kan Abdoul kowa yana kiransa.
Khairy cikin farin cikin ganin iyayan nasu, ta fara kuka tana dariya tace.
“Yawwa iyayanmu kuzo kuga Yaya Abdoul yana tsakarmin nasiha ya k'yale ji idanunsu shi ba bacci ba shi ba sumaba.”
Ammi kallo d'aya tama d'anta ta zube jikinsa ta fashe da wani irin matsiyacin kuka tana fad'in.
“Abdullahi me yasa zakamin haka? Me yasa bazaka jiraba nazo muyi maganar k'arshe? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Ta k'arashe maganar tana shafe masa idanu.
Shattima kamar gumki ya tsaya Inda yake ko motsi ya kasa, Aminu ne ya k'araso yana janye Ammi daga jikin gawar.
Mamy ta kalli Abdoul ta kalli Khairy ta kalli Shattima ta kalli Aminu ta kalli Doctor, jikinta na wani irin tsuma ta kasa koda k'wak'waran motsi itama.
Khairy kuw tace.
“Dr nifa ban ganeba me yake faruwane?”
Doctor Kimo da harshen turanci yace.
“Ya rasu kuyi masa addu'a itace yake buqata ayanzu Allah ya jiqansa da rahama.....”
Khairy ta fasa wani irin gigitaccan ihu sai kuma ta sheqe da dariya tai wani tsalle ta cakumi wuyan doctor bada wasaba, ta Kama masa wuya....
_Rahma Real Ladingo ce_

_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 23&24*


Ga baki d'aya hankalin su ya yi kan Ummulkhairi, jin ta sheqe da dariya ta cakumi wuyan Dr, tana fad'in.
“Wallahi k'arya kake kayi kad'an ka kashe shi A barka, nima kasheka zanyi,yaya Abdoul tashi ka gani zan rama maka, shima kashe shi zanyi.”
Ta k'arashe maganar tana wata irin dariya.
Shattima ganin halin da Ummulkhairi ta shiga, ba qaramin tayar masa da hankali yayi ba.
Cikin wani irin sauri shi da Mamy suka iso wajansu, bakin Shattima na maimaita kalmar.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Khairy! Meye hakan?”
Ya k'arashe mgnar yana sanya dukkan hannayensa ya kamo hannayenta da ta shaqe Dr tana sambatu alamar dai ta samu matsalar k'wak'waluwa.
Wani irin riqo Shattina ya mata tana fuzgewa tare da maido dukkan bala'in da takeji akansa, ta kamo tsokar damtsen hannunsa da haqoranta, ta danna masa cizo, iya qarfinta se da ya runtse idanu ya bud'e yana kallonta, yace.
“Baby! Ki nutsu don Allah ki amshi k'addaraki kinji?”
Dariya ta sheqe da shi tana cakumar wuyansa, sai kuma ta fashe da kuka ta rungumeshi kamar zata tsagashi gida biyu, tana wasu irin surutai.
Sbattima ya matseta gam, tare da mata rad'a a kunnenta.
“Don Allah Baby ki dinga maimaita kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fii musibati hi wakhlifni khairan minha, pls ki dawo nutsuwarki ki aminshi dukkan k'addaraki da Allah yake jarabtarki da ita, insha Allah agaba komai zai wuce, bake kad'ai ba kika rasa Abdoul, ayanzu addu'armu yake buqata karki d'orawa kanki haukan gangan na rok'eki da girman Allah kinji Ummulkhairi? ”
Kuka kawai take tana sake lab'ewa ajikin Shattima, se kuma ta sheqe da dariya.
Shattima ya runtse idanunsa tare da furta.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil, la haula wala quwata Inna billah, Dr please kayi wani abun a bata taimakon gaggawa koda allurna bacci kafin ta dawo hayyainta Ina ji ajikina batada wata larura ta k'waluwa tsabar tashin hankaline.”
Dr yace.
“Ok riqeta muje d'akin da ya dace akula da ita, bani zan bin ciketa ba.”
Shattima ya jinjina kansa ya fara k'ok'arin zareta daga jikinsa, yana fad'in.
“Muje Baby amiki allura ki samu nutsuwa don Allah da zaran kin tashi ki dawo normal OK?”
Dariya ta sheqe da ita tana qara maqalewa jikinsa sai ta fashe da kuka tana girgiza kanta.

Mamy ta fashe da kuka ta zube qasa dab da k'afafunsu, tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fii musibati hi wakhlifni khairan minha Baby don Allah karki d'orawa kanki ciwon hauka da wanne zamuji, ga gawar mijinki a shimfid'e.”
Aminu da Ammi, ganin halin da ake ciki, se hankalinsu ya qara tashi sosai bayan sun lullub'e gawar.
Aminu yay gyaran murya yace.
“Dole za'a kai Abdoul wajan ajiyar gawa har muga jikin Khairy zuwa gobe kafin mu wuce da gawar gida ayimasa suttura, duba kaga halin da take ciki, ubangiji ka kawo mana d'auki kasa k'wak'waluwarta bata samu matsala ba.”
Ammi da Mamy kuka kawai suke basu iya sake cewa uffan ba.
Shattima dak'yar ya samu suka fita da Khairy aka kaita b'angaran masu matsalar k'wak'waluwa, aka shiga bincikar lafiyarta.
Gawar Abdoul kuwa an kaita wajan ajiye gawawaki.
Khairy anci uban fama da ita kafin asamu ayi mata bincike, tare da banka mata alluran bacci na tsawon 24 hours, domin k'wak'waluwarta ta samu ta huta, dan da gaske ta samu gushewar k'wak'waluwa, abubuwan ba qaramin razanata sukayi ba,bata san me take ba ayanzu.
Shattima zaune suna facing da Dr David wanda ya gama duba Khairy ya kuma rattabowa Shattima bayanai tsaf d'aya bayan d'aya.
Manyan lumsassun idanunsa masu haske wanda suka rikid'e sukayi ja, ya zubama Dr baya ko k'iftawa jin da gaske Khairy ta samu matsalar k'wak'waluwa.
Dr David ya kalli Aminu yace.
“Ku kwantar da hankalinku zata dawo normal amman sai a hankali ba wai yanzu Kai tsaye ba, dan haka Ina baku shawara kubar mutum d'aya ya wadatar ku tafi domin suttura shi yaronku da ya rasu, karku ajiye gawar kuce sai taji sauqi.”
Shattima ya sauke numfashi tare da jinjina kansa, yace.
“Insha Allahu ayau zamu wuce har itan tinda baccin nata zai d'auki 24 hours, zamuyi mata magani agida...”
Abba Aminu yace.
“A'a Sam hakan bazai yuba waye baisan laruraba, ku zauna don Allah akwana biyu har ta dawo hayyacinta, sai kutafi ni kaina badan dole ba inda zamuje sai Kharynmu ta samu sauqi.”
Shattima kallon Aminu kawai yake baice komai ba, shi kam baisan irin abokin da Allah ya had'ashi da shi ba nagartaccen mutum...
Washegari kuwa Shattima Bilkisu ya bari wajan Khairy ya biyo su Aminu Nigeria dan Sam bazai iya zama ba acan ayi jana'izar Abdoul babu shi ya gwammaci kome zai faru da Khairy ya faru akan dai ya zauna a Singapore wajanta yabaro amininsa.


*Gumel*
Usman tinda suka iso Gumel tin bayan kwana biyu da suka wuce, hutawa kawai yake bai fita ko nan da can ba.
Tsaye yake gaban madubi yana kallon kasan, shi da kasan yasan yayi kyau matuqa, sannan shi d'in kyakkyawan baqin bafulatani ne.
Sanye yake da jeans da T-shirt baqa ya gyara sumar kansa mai bala'in taushi. Turarensa mai tsada ya fesa ya ajiye yana kallon wayansa da take fama ringing.
Ganin me kiran ya saka shi d'aukan wayan, tare da yin picking call d'in yakai kunnensa, tare da sallama yana murmushi yace.
“Allah shi taimakeka ya gari ya fama da jama'a?”
Kome aka ce masa ya k'yalk'yale da dariya yace.
“Toh ni kam yanzu duk wannan ba shine gabana ba, har na nutsu na kammala abubuwan gabana idan yaso sai na fara neman macan da zan aura.”
Ya jima yana wayan kafin ya gama ya zura wayansa cikin aljihu ya fito.

Falon ba kowa sai hajiya Karima ta hakimce tana waya sai wani shan qamshi take.
Usman ya qaraso ya zauna kusanta ya jingina kansa da kafad'arta.
Tana idar da wayan ta shafi kansa tana fad'in.
“Yanzu de se ayi mgnar aurenka my son Nadiya nafison ta kammala karatunta.”
Usman yay murmushi har dimple d'insa ya lob'a yace.
“Mom yanzu? Kuban lokaci har na fara aikina insha Allah zan nemi mace ta gari.. Wai Mom har yanzu babu labarin Auntie Zainab ne...¿ dan sun rabu da Baba ba shi zai saka ace zumunci ya qareba, insha Allah zan shirya naje katsina wajanta na ganta, k'ilama tayi aurenta.”
Hajiya Karima taji gabanta ya fad'i, ta wayance ta fara kukan munafurci tana fad'in.
“Usman! Al'amarin Zainabu mun rasa kan gadonsa, babu ita babu labarinta shekaru biyar, sbd Allah dan an sakeki sai ki yanke alaqa damu.”
Usman yace.
“Kinsan da yake ba baki gareta ba, sai haquri zan nemeta idan na nutsu insha Allah. ”
Hajiya Karime aranta tace.
“Insha Allah bazan tab'a barin hakan ta faru ba.”
Amman azahiri se tace.
“Gaskiya ya kamata anemeta aji lafiyarta watarana, amman ka bari har ka nutsu.”
Usman ya jinjina kansa yace.
“Insha Allah Mom, bari na d'an zagaya gari na dawo gobe zanje Abuja kuma kwanaki zan d'anyi.”
Fatan alkahiri ta masa ya fice, ita kuma ta miqe hankalinta A tashe ta d'auki wayanta ta danna kiran wata lamba ta nufi stairs.


Tin kafin su Commissioner Aminu su iso k'asar Nigeria, mutuwar babban d'ansa ta bazu aduniya 'yan Uwa da abokan arziqi sun shiga jimami ba kad'an ba.
Maryam lokacin da taji labarin wajan Kawu Bala, fad'uwa tayi ta suma har yanzu batasan inda kanta yake ba.
Kasancewa tsakiyar dare suka iso, asibiti suka Kai gawan, ta kwana acan.
A cikin daren nan Shattima ya nufi gidan mahaifinsa, da yake unguwar galadanci.
Baffa liman na zaune samman darduma kamar kullun a d'akinsa a keb'ance, yana neman kusanci da ubangijinsa.
Qaran tab'a k'ofa yaji can falo, bayan kamar minti 10 sai yaji ana nufo wajan d'akinsa yana jin muryar inno matarsa.
Qofar d'akin aka bud'e aka shigo da sallama.
Amsawa yayi yana kallon inno tana riqe da hannun Shattima.
Zaman sa ya gyara yana kallonsu.
Shattima ya zauna qasa kusan mahaifinsa yana fad'in.
“Baffa! Barka da dare ina yini?”
Liman ya amsa tare da fad'in.
“Abdallah! Lafiya kuwa cikin daren nan? Ina tafiyar da kace zakuyi? Ya jikin na Abdoul?”
Shattima yay k'asa da kansa fuskarshi na nuna tsantsar damuwa, yama mahaifinsa bayanin komai da ya faruwa.”
Liman ya furta.
“Qalu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Abdoul ya rasu? Ummulkhairi hauka? Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarmu da k'addaramu, Allah ya jiqan Abdoul yasa Annabin Rahma ya cecesa, Khairat Allah bata lfy yabata ikon cinye jarabawar da take baibaye da rayuwarta Amin.”
Shattima ya amsa da.
“Ameen Baffa.”
Inno tace.
“Yanzu kuma ya za'ayi kabar Bilkisu ita kad'ai zata iya da jinyarta kafin ka koma?”
Shattima yace.
“Eh insha Allah da anyi sadakar uku zan koma, da Auntie Aisha zan tura su zauna tace ba komai zata zauna har nazo, munyi mgna Dr ba wata matsala insha Allah. ”
Inno ta goge hawayen fuskarta tace.
“Ai kawai taren zaku tafi Allah ya bata lfy...”
Shattima bai koma can gidan sa ba, nan ya kwana wajan mahaifinsa sai bayan sallar asubah aka kaisa gidan ya shirya ya nufi gidan commissioner Aminu, wanda suke cike da jimami.
Tin bayan sallar asubah gidan commissioner Aminu ya fara d'aukar jama'a, aciki harda Liman Umar da duk wani dangin Shattima na kusa wad'anada suke cikin gari da ruga.
Misalin k'arfe 10 am, aka suturta gawar Abdoul, bayan Aminu ya masa addu'a ya umarci Abida Ammi tayi masa addu'a.
Cikin kuka ta rungume gawar tana fad'in.
“Abdullahi na yafe maka duniya da lahira, ni daman baka tab'a min laifi ba yanzu shi kenan ka rasu? Ka tafi tafiya ta har Abadan....?”
Aminu ya janyeta akan gawar sauran 'yan uwansa suka masa addu'a harda Maryam da ta dawo hayyacinta ta dake ta masa addu.”
Haka sunaji suna gani aka fitar da gawar Abdul aka sallaceta aka kaisa makwancinsa.
Fad'in irin jama'ar da ya samu b'ata lokaci ne.
Dole idan ka shigo wannan ahali su baka tausayi har shi Aminun da yake b'oye damuwarsa Amman kallo d'aya zaka masa ka gane mutuwar d'ansa ta shigesa.

Azizah lokacin da taji labarin rasuwar Abdoul, har an binnesa haukane batayi ba, ta gigice ta fita hayyacinta, kuka idanunta se da suka kumbura.
Aguje ta shigo falon duk ana zazzaune ta zube tana kuka tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Abdoul Allah ya jiqanka ka yafemin abinda na maka, ashe Kai d'in ba mai tsawon kwana bane, ashe ni ba matarka bace ba, wayyo duniya wlh naji na tsani komai da nake aikatawa ashe duniya batada tabbas. Astagfirullah wa'atubu alaikhhh, anya Khairy mutunce kuwa? Ace duk wanda ta rab'a sai masifa ta riske shi Abdoul ka tafi ka barni ya zanyi da raina...? Khairy bazan tab'a yafe miki ba.”
Kowa kallonta yake a falon, cike da mamakin furucinta.
Ammi idanu kawai ta zuba mata casbi ahannunta tana ja, idanunta cike tab da hawaye, shi kenan ta rasa d'anta? Amman jin kalman Azizah ya saka ta zaburo tana fad'in.
“Ke! Tashi ki fice karki b'atamin gawar d'ana, mu mun dogara da Allah da manzonsa, ba maiyi se Allah kuji wata musiba wa ya isa ya d'orama k'addara idan ba Allah ba...”
Azizah tana kuka tace.
“Kuyi haquri nima abinda naji ne ana fad'a agari shiyasa,amman nima bazan kuma ba Allah ya jiqan Abdoul..."”
Ammi tace.
“Amin kije kawai Allah ya bada lada ba wanda ya isa ya jama wani masifa ko bala'i sai daman can ubangiji ya k'addara masa. Wanda suka yardama da mgnar wlh rashin tauhidi ne, duk mai tauhidi bazai yarda wani yana kashe wani ba tare da lokacinsa yayi ba, ko ya rayashi ko ya azutarshi ko ya talautashi. Don Allah ki tashi kije mungode.”
Ta k'arashe mgnar tana satar kallon wajan da su inno suke zaune su Auntie Aisha, sai taji bala'in kunya ta kamata, barin irin mugun kallon da taga Auntie Aisha nayima Azizah na qasqanci.
Azizah ta miqe cike da kunya batayi tunanin hakan ba ta zaci Ammi zata kama zancanta.
Umma Sa'idah de kallon ammi take da mamaki ga abunan azahiri ya fito Amman sunqi su gask'ata shi.
Baki ta tab'e ab'oye aranta tana fad'in.
“Allah de ya rufamana asiri da yanzu Salim ne ya rasu.”


Salim kuwa koda yaji rasuwar Abdoul bai ji wata damuwaba dayawa asalima farin ciki yake aganinsa Khairy ta kusa zama tashi shi kad'ai.
Sanye da bugaggar shaddah fara k'al yana fesa turare, wayansa ta d'auki ringing, yana ganin mahaifinsa ya d'auka yana fad'in.
“Hello Father! ”
Hashim daga can yace.
“Ashe Salim rashin imaninka har yakai haka ban saniba? Ace anyi rashi har an binne baka zoba jana'izah?”
Salim yace.
“Afuwa Father wlh yanzu zan tafi ai dole naje gaisuwa kodan ya barmin matata ma...”
Tsaki Hashim yayi yace.
“Mahaukaci dai baxai tab'a warkewa ba, dan ubanka bakada mata se Aliyah,sauran kazo ka gwada shirman har asanya zargi wani akanka, abanza akamaka wlh kuma ba inda zanje tinda kai bazaka tab'a hankali ba.”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran.
Salim ya sheqe da dariya yace.
“Wlh akan Jewel akirani da abinda yafi mahaukaci ma na d'auka.”
Ya fad'a yana kiran lambar Abdurrazaq abokinsa, bugu d'aya ya d'aga yace masa.
“Kazo na shirya muwuce wajan gaisuwar mijin matata da ya rasu Abdoul Aminu Kazaure.”
Abdurrazaq daga can yace.
“Ni ai ba d'an isaka bane irinka na tsaya har wannan lokacin ban tafi ba,ai dani aka binne shi.”
Yana gama fad'in haka ya katse kiran.
Salim ya d'aga kafad'a yace.
“Mutuwarnan fa kowa lokaci yake jira sbd Allah, ai ni an taimakamin sbd bankai aikata abunda nayi niyaba Abdoul ya cika da kansa, ai ko daga haka sai agane Allah yana sona da Jewel Khairy...”
Ya k'arashe maganar yana murmushi ya fice daga d'akin.
★★★
Bayan kwana uku Shattima ya fara shirin tafiya Singapore shida yayunsa Munnir da auntie Aisha sai Adamu yayan Bilkisu, dan yace dole itama k'anwarsa tana buqatar ganin nata akusanta.
Washegarin kwana uku yama Aminu sallama suka nufi Abuja dan tafiya.

Acan kuwa Singapore Khairy tin bayan da allura ta saketa, hauka tuburan take cizo yak'ushi ga wata irin dariya da takeyi,abun sai muce Allah bata lafiya,alluran bacci da wanda zasu sanya k'wak'waluwarta ta dawo daidai sannu sannu aketa maka mata sune hutunta.
Mamy Bilkisu duk ta rame se kuka da yawan salloli tana roqon Allah ya kawo ma Khairy lafiya.

Mamy zaune a reception kamar kullun casbi ahannunta tana ja, sosai take farin cikin zuwan da su Shattima zasuji harda yayanta Adam.
Se yau sosai takejin zazzab'i ajikinta ga shi lokacin farkawar Khairy baiyi.
Hawayen fuskarta ta goge ta miqe tsaye ta nufi room da Khairy take kwance.
Kamar kullun ta window ta leqa Khairy.
Kwance take gashin kanta ta hargitse dogon baqin gashinta ya bazu agefen fuskarta, kallo d'aya zaka mata kasan ba cikakken hankali, atare da ita, sbd yadda take hargitse kayan jikinta da gashinta, tana sanye da uniform irin wanda ake sakawa duk wani mahaukaci da yake zaune a asibitin.
Mamy cike da mamaki take kallon Khairy idanunta abud'e tana kallon silin d'akin hawaye da majina jargab akan fuskarta, alamun sun nuna yau ta farka acikin hayyacinta.
Cikin farin ciki Mamy ta nufi office d'in doctor d'in da yake kula da mahaukatan tana kukan farin ciki alamaun Khairy ta dawo hayyacinta...

Acan kuwa Abuja misalin qarfe 1 na Rana agogon Nigeria aka fara sanarwar jirgin matafiya sauran 10 minutes ya tashi.
Shattima sanye da wani tattausan boyel mai bala'in kyau ga tsada fari k'al, kasancewarsa mutum mai son farin kaya.
Ya kalli tsadaddan agogon da yake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya miqe yana jin zuciyarsa wata iri baki d'aya bayada wani farin ciki ko daidai da k'wayar zarra tin ranan da wannan al'amari ya faru, zagayawa yayi sbd fitsarin da ya keji gashi da kyankyami duk da yasan ana qoqarin gyara toilets d'in.
Anutse yake tafiya,aransa banda Kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ba abinda yake fad'i.
Daidai corridor d'in da zata sadashi da toilet d'in yaja burki ya tsaya Sam yaji bazai iya shiga ba ya juyo da zumar komawa yaji yayi Karo da mutum.
Da sauri yaja baya yana fad'in.
“Subahanallahi.”

Ya k'arashe mgnar yana d'ago da kansa da niyar ganin waye ya buge bisa kuskure.
Idanunsu suka shige waje d'aya.
Minister Shattima yayi wata irin zabura amutuqar gigice da firgici tsoro tashin hankali, da mamakin abinda yake gani agabansa idan dai ba gizo idanunsa suke masa ba toh tsaf fuskar....
Za'a Fara fa!😂Muhad'u gobe insha Allah.💃🏻🚶🏻‍♀️

Uwar Farisah

_YI WA KAI...!_

_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 25&26*

In de ba gizo ba idanuwansa suke masa ba, tsaf fuskar da ba zai bayyana waye ba ya gani A fuskar Usman sak, wanda yake tsaye agabansa, sak kamar an tsaga kara, har baqin da dogon hancin idanunsu kawai suka banbanta, amman har gashin giransu iri d'aya ne, haka bakinsu, nazarin second 5 Shattima yayi, ya kafe Usman da idanu.
Security Shattima wanda ya yinquro domin kama Usman.
A kuma dai-dai lokacin Usman ya bud'e baki da niyar ba shi haquri, ganin minister Abdallah da kansa dan ya sansa a Tv.
Ganin irin kallon da Shattima yake ma Usman, ga securitynsa na shirin rik'eshi, se Usman d'in ya d'an tsorata cikin sauri yace.
“Don Allah kayi haquri yallab'ai ban kula da kai ba.”
Shattima ya dakatar da security'n ya masa nuni ya tafi.
Cikin dattakunsa yace.
“d'an saurayi Kai na inane? Ba lokaci Amman don Allah inaso ka ban address inka idan ba damuwa OK?”
Usman cike da mamaki yace.
“Ni yallab'ai? Allah yasa ba wani matakin zaka d'auka akaina ba? Wlh ban ganka ba se da guri ya k'ure.”
Shattima ya dafa kafad'arsa yace.
“No! Ba ko d'aya ka ban.”
Usman ya zaro katin address d'in gidansu ya beqawa Shattima, ya amsa yana dubawa yaga harda katin wayarsa ajikin, yace.
“Ngd se na nemeka insha Allah, amman dan Allah ka amince inason zan maka hoto.”
Usman yace.
“Ok ba damuwa inada yaqinin bazaka tab'a cutar dani ba.”
Shattima ya jinjina kansa ya zaro zungureriyar tsadaddiyar wayarsa yama Abdoul hoto, yace “Ngd Allah yama albarka.”
Ya k'arashe mgnar yana tafiya cikin nutsuwarsa, amman wani b'angaran hankalinsa yayi bala'in tashi sbd wani al'amarin da yake shirin faruwa.
Usman yabi Shattima da kallo yay murmushi yace.
“K'ila na burgeshi ba mamaki wani aiki me matsayi zai samamin.”
Ya qarashe mgnar yana nufar toilet.

Shattima yana dawowa da 5 minutes suka shiga jirgi, bayan 'yan mintina jirgin ya tashi.
Yayin da jirginsu Usman shima ya d'aga zuwa dutse.


*Singapore*
Mamy se da tayi knocking d'in k'ofar kafin a bata iznin shiga.
Jiki na rawa ta bud'e ta shiga.
Dr David ya ajiye biron hannunsa yana kallonta.
Cikin kukan farin ciki da harshen turanci tace.
“Doctor! Ummulkhairi Abdallah ta farka,da halamun tana cikin hayyacinta, naga tana kuka.”
Dr David ya miqe tsaye yace.
“Ok muje.”
Yana bud'e k'ofar d'akin da Khairy take yace da Bilkisu.
“Ki d'an jira karki iso har na tabbatar da abinda kike zargin.”
Kai ta jinjina.
Anutse ya k'araso wajan gadon, yana kiranta.
“Ummulkhairi! Tashi muga.”
Da wani irin sauri Khairy ta waigo ta kalli Dr David, hawaye sharaf akan fuskata ta miqe zaune tana turo bakinta gaba, tana harba k'afafunta.
Dr ya tafa hannayensa, yace.
“Bravo! Toh wacece waccan?”
Ya tambayeta yana nuna mata Mamy da ta rakub'e jikin qofa sbd bazata manta shaqar da ta mata shekaran jiya ba.

Khairy ta k'urama Mamy matsagaitan idanunta masu kyau, ko giftawa batayi.
Ahankali tayi 'yar dariya tace.
“Wannan ba ita bace jirgin sama da muke hawa zuwa kamo fara?”
Dr David yace.
“Oh! My God! Wannan mahaifiyarki ce, Kahiry ki nutsu ki tuna ke wacece?”
Khairy ta sheqe da dariya ta kamo gashinta ta laulaye yatsunta tace.
“Wallahi natuna nice jakar nan wacce ake lodamin kaya ko? Kawo kayanka na wanke maka...”
Mamy Bilkisu ta fashe da kuka ta nufi Khairy da gudu da zunmar ta rungumeta.
Khairy kuwa ta sheqe da dariya, ta k'udundune waje d'aya tana fad'in.
“Wayyo jirgin zai bi ta kaina ni yau bazanje kamo fara ba...”
Dr David, yace.
“Karki isa wajanta kiyi hqr zata dawo normal, bari na mata alluranta, magugunan cikinsu na tabbatar miki zasuyi magani se ahankali,ba wai kai tsaye ba.”
Ya fad'a yana danna wata 'yar na'ura.
Nurses uku suka shigo, bayan ya had'a alluran, cikin dubara suka riqe masa ita ya mata alluran, Mamy na gefe tana kallo tana kuka.
Bayan ya gama mata alluran, ya jona mata na'ura yana bincike yaga cigaban da aka samu, ba wani cigaba sauqi se awajan Allah.
Dak'yar ya samu Mamy ta fito ta zauna wajan zamanta tana kuka se da ya isheta ta miqe take tayo alwala ta fara sallar nafila kamar yadda ta saba, tana idarwa ta koma jikin window tana leqen Khairy.

K'arfe 1 na dare jirginsu Shattima ya isa k'asar Singapore.
Lokacin da suka iso asibitin Bilkisu ta tafi masaukinta, hotel d'in na nan dab da asibitin duk na mutum d'ayane, hotel d'in ta had'u iya had'uwa,sbd ba'a kwana a hospital d'in wajan majinyaci wunine akeyi.
Bayan su Shattima sun duba Khairy wacce take bacci, suka nufi masaukin nasu hotel d'in da Mamy take, sbd Shattima ya saka Mamy ta kama musu d'akuna kowa da d'akinsa, banda Shattiman wanda d'akin Mamy ze zauna, se da kowa ya shige masaukin sa ya musu se da safe ya nufi room d'in da Mamy take.
Cikin bacci wanda yake cike da mafarkan da ta saba se de na 'yan kwanankin nan sun sawwaqa tasan kuma dalilin.
Mamy taji ana knocking d'in k'ofar.
Idanunta Wanda suke cike da barci ta bud'e, bakinta d'auke da salati ta miqe zaune, tana gyara hular kanta ta sauka daga saman bed d'in, tana sake gasqata mafarkin da take yanzu ta samu amsarsa dole kuma zata cika duk abinda take gani A mafarkin nata domin hakan zai zama _(Yi Wa Kai)_ kuma jahadi taimakon kai da kai duk da tasan zata fuskanci k'alu bale iri-iri.

Tana bud'e k'ofar taga Shattima tsaye.
Asanyaye ta masa sannu da zuwa tana basa hanyar shigowa.
Anutse ya shigo yana kamo hannunta tare da rab'ata ajikinsa yaji jikinta zafi rau, cikin amon muryasa mai dad'i ya furta.
“Subahanllahi sweetheart! Kina zazzab'i koh? Ya Rabbi! Ki rage damuwa.”
A tare suke rufe k'ofar, yajata suka nufi kan sofan da take ajiye a falon.
Kallonsa take cike da tsantsar damuwa da kewarsa hawaye kwance saman kumatunta.
Rungumeta yay yana share mata hawayen da tafin hannunsa yace.
“Sweetheart! Kukan ya isa haka, sweet daughter Allah ze bata lfy, muci gaba da mata addu'a kinji? Oya muje hospital d'in a miki koda allura ce.”
Jikinsa ta lab'e tana nuna d'an madedecin table agefensu tace.
“Ga mgugunan can da nazo dasu ina sha.”
Kai ya jinjina ya kamata suka miqe yace.
“Toh kisha se ki kwanta OK?”
Kai ta d'aga, shi b'allo maganin ya bata tasha, ya taimaka mata ta kwanta ya janyo k'aramar trolley d'insa ya zaro towel ya shiga bathroom.
Wanka yayi ya d'auro alwala ya fito ya goge jikinsa,

Please Login or Register in order to submit comment