Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iskeka can anjima, ka gaishemin da Bilkisun bye."
Shattima yace.
"Ok yanzu zan fito ina sha Allah bye."

Ya ajiye wayan yana kallon Mamy da ta tsare shi da manyan fararen idanunta.
Kamar zatayi kuka tace.
"Bakaji har yanzu ana danna doorbell ne? Su Laraba basa nan ɓangaren bare su buɗe."
Lips ɗinta ya ciza kaɗan, yana sake shigar da hannunsa cikin rigarta, yana wani lumshe mata kaifafan idanunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke tana ɗora hannunta ɗaya ƙirjinsa, tanajin wani irin fitinannan salon da yake mata yatsunsa cikin rigarta, har cikin ranta abon yake ratsara.

"Allah na godema da ka bani miji rikitacce, Please Mi Amor ka sakeni naje na buɗe ƙofar nan, inaga fa Maryam ko su Balaraba ne."

Murmushi me kyau ya yi, yana mata wani irin kallo, can ƙasa-ƙasa yace.
"Sweetheart har murna kikeyi zaki tafi ki barni koh? Je ki buɗe musu toh."

Ya faɗa yana zare hannunsa daga cikin rigar tata.
Ai kuwa ta miƙe anutse ta tafi, ya bita da mayataccen kallo, yana murmushi yana shafa kansa.

Mamy tana buɗe ƙofar ta hango Ammi da Maryam sun juya zasu tafi.
Murya ta ɗaga tace.
"Hajiyata afuwa don ALLAH."
Ammi ta juyo tana murmushi tace.
"Ai wlh nazaci kun tafi ne."

Rungume juna sukayi Ammi tana faɗin.
"Masha Allah Hajiyata irin wannan kyau haka?"
Mamy tayi dariya tace.
"Kai tsokana Hajiyata."
Maryam ta gaishe da Mamy suka shiga ciki.
Shattima yana hangosu ya miƙe ya kwashe wayoyinsa.
Cikin girmamawa suka gaisa da Ammi Maryam ta gaishesa, ya amsa ya nufi hanyar falon.
Mamy ta bi bayansa.
Rungumeta ya yi, ya haɗata da jikin ƙofar, yana sunsunata, cikin narkarkar murya yace.
"Yau zanyi missing ɗin rashinki kusa dani, Allah ya saukeku lafiya."
Mamy wani irin begen mijinta takeji ta maƙaleshi tana kissing nasa tare raɗa masa zafafan maganganun soyayya.
Idanunsa lumshe yake mayar mata.
Mamy tai saurin zame jikinta tana dariyar yaƙe tace.

"Bye Mi Amor ana jirana I love you."
Ta faɗa da sassarfa, tana barin wajan tasan zai iya damƙota.
Murmushi ya yi yana fitowa yaja ƙofar ya rufe, ya nufi compound ɗin gidan inda Maleek da Guards ɗinsa suke jiransa.

Mamy ta zauna kusan Ammi tana murmushi, tace.
"Afuwa Hajiyata na barku."
Ammi kallonta take cike da mamakinta, tace.
"Sannu ƴar aljanna, wlh bazanyi kaffara ba, ke ɗaya kika rage aduniya, kyautar miji wa ƴar shila ki duba yadda fa ya koma tun bata shigoba, sai wani irin fitinannan shiri yake haƙuransa basa rufuwa, ai wlh ko guzuma bazan ba mijina ba, bare ɗiya irin Ummulkhairi. Duk nasan ƴarmu ce bazata cutar damuba, amman ina Ni baza'ayi haka daniba wallahi."

Mamy ta ɓata fuska tana kamo hannun Ammi tace.
"Nifa gaskiya bana son haka kinsan dai Khairy bazata cutar daniba, ai na taɓa faɗa miki ita kawai zan iya mallaka wa mijina, sabida ina mata son da bakina bazai iya faɗinsa ba."
Ammi ta dafa ƙirjinta tace.
"Nasani Bilkisu kawai ƙara jinjina miki nakeyi, shiyasa na faɗi miki gaskiya Ni dai bazan iyaba duk yadda nakeson mutum Ah toh."
Mamy ta girgiza kanta tana faɗin.
"Ƙaddaraki ce bata rubuce da lokacin da zakiyi baki saniba, bakisan baƙin kishina ba,wlh shiyasa kike cewa hakan, da kinsan irin baƙaƙen mafarkan da na dinga yi abaya koh hummm! Allah yasa mu dace Ni dai Khairy zan iya sadaukar mata da komai nawa."
Ammi tace.
"Ga saƙon ƴarmu kishiyarmu, sai goben in Sha Allah zanzo, fatan goben zaku dawo?"
Mamy ta girgiza tana murmushi tace.
"Madallah mun gode, eh gobe in Sha Allah da an wuce da amarya zamu juyo masu rakiya zasu wuce daga can."
Ammi ta jinjina kanta, ta shiga wata hira daban, Maryam dai kallonsu take.

Ba jimawa da zuwan su Ammi Auntie Aisha ta iso, sosai suka gaisa cikin girmamawa, sai dai Ammi tana hararenta a ɓoye ganin yadda ta zaƙe tana iyayi bini-bini tana hira da Khairy a waya ko Shattima, ta kira Balaraba tana famar faɗa suyi su iso su wuce, dan sai sun biya sun ɗauki Inno.
Mamy ko aka bata kawo ba, sha'aninta take.
Balaraba da Fauziyya suna zuwa ba jimawa suka fito cikin shirin tafiya.
Motoci biyu suka tafi dasu.
Ammi ta koma gida cike da mamakin dangin miji ashe idan ɗan uwansu zaiyi aure, haka suke rawar kai??

Shattima sai da yabiya can gidan wajan liman ya gaishesa, kafin ya wuce wajan aiki, yana zuwa ba daɗewa Abba Aminu ya iso.
Bayan sun gaisa suna hira cikin raha, Abba Aminu ya yi gyaran murya ya fuskanci Shattima.
"Yawwa daman abinda yasa nace inason zamu tattauna, aure nake son ƙarawa, wlh yarinyar naban tausayi gwara a shigar da ita ciki a bata kulawar da ta dace ko ya kagani?"

Shattima ya kalleshi yana ƙunshe dariyasa yace.
"Ita yarinyar nan wacece haka da ake tausayinta? Ai tausayi sone, toh sunnar Ma'aiki zan ce karkayi ne? Ni dai maganar gaskiya badan Sweetheart ba, bazan ƙara wani aure ba wlh har zuciyata, amman idan kana sonta tana sonka ka ƙara kawai Allah ya tabbatar da alkhairi."

Shattima ya ƙarasa mgnan yana sheƙewa da dariya.
Abba Aminu ya kai masa duka yace.
"Abdallah! Yaushe ka zama mutumin banza? Wato kana nufin kar Ni nayi auren, duka shekarun da na baka basufi biyar ba fa!"
Shattima ya sosa kansa yace.
"Wlh ina hango rikicin da zakuyi da Abidah ne, kasanta ai ba sauƙi."
Hararensa ya yi yace.
"Kana nufin sabida ita sai naƙi bawa zuciyata abinda take so?"

Shattima ya ɗaga hannayensa yana dariya🤚🏾😂✋🏾”A'a Commissioner Ni ban ce ba karka ba zuciyarka abinda take so, wai babba ce ko ƙarama?"
Hararensa ya yi yace.
"Ban saniba, kai taka babba ce?"

Shattima ya shafa sumar kansa yana murmushi, yace.
"Na tuba yanzu dai daga yau zuwa gobe kafin na wuce Abuja akaini naga me sa'ar nan."
Abba Aminu ya saki murmushi yace.
"A'a kaje ka gama cin amarcinka ka dawo zamuje."
Ya faɗa yana danna number Kausar bugu biyu ta ɗaga, tare da sallama.
Wayar ya saka speaker, muryata ta karɗe wajan.
Anutse ya amsa yace.
Baby ykk kin shirya ganin babynki?"

Shattima ya danne dariyasa yace.
"A'a tsakani da ALLAH ku canza suna Baby kuma?"
Aminu ya zabga masa harara.
Daga can Kausar ta yi dariya tace.
"Toh Baby ba kai bane duk ka ruɗani da ƙaunarka kaƙi bayyanamin kanka."
Murmushi ya yi yace.
"Karki damu akwai abinda nake shiryawa nan kusa zan bayyana in Sha Allah."

Shattima idanu ya zubawa Abba Aminu yana kallon ikon ALLAH, yana danne dariyasa, wai ashe baima haɗu da yarinyar ba azahiri ko ya ne abun yake?


*Gumel*
Khairy ita dasu Suhailat Nadiya Jamilah da wasu daga cikin baƙin da suka zo bikin, ƴan uwan Ummanta da Dad ɗin ta.
Suna cikin bedroom ɗinta zazzaune, idan ka kalleta sai kasha mamakin yadda ta zama, ƙamshinta kaɗai ya isa gigita mutum.
Abinda zai baka mamaki irin yadda tayi wani irin fitinannan kyau, da hasken gyara da murza da tasha, dole ta burgeka.
Kanta ta jingina da allon gadon tana lumlumshe idanunta, tana sauke numfashi.
Suhailat ta kamo hannunta wanda ya ƙara wani irin shegen laushi tace.
"Wai meye kike ta mutsu nutsu? Ko bakida lfy?"
Matsagaitan kyawawan idanunta ta ɗago tana kallon Suhailat, ta gaza mgna sai hawaye sharrr.

Nadiya ta riƙo hannunta zatayi magana, sai ga Rayhana da gudu tana faɗin.
"Auntie Khairy gasu Mamy Can afalo sunzo su dayawa..."
Khairy cikin wani irin farin ciki ta miƙe ta sauko daga bed.
Suhailat ta riƙeta tace.
"Don Allah ki nutsu ki zauna kinsan dai zasu shigo koh."

Khairy ta ɓata fuska tace.
"A'a wlh tafiya zanyi, bafa auren farko bane za'a dinga wani laɓeni ai bana haɗa Mamy da kowa yaushe zan jira sai ta iskoni."
Ta faɗa tana zame hannunta ta gyara dogon hijab ɗin jikinta, ta fice tanawa Suhailat gwalo.

Zazzaune suke a falon anata gaggaisawa, Khairy ta sauko wajan Mamy ta nifa, ta rungumeta ahankali sabida cikin jikinta.
Kuka ta saki tana maƙalƙaleta kamar zata koma cikinta, ta ɓoye fuskarta ƙirjin Mamyn.
Mamy hawaye masu ɗumi taji sun sauko akan kumatunta ta rungume Khairy gan tana buga bayanta ahankali tace.
"Baby ya isa haka Ok? Missing ɗin Mamy dayawa koh?"
Khairy ta ɗago tana kallon Mamy ta jinjina kanta, tana saurin sadda kanta ƙirjin Mamy yau haka kawai takejin wani irin mugun nauyin Mamyn ba kaɗan ba.
Kowa kallonsu yake cike da burgewa Zainabu kuwa kitchen ta nufa tana zubar da hawaye haka kawai takejin mugun tausayin Mamyn tayi abinda ko ita bazata iyaba.

Auntie Aisha tace.
"Khairy mu kam bazamu sannu ko sannu da zuwan ba? Ai ke kam idan kina ganin Bilkisu bakya tuna kowa koh?"
Mamy ta yi murmushi tana gogema Khairy hawayen fuskarta, anutse tace.
"Haba! Baby irin wannan kyau haka kina kuka zaki ragemana kyanki, bana so karki kuma. Auntie ayimata afuwa, missing ne yamana yawa, je ku gaisa dasu Auntie's ɗinki ga Maryam ga Inno duk baki kulaba sai Mamynki kaɗai."
Khairy ta kamo hannun Mamy tana wasa da yatsunta ahankali cikin sanyin Murya tace.
"Mamy suyi hkr ban luraba ne ALLAH idan na jima ban ganki ba, banida nutsuwa idan naganki sai najini ajikinki. Don Allah Mamynah idan na ɓata miki rai afili ko aɓoye ki yafemin kinji?"
Mamy ta mintsineta tana zaro mata dara-daran idanunta tace.
"Zan cire bakin son ɗorawa kansa laifi ba tare da ya yi laifin ba, koda kinyi na yafe bare bakiyi ba, kije ku gaisa da su Auntie's ga inda kikayi laifi can."

Ta ƙarashe magana tana sumbatar goshinta.
Miƙewa ta yi ta isa wajan Inno ta rusuna ta gaisheta tare da mata sannu da zuwa.
Inno tana dariya tace.
"Lallai yanzu Khairy surukunta kike dani?"
Khairy ta isa wajansu Auntie Aisha ta rungumeta tana gaisheta.
Ta gaishe dasu Fauziyya da Balaraba.

"Ai nazaci yau ba'a yina Baby? Bayan yanzu dani za'a zauna Abuja, ba Mamy ba."
Khairy ta sadda kanta batace mata komai ba.
Mamy ta kalli Auntie Aisha tana girgiza kanta da mamakin ƙarfin halinta, ko nauyinta bataji farat ɗaya take sako magana, ala dole tana son nunawa duniya tafi iko da Khairy ayanzun, se dai Khairyn ta nuna ba kamarta.

Fauziyya ƙanwar Mamy da Abun yama zafi awayance ta maida mata magana.
"Mummy kinsan tsakanin Khairy da Auntie Bilkisu sai Allah, duk inda ta tafi ƙaunarta da fifitata akan kowa, daban yake akanta, ai ko Saudiya zata zauna bata haɗa Auntie Bilkisu da kowa, kina gani yanzu ta nuna mana banbanci dole kuwa zamu haƙuri dan darajarce ba ɗayaba."
Mamy ta kalli Fauziyya da ta gama mgnan tana ƴar dariya.
Kai ta girgiza tana kallon wayanta da kira ya shigo, ganin Shattima ne ta ɗaya anutse ta miƙe tabar wajan.

Auntie Aisha tace.
"Ai dole zata saba yanzun tunda ba Bilkisun."
Khairy ta miƙe ta kama hannu Maryam tana mata sannu da zuwa, suka koma can ɗakinta, nan ta bata saƙon Abbanta tayi godiya sosai, ta kaima Mamy kuɗin tace ta ajiye mata Abba Aminu ya bata.

Umma Zainabu ta cika musu gabansu da kayan ciye-ciye.
Bayan sun nutsu aka kaisu masukinsu.
Khairy sai nunawa ƴan uwansu take Maryam ita ce matar Usman, Maryam tanata sunne kanta.
Da dare bayan sunyi dinner Khairy tace da Mamynta zata kwana ba abinda zai rabasu, Mamy taƙi, Khairy harda kukanta ta kira Shattima ta kai ƙaranta wajansa.
Shattima ya furzar iskar bakinsa yana sosa ƙeyarsa anutse yace.
"My Baby Wai kin fasa yayina ne yanzun koh? Zan kamaki gobe ai naji wa ya hanaki kuka Ruhunki"

Khairy ta kalli Mamy wacce hankalinta wajan Inno suna magana, can ƙasa tace.
"Dadynah Ni ka roƙarmin Mamy mukwana tare kaji?"
"Ok naji Baby bani ita zan kamaki ne, bani kika susutaba."

Baki ta zumɓuro gaba, tana beƙawa Mamy wayan tace.
"Mamy Dady zaiyi magana dake."
Mamy ta amsa tana kai wayan kunnenta, ta masa sallama.
Numfashi yaja me tsayi kafin ya amsa, ya ce.
"Matata! Ni haka kike so na kwana bakya kusana?"
Mamy ta miƙe tabar wajan tana faɗin.
"Zanzo ma cikin baccinka Mi Amor, shi kenan koh?"
"Uhmmm! Goben dai kizo da wuri muyi sallama me kyau na tarawa mutum gajiya."
Murmushi tayi tace.
"Hummm Mijina kenan shiyasa nake sonka dayawa."
Shattima murya ƙasa² me taushi yace.
"Yanzu dai Baby tana son ku kwanta tare Please ki amince tana kewar Mamynta dayawa."
Mamy tace.
"Naji Mi Amor yadda kake so hakan za'ayi."
Shattima yace.
"WOW! Sweetheart shiyasa nake bala'in sonki wlh muahhhh I love you."
Mamy tace.
"I love you too Mi Amor."

Toh haka akayi Khairy ta samu yadda takeso sun kwanta da Mamy tana lafe ajikinta suna hirasu har bacci ya ɗaukesu su dukan.
Usman da Maryam kuwa ba'a samu daman keɓewa ba sun dai gaisa da ya shigo yama su Mamy sannu da zuwa.

Washegari ranar wunin biki, idan na tsaya zayyano muku shagalin da akeyi tun safe, kafin amarya wuce, to fah zan cika wayana da bayani, kuma hakan zai ɓatamin lokaci, masu karatu ku wassafo da kanku irin taron bikin da yake gudana, anci ansha anyi walimar safe saboda amaryar da wuri zasu wuce zuwa gidanta Auntie Aisha ta ƙarasa shagalinta acan.

Amarya tasha kwalliyar kece raini haka ƙawarta Suhailat, da ƴan uwanta, Mamy kyanda ta zuba ba'a cewa komai, duk wacce aka nunawa Mamy akace kishiyar amarya ce sai mamaki ya kasheta awajan.

Da misalin 11 na safe motocin ɗaukan amarya suka jeru a ƙofar gidansu Khairy.
Sanye take da narkeken material me masifar tsada riga da skirt an naɗeta da fitinanniyar lafaya mai shegen tsada da kyau, tana tsugune gaban Mamy bayan Dad da Zainabu sun gama mata nasiha kuka kawai take, dan ta ɗauki nasihar su sosai, ita kanta tasan idan taci amanar Mamy ko daidai da ƙwayar zarrane Allah bazai barta ba, shiyasa ƙaunar Mamy daban take azuciyarta.

Mamy tace.
"Auntie Aisha kuje Allah Basu zaman lafiya ya kaɗe fitina tsakaninsu Allah basu zuri'a ɗayyiba."

Ta faɗa tana murmushi.
Khairy ta fashe da kuka tace.
"Mamy! Dake zantafi dan Allah karki ce bazaki ba, Ammi dan Allah kice tazo mutafi."
Abidah aranta tace.
"Kai yau naga abinda ya isheni bai ishi ALLAH, wannan su kuwa wane irin so saukewa junansu? Rabon auren nan ne ya kashemin ɗana.
Azahiri tace.
"Ai duk muna zuwa kuje mota muna tafe Khairy."
Khairy tace.
"Mamy hakane tare zamu?"
Mamy tace.
"Wai kina zaton bazanje ba? Ku shiga mota ganinan ki yarda dani Baby."
Khairy ta jinjina kanta tana kuka.
Inna ADAMA da Inno da Auntie Aisha suka kamata suka fice tana kiran Mamy da Ummanta.
Mamy ta ƙara sakawa kanta juriya tana ɓoye tarin damuwarta da kukan da yake son fin ƙarfi ta, tace.
"Suhailat kuje mana keda Nadiya kun isa ga Auntie Aisha nan ba sai anje da ƴan rakiya dayawaba Ok?"
Suhailat tace.
"Toh Mamy."
Maryam tana son tace zataje amman Usman yace bai yardaba.
Ammi dai kallon jama'a take tana kallon Mamy da Allah ya bata ikon jure wannan lamari.

Wata narkekiyar mota fara aka saka Khairy.
Auntie Aisha gefenta sai Suhailat, Nadiya tana gaba.
Inno da inna ADAMA suka ƙara mata nasiha suka koma ciki.
Jamilah harda kukanta akan zuwa Abuja amman An hanata, suna ji suna gani motocin saura ba kowa suka ja suka tafi Khairy se tambaya take ina Mamy akace tana motor baya ita dasu Balaraba.
Sosai taji nutsuwa ta saukar mata, tunda akwai Mamy...
Su Mamy basu baro Gumel ba sai bayan sallar azuhur, Shattima har ya gaji da kiranta, ya addabeta ta dawo.

Ammi har ahanya idanu take zubawa taga ko Mamy zatayi kuka amman ina ko alamu babu sai hirama da take janta da shi.
Maryam harda kukanta da bata samu zuwa Abujan ba.
Misalin 4 da minti 10 na yamma Shattima zaune cikin katafareren falonsu wanda ya gaji da haɗuwa, zuwansa kenan daga masallaci, Sai kaya da ya cire.
sanye yake cikin ƙananun kaya, yana danna laptop.
Ƙaran doorbell yaji ya miƙe anutse.

Tana tsaye fuskarta ɗauke da murmushi, ya buɗe ƙofar.
Kallonta yake cike da tsantsar ƙaunarta, ya kamo hannunta yana janyota ciki ya maida ƙofar ya rufe, yana kallonta, anutse yace.
"Welcome back Sweetheart."
Fuskarshi ta shafa tana murmushi tace.
"Ngd Mi Amor Amman Wai daman baka wuce ba?"
Hannunsa saman cikinta yana shafawa ya sumbaci bakinta, ya basar da tamabayan yana ɗaukan ta kamar Baby yace.
"Kin barmin kanki da yunwa hakan ya shafi Babyna yana kuka koh?"
Dariya tayi tana lasar fuskarsa, ta sumbaci idanunsa tace.
"Wlh naci abinci Mi Amor muna Shirin zuwa."
Kan dining ya direta ya haɗa mata abinci da kansa ya bata taci sosai suna hira tana basa labarin yadda akayi shagalin bikin da irin yadda ƴan uwan maman Khairy da babanta suka karrama ta.
Bakinta ya goge mata da tisseu yana faɗin.
"Masha Allah, sweetheart muje kiyi wanka na miki massaging."
Kallonsa take tana ɓata fuska tace.
"Ni fa ban ganeba, yaushe zaka tafi Abujan?"
Cicciɓeta ya yi yace.
"Sai gobe shiru bana son kina yawan magana kin gaji dayawa kina buƙatar mijinki bana son wata magana anan."

Mamy ta kifa fuskarta ƙrjinsa tana sauke numfashi ta cusa hannayenta cikin sumar kansa tana cakuɗawa.
Kallonta ya yi yanajin mugun tausayinta yasan dauriya kawai takeyi badan bata jin zafi azuciyarta ko kishinsa ba.

Cikin bathroom ɗin ya direta yana cire mata kayan jikinta.
Kallonsa take murya can ƙasa tana ƙara ɓoye yanayinta da damuwarta tace.
"Ina son Abdallah Shattima fiye da son da nakewa kaina, shima ya sani, dan haka bazan taɓa yarda na halakar da mijina ba, maganar ka kwana wajena ko na baka kaina ayanzu ya haramta yanzu adaidai wannan lokacin idan ka kusanceni mun shiga haƙƙin Baby, haka idan ka kwana agarin nan ayau shima mun shiga haƙƙinta, Allah zai saka mata, shekaru ashirin da nawa muna tare, sai idan baka ƙasar sati biyu kawai da na baku, zakayi wajan bazai ragemu da komai ba, bare yanayin aikin ka nan yafi Abujan yawa, dan haka har yanzu zanfi ganinka akan Baby shiyasa ban yarda abarmin ƴata can ba, inda ta shekara a tattara amaidomin abata, idan kana son nayi farin ciki na kwana ba ba tare da damuwa ba, toh yanzu ka shirya ka tafi jirgi 6 zai tashi kasani koh? Dan wlh ban yarda ayima Baby ke uku ba, ta wuce hakan ita tama fi karfin budurwa wajena haka nake kallonta."

Shattima banda kallonta ba abinda yake.
Tabbas duk randa Khairy ta kuskura koda mistake tayima Bilkisun sa,wani abun akan kishi ko ba daidai ba akansa zai nuna mata baida kamar Bilkisun aduk duniya idan aka cire iyayansa.

Shower ya kunna yana manneta ƙrjinsa ruwan na ratsa jikinsu, ya tallabo fuskarta ya tsareta da kaifafan lumsassun idanunsa.
Dariya tayi marar sauti tana dukan ƙirjinsa ta shagwaɓe murya cikin sigar da yafi son ta masa magana tace.
"Mi Amor wannan rikitaccen kallon dba, ai sai kasa na cinyeka fa!.."

Bakinsa ya ɗora kan nata, yana riƙo ƙugunta da hannun ɗaya ɗayan riƙe da fuskarta, ya shiga bata wani irin fitinannan kisses.
Lafewa ta yi jikinsa sosai tana basa haɗin kai tare da shashafa sassan jikinsa, ruwan na sauka akansu.
Jin ya fara wuce misali ta zare bakinta tana dariya ta turesa tana faɗin.
"Wayyo Mi Amor baby ya takure tsaya."
Ai kuwa ya riƙota yana faɗin.
"My Sweetheart! Sannu na bari baby ya yi haƙuri, bari na maki wanka."
Ya faɗa yana ɗaukan tattausan sosan wankansa ya matso sabulu ya shiga wanka mata yana sumbatarta...
Da kansa ya shiryata cikin doguwar rigar ta material cikin kayanta da suke ɗakinsa ya fesa mata turarensa.

Ƙarfe biyar cif ta gama shiryasa cikin wata ɗanyar shadda milk colour, ɗinki kawai zaka kalla kasan eh shi ɗin wani ne.
Komai na jikinsa milk colour ta shiyarsa.
Da kanta ta fito da trolleyn ɗinsa taba Laraba ba ɓata Lokaci takai can mota Maleek na jiransa zai kaisa airport.
Da idanu yake binta baida bakin magana.
Hannunsa ta kama suka nufi hanyar fita daga falon.
"Mi Amor na baka amanar Baby wlh ban yarda amata garaje ba,dan nasan zamanta da Abdoul ba wani horuwa tayi sosai ba ALLAH ya amshi abinsa..."

Shattima ya matseta da bango yana mata wani irin fitinannan kallon ƙauna, yace.
"Ni kikawa rowa zaki barni na tafi da ƙishirwarki koh?"
Wani fitinannan kamu tama manhajarsa tana kashe masa ido ɗaya still wasan da ya kusa sakashi sakin ƙara take masa tana fito masa da harshenta.
Kamuwa yayi yana tsotsa ta zare abunta tana janye hannunta jin zai cusa hannunsa cikin rigarta.
Gaba tayi ta barsa nan tsaye yana Binta da kallo yadda cikin jikinta ya sakata ɗan jiki mulmul.
Rakiya har wajan mota suna ɗagawa juna hannu cikin so da ƙaunar juna.
Ta juya tana murmushi ta shiga.
Tana zuwa falon ta kunna Tv tana ƙara maida hawaye da yake son zubowa sanin falon akwai cctv Camera Shattima zai iya duba komai anutse dan ganin tayi kuka ko batayi ba, duk randa ya dawo.
Wayarta ta ɗauka ta kira Anne Mahaifirta suka sha hira tana dariya tana bata labarin yadda biki ya ƙayatar. Tana gama hira da Anne ta kira mahaifin Alhaji Bilal suka sha hira ta kira Adam ƴaƴanta, sun jima suna hira kafin ta miƙe ta haye upstairs.

Ɗakinta ta shiga ta kashe dukkan hasken ta haye bed tayi fatali da kayan jikinta, ta shiga cikin Duvet, tana sakin wani irin fitinannan kuka wanda har ɗan cikinta yana motsi, wani irin kuka take wanda bata taɓa irinsa ba aduniya tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Daman idan zaka rabu da mijinka zai je wajan wata haka mata sukeji? Ya Allah ka sassauta min abinda nakeji ko dan ɗan cikina ya rayu, shi kenan Baby zata dinga samun duk irin soyayyar nan da Mi Amor yake min ita zai mata, amman ba komai Baby ce...."
Ta ƙarashe maganan tana kuka sosai tana shafa cikinta wanda ya tasa...

Acan kuwa Abuja tunda suka sauka ake shagali gidan Auntie Aisha, sai bayan Maghrib aka kai Khairy gidanta, wanda ya gaji da haɗuwa, an zuba dukiya kamar ba gobe.
Khairy dai sai kuka take bataga Mamy ba, sai wayo Auntie Aisha take mata.
Shattima lokacin da yazo akwai mata sosai acikin gidan, dan haka bai shigo ba falonsa na hutawa ya sauka ya yi sallar Maghrib da isha.

Auntie tsaye tana famar lallashin Khairy taƙi tana kuka.
Kiran Shattima ta yi awaya.
Bugu biyu ya ɗaga.
"Abdullah! Babynka ta rikice Bilkisu take nema ido rufe, ta hanani tafiya gida nace mata ga Suhailat ga Nadiya taƙi zama, zo dan Allah ko nasamu natafi gida."
Anutse ya furta.
"Auntie bata wayan muyi magana da ita"
Real Ladingo Omu Farisah

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = ₦500. 500Mb ₦500
2.9GB = ₦1200. 1.5GB ₦8000
4.1GB = ₦1600. 2GB ₦1600
5.8GB = ₦2100. 3GB ₦2000
7.7GB = ₦2700. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

😥 _A'ISHATOU NAH ALLAH ya jiƙanki ya gafarta miki.🤲🏼😥_

*YI WA KAI!*

9/1/2023

_#MatarɗanAlhaji🫣_


*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*104*

Auntie Aisha ta kamo hannunta ta saka mata wayan, a hannunta tace.
"Dadynki ne, yi magana yana jinki."
Wayan ta kai kunnenta, shasheƙar kukanta yake fitowa ahankali batayi magana ba.
Idanunsa ya ɗan lumshe, cikin taushin murya anutse ya furta.
"Baby kina jina?"
Kai ta ɗaga kamar tana gabansa, ahankali cikin kuka tace.

"Eh Dady."

Iskar bakinsa ya furzar anutse yace.

"Yawwa Mamynki gata nan muna tare, a falona, kibar Auntie Aisha ta tafi ku zauna dasu Suhailat, anjima zata shigo Ok my baby?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana tsayar da kukan, dan har cikin ranta ta amince Mamy suna tare da Dadynta.

"Toh Dady se kun shigo."

Murmushi mai taushi ya yi yace.
"Ok My Babyn Ruhi, bani Auntien."

Wayan ta beƙa ma Auntie Aishs.
Ta amsa tace.
"Toh ki zauna kafin su shigo, Nadiya! Suhailat! ku kula da ita kafin su shigo."
Ta faɗa tana ficewa cikin dubara.

Khairy ta bita da kallo tana zama kan Royal bed ɗinta mai bala'in girma.
Suhailat tace.
"Na kawo miki abinci kici koh?"

Kai ta girgiza tana share hawayen fuskarta, ta gyara lafayarta tace.
"Ku hayo mu kwanta."
Suhailat ta zaro idanunta tace.
"A'a wlh mu masaukin mu na can ƙasa, ta ya zamu kwanta kan gadon Sunna, ai babu kyau."
Khairy kamar zatayi kuka tace.
"Kamar ya ƙasa? Duk ɗakunan da suke nan sama, sai kun sauka ƙasa?"
Nadiya tace.
"Eh munfi son can, Auntie Aisha ta zaɓa mana, ke sai ku kwanta da Mamy anan."

Nadiya ta fada kamar yadda Auntie Aisha ta tsara mata, suyima Khairy wayo.
Numfashi Khairy taja, tace.
"Shi kenan tunda kunfi son ƙasan, da Mamy ba sai ta kwana ɓangaren Dady ba, idan kunyarta kukeji."
Suhailat tace.
"A'a gaskiya, gwara mubarku ku kwana kuna hira, bari mu sauka muyi kallo."
Khairy ta miƙe tace.
"Ina zuwa."
Suhailat ta kama hannun Nadiya tace.
"A'a ki bari Mamy da Dady idan suka shigo sai ku sauka tare."
Bata musaba ta koma ta zauna tana binsu da ido

Please Login or Register in order to submit comment