Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanya Alhmdulillah."
Shattima yace.
"MASHA ALLAH, muje ciki ana taro idan an gama muje masallaci daga can kuma sai muje gida."
Usman ya amsa da.
"Toh ba damuwa Yallaɓai, Amman irin wannan waje naku na manya har dani na shiga?"
Shattima kai ya girgiza yana kauda kansa daga kallonsa sabida fuskar Ummul khairy sak ba wani banbanci sai manyan idanu da ya fita, amman har kalar baƙinsu sak ɗayane duk kuwa jin ɗaɗi da hutun da take samu baƙinta sai dai yay wani irin kyau yayi sheƙin jin daɗi da hutu.

Tin basu ƙarasa cikin tsakiyar hall ɗin ba, aka tarbesu tare da kaisu wani keɓantaccen wuri saman wasu luma-luman kujeru suka zauna.
Shattima anatse yake kallon komai yana mai cike murna, hango matan da suke tsaye cikin harda matar da yake so Usman ya gani.

Zainabu sanye take atamfa kalar blue mai ratsin baƙi, riga da zani sai hijab shima yasaka duhun baƙin takalmin ta baƙi, komai sabone ajikinta, tayi kyau MASHA ALLAH.
Anutse cikin maganar bebaye take bayani kamar jiya da shekaran jiya, sai dai yau bayaninta ya sha banban da sauran bayanin shekaran jiya da kuma jiyan, salon yadda take bayanin da hannayenta abun ya burge jama'a, barin kuraman da aka gayyato sukazo taron da yake sunfi gane me take nufi sai tafi suke suna jin ƙwarin guiwan lallai zasu dage da karatu su tsaya kan ƙafafuwansu su nemi na kansu.
Usman sam bai ankare da ita ba sai lokacin da ta ɗaga hannayenta da tana kwararo addu'a, jama'a suna amsawa da AMEEN, saboda yadda take yi kowa ya gane Addu'a takeyi.
Zuwat ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Auntie Zainab!"
Ya Kira sunanta da ɗan ƙarfi yana nufar wajanta. Karaf taji sunanta da aka kira har tsakiyar dodon kunnenta, Kasancewar wajan da suke zaune saitinsu ne ba jama'a sosai da suka masu shamaki da juna, karaf idanunta suka sauka akan Usman, ta zazzaro idanunta waje cikin tsananin tsoro...

Iya firgici Zainabu ta shiga firgicin ganin Usman, amman ganin inda take taron jama'a ne, sai kawai ta sakawa zuciyarta jarumta, ta waske kamar bata san shi ba, sabida kar jama'a su gane halin da take ciki, taci gaba da addu'arta, har lokacin da ta kammala, tana ƙoƙarin barin wajan, sabida kukan da yake son cin karfinta ya kuɓuce mata.
Dakatar da ita akayi sabida kyaututtukan da za'a basu.

Shattima ganin da gaske Usman wajanta zai tafi, yay saurin kamo hannunsa yana faɗin.
"Calm down Usman! Me yake faruwa ne? Ka nutsu ko saboda gobe, ba'a nunawa mutum sani irin haka na tashin hankali cikin jama'a, karka je zauna, me yake faruwa ne?"
Ya faɗa yana zaunar da shi.
Numfashi mai zafi ya sauke yana sake damƙe tattausan hannun Shattima, yana kalleshi yana faɗin.
"Yallaɓai Auntie Zainab ce ita ce nake baka labarin..."
Shattiman yay saurin saka tattausan tafin hannunsa ya rufe masu baki, anutse cikin taushin murya yace.
"Mubar mgna anan wajan har mu nutsu Ok? Abinda nakeso ka bari a tashi zamu sameta keɓance sai kuyi magana."
Kai Usman ya jinjina yana sauke numfashi, ya lalubo wayar cikin aljihunsa yana shirin kiran Mustapha Shattima yace.
"Karka kira kowa yanzu anan ka nutsu Ok?"
Kai ya jinjina.
Kyaututtuka aka fara basu Zainabu wanda kyautar Shattima da kansa ya bata tana godiya tare da jinjina masa.
12:15 daidai aka gama taron.
Shattima basu bar wajan taron ba sai dai ya gana da shugaban jagoran ƙungiyar tasu Zainabu ya amshi address ɗin masaukin su da lambar shugaban tafiyar nasu akan zai kirasa zuwa yamma, kafin su tafi.
Kai tsaye gida Shattima ya saka aka maidasu, Usman yay alwala wanda ya gaza haƙura sai da ya kira mahaifinsa.
Wanda alokacin shima yana shirin tafiya masallaci ya labbarta masa komai yace kawai bayan sallar juma'a ya taho Jigawan ya ganewa idanunsa sak Zainabu ce Amman ta nuna bata sansa ba......

*Gumel*
*Ƙarya ta ƙare bori ya kashe boka*

Masu iya magana suka ce.

_("Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya.")_

A komai idan mutum zaiyi ya dinga tunawa akwai ALLAH, sannan Allah baya bacci, sannan baya zalumci baya barin zalumci ya ɗore adoron duniya, duk yadda ki/ka kai da cin nasara koda abun alkhairi ne ka tuna watarana fa sai ka faɗi balantana sharri, tsubbu shirka, yau dai ƙarshen tika tika tikkk, asirin Karima ya gama karyewa, komai ya fashe.
Abun kuwa da ya faru shine.
Bayan ta fito daga gidanta taje ta kawai wanda zai samo mata abubuwan da YANKA WUƘA ya sakata ta samo, ta dawo gida tana zaman jiransa.
Bayan fitarsa babban al'amari ya faru da shi, wato yana kan kashin yana waya da wata hatsabibiyar karuwa wacce ya sakata ta samo masa dukkan abinda aka lissafa, an kuma yi nasarann samowa kasancewar uwarta babbar hatsabibiyar boka ce.
sai me zai faru....?

Babbar mota tabi ta kansa tayi masa raga-raga da shi ƙwaƙwalwan sanya awaje aka tattara yana dab da isa gidan matar hatsarin ya afku.
Hajiya Karima shiru-shiru ba labari hankalin ta yayi bala'in tashi ga tana kiran wayansa bata samu, ta shiga tashin hankali ga wa'adin da YANKA WUƘA ya bata awannin sun ciki, dole ta sake satan hanya ta tafi neman Qaya wanda ta iske mugun labarin kaɗan ya rage zuciyar Karima bata buga ba, da kuka ta dawo gida ta shige bedroom ɗinta ta kulle kanta baki ɗaya a hargitse take, ta kira YANKA WUƘA tana kuka tace.
"Ya zanyi Qaya ya mutu wa zai samomin abubuwan nan ayau YANKAN WUƘA kayi wani abun tun kashina bai bushe ba,.ga asaraka miliyan ɗaya da nayi."

Toh adaidia wannan lokacin ne Usman yaga Zainabu.
YANKAN WUƘA ya kece da dariya yace.
"Aikin gama ya gama ayanzun ba abinda zan iya mintina ƙalilan suka rage KASUBU ASAKA yabar jikin Mustapha idan kinada dama ki hanzarta kizo yanzu nan zanyi iya ƙoƙarina na dakatar da shi da maniyin jikinki..."
Cikin rawar jiki ta miƙe tace.
"Na amince kayi komai idan dai komai bazai buɗeba natsani Zainabu bazan taɓa bari ta dawo rayuwar Mustapha ba."
Ta faɗa tana katse wayar a gaggauce ta shirya ta warci makullin mota ta fice daga gidan lokacin Mustapha yana wanka tafiya Juma'a.

Yana fitowa kaya kawai ya zura yana saka hula cikin ikon Allah Usman ya kirasa yana ɗagawa yaji labarin da sanya kusa bugawar numfashinsa.
Jiri ya fara ɗibarsa, kasan ya shiga juyawa ya dafe kansa yana kiran sunan ALLAH.
Atake jikinsa ya ɗauki wani irin duhu wani baƙin hayaki ya fara fitowa daga sassan jikinsa, kafin ya yanke jiki ya faɗi wata irin halitta mai girman gaske wacce batada gaban kwatance Ta fita daga jikinsa tana wani irin ihu atake ta rikiɗe ta zama wani irin baƙin maciji mai girman gaske ta sulala ta window ta fice.
Yayin da Dad Mustapha yayi wata irin Zabura yana kiran.
"Zainab! Kina ina ya ciwon kan naki...."
Rahma Ladingo Omu Farisah ce.
Asha weekend lafiya.😍


*YI WA KAI!*


*Free Novel*

_#MatarɗanAlhaji🫣_
_November 27/11/2022_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*69&70*


Karo sukaci da Nadiya wadda ta fito daga bedroom ɗinta aguje, jin yadda mahaifinta yake kiran Zainab iya ƙarfinsa.
Riƙe shi tayi tana kallonsa cike da mamaki, tace.
"Dad! Ina kaga Umma Zainab ɗin? Ina take? Wlh nima kwana biyu tana raina kawai dan Mom bata son maganarta ne yasa na riƙe abun araina."
Mustapha ya ƙura ma ƴarsa idanu cike da mamaki ƙirjinsa na matsanaicin bugawa, yace.
"Nadiya! Ban gane ba kwana biyu tana ranki? Ina Zainab ɗin ta tafi ban saniba? Ba kanta yake ciwo ba tace na barta ta huta daga shi ne ya faru ne? Wlh Ni duk na rasa gane kan lamarin, muje na ganta ko ta farka daga baccin."
Ya faɗa yana kama hannun Nadiyan ya nufi stairs da ita, sabida part ɗin Zainabu daban a ƙasa gate ɗinta daban, Amman tsabar ya gigice ne yake kiranta daga sama.
Nadiya ta riƙe hannayensa tana faɗin.
"Dad ban fa ganeba umma Zainab ta dawo gidan ne ko ya akayi ne kawai sam ban ganeba fa?"
Mustapha yace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kenan dai da gaske ne Usman da ya cemin ya ganta a Jigawa?"
Nadiya tace.
"Dad muje ƙasa mama bayani yadda zaka gane."
Bai musaba suka sauko ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge ta tsiyaya Masa a cup yasha, yana sauke numfashi yace.
"Nadiya! Ina jinki?"
Nadiya tace.
"Dad! Ka manta shekaru biyar da suka wuce, ranan bazan mata ba weekend ne mun taso daga makarantar islamiyya tin daga gate na hango kana dukan Ummu Zainab, tare da faɗin ka saketa saki uku ka tsaneta, tana kuka tana baka haƙuri da bebanci amman ka rufe idanu kaci mutuncinta, aranan ka saka aka kwashe mata kayanta a babbar mota da ita kanta kasa aka Kaita har Katsina, nida Yaya Usman har kuka mukayi muna baka haƙurin duniya kaƙi, kace zaka tsine mana, ni lokacin inada ƙarancin shekaru amman nayi tunanin ko dai baka cikin hayyacin ka, na jima ina kukan rashin umma Zainab, aɓoye, sbd tsoron yadda muka ga ka rikice lokaci ɗaya, har Mom bata yadda ta shiga magana ba saboda yadda kamana mummunan kashedi akan duk wanda ya maka mgnar Zainab zai ga irin mummunan hukuncin da zaka ɗauka akan mu. Amma yanzu Dad ka nuna baka san ko mai ba me yake faruwa ne?"
Mustapha ya dafe ƙirjinsa yana faɗin.
"Ni Nadiya nayima Zainab haka? Tsawon shekaru biyar kamar wanda nayi losing memory ace na rayu ba Zainab tsawon shekaru haka ban saniba?"
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fi musibatihi wakhlifni khairn minha. Kina nufin Zainab shekaru biyar bama tare? Kira min mamarki yi sauri."
Ya faɗa yana miƙewa tsaye zufa ta gama wanke masa fuska ya fara kai komo.
Nadiya ta nufi upstairs da saurinta.
Ya kasa haƙurin jiransu ya fice a hargitse, ya nufi part ɗin Zainab ɗin.
Yana zuwa yaga ƙofar arufe gate ɗin yayi ƙura sosai alamar an jima ba mutum da yake shiga cikinsa.
Juyawa yay kamar wani zararre ya nufi wajan Baba Halilu mai gadi wanda aƙalla shekarun su kusan 17 yana musu aikin gadi.
Ko sallama bai masaba ya tsaya kansa yana faɗin.
"Baba Halilu don Allah dan darajar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam, me ka sani akan abinda ya haɗa mu da Zainabu matata, yanzu ƴata take ban labari wai na saketa saki uku tsawon shekara biyar, shin da gaske ne? Idan da gaske ya akayi haka ta faru? Nayi ciwon haukane na tsawon shekarun biyar ko nayi losing memory ne duk ban saniba? Dan dai Ni wallahi tallahi ban saki matata ba ina sonta ina ƙaunarta, idan dai wani ta aura sai naja shari'i da shi matata ta dawo hannuna wlh ko amafarki ban taɓa jin son nayi mata wasan saki ba..."
Baba Halilu ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil la haula wala Quwata illah billah! Alhaji kaine yau da bakinak kake cewa baka saki Hajiya ba? Bayan anan har Ni kamin barazanar korata randa kaci mata mutunci ka korata garinsu da kayanta cikin mota."
Dad Mustapha yace.
"Na rantse da wanda rayuwata take hannunsa bansan nayiba Ni ban saki matata ba, bari amman zanyi maganin komai ayau, ba ance tana Jigawa Ba, ɗan kuma yana can..."
Ya faɗa agigice yana juya cikin gidan.
A ƙofar falon suka gamu da Nadiya tana riƙo hannunsa tace.
"Dad ka nutsu mana dan Allah kaje sallar juma'a ka dawo na dabu Mom bata nan inaga ta fita fa!"
"Yi sauri jeki ɗakina ɗauko min waya da hula ki sameni mota, zaki rakani Jigawa bayan nayi sallar juma'a idan yaso ke ko ahanya ne zakiyi sallan."
Nadiya tace.
"Tom Dad Amman direba zai kaimu yadda kake ɗin nan bazaka iya driving ba!"
"Ok naji je ina mota ki sameni."
Ba musu taje ta ɗauko abinda ya aiketa ta canza kaya Abaya red da mayafinta da wayanta bata yarda ta kira Mom tabi mahaifiyata suka tafiyarsu...

Ɓangaren Karima tana isa wajan Boka YANKAN WUƘA, daman yayi ƙoƙarin sallamar baƙinsa yana jiranta.
Wani baƙin bokane ƙaton gaske mai ƙaton tumbi, yanada wargajejan baki, idanunsa jajir kamar gauta. Kana kallon fuskarsa kasan ba imani ba tsoron Allah.
Tana zama hankalinta atashe tace masa.
"Toh YANKAN WUƘA kayi sauri ayi me yuwa kafin ƙaryata ta ƙare."

Wani yawun sha'awarta da ya jima yana addabar sa ya haɗiye yace.
"Yawwa dole sai kin cire kayan ki baki ɗaya, kin kwanta ki ɗaga ƙafafunki sama, ki meƙe hannayen ki, ki rufe idanun ki, zanyi aikin ina daga nan duk abinda kikaji agabanki karki kuskura ki buɗe idanun ki ko kiyi magana, ki jure duk abinda kikaji, nan buƙata zata biya idan kikayi kuskuren magana ko buɗe idanunki toh babu ruwana buƙata bazata biya ba, kinga kuma lokaci ya ƙure ya kika gani zaki jure da abinda zai farun ko abari aljanin jikin Mustapha ya fita, ayau yaga Zainabu..?"
Cikin sauri ta katseshi a harzuke tana faɗin.
"A'a bana buƙata ayi komeye idan dai buƙata zata biya, ranan biyan buƙata rai bakin komai yake ba..."
Ta ƙarashe maganan tana miƙewa tsaye, Wa'iyazubillah.
Nan take tayi duk abinda yace ta kwanta saman tabarma ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar sabida ƙibarta ga rushe shan cikinta nan, ta rufe idanunta.

YANKAN WUƘA, har wani irin yawu ya haɗe, jikinsa na rawa ya miƙe yaje ya rufo ƙofar gidan ya dawo ya rufe ɗakin, ya duƙa gabanta kai tsaye sanya hannunsa tsakanin ƙafafunta yana shafawa, zuwa can ƙasanta ta ɗan zabura amma ba daman buɗe idanunta.
Ƙaton cikinta da zubabban ƙirjinta ya shiga shafawa yana sauke numfashi, jikinsa har rawa yake ya koma ƙasanta ya tura kansa ya shiga zuƙar.....
Kafin wani lokaci YANKAN WUƘA ya haye saman Karima yana alfasha da ita iya iyawansa yake nemanta ya susuce aiki kawai yake ba ƙaƙƙautawa.
Karima iya tashin hankali ta shiga tashin hankali duk abunta nan bata taɓa zina da kowaba, amman yau abun yazo mata abazata ga shi tana son biyan buƙatarta tanajin tana gani YANKAN WUƘA ya dinga dira samanta harda ihunsa yana faɗa mata shekarun da ya kwashe yana sha'awarta.
Sai da yayi awa ɗaya kanta cur kafin ya juye mata masifar sa cikin marata ya miƙe.

Karima ta maida kayan jikinta da ƙyar cikin jigatuwa wanda cinyoyinta ma azabar zafi suke bare can manhajar ba'a magana.
Kallonsa tai cikin wuyar duniya tace.
"Fatan komai yanzu zai tafi daidai?"
YANKAN WUƘA yana washe baki yace.
"Wannan haka yake jeki abunki ki jira kigani me zai faru."
Kai ta jinjina tana ɗingisa ƙafafunta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice...
Wata irin dariya YANKAN WUƘA yayi yana faɗin.
"Banida yadda zan miki ayanzun kam bakin tika-tika-tikkk."

*Dutse*

Ƙarfe 1 Mamy ta tattara suka taho gida, Khairy dai tayi wani luƙus da ita sai lumshe-lumshen idanunta take, Mamy tace da Suhailat ta rabu da ita wani lokacin haka take idan batada lafiya.

Bayan taje ta watsa ruwa ta saka riga doguwa marar nauyi, ta saka Laraba ta gyara mata kayan miya ta ɗora musu girki.
Khairy kuwa taja Suhailat suka haye sama yanzu ma ɗakin Mamy taje tai wanka ta saka Suhailat taje ɗakinta ta zaɓo mata abinda zata saka...

Bayan sallar juma'a Shattima sai da suka bi liman can gidansa da Usman, Shattiman yama Liman bayanin duk halin da ake ciki da zuwan da zasu wajan Zainabu bayan la'asar, yace idan sunje suzo da Zainabu yana son ganinta.

Zainabu tun bayan zauwarsu daga wajan taron, sai duk abinda Mustapha ya mata ya dawo mata sabo, ta kuma ga Shattima suna magana da shugaban tafiyarsu tanada tabbacin zasu dawo nemanta ne, bayan tayi sallar juma'a, ta tattara yanata-yanata ta sanya ƙaton hijab, tana rataye da jakarta, kamar wacce take neman wani sai da ta takaici idanun jama'a tayi wuff ta fice daga masaukin su, cikin ikon Allah bata haɗu da kowaba sai mai gadi shi kuma bai saka komai aransa ba tinda wani lokacin tana fita ƙofa siyan abu.
Kai tsaye tana fita ta samu me adaidata sahu, bayan ta shiga ta zauna ta ciro paper da biro ta rubuta masa.

"Tasha motar da ƴan Katsina zaka kaini."

Ta beƙa masa.
"Ok Hajiya ba damuwa amman yanzun kamar waje ya ƙura miki tinda hanyar taku akwai haɗari tafiyar dare."
Kai ta girgiza ta masa kwatance da hannu.
"Allah yana tare da bayinsa masu gaskiya, kuma koda wani abun ya sameni toh daman can Ƙaddara ta ce."

Duk bai wani ganeba ya fahimci dai bazata fasa ba, ya jinjina kai kamar ya gane bai ce uffan ba yaja adaidatan yana tafiya yace.
"Ɗari biyar zaki bani akwai nisa sosai wajan."
Jakarta ta buɗe ƴan kuɗaɗen da ake basu, ta zaro ɗari biyar ta beƙa masa ya amshe...
Cikin ikon Allah suna zuwa tashar motar Katsina sauran mutum biyu tace zata biya na mutum ɗayan.
Kowa ya biya kuɗinsa, ita ta biya na mutum biyu, aka sallami kamashon direba yayi addu'a ya haye mota yaja suka tafi.
Wata irin ajiyar zuciya Zainabu ta sauke lokacin da taga motarsu ta ɗauki hanyar Katsina ɗoɗar...


Zaune suke akan dining suna lunch, Khairy sanye da riga da skirt ƴan kanti yellow colour, masu taushi sun lafe ajikinta MASHA ALLAH, ba ƙaramin kyau suka ma lafiyayyen jikinta ba.
Kanta sanye wula pink sai tayi kyau kamar wata ƴar babu, sai turo baki gaba take tana juya spoon ɗin hannunta.
Yayin da Suhailat da Mamy suke kwasar daddaɗan girkin da Mamy tai musu sharf-sharf ba ɓata lokaci, na jalof ɗin macaroni taji kayan lambu da kayan ƙamshi, taji attarigu da niƙaƙiyar kaza, ba dai daɗi ba, Suhailat sai zuba santi take yi.
Mamy tayi murmushi tana kai spoon bakinta tace.
"Kai Suhailat koda yunwa kikeji shiyasa kikaji girkin ya miki daɗi.
Ta faɗa tana kallon Khairy, wadda take kwakwaɓe fuska.

"Baby! Kici mana ko rigimar ce? Naga kan naki da sauƙi, zo naji kan."
Khairy ta narke tana rau-rau da idanunta, ta miƙe ta dawo kusan Mamy taja kujera ta zauna tana kwantar da kanta ƙirjin Mamy tana lumshe idanunta.
Mamy ta taɓa kanta da wuyanta, cikin kulawa tace.
"Baby! Bakida zazzaɓin ba ciwon kan kasala ne koh?"
Khairy ta ɗaga kanta alamar.
"Eh"
Suhailat ta sheƙe da dariya tana faɗin.
"Mamy! Babyn nan taku rigima dai takeji wlh."
Mamy tace.
"Toh daure kici abincin kaɗan kije ki kwanta Ok? Ke kuma Suhailat Bama son haka fa tau, maza ci abincinki rabu da ita."
Khairy ta ɗaga kanta tana zama sosai ta janyo plate ɗin ta fara ci.

Shattima da shigowarsa falon kenan kai tsaye ya nufi kan dining dan zatonsa Mamy da Khairyln duk sunyi bacci, dan mafi yawa irin lokacin nan da sunyi sallah bacci sukeyi sai la'asar suke tashi.
Anutse yake takawa cikin takunsa na girma da kamewa zaka rantse wani basarake ne.
Da sauri yaja baya ganinsu akan dining ba komai yake ji ba sai Khairy gudun karta ɓullo masa ruwa gaban Mamy. dan ya hango yadda take tauna abincin bakinta a shagwaɓe tana rau-rau da idanunta. Mamy na aikin lallashi Suhailat na musu dariya.

Mamy ta shaƙo fitinannan ƙamshinsa wanda ya mamaye ƙofofin hancinta ta ɗago kanta, karaf suka haɗa idanu yana shirin juyawa.
Da yatsar shi ya mata nuna shiiit! Kar tayi magana ya sulale ya juya.
Mamy ta ƙunshe dariyata, tana miƙewa tace.
"Baby!
Bari na ɗauko miki fura Rufaida zaki sha koh?"
Khairy ta miƙe tana faɗin.
"ALLAH Mamy ni bana son cin komai bari naje na kwanta."
Ta faɗa tana shaƙo ƙamshin Dadyn nata, da sauri ta shiga waige-waige, tana buɗe ƙofofin hancinta tana shaƙar ƙamshinsa da ya gauraye wajan.
Mamy tace.
"Toh zauna Suhailat ta gama sai ku haye stairs ɗin tare ya zaki barta ita ɗaya."
Zama tayi tana turo baki gaba, batace komai ba, sabida ƙamshin Dadynta ya gama ƙarasa saka mata kasalan kewarsa da takeji har ɓargon ƙashinta, ayanzu batajin idan ta gansa zata barsa bata masa rigima ba ya lallasheta.

Mamy da sauri tabar wajan, tana murmushi Khairy baki ɗaya ta gama shagwaɓe wa yanzun, tun bayan da suka mata aure da Abdoul rigimanta ta ƙuru, duk da daman gwanace.

Shattima ko tuntuni ya haye upstairs yasan Mamy zata isko shi ne.

Falonsa ta murɗa ƙofar ta shigo baya nan, ta wuce bedroom.
Yana zare gayan jikinsa.
Da sassarfa ta ƙaraso wajansa tana taimaka masa cire kayan, ƙaramin towel ta ɗaura masa iya ƙugunsa ta shige masa tana lefe ajikinsa, ahankali can ƙasa tace.
"Mi Amor! Sannu da zuwa, ina ka tsaya naga ka makara dawowa gida?"
Rankwafo yay ya sumbaci ƙirjinta yana riko ƙugunta ya sake ƙasa da kansa ya lashi gefen bakinta wajan da romon macaroni ya taɓa, ya raɗa mata akunnenta, ƙasa² cikin kulawa anutse.
"Mun biya gidanmu ne wajan Baffa yana gaisheki, bari nayi wanka, ki haɗa mana abinci zamuji da baƙo yanzu Ok? Amman ki janye Khairy taje ta kwanta bana son ta gansa yanzu ta kama rigima, Usman ne...."
Nan ya bata labarin komai.
Mamy tai murmushi tana shafa yalwataccan gashin ƙirjinsa ta sumbata tace.
"Ok Mi Amor yanzu kuwa bari naje na turota ta kwanta, amman.m nayi farin cikin ganin Zainabu nan kusa wlh."

Bakinta ya sumbata ya furta.
"Thank you Sweetheart matar ƙwarai."
Wani bangare na jikinsa ta shafo tana kashe masa idanu, ta janye da sassarfa ta nufi hanyar falonsa.
Shattima ya bita da malalacin kallo yana sakin fitinannan numfashin tare da furzar da iska me ɗumi, ya nufi bathroom.

Mamy tana saukowa taga su Khairy a falo suna kallon wani Film na ƴan Ghana atashar Afrika magic.
Mamy ta tsaya tana kallon Khairy tace.
"Baby kije mana ki kwanta ki huta, ko kuje can saman sai kuyi kallon a ɗakinki ba!"
Khairy ta kalli Mamy tana kwaɓe fuska tama yi kwanciyarta tana miƙe ƙafafuwanta murya narke tace.
"Sweet Mamy ni ai baccin ne bana so yanzu kalla fa ƙarfe uku ta kusa, zanyi mura, Ni dai kallo zanyi."
Mamy ta matso ta sunkuya tana kamo tattausan hannayenta tace.
"Ni Kum Mamynki nace kuje can sama kuyi kallon ba, nan baƙi zanyi ko ban isaba da ke?"

Khairy da sauri ta rufe ma Mamy baki da hannunta tana girgiza kanta, ashagwaɓe tace.
"Toh Mamy kiyi haƙuri zanje amman ɗakinki ɗakina wlh tsoro nakeji ƙadangare nagani."
Mamy tace.
"Oh! Shine kikeje kika hargitse min toilet koh? Ok jeki can ɗin idan Dadynki ya dawo zai nemosa ya kashe shi."
Kai Khairy ta jinjina ta miƙe suka tafi itada Suhailat.

Mamy ta kira Laraba ta kwashe kayan da suka ɓata, wajan cin abinci ta goge table ɗin ,ta shiga kitchen da kanta ta sake sarrafa musu abu mai sauƙi cikin 20 minutes, Laraba ta jera, ita kuma ta koma wajan Shattima.
Ya shirya Tsaf cikin fararen kaya na shan iska na zaman gida MASHA ALLAH yayi bala'in kyau, sai fitinannan ƙamshi yake tashi ajikinsa kansa mai yalwar suma tasha gyara sai sheƙi take, furfuran da bata wuce guda goma ba akansa ta saka gashin ya bada wani irin kyau.
Zaune ta isko shi yana waya.
Ta zauna kusansa tana faɗin.
"Wannan kyan fa Mi Amor!? An shirya komai sai ka miƙe. Ni kam bari na shige bedroom ɗin ka na ɗan mike kaɗan kafin la'asar."
Katse kiran yay yana kallonta yace.
"Na gode Sweetheart."
Ya faɗa yana miƙewa tsaye ya miƙar da ita yace.
"Oya je ki huta."
Bedroom ɗinsa ta shige ta rufo ƙofar, shi kuma ya nufi hanyar fita, daga falonsa yana danna lambar Usman.

Khairy suna cikin kallon ta miƙe tace.
"Besty zaki sha fura na kawo miki ta Rufaida? kinsan dai akwai daɗi."
Suhailat tace.
"ALLAH naci girkin Mamy dayawa kamar zanyi amai nakeji sai anjima idan munyi sallar la'asar zan sha, ke kam je ki kawo Kisha tinda bakici wani abun kirki ba. Sai kizo muyi fita da kika ce zamuyi inzo"
Khairy a sanyaye tace.
"Tom bari nazo sirri ne zamuyi ɗagani sai ke."
Ta faɗa tana ficewarta dan sauka ƙasa ta dauko furan a fridge ɗin su na kayen lashe_lashe.

Ya buɗe ƙofar ya fito yana takawa cikin nutsu, yana faɗin.
"Usman! Fito daga falon baƙin ka shigo muyi lunch falona ina jiranka."
Ya faɗa yana katse wayan.
Ƙaran bude ƙofar Mamy yaji ya waiga da sauri.
Karaf idanunsu ya haɗe waje guda da Khairy, tuni ta kwaɓe fuska idanunta har sun fara tara ruwa.
Shattima aransa ya furta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."
Real Ladingo Omu Farisah


*YI WA KAI!*


*Free Novel*

_#MatarɗanAlhaji🫣_
_November 29/11/2022_

_*DEDICATED TO*_
_Yaganah Musa Bulama mai samari, alkhairin ALLAH ya kai miki har gadon baccinki, nagode Allah yasa na saka miki, fiye da yadda kika min.🙏🏼🥰_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*71&72*


Usman Shattima yana katse kiran da masa, ya fito daga lafiyayyan falon baƙin da aka sauke shi, a ƙofar falon suka haɗu da wanda zai gwada masa ɓangaren na Shattima.
Tafe suke a wayance, Usman yake ɗan waige-waigen sa, sosai yake more wa kallon yanayin tsarin gidan na ministan, komai ya haɗu ba ƙarya, ko ina franni ne masu kyau da tsari, da ƙayatarwa, shiru gidan ba wani hayaniya kamar ba jama'a.
Doguwar tafiya sukayi daga idan aka sauke shi zuwa asalin inda zai sada shi da falon na ministan.
Yana isowa jikin ƙofar kira ya shigo wayansa.
Ganin Dad Mustapha ya saka shi ɗagawa dole tare da sallama.
Daga can Mustapha yace.
"Usman mun san so Dutse yanzu kana ina? Wlh ayau idan banga Zainab ba, ta faɗa min matsayin aurena ba, zuciyata zata iya bugawa,

Please Login or Register in order to submit comment