Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsoron hukuncin da zai yake min baya komai ya faru, yayi binkicen Emanuel ya tattara masa shaidar nice na saka shi. Ya Allah ka kawomin sauqin lamarin nan, Allah kaga abun nan da zanyi sabida had'esu ne cikin sauqi ya Allah idan abin zai zama fitina ka kawo sauqin lamarin ta hanyar da kaga ya dace....” Wayarta ta d'auki ruri, cike da zak'uwa ta d'aga kiran. Daga can wani yayi magana cikin harshen turanci. “Madam wlh ban samo ba, nayi ta bin pharmacy's duk Inda naje sai ace maganin yayi wuya,kiyi haquri.” Mamy bata San lokacin da miqe zaune ba, tana sauke ajiyar zuciya da harshen turanci ta mayar masa. “Ok Emanuel hakan yayi daman an fasama gwara da baka samo ba, thank you so much.” Ta katse kiran,tana sake d'aga hannunta tana godema Allah. Ta miqe ta shiga bathroom.

Washegari da musalin k'arfe 10 na safe Shattima ya fito cikin shiri, sanye da wani irin tattausan boyel fari mai ratsin baqi, d'inki tamkar dan shi akayi yayi bala'in kyau, agogon da yake d'aure A tsintsiyar hannunsa kawai abin kallo ne. Rufaffan takalmi ne a qafafunsa, kyakkyawar baqar fuskar shi na sanye da farin glass wanda ya qara fito da kyawunsa da haibarsa, sai wani irin bala'in k'amshi yake bazawa, yana riqe da wayoyinsa wanda baima kunnasu ba har yanzun. Yana isowa dab da k'ofar d'akin Khairy ya kalla yana shaqo dadda'an k'amshinta, ya girgiza kansa, yasan tana can downstairs. Zaune take saman sofa, ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, cikin shigar rantsatsun wasu English wears ta d'ora after dress, sabida English wears d'in sun d'an dameta sbd yadda ta D'an bud'e kad'an ko ina dum-dum Masha Allah, shiyasa ta d'ora after dress, dan sun jima yanzu ta gansu acan qasa cikin uban tilin kayanta na wardrobe, da Mamy take siyamata idan sunzo Abuja. Sosai shigar tai mata bala'in kyau, sai shegen qamshi take ga sanyin Ac ga k'amshi turaren wutar da ta kunna burner ta zuba,hankalinta kwance take zaune ta hakimce, idanunta akan Tv tana kallon wani film na ibu atashar Africa magic. Daga nesa take jiyo takun saukowarsa. Kyawawan matsagaitan idanunta ta d'ago tana kallon hanyar upstairs. Anutse yake saukowa tafiya mai cike da nutsuwa da kamala, duk qamshin da yake cikin falon dana jikinta bai hanata shaqo qamshin sanyayyan turaren Shattima ba. Hancinta ta bud'e sosai tana shaqar k'amshinsa tin bai iso ba. Kasa haquri tai ta miqe ta nufi wajansa da sassarfa tana fad'in. “oyoyo ga sweet Dady ya sauko, nayi masa girkin breakfast me dad'i.” Ta qarashe mgnar tana isa wajansa, da niyar fad'awa jikinsa yay saurin kamo tattausan hannayenta ya matsar da ita nesa da shi, ya shafi gefen fuskarta cikin tsadaddiyar muryashi mai bala'in taushi tare Jan ajinsa cikin magana mai nagarta yace. “Good morning sweet daughter kin tashi lfy? Hopa bakiyi mugun bacci ba, wuyanki ya qaqe?” Ya k'arashe mgnar yana jan hannunta suka nufi manyan kujerun falon. Cike wata irin shagwab'a ta qanqame hannunsa, tace. “Morning sweet Dadynah, lfy lau na kwana banyi mugun kwanci ba, dady bakace nayi kyau ba.” Wani irin murmushi mai tsada ya Saki saida dimples d'insa ya lob'a ya d'ago hab'arta yana kafa mata kaifaffun idanunsa masu bala'in tasiri azuciyar mata harda mazan tsabar kwarjininsa, cikin taushin murya da wani irin bala'in aji yake fad'in. “Ai ni na haifi abata bana jin akwai watarana da zanga Baby tafi watarana kyau, tin randa kika diro duniya kyan ki bai tab'a sauyawa dadynki ba, kullin baby kyakkyawace wajan dadynta OK ” Ya k'arashe mgnar yana sakar mata lafiyayyan murmushi, ha saki hab'arta yana jan hannunta. Tsalle tayi ta dire tana fad'in. “Wayyo dad'i sweet Dady yace baby Khairy kullun mai kyau Ce, Dady muje kayi breakfast.” Ta fad'a tana Jan hannunsa, dole ya bita kan qaton dining area d'in. Waya biyu ya kunna, wanda basu rufe 30 seconds ba Kira ya shigo cikin Samsung d'in, ya d'aga yana mgna a nutse. Da kanta ta had'a masa tea mai kauri ta ajiye agabansa, tana fad'in. “Dady dan Allah kasha kafin na zuba abinci, kabar wayan Dady, Allah sai ulcer ya Kama min kai zaka saka Mamynah damuwa gani autah agefe.” Ta k'arasa mgnar ashagwab'e tana kallonsa. Kallo d'aya ya mata ya janye idanunsa,kai ya d'aga mata, yana d'aukan cup d'in tea yakai bakinsa ba tare da ya gama wayan ban. Kurb'a yay ya lumshe idanunsa sabida bala'in dad'in tea d'in yaji kanafari da citta ga wadatacciyar Madara da Milo. Ganin yana Sha tayi murmushi tana sunkuyowa ta sumbaci goshinsa tace. “Thank u Daddy. ” Ta fad'a tana bud'e warmers ta zuba masa lafiyayyan sinasir sai wani bala'in qamshi yake tashi. Miyar ganye taji nama rago ta zuba masa, ta ajiye gabansa, tana zubo masa soyayyen dankalin turawa ba kwai sbd baya son abu mai k'wai Sam baya ci haka ta soya masa, da cinya d'aya tak,sbd bata fiye son kaza ba ita kuma. Zama tayi tana kallonsa kamar zatayi kuka tace. “Dady! Please mana kaci.” Kallonta yay yana katse wayan, ya harareta tare da Jan dogon hancinta yace. “Baby! Ni dawa zamuci duk girkin nan? Kenan bakiji maganata ba da nace miki ki bari kar kiyi girkin Emanuel zaiyi kin qi koh? Toh sannu Allah miki albarka Baby, ke kinci koh?” “Ameen Dady eh naci tin yaushe ma, ai wlh ba qaramin dad'i najiba ganin akwai komai a kitchen na buqata, da Rana ma ni zanyi Dady.” “No! Baby ki huta kinga yanzu idan na fita sai yamma ko dare, yanzu zamu biya na kaiki gidan Auntie Ok?” Ya idar da mgnar yana kai sinasir d'in bakinsa, ya lumshe idanunsa yana ya fad'in. “Allah yama sweetheart albarka da ta horamin yarinya da iya girki surukina zai sha girki mai dad'i.” Ya k'arashe mgnar yana kallonta, takwanto da kanta kafad'arsa, ta saqala hannunta d'aya wuyansa tana kuka marar sauti harda shasheqa. “Uhmm!” Ya fad'a yana kai loma ta biyu tare da k'atuwar tsoka yana taunawa yana kallonta, murmushi na sub'uce masa, dan tsaf yasan kukan nata bai wuce bazataje gidan Auntie Aisha ba. Yaso yayi banza da ita zuciyarsa ta gasa haqura ya ajiye spoon d'in ya d'agota yana goge mata hawayen fuskarta cikin taushin murya yace. “Shi kenan naji bazaki koma ba, yi shiru to na gama breakfast anutse, idan kuma bakya son naci na bari na fita da yunwa Ok?” Shiru tayi ashagwab'e tace“Nayi shiru dady kaci dayawa.” Ta fad'a tana lab'e akafad'arsa tana cusa kanta k'afar tasa. Yana cikin cin abincin kafin ya gama yayi waya tafi goma dak'yar ya samu ya gama, suka dawo falon,samun waje yay ya zauna sai da ta sake sosai hankalinta wajan kallo, ya miqe ya kamo hannunta yace. “Oya muje mu gaisar da Auntie ki zauna da yamma zanje nad'auki Ok?” Baki ta zumb'uro gaba tana shirin fashe masa da kuka ya had'e gira sama da ta qasa yace. “Ina wasa dake ne? Ko idan nace a can zaki zauna kin isa ki qi zama?” Kai ta girgiza ta sakar masa kuka tana shigewa jikinsa, tana kuka kamar ance Mamy ta mutu, haka kawai taji bata son matsawa daga kusan Dadynta. Wata qatuwar ajiyar zuciya ya sauke tare da Jan dogon numfashi, yana lumshe kaifafan idanunsa cikin kamewarsa sauti mai taushi yake fad'in. “Ya Ilahi! Baby me hakan? Shi kenan kar naje abinda ya kawoni garin na zauna na sakaki gaba? Koh na dinga yawo ziyara da meetings dake?” Kai ta d'aga masa alamar “Eh” Sihirtaccan murmushi yay ya janyeta daga jikinsa, tare da riqo fiskarta ya share mata hawayenta, yace. “uhmm! Baby kenan oya jeki d'auko hijab a tarin hijab d'inki na nan ki saka mutafi bana son kice komai kiyi yadda nace OK?” Marairaice fuska tayi tana kallonsa ta d'aga kanta tana sakin hannunsa ta nufi upstairs. Kai ya girgiza ya zauna yana d'aukan iPhone d'insa, ya lalubi lambar Mamy ya danna mata kira. Tana zaune office tana famar duba files, kiran ya shigo. Ganin Shattima ne ta d'auki wayana kai tsaye tare da d'aga kiran,tana sallama, ta d'ora da cewa Mi Amor barka da safiya ka tashi lfy?” Shattima ya amsa sallamar yana amsa gaisuwarta, tare tambayarta. “Sweetheart! Fatan kina cikin k'oshin lfy? Fatan ana missing d'in Shattima? Shi kam ga shi nan kamar zai haukace sabida rashinki.” Yadda ya mata mgna abun ya bata dariya, ta murmusa tana fad'in. “Kai mi Amor wlh kaban dariya ai missing d'inka kamar zai rabani da numfashina, nakeji I love you Mijina.” Idanunsa ya lumshe yana wani irin murmushi na jan aji yana shafa sajansa yace. “Ngd sweetheart I love you too, insha Allah ina tafe ki shiryawa mijinki na ke d'aya har abdan kamar yadda kema tawace, ina tafe kwananan.” Mamy ta lumshe idanu tana sauke numfashi ta tattaro jarumtarta tace . “Mi Amor ni dai ba ruwana yanzu fa ba ni kad'ai bace mai kai.” Ta k'arashe mgnar tana murmushi. Shattima yaja guntin tsaki yana fad'in. “Ai sai kimin auren wlh karki sake min irin wannan shirmen, ni kam me zanyi da mata bayan inda ke wlh ba wata mace da zata burgeni, dan kece ma Zan barki ba tare da na d'auki mataki ba, aure yana burge wasu mazan ne idan basuyi dacan mace ba, ko rashin gamsuwa ko qazanta ko rashin hali me kyau ko rashin iya girki ko wacce bata ganin girmanka dana iyayanka dai sauran halayyar mata toh ni banci karo ko d'aya daga cikin abubuwan dana lissafo ba, ni karo nayi da mace tagari kyakkyawa mai kunya da addini da sanin yakamata, 'yar fara siririya nagartacciya wacce tasan darajata da ta iyayena, take tattalina ta ko ina bata gajiyawa dani ta ko ina tattalina take duk wani abun da yafito daga wajena tana kulawa da shi da basa daraja, ta haifamin kyakkyawar baqar 'yata, ni kuwa me zanyi da wata mace aduniya me narasa wajanki? Toh wlh zami samu matsala idan kika sake min mgnar wata mace bye Zan kiraki Zan fita yanzu inada meeting. ” Mamy baki d'aya jikinta yayi sanyi yabon da ta samu awajansa wanda ba sabin abu bane amman na yau yasha banban, kawai sai taji kuka ya k'wacemata tabbas tasan Shattima yana sonta so sosai ma, Amman nan gaba kad'an dole zai raba musu abiyu itada Ummulkhairi. Shattima ya lumshe idanunsa jin sautin kukanta adodon kunnensa. Ahankali ya furta. “Sweetheart! Please kiyi shiru me na miki kuma? Kinsan dai bana k'aunar kukan ki koh?” Kamar yana gabanta ta d'aga kanta,tana qoqarin had'iye kukan, tace. “Mi Amor Baby fa? Bani ita zamuyi magana, bamu gaisa ba.” Shattima zaiyi mgna Khairy ta iso nesa da shi ta tsaya, tana turo baki. “Gata nan zamuje na sauketa gidan Auntie Aisha. Baby zo mana Mamy Ce...

Ladingon Farisatourh

*YI WA KAI*

Free Novel

_November 3/11/2022_



*49&50*

Da sassarfa ta iso wajan Shattiman, ta zauna kusansa, tana amsar wayan. “Hello sweet Mamy! Ina kwana? I miss you so much billahi.” Mamy daga can tana murmushi tare da goge hawayen kukan yabon da ta Sha wajan Shattima. Ta saita nutsuwarta tace. “Baby I miss you too, hope kin tashi lfy Dadynki yana kula dake? Me kikaci?” Murmushi Khairy tayi tana kamo hannun Shattima d'aya, tana wasa da zoben gold d'in hannunsa, tace. “Ina lfy Sweet Mamy, wlh sinasir nayi mana da miyar ganya kinji dad'in tambayi sweet Dady kiji.” Shattima ya girgiza Kansan yana zame hanunsa ya miqe yana fad'in. “Baby ki sameni amota idan kun gama.” Kai ta d'aga masa tana sauraron Mamy tana mata mgana. “Baby! Yaushe zaki dawo ne? Kinbar Mamynki cikin kewarki?” Khairy tace. “Yawwa Mamy wlh Dady zan biyo mu taho tare.” Mamy tace. “Ok baby sai anjima ina hospital ki gaishemin da auntie Aisha, ban saniba zuwa gobe koda yamma su Madinah zasuje dubaki yau suke shiga Abuja.” Khairy tace. “Allah kawosu lfy wlh bakiji dad'in da naji ba, Mamy.” Dak'yar Mamy da Khairy sukayi sallama. Tin kafin ta iso aka bud'e mata qofar motar, ita kuma anutse cikin milk d'in hijabin take tahowa tamkar tarwad'a, tana isowa ta shige gidan bayan ta zauna kusa da Dadynta, aka rufo motar. Kallon Shattima take yadda ya kame cike da nutsuwa da kamun kai yake amsa wayan, hannunsa d'ayan riqe da news paper yana jujjuyawa, yana magana har Maleek direba yaja motar ya nufi tamqameman gate d'in gidan yana zuba horn. Khairy ta jingina kanta da kafad'ar Shattima, tana shaqar fitinannan k'amshin sa, wanda ya baibaye motar ya had'u da sanyi A.C ga k'amshin turaren motar na musamman. Kallon kyakkyawan bakinsa take mai tsari da sanin me yake fitowa daga cikinsa, yana mgna anutse, da harshen turanci, wani bala'in na fitowa daga ciki. “Ka tabbatar da abinda kuka bincika hakane?” Ya k'arashe tambayar yana kallon Khairy da take kallonsa, ya hura mata iskar bakinsa, yana janye idanunsa yana maida hankalinsa wajan wayan. “Ok toh na gamsu kubar binciken haka daman dan na tabbatar ne bye.” Ya fad'a yana katse wayan. Khairy ta langwab'ar da kai ashagwab'e tace. “Please sweet Dady ka ban wannan wayar.” Kallonta yay yana janye idanunsa akanta yace. “No! Baby zan baki amman ki d'an jinkirta OK?” Baki ta zumb'uro gaba, tana kamo dukkan hannayensa idanunta sun tara kwallo tace. “Dady don Allah watana 9 banida waya kabani ni dai ita nakeso.” Ta fad'a tana sakar masa kukan shagwab'a ta saki hannunsa ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta. Shattima murmushi yayi na gefen baki yana shafa sajansa, can qasa-qasa cikin kamewarsa ya furta. “Zamu wa zakima rigiman banzan idan kin tafi gidanki, rigimammiya kawai, waya je ku qarata keda ita ciromin Sim card na auntie ta siya miki layi kafin mu wuce gida.” Da wani irin murna ta d'ago kukan ya koma dariya ta qanqame hannyensa tana fad'in. “Thank you my sweet Dady much love, ni dai Dady kai zaka siyamon Sim card da kanka kaji?” Ta k'arashe mgnar cikin zallar shagwab'a tana langab'ar da kanta gefe. Hararanta yay yana zame hannunsa, anutse yace. “Ni yaronki koh?” Dariya tayi tana kiciniyar fito da layin na Shattima daga wayan. Amsa yay ya cire da kansa ya gogo komai lambarsa da ta Mamy and Liman su Aminu ya barmata ya shafe komai nasa ya dingura mata wayan yana fad'in. “Gata mabaraciya.” Dariya tayi tana kissing wayan... Ahaka suka qarasa gidan Auntie Aisha. A gate motocin suka tsaya aka bud'e musu suka fito Khairy na maqale da hannun Shattima, ranta fari qal tayi waya wuleliya sabuwa, dan baiyi wata da siyanta ba. Ilham na tsefe Mummy kanta sabida yau weekend ne, sukaji sallamar Khairy aguje tana kiran “Mummy! Kina ina sweet Dady yaban sabuwar waya billahi.” Ta k'arashe magnar tana fad'awa jikin Mummyn. Ilham tace. “Wow! Auntie Khairy! Wannan zabgegiyar Samsung? Kawai k'wace kikama Dadynmu.” Dariya Khairy tayi tana kallon Mummy tana fad'in. “Bakyaji Khairy d'agani karki karyani irin wannan dira samana, shine jiya kika sakamu tashin hankali koh? Ina Shattiman?” Khairy ta miqe tana fad'in. “Yana k'ofar falo wai sai an masa iso. ” Ta idar da maganar tana nufar hanyar falon. Kallonsa tayi yana amsa waya ta kamo hannunsa tana jansa tare fad'in. “Kai Dady wlh kunnenka sai yayi ciwo kowane lokaci waya, ni dai kar a b'atawa sweet Dady kunnensa.” Kai ya girgiza yana biye da ita kamar raqumi da akala. Ilham aguje ta nufosu tana masa oyoyo. auntie Aisha ta amsa sallamar Shattima tana fad'in. “Khairy! Kece bakya barin Shattima yayi k'iba, kamar chingum kike. Abdullah barka da zuwa.” Zama yay saman kujera 1 seater yana katse wayan ya gaishe da yaayar tasa cikin girmamawa, yana murmushi ganin yadda take wanke Khairy, k'ilama wayan k'wace tayi masa. Lemon da Ilhma ta tsiyaya masa ya kurb'a yana fad'in. “A'a fa Auntie ni na bata ba k'wace tayi ba, ya su Suhal ko bai tashi ba? Ina Marfu'ah? Tasha kuka ko? Baby ai bataji tare zamu wuce Jigawa satin sama ida na kammala uzurina.” Auntie Aisha ta zunguri Khairy tana fad'in. “Wlh nima nayi kuka ba Marfu'ah kad'ai ba! 'Yar mutane ta b'ata ina nake shiga ai Baffa kad'ai ya isheni.” Murmushi Shattima yayi. Fira kad'an sukayi ya miqe yamusu sallama kud'i mai yawa yaba ilham yace tasha ice cream, suka karakashi har gate, Khairy tana masa bye, daman yasan tinda ya bata waya bazatayi kukan rashinsa ba! Ai kuwa aranan aka siyo mata Sim card, ta Kama kiran 'yan gidansu Dadynta dana su Mamy duk wanda Mamy ta turo mata lamba sai da ta Kira, k'arshe ta Kira Suhailat suka Sha fira. ★ Misalalin qarfe 2 na rana su Abbu suka iso garin Abuja, tarba mai kyau suka samu daga wajan uban gidan nasu, abinci mai rai da lafiya sai da suka Bari. Washegari akayi d'aurin aure bayan sallar azuhur, su kuma ana la'asar suka d'auki hanyar kataina tare da adsu'ar sauka lafiya sabida yadda hanyar bata kyau. Cikin hukuncin Allah kuwa suka sauka katsina lafiya wajejan 10 na dare. Karkaso kaga murna wajan Inna ADAMA dasu Zainabu da Jamilah, dan Khabir da Raihana sunyi bacci. Inna ADAMA tana ajiye masa ruwa mai sanyi a cup d'in silver, take fad'in. “Wlh babansu tin d'azu nakema Zainabu mita akan tafiyar Daren nan hankalina ya kasa kwanciya, Alhamdulillah tinda kunzo ladiya anyi sabga lfy.” Murmushi Abbu yayi yana d'aukan cup d'in ruwan yasha ya ajiye, yace. “Wlh lfy lau muka zi ba wata matsala anyi sabga lfy an tashi lfy. Zainabu ya gida? Da aiki kuma?” Kai ta jinjina tana amsa masa lfy lau, ta shiga masa hira da bebancin. “Yaya muma zamuje taro na malaman makaranta na kurame a jigawa k'arshen wata kwana uku za'ayi ana gudanarwa insha Allah anan Katsina mu 10 aka zab'a daga makarantu daban².” Kasancewar Abbu yama hira Zainabu farin sani tin daga lokacin da abin ya sameta tsawon shekaru ashirin da biyu, tsaf ya fahimci maganar tata, yace. “Masha Allah, ubangiji ya kaimu lokacin nan da kwana 15 koh?” Kai Zainabu ta d'aga tana miqewa ta shiga d'akinta tana murmushi sabida tinda aka ambaci tafiyar takejin bala'in son tafiyar kamar ta matso nesa tazo kusa takeji. Inna ADAMA ta zobo masa abinci yana ci suna hira da Jamilah wacce take basa labarin Badiyya d'iyar yayanzu Marwan.... ★ Bayan kwana 10.

Aliyah zaune ta kafawa idanunta Tv sam batasan me akeyi ba, tsabar tashin hankalin Salim, ga laulayi abun ya zame mata biyu, magani idan ya bata tasha maqaleshi take qasan harshenta bata tab'a yarda ta had'iye ba, dan bazatayi kisa ba. Daga bedroom ya fito yana kallonta, yaja tsaki yace. “Anyama kina shan maganinan dan ubanki? Kazar banza kawai sai d'aukan ciki dududu sau nawa ne nayi da kika tare idan ba jarabarki ba? Amshi kisha wannan jiqon ancemin kalfiyan ne zai zobe nan da 24 hours.” Miqewa tayi tsaye tanaja baya hawaye ya wanke mata fuska tace. “Amman dai agabanka nakeshe koh? Wai so kake sai na mutu ko me? Idan baka son zama dani ka sakeni kawai Yaya Salim ba dole fa! Amman wlh nagaji nagaji wace irin rayuwace wannan saboda Allah...” Cikin zafin nama tare da b'acin rai ya fizgota zai d'auketa da mari, yaji ana knocking d'in k'ofar falon. Cike da tsoro ya saketa yana fad'in. “Wuce ciki munafuka, amshi cup d'in d'akinki ki shanye.” Ya bata ya nufi k'ofar.... Kusan suman tsaye yayi ganin umma Sa'idah kamar an jefota, kallon da take masane yasha jinin jikinsa, yana rarraba idanu yace. “Sannu Umma wuce mana.” Shigowa tayi tana kallon Aliyah wacce ta nufi bedroom da Sauri. “Dakata! Aliyah.” Can ta tsaya tana fashewa da kuka. Gabanta ta zagayo tana tafa hannayenta ganin irin ramar da Aliyah tayi, tace. “Bakida lafiya ne?” Salim yayi karaf yace. “Wlh batada lfy umma basir yake damunta, yanzu ma magani na had'a mata.” Aliyah ta kalleshi da sauri kuka na k'wace mata, tace“Wlh umma Salim kasheni zaiyi dan Allah Ku rabani da shi maganin zubar da ciki kawai yake bankamin wai bayason haihuwa...” Zaiyi magana ya nufota cikin b'acin rai Umman ta d'auke shi da mari tana fad'in. “Karnaji bakinka wajan nan d'an iskan yaro kawai, Aliyah fad'amin duk abinda yake miki.” Cikin kuka ta zayyano mata komai. Umma Sa'idah ta Kama hannunta tace. “Muje tinda d'ane bakaso mu munaso zamu kula da ita har Allah ya sauketa lfy zakaci ubamka Salim damu kake zancan wlh.” Ta fad'a tana amsar cup d'in hannunta tayi jifa da shi tajata suka fice Salim yana tsaye kamar gumki dafe da kumci. Suna fita yaji ransa yayi bala''in b'aci Amman ya dake ya zauna ya zaro sigari ya kunna yana zuqa yace. “Wlh duk Randa Nagano mijin Jewel Khairy sai na kasheshi dan ubansa, Aliyah zakici uwarki ba kin had'ani da iyayena ba! Hummmm!”

Misalin 1 na rana yau ta kama weekend Mamy tana gida, ta gama girkin tarbar Shattima da Khairy dan yau suke dawowa. tsaye take a bedroom d'inta, gaban tafkeken dressing mirror sai sake shafa humrah take lungu da saqon jikinta. Wani rantsantsan lace mai bala'in taushi ta saka, baqi ne mai adon flowers pink yaji duwatsu, manya dinkin doguwar riga mai fad'i daga k'asa saman ya d'an kamata qaramin k'ugunta ya fito, ba wanda zai kalli Mamy yace tayi shekara 41 a duniya, tsabbar kyan jikinta da kuma qaramin jikinta. Ta murza d'aurin d'an kwali na zamani wuya da hannunta sunsha sarqar gold sai k'yalli take, tayi simple makeup, Sosai tayi kyau, takalmi flat baqi ta saka ta d'auki siririn mayafi baqi ta d'ora akafad'arta ta d'auki wayanta ta sauko qasa. Sabida tana fashin sallah. Tv ta kunna tashar Mbc action. Laraba ta kirawo ta kunna burner ta zuba turaren wuta mai qamshi wata Kala daban ba irin na d'azu ba, ko ina bala'in qamshi yake tashi ba falon ba har wajan falon duk girman gidansu qamshi yau tashi yake,akowane kusurwa. Wayar Mamyn ta d'auki ringing ta kalli wayan sunan Mi Amor taga yana yawo akan screen wayan. D'auka tayi kai tsaye ta d'aga kiran tare da sallama. Shattima da yake zaune hakimce acikin mota side d'in baya sanye da wata rantsatsiyar shadda fara qal, yayi wani bala'in kyau, da haske baqar fatar tashi ta qara wani irin qyalli, Khairy kusansa zaune tana famar chat da k'awayenta, ya amsa mata sallamar tare da fad'in. “Gamu muna bakin gari sweetheart mijinki yunwa ga gajiya ki shirya kafin ya shigo gidan OK? ” Mamy tayi murmushi tace. “Wai da gaske kuwa ba jirgin kuka shigo ba a mota kuka zo? Sannunku ina Baby? Mi Amor komai ya kammala sai kun qaraso ina jiranka komai zaka samu nawan.” Murmushi yay yana kallon Khairy da take famar chat batama San yana wayan ba. “Ngd sweetheart sai na qaraso ba!”. Ya fad'a yana katse kiran. Mamy ta murmusa tana ajiye wayan saman center table ta miqe cike da murna. After 18 minutes. Wata rantsatsar mota ce ruwan qasa ta zamani ta mata, tayi parking k'ofar gidan minister. Sojejin da suke shawagi a qofar gate d'aya ya iso kusan motar daidai lokacin direban ya janye glass d'in motar. Sojan yace. “Wajan wa kuka zo?” Direba ya fito ya bud'e ma Hajiya Karima qofa, tana hakimce acin ubansu lace mai tsada da kyau ansha daham wuya da hannu,haka itama Hajiya Shaheedar, Karima ta leqo tace. “D'ana wajan Hajiya Dr Bilkisu mukazo Matar gidan, munzo godiyane Amman batasan da zuwan mu ba.” Sojan yace. “Ah toh sai kuyi haquri ba'a zuwa wajanta ba saninta ba'a bamu ikon bada izinin ad'aga muku gate Ku wuce ba...” Ranta ya b'aci amman sai ta dake tace. “Ayi haquri kirata ka shida mata idan tanada daman sai mushiga.” Kiran lambar Mamy yayi lokacin tana dining area tana qara gyara wajan, da kanta, taji qaran wayan tazo ta d'auka. “Agaskiya banida sanin ko suwaye ga shi yanzu minister zai shigo,amma kuma wulaqanta d'an Adam baya cikin tsarina kawai kace musu su shigo sai dai banida wadataccan lokaci OK? ” Kai sojan ya jinjina tare da cewa. “Ok Hajiya.” Ya katse kiran ya musu bayanin da ta musu ya bada umarni a bud'e musu gate su shige. Hajiya Karima ana bud'a hanci ala dole ita watace motarsu ta kutsa cikin tamfatsetsan gidan wanda sai da ta raina kanta tana d'aukan gidansu wata tsiya sai yau taga ashe gabama da gabanta aljani da ya taka wuta, kuma ko a

Please Login or Register in order to submit comment