Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi shirun."

Murmushi mai ƙayatarwa ya yi anutse yace.
"Good Baby yanzu faɗa min kina lafiya? Bakiyi kuka ba da muka tafi kina bacci?"
Kwanciya tayi idanunta a lumshe tana sauke numfashi, wani bala'in shaukin Dadyn nata takeji, yadda yake mata magana, cikin tattausan harshe anutse kamar yana mata raɗa cikin kunnenta.
"Hello Baby kina jina?"
Firgigit ta dawo hayyacinta, daga duniyar tunanin da ta tafi.
Ajiyar zuciya ta sauke tana narkewa akan katifa da wani irin kalar shagwaɓa ta kirasa.
"Sweet Dadynah! Inata missing ɗinka da gaske ALLAH."
Murmushi ya saki ya ja numfashi anutse yace.
"Kiyi haƙuri zanzo baby kafin nayi tafiya, Ok?"
Khairy tace.
"Tom Dadynah kazo dan ALLAH."
"Insha ALLAHU Baby, ya kowa hope duk suna lafiya?"
"Alhamdulillah kowa lafiya Dady inaso Baffa? Nadiya sun wuce ne?"
"Baffa na lafiya Yeah sun wuce idan kin dawo kema zakije wajansu Ok?"
Cikin murna tace.
"Thank you Dadyna."
Murmushi yay yace.
"Kinci abinci?"
"Eh kaɗan tunaninka ya hanani cin dayawa Sweet Dady."
"Oh! Baby toh gani kinji ina lafiya oya je ki ƙara cin abincin bana son na ganki da rama Ok?"

Baki ta zumɓuro gaba tace.
"ALLAH NI Dady kasan bana son Jiki hakan ma sonake na rage."
Kansan ya shafa yana murmushi ƙasa-ƙasa yace.
"Ni inaso karki rame Babyn Dadynta tafi kyau idan batada rama, yanzu dai tashi kije ki ƙara abinci."
"Allah Dady banajin yunwa."
"Toh shi kenan Baby zan kiraki gobe kiyi bacci me Dady kiyi addu'a Ok?"

Asanyaye ta amsa da.
"Tom Dadynah."
Shattima yay murmushi yana katse kiran jin tana son sakar masa kuka.
System ɗin ya rufe ya ajiye wayan ya miƙe ya nufi Stairs dan taso Mamy suyi abinci, tayi sallar Isha'i...
★★★

Bayan kwana biyu Shattima ya fara shirin tafiyar da, take gabansa zuwa Moscow.
Yau ta kama Saturday Shattima yace ma Mamy su shirya suje gidan commissaire Aminu.
Mamy shegen baccin da ya addabeta wanda kwana biyu wajan aikinta ba karamin juriya take ba wajan duba marasa lafiya, haka ta shirya suka tafi.

Da yake commissaire Aminu yasan da zuwansu, an gama shirya komai nan falonsu na taraba su dan ba'a kaisu falon baƙi sunfi ƙarfin hakan.
Maryam jin zasuzo gidan tayi kwalliyarta ta kece raini wata doguwar ta saka pink mai adon stones buɗaɗɗiya ce daga ƙasa sama ta ɗan tsuke tayi kyau sosai.
Tanajin ƙaran Doorbell ta zabura ta tafi aguje.
Ammi tace.
"Kaga rawar kai da ta faɗi taji ciwo Maryam da Bilkisu sai ALLAH."
Abba Aminu yay dariya yace.
"Uwa ai ba wasaba."
Tana buɗe ƙofar idanunta akan Shattima wanda ya haɗe cikin wani lallausan boyel fari ƙal mai shegen kyau da tsaya iya tsada, ɗinkin kawai abun kallo ne, yayi wani irin fitinannan kyau.
Idanunsa ya janye daga kanta baya jin daɗin kallon da take masa.
Da sauri ta rungume Mamy tana dariya tace.
"Oyoyo Mamy ina Auntie Khairy? Dady Barka da rana sannu da zuwa."
Shattima ya amsa yana shigewa ya barsu tsaye.
Mamy ta kamo hannunta tana murmushi tace.
"Yau dai tare zamu kin kwana biyu baki leƙa muba."
Cikin murna tace.
"Zanje ranan Abba yace kunyi tafiya.
Mamy tace.
"Lah! Kwana ɗaya fa kawai mukayi acan ɗin."
Da sallama suka shigo falon.
Abba Aminu ya miƙe ya tarbi Shattima, suka rungume juna.
Yayin Ammi ma ta rungume Mamy suna murmushi.
Zama sukayi aka shiga gaishe-gaishe.
Yayin da Maryam ta samu damar ƙarema Shattima kallo tana sakin murmushi zuciyarta na wani irin sanyi, tana lumshe idanunta, shi kuma baima san me take ba.
Ita ce ta basu ruwa da lemon, na Dadyn Khairy harda durƙusa masa tana basa da gangan ta haɗe yatsun su wajan basa Cup ɗin.
Sam bai wani ankareba.
Abba Aminu yace.
"Ya wajan ɗiyata tana lafiya? Zata jima Katsina ne?"
Shattima ya murmusa yana faɗin.
"Eh toh yau kwanta shidda zatayi ko sati uku haka, farkon azumi zata dawo sai ta wuce Gumel, can ta musu suma satin uku sai tazo sallah gida."
Abba yace.
"Masha Allah Ubangiji ya ƙara tabbatar mana da alkhairi."
Shattima ya amsa da.
"Amin."
Yana kurɓar lemon inabin.

Ammi taja Mamy ɗaki suka kaɓe.
"A gaskiya na jinjina miki Hajiyata kinyi abinda ba zan iyaba ko za'a saka wuƙa ayankani, kyautar miji, miji ma iirn naki Tabb.
Amman kun cika mutanan ƙwarai wai duk alaƙar mu daku bamu san wannan sirrin ba."
Mamy tayi murmushi tana faɗin.
"Kai Hajiyata ai Yi Wa Kai ne, wlh ban taɓa jin baƙin cikin haɗa Baby da Mi Amor ba! Fatana Allah bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah basa ikon kamanta adalci atsakaninmu. Sam banajin Baby bazata taɓa cutar daniba nasani inajin haka ajikina, kishi doke zanji kishi ko na wata daban bare na shagwaɓaɓbiyar mu, amman haƙuri da juriya da kauda kai, shine zai bamu zaman lafiya, bare naji Auntie Aisha tace Abuja zata zauna, zan basu lokaci ne su mori amarcinsu sai na roƙeshi ya maidomin ita kusana, wlh bana son abinda zai nisanta Ni Baby ƙaunarta ajinina take. "
Ammi tace.
"Ameen ya ALLAH, sannu da ƙoƙari ina tunanin azamanin nan ke ɗaya ce ALLAH ya bari, banajin za'a samu mai irin halinki duk sun rasu basa duniya sai iirnmu aka bari gaskiya bazan iyaba maganar gaskiya."
Mamy tayi dariya tana faɗin.
"ALLAH baza rasaba, da kinsawa zuciyarki zaki iya, zaki iya fa! Hajiyata..."
Ammi tace.
"Bana saka ba, kedai da Allah ya ba iko mun gode."
Dariya sukayi suna tafa hannayensu...

Sai bayan la'asar suka tafi wanda Mamy taja Maryam suka tafi da ita, ranta fari ƙal yau gata ga Shattima.

Can Gumel Karima abu yaci tura wasu irin ƙuraje suka fito mata addukan jikinta, masu wani irin ruwa maroon, gabanta ya caɓe sabida ƙaiƙayin da yake mata, idan ta sosa sai jini, da baƙin ruwa yake fitowa.

Dole aka maida asibiti normal dan dubata duk iya bincike su basu gano ciwon ba su sunce Bama su taɓa cin karo da mai irin ciwon ba.
YANKAN WUƘA, ya sauya kama kamar na kwarai yayi kamar wani yazo nema ɗakin da take yake cewa Usman yanada irin maganin amman akwai tsada shirine aka mata mamansa na bada maganin zai warkar da ita.
Usman ya amince ayi maganin zai biya ko nawane.
Shi kenan yace zai dinga kawowa amman sharaɗin kuɗin biyan maganin sai ta warke zai faɗa idan ba'a biyaba ciwon zai dawo.
Haka Usman da Nadiya suka yarda su dai burunsu mahaifiyarsu ta warke.
Maganin ya fara kawowa yace idan ta cika kwana arba'in ba ɗaya zata warke ras.
Murna suka dinga yi sosai suka fara mata maganin.

Acan Katsina tun Khairy tana saka ran zuwan Shattima har ta haƙura.
Dan Shattima yama tafiyarsa Moscow batada labari, dan suna chatting sosai ta WhatsApp suna video call shiyasa ɓata damu da rashin kiransa normal ba.

Inna ADAMA ta fara shirya Zainabu sabida cikin satin nan zata tare.
Yau ya rage azumin Ramadan sauran ukku gobe Zainabu take tarewa Gumel, Dad Mustapha ya gama shirya mata komai najin daɗin rayuwa agidanta.
Yayin da Karima yau kwana 14 da fara mata magani.
Khairy murna take zata dawo wajan Khairy wadda ta cancarawa Zainabu ƙunshi da kitso ita ce ta mata.
Masha Allah kitson ya yi kyau haka ƙunshi, manyan flowers aka mata na jan lalle da baƙi, kitson ƴan ƙananu masu kyau wanda jelar sai da ta sauka kusan tsakiyar gadon bayanta, ga wani irin murjewa da ta yi, kamar tana cikin A/c a Katsina fatarta bata wani sauya ba dan ba karamin kulawa da ita Zainabu take ba,sabulan gyaran fata ta haɗa mata tana wanka da su tana bata cimma mai kyau, na kayan itatuwa hakan ya sakata ƙara zama wata ƴar mulmu sai baby take ƙara zama fatarta na sheƙi luwai.
Yau zasu taso Shattima yace su ajiye Khairy a Jigawa su wuce zuwa jibi zai tura Maleek ya kawota Gumel Mamy tayi missing ɗinta tana son ganinta.

Hakan ba karamin daɗi takeji ba, dan tasan yanzu Dadynta, baya nan amman zai shigo ƙasar cikin satin bai da faɗa mata ranan ba.

Zainabu kuka take sosai kamar ƙaramar yarinya zata rabu da gida.
Abbu yace.
"Haba! Zainabu dan ALLAH ki daina, bafa rabuwa Mukayi ba, idaba zaki kiyi, yanzu dai ki yawaita addu'a dan ALLAH karkiyi wasa da azkhar ɗin safiya da marece, kuje Allah ya baki zaman lafiya."
Inna ADAMA sabo ita kukan take ta rungume Zainabun, tana mata nasiha.
Khairy tayi dariya tace.
"Kuji sai wani kuka kuke sai kace zaku rabune har abadan."
Marwan yace.
"Kaji ƙarfin hali ɓarawo da sallama, nan ca nake wata har kuka take idan Mamy ko Dady basu kirata ba."
Abbu yace.
"Ah Toh ta manta ne. Ke kam Khairy sai murna yau zaki tafi wajan Mamynki koh?"
Ƴar dariya tayi tace.
"Abbu zan dawo bayan sallah insha ALLAHU sai mutafi da Jamilah da Rayhana da Khabir, ai zakuje ko? Kai Yaya Marwan harda sharri Ngd."
Marwan yace.
"Ba wani sharri sai gaskiya."

Rungumeta su Jamilah sukayi cikin murna sukace.
"Eh zamuje muna jiranki."
Har wajan mota Abbu inna ADAMA.suka rakashi ita ce ta sakata mota.
Abbu yace ma Mustapha.
"Ga amanar ƙanwata akaro na biyu na baka."
Dad Mustapha yace.
"Na amsa zan riƙe insha ALLAH Abbu nama alƙawalin hakan."
"Masha Allah, Allah Ya tsare hanya."
Khairy tana zaune kusan direba su suna side ɗin baya.
Yana riƙe da hannunta yana lallashinta haka Naziru direba yaja suka tafi.
Khairy sai murmushi take, yau zataga Mamynta.
Waigowa tay taga Zainabu kanta ƙirjin Dad Mustapha yana buga bayanta.
Ƴar dariya ta yi tace.
"Kai su Umma love, kai Dady bazaka ma turo ƴan uwa suzo ɗaukan amarya ba, da kanka kazo abinka, Ni kuma Sweet Dady zai kaini gidana, idan nayi aure."

Zainabu tai saurin janyewa daga jikinsa tana beƙa hannun ta kaima Khairy duka. Dad ya riƙeta yana dariya yace.
"Wannan ƴar taki fa baturiya ce rayuwar gidansu abun burgewa wannan Dadyn nata bakiga ɗan soyayya bane. Karki dokar min ƴata."

Rau-rau Zainabu tayi da idanunta, tana masa nuni ita kunya takeji.
"Ba wata kunya my love..."
Da sauri ta rufe masa baki, tana zaro idanu.
Khairy ta k'yalk'yalewa da dariya ta kira Shattima vdcll.
Lokacin yana tsakiya da shairi zai tafi meeting ɗin ƙarshe yau sauke gamawa gobe zai taso zuwa Nigeria.

Sanye yake da kayan sanyin riga da wando farare ƙal masu taushin gaske sunada kauri sosai, yana sanya hular rigar kiran ya shigo sabida yabar data a kunne zai kira Mamy kafin ya fita, yaga kiran Khairy.

Yana fesa turare ya ɗaga kiran yana kallonta tana dariya.
Murmushi yay yana faɗin.
"My baby wannan ƙunshin fa? Dariyar me kike haka kar cikin ki yayi ciwo fa! Kun fito kenan yau sai kwana Jigawa wajan Mamy ?"
Idanunta ta zuba masa ganin wani irin bala'in kyau da ya yi, ta kwaɓe fuska ashagwaɓe tace.
"Sweet Dadynah kayi kyau dayawa wlh."
Shattima zaiyi magana suka haɗa idanu da Mustapha yace.
"Ya SALAM Baby! Ashe tare kuke amota ɗaya da Dad inki? Ki gaishe min dasu zan kiraki Anjima iya rigima."

"Ni Please Dady ka bari muyi hira kaɗan, yaushe zaka dawo ne?"
Murmushi yay yana ajiye kwalban turaren anutse yace.
"Bazan faɗa ba canka da kanki zan kawo miki wani abu."
Fuska ta kwaɓe tace.
"Ɗaya ga azumi na canka koh?"
Dariya yay ya mata gwalo ya katse kiran.
Khairy ta waigo tana kallon iyayan nata, Dad Mustapha yana mata dariya ta fashe masa da kuka, Zainabu kallon ikon ALLAH take kallo wannan ƴa tasu akwai shagwaɓa...

Jigawa
Mamy kuwa tunda Shattima ya tafi sati biyu cif batada wata isassar lafiya.
Yau kam tayi alƙawarin yima kanta gwaji sbd zargin abinda take bai wuce tanada ciki ba, sabida kakaf nazarin ta nan ya tsaya.
Dan haka tana gama operatoins da gareta tayima kanta da kanta gwaji.

Zaune take akan kujeran office ɗinta, yana kallon abinda sakamakon ya bada, cikin Shattiman ta, ɗauke a marata tsawon kwana 22 cif.
Wani irin kuka ne ya kuɓuce mata ta kifa kanta saman table, cikin kuka tana faɗin.
"Alhamdulillah! Allah kayi dadin tsira ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam, Allahumma salli ala sayyadina Muhammadin wasallim."
Ta faɗa cikin kuka mai tsanani ta miƙe tana kuka ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta shimfiɗa darduma ta sanya hijab ta tayar da sallar nafila ta godiya ga ALLAH.
Raka'a huɗu tayi, kowace idan tayi sujada bata san iya adadin daɗewar da take ba tana addu'a dayiwa ALLAH kirari. Yau tana cikin farin cikin da baida Misali.
Bayan ta gama tayi salatin Annabi ta ɗaga hannunta tanama Allah subhanahu wata'ala kirari.
Wayanta ta ɗauki ringing.
Ta shafa addu'a ta miƙe ta ɗauke sallayan ta linke ta nufi wajan table ɗin.
Ganin Shattima ne vdcll ta ɗaga.
Suna haɗa idanu, cike da kulawa anutse yace.
"Sweetheart! Kukan me kikayi? Me ya sameki?"
Ƙasa riƙe kukan tayi ta fashe masa da kuka tana zama saman kujeran....

Real Ladingo Omu Farisah

*YI WA KAI!*


*Free Novel*
_December 16/12/2022_

_#MatarɗanAlhaji🫣_

*JUMA'AT KAREEM🕋*

*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*89&90*

Zazzafar iskar bakinsa ya furzar yana lumshe kaifafan idanunsa, wanda suka nuna alamun gajiya da bacci a tare dasu ƙarara.
Cikin wani irin cool voice ya furta.
"Ya ALLAH! Sweetheart me ya saka min ke kuka haka? Please karki ɗaga min hankali, kiyi haƙuri kalleni muyi magana kinji ƴar Babytah."
Ya faɗa cikin wani irin yanayi yana jin kukan nata har ƙasan zuciyarsa.

Mamy wani irin sanyi taji har cikin zuciyata, sai ta nemi kukan da take ta rasa, ta ɗago tana kallon screen ɗin wayan, idanunta cikin nasa suna kallon juna, ya sakar mata wani irin tattausan murmushi.
Ta mayar masa ta goge hawayen fuskarta tana murmushi.
Tace.
"Ni kam Mi Amor bana son Baby ni baby daughter Khairy Babynmu, sunan yafi cancanta da ita, Ni abar min Sweetheart ɗina yafi min daɗi."
Ta faɗa tana ɗaga masa gira tare ta cire mayafin jikinta, tana janye rigarta shafaffan cikinta ya bayyana fari tass, tana shafawa.

Shattima ya murmusa yana gyara zamansa, tare shafa sajansa idanunsa akan shafaffan cikin Mamy.
Anutse cikin bata dukkan kulawarsa cikin muryasa mai fitar da daddaɗan lafazi yace.
"No! Naƙi kema babyna ce, kuma Sweetheart nah. Please fad'a min me ya sameki kike min asaran hawayenki? bana kusa bare na shanye abuna, na lallasheki, Sweetheart ƙara gaba da riganki naga abuna."
Ya faɗa yana murmushi yana lumshe mata kaifafan lumsassun idanunsa.
Mamy tayi dariya tana janye rigar tare da janye bra ɗin ta.
"WoW! Baby sweetheart kice musu ina missing dayawa, muahhhh i love You.
Yanzu faɗa min me ya sakamin ke kuka kafin naji matsalar zanfi nutsuwa"

Mamy tana murmushi ta maida bra ɗin tana sakin rigarta, a tausashe tace.
"Nayima alkawarin faɗa maka idan ALLAH ya kawo min kai gida lafiya Mi Amor."
"Anutse yace.
"Kin tabbatar? Sannan kimin alkawarin bazaki sake kukan ba, ko meye sai nazo ki faɗa min, Ok?"
"Wlh Mi Amor nayi maka alƙawali, ai yanzu ma ka sakani farin cikin da bazan iya cigaba da kukan ba!"
"Very good Sweetheart, toh ya kike ya aiki?"
Fari ta masa da kyawawan idanunta tace.
"Alhamdulillah mijina."
Dariya sukayi tare yana nuna mata wani abu tare da ɗaga mata gira cikin wata fitinanniyar muryasa yace.
"Tana missing ita da uban gidanta."
Mamy ta langwaɓar da kanta gefe tace.
"Wayyo Mi Amor I miss u kace mata muna jiranta."
Kusan 30 minutes suka kwashe suna hirasu ta ma'aurata, kuma masoya, kafin suyi sallama da juna.
Mamy baki ɗaya yau cikin farin ciki take marar misaltuwa.
Ƙarfe ɗaya da rabi ta tattara ta tafi gidansu dan faɗin abun alkhairin da ya sameta daga sai ta wuce gida dan tarbar Baby Khairy.

Hajiya Hafasatu, (Anne) zaune cikin haɗaɗɗan falonsu ƙafafunta miƙe, Fauziyya da bata jima da zuwan tana matsa mata ƙafafuwan, suna hira.
Kamar daga sama sukaji sallamar Mamy.
Anne ta amsa cikin farin cikin ganin ƴarta, tana faɗin.
"Barka da zuwa Dr mai gadon zinari."
Fauziyya tace.
"Oyoyo Auntie Billynmu, inada niyar biyawa gidanki wlh."
Mamy ta iso cikin falon tana murmushi ta cire mayafin jikinta ta ajiye jakarta, ta rungume Anne ta mata raɗa akunnenta.
Anne tayi wani irin zabura tana riƙo kafaɗun Mamy tace.
"Dan Allah Bilkisu da gaske?"

Mamy ta ƙyalƙyale da dariya tana rungume mahaifiyar Tata, tace.
"Wallahi Anne da gaske nake sati Uku."
Anne cikin farin ciki tace.
"Alhamdulillah ! Alhamdulillah! ALLAH abin GODIYA, ALLAH sarki Bilkisu ashe da rabon zamuga ƙwanki aduniya."
Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kukan murna.
Mamy ta fara kuka tana faɗin.
"Don ALLAH Anne kibar kuka ki min Addu'a Allah ya saukeni lafiya."
Fauziyya tai wani irin ihu tana rungume Mamy tace.
"Auntie ciki gareki?"
Bilkisu ta ɗaga kanta tana gogema Anne hawayen fuskarta.
"Alhamdulillah ALLAH mun godema wayyo dangi kowa sai ya ji wlh."
Ta faɗa tana ɗaukan wayanta Adam babban yayansu ta fara kiransa.
Yana ɗauka tace.
"Yayanmu katayamu murna Auntie Bilki Allah ya bata ciki."
Daga yace.

"Kai MASHA ALLAH Alhamdulillah! Ina Bilkisun?"

"Gatanan Yayanmu."

"Ok ban ita."

Fauziyya ta beƙawa Mamy wayan, ta amsa tana masa sallama.
Ya amsa yana faɗin.
"Wlh na tayaki murna Dr ALLAH ya saukeki, lallai mahaƙurci mawadaci ne yau muna cikin farin ciki."
Mamy ta share hawayen fuskarta, tace.
"Ngd Yaya Adam ALLAH yabar zumunci..."
Suna gama wayan Fauziyya ta amsa ta shiga kiran ƴan uwa tana bada labari Mamy murmushi Kawai take.
Kafin kace me kira wayan Mamy har ta rasa kiran wa zata ɗaga.
Auntie Madinah tace tana tafe gidan Mamyn murna sai gaba da gaba.
Anne tana kallon Mamy tace.
"Toh yanzu me zakici agirka miki?"
Mamy ta kalli tsaddan agogon da yake ɗaure atsintsiyar hannunta, taga lokaci yaja tace.
"Anne bana jin yunwa, amman azubomin abinda aka dafa zan ɗan ci..."
Baba Bilal kansa da shigo ya isko wannan labarin, ya ji daɗi marar misaltuwa, daman tunda abun nan fito Khairy ba ƴarsu bace, yake jin tausayin ƴarsa, yau kam yana cikin farin ciki ya mata addu'a ALLAH ya sauketa lafiya.
Sai 3 Mamy ta tafi gida ita da Fauziyya suka tafi.

Su Khairy sai ƙarfe 4 da ashirin da shidda suka iso Jigawa, sabida basu fito da wuriba.

Tun shigowarsu gari Khairy ta kira Mamy tana faɗa mata, tace su Zainabu su tsaya zata fito su gaisa.
Kafin su shigo ta fito, ta zauna lafiyayyar rumfar shaƙatawarsu, tana shan iska tana jiran su.
Fauziyya na ciki tana musu girki mai sauƙi.
Suna isowa har ciki motar ta shigo.
Mamy suka gaisa da Mustapha da Zainabu suka wuce, Mamy na riƙe da hannun Khairy suka nufi ciki, Maleek na janye da trolleyn Khairy.
Suna shiga falon Khairy tai tsalle ta ɗare Mamy kamar zata koma cikinta tana sumbatarta, tana faɗin.
"I miss You so much Sweet Mamynah."
Mamy tana murmushi tace.
"Wayyo Baby zaki ɓalle min baya bakya ganin kinfi Mamyn kauri."
Dariya Khairy tai tana sake shigewa jikin Mamyn tana faɗin.
"Mamynah kin ƙara kyau da fari wlh."
Mamy tace.
"Ke kam Baby kin ganki kuwa? Tabb kin ƙara fresh abunki, ƙunshin ya yi kyau fa!"
Fauziyya ta fito tana faɗin.
"Barka da zuwa ƴar Mamy ki sassauta riƙon Mamyn taki karki muku asaran ɗa ƙani..."
Khairy ta kalli Fauziyya tana faɗin.
"Auntie Fauzah ban ganeba...?"
Mamy tace.
"Babu muje ki wanka kizo kiyi abinci bar shirman Fauziyya nima ban gane ba."
Khairy tayi dariya tana kama hannun Mamy suka nufi Stairs tanama Fauziyya gwalo."
Dariya Fauziyya ta yi tace.
"Ke kika sani da kin bini da kinsha labarai."
Khairy tace.
"Na me Auntie?"
Mamy tace.
"Ke kam da kike biye mata muje."

Laraba ta biyosu da trolleyn Khairy.
Wanka ta yi, tay sallar La'asar ta saka riga da siket ƴan kanti ko takan ɗan kwalin bata bi ba ta ciro wayanta cikin handbag dinta tana kwanciya saman narkeken royal bed ɗin, ta kira Shattima vdcll.
Data bata kunne bai ganiba, kira ɗaya ta gane hakan ta miƙe zaune kamar zatayi kuka, ta sauka daga bed ɗin ta gwada kiransa.
Kiran ya shiga, yana dab da yankewa ya ɗaga, anutse yace.
"Babyn Dady ta iso dutse koh?"
Komawa tayi ta zauna kan bed ɗin, tana murmushi.
Ashagwaɓe tace.
"Sweet Dadynah! Ya akayi ka sani? Na kiraka naga fuskarka amman ban samuba."

Murmushi mai sauti ya ɗan yi yana shafa kansa yace.
"Na sani mana, kinyi wanka gajiya ta fita koh?"
Ashagwaɓe tace.
"Eh Sweet Dady, toh yaushe zaka zo Please?"
"Baby nace ki canka kin kasa baki shirya ganin Dady ba."
Kukan shagwaɓa ta sakar masa tana harba ƙafafunta, tace.
"Dady na canka kace banci ba, toh ya kake so nayi da raina?"
Shattima ya ɗauki Cup glass ɗin da yake cike da ruwa ya kurɓa, anutse cikin kamewarsa ƙasa² yace.
"Bana son kukan fa baby yi shiru ya isa, haka goge hawayenki Dadynki gobe zai shigo komin dare."

Ihu tai tana faɗin.
"Yeeee nayima Dady wayo ya faɗa min, Allah ya kawo ka lafiya, Dady ina son chocolats da biscuits and lollipops ɗin Moscow karka manta."
Idanunsa ya ɗan lumshe yana murmushi ahankali cike da kamewa yace.
"Ok za'a kawo Baby, oya je kici abinci bana son kina wasa da cikinki."
Dariya ta yi tana faɗin.
"Toh Dady zamuyi vdcll da dare koh?"
"Yeah Baby insha ALLAHU bye."
"Bye Dadynah."
Murmushi yay yanaji ta katse kiran.
Wayan ta ajiye kan bed ta miƙe ta fito, tana murmushi.
Mamy kuwa tun tuni tayi bacci ba tare da ta shirya Ba.
Fauziyya da Khairy sauketa hirasu, haka Auntie Madinah ta isko su bataso ta isko Mamy na bacci ba, amman tace zata dawo kar atashe.
Fauziyya sai da sukayi dinner ta tafi kasancewar mijinta baya gari.
Mamy taja Khairy suka tafi Galadanci, suka gaishe dasu Inno...

Zainabu suna isa ta samu tarbar wajan tsirarun danginsa, kowa sai murnan dawowarta ake.
Nadiya tayi murna sosai lokacin da ta dawo daga asibiti wajan Karima ta isko Zainabu.
Nadiya ta rungumeta tana murna sosai dan tasan tayi uwa ta biyu.
Misalin ƙarfe 9 na dare Dad Mustapah ya kira Usman da Nadiya.
Zaune suke ƙasa kusan ƙafafunsa, Zainabu na gefensa.
Gyaran murya yay ya buɗe taron da addu'a, yace.
"Alhamdulillah ina murnar wannan rana da ta kasance Zainab ta dawo gareni. Usman! Nadiya! Kuyi haƙuri da rashin zaɓa muku uwa ta gari, duk da ba laifi na bane bawa baya tsallake ƙaddara, laifina ɗaya sakaci wajan addu'a da azkhar har Karima ta yi galaba akaina, amman daman Allah ya ƙaddara ta tsatsonta zaku fito. Ina godiya ga Allahu subhanahu wata'ala da ya karemun ku baku gadotaba, naji daɗin rashin haihuwan ƴaƴa dayawa da ita, da tabbas sai an samo magajinta.
Abinda nakeso da ku ku zauna lafiya da Zainabu, bana son wata matsala ta ɓullo ku bata girmanta.
Kema Zainabu ga ƴaƴana nan amana ki kulamin dasu, ki ɗauka kamar kece kika haifesu, ina son yarana sosai Allah ya bamu zaman lafiya da juna."
Usman da Nadiya suka amsa da.
"Ameen Dad zamu zama masu biyayya agareta, ko baya bamu samu matsalaba da ita bare yanzu. Dad yaushe Ummulkhairi zata zone?"
Mustapha yace.
Shattima yace nan da kwana biyu, zuwa uku za'a kawota nasan ɗaya ga azumi ko biyu zata zo."
Sosai sukayi murnan hakan.
Zainabu dai murmushi take tana riƙe da hannun Nadiya.
Awannan dare Mustapha ya shayar da Zainabu madara ƙauna, ta basa haɗin kai ɗari bisa ɗari suka jiyar da zukatansu daɗi tare da abubuwan da basai na faɗa ba, amman Zainabu an gurzu ba kaɗan ba, sai narke masa take wanka ma da taimakonsa tai kafin su kwanta bacci rungume da juna zuciyoyinsu fal cike da farin ciki...

Washegari Mamy sanin Shattima yana hanya bataje aiki ba, kitso da ƙunshi aka mata, suka ɗora girki da Khairy Laraba na taimaka musu.
Kamar kullun duk kalar abincin da Shattima yake so an girki anyi masa lemonsa na inibi.
Kafin ƙarfe shidda na yamma sun kammala komai, ƙaton falon masu manyan kujerun alfarma, yasha kayan alatu ko ina ƙamshi yake tashi.
Mamy wani mayen bacci takaeji amman ta daure tayi wanka ta cancara kwalliya, da wani shegen lace mai taushi doguwar riga ta murza ɗauri, tasha makeup, kace gasar kyau zataje.

Khairy sam batayi kwalliya ba saboda ba gwanar kwalliya bace, ta dai saka wani material Ash kala riga da skirt ya mata shegen kyau, ta shafa lipstick sbd tana bala'in sonsa.

Har 9 na dare Shattima bai shigo ba Mamy bacci ya fara rufe mata idanu, sai hamma take, tana gyangyaɗi, har ta ɓingire akan 3 seater.
Khairy ta matso ta kamo hannunta kamar zatayi kuka tace.
"Wai Mamy baccin lafiya haka? Ko mutafi asibiti kafin Dadynah ya dawo ne?"
Mamy da baccin ya fara fizgarta tayi murmushi tace.
"Baby kin manta ni likitace? Ina lfy ki bari nayi bacci kaɗan Baby karki hanani har jiri nakeji wlh, ga idanuna zafi, idan Dadynki yazo sai ki tasheni."
Khairy ta kwantar da kanta bayan Mamy tace.
"Toh Mamy kar kwalliyarki ta ɓaci."
Ai tuni Mamy ta ƙara tafiya batama jinta.
Khairy ta ɗago tana komawa 2 seater ta zauna tana ɗaukan remote ta canza tasha zuwa Bollywood.
Miƙewa tai ta nufi kitchen.
Black tea ta dafawa kanta.
Ta dawo ta zauna tana sha tana kallo.
10 pm Khairy taji ƙaran doorbell, cikin farin ciki ta miƙe ta iso wajan Mamy tana shafa fuskarta.
"Mamy! Dadynah yazo ki tashi."
Mamy ta sake gyara kwanciyarta tana baccin tsakani da ALLAH.
Ashagwaɓe tace.
Mamy dan Allah ki tashi."
Mamy sama taji Khairy kamar mafarki shiyasa bata buɗe idanunta ba tace.
"Je ki buɗe masa."
Ta faɗa cikin magagin bacci.

Khairy jin anata danna Doorbell ɗin ta nufi hanyar falon tana bin corroder ɗin da zai kaita ƙofar.
Tattausan hannunta ta ɗora saman key ɗin da yake jikin ƙofar ta murza tana faɗin.
"Welcome back Dadynah."
Ta faɗa tana kama handle ɗin tana buɗe ƙofar.
Tsaye yake sanye da wani farin shegen tattausan yadi fari ƙal, mai bala'in kyau da tsada.
A kallon farko zaka san wannan yadin ba sawar kowa bane sai wanda sukaci suka tada kai ko kana wanda ya tsaya ma.
"Oyoyo Dadynah."
Ta faɗa tana murmushi ta kamo hannunsa, tana kallonsa har idanunta sun ciko da ruwan ƙwalla.
Wajen ya ƙarasa janyota, yana

Please Login or Register in order to submit comment