Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ba mak'wabta bane,naji qauri d'azu tare da gumi yana kusantowa A falon mu, idan bake bace waye? Wuce muje.”
Ya k'arashe mgnar yana kamo hannunta ya nufi k'ofar da ita, sai masifa yake kirta mata.
Ta tirje tana kallonsa tare da fad'in.
”Yaya Abdoul! Kanada imani kuwa? Amatsayin ka na babba namiji wanda Kaine ya kamata ka shiga gaba ka duba me yake faruwa, amman wai kace ni mace zan duba maka? idan lamarin babba ne fa ya girmi tunaninmu? Toh bari naje ni na mutu idan anan ne wutar ta cinyeni.”
Ta qarashe maganar cikin k'ufula tana janye hannunta ta nufi qofar fita, ranta ya b'aci sosai, duk da ta kasance ba mai saurin fushi ba.
Abdoul jikinsa yayi sanyi haqiqa gaskiya ta fad'a shine ya kamata yayi wani abun ba ita ba, sbd tabbas ya tabbata idan wutar a gidansu ne komai zai iya faruwa.
Cikin fad'uwar gaba yabi bayanta da gudu hankalinsa atashe.
Daga can kuwa Abba Aminu kakaf yaji abinda yake faruwa awayan,sabida jifan da tayi da wayan Allah yasa bata mutu ba, yaji har k'aran gaz da duk maganar da sukayi, hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba A take zufa ta karayo masa, ya miqe tsaye daga kan kujeran da yake zaune yana fad'in.
“K'ALU innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fii musiibatihi wakhlifni khairan minha.”
Ya fad'a yana zagaya tafkeken office d'in nasa, sai zufa yake ya kasa kunnuwa bayajin komai alamun sun fita sunbar wajan da suke wayan na yashe a k'asa.

Ummulkhairi na fitowa falon tayi tozali da masifar da tafi qarfinta, sabida baki d'aya wuta tama falon qawanya, ko hanyar kitchen ba'a gani baki d'ayan kujerun falon da duk wani abunda yake falon ci yake da wuta, saura qiris ya k'araso qofar d'akinta.
Sai ta fara jin ihun jama'a ana kishin qofar tasu.
Hannayenta ta d'ora akai cikin masifar tashin hankali ta juya aguje,sukayi Karo da Abdoul yana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fii musiibatihi wakhlifni khairan minha. Ummulkhairi mun mutu shi kenan, ta ina zamu bud'e qofa mu fita? Kinji yadda jama'a suke ihu.”
Ummulkhairi ta rungume Abdoul tana fad'in insha Allahu bazamu mutuba sai kwanan mu ya k'are, kazo hakanan mu laluma cikin wutar mufita don Allah...”
Janta yayi cikin sarewa da duniya suka koma d'akin yana fad'in.
Bakida hankali? Taya zamu iya tseratar da rayuwarmu, kina ganin wuta ta mamaye dukkan falon da hanyar fita? Zo muga ta window toilet kafin wutar ta iso Inda muke.”
Ya k'arashe mgnar yana janta zuwa toilet.
Kuka Ummulkhairi takeyi sosai hankalinta ya tashi ganin wutar fa ba ta wasa bace ba.
Window'n toilet d'in ya shiga qoqarin girgid'ewa amman ya kasa sbd ciwon da yake hannunsa.
Khairy tajasa tana fad'in.
“Muje kawai insha Allah bazamu mutu ba.”
Fizgewa yay yana fad'in.
Bakida hankali ne? Bakiga yadda wuta baki d'aya ta gama kewaye ko ina ba ta Ina zamu tsira bayan nan? Kawai ki Kama mu jijjige window nan, tin kafin wuta ta iso garemu.”
Ba yadda ta iya ta Kama tana rusa kuka suna famar jijjige window, wutar har ta shigo bedroom d'in, abinda da ya sake d'aga musu hankali kenan suka sarewa al'amarin.
Cikin ikon Allah mak'wabtan su biyu suka zagaya ganin 'yan kwana-kwana sunzo ana kashe wutar amman kamar ana qarawa wutar qarfi.
Kuma ba inda wutar ta shiga iya gidansu, ko gaz idan yayi bindiga da yake tafiya wani waje mai nisa kafin ya watse dukkansa,su iya falonsu da kitchen ya tarwatse, shiyasa wutar ta mamaye ko ina ba mafita.
Cikin ikon Allah dasu da mak'wabtansu suka samu suka cire window, Abdoul ya ciccib'a Khairy ta fara fita, mak'wabtan suka taimaka mata suka amsheta.
Shima cikin ikon Allah ya fito Amman baki d'ayan karayar hannunsa ta tashi ta dawo sabowar karaya.
Yana fitowa aguje suka bar wajan su hud'u, sbd wutar ta iso wajan.
Tsabar tashin hankali ba wanda ya lura Khairy towel ne na wanka ajikinta, burinsu su tsira da rayuwarsu.
Lokacin da jama'ar da ta cika qofar gidan nasu suka hango su sun fito tare da mak'wabtansu, ba qaramin farin ciki sukayi ba, suna dab da isowa wajan jama'ar da suke bayan 'yan kwana-kwana suna kuka kawai wayar wuta ta yanke bata tsaya ko ina ba sai a wuyan Abdoul.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Shine abinda tsurarun musulmin da suke unguwar wad'anda suka wajan suke fad'a, baki d'aya kowa yayi takansa ganin al'amarin ba na wasa bane.
Khairy aguje tayi kansa tana ihu tareda kiran sunansa.
“Yaya Abdoul! Ka tashi wai meye hakan don girman Allah..?”
Masu kishin wutar mutum biyu suka riqeta daidai lokacin aka d'auke wuta d'ib, haka lokaci d'aya wutar da ta gama cinye gidan iya na Abdoul kad'ai ta mutu murus kamar d'aukewar ruwan sama, ta cinye komai kakaf babu abinda ta bari agidan sai su da suka fito.
Masu neman ceton Abdoul suka tsayar da qoqarinsu na son ta yadda zasu tsiratar da shi daga wajan, sai dai ya gama jikata babu abinda yake motsi ajikinsa.
Khairy kansa ta fad'a ta ruqumqumeshi tana kuka iya k'arfinta tana kiran sunansa, tare da jijjigasa tana sambatu.
Daidai lokacin motar asbiti da 'yan sanda atare sukazo, aka kwashi Abdoul zuwa asibiti.
Lina ganin Khairy bata hayyacinta haka zata bisu asibitin ta cire rigar jikinta har qasa ta sanya mata. Ita kuma ta tsaya da iya jeans da qaramar riga.

Can Nigeria commissioner Aminu hankalinsa ya gama tashi, tinda yaji halin da yaran suke, wayan tana kunnensa har lokacin da suke qoqarin cire window su tsiratar da ransu.
Anan ne hankalinsa yay mummunan tashi, ya katse kiran,ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kira wata lamba ya jima yana magana kafin daga k'arshe ya fito ya nufi gida, cikin halin tashin hankalin da bai tab'a jin irinsa ba.

*Bayan awa biyu da rabi*
Commissioner Aminu ya gama duk wani shiri ya kuma ji duk abinda yake faruwa daga bakin Johnny, ya kuma amshi dukkan k'adadran da ta tunkarasa.

_Khairy clinic and maternity._

( *Yawwa 'yan uwa afuwan ranan na saka clinic khairy hospital, ban tsaya na gyaraba, afuwan sunan hospital d'in da Shattima ya ginawa Mamy Bilkisu Khairy clinic and maternity*.)

Wani had'add'an office ne ajikin qofar daga sama an rubuta.
_*DR BILKISU BILAL*_
Aqofar office d'in kujeru ne ajere mutane zazzaune suna bin layi d'aya bayan d'aya suna shiga dan ganawa da ita.
Mamy Bilkisu zaune saman lafiyayyar kujerata, ta sha farin glass, ta fuskanci wata mata tana sambad'o mata tambayoyi tana bata amsa, daki-daki tana rubutawa.
Miqewa Bilkisu tayi tana gyara rigar
aikinta ajikinta,tace.
“Muje nagani.”
Ta fad'a tana nuna mata wata qofa, Matar zata Kai shekaeu 33 tabi bayanta.
Suna tashi wayanta ya d'auki ringing, amman ba halin d'auka.
Dukkan jama'ar da suke jiranta sai da ta auna kowa d'aya bayan d'aya, kafin ta samu ta zauna ta duba files d'in wanda za'ama operations.

*Asokoro*
Aliyah ras ta warke sosai umma Sa'ida ta kula da ita, Salim ganin iyayansa sun gama ganosa yaqi dawowa garin, tsabar kunya ya kafe akan shi bai san komai ba akan abinda ya samu Aliyah, sai Hashim yace zai masa mumunar addu'a idan ya kuma cewa bashi bane ya kusanci Aliya kafin aka samu yayi shiru da bakinsa akan cewa ba shi bane ba.
Aliya zaune a falon yanzu ta gama shirya kayanta anjima da sun dawo zata tafi gida.
Tana kallon Tv falon ba kowa, sai ita d'aya.
Kamar daga sama taga Salim sanye da k'ananun kaya, yana dinfaro falon fuskarshi tam a had'e.
Miqewa tayi jikinta na rawa, mugun tsoronsa ya kamata, hanyar guduwa take nema tana kiran sunan Allah.
Hanyar kitchen tayi da gudu sanin mai aiki tana ciki.
Baiyi yinqurin binta ba,da gudu har ta shige kitchen.
Ya kyalkyale da dariya yana tafa hannayensa yace.
“Kaji jakar mata me zan kuma yi dake bayan na shanye roman? Mitsssw!”
Ya fad'a yana zama saman kujera tare kiran.
“Umma! Umma!! Kina Ina?”
Ya k'arashe mgnar yana miqewa ya nufi kitchen d'in.
Aliyah kuwa baki d'aya hankalinta atashe yake batada nutsuwa sai raba idanu take.
Sharifa me aiki ta kalleta tace.
“Aliyah lfy kuwa..?”
Salim ne ya shigo yace.
“Fita Sharifa.”
Aliyah ta zaro idanu tana riqe Sharifa tace.
“Don Allah karki fita ki barni natuba...”
Wata fincika ya mata ya dakawa Sharifa tsawa.
“Ke! Ba cewa nayi ki fita ba.”
Jikin Sharifa na rawa ta fice tana had'a gumi.
Aliyah ta fashe da kuka tace.
“Don Allah yah Salim me na maka aduniya ka zab'i azabtar dani?”
Salim ya matseta jikin kanta ya riqo k'ugunta da hannu d'aya d'ayan ya zura cikin rigarta, ba kunya bare tsoron Allah ya fara lagudata, yana fad'in.
“Wow! Da ace ina sonki ba abinda zai Hana na zauna dake akwai kayan more rayuwa ba laifi duk da baki Kama k'afar Jewel Khairy nah ba, dan haka abinda nakeso dake kice bakya sona araba aurenmu idan ba haka ba zan maidake abar kwatance.”
Ya k'arashe maganar yana qoqarin cire mata riga tare da qoqarin kissing d'inta.
Wani irin k'arfi yazo mata ta ingijeshi sai gashi k'asa wanwar akwance saman tayis, abinka da anyi shaye-shaye ba k'arfin jiki.
A guje tabar kitchen d'in tana fitowa bata tsaya d'aukan kayan jikinta ba ta fice aguje, bata zame ko ina ba sai gate tana fita taci gaba da gudu har ta isa inda zata samu abin hawa.

Shattima zaune a cikin tsararran office d'insa zaune, sanye yake da wani d'anyan boyel Ash colour d'inkin alfarma ya yi bala'in kyau, sosai hular ta zauna akansa, sai wani bala'in kyau da kwarjini da ya yi.
Sakataransa ne Alhj Rabi'u, tsaye dab da makeken tebirin Shattima wanda yake shaqe da takardu, riqe da manyan files, yana rattabo masa bayanai.
Shattima kansa yake jinjinawa yana sanye da farin glass akan kyakkyawar fuskar shi, yana famar rubutu.
Beqa masa takardun da ya cike yay ya amshi na hannunsa ya ajiye, ya masa godiya ya fita ya rufo masa qofar.
Shattima sosai hankalinsa wajan files d'in, yaji wayansa ta d'auki ringing.
Kyawawan idanunsa ya zubama wayan ganin me kiran ya sakashi d'aukan wayan, yana shafa kyakkyawan gemunsa da yasha gyara, zuwa sajansa.
“Assalamu alaiki sweetheart ykk? Y aikin hope ya rage miki?”
Daga can Mamy ta numfasa tana sauke k'aton numfashi, A sayanye tace.
“Mi Amor! Wlh nagaji, ni ba shi ba ma wlh gabana na azabar fad'uwa duk addu'ar da tazo min yi nake amman har yanzu ina fad'uwar gaban, dak'yar na samu na duba jama'a, inata kiran Baby da farko tana ringing ba'a d'auka,yanzu kuma bana samunta.”
Ta k'arashe mgnar kamar zatayi kuka.
Shattima ya furta.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil, sweetheart! Ki nutsu kawai dan kin kira bata d'agaba,daga baya baki sameta ba, ba shi yake nuna tana cikin matsala ba, k'ila network ne, anjima Zan kirata naji ki kwantar da hankalinki kinji sweetheart?”
Mamy Bilkisu ta lumshe manyan idanunta tana sauke ajiyar zuciya, dak'yar ta bud'e bakinta tace.
“Ok mi amor naji amman Sam banida nutsuwa gabana fad'uwa yake.”
Shattima zaiyi mgna kenan idanunsa ya kai kan Tv da take manne ajikin bangon office d'insa, tashar CNN Kai tsaye ana hasko abinda ya faru a Singapore, gobaran da ta rikita jama'a ta d'aga musu hankali da tsoro sakamakon ba gidan da wuta taci sai gida d'aya tak.
Tsaye ya miqe lokacin da aka hasko fuskar Ummulkhairi a hospital, 'yan jarida suna son ji me ya hassasa wutar taya suka tsira daga gidan basu k'oneba bayan gidan ya qone qurmus,ana mata tambaya taqi mgna sai kuka take hannayenta saman kai ta kasa magana burinta ta shiga cikin emergency wajan da aka shigar da Abdoul amman an hanata.
Shattima ya miqe tsaye zufa tana karyo masa duk sanyin Ac'n hakan bi hanasa zufa ba, cikin wani irin saurin magana yace.
“Ina zuwa nayi baqi zan kiraki je kiyi aikin da yake gabanki, but kima kashe wayan baki d'aya har lokacin tashi, zan biyo na d'aukeki.”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran tare da rintse idanunsa,daidai lokacin wayar office ta d'auki ringing alamar sakatarinsa ne.
K'in bud'e idanunsa yay ma bare yaje wajan wayan, sbd yasan bai wuce ace yayi baqo ana son ganinsa,shi kuma a halin da yake baijin zai iya mgna da ko waye banda kiran suna Allah babu abinda yake.
Dogon numfashi yaja tare da fad'in.
“Innalillahi wa'inna ialaihir raji'un! Allahumma ajirni fii musiibatihi wakhlifni khairan minha.”

*Gumel*
Karkasara
Yau an tashi da shirye-shiryen zuwan Usman tin safe girke-girken launikan abincin da aka san Usman naso ake girkawa.
An gyara b'angaransa fes ko ina sai k'amshi yake tashi.
Ana gama girke-girken bayan an jera akan dining area, hajiya Karima akasha wanka akayi shirin tafiya jigawa tarbo Usman acan airport.
Nadiya ta fito falon cikin shiri sanye da wani material mai kyau, da tsada sosai take tsanani kama da usman yayanta, wanda shi kuma mahaifinsu ya d'auko.
Falon ba kowa hakan ya saka ta nufi stairs tana kiran.
“Mom! Kina ina nafa gama shiri wai bazaku fito ba sai guri ya k'ure mana?”
Hajiya Karima kuwa anci ubansu lace na kece raini tamkar wata matar gwamna, tana tsaye tana kallon mijin nata, yana fesa turare a duniya bataga abida take so ba kamar mijinta kyawunsa da nutsuwarsa tare da kamalarsa tana bala'in burgeta, Uwa uba yadda ta mallakesa gaba da baya, take murza kambunta yadda take so.
Murmushi tayi tana fad'in.
“Fulani na kayi fa kyau sosai, ina kishin kwalliyar nan, kawai dai bazance komai ba sabida ina son yaronmu yaga yadda mahaifinsa yake har yanzu ba!”
Murmushi yay yana ajiye kwalbar turaren tare da fad'in.
“Ah iya yi kikafi wayo baki san sauran tattalin miji ba,kina tsaye na gama shirina tsaf ba taimakawa sai iyayain.”
Rai ta had'e tana fad'in.
“Ni muje shirin ne sai na tsaya na maka geme-geme da kai? Haba yaushe ma.”
A qofar sukaci Karo da Nadiya.
Alhaji yace.
“Nadiyata! Kema fa jiya kika zo bazaki huta ba binmu jigawar zakiyi?”
Rungume mahaifinta tayi tana dariya tace.
“Kai! Baba wai kaga kuwa ka zama kamar wani saurayi D'an shekaru 44.”
Karima tace“Dan babanki sai ki auro masa yarinya tinda ni nayi tsufan da bazaki yabani ba sai shi.”
Dariya sukayi ya kama hannunta suna tafe suna hira Nadiya tace.
“Kai Mom kishi me ya kawo wannan mgnar kuma? Ai kinsan dai akwaisu ya kikaga auntie...”
Baki Karima ta buge mata tana huci tace.
“Na rantse da Allah kina mgnar da bata minba bazaki bimu ba, shegiya mai mugun alkaba'i.”
Nadiya taja bakinta tayi gum, salin halin uwar tata.
Ko A mota haka suka d'auki hanyar Dutse ba mai mgna sai Alhaji da yake waya da abokan business d'insa.
Tafiyar 1 hour ta kawosu Dutse Kai tsaye airport suka nufa...


_YI WA KAI...!_

_Free Novel_

*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭



_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_



*P 21&22*


A can Singapore jami'an tsaro ne suka kore 'yan jaridun da suka tisa Ummulkhairi gaba da tambayoyi.
Zaune take ta had'a kai da guiwa tana kuka abin tausayi.
Liza matar Johnny,ta kamota cikin harshen turanci take lallashinta.
“Kiyi haquri Khairy Abdoul zai samu sauqi kiyi masa irin addu'arku, muma munayin namu.”
Khairy cikin kuka tace.
“Aunt Liza! Ya zanyi da raina? Abun yamun yawa,mun rasa gidanmu da komai namu, Abdoul na cikin jinya, sai ga wannan musibar,na rasa lafiyar yaya Abdoul wanda yake tsakanin rayuwa da mutuwa, idan iyayanmu sukaji wannan labarin hankalinsu ba k'aramin tashi zai yi ba.”
Ta k'arashe mgnar cikin matsanaicin kuka, tana rungume Liza.”
Johnny yayi gyaran murya yace.
“Kiyi haquri mijinki zai warke da yarda ubangijin ku.”
Khairy kuka kawai take bata sake ce musu komai ba.

*Nigeria*
Dutse
Kiran commissioner Aminu ya shigo wayan Shattima yana ganin sunansa ya
kasa d'agawa, ya yi saurin d'aukan remote ya kashe Tv'n, dai-dai lokacin
Sakatarinsa ya yi knocking d'in k'ofar.
Shattima yana sharce zufar goshinsa ya bada umarnin A shigo.
Sakatarinsa ne ya shigo ya rusuna tare da fad'in.
“Yallab'ai! Commissioner ne yake son ganinka.”
Dab'as ya koma ya zauna akan kujeran, ba tare da ya iya magana ba ya jinjina kansa alamar ya shigo.
Aminu yana shigowa bakinsa d'auke da sallama ya k'urama Shattima idanu yana zaune, idanunsa sun kad'a sunyi jajir.
Zama yayi kan kujeran da take facing d'insa, yana fad'in.
“Muyi haquri da k'addaramu kallo d'aya na maka nasan kasan komai, dan haka mu fauwalawa Allah komai shine zaiyi mana maganin komai. Na gama shirya mana tafiya mu biyar, ayau jirginmu zai tashi, ka Kira Dr Bilkisu ka sanar da ita please. ”
Shattima ya tsurama commissioner kaifafan idanunsa, ya kasa furta komai, sai kalmar.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Kalmar da yake ta maimaitawa kenan.
Commissioner Aminu yace.
“Abdallah! Don Allah karka sa komai aranka, miyi musu addu'a kayi abinda zakayi, mu wuce.”
Kai kawai Shattima ya jinjina yana cizon lips d'insa na qasa.
Ganin hakan Aminu ya miqe sanin idan har Shattima yana cikin mugun yanayi baya mgna hakan da yake ayanzu idan duk duniya zata taru akansa hakan zai ci gaba da yi, Liman kawai zai iya sakawa yayi mgna ko baya so koda kuwa kukane zai biyo bayan mgnar.
Hannunsa ya kamo ya riqe anasa yace.
”Na tafi gida mu shirya don Allah ka tashi ka tafi.”
Yana idar da mgnar ya sakeshi ya fice daga office d'in.
Shattima kansa ak'asa fuskar Khairy take masa gizo lokacin da take sharb'ar kuka hannunta biyu akai, sai hoton gidan da ya cinye yake masa gizo hakan yana nufin Abdoul ya rasa komai nasa na karatu da yake cikin gidan?
Dak'yar ya miqe tsaye ya nufi toilet dafe da kansa.


Zaman 30 minutes sukayi a airport jirginsu Usman ya sauka a filin jirgin jigawa.
Anutse yake saukowa daga cikin jirginsa,sanye yake da suit baqaqe, yana baqi ne kyakkyawa mai tsananin kama da mahaifinsa, dogo mai d'an fad'i kad'an, ma'abucin fara'a.
A wajan tarbar baqi ya tsinkayo iyayan nasa, yana janye da trolley d'insa.
Nadiya ce ta tarbesa aguje tana ihun murna.
Rungume juna sukayi tana masa barka da zuwa.
Cikin d'okin ganin k'anwarsa ya amsa yana fad'in.
“Nadiya 'yan mata! Zauwan jiya har kika biyo su Baba?”
Ya fad'a yana sakinta ya rungume mahaifinsa, tare da fad'in.
“I miss you my Dad.”
Alhaji Mustapah yace.
“I miss u too my son barka da zuwa ya gajiya?”
Ya amsa yana sumbatar mahaifinsa ya sake shi ya runguma hajiya Karima, yana gaisheta.
Cikin farin cikin ganin yaron nata, ta shafi bayansa tana fad'in.
“Barka da zuwa yaron kirki Masha Allah ka ganka kuwa?”
'Yar dariya Usman yay yana sakin hajiya Karima yace.
“Ngd Mom.”
Mota suka d'inguma zuciyoyinsu cike da farin ciki.
Suna shiga mota direba yaja suka d'auki hanyar *Gumel.*

Dutse Yalwawa.
Aziza tsaye kamar mahaukaciya sai zunduma ihu take da kururuwa, tana kiran Abdoul, tinda ta samu labarin abinda ya faru take kuka harda majina iyayanta sunyi lallashin duniya taqi tayi shiru.
Salisu yayanta ne ya shigo bedroom d'inta a fusace da wayar chaji ya shiga lafta mata tana ihu.
“Dan ubanki mu zaki maida mahaukata? Shegiya wacce bata san ciwon kanta ba,namiji da ya gujeki kike hauka akan abunda ya same shi? Wlh na sake jin kukanki zakiga yadda Zan fasa miki jiki sakara kawai.”
Ya k'arashe mgnar yana zuba mata wayar chajin yana ficewa daga d'akin.
Azizah cikin kuka tace.
“Wlh wannan Khairy ta zame mna musiba annoba, ga shinan abinda wasu sukayi gudu an jajib'a masa ga abinda ya faru nan...”

*Asokoro*
Salim kuwa cikin masifa ya taso lokacin da Aliyah ta turo shi ta gudu, yana zurhuta mata zagi,launi-launi amman kafin ya fito ta arce, ya dinga zazzaga masifa, tare da fad'in.
“Banga uban da zai hanani sakin wannan shegiyar yarinyar ba wallahi...”
Muryan Sa'idah yaji tana fad'in.
“Sai ni dan ubanka, sakaran mutum wanda baisan gata ba, ga shi can ko Ina ka wuce zancan Abdullahi Aminu akeyi wuta ta cinye gidan da suke A Singapore k'urmus dan ubanka da kaine.”
Salim ya k'yalk'yale da dariya, har yana wuntsuwala kan kujera, yace.
“Alhmdllh ai duk wanda ya shiga tsakanina da Jewel Khairy dole zai had'u da musiba iri-iri, kad'an yagani muna nan zai sakomin abata na aure,aure no ban canfata ba...”
D'auke shi da mari Sa'idah tayi tana huci tare da cewa.
“Idan baka gyara kalaman bakinka ba, wlh Zan zubar maka da haqora, zanyi maganin k'aramin haukanka, wuce ban waje.”
Salim baiyi mgna ba ya ciza baki yabar wajan.
Sa'idah ta zauna tana dafe kanta masifar Salim ta isheta...

*Katsina* Malali
Abbu hannunsa d'auke baqar Leda ya shigo gidan tare da sallama.
Zainabu da take zaune a rumfar Inna ADAMA ta amsa sallamar irin ta kurame ta miqe tana murmushi ta nufesa ta amshi ledar.
Abbu yace.
“Ah Zainabu! Sai ke d'aya agidan?”
Kai ta jinjina tana murmushi ta ajiye masa ledar qofar d'akin ADAMA ta kawomasa ruwa ta tsuguna ta ajiye masa, ta koma ta zauna.
Zama yayi yana kallonta cikin farin ciki yace.
“Yara ana islamiyya ADAMA antafi kasuwa?”
Kai ta jinjana.
Abbu yace.
“Naji dad'i yadda naga kin saki jikinki kwana biyu, Allah ya qara baki dangana, ya miki zab'i mafi alkhairi acikin rayuwarki, insha Allahu zaki samu miji wanda ya fiye miki Mustapah insha Allahu addu'ar da muke bazata fad'a k'asa ba, inaso naga k'wanki aduniya Zainabu.”
Hawaye ta share akan fuskarta ta jinjina kanta tanajin wani tsohon miki na taso mata acikin zuciyarta.
Nasiha ya mata yace.
“Akwai wani uban gidana mai taimako sosai, acan ma'aikatar da nake gadi, naga yana taimakon nakasassu inason Zan masa mgna ya taimaka mana kici gaba da koyarwarki koda makarantar gwamnati ne na kuramen kinga kafin Allah ya kawo miki miji zamu samu ki qara warwarewa ko ya kiga gani?”
Zainab ta jinjina kanta ta shiga mgnar kurame da hannunta.
“Toh Yayaba damuwa insha Allah zanyi qoqarin hakan, Ngd Allah ya saka da alkhairi.”
“Ameen Zainabu ba komai kedai kici gaba da haquri tare da addu'a komai zai wuce.”
Kai ta jinjina, nan yaci gaba da mata nasiha,suna hirasu irin ta yaya da k'anwarsa.

Mamy Bilkisu tin lokacin da Shattima ya katse mata kira,yace ta kashe wayanta,zaizo ya kirata taji hankalinta ya kasa kwanciya, amman tabi umarninsa ta kashe wayan, taci gaba da aikinta.
Zaune take tana duba wani files, akayi knocking d'in qofar.
Glass d'in idanunta ta gyara ta bada umarni ashigo,dan tsaf ta gane ko waye sbd knocking d'insa na musamman ne, ta haddace shi.
Bud'e qofar yay bakinsa d'auke da sallama ya danno kansa cikin office d'in.
Fitinannan k'amshin turarensa ya fara kawoma hancinta ziyara.
Ta lumshe idanunta ta bud'e tare da kallon k'ofar ta amsa sallamar,tana ajiye biron hannunta ta miqe tsaye tana sakar masa murmushin qarfin hali.
Murmushin k'arfin halin shima ya mayar mata, yana isowa wajanta.
Jikinsa ta shige tana zagaye hannayenta bayansa, ta sauke wata irin ajiyar zuciya.
Bayanta ya buga kad'an, ya tallabo fuskarta, ya sumbaci bakinta da goshinta, bakinsa dab da kunnenta ahankali ya furta.
“Muje koh?”
Kai ta d'aga masa tana janye jikinta, ta isa wajan table d'in ta tattara kayanta, zuba ajakarta ta iso dab dashi tana kamo tattausa hannunsa tace.
“Mi Amor! Muje koh?”
Kai ya d'aga yana sumbatar hannunta yajata suka fice.
acikin mota suna side bayan zaune hannunsu sarqe da juna.
Bilkisu tace.
“Mi Amor! Akwai matsala koh?”
Wani kallo ya mata wanda ya sakata kwantar da kanta saman kafad'arsa, tana sauke numfashi.
Hannuta ya murza,cikin muryasa mai fitar amon sauti mai taushi yace.
“Sweetheart! Muna zuwa gida shirin tafiya Singapore bana son ki tambayeni dalilin tafiyar har mu isa OK?”
Da sauri ta d'ago kanta ta kalleshi zuciyarta na tsanaita bugawa tace.
“Mi Amor! Wani abun ya samu Khairyn ko? Wlh naji hakan ajikina tin lokacin da na kirata bata d'agaba.”
Ta k'arashe mgnar tana fashe masa da kuka.
Shattima ya sanya tafin hannunsa saman bakinta ya rufe yana buga bayanta cikin lallashi yace.
“please sweetheart ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tayar da hankali bane inaso kiyimin alqawalin bazaki sake kuka ba ko tayar da hankalinki har muje OK?”
Ahankali take kukan bata iya tanka masa ba.

Can gidan commissioner Aminu ma lokacin da ya sanar da Abida taci kuka har ta gode Allah, hankalinta ba qaramin tashi yayi ba.
Haka Maryam dasu Nafisa Habib kuka suke sabida A tv sungani gidan ba dad'i kowa hankalinsa atashe dak'yar yasamu ya musu Nasiha, Hafsatu MATAR kawu Bala tazo ta zauna da yaran kafin su dawo tafiyar kuwa da kawu Balan za'ayita.

K'arfe 6 na yamma abinka da masu akwai an gama komai jirginsu zuwaira Abuja ya d'aga.
8 na dare daga Abuja jirginsu na Singapore ya cira sai muce Allah ya kaisu lafiya Amin.

A can Singapore kuwa Khairy yadda taga Rana haka taga dare,dak'yar take samu tayi sallah, tayi kukan duniya abarta taga Abdoul an hana yana d'akin matsi.
Misalin 9 na safe agogon Singapore.
Ummulkhairi sanye da hijab har qasa wanda Liza ta aro mata wajan mak'wabciyarsu musulma.
Zaune suke a qofar emergency, idanunta akumbure sunyi luhu-luhu kallo d'aya zaka mata dole idan kanada imani ka tausaya mata.
K'ofar room d'in aka bud'e nurse ce ta fito aguje da Dr nurse d'in ta wuce.
Khairy azubure suka miqe ita da Johnny da Liza suka nufosa suna tambayarsa.
“Dr don Allah ya farfad'o?”
Dr Kimu yace.
“Ina Khairy? Da Abba da Ammi? Abdoul na nemansu...”
Khairy cikin rawar jiki tana goge majina, tace.
“Ga ni Dr don Allah muje ka kaini nice dukkan kanbacinsu banason suji sai ya warke.”
Dr yace.
“Muje toh.”
Jikinta yana rawa tabi bayansa tana goge hawayen fuskarta.
Johnny

Please Login or Register in order to submit comment