Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta matsa akan Dad ya faɗawa Shattima su Khairy suzo yaƙi.
Acan Dotse
11 na safe su Khairy an gama shirin tafiya, sai rikici take ma Mamy akan zatayi missing ɗinta, Auntie Aisha na musu dariya.

Shattima ne ya sauko daga upstairs yana amsa waya cikin nutsuwar sa, sanye yake da wani fitinannan ɗanyan Boyel, fari mai shegen kyau.
Khairy ya kalli tana jikin Mamy tana mata magana ashagwaɓe.
Ƙamshinsa ya saka ta ɗago kanta, anyi rashin Sa'a yanzu basu yake kallo ba idanunsa ƙasa yana magana yana takowa anutse.
Mamy ta kafa masa idanu tana murmushi.
Auntie Aisha tace.
"Abdallah! Zamu makara fa fisabilillah."
Murmushi me taushi ya sauke yana katse wayan ya iso falon yana zama idanunsa akan Mamy yace.
"Sweetheart! Tashi ki shirya zamuje Gumel sharf-sharf mu dawo kafin La'asar, mahaifiyarsu Usman Allah ya mata rasuwa jiya."
Mamy tana riƙe da hannun Khairy tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amman har Khairy koh? Daga can sai su wuce..."
Auntie A'isha tace.
"Wa ni!? Wlh bazanje ba, sai dai na wuce da kayan Baby daga can kun turata, wlh bazan jeba."
Shattima ya miƙe ya dawo kusanta ya zauna yana kama hannayenta yace.
"Calm down Auntie, ba Wai daman dake za'a jeba kiyi haƙuri kitafi yanzun da dukkan kayan Babyn in Sha ALLAHU zan tura miki ita ta jirgi nan da kwana uku zamu barta ta zauna kwana biyu can sabida ƴan uwanta zasuji daɗi idan anyi kwana uku zan tura Maleek ya ɗaukota, sai na turota a jirgi Ok?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace.
"Yawwa yanzu naji batu, ina jira Allah ya kaimu gatan."
Shattima yana murmushi yace.
"Ameen my Auntie godiya muke."
Mamy tace.
"Mun gode Auntie Allah ƙara girma, Allah saukeki lafiya, bari na shiga na shirya."

Auntie Aisha tace.
"Ameen Bari naje direba na jirana, kuma Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lafiya."
Khairy ta saki Mamy ta kama hannun Auntie Aisha tace.
"Ameen Mummy bari na rakaki mota."
Ta amshi ledar hannunta mai ruwan zamzam da turarukan da Mamy ta haɗa mata tsarabanta ta riƙe suka nufi hanyar falon Shattima na take musu baya, yana amsa wayan da aka kirasa....

Real Ladingo Omu Farisah

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = ₦500. 500Mb ₦500
2.9GB = ₦1200. 1.5GB ₦8000
4.1GB = ₦1600. 2GB ₦1600
5.8GB = ₦2100. 3GB ₦2000
7.7GB = ₦2700. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_


*YI WA KAI!*

4/1/2023

_#MatarɗanAlhaji🫣_

Washhh! Bayana🤣 Nakusa dai na huta.😟😫

_*KYAUTAR PAGE, Nafisa Bashir, Allah miki Albarka yasaka miki da mafificin alkhairi, Ngd sosai da alkhairin ki gareni, Ubangiji ya maida miki dubunsa.😍*_

Love kai soyayya tayi fa arayuwa, idan kayi dace da masoyi Billahi.😍 Shattima na Mamy da Khairy, naji ance Khairy tanada ƴan adawa dayawa abayan fage masu taya Mamy kishi.😂

*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*101*


Suna zuwa Gumel sharf-sharf suka juyo bayan sun yi wa, Usman da Nadiya gaisuwa, sosai Usman ya ji daɗin zuwa su Shattima.
Acan suka bar Khairy zata zauna sai bayan sadakar uku, Maleek zai zo ya ɗauketa.
A koda wani lokaci Khairy tana tare da Nadiya da ummanta Zainabu, acan gidan zaman makokin, wanda sai da Zainabu ta yi da gaske ya barta take wuni can.
Agida dukkansu suke kwana tunda safe ne suke tafiya wajan zaman makokin har Usman.
Maryam tunda Khairy ta kirata ta faɗa mata, ta kira Usman da Nadiya ta musu gaisuwa. Usman ya ji daɗi sosai.

Yau aka shigar dasu Azizah kotu, wanda dole ƴan uwansu suka kasance awajan.

Ɓangaren Kausar ma Aminu ya tura aka ɗaukota.
Takarda aka basu suka saka hannu akan duk abinda ya samu Khairy ko shattima ko Kausar, sabida ta tona musu asiri akan ƙuɗirinsu, daga nan har tsawon wani lokaci, kotu zata musu mummunan hukunci.
Kowane yaci ubansa yasan ALLAH ɗaya ne, sun yarda sun saka hannunsu tare da rantsuwa sun fita harakarsu har abadan.
Azizah suna zuwa gida ta rufe kanta a ɗaki taci kuka kamar ba gobe, bata taɓa zaton kuɗin ubanta da gatan da take da shi ba, za'a iya cimata mutunci har haka akulleta, tsawon kwana uku gidan horo daga ƙarshe akaita kotu, taji ta tsani duk wani ƙyale-ƙyalin duniya, tunda wani lokacin kuɗi da gata basa aiki.

Ɓangaren Salim hakane shima yanzun, kunyar Aliyah da abokinsa Abdurrazaq yake.
Yadda yake nuna musu shi ɗin wani ne, ƙarshe sai ga shi Commissioner Aminu ya sake ya zama ba kowaba.
Sosai ya tsorata da lamarin, baisan Khairy da Shattima mutane ne masu daraja da kima ba wajan Aminu har haka sai da hakan ta faru. Wai abun ya tsaye ma haka dan Shattima bai saka hannu ba, ya barsu da Commissioner Aminu
Umma Sa'idah ranta fari tass tasan yanzun Salim zai nutsu ya dawo mutum.
Ɓangaren Kausar hankalinta ya kwanta yanzun, tasan ba mai farautar ranta tsakanin Azizah da Tasi'u, tunda batada case da Salim.
Commissioner Aminu ya tura akaina su Kasar kayan abinci da kuɗi masu yawa, wanda har kuka ta yi ta iskosa har police station ɗinsu ta Masa godiya, yace Yi Wa Kai ne ba damuwa.
Washegari ne Kausar suna zaune suna kwasar girki yasha nama suna cikin farin ciki.
Shattima ya turo akai babanta asibiti, da kuma masu kwasar kaya sabida za'a zubar da gidan a fara gina sabo kamar yadda Khairy ta nema ataimaka musu.

Kausar kuka take sosai farin ciki ya isheta. Wani gida ɗan ƙarami me kyau suka koma, kafin rushe masu gidansu afara gina musu sabo.
Kwantar da mahaifinta akayi a asibitin Mamy, yana samun kulawa sosai.
Yanzu ma zaune take kusansa yana bacci, tana kukan farin cikin tace.

"Lallai idan Allah yaso ka da rahama ba wanda ya isa ya hana hakan, kaɗan ya rage na YIWAKAI Na babbar illah arayuwarta, na tashi a tutar babu na halaka kaina, sai Ubangiji ya dubeni da idanun rahama ya tausaya min, naji tausayin Khairy na temaketa, sai ga hanyar alkhairi ta ko ina. Allah na gode maka da kabani wannan ni'ima."

Wayanta ta ɗauki ringing ta duba lamaba ba suna, ta ɗaga tana sallama.
Murya anutse aka amsa tare da cewa.
"Kausar! Kin shiyar aure?"
Idanunta ta zaro tana dafe ƙrjinta tace.
"Ni yaushe ma na nutsu har nayi samari, tunda maza wajan huɗu suka fitomin duk ba aureba maganar banza suke min na jinginesu gefe ina neman abinda zamuci da babana da kannena, waye dan Allah?"
Murmushi akayi akace.
"Yanzun bazaki sanshi ba sai kin amince zaki sansa bye."
Aka katse kiran.
Idanu ta shiga rarraba wa, tana tuna inda tasan murya.
"Gaskiya A'a ina aka taɓa cininki kifi aruwa ko waye idan ya matsu zai fito."



Yau ne sadakar uku Zainabu basu tafi ba ita da Khairy, sabida Khairy ta tashi da zazzafan ciwon kai, wanda mura da ta tashi da ita ta saka mata ciwon kan.
Mustapha dasu Usman suka tafi.
Ana gama fatiha sadakar uku, Mustapha ya tafi domin su kai Khairy asibiti.

Asibiti suka tafi aka rubuta musu magunguna da zasu siya mata, suna dawowa gida ta sha tea da magungunan sai bacci, Zainabu ta shirya dan tafiya gidansu Karima.
Dad Mustapah ya fara ma Zainabu faɗa akan bazata tafi ba, tabar masa ƴarsa ba lafiya ba.
Zainabu cikin damuwa ta matso kusansa tana ɗora tafukan hannayenta saman ƙirjinsa, tana ɗan shafawa alamar ya yi haƙuri, ta tsare shi da ido tana basa haƙuri.
Kansa ya kauda daga kallonta yace.
"Ai ke baki san ciwon kanki ba, tunda kince sai kinje se kinje, har kin manta musibar da ta sakaki, ta sakani? Kuma ai kin sani yaune Maleek zai zo ya ɗauketa."
Kiss ta kaiwa kumatunsa tana murmushi.
Hannayenta ta janye daga ƙirjinsa, tana masa nuni da hannunta ta yadda zai fahimta da kyau.

Kayi haƙuri mijina komai me wucewa ne, yanzu ita tana ina? Kaga tabar duniya baki ɗaya, Ni nayafe mata kaima ka yafe mata albarkacin ƴaƴanta nagari, dan Allah ka barni na tafi tana bacci ta sha magani,har nazo bazata farka ba, ba zan jima ba sabida kar azo ɗaukan ta bana nan, kaji mijina?

Ajiyar zuciya ya sauke yace.
"Ok jeki sai kin dawo idan kin daɗe ke kika sani, Naziru na nan waje, je ya kaiki."
Zainabu ta san baya son ta tafi ne, shiyasa ta yi murmushi ta shafa fuskarsa, ta miƙe tsaye.
Wayarsa ta ɗauki ringing.
Sunan Shattima ya bayyana, ya kalleta yana faɗin.
"Kinga irinta ko ga shi yana kira bazai wuce ya turo a ɗauke ta ba."

Zainabu ta langwaɓar da kai gefe kalar tausayi, tana jan ƙafafuwanta tana barin wajan tun kafin ya hanata.
Picking call ɗin ya yi yana kai wayan kunnensa tare da sallama.
Daga can Minister ya amsa yana gaishesa tare da cewa.
"Anjima kaɗan Maleek zai iso ya taso Khairy ta kasance cikin shirin tafiya."
Dad Mustapha yace.
"Ok toh in Sha Allah, tana bacci ma yau da mura ta tashi da ciwon kai."
Shattima ya lumshe Idanunsa, yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa, anutse cikin taushin murya yace.
"Subahanallahi, tana kwance kenan?"
Mustapha ya yi murmushi yace.
"Eh tasha maganine munje asibiti."

Wani irin numfashi yaja bai iya cewa komai ba, akan ciwon nata saboda yadda yakeji ajikinsa, tana jin jiki da dukkan alamu.
"Sai anjima agaishe min da umman Khairy."

Ya faɗa yana katse kiran, ya kira Maleek bai samesa ba, yana wajan da ba network.
Number Khairy ya kira, yana ɗan murza goshinsa.
Kwance take tana saman bed tana sharara bacci, wayan nata famar ringing batama San tanayi ba.
Kira uku ya mata bata ɗauka ba, yasan da idanunta biyu bazata ƙi ɗauka ba.
Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayan, ya shiga duba tarun takardun gabansa.

Zainabu koda taje bata daɗe sosai ba, ta cewa Nadiya Khairy batada lafiya zata koma gida.
Nadiya taji daɗin zuwan Zainabun sosai , se dai bataji daɗin rashin lafiyar yayar tata ba! Zainabu tana dawowa ta ɗora girkin rana.

Boka YANKAN WUƘA sai da wuni ya kwana yana shan azabar duniya kafin ya mutu, ba gaba kare ya cinye duk ya cire naman hannunsa ya cinye, yana haushi ƙoda na bin jikinsa haka ya mutu, gawar ta kwana ta wuni da ƙyar aka samu Fulani mutum uku suka tattara sa suka binne dan kar warinsa ya cutar dasu.

Har Maleek ya shigo garin Gumel Khairy bacci take.
Tun yana bakin gari ya kirata, bata ɗauka ya kira Shattima ya faɗa masa.
Shattima duk ya tashi hankalinsa, sai yakejin kamar amatse take.

Kiran Dad Mustapha ya yi ya sanar da shi a tashi Khairy, Maleek ya iso, koma ya takejin jikin nata su taho Mamynta zata dubata da zaran sun iso.
Mustapha tunda Shattima ya gama bayanin ya katse kiran, yake dariya ya kama hannun Zainabu yace.
"My Zeey muje a tasheta alamun yadda yake magana ba zai fahimci karatun ba, na ya barta zuwa goben idan ta warware Naziru ya kaita, yace a tasheta."
Zainabu cike da kewar ƴarta tun kafin tabar garin, ta jinjina kanta tana binsa.
Suna hawa upstairs, ɗakinta suka nufa.

Tana laɓe cikin Duvet bacci take sosai, tana rungume da pillow.
Zainabu ta zauna gefen bed ɗin, tana janye Duvet ɗin ta ɗago kanta tana ɗaukan handkerchief ɗin da yake ajiye gefe, ta goge mata majinar da ta fara fitowa.
Dad Mustapha ya buga kumatunta, yana kiran sunanta.
Idanunta da suka mata wani irin nauyi, ta fara ƙoƙarin budewa.
Kallon iyayanta take tana lumshe idanunta, ashagwaɓe tace.
"Dad bacci bai isheni ba, kaina ciwo yake har yanzu, hancina zafi. Ummana kinje wajan sadakan?"
Zainabu ta ɗaga kanta tana murmushi, tana taɓa kanta taji akwai zafi.
Dad yace.
"Ki tashi ki daure Maleek ya iso kafin ya shigo ki shirya."
Majina ta fitar tana sauke numfashi, tace.
"Toh bari na saka kaya bazan sake wanka ba, zamu biya wajansu yaya Usman na musu sallama."
Zainabu ta jinjina kanta tana shafa fuskarta.
Dad ya miƙe yana faɗin.
"Toh kiyi sauri sai kinci abinci."

Kai ta ɗaga tana kissing ɗin Zainabu ta sauko daga bed ɗin.
Wayanta ta duba taga kiran Shattima kusan goma.
"Wayyo my Dady love I'm sorry Babynka ba lafiya."
Ta ƙara she maganan tana tura masa message.

*"Hello Sweet Dadynah muahhhh kayi haƙuri ina bacci ne, yanzu na farka naji sauƙi karka tasarmin hankalinka, yanzu zamu kamo hanya, i love You madubin dubawata."*
Haka ta tura masa ta kashe wayan tana jefawa cikin handbag ɗinta.

Akasalance ta shirya sabida yadda jikinta ya mutu.
Riga da skirt ta saka na shadda blue sosai ta yi kyau, ta saka baƙin takalmi mayafi baƙi handbag ɗinta baƙa.
Turarenta me sanyin daɗi ta fesa, tayi juyi tana kallon Zainabu tace.
"Umma! Nayi kyau sweet Dadynah zai yaba koh?"
Zainabu ta zaro idanunta tana kai mata duka ta mata nuni da hannunta.

Bakida kunya mijin Mamynki kike wa kwalliya?
Ƴar dariya Khairy ta yi tace.
"Toh ya zanyi Umma ina sonsa dayawa, Umma Mamy tasan dole zanso Ruhina Dady Shattima, yanayinsa da tsarinsa banajin akwai macan da zata ƙisa sai wacce bata samu ba, tasan dole ina son mijinta, kawai ina ɓoye matane,
ba yanda zanyi,bana nunawa gabanta ina sonsa fa! Umma dayawa."

Zainabu ta rufe baki tana kallon Khairy, cike da mamaki.
Khairy ta fitar da majina tana maida handkerchief ɗin cikin handbag, tana kama hannun Zainabu tace.
"Muje kimin addu'a mu sauka lafiya."
Zainabu ta yi murmushi tana mamakin ƴar Tata.
Suna saukowa Maleek yana kiran Dad akan yana ƙofa.
Khairy a gaggauce taci abincin kaɗan sabida bakinta ba ɗanɗano.
Maleek ma sai da ya ciki tumbinsa, suka tafi harda kukanta rabuwa da iyayanta dan yanzu sosai take son su tun zaman da tayi dasu da azumi.
Can gidansu Karima suka biya, tayima su Nadiya sallama da kuka ita da Nadiya suka rabu da juna abun tausayi...

_Khairy clinic and maternity_

Mamy ce ta fito daga cikin toilet ɗin office ɗinta.
Zama tayi tana faɗin.
"Washhh ALLAH nah?!"
Ta ƙarashe faɗa tana lumshe idanunta.
Wayarta ta fara ruri.
Manyan gajiyayyun idanunta ta buɗe tana saukewa akan wayan.
Lambar ba suna har ta share sai kuma ta ɗauki wayan tana ɗaga kiran.
Muryan Sa'idah taji.
Da mamaki take amsa sallamar.
Umma Sa'idah tace.
"Bilkisu! Don Allah kiyi haƙuri ki yafe mana abinda ya faru, wlh na gane kuskurena, ki yafemana mu dawo kamar da ko fiye da hakan, wlh shirye nake zama daku da zuciya ɗaya keda Abidah na gano rashin ku giɓine cikin rayuwata."

Mamy ta gyara zamanta tana jinjina kanta tace.
"Ayyah! Wlh ba komai Sa'idah daman Ni bana riƙe mutum araina, na yafe miki, amman kiyi haƙuri bana dawo da hannun agogo baya, idan halin agaisa ya kama za'a gaisa amman ba mgnan adawo da aminci ya ƙare Ngd da kulawa Sa'idah."
Sa'idah kamar ruwa ya cita haka taji sai ta rasa bakin magana tace.
"Toh Ngd Bilkisu sai anjima."
Mamy tace"
"Ok bye."
Ajiye wayan ta yi tun bata katse kiran ba, tana kunna laptop tana abinda yake gabanta.


Maleek na shigowa gari inda Shattima yace ya kai masa Khairy ya nufa, can office ɗinsa.
Zaune yake ya zuba dogayen ƙafafuwansa akan table, yana ɗan ciza pink lips ɗinsa, yana lumshe idanunsa.
Knocking din ƙofar akayi, ya bada umarnin shigowa, dan tun shigowar motarsu ya gansu ta cctv camera, har fitowar Khairy daga motar, shiyasa ya bada umarnin tana zuwa abata hanya duk da daman bazasu hanataba.

Anutse ta buɗe ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Idanunsa lumshe ya amsa yana girgiza ƙafafunsa akan table ɗin.
Khairy ta rufe ƙofar anutse ta nufo wajansa da mamaki tana kallonsa, kwana ukun da ta yi sai taga ya ƙara kyau da kwarjini.
Ashagwaɓe ta kirasa.
"Sweet Dadynah baka kallona naji sanyi dan ALLAH? Dadynah kalli rashinka ya susutar dani, ga mura tana azabtar maka dani, daga jiya zuwa yau."

Ta faɗa kamar zatayi kuka, ta ƙara so ta haye jikinsa tana sanya hannayenta ta rungumesa gam, tana sauke ajiyar zuciya, tace.
"Dady love ka kulani kaji Baby ce fa me namaka please, taɓa kaina kaji banida lafiya."
Ta ƙarashe maganar cikin shasheƙar kuka marar sauti.
Hannayensa ya sanya duka ya rungumeta gam, yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗago fuskarta da take jiƙe da ruwan hawaye da majina, cikin wata irin murya me taushi ya furta.
"My Baby buɗe kyawawan idanunki kalleni."
Ya faɗa yana cire mata mayafin jikinta, ya fitar da ɗan kwalin, yana taɓa kanta akwai zafi sosai.
Ahankali ta buɗe idanunta tana kallonsa, tana masa kukan zallar shagwaɓa.
Kai ya girgiza mata yana ɗan jujjuya mata lumsassun fararen idanunsa, ya ɗan janyeta kaɗan ya zaro handkerchief, ya goge mata majinar tare da hawayen.

Harshensa ya fito yana lashe mata hawayen, ya yi kissing idanunta, yana tallabe da fuskarta, ahankali cikin raɗa, fuskarsa dab da Tata yana ɗan shafa goshinta, ya furta.
"My Baby sosai majina ta kama min ke, sannu kinji, amman ba na hanaki yawo da mayafi ƙarami ba bakya jine? shiyasa yanzu kikayi shiga me kyau haka, kika fito da mayafi kika ratso cikin ma'aikatar mu har nan cikin office haka securities suka kalleki?"
Ya ƙarashe mgnan yana zaro mata mayan kaifafan lumsassun fararen idanunsa masu bala'in tasiri akanta.

Wata kalar shagwaɓa ta fara masa tana ƙanƙameshi, ta saki kuka tana ɓoye kanta cikin ƙirjinsa, cikin kukan tace.
"Don Allah Sweet Dady kayi haƙuri bazan ƙaraba, Ruhina karkayi fushi dani."

Idanunsa ya lumshe yana matseta jikinsa sosai yana buga bayanta, bakinsa ya kai kunnenta yana sauke mata numfashinsa me ɗumi can ƙasa² ya raɗa mata.
"Shiru ya isa idan kin kuma bazamu kwashe ta daɗi ba, Ok?"
Kai ta ɗaga tana haɗiye kukan, tace.
"Ok my Dady wlh bazan ƙara ba in Sha Allah."

Fuskarta ya ɗago yana lashe hawayen yana mata wani irin fitinannan kallon da ya ƙarasa kame zuciyarta da ruhinta tare da gangar jikinta, ashagwaɓe ta shafa sajansa tace.
"Sweet Dady love my Ruhina I love u kaca-kaca kaji Ruhina."

Ta faɗa tana rufe idanunta ta kwantar da kanta ƙrjinsa.
Cikin muryan da bata zataba yace.
"My Ruhi sunan ya min kema Baby My Ruhi i love You more."

Ya fad'a yana sumbatar idanunta da hancinta kumatunta ya kamo laɓɓanta duka ya fara tsotsan su anatse.
Kallonsa ta yi tana jin wani bala'in farin ciki da shauki na shigarta, jin zai kamo harshenta ta zare bakinta tana kallonsa tace.
"My Ruhi zakayi mura ai idan ka sha harshena kayi haƙuri bana son mura tama abinda tamin daga jiya zuwa yau."

Murmushi kwance akan fuskarsa anutse can ƙasa, idanunsu cikin juna ya furta.
"My Ruhi ƙara matsowa na raɗa miki wani abun."
Ashagwaɓe ta sake maƙaleshi ta manna kunnenta akan bakinsa, tana zagaye hannunta wuyansa, tace.
"Toh na matso Dadynah faɗa min."
Kiss ya sauke mata tana dariya, tare sake maƙaleshi.
"My Baby Ruhina ai nafison ki barmin wani abu naki ajikina da zai jima bai barni ba, dan kar tunaninki ya matsa nan da can, Ok?"

Ɗagowa tayi tana kallonsa hannayenta zagaye da wuyansa take kallonsa cike da sonsa da ƙaunarsa, kamar zatayi kuka tace.
"My Ruhi mura akwai wahala fa! Allah Ni bana son wani abun ya sameka. Toh kasha kaɗan ga shi."

Ta ƙarashe maganan tana tura masa bakinta tare haɗe face ɗinsu, suna shaƙar numfashin junansu, still kallon juna suke.
Anutse ya haɗe laɓɓansu yana gogawa ya riƙe fuskarta sosai yace.
"My Babyn Shattima me yasa muke son juna har hakan ne?"

Kamar zatayi kuka tana kallonsa ta zaro hannunta ɗaya tana kamo hannunsa ta ɗora a saitin zuciyarta tace.
"Wlh nima ban saniba Sweet Dady Ruhina."
Da sauri ya janye hannunsa daga wajan yana tallabe kanta ya tura harshensa cikin bakinta ya kamo nata ya fara mata wasan kissing ɗin da taka jurewa ta zare bakinta tana maida numfashi tace.
"Allah Dady kaina juyawa yake Ni dai bana so."
Ta ƙara she maganan tana lashe yawunsa ta kwantar da kanta ƙirjinsa.
Kanta ya shafa yay magana can ƙasa yace.
"Muje muje asibiti, ƙarfe biyar jirgunku zai wuce."
Ƙara narkewa ta yi ajikinsa tana tutturo bakinta gaba, tace.
"A'a Ruhina bana son allura kasan Mamy allura zata min, ga magunguna nan da aka rubuta min da safe Dad ya siya."
Bakin surutun ya sumbata yana taɓa kanta yaji akwai gumi sosai.
Kallonsa ta yi tana rau-rau idanunta, tace.
"My Ruhi!"
Kallonta ya yi yana janyeta daga jikinsa tun bai ƙarasa tafiya ba, ya kamo Twins ɗinta akayi abun kunya gwara su tafi.

Anutse ya amsa.
"Na'am Babyn Shattima Ruhin Shattima, Menene?"
Ƴar dariya ta yi tana rufe fuskarta tace.
"Don Allah Ruhina ina Mamynah? Allah duk kaine ka saka ban tambayeta ba."
Ta ƙarashe maganan tana turo bakinta gaba.
Murmushi ya yi yana ɗaukan wayoyinsa yace.
"Ba wani ni nida ko kiss yau an min ruwansa Baby."
Wayoyinsa ta amsa tana dariya tace.
"Eh kam Dady to kaji wasu manyan tsutsotsi da suke min yawo akaina hsky bana so."
Kai ya girgiza yace.
"Muga magungunan."
Handbag ɗinta ta buɗe ta gwada masa.
Ya karantasu yace.
"Eh sunayi anjima kafin ki tafi sai Kinsha na yamma."
Ya faɗa yana kallonta.

Gabansa ta tsaya tana kamo hannunsa mai tashi tana wasa da yatsunsa.
Murmushi ya yi yace.
"Muje wajan Mamynki."
Kai ta ɗaga tana kallonsa tana murmushi.

Gira ya ɗaga mata, yana rankwafo ya bata fuskarshi.
Ta sumbaci kumatunsa, ta lashi lips ɗinsa, tana kallonsa, ta yi saurin kamo laɓɓansa ta tsotsa kaɗan ta saki tana dariya, ta ɗauki handbag ɗinta tana ɗaukan wayoyinsa.
Kai ya girgiza yana faɗin.
"Zanyi missing daughter Baby Ruhina har wucin wata ɗaya, oh! Ya Rabbi!"

Khairy ta riko hannunsa tana rau-rau da idanunta."
Sumba ya bawa bakin, anutse yace.
"Oya muje Baby."
Ya faɗa yana ɗaukan makullin motarsa ya kama hannunta suka fita.

Duk inda suka gilma kallonsu akeyi acikin ma'aikatar, da kansa yake driving tana gefensa tana game da wayansa, Samsung.

Suna shiga cikin hospital ɗin Mamy na na fitowa, wata nurse na biye da ita da jakarta, wanda suka haɗu ta amsa alamar suna bala'in girmamata sabida Dattakunta, da iya zama da kowa lafiya.
Makullin motarta take karkaɗawa tana amsa waya.
Shattima yay parking yana faɗin.
Babyn Dady ga Mamynki ta fito alamu sun nuna gida zata tafi."
Ya faɗa yana kallon agogon motarsa ƙarfe 3 da minti 13.
Khairy ta kalli wajan da Shattima yake nuna mata.
Mamy ta gani lokacin ta idar da wayan tana murmushi, tanawa nurse da take riƙe da jakarta magana.
Khairy tace.
"WOW! My Dady Mamy ta ƙara kyau sosai wlh tayi fari Mamy sai kace baturiya,bari na tarbota."
Ta faɗa tana ɗora masa wayan akan cinyarsa, ta fara ƙoƙarin buɗe motar...

Idan kun watsa comments gobe zaku iya jina, next page shagali pagen auren Ruhi da Ruhi. Idan bakuyi ba ba ruwana sai naji typing zaku ƙara ganina.🚴

Ƴan zuwa rakiyar gyaran amarya Abuja ku shirya,💃haka ƴan zuwan gyaran gidan amarya Abuja ku shirya,💃 haka ƴan zuwa gulma ma ku shirya💃😂🤣😂🙄😏
Real Ladingo Omu Farisah

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = ₦500. 500Mb ₦500
2.9GB = ₦1200. 1.5GB ₦8000
4.1GB = ₦1600. 2GB ₦1600
5.8GB = ₦2100. 3GB ₦2000
7.7GB = ₦2700. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*

5/1/2023

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*102*

Mamy bata ankare ba tana magana da nurse ɗin nan, taji Khairy ajikinta ta rungumeta tana faɗin.
"I miss You sweet Mamy."
Mamy cike da farin cikin Khairy ta saka hannunta ta rungumeta, tana faɗin.
"Ah Baby yanzu kika shigo ne? Ina Dadyn naki? Kina mura sosai har muryanki ya canza haka? Kinsha magani koh?"
Ta mata tambayar tana kawar damuwar da take ji, sabida baki ɗaya Khairy jikinta bala'in ƙamshin Shattima yake, alamun sunyi ta cakumar junansu.

Da yatsa Khairy ta nuna mata parking spaces, ta ɗora da cewa.
Har asibiti mukaje da safe acan Gumel, naji sauƙi Mamy."

Motar da yafi so cikin motocinsa ta hango, sam bata luraba hankali yake gani.
Murmushi ta yi tana kama hannun Khairy tace.
"Ban luraba Baby

Please Login or Register in order to submit comment