Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutafi Ina ruwanki da sabgarsu zaki shiga? Kinga ki raba kanki da shiga irin wannan abun, mutafi don ALLAH."

Hararenta Khairy ta yi tace.

"Bazanje ba sai naji abinda yake tsakaninsu, da har ya iya dukanta da tsohon ciki. Ke faɗa min waye shi awajanki?"

Cikin kukan munafurci tace.
"Mijina ne auren dole akai mana da shi, kullun haka yake zalumtata, duka hantara kyara, yanzu mahaifiyata ce batada lafiya aka kirani, tana asibiti ya hanani tafiya, shi ne na fito zuwa asibitin shine ya biyo yana dukana."
Khairy tace.
"Kaji kunya wallahi."
Dariya ya yi yace.
"Kije na sakeki saki ɗaya sai kibita gidansu daga asibitin, gake ga itanan mai tausayin naki."
Ya faɗa yana barin wajan, bayan yamata magana da idanu, ta mayar masa, Tsaf akan fuskarta samun Nadiya, daman sam bata yarda dasu ba, har cikin zuciyarta.

Khairy baƙin ciki ya sakata gaza magana, ta kama hannunta tace.
"Ke yanzu dan rashin sanin ciwon kai kuka kike dan wannan da baisan darajar mutum ba, ya sakeki? Muje na kaiki asibitin."
Hawayen fuskarta ta goge tabi Khairy har mota, side ɗin baya ta buɗe mata ta shiga, Nadiya ta shiga wajan zamanta, Khairy tana jan tsaki tama motar key tana faɗin.
"Wane asibitin zamuje?"
_"Khairy clinic and maternity."_
Da sauri Khairy ta waigo tana kallonta, cike da mamaki tace.
"Toh me ya kawoki nan wajan airport keda zakije can?"
Cikin inda-inda tace.
"Ai nan wajan gidana yake kuma can ba ƙarfinmu bane, yasa aka kaita hospital ɗin, maƙwabcinmu ne mai hali shine ya taimaka ya kaita yace zai biya komai na magani da za'a mata."
Khairy tace.
"Ok ba damuwa ai asibitinmu ne ba'a tsawwala, Allah bata lafiya."
Nadiya tace.
"Auntie kina nufi mun fasa zuwa airport ɗin sai mu kaita asibitin?"
Khairy tana driving tace.
"Yes Nadi, ai su Dadynah basu isoba ƙilama ko daga Abuja basu taso ba, ciwon mace na mace ne fa Nadiya! Kiga yadda wulaƙantata abakin titi, gata da tsohon ciki ajikinta. Kina nufin idan ke ɗaya ne zaki tafi ki barta bazaki taimaka mata ba? Ga mahaifiyarta ba lafiya, tana burin su haɗu?"

Nadiya ta kasa magana batasan yadda zata fahimtar da Khairy matar nan munafuka ce ba, dole taja bakinta ta yi gumm.
Se de tana ankare da matar ta madubi kamar yanayinta ya canza sosai.
Sai da sukayi tafiya mai ɗan nisa, Kausar cikin wani irin rauni tace.
"Baiwar ALLAH na gode haƙiƙa irinku basuda yawa aduniya, wallahi ban taɓa jin tsoron Allah ko tausawa wanda zan cutar ba ayau sai ke, duk da ban taɓa cutar da wani ba, ta irin wannan hanyar, don ALLAH kiban motar na kuɓutar dake."

Khairy ta taka burki da wani irin sauri tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ki cutar dani kuma? Da nayi miki me baiwar ALLAH?"
Ta ƙarashe tambayar tana gangarawa bakin titi ta yi parking tana waigo ta kalleta tace.
"Ina jinki baiwar ALLAH?"
Matar ta ciro abun da ta yi cikin ƙaryan da shi, tana faɗin.
"Kinga na farko yanzu bamuda lokacin bayani anan idan kin yarda wuce gidanku kai tsaye na miki bayani, can akwai tsaron da ba wanda zai iya taɓa Ni Ko ya taɓaki, kinga nan tsayuwarmu haɗarine ki fasa zuwa airport ɗin."
Khairy jikinta har rawa yake tama motar key tabar wajan, tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ni kuwa me na muku har haka baiwar ALLAH? Yanzu tsakaninki da Allah bazaki cutar sani ba? Kuma dama zuwa asibitin ƙarya ne ba gaskiya ba?"
"Humm wlh da inada niyar cutar dake bazan tsaya dogon bayani ba, da tuntuni na shaƙa miki wannan abun an wuce wajan. Eh zuwa asibitin ƙarya nake."
Ta faɗa tana nuna mata wata ƴar kwalba, a hannunta.
Khairy ta jinjina kanta, tsorone fal azuciyarta, bata sake magana ba, tama motar key ta fizgeta aguje tabar wajan, tana faɗin.
"My Nadi kiramin Dadynah ko Mamy muga ko za'a samesu."
Nadiya tana dialing number Mamy tace.
"Auntie tun ɗazu abunda nake so Ankara dake kenan, kika gaza ganewa, ALLAH ne ya dubu zuciyarki ya tseratar dake."
Khairy tace.
"Tunda kika ce ALLAH ai an wuce wajan, ALLAH ya ƙara tsaremu ya shiga tsakanin nagari da mugu Amin."

Kira uku Nadiya tama Mamy bata shiga ta kira Shattima, cikin Sa'a ta shiga, ta kalli Khairy tana faɗin.
"Auntie lambar Dady ta shiga."
Cikin farin ciki ta beƙa hannunta tace.
"Ban wayan."
Nadiya ta bata wayan, daidai lokacin kiran ya katse.
Khairy tace.
"Wayyo ALLAH Nah! Dadynah ka ɗauka mana."
Ta faɗa tana sake kiransa.
Bugu ɗaya ya ɗaga.
Cikin farin ciki tace.
"Alhamdulillah! Assalamu alaikum Dadynah! Barka da zuwa kuna ina don ALLAH? Ina Mamynah?"

Ta ƙarshe maganan cike da shagwaɓa.
Daga can Abuja Shattima da suke airport yana zaune, Mamy kusansa tare da sauran abokan tafiyarsu.
Shattima ya yi wani irin kyau har wani ɗan cikowa yay kaɗan kamar ba azumi suka idar ba.
Sanye yake da wata narkekiyar Shadda fara ƙal mai shegen tsada, ɗinkin na manyan mutane yasha uban zubin zare blue, kansa sanye da hula fara irin ƙaramar nan ta Saudiya Wada taba lallausan gashinsa bayyana gefe, Takalmi rufaffe ne a ƙafafunsa, masu tsadar gaske.
Anutse ya amsa sallamar yana sakin murmushin farin cikin jin muryata, yace.
"He! Baby kina lfy koh? Ya Gumel?"
Cikin farin ciki ta maƙala wayan, kunnenta da kafaɗarta, ta sanya hannun guda tana karya kwana tace.
"Muahhhh! Dadynah i miss You, Alhamdulillah! muna lfy kaɗan, gari ba Dady da Mamy ba wani dadi wlh.
Dady ga ni ina Dutse, har na fito tarbanku, ina Mamynah? Ka bani ita."
Shattima kansa ya girgiza baice komai ba, yana mannawa Mamy wayan akunnenta, anutse ya furta.
"Baby ce
"
Mamy ta riƙe wayan tana murmushi tace.
"Hello Baby kina lafiya?"
Khairy tace.
"Ni Mamy yaushe ma zanyi lafiya bana ganinku, amma Alhamdulillah zance, Mamy kuna ina yanzun?"

Mamy tace.
"Gamu airport Abuja anjima kaɗan zamu tashi."
"Cikin murna tace.
"Tom Allah kawoku lafiya, bye."
Ta faɗa ta katse kiran tana beƙa wa Nadiya wayan ta maida hankalinta akan driving.
Kira kusan goma Azizah tama Kausar taƙi ɗauka, dan taji har zuciyarta bazata iya cutar da Khairy ba.

Azizah da Tasi'u da suke bin bayan Khairy a mota, hankalinsu ya tashi ganin motar Khairy ta ɗauki hanyar Commissioner's Quarters.
Azizah ta sake kiranta tana wani irin zagi, tace.
"Tasi'u! Ban fa ganeba wannan ƴar jakar uban ba fa, ina kiranta bata ɗauka."
Tasi'u yace.
"Kinga yanzu kuma an shigo tsakiyar jama'a ba yadda za'ayi mu tari gabansu, hankalina ya tashi sosai ban gane komai yanzu."
Azizah tsabar baƙin ciki kasa cewa uffan tayi, tana biye dasu taga iya gudun ruwansu.
Khairy tana shigowa layinsu Azizah ta juya da mota, tana faɗin.
"Na rantse ALLAH ba mai hanani ɓatar da Kausar matuƙar asirinmu take shirin tonawa sbd kwaɗayin abun duniya, sai na shayar da ita mamaki."
Tasi'u yace.
"Anya kuwa? Nafi tunanin akwai tuggun da take shiryawa."
Azizah sabida ɓacin rai bata sake magana ba, gudu kawai take shararawa ta nufi gidan da zasu kai Khairy dan jiran Kausar suga iya gudun ruwanta...

Khairy tana shiga cikin hamshaqin gidan nasu, tama Kausar jagora zuwa falon baƙi.
Zaune suke Khairy ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana fuskantar Kausar, tace.
"Ina jinki suwa suka sakaki aikata hakan gareni Allah bai baki iko ba? Kinsan ayanzun idan Dady yasan haka har ke duk da baki aikata ba ba lallai ki tsiraba, za'a iya kamaki?"
Kausar ta yi murmushi tana girgiza kanta tace.

"Abun kiriki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake yi.
Amshi kiga wannan hoton ko kin santa."
Kausar ta faɗa tana beƙawa Khairy wayanta.
Khairy ta amsa wayan tana kallon screen ɗin wayan.
Idanunta ta zaro tana faɗin.
"Azizah budurwa marigayi Yah Abdoul?
Ina kika santa? Ita ce ta turo kimin wani abun? Me haɗina da ayanzun tunda wanda take dominsa ya barmana duniyar?"
Kausar tace.
"Ki saurareni da kyau, siyena aka haɗa baki dani akamar dai yadda kika gani munyi da wannan gayen. Da kin shiga hannunsu yau wannan gayen zai farmaki ne yadda zuciyar Minister zata tarwatse, daga baya Salim zai zo wajan ya sacek, bayan ta ɗauki fansar Abdoul sabida tana zargin wanda ya aureki shi ya kashesa..."
Labari Tsaf tabata yadda suka tsara komai akanta.
Khairy ta fashe da kuka tace.
"Kawai dan baƙantawa Dadyna za'a saceni aje ayi wani abun dani bayan inada aure? Har zargin Dadynah zai iya kissa ake tsabar ɗaukan alhakinsa Allah ya isa tsakanina da Azizah da Salim n'a tsanesu tsana mafi muni. Toh ke dalilinki na cetona?"

"Wlh haka kawai naji kin kwantamin azuciyata sabida kyakkyawar zuciyarki, kinyi niyar taimaka min da zuciya ɗaya, duk da baki saniba kinyi kasadar ɗaukana, bayan kinci mutuncin wanda yaci nawa mutuncin."
Nadiya da har yanzu Kausar bata kwanta mata ba, tace.

"Hummm ta nan muka faro, kuturu ya ga mai ƙyasbi."

Kausar tace.
"Hummm akunkumi, ya fi ƙarfin bakin kaza.
ALLAH ya sani naji har zuciyata bana son acutar dake ne, yanzu haka wannan ceton naki da nayi Allah kaɗai yasan me zai biyo baya, bazu barni ba, Ni kuma wlh ta ɓangarena bazan cutar dake ba."

Khairy ta numfasa tana haɗe hannayenta tana lanƙwasa yatsunta, tace.
"Ok har yanzu Azizah na bibiyata koh? Good hakan ya yi. Ngd baiwar ALLAH kije wlh bazan fasa zuwa airport tarbo su Dadynah ba, daman can idan kinga sun kamani toh ƙaddarata tazo ahaka."
Ta ƙarshe tana miƙewa tsaye tana gyara lafayar jikinta.
Kausar tace.
"Karki je koda zaku tafi ki tafi da securities, kuma Ni kaina yanzun fitana ba tare da an mana tsakani ba dasu a police station babban haɗarine."
Khairy ta jinjina kanta tace.
"Ok shi kenan bari na kira Abba Aminu na masa bayani, sbd agaskiya bana son abinda zai tayarwa da iyayena hankali daga saukarsu a ƙasa shi nasan za'ayi komai a gama bazai bari Dady da Mamy suji ba."
Kausar ta jinjina kanta, tana haɗiye yawun tsoron haɗuwarta dasu Azizah.

Zama ta yi tana amsar wayanta wajan Nadiya, ta shiga ma'adar lambobi ta dannawa lambar Commissioner Aminu.
Bugu ɗaya biyu ya ɗaga kafin ya yi magana har ta yi masa sallama tana gaishesa cikin girmamawa.
Ya amsa yana faɗin.
"Daughter! Ya Gumel ɗin fatan kowa lafiya?"

"Alhamdulillah! Abba ai tun safe na shigo, ina nan am Abba! Daman wata matsalace ta samu yanzu, kuma bana son su Dady su sani shine nace bari na kiraku na shaida muku nasan zakuyi maganin abun."
Abba Aminu ya gyara zamansa akan kujeran office ɗin sa yace.
"Subahanallahi daughter toh Ina jinki."
"Abba daman muna kan hanyarmu ta zuwa airport ne...."
Tsaf ta zayyane masa komai da ya faru da abinda Kausar ta faɗa mata.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Daughter lallai kin auna arziƙi, yanzu kuna tare da ita yarinyar?"
Khairy tace.
"Eh Abba gata tace tsoro takeji bazata iya tafiya sai an shiga tsakaninsu da ita zasu iya neman rayuwarta."

"Ok bani ita zamuyi magana."

Khairy ta beƙama Kausar wayan, ta amsa hannunta har rawa yake.
Gaishesa ta yi ya amsa yace.
"Zaki iya kai ƴan sanda inda za'a samu abokan aikin naki?"
Kausar ta fara kuka tace.
"Na rantse da Allah ban saba aikin nan ba, ko motama na koya ne lokacin ina makaranta wajan ƙawata Sajida, ita tace bakiyi mota sabida halin rayuwa ba, wai sai Kanada halin siyaba akwai juyin da za'ayi watarana mutum na naiman taimakonsa ya kasance kaine, alokacin kusansa yake buƙatar taimakonka idan baka iyaba zakaji baƙin ciki sosai.
Ajiyama ina cikin mawuyacin haline, munyi rashin mahaifiyarmu kusan shekara ɗaya,ta rasu inada ƙanne uku mahaifinmu bashida lafiyar kirki baya iya fita nemo mana abincin da zamuci nice nake faɗi tashin neman abinda zamuci, kwana biyu komai ya tsaya min daman wake da shinkafa nake na siyarwa, jiya na fita yawon neman aikatau na faɗa gidansu Azizah, tamin tayin abun nan da maƙuddan kuɗi kusan dubu ɗari da ashirin ban taɓa riƙe dubu goma shabiyar na kaina ba shiyasa na kwaɗaita da tayin nasu sai dai na kasa aiwatarwar na taimaketa."
Ta ƙarashe maganan cikin kuka.
Abba Aminu ya jinjina kansa yace.
"Allah ya miki Albarka kinyi ƙoƙari sosai, zaki iya kaisu inda za'a kamasu"?
"Eh nasani."
Abba Aminu yace.

"Alright ki jira zan turo yanzu ɗauke ku har Khairyn, bata wayan."

"Tom shi kenan."
Ta faɗa tana beƙawa Khairy wayan, kome yace mata oho tana ta amsawa da.
"Toh Abba sai sun zo."
Ta katse kiran tana jujjuya maganganun Kausar wato babu ta kusa sakata shiga wannan mummunan sana'ar?
Idanunta ta lumshe tana sauke numfashi.
Kamar bayan 30 minutes Abba Aminu ya kira Khairy yace su fito anzo ɗauka su, amman Can baya inda Shattima ko ya kunna cctv Camera bazai ga komai ba.
Khairy taji daɗi sosai, suka fito a ƙafafunsu suka fita, har security nayima Khairy ya zata fita aƙafa tace ba inda zataje.
Suna fitowa can bayan kuwa motoci gudu biyu, ɗaya ta ƴan sanda ɗaya kuma batasu ba ita Khairy da Nadiya suka shiga, yayin da Kausar ta shiga ta ƴan sanda suka bar wajan.
Kausar ta faɗa musu anguwan tana nuna musu, da hannun bayan sun shigo anguwan har sukazo ƙofar gidan.
Kausar ta fito tare da ƴan Sanda uku riƙe da bindigogi.


Mai rabon shan wahala sai yasha.🤣

Salim dai ta ritsa da shi, bayan zuwan su Azizah suna zaune ita da Tasi'u, suna jiran isowar Kausar, dan basu taɓa tunanin za'a ritsa dasu ba.
Kiran Salim ya shigo wayarta, tana ɗagawa yace.
"Daman dan naji ina muka kwana ne, kince bayan salla yanzu anyi an gama sai me?"
Azizah tace.
"Ai ga Ni akan aikin yanzu haka na tura a ƙwamuso min Khairy dan kama Minister cikin sauƙin."
Salim yace.
"Mutanan kirki kika aika wanda bazasu taɓa min lafiyarta ba koh?"
Azizah ta sheƙe da dariya tace.
"Kwantar da hankalinka macace ma."
Salim yace.
"Ok faɗa min inda kuke yanzun zanzo, muyi kaca-kaca da ɗan iska."

Azizah tana dariyar mugunta tace.
"Wai ka manta matarsace ta ina zaka mallaketa? Kuma kai yanzu kana son Shattima ya ganka anan Khairy ta ganga? Ai wasan zai ɓaci."
"Ba ruwanki faɗa min kiga yadda zan baki gudunmawa cikin burinki."
Azizah ta faɗa masa wajan tana dariyar mugunta, dan ta shiya komai akansa sai bayan sun gama cinma burunsu...
Salim bai jima da shigowa ba ƴan sandar suka iso.

Kausar ce ta ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar.
Azizah tace.
"Tasi'u! Je kaga ko shegiyar ce."
Baiyi magana ba ya miƙe ya fito.

Yana buɗe wa ya yi arba da DSP tare da yaransa biyu, da Kausar.
Juyawa aguje zai koma, DSP Labaran yace.
"Ka dakata! Ko na saka a harbeka."
Cak ya tsaya yana ɗaga hannunsa sama.
DSP Labaran yace da Kausar.
"Muje."

Azizah jin ƙaran taɓa ƙafa ta ɗago kanta, tayi arba da DSP tare yaransa mutum biyu, sai Kausar na bayansu.
Salim da Azizah suka zabura suna faɗin.
"Innalillahi."
Atare.
Azizah ta kalli Kausar tace.
"Ni zakici amana? Kinsan kuwa Ni wacece?"
Dsp Labaran yace.
"Ke wacece? Miƙa kanki Malama."
Salim ya ɗaga hannayensa yace.
"Na gode Allah da bana cikinsu."
Dsp yace.
"Ai yanzu gidan ubanka muka kama koh? Ku tisa ƙeyarsu gaba muje mota."

Baki ɗayansu aka tisa keyarsu zuwa mota, Salim yaso kawo musu tangarɗa suka buga masa bakin bindiga sai da ya suma, suka shaƙa masa ruwa suka kwashesa zuwa mota.

Khairy har suka isa police station ɗin su Abba Aminu kuka take da mamakin wai duk wannan mutanan suna son cutar da ita ne.
Zazzaune suke cikin office Commissioner Aminu, ya kalli Kausar yace.
"Ina son ki maimaita abinda kika faɗa min ta waya.
Kanta ƙasa ta faɗa masa komai.
Azizah tace.
"Ƙarya kike wlh, ina nasanki munafuka."
Tsawa DSP ya daka mata yace.
"An kira sunanki ne?"
Abba Aminu ya kalli Tasi'u yace.
"Muna son ka faɗa mana gaskiya kafin asaku ku faɗa ta ƙarfi."
Tasi'u yace.
"Ni fa bansan abinda kuke magana akai ba, wlh yarinyar nan munafuka ce."
Abba Aminu yace.
"Good ke Azizah zaki da kai Salim zamu iya jin dalilinku na son nakasa rayuwar Ummulkhairi?"
Azizah tace.
"Wlh sharri akemin ba haɗina da ita."
Salim yace.
"Wlh Abba amsar saƙo nazo ai Ni na fita daga harakarta tuntuni banida haɗi da ita."

Abba Aminu ya kalli Dsp yace.
"Wannan fa sai ka saka an tambaye su kuje."
Sara masa ya yi yace.
"An gama Sir."
Ƙeyarsu aka tisa gaba, zuwa ɗakin horo.
Abba Aminu ya kalli Kausar yace.
"Ki kiyaye rayuwarki da shiga irin wannan tarar aradu da kai, zaku tafi in Sha Allah azabar da za'a musu, bazasuyi kuskuren taɓa lafiyarki ba, za'a maidaki gida in Sha Allah kun daina kukan rashin cin abinci, Mahaifinki zai samu lafiya."
Ya faɗa yana kallon Khairy yace.
"Daughter ki kwantar da hamklinki Dadynki bazainjiba har muyi abinda ya dace, yanzu zakije airport ko gida zaki koma?"
Khairy tace.
"Zan tafi airport Abba, nace Abba zan sauke Kausar gidansu dan naga gidan inaso zan taimaka musu nima."
Abba Aminu ya jinjina kansa yace.
"Ok kuje arakaku ki nutsu kar Dadynki ya gano akwai matsala fa! Daga can sai ya kaiki airport koh?"
Kai ta jinjina tace.
"Ok Ngd Abba Allah ya ƙara girma."
"Ameen daughter."

Abba Aminu ya bada umarnin akai su Khairy, gidansu Kausar.
Sosai Khairy ta yi kuka ta tausayama Kausar, yadda suke rayuwa cikin wanga gida, tayi alƙawarin sai ta canza musu rayuwa, in Sha ALLAHU tasan Dady baida matsala zai mata duk abinda take so.
Khairy daga gidansu Kausar airport aka wuce dasu ita da Nadiya.
Acan suka isko Auntie Balaraba da Fauziyya ƙanwar Mamy, gefe Maleek da security gudu biyu.
Khairy tunda suka zo zaune take ta yi kalar tausayi, har Balaraba tana tambayarta.
"Babyn Dady yau lafiyarki kuwa bakya murnan ganin iyayan naki ne?"
Kai ta girgiza cikin sanyin murya tace.
"Ban jin daɗi ne."
Auntie Balaraba tace.
Ayyah sannu Baby."
Khairy batace komai ba, tana latsa wayanta.
*After 45 minutes*
Jirginsu Shattima ya sauka lafiya.

Khairy tunda taji saukar jiragin take ɗaukin, ganin Mamy da Dadynta.
Suna tsaitsaye wajan tarbar matafiya Khairy ta hango Mamy da Shattima kowane cikin shiga ta alfarma....

Real Ladingo Omu Farisah

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_


*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 28/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*97*

Yau kam Mamy da Shattima sun sha mamakin Khairy, da bata musu rigima ba. Cike da ladabi da nutsuwa ta tarbesu ta musu sannu da zuwa, ta kama hannayensu, suka isa wajansu Auntie Balaraba.
Balaraba da Fauziyya suka gaishesu, tare da musu sannu da zuwa.
Shattima cike da kulawa ya amsa musu, yana kallon Khairy wanda yanayinta ya nuna tana cikin damuwa ɓoyewa take.
Su Maleek suna gaishesu cikin girmamawa tare da musu sannu da zuwa.
Hannunsa ya beƙa musu sukayi musabaha, yana mai faɗaɗɗa fara'asa.
Bayan su Maleek sun kwashi kayansu sun zuba booth, suka fita daga airport, Khairy tana motar su Shattima gaba kusan Maleek.
Kai tsaye motar da abokan tafiyar su Shattima suke ciki, Lawan ya fara nufar Galadanci dan sauke maƙwabcin Liman kafin ya nufi gidajan sauran.
Fauziyya da Auntie Balaraba suna motar Balaraban sabida unguwansu ɗaya, layinsu ɗaya shiyasa take biya mata idan tafiya waje ta kama zasu haɗu, saboda ƴan uwan Mamy dana Shattima suna zumunci sosai.
Suna zuwa gida bayan Shattima ya amsa gaisuwar ma'aikatansa, yana shiga falon ya haye upstairs yabarsu nan falon.

Khairy ta maƙale Mamy.
Tsaye Mamy take tsakiyar ƙaton falon nasu, wanda yake fitar da azababban ƙamshi, ga sanyin A/C.
Khairy sosai ta maƙale Mamy tana mai cike da nuna farin cikin wanda bata nuna acan airport ba.
Su Fauziyya na musu dariya tace.
"Kai Khairy ki saki Mamynki mana ta zauna ta huta."
Khairy tace.
"Dan bakisan irin kewarsu da nayi ba wlh.
Mamy! Sannunku da zuwa ya gajiya?"
Mamy ta amsa akaro na biyu tana murmushi tace.
"Amman Baby kamar bakida lafiya koh?"
Khairy ta saketa tana ƴar dariya tace.
"Ni kam lafiya lau nake Mamy kije kiyi wanka kizo kici girkin ƴarki mai daɗi."
Mamy tace.
"Ai dole Baby, Nadiya kunyi mana girki me daɗi koh?"
Nadiya tana murmushi tace.
"Eh Mamy munyi."
Mamy tace.

"Masha Allah, Allah ya muku albarka, bari naje na watsa ruwa na fito. Baby ki kirasu su shigar da kayan nan da suke tule nan."
Khairy tace.

"Tom Baby."

Mamy sosai ta ƙara jin son Khairy ganin yadda ta gyara mata ɗakinta Tsaf komai gwanin sha'awa da burgewa.
Kayanta ta cire ta shiga bathroom dan yin wanka.

Ɓangaren Shattima ma yana shiga ɓangaren sa tun falon ya shiga sakawa Babynsa albarka.
Kayansa ya cire ya ɗaura towel, ya shiga bathroom, ya shige cikin ruwan ɗumin da Mamy ta shiga ta haɗa masa kafin ta shige ɓangarenta.
Sosai ya yi wanka ya fito ɗaure da lawala sabida Maghreb ta kusa.
Mamy ce ta shigo falon Shattima cikin shiga ta alfarma, ta yi kyau sosai saboda tasan zatayi ta amsar sannu da zuwar ƴan uwa da abokan arziki.
Sanye take da lafiyayyan material Ash colour abinka da farar mace, ba karamin kyau ta yi ba, ɗinkin riga da skirt bazaka taɓa cewa Mamy babbar mace ba, tayi kyau matuƙa abinka da mai ƙaramin jiki, shiyasa ka da yaushe take cin lokaci, sai baza ƙamshi take.

Shattima baya falon sai wayoyinsa ajiye akan Centre table.
Ɗan murmushi ta yi tana nufar bedroom ɗin nasa.
Tsaye yake agaban ƙaton dressing mirror ɗinsa, yana gyara sumar kansa da cumb.
Sanye yake da fararen kaya na shan iska masu taushi sun zauna a lafiyayyar baƙar fatarsa mai sheƙi da taushi, sai wani irin fitinannan ƙamshi yake tashi ajikinsa.
Isowa gabansa ta yi ta tsaya tana raɓuwa da jikinsa, ta amshi cumb ɗin tana kallonsa fuskarta cike da murmushi, anutse tace.
"Mi Amor irin wannan kyau haka, sai kace zaka je zaɓan Miss uhmm?"
Ta faɗa tana zaunar da shi akan stool tana taje masa sumar kansa, tana shafa masa man gashi na maza mai ƙamshi da taushi.
Kan cinyarsa ya zauna da ita,yana shafa cikinta, ya sumbaci ƙasan wuyanta, can ƙasa² cikin narkarkar murya anutse ya raɗa mata.
"Sweetheart idan ana maganar kyau, ke ai ƙarshe ce, kinga kuwa yau sak ƴan mata kika koma, faɗamin meye sirrin matar Shattima?"
Ya ƙarashe mgna yana ɗan cizon fatar kunnenta.
Ɗan ƙara ta saki tana dariya, ta daki ƙirjinsa tace.
"Muje kaci wani abu kaɗan kafin Akira sallar Maghreb, Please Mi Amor."
Gira ya ɗaga mata yana manna bakinsa kunnenta, anutse yace.
"Yau kam dai za'a biya bashi uhm?'
Mamy sanin inda ya dosa ta sumbaci laɓɓansa tana murmushi tace.
"Dole ma Mi Amor ai kaine kake tsausaya mun."
Ƴar dariya yay yana sauketa yana faɗin.
"Sai bayan sallar Isha'i ko zan samu daman cin wani abun, Ok?"
Sanin halinsa tunda yace hakan, bazai ciba ta sumbacesa ta fice.
Anutse ya fito falonsa ya zauna yana duba wayoyinsa kira yaga har ba adadi, cikin lambobin da yaga zai iya kira ya kira kafin lokacin Maghreb ya ƙara kusantowa, ya tafi masallaci.

Mamy tana saukowa Khairy tarbeta tana kama hannunta tace.
"WoW! Mamy kinga yadda kikayi kyau kuwa? Mamy muje kici abinci dan ALLAH."
Mamy tana murmushi tace.
"Ni ƴar gatan Baby Khairy, Ok muje."
Balaraba tace.
"Ni kam Khairy bazaki bari mugaisa da Auntie Bilkisu ba, duk kin taremana ita?"
Khairy tace.
"Kai Auntie B ai gata ku gaisa, naga tun ɗazu kun gaisa, kutashi muje kan dining kuji kalar girkin ƴarku."
Fauziyya tace.
"Balaraba muje muji kam kar dare yamana anan."
Mamy taja hannun Khairy tana murmushi suka nufi kan dining area.
Anutse Shattima ya sauko yana amsa waya, kyakkyawar fuskarshi ɗauke da murmushi, anutse magana cikin tausasa harshe.
Falon yake ƙarema kallo ya waigawa ya yi hanyar dining area, inda yakejin ƙara cokula tare da sautin muryoyi na tashi.
Anutse ya nufi corroder ɗin da zata sada shi da ƙofar falon.


Da misalin ƙarfe 8 na dare.

Can ɓangaren su Azizah da Salim and Tasi'u, ba ƙarama azaba aka gana musu ba, se da kamanninsu suka canza ba kaɗan ba, dan Abba Aminu bai duba alaƙarsa da Hamshi ta baya ba, ya saka akaci ubansu, kafin su amsa laifinsu.
Abba Aminu da yake zauna cikin falonsa acan gidansa yana kallon komai kamar agabansa, ta cikin laptop da ya juye cikin wayan, yadda Azizah ta zage tana faɗar gaskiya tana kukan azabar da ta sha, dan bata taɓa zaton za'ayi mata irin wannan baƙar azabar ba.
"Wlh tallahi na naje ɗaukan fansar da nakeson yi akan Khairy na haƙura wlh ko Kausar bazan shiga sangarta ba, natuba na daina duk abinda nakeyi."
Ta faɗa cikin wani irin jan numfashi tana rufe idanunta tanajin raɗaɗin azaba na shigarta.
Dsp yace.
"Au har kin karaya da wuri haka? Gaskiya ban zaci haka daga gareki ba, kamata ya yi akai ruwa rana kafin ki amsa laifinki."
Cikin jigata tace.
"Wlh nayi alƙawarin bazan sakeba, kuyi haƙuri don ALLAH."

Dsp Labaran ya kalli Salim yace.
"Kai ƙaramin shege wlh sai mun shigar daku kotu sabida ko ta kwana ku saka hannu daga nan har tsawon shekara ɗaya idan wani abun ya samu Ummulkhairi ko Minister ko yarinyar da kuka so jefawa cikin halaka."
Ya ƙarashe mgna yana nuna Tasi'u da yatsarsa, wanda yaci ubansa, sai hawayen azaba yake yace.
"Kai ƙaramin ƙwaro kaban mamaki kuka kake wai akan wannan ƴar azabar da kasha? Tabb."

Salim tsabar azabar da yasha da ƙyar yake faɗin.
"Wlh na janye neman Khairy na haƙura zanma iya barin ƙasar baki ɗaya, har komai ya lafa yauma banida wani niyar ɗaukan fansa, dan ALLAH kubarni na tafi gida inada mata da ciki tana buƙatata. Dan Allah kar abari iyayena suji wannan mummunan labarin, dan Allah zaka iya haɗani da Abba Aminu..?"
Bakinsa Dsp ya buge sai da ya fashe yana fitar da jini, yace.
"Kai waye baisan halinka ba, munafukin banza, anan zaku kwana cikin wajan nan bazan sauya muku wajeba, Sir baida lokacin jin shirmenka. ke tashi ki koma wajan mata masu laifi ƴan uwanki munafukar banza, ina ganta naki da kike ikirarin kinada shi?"

Azizah da ƙyar ta miƙe tana kuka tace.
"Allah na shiryu bazan

Please Login or Register in order to submit comment