Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shafa mai ya danya jallabiya milk colour mai taushi ya fesa turare ya shimfid'a sallaya ya tayar da da sallah.
Se k'arfe 3 na dare ya gama ibadarsa yayi addu'o'insa ya miqe ya kashe wutan d'akin ya hauro saman bed d'in, ya kwanta tare janyo Mamy jikinsa ya zagaye hannunsa d'aya cikinta, d'ayan yana yawo da shi akan fuskarta bakinsa dab da kunnenta,ahankali cikin rad'a ya furta.
“Sweetheart! Ya jikin?”
Saukar numfashinta yaji anutse alamar baccinta yayi nisa.
Murmuahi ya Saki na dole ya birkito Mamy suna facing juna, ya sumbaci goshinta, ya rungumeta tsam ya runtse idanunsa, take fuskar Usman ta fara masa gizo.
Ahankali ya furta.
“Ya Allah kasa kamar nan ta kasance ta jini ce Amin Amman zanci quya kafin gaskiya iron wannaan ta bayyana, sai mutum yayi da gaske...”

Washegari har rana Khairy bata farka daga baccin ba, haka Shattima ya sakata gaba zaune yana riqe da hanunta yana tofa mata addu'a,Mamy sosai taji sauqi sbd yadda Shattiman yake kula da ita, yana bata maguguna tare da tsareta taci abinci.


Can Nigeria dutse
Maryam zaune kusa da mahaifiyarta cikin falonsu,ta rabka tagumi abu goma da ashirin, ta rasa yayanta mai k'aunarta mai tattalinta, ga auntie Khairy na fama da laluran hauka, ga rashin Shattima da ya addabeta, duk abun nan yana manne cikin zuciyarta.
Ammi ta janye hannun Maryam daga tagumin, tana fad'in.
“Don Allah Maryam! Ki fauwalawa Allah lamarin nan, nima da na haife shi haquri nayi, mubisa da addu'a.”
Maryam ta share hawayen fuskarta tace.
“Ammi! Bazan iya manta Yaya Abdoul ba,zanci gaba masa addu'a, auntie Khairy kuma Allah bata lfy.”
Ammi ta amsa da.
“Ameen ya Allah.”
Ta k'arashe mgnar tana goge k'wallar idanunta.

Asokoro
Misalin 8 na safe Hashim tare da iyalansa zaune akan dining area, yayi shirin tafiya wajan aiki, ya kalli Salim yace.
“Ka soma shiri mun tsayar da bikin ku wata biyu masu zauwa, sannan maza kana gama breakfast kaje kakai Aliyah asibiti batada lfy, wlh Salim zan maka baki, akan Aliyah, tinda kai d'an isakane Ashe ranan Kaine ka korata gida?”
Salim ya furzar da tea d'in bakinsa ya miqe yana fad'in.
“Kai Father! Wai me akeso Dani ne? Wlh se dai ajira Khairy ta gama takaba a had'a dan wlh Ina sonta...”
Cup d'in hannunsa ya jefa masa ya goce aguje ya fice yana dariya.
Umma Sa'idah tace.
“Zakaci k'aniyarka wlh tallahi ba dai agidan nan, wannan Salim da nasan haka zaka zame mana musiba da tin kana ciki zan Sha maganain zubar ciki nayi fitsarinka...”
Hashim yace.
“Kinbar gini tin ran zane,barni da shi wlh zaici k'aniyarsa Aliyah ce matarsa ko bayaso.”

Salim yana jinsu yabar falon ya nufi b'angaransa ransa b'ace ya warci key ya shiga mota yabar gidan.
Aliyah na kwance sai rawar sanyi take ummunta ta shigo tana fad'in.
“Aliyah kiyi haquri ki tashi ga Salim yazo kaiki asibiti kutafi.”
Cikin kuka tace.
“Wlh ummta bazanje ba gwar na mutu na tsaneshi bashida imani don Allah ummata ki temakeni ki kashe wannan auren...”
Kai Rakiya ta girgiza tace.
“Addu'a kawai zan miki nasan kuma addu'ar mahaifi bata fad'uwa k'asa tashi kuje insha Allahu lfy zai kaiki ya dawo dake kinji?”
Kai ta d'aga tana hawaye, Rakiya ta kamata suka nufo falon...
A mota ko kallo bata ishesa ba da mugunta yake tuqin, sai tayi kamar zata fad'o jikinsa tsabar wuya sai ta riqe kujera, ya k'ure motar da sautin kid'a, ita kuwa se kuka take sbd ciwon kai, har suka isa General hospital bai tankata ba, dan yace bazai kaita private ba.
Bayan an dubata aka mata allurai aka rubuto magani ya siya yana masifa, haka ya dawo da ita gida a gate yatsaya ya wurga mata ledar maganin yana fad'in.
“Se ki fita,kuma ki shirya yarinya na kusa auren wadda nakeso daga ta gama takaba, dan zaman haquri zakiyi damu.”
Aliyah ta kalleshi tayi murmushin k'arfin hal,zuciyarta cike take da k'iyayyarsa,bata tanka masa ba ta bud'e motar tana d'aukan magugunan ta fito ta rufe masa motar ta nufi gidansu.
Baki galala ya Saki yana kallonta ya bushe da dariya yama motarsa key yabar k'ofar gidan.

*Katsina*
Zazzaune suke a rumfa Inna ADAMA tana gyara alayhun da zasuyi dambu da shi.
Jamila tana tsefe kanta, yayin da Zainabu takema Raihana kitso.
Marwan ya shigo yana riqe da hannun 'yarsa Badiyya, bakinsa d'auke da sallama.
Khabir ya zabura cikin murna ya nufi yayan nasa.
Rungumesa yayi yana murnar ganinsa.
Inna ADAMA tace.
“Ah yau de ashe girkin zanyi shi ne da rabon kishiya, ai kam na fasa Jamila zo kiyiwa d'iyarku girki, ni kam bazan ma kishi girki ba.”
Zainabu tayi murmushi tana sakin kan Raihana, ta ta fara mgnar kurame tana ma Marwan sannu da zuwa ta beqawa Badiyya hannu.
Aguje ta iso wajan Zainabu ta fad'a jikinta, ta rungumeta.
Marwan ya k'araso yana murmushi yace.
“Toh inna idan ba'ayi ba dan Badiyya se ayi dan ni dan wuni mukazo mamarta na baya daga gidansu zasu taho.
Umma Zinabu barka da rana.”
Ya k'arashe mgna yana zama.
Jamila da Raihana suka gaishesa ya amsa yana fad'in.
“Raihana! Ummata kikeba wahala koh?”
Inna ADAMA tace.
“Ya jikin Muhseen?”
“Da sauqi da shi ma zamuje juma'a inna inama girki fa mai dad'i.”
Ya fad'a yana ajiye baqar ledar hannunsa shaqe da naman Sa da kayan miya da macaroni Leda uku.
Inna tace.
“Kai Masha Allah Ashe de kishiyata dole taci girkin kishiyarta, Amman fa mu dambu zamuyi mu'ajiye macaronin har yamma koh tin se dare zaku koma?”
Marwan yace.
“Eh hakan ma yayi inna burinmu muci girkinki ko Badiyya?”
Ya tambayi 'yarsa wacce bata wuce shekaru 7 ba tace.
“Yeah Abba.”
Abbu ya shigo bakinsa d'auke da sallama, alamu sun nuna yana cikin farin ciki.
Khaibir ya taresa tare da riqe masa ledar.
Marwan ya masa sannu da zuwa, ya amsa yana fad'in.
“Wai yau ashe ni angone Badiyya! Ina maaman naki da Muhseen?”
Sakin Zainabu tayi ta nufosa tana dariya tace.
“Yawwa Abbu gwara da kazo daman inna ADAMA tace bazata min girgi ba kuma harda nama na kawo.”
Dariya yayi yana kama hannunta yace.
“Kai wace ita da ayau ake wanko min ke na korata ki shige d'akin.”
Jamila ta kyalkyale da dariya tace.
“Aikuwa da taci duka se na ajiye d'iyan can a gefe.”
Abbu yace“Wace ke yarinya. Yawwa Zainab! Munyi magana da wannan mutumin yace ba matsala yau tashi d'aua suke amman zuwa litinin insha Allah yace muje dake ze miki tambayoyi kafin yasan abun yi.”
Cikin murna ta had'e hannayenta tana godiya, tare dama yayanta addu'a.
Yana amsawa da Amin.
Nan sukaci gaba da hirasu daman duk juama'a kafin lokacin zuwa juma'a inna ADAMA tana firkin dambunta.

*Singapore*
Yay kwanansu Shattuma uku, Khairy sauqi za'ace dan ta rage sambatu da buge-buge, idan dai zaka cema Kaine Abdoul zata zauna d'am ta riqe hannunk tana murmushi, haka Shattima yake mata, sosai kuma aka samu ci gaba ta daina bugu har an fasa mata alluran bacci.
Yanzu ma zaune take an sanyama mata hula akanta pink kala, tana sanye da doguwar riga maroon colour, wayar Shattima a hannunta, sai dannawa take ko ina shiga take tana kyakyala dariya se ta tab'a hannayenta.
Mamy tana gefenta nesa da ita tana share hawaye.
Munnir da Auntie Aisha yayun Shattima suna gefenta na dama zaune Aisha addu'a take tofa mata yayin da Shattima da Adamu yayan Mamy suna wajan Dr suna magana.
Khairy tana famar danne-dannen nata ta shiga gallery, tana kallon pictures.
Ganin hotonsu su uku Shattima agefe ita atsakiya mamy agefe ta rungumesu tana kallonsu fuskar Shattima yayin da mamy take dariya yatsarta akan hancin Shattima, suna sanye da shadda ruwan k'asa su dukkansu.
Dariya tayi ta ajiye wayan tana tafa hannunta, ta nuna mamy da yatsa.
Mamy tace.
“Baby Abdoul kika ganine?”
Khairy tayi kiskirin kamar me nazari batace komai ba.
Se ta d'auki wayan ta sake kallon wasu hotunan, karaf idanunta ya sauka akan hoton Usman.
Ihu ta Saki tayi jifa da wayar atake ta tarwatse glass d'inta ya farfashe taci screen, tana fama sauka daga saman bed d'in.
Aisha da Munnir da Mamy atare suka riqeta gudun kar tayi wuff da mutum d'aya dan se yaji ajikinsa, suka riqeta tare da kiran sunanta,tayi wata irin fizgewa tana ihu tare da runtse idanunta tana son yin magana ta kasa.
Shattima ne da Dr suka shigo aguje, jin ihunta.
Shattima yace.
“Ku saketa Baby menene? Don Alkah ki nutsu karki koma baya an fara samun cigaba, taho fad'amin menene ya tsorataki?”
Da kuka ta fashe tana nuna masa wayar ta nufi wajan Shattima da gudu ta fad'a jikinsa ta masa wani irin riqo ta qamqameshi kamar zata koma cikinsa tana fad'in.
“Dady!”
Kashhhhhh! Yau naso zuwa Inda nakeso Amman ina labarin zafi gareshi wollah......😫🥺
Auntie ladingo💃🏻

_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_



*P 27&28*


“Dady! Ka b'oyeni Dodo
nake gani afuskar wayan can, wayyo ya saci fuskata wlh nice sak, Dady! Me nake anan? Ina Abdoul? Don Allah kace bai mutu ba, mafarki nakeyi Dady?”
Ta k'arashe mgnar cikin k'araji tana wani irin kuka, se kuma ta fara qoqarin yakushin Shattiman, zata fara surutan marasa kai bare k'afa, se kuma ta kasa tayi luf k'irjinsa tana wani irin kuka.
Shattima ya riqeta sosai ya tallafo fuskarta cikin tsawa yace.
“Dakata! Baby kalleni ido cikin ido muyi magana karki kuskura ki d'auke idanunki har mu gama magana, idan ba haka ba zaki sani kinsan de halina zan ajiye lelen agefe se na gama ladabtar dake koh?”
Ya k'arashe maganar yana sake riqo fuskarta, ya zuba mata narkakkun kaifafan fararen idanunsa, fuskar shi babu alamun wasa.
Khairy wacce tsoron Shattiman ya gama shigarta, ga tsaretan da yayi da kaifaffun idanunsa, yasa ta nutsu tana kallonsa hawaye ya gama wanke mata fuska, bakinta na rawa tace.
“Dady! Na rantse da Allah yanzu ba jimawa nasan wacece ni, bansan ko na aikata maka laifi abaya ba, kawai naga pictures d'in wani kamarmu d'aya sak. Dady se maganar yaya Abdoul don Allah ya rasu ko duk ciki mafarkan da nayi ne yana raye? Idan yana raye yana ina?”
Ta fad'a cikin shashek'ar kuka, tana kallonsa.
Tafin hannunsa ya sanye ya rufe mata baki yace.
“Shiiit! Baby na yarda tinda har kika rantse, na kuma San halinki tin asali, kawai nayine dan na gwada naji yaushe ne kika dawo hayyacinki, Alhamdulillah,Amman me yasa kikeson sake komawa ruwa? tin jiya na fara ganin alamun zaki dawo hayyacinki, shiyasa na baki wayata ko Allah zai saka ki kalli abunda zai saka ki dawo hankalin ki, ko tunaninki ya dawo normal, kuma Alhamdulillah maganar Abdoul duk mafarki kikeyi yanzu dai nunamin su waye wad'an nan?”
Ya k'arashe tambayarta ya sakar mata fuska, bayan ya goge mata hawayen fuskarta.
Khairy cikin farin ciki ta rungume Shattima tana dariya tace.
“I love you sweet Dady, wlh daman nasan duk abubuwan da suke faruwa mafarki nake se yau Allah ya tasheni,Muahhhh Dady.”
Ta k'arashe mgnar tana sumbatar Shattima a kumatunsa.
Kai ya girgiza cike da tsantsar tausayinta, ya kamo hannunta suka nufo wajansu Munnir.
Wad'anda suka zuba musu idanu cike da tausayin Khairyn.
Munnir yace.
“Abdallah! Afad'ama daughter gaskiya zai fi fa...!”
Auntie Aisha tace.
“Eh daman za'a fad'a bari ta nutsu.”
Shattima yana kallonsu baiyi mgna ba, ya nuna mata Mamy yana murmushi yace.
“Wacece wannan?”
Khairy ta kalli Shattima tace.

“Sweet Mamy mana Dady.”
Sumbatar goshinta yay yace.
“Good Baby, wannan fa!?”
Ya nuna mata Auntie Aisha da Munnir and Adamu yayan Mamy.
Kai ta langwab'ar tana diddira k'afafunta tace.
“Kai Sweet Dady Mummy ce fa da sweet Kawuna M da Sweet Kawu A fa!”
Shattima yace.
“Good Baby Dr a duba mana ita idan ba wata matsala zuwa gobe mu fara shirin tafiya.”
Khairy ta Saki hannun Shattima ta nufi wajan Mamy da gudu suka rungume juna, kamar zasu koma cikin junansu.
Auntie Aisha tace.
“Oh! Mamarki kawai kika gani Ummulkhairi? ”
Khairy ta Saki Mamy tazo ta rungume Munnir ta sakeshi ta rungume Adamu ta sakeshi, ta Auntie Aisha tana kuka k'asa-k'asa tace.
“Mummy! Don Allah ina Abdoul?”
Auntie Aisha tace.
“Daughter don Allah kiyi haquri kiyi tawakli ki barma Allah ikonsa, ki amshi k'addaraki da hannu biyu,kisani ba wanda yake wuce lokacinsa, Abdoul lokacinsa yayi second 1 Allah bazai k'ara masa ba, tinda kin dawo hayyacin ki,ki sani daga yanzu takaba ta hau kanki. Dr please aduba mana ita.”
Auntie Aisha ta k'arashe mgnar tana Jan hannun Khairy tana famar kuka kamar zata shid'e, tana kallon Shattima da Mamy.”
Kai Shattima ya girgiza mata sanin halin yayar tasa bazai ce ya kamota gare shi ba, shi bazai iya da masifarta ba.
Ya k'arasa wajan da Khairy tayi jifa da wayan nasa ya d'auka ta tashi daga aiki se an canza screen, dole zai canza,sbd abubuwan cikin wayan, duk da ba babbar wayansa bane.

Mamy ma hqr take ba Khairy da hannu cike da tausayinta, ganin irin kukan da take.
Dr David ya jona wasu na'urori, ya farama Khairy gwaje-gwaje tsawon 20 minutes, daga qarshe dole ya mata allura bacci marar k'arfi sosai sbd kukan da take tana kiran yaya Abdoul da Shattima and Mamy...
★★★
Bayan kwana biyu
Nigeria Dutse kwance tashi ba wuya har anyiwa Abdoul sadakar bakwai, jm'a na nesa da kusa su watse ciki harda Azima k'anwarsa wacce take aure a Paris.
Commissioner Aminu kullun se sunyi waya da Shattima yaji jikin Khairy, sosai yayi murnan warkewarta, gashi har yau suke tasowa zuwa gida.
Misalin 2 na rana Ammi zaune, tana amsa waya, ita da Azima suke waya kan ta isa lafiya se famar kuja take tana lallashinta. Maryam tayi matashi da cinyarta Nafisa na kwance saman 3 seater tana duba wani littafin addini.
Ammi tace.
“Azimah! Nima de da na haifi Abdoul na haqura don Allah kiyi hqr ki bisa da addu'a Bari kukan kar kanki yayi ciwo.”
Khairy ma yau suke isowa jiki yayi kyau, baiwar Allah se takaba.”
Maryam ta d'ago tana kallon mamar tata, cike da son jin labarin tace.
“Ammi! Su Dady Shattima yau suke dawowa kenan? Toh wa zai musu girki? Bari na d'ora musu girki anan, idan sun iso se na kaimusu koh?”
Ammi bata kulata ba se da ta gama wayan ta kalleta, tace.
“Maryam! Ba wai zan hanaki bane, kiyi hqr har akwana biyu ayanzu suna buqatar hutu ki zauna idan an kwana biyu se kije OK? Mgnar wa zai musu girki kuwa so kikayi ba sunada 'yan aiki ba”
Maryam badan ranta yaso ba ta amsa da.
“Toh Ammi.”
Ammi tace.
“Yawwa Allah ya miki albarka Maryam.”
Ta amsa da.
“Amin Ammi.”
★★★
Da misalin qarfe 9 na dare jirginsu Shattima ya dira Nigeria Abuja.
Auntie Aisha fafur taqi Shatyima su wuce da Khairy tace nan wajanta zata zauna, sbd tace acan bazasu saka idanu akanta ta cika taka yadda yadace ba, sabida shagwab'a, a nan abujan take aure ita.
Shattima ba yadda ya iya ya amince suka barta Khairy tana kuka suka rabu da iyayanta, su suka nufi gida A motar da akazo d'aukansu, su Shattima kuwa suka shige jirgin Dutse.

A dutse kuwa hankalin Salim ba qaramin tashi yayi ba, lokacin da ya gama iskancisa yaje yama Shattima gaisuwa, da ga can bakin gate aka hanashi shigowa, lokacin su Shattima na hanya basu isoba dan Sam Salim baisan halin da Khairyn take ciki ba.

*Gumel*
Karkasara
Usman zaune a falonsa shigowarsa kenan yana waya,agijiye yake sosai sanye yake da suit baqaqe, sum masa kyau sosai se murmushi yake.
Hajiya Karima ce ta shigo falon d'auke da cup ahannunta ta zauna tana murmushi tace.
“Usmanuna se yanzu? Goma ta wuce na dare nagaji da jiranka, yanzu naji qaran motarka.”
Ta fad'a tana zama.”
Usman se da ya gama wayansa ya fuskanci mahaifiyarsa yana murmushi yace.
“Wlh kuwa Mom,ya gida?”
“Lafiya lau?”
Ta amsa tana kafa masa cup d'in abaki tare da fad'in.
“Shanye ruwan addu'a ne.”
Bismillah yayi ya shanye tass yana janye kansa.
Karima tace “Ka taso kaci abinci ko na turo Nadiya ta kawoma?”
Usman ya lumshe idanunsa yace.
“Wlh Mom banida yunwa wanka zanyi na kwanata.”
“Ok se da safe Allah ya tsaremin kai da dukkan abin qi.”
Usman ya amsa da.
“Amin Mom bye.”
Ya miqe zai nufi bedroom wayarsa tayi qara.
Lamba ba suna har zai wuce ya dawo baya, ya d'auki kiran tare da sallama.

Daga can Shattima wanda yake zaune akan sofa A falonsa, sanye da kayan bacci milk colour se baza k'amshi yake yayi bala'i kyau, yalwatacciyar suman kansa se sheqi take, dogayen qaffunsa miqe akan table d'in glass, ya amsa sallamar yana fad'in.
“Usman! Kana magana da minister Shattima Abdallah Umar.”
Usman ya koma ya zauna yana fad'in.
“Yallab'ai barka da dare.”
Shattima ya shafi sumar kansa ya amsa da.
“Barka dai don Allah 'yan tambayoyi nakeso na maka, ko zan iya sanin cikakken tarihinka please? ”
Usman cike da mamaki yace.
“Yallab'ai tarihina kuma? Kodai wani abun nayi makane arashin sani bayan had'uwar airport? ”
Shattima ya furzar da iskar bakinsa yace.
“No! Kawai inason k'ulla alaqa da kaine ta alkhairi, please karka b'oyemin komai naka?”
Usman ya sake gyara zama yace.
“Sunana Usman Mustapah Basiru Niger, asalin kakanina 'yan Niger ne qauyen magaria wata rugar fulani me suna mai maje, mu biyune wajan mahaifinmu nida k'anwata Nadiya, d'aya d'an kishiyar mamarmu an haifesa ba rai ya rasu shekaeu ashirin da d'aya da suka wuce, ko gawarsa auntie amarya bata ganiba aka binnesa lokacin mahaifinmu tafiya ta kamasa baya qasar,daga kansa ba'a sake haihuwa agidanmu ba, mun samu karatun addini da na boko mai kyau, bayan gama jamu'a ta a Abuja na tafi Mexico acan nayi karatuna a fannin aikin gidan wuta NEPA, k'anwata tana karantar communication wato aikin jarida.”
Shattima se da ya kusa fad'uwa, jin bayanan Usman,bai tab'a zaton zai rattabo masa bayanai haka ba.
Shattima ya saita kansa yace.
“Masha Allah sannu Usman naji tarihinka na gamsu, kace Ku 'yan gatane Ku biyu rak haka wajan iyayanku? Inajin labarin Mustapah Niger d'an kasuwa kuwa, toh ngd Usman amman gsky nan dutse zakayi aiki nayi d'a,kuma anan gumel ne k'anin naku ya rasu ko a wane gari?”
Usman yace.
“Toh Dad ba wata matsala ai kune garin se nayi awajanka d'in, A'a wai dutse ne sunje wajan rasuwar kawun Mom d'ita ne ashe wai watan haihuwarta ne ya Kama,acan aka binne...”
Shattima aransa yace.
“Anzo wajan Babyna ba gurb'ataccan jini bace 'yace 'yar halak mai cikakken asali.
Hira sukayi kad'an Shattima ya masa sallama ya katse kiran ya miqe tsaye yana zagaya falon tsaf a iliminsa da Allah ya basa har ya gama gano gaskiyar lamari ba maganar an haifi qaninsu ya rasu ba Khairynsa itace k'anin nasu da akace ya rasu mahaifiyarsa bata ganiba an binne sannan mahaifinsu baya gari... Wato Khairy tana dirowa duniya ta had'u da kaidun matar uba.
Zufar goshinsa ya goge ya koma ya zauna dab'as yana fad'in.
“Allah ya Baku haquri Ummulkhairi ita ce sanyin idaniyarmu ita ce ta rufa mana asiri lokacin da dangina suka uzurama Sweetheart, duk duniya ba wanda yasan hakan,Amman koh bazan nagodema Allah sanin wani na jinin Khairy se dai abadan bazan tab'a bari su had'uba bazan Iya rabuwa da gudan jinina ba Khairy ita ce farin cikina farin cikin Sweetheart, ita sanyin idaniyarmu... ”

*Abuja*
Games villages 12 pm.
Khairy kwance saman lafiyayyan bed d'in Auntie Aisha.
Bayan Auntie ta sakata tayi wanka taci abinci dak'yart, ta nan d'akinta dan tafison duk motsinta akan idanunta, da taso kaita d'akin autarta Ilham wacce bata wuce shekaru 16 ba, ammaan can bazata ga komi Nata akan idanunta ba.
Auntie Aisha na saman darduma tana kallon Khairy se juyi take ta kirata.
“Khairat! Khairy ta kalleta tana matsar k'wala ta amsa da.
“Na'am Mummy. ”
Auntie Aisha tace.
“Don Allah ki ajiye hankalinki har ki kammala takaban ki, Allah ya baki mijinki kiyi aurenki OK?”
Kahiry ta sanya kuka tana fad'in.
“Mummy bana son aure ni na tsani aure, kina ganin yadda abun ya kasance yaya Abdoul ya tafi ya barni,wlh dik da auren had'ine ya azabatar dani naso nayi rayuwa da shi na masa biyayya nasamu lada,ga Nasihar da Dadyna ya min Mummy, amman se gashi kashhh ba'aje ko ina ba mutuwa ta rabamu..”
Ta k'arashe maganar cikin kuka.
Auntie Aisha ta miqe tsam daga saman darduman ta nad'ewa ta cire qaton hijab d'in jikinta ta linke ta sanya jallabiyarta ta bacci ta hauro saman bed d'in ta rungume Khairy tana lallashinta tare da mata nasiha ta d'ora da cewa.
“Idan bakya kuka kullun Zan baki Dadynki da Mamynki ku gaisa.”
Da haka ta samu tayi bacci.

*Commissioner quarters*

Kwance suke sanye da kayan bacci Mamy tana manne jikinsa, kuka take k'asa-k'asa, yayi lallashin duniya taqi.
Shattima ya gyara mata kanta ya maida kan k'irjinsa mai cike da yalwar gargasa, ya shafo hawayen fuskarta, ya numfasa ya had'a face d'insa ya zuro harahensa yana yawo da shi akan fuskarta, tare da sake matsota jikinsa yana matsa k'ugunta, yay gyaran murya can k'asa² ya furta.
“Meye matsalarki ayanzun sweetheart?”
Ya mata tambayar yana mata wani shu'umin kallo kamar bai san matsalarta ba, shi kuma yasan matsalarta amshe Khairy da auntie Aisha tayi ne.
Mamy Bilkisu ta girgiza kanta alamar ba komai.
Sumbatar labb'anta yayi yace.
“Sweetheart! Nasan damuwarki, Baby koh?”
Kai ta d'aga.
Murmushi yay yana yawo da hannunsa sassan jikinta, yace.
“Kinsan yadda Auntie Aisha taken sweet daughter, zatafi bata kulawa akan mu tayi takaba dakyau.
Sweetheart wani abun mamaki nagani wanda har na d'auka picture wani yaro kamarsu d'aya da baby sak kamar an tsaga kara,idanuwansu ne kawai ba iri d'aya ba, amman har yatsun k'afafunsu iri d'ayane, ga katinsa da na amsa d'an gumel ne....”
Kakaf ya bata labarin da Usman ya basa.
Tayi wata irin zabura daga kwancan da take ajikinsa tana riqe Shattima tace.
“Allah da gaske mi amor? Se ta fashe da kuka tace.
“Wallahi mafarkina ya tabbata daman nasan ko bajima ko ba dad'e hakan sai ta faru, anyi min nasiha a mafarkin nan yafi sau nawa akan nayi wannan had'in batada mijin da ya wuceka mi amor naqi, nace sam hakan bazata tab'a faruwa haakan yana nufin tonuwar asirinmu,nasan hakan daidai yake da fitar numfashina,an nunamin duk abinda yake samun mazan da take mu'amula dasu ba daga ita bane k'addarasu ce tazo daidai had'uwarsu, mutanene kawai suke canfa abin ko ince gidan Hashim ne suka canfamin Baby.
Nazo nasa damuwa araina ciwo nacina nabi na rame sabida damuwa,taya za'ace macan da take gidan wani namiji ace nayi qoqarin had'aku aure, sannan duk duniya ba wanda yasan Khairy bamune muka haifeta ba harda Baffa da Inno da iyayena shin ta Ina zan Fara? Ashe ba'a ma Allah wayo, hakan ya saka se nasaka araina inada aljanune ni nasan alqawalin Allah baya tashi, idan Allah yace _kunfa yakul,ba mai cewa LA ta yakul._
Mi Amor kai nakeso ka auri baby da zaran ta gama ta kaba tin kafun maza su mata caaaaa....”

Shattima ya yi wata irin zabura ya ungije Mamy daga jikinsa ya shaqo wuyanta ya kifa mata Mari cikin tsawa yace.
“Ni zaki wulaqanta Bilkisu? Ni kikecewa na auri Baby? Ni D'an iskan wata qasane? ko akundun tarihi kin tab'a jin irin wannan jahilcin da kike shirin yi? Na rantse da Allah ban tab'a ma Ummulkhairi wani kallo na daban ba aduniya bayan d'iyar cikina wacce na duqa na haifeta kamar yadda duniya ta Sani, idan kika sake maimaita min wannan Kalmar Zan Iya tsinke igiyoyin aurena da suke kanki, kakaf zuri'armu ba wanda aka samu da abun kunya se dai ko wasu dangi namu da bamu San da suba na b'oye bare kice danginmu sun Saba abin kunya har zaki kawomin hauka ni Zan auri d'iyata!? Ubanme Zan mata? Ko turzaci da tofin Allah tsine kika shirya janyo mana a fad'in Nigeria? ”
Ya k'arashe maganar cikin k'araji yana sakinta yayi wata irin dirowa daga saman bed d'in da nufin barin d'akin.
Mamy tinda take bata tab'a shiga cikin tashin hankali da musuba ba irin ta you ba, ganin Shattima ya canza mata lokaci d'aya ya zama me mata wani zaki idanunsa sunyi jajir sai huci yake yana dab da fita ta diro cikin wani irin gudu ta ruqumqumeshi ta baya ta fashe da kuka mai bala'in tsuma zuciya tace.
“Don Allah Mi Amor kayi haquri na tuba nabi Allah na bika ka auri Baby wlh ba mai zaginmu ni na....”
Wani irin mari ya sake kifa mata tare da cewa.
“Bakiji nace zan sakeki akan wannan maganar bane?....”
_*YI WA KAI...!*_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_



*P 29&30*


“Idan dai kina k'aunata kina k'aunar farin cikina, sannan kina k'aunar Baby tamkar baya, kin kuma aminta da 'yarmu ce, toh ki rufe wannan maganar karki sake tayar min da ita.
Ki rufeta daga yau bana son ko amafarki ki sake maganar nan, hakan shine zamanmu lafiya ni dake, ke yanzu idan mgnar nan ta fita waje me duniya zata kallemu? Me zamuce ma iyayanmu? Ko kinaso Baby taji zuciyarta ta buga lokaci d'aya? Ni

Please Login or Register in order to submit comment