Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune idar da breakfast d'insa kenan , wanda haka yake daman baya breakfast da wuri ko yanada lafiya, wannan ma sai da Johnny ya matsa masa ganin har lokacin shan nayaman na qoqarin shigowa, ya yardayaci abinci kad'an, ya basa maguguna yasha, ya masa nuna ya beqo masa wayansa.
Wayan ya ciro masa acaji ya beqa masa, da harshen turanci yana fad'in.
“Please bani address d'in gidanku naje anutse nayima iyayanka bayani,sai muzo dasu koh?”
Abdoul ya lumshe fararen manyan idanunsa,baice komai ba, ya shiga ma'adanar lambobinsa,yay dialing number commissioner Aminu.
Daga can Nigeria sun hallara akan dining area suna breakfast, Ummulkhairi kanta aqasa dak'yar take breakfast d'in sabida kunyar surukan nata.
Wayarsa da ta d'auki vibration, commissioner, ya zaro wayan gaban aljihun rigar suit d'in da take jikinsa, ganin sunan me kiran ya sanya shi ajiye spoon d'in hannunsa, ya cira tissue ya goge bakinsa, ya d'auki wayan tare da sallama.
Farar fuskar shi ta gushewa tare da kallon Ummulkhairi yana fad'in.
“Ok karkaji komai.”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran ya ce.
“Daughter Khairy! Idan kin gama ki sameni mota, ina jiranki...”
Ummulkhairi cike da girmamawa ta amsa da.
“Toh Abba.”
Ta k'arashe mgnar tana cira tissue ta goge bakinta had'i da miqewa.
Abinda ta biyosa tana tambayar shi.
“Abban Abdoul lfy? Ina zaka da ita?”
Bai juyoba ya ce.
“Nan kusa.”
Ya fad'a yana tafiya.
Khairy kuwa daman cikin shigarta tsaf take sanye da hijab tama Ammi sallama ta fito.
Motar da taga securities a tsatsaye nan ta nufa kanta a qasa, tafiyarta cike da nutsuwa duk da tana sanye da hijab har qasa, amman jikinta haka yake motsawa kamar tarwad'a masha Allah.
Tana dosar motar ta ga an bud'e mata side d'in baya idan commissioner Aminu yake zaune, riqe da jarida hannunsa yana dubawa.
Da sallama ta shigo zauna kanta k'asa, ya amsa sallamar ya ce.
“Yawwa daughter kin qara so? Garba muje koh.”
Daidai lokacin ne kiran Abdoul ya shigo wayansa.
Bai d'aga ba har direba yaja motar ya nufi gate...
Real Ladingo..

_YI WA KAI...!_

_Free Novel_

*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_

*P 9&10*

Har motar ta hau kan titi lokacin kiran ya katse, an kuma wani bai d'aga ba.
Ummulkhairi ta kalleshi ta ce.
“Abba! Anata kiranka.”
Murmushi yay yana duba jarida ya ce.
“Zan d'auka daughter.”
Kira na 3 ya d'auka ba tare da yace komai ba.
Daga can Abdoul ya yi sallama tare da gaishe shi cikin girmamawa.
Commissioner ya amsa yana fad'in.
“Abdoul! Lafiyar ka kuwa?”
Abdoul ya yamutsa fuska ya ce.
“Wlh Abba na had'u tsautsayi hannuna ya karye, ga ni a hospital amman da sauqi.”
Hankali Aminu tashe ya ce.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!
Abdoul! Accident kukayi ne?”
“A'a Abba...!”
Kakaf ya fad'a masa yadda tsautsayin ya faru, ya d'ora da cewa.
“Abba! Ka kwantar da hankalin ka zan warke insha Allah.”
Aminu ya ce“Wani irin na kwantar da hankalina kana gadon asibiti Abdullahi? Ai yanzu zamu fara shirin tafiya insha Allah zuwa jibi mun shigo har matar taka.”
Ya fad'a yana katse kiran.”
Ummulkhairi ta kalleshi har zatayi magana sai ta k'yale bata ce komai ba, motar su na sharara gudu saman titi.

*Unguwar Takur*

Wani hamshaqin office ne tsararre, banda sanyin A.C da qamshi babu abinda yake tashi a cikin office d'in.
Shattima zaune saman lafiyayyar kujera shi, yana juyi a hankali ba abinda ya masa zafi, waya yake fuskar shi aske yanayi yana k'urbar sansanyan lemon inabi da Mamy Bilkisu ta masa ta turo masa tare da breakfast d'insa, sbd yau fitar sassafe ya yi, tea kawai ya sha.
Yana sanye da wani farin tattausan yadi mai bala'in kyau da tsada, d'inki ya zauna masa sosai a siririn tattausan jikinsa, sai bala'in k'amshi yake tashi ajikinsa.
Abinda zai baka mamaki Salim ne zaune suna facing d'in juna.

(😂Ni kuma nace ya akayi Salim ya samu ganin minister Shattima?).

Ummulkhairi tinda taga wajan da suka zo, tin kafin su fito daga mota da mamaki take kallon surukin nata, ganin inda ya kawota wajan aikin mahaifinta.
Kamar ya sani yayi murmushi lokacin da aka bud'e masa mota, ya fito itama aka bud'e mata tafi fuskarta fad'ad'a murmushi.
Ciki suka nufa.
Duk inda suka gifta sai an gaishe da commissioner, ya amsa A mutunce.
Kai tsaye aka bud'e musu qofar farko suka shige suka haye stairs.
Duk Shattima na kallonsu ta CCTV camera.
Tin kafin su k'araso ya miqe yana amsa waya anutse ya bud'e k'ofar yana jiransu, yay sallama da wanda suke wayan.

Aminu tiris yay ganin Shattima aqofar.
Musahaba sukayi tare da rungume juna.
Ummulkhairi ta gaishe da mahaifin nata cikeda ladabi.
Ya amsa, yana kamo hannayenta yana murmushi, yace.
“My sweet daughter d'iyar commissioner Aminu...”
Salim ya katse masa magana A gabansu suka ganshi, ya zube qasa dab da qafafun Ummulkhairi, ya riqe qafafun nata, yana fashewa da kuka tare da fad'in.
“Dady! Don Allah kamin rai ka raba auren Khairy da Abdoul ka auramin ita,wallahi ina sonta ba laifina bane, laifin Father ne da Umma, su suka canfata ni wlh Ina sonta...”
Kakaf Salim ya zayyana musu abunda iyayansa suka zayyane masa.
Wata irin hankad'a Shattima yama Salim, tsabar jin zafin hankad'ar bai San lokacin da ya saki qafafun Khairy ba.
Ya sake miqewa yana shirin sake riqota, Aminu ya riqeshi tare da kai masa mari yana fad'in.
“Kai mahaukacin inane matar muta ne kake kamawa haka sai kace muharamarka?”
Shattima ya ce.
“Alhmdllh! Koda a kace yana son ganina ban hanaba ya ganni, nasan akwai wani abun kuma zanji a wajansa sabida shi baya rufi, tsaf yamun bayanin abinda ya saka iyayansa qin ya auri Khairy nah, kaji masifar da suka laqaba mata, shiyasa nace kuzo tare komai ayisa da hujja, taji da kunnenta irin gidan masifar da muka so sakata ciki.”
Aminu
Yace.
“Naji nagani Allah ya kyauta, duk duniya ba wanda ya isa ya tsiyata wani ko saka shi acikin musiba da bala'i bayan daman can Allah ya k'addara masa,dan ya jarabeka.
Gaskiya alhaji Hashim yaban mamaki, Allah yasa mudace, Salim kaje kawai amman bakai ba Ummulkhairi, sbd kasan dai matar wanine ayanzu, ba mgnar a saketa ka aura, Khairy bata dace da shiga zuri'arku ba.”

Ita kuma Khairy nan saman tayis ta zube tana wani irin kuka mai tab'a zuciya, tare da jin tsanar iyayan Salim d'in, wato ita ce annobar? Duk abinda ya sameshi ita suka laqama? Allah bazai jarabi mutum ba, sai dole an laqawa wani ace shine.

Shattima ya rusuna ya kamata ya miqe tsaye tana kuka, idanunta akan Salim take fad'in.
“Na godewa Allah da ban aureka ba, kaima ka godewa Allah da baka auri annoba ba, kamar yadda iyayanka suke fad'a, Salim nayi nadamar alaqar baya ma da ta had'amu, kaji wlh ko akan titi ka sake nuna ka sanni sai nayi qaranka,kotu Allah baka wacce ba annoba ba.”
Salim ransa yayi bala'in b'aci yadda dukkansu suka had'u suna daddatsa masa magana, shi kuma yazo a zatonsa zasu ciresa cikin mazu laifi, ashe komai ma akansa zata k'wange.
Had'iye b'acin ransa yay baice komai ba, shi yasan me zai shirya yasan ya zaiyi Khairy ta zama tashi nan bada jimawaba, hakan yasa yana kukan munafurci yace.
“Ku yafemin wallahi banida laifi kuma na amshi k'addarata Ummulkhairi ba rabona bace na haqura, zan zauna da wacce suka auramin.”
Ya k'arashe mgnar yana share hawayen fuskar shi ya tafi.
Shattima ya zaunar da Khairy saman kujera, ya zaro handkerchief ya goge mata fiskarta yana fad'in.
“Kul na sake ganin kukan Babyna akan wannan zuri'ar masu canfi, oya murmushi sweet daughter. ”
Ummulkhairi ta murmusa,yaja dogon karan hancinta.
Aminu yay dariya yace.
“Wannan soyayya ta Khairy da Shattima, yanzu dai dole abarmun 'yata.”
Ya k'arashe maganar yana zama tare da masa bayanin abinda ya samu Abdoul, tare da fad'in.
“Yanzu muna komawa zan Fara shirin tafiya har Kahiry zamuje sai ta zauna acan kafin ya warke.”
Shattima yace.
“Ya Allah! ga shi gobe munada tafiya London, taron k'asa-da-k'asa, amman zamuje dubasa da Bilkisu insha Allah, a gaishe min da shi kafin nazo, zan kirasa anjima.”
Ummulkhairi gabanta haka kawai yake fad'uwa kanta a qasa ta kasa magana sai da zasu tafi tace.
“Sweet Dady! Agaishe min Mamy da Maryam. ”
Murmushi ya mata yana riqe da hannunta ya rakosu har k'asa can wajan motarsu sai da suka tafi ya koma.


Washegari misalin 10 am.
Shattima tsaye gaban dressing mirror sanye da black suit, masu bala'in kyau da tsada.
Bilkisu na fesa masa turare ta wani lab'e a jikinsa, kamar zatayi kuka takeji.
Janyeta yay ya zaunar da ita saman, stool ya rankwafo ya sumbaci kumatunta, qasa-qasa kamar mai rad'a ya ce.
“Shekaru ashirin da uku muna d'aya kin kasa sabawa da rashin mijinki sweetheart, kiyi hkr mana kwana 7 kawai fa wannan Karon, sai dai idan da halin wucewa wani wajan.”
Ya k'arashe mgnar yana manna bakinsa saman nata ya sumbata tare da tsotsar leb'anta na k'asa, ya saki yana murmushi ya beqa mata kumatunsa.
Sumbatar kumatun tai tare da tallabo fuskarshi ta had'e face d'insu anutse ta had'e bakinsu, ta lalubo harshensa ta fara Sha kamar ta samu sweet, tana shafa lallausan suman kansa tana sauke numfashi.
Idanunsa ya zuba mata yana sake matsota jikinsa tare da shafa bayanta, yana bala'in jin dad'in yadda take kissing nasa.

Kusan 10 minutes suna haka kafin ta sakeshi tana maida numfashi ta, gyara masa sumar kasan ta kwanta luf ta miqe tsaye tana kamo hannayensa.
Murmushi yay yace.
“Kalass sweetheart?”
'Yar dariya tayi tana sakinsa tare da d'auko qaramar trolley d'insa, tace.
“Muje karka makara.”
Kai ya girgiza suka fito hannunsu saqale da juna, d'ayan tana riqe da qaramar trolley d'insa.
Haka suka sauko daga upstairs.
Maryam zaune tana kallon TV.
Jin takunsu da fitinannan k'amshin Shattima, ya saka ta waigo ta saci kallonsu ba k'aramin kyau suka mata ba, har batasan lokacin da labb'anta suka motsaba, tana fad'in.
“Ya Allah! Dady Shattima kayi a ko Ina Allah ya barka da Mamy har abadan. ”
Karaf abinda ya shiga kunnuwansu kenan.
Dariya suka mata atare suka amsa mata da.
“Amin ya Allah daughter.”
Bala'in kunya Maryam taji ta sunne kanta k'asa tana murmushi tasan mgnar farko basu jiba amman ta biyu dole suji sbd abayyane tayi ta.
Mamy ta k'walama Harira kira ta iso aladabce ta rusuna tana gaishesu.
“Yawwa d'auki akwatin nan je ki bada asaka a mota.”
Cike da ladabi ta amsa da.
“Toh auntie an gama.”
Ta d'auka ta tafi.
Shattima yace.
“Daughter! Ki zauna da mamynki sai na dawo OK?”
Kai ta jinjina ta kasa kallonsa tace.
“Tom Dady Allah ya tsare ya saukeka lafiya.”
Yana tafiya ya amsa da.
“Amin ya Rabbi daughter.
Bilkisu sai da motarsu Shattima ta bar gidan ta koma tana tsaye can nesa tana kallonsu.
Kai tsaye unguwar Galadanci motar ta nufa gidan iyayansa.
anan rumfar k'ofar gate idan liman da suke zama da muqarrabansa ya samesu.
Bayan sun gaisa suka shiga ciki.
Inno dattijuwa fara kyakkyawa mai tsafta uwar gidan liman Umar, kishiyar mahaifiyar Shattima, mahaifiyarsa ta rasu tin randa yazo duniya ita ce ta riqesa kamar uwar da haifesa shiyasa yake masifar k'aunar tsohuwar.
Zaune a falo suna kallon tv tashar arewa,ita da jikokinta suka shigo da sallama.
Bakinta awashe ta amsa tana fad'in.
“Wlh yanzu kazo min rai nace ajima nasaka akaini na dubo lafiyarka daga can na wuce nago baqar kishiyar nan tawa, duk da ma tabarmin mijina.”
Ta k'arashe maganar cikin raha.
Yaran baki d'aya suka gaishe da Shattima suna miqewa suka bar falon.
Liman yace.
“Idan ita ta haqura ni ban haqura ah toh.”
Shattima yana murmushi ya qaraso ya zauna kusanta tare da d'ora kansa kafad'arta, yana gaisheta.
Kansa ta shafa tana amsawa tare da tambarsa wajan Ummulkhairi.
“Tana lfy inno, ni zanyi tafiya sati d'aya zanyi sai nadawo.”
Ya k'arashe mgnar yana bawa kowannen su, d'aurin 'yan d'ari biyar² na dubu hamsin.
Inno tace“Kajika toh me zamuyi da kud'i bayan ka wadatamu da komai Allah ya maka albarka Abdullahi ubangiji ya tsare gabanka da bayanka.”
Goshinta ya sumbata ya amsa da.
“Amin innota.”
Sun tab'a hira ya musu sallama yatafi suka bisada fatan alkhairi.

A cikin kwana biyun Aminu ya gama shirya musu komai na tafiya, an samu biza su uku zasu tafi.
Mamy Bilkisu na zaune a falo tana ma Maryam kalba, suna hirasu gwanin burgewa.
Maryam tace.
“Mamy! Anjima sai na tafi gida naga su Ammi da auntie Khairy na dawo, tinda Dady yace sai ya dawo daga tafiya Zan koma gida.”
Mamy Bilkisu tace.
“Ai tare zamuje na tambayi Dadynki.”
Qaran danna doorbell d'in falo sukaji.
Kafin Maryam ta miqe Laraba suka hango ita da Harira suna rigai-rigai d'in zuwa bud'ewa.
Laraba na bud'ewa,Ummulkhairi suka gani tsaye sanye abaya red ta yane kanta da mayafin tayi wani irin sahihin kyau, Nafisa akusanta.
Zubewa sukayi zasu gaisheta ta kamo hamnunsu tana had'e ranta tace.
“Wai har sau nawa Zan fad'a muku bana son irin abubuwan nan da kuke min? Kunfa girmeni auntie Harira kefa ko Mamy ta girmeki da kad'an ne, ke kuma Laraba zaki ban shekaru koda biyar ne so kinga ba dad'i kuna k'ask'antar da kanku wajena.”
Godiya suka mata suka shigo falon tare.
Aguje ta nufi wajan Mamy tana ihun kiranta.
Mamy ta miqe tana fad'in.
“Don Allah kibi asannu karki fad'i saman tayis d'in nan mai sulb'i.”
Jikinta ta fad'a ta k'amk'ameta tana dariya tare da fad'in.
“I miss you Sweet Mamy.”
Bilkisu ta amsa da.
“Me too my sweet daughter, amman ya akayi kika fito yau?”
Nafisa ta gaishe da Mamy tana zama kusan Maryam.
Maryam tace.
“Auntie don Allah ki kulani nima.”
Ummulkhairi ta zaki Mamy ta rungumr Maryam tana dariya tace.
”Allah Maryam duk kewar Mamy ne yasa ban ganki ba.”
Mamy tayi murmushi tana Jan hancin Khairyn.
“Mamy Dady ya tafi tin jiya koh?”
Kai Mamy ta d'aga mata, tare da tambayarta.
“Ya jikin na Abdoul?”
Khairy tace.
“Da sauqi anjima jirginmu zai tashi nida Abba da Ammi...”
Maryam tace.
“Wlh nima idan kun dawo sai naje.”
Dariya sukayi.
Khairy ta haye stairs.
Mamy sai da ta bari Maryam da Nafisa sunyi nisa a hirasu ta miqe tabi bayan 'yarta.
Ummulkhairi na bedroom d'inta tana zabar kaya da take buqata, hawaye take sharewa akai aksi, Sam bata son tafiyar amman ba yadda ta iya.
Qaran tab'a qofar da tajine yasa tai saurin goge hawayen da ya gangro mata.
Mamy Bilkisu ta k'araso tana fad'in.
“Karki goge na ganki Baby me ya faru kuma?”
Ummulkhairi ta daure ta saki murmushi tace.
“Allah Mamy ba komi fa! Kawai kewar Dady ne dake.”
Mamy ta kamata suka zauna gefen bed.
Anutse ta fara mata magana.
“Sweet daughter! Don Allah kiyi haquri ki amshi k'addaraki, idan kika nutsu zakiji dad'in zama da Abdoul da Abida har mahaifinsa da k'annensa, sbd mutane ne na kirki masu k'aunarmu, dan Allah idan kuntafi duk abinda Abdoul zai miki na sauyi karki damu ko sakashi aranki, kiyi haquri ki jure kiyi masa biyayya da kulwa da shi ta yadda zaki k'ara kima da daraja wajan iyayansa da shi kansa, ga dubbin lada wajan ubangijin ki.
Wallahi koda baya sonki yanada niyar miki wani abun ab'oye idan kin ajiye hankalin ki kina kyautata masa zakiga cikin ruwan sanyi hankalinsa ya karkata ya dawo wajanki, ina miki fatan alkhairi Khairy.”
Ummulkhairi ta rungume mahaifiyarta tana hawaye cikin kuka tace.
“Nifa Mamy bama batun Abdoul ba maganar da shekaran Salim yaje ya fad'awa Dady a office akaina akan abinda ya saka suka fasa aurena wallahi naji zafi abun ya kasa barin zuciyata...”
Ta zayyanewa Mamy komai.
Mamy hawaye taji ya wanke mata fuska tace.
“Amman Mi Amor bai fad'amin ba, haka suka canfaki? Toh aniyarsu ta bisu, insha Allah babu wani da yake tare dake...”
Ummulkhairi bata bar gidansu ba sai anan sauran awa biyu jirginsu ya tashi suka tafi da Nafisa, tana kukan kewar Mamy, sai da ta saka direba ya biya gidan liman kafin su wuce gida.
Qarfe 3 na yamma jirginsu Ummulkhairi ya tashi, abuja suka tafi daga can jirgin Singapore ya d'aukesu, suka keta hazo... Asauka lafiya.

_YI WA KAI...!_

_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 11&12*


Tafiya mai dogon zango sukayi asararin samaniya, kafin su sauka k'asar Singapore, cikin talatainin dare.
Ga ruwan sama yana sauka kamar da bakin k'warya, ga bala'in sanyi da akeyi.
Rigunan leda aka basu suka sanya, daga wajan sauka zuwa bus d'in da zata kaisu ciki.
Suna saukowa daga jirgi Ummulkhairi ta fara had'e jikinta waje d'aya, sbd sanyi.
Ammi ta riqe hannunta tana fad'in.
“Daughter! Sanyi ko? Na sanki bakya son sanyi sosai.”
Idanunta wanda suke cike da gajiya da bacci ta lumshe, tana tsotsar lips d'inta na k'asa, tana jimamin irin tarbar da Abdoul zai mata.
Daurewa tayi ta b'oye damuwarta a hankali ta furta.
“Ammi! Ashe haka Singapore takeda sanyi...?”

Bayan sun gama duk abinda ya dace na shigowa k'asar,commissioner ya loda musu kayansu cikin abin tura kayan, suka nufi wajan tarbar baqi.
Johnny tinda jirgin ya sauke yake raba idanunsa, ta inda zai hangosu.
Tin 12 na dare yake airport zaune yana jiransu, sbd Abdoul ya mishi bayanin zuwan iyayansa, ya ji dad'i sosai yace shi zaije airport ya zauna har su iso, dan hakanr m Abdoul yama iyayan nasa bayani, akwai wanda zaizo ya d'aukesu,sbd hotonsu Abdoul ya nuna masa awaya kafin ya tafi.
Yana hangosu ya miqe ya nufi wajansu yana washe baki.
Sallama ya musu duk da ya kasance ba musulmi ba.
Commissioner Aminu ya amsa da.
“Wa'alaika.”
Suka gaisa yace.
“Nine Johnny wanda zai d'aukeku zuwa asibiti.”
Aminu bai musaba suka nufi mota, ya bud'e musu suka shiga, Ammi da Khairy abaya shi kusan direba, yaja suka tafi.

Acan hospital kuwa Abdoul ya kasa bacci sai rarraba manyan idanunsa yake, casbin dannawa maqale a yatsar hannun shi mai lafiya yana dannawa, yana istigifar da salatin Annabi.
K'aran tab'a qofa yaji, ya maido idanun kan k'ofar, dai-dai lokacin suka shigo bakunansu d'auke da sallama.
Johnny ne a agaba, Abba na binsa Ammi da Khairy baya.
Amsa sallamar yay cike da farin cikin ganin mahaifinsa, yana qoqarin miqewa, Abba Aminu ya qarasa wajansa da sassarfa, ya dafashi tare da fad'in.
“Zauna mana Abdoul, sannu ya jikin? Allah ya baka lfy.”
Ya amsa da.
“Ameen Abba.”
Ya k'arashe maganar yana kallon qofar.
Idanunsu suka sarqe da na Khairy.
Wata irin fad'uwar gaba ta ziyarce shi, haka kawai yake jin k'unci har can k'asar zuciyar shi, jikinsa tamakar an zuba masa ruwan zafi.
Yay saurin waskewa, ya saki fuskar shi yana mata wani irin malalacin kallo na cikin k'wayar idanu, wanda ita d'aya zata gane me yake nufi.
Ya saki murmushin da yafi na kuka ciwo yana fad'in.
“Ammi! Barka da zuwanku, Khairy sannu ya hanya?”
Ya k'arashe maganar yana kallon Ammi Abida.
Khairy kuwa wani irin bugu zuciyarta ya yi, sbd taga tsaf irin malalacin kallon da ya mata, aranta take kiran sunan Allah.
Fuskarta asake suka qaraso ta rusuna ta gaishesa.
“Yaya Abdoul ina yini? Ya jikin Allah ya baka lfy, ya kiyaye gaba.”
Ba tare da ya kalleta ba ya amsa da.
“Ameen Khairy.”
Ammi ta zauna dab dashi tana kallon hannun da akaima d'orin, tace.
Kamar fa akumbure?”
Murmushi ya yi yace.
“A'a Ammi wannan ai da sauqi sosai ba kamar lokacin da akayi ba. Abba! Ammi! Wannan shine Johnny yanada kirki shi yake kulawa dani tinda tsautsayin ya afkuwa, kawai fa dan 'yarsa tayi jifa da robar ice cream, ai na fad'ama.”
Abba Aminu da harshen turanci yace.
“Johnny! Mungode kayi d'awainiya da yaro, sannu Allah ya biyaka.”
Murmushi yayi bai ce komai ba, yama musu sallama zai tafi.
Abdoul yace.
“Ammi kuje gida johnny ya san gidan, sai kuyi wanka ku huta, kafin sallar asallar asubah.”
Abba yace“Su suje ni sai na tsaya.”
Abdoul yace.
“Ba'a barin majinyace ana kula damu sosai, kuje Abba ka huta please. ”
Khairy dai bata sake yarda ta kalleshi ba, sbd kallon da ya mata ya tsaye mata arai.
Johnny ya kaisu har gidan, Abdoul har yanzu tsula ruwan sama ake.
Hawa na uku Abdoul yake sosai Khairy ta yaba da tsarin gidan, bedroom na bacci biyu sai k'aramin kitchen, da d'an qaramin d'akin da azuba kayan motsa jikinsa, duka d'akin biyu akwai toilet.

Abba Aminu ya shiga d'akin Abdoul su Ammi d'ayan d'akin akwai katifa da zanin gado harda qaramin carpet.
Bayan sunyi wanka sun rama salloli, b'arawo bacci ya sace su ana gab da kiran sallar asubah.

Bayan sati d'aya.

*Katsina*
Unguwar Malali.
Gidane 'dan qarami mai d'auke da soron qofa, daga ciki akwai d'akuna guda uku, biyu ciki da falo d'aya ciki d'aya, sai band'aki atsakar gida, sai k'aramin kitchen, sauran filin bai fi a shimfid'a tabarma babba ba da qarama ba, haka mutan gidan suke rayuwarsu, a tsaftace gwanin sha'awa.
Hayaniya take tashi ta yara karku d'auka yara dayawane, su uku ne kawai. Babbar budurwa ce zatayi shekaru 16 sai mai bi mata bazata wuce shekaru 14 sai namiji d'an shekara 9, amman hayaniyarsu ta cika gidan.
Zaka rantse da Allah ba babba agidan.
Wata mata farar sal, kyakkyawa mai matsagaici tsayi, batada qiba batada muguwar rama, shekarunta na haihuwa bazasu haura 37 ba! Zaune saman tabarma tayi tagumi tana binsu da kallo.

'Yar matashiyar budurawar zaune take rumfar k'ofar d'akinsu, da kayan kwalliya tana cin ubansu makeup, tana fad'in.
“Ke kam Raihana kinyi k'ibar banza kika tsaya Kabir ya tiqaki da k'asa yaron da kusan shekaru shidda atsakaninku, tirrr wlh anyi fad'uwar baqar tasa.”
Jamila ta fad'a, tana kewaye lips d'inta da lipstick.
Raihana tace.
Wlh auntie Jamila idan baki fita ba, daga sabgata kutumar ubanki zanci, yaje ya kayar dani d'in shegiya me bin maza, ina ne zaki yanzu da kike kwalliya?”
Ta fad'a tana cin d'amara.
Jamila tayi dariya tace.
“Na gode Raihana ba maza ba dai bari Abbu da inna su shigo zaki fad'i musu inda kika kamani da maza ni bazan miki komai ba.”
Raihana ta k'yalk'yala dariya, tace.
“Au ashe sharri ba dad'i ranan naji kina gayama Mamah Zainabu.
Shi mutum bashida aiki sai tagumi da zurawa mutane idanu yo Ina dalili, an gaji da yawon karuwanci an dawo gida humm, wlh mudai Allah ya had'amu da masifa da bala'i Ina dalili dangin mayu kawai...”
Kinfa ji abinda kika fad'awa Mamah Zainabu, kin kyauta? Kuma kinsan tana jinki, idan Abbu yaji zai yarda? Wlh sai ya kusa kasheki, k'anwarsa ce fa uwa d'aya uba d'ayakuma kinaji yana cewa su biyun nan su kad'ai Allah yaba iyayansu har suka mutu, gasu basuda wasu isassun dangi.”
Jamila jikinta yayi sanyi ranan bata San me ya hau kanta ba, ta mata rashin kunya, harda laqabata da maita,
Kawai dan tana bugun Kabir ta amshe shi tana mata fad'a da hannu.
Zainabu idanu ta zuba masu.
Jamila tace.
“Ni wlh ranan kamar nasha k'wayane amman bazan kuma ba, idan Abbu yaji Allah kasheni zayyi, Mamah! Ki yafemin kinji? Kar haqqinki ya tambayeni bazan sake ba.”
Ta k'arashe maganar tana isowa wajanta ta kamo hannayenta.
Kai ta girgiza alamar ba komai ta shafi fuskarta, ta yafito Raihana da Kabir da hannu,suka iso ta had'a ta rungumesu ta fashe da kuka.
Suma kawai sai suka saki kukan.
Abbu ne da Inna suka shigo da sallama.
Tiris suka tsaya, suna kallonsu.
Inna tace.
“Zainabu! Me kuma ya faru yaran suka miki wani abun?”
Kai ta girgiza tana sake rungume yaran.
Abbu ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in.
“Haba! ADAMA! Sha'anin Zainabu ai sai dai muyita mata addu'a.”
Ya iso wajan yaran ya sunkuya ya Kama hanunta yace.
“Muje ki kwanta ki huta kinsan dai kanki zaiyi ciwo ko?”
Kai ta jinjina ta saki yaran ta miqe tsaye ya rakata har cikin d'akinta ta kwanta, yace.
“Kiyita salatin Annabi kina yawanta karanta yasin Zainabu Allah ya yaye miki damuwarki.”
Fanka ya kunna mata ya janyo mata k'ofar ya fito.
Inna ta zauna tana fad'in.
“Allah ka shiga lamarin baiwarka ka bata farin cikin duniya da lahira Allah ka cire mata son wannan bawa naka da ta kasa dangana duk da ya mata saki uku ya mata Kora kare.”
Abbu ya amsa da.
“Ameen ya Allah ADAMA, Allah ya bima haqqinmu shine buwayi gagara misali. Ke! Kuma Jamila Ina zakije kike wannan kwaliyan irin ta 'yan daudu?”
Dariya Jamila tayi tace.
”Kai Abbu! Ka manta da safe nacema yaune kamun Bushura k'awata.”
“Wlh na manta toh karki jima dai Allah ya tsare.”
“Ameen Abbu bari na saka kayana.”
Kabir yace.
“Abbu auntie Raihana tacema auntie Jamila karuwa...”
Inna ta zaro idanu tana salati tace.
“A gidan namu ake wannan iya shegen, sbd munje asibiti dubiya? Ga ummanku ba lafiyar da zata Hana?”
Jamaila zatayi mgna taga Abbu ya damqi Raihana yana tsula mata casbi yace.
“Raihana irin tarbiyar da na baku kenan aibata 'yan uwanku?”
Ihu take tana fad'in.
”Wlh Abbu wasane nake mata bazan sakeba.”
Zainab ta fito aguje tana gungunin kurame ta riqe hannun yayan nata ta shiga basa haquri.
Inna Ma'u tace.
“Zainabu da kin bari ya karyata kina ta kanki me had'inki da rabo.”
Hannun Raihana Zainabu ta Kama suka shiga d'akinta, tana lallashinta.Abbu daman akwai rikici ya fara fad'a kamar zai ari baki, Inna kanta bakinta taj ta tsuke sanin halin mijin nata idan ya hau, duk gidan Zainabu kawai zata hana ya hanu.
Ai Jamila sum-sum ta shige d'akinsu tana raba idanu, ta kasa saka kayan ta tafi wajan kamun Bushuran.
★★★

Jigawa.
Commissioner Quarters.
Tin daga falon kake

Please Login or Register in order to submit comment