Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biki wallahi na tafka kuskure nima na Sani ban kyauta ba, abinda na miki, kiyi haquri na bar miki mijinki, Allah bai k'addaraba ni matarsa.”
Khairy mutum ce mai haqurin gaske bata iya fad'aba ko riqe mutum aranta, sai dai fa tanada kafiya idan tazo wuya babu mai iya tarota sai Shattima.
Riqe Aziza tayi tace.
“Ba komai Allah ya yafemu baki d'aya tinda kin gane gaskiya.” ta roqi Shattuma ma bai ce uffan ba ya dai jinjina kansa ba tare da ya kalleta ba, yace.
“Don Allah kiji tsoron Allah cikin lamarinki, kisan ke macace aba mai daraja, Allah ya miki daraja ki daina watsar da kanki.”
Miqewa tayi tace.
“Ngd Khairy Dady na gode insha Allahu natafi, Abdoul kaima kayi haquri.”
Ta k'arashe maganar tana Jan akwatinta.
Abdoul zai zauna Shattima yace.
“Je karakata mana.”
Zama yayi baice komai ba kansa aqasa har yanzu kunyar Shattima yakeji.
Aziza tana fita kai tsaye hotel taje ta kama d'aki ta kira Hamida tana mata bayanin abinda ya faru, da irin shirin da zata koma tayi tinda wannan kwallin baiyi tasiri ba sosai.
★★★
*Gumel*
Unguwar Karkasara
Unguwace sabuwa da masu hannu da shuni, suke sabbin gine-gine na zamani, Masha Allah, har masu k'aramin k'arfinma akwai.
Wani babban Maison ne mai bene hawa 2 tafkeken gaske, gidan ya tsaru akwai garden babba aciki tsararre.
Falo ne k'aton gaske wanda yaji kayan alatu an zuba manyan kujeru har seats biyu, komai atsare a falon.
Tv plasma a kunne tashar arewa 24 ana haska film d'in Hausa me suna Izzatu.
Mata ce zaune an kame saman 3 seater , wasu mata biyu agefenta, alamar baqine tayi yanzu,sai d'ai d'ayar suna tsananin Kama da hajiya Karima.
Matar zata kai shekaru arb'in da biyar, jibgegiya ce mai tumbi, anci uban lace mai tsadar gaske, ansha gwala-gwalai, haqorinta sanye da haqorin makka, biyu sama da qasa, kana ganin farinta kasan farin bilicin ne.
Matar d'ayace mai Kama da ita ta kalle tace.
“Gaskiya aunty Karima Allah ya baki duniya sai ki nemi lahira itama kya samu.”
D'ayar wacce take aminiyarta tace.
“K'awata ya kamata fa cikin satin nan ace mun shiga Dubai ko ya kika gani?”
Fari tayi da idanu tace.
“Ai wlh bazan iya fita asatin nan ba sai Usman ya iso lfy daga Mexico, ko kin manta yau sauran kwana 6 ya iso?”
Hajiya Shahida tace.
“Kai anyi hakan toh Allah ya kawosa lafiya dole mujirasa, ita kuma Nadiya fa!yaushene take kammala karatun nata? Ayuba ya addabeni fa shi dai duniyar nan Nadiya tai masa.”
Hajiya Karima tayi dariya tace.
“Ayuba kenan yaji daga gareta mana ai zaifi koh?”
Wani baqi dattijo ne kyakkyawa kallo d'aya zaka masa kansan jinin fulanine zai kai shekaru 57 ahaife, anutse yake taka matattakalar benen, yana amsa waya,sanye yake da manyan kaya shadda blue.
Karima ta d'aga kanta tana kallonsa sai ta wani had'e rai ganin irin wanka da yayi ta miqe da uban rusheshen tunbinta tana tafiya da kyar ta nufi wajansa.
Kallonta yayi lokacin da yake sallama da wanda yake wayan.
“Uwargida sarautar mata ya dai?”
Rai b'ace tace.
“Wlh ban amince ka fita ba yanzu Sam zuciyata bataamince ba akwai shegiyar da zata kallemin kai.”
Kamar wani soko yace.
“Toh muje ki shiryani da kanki ana jirana meeting gareni a kano qarfe 4:30 na yamma.”
Ai kuwa da kanta ta shiryasa cikin wani yadi taqi fesa masa turare amman dayake ma'abucin k'amshine, kayansan sun Kama da turarensa, kuma yadin ya amshesa matuqa ahaukanta ne take ganin baiyi kyan da wata mace zata kalleshi ba, bayan shi mai kyaune ga kud'i.
Bayan ta rakasa har qofa ta dawo Habiba kanwarta tace.
“Su aunty an samu duniya fa anan,kina murza kambunki.
hajiya Shahida tace.
“Ai mu da kika ganmu duk 'yan k'ungiyarmu ba wacce namiji ya isa ya nuna mata yatsa, ai Karima da sauqinta akanmu ko ni,da ni ce wannan b'acin ran da ta nuna wlh bai isa ya cira k'afafunsa yabar gidan ba.”
Suka kwashe da dariya.

Kwanan Shattima biyu atare dasu Khairy ta murmure ta samu kwanciyar hankali, ganin mahaifinta sosai Abdoul ya yarda kansa yana sakin jiki suyi hira su ukun hakan ba k'aramin dad'i yama Shattima ba.
Tsaye suke a airport jirginsu Shattima zai d'aga.
Kuka take harda majina ta maqale jikin Shattima, kamar zata koma cikinsa.
“Oh! My God! Baby! Kiyi haquri kunfa kusa dawowa, kinga mijinki ba lafiya kiyi hqr ya warke da zaran ya warke ki kirani zanzo na tafi dake, OK sweet daughter? ”
Ashagwab'e cikin kuka tace.
“Promise sweet Dady?”
Murmushi yay yana Jan dogon karan hancinta yace.
“Yeah Baby nayi, Abdoul kamata kuje.”
Kafad'a ta maqale tana sake shigewa jikinsa tayi luf tace.
“Ni sai ka tafi zamu tafi kace Sweet Mamy ta aikomin dambun zabo.”
Abdoul ma dariya yayi ba Shattima ba.
“Ok za'a aiko sakani Baby kinsan babanki ba wata tsokaba tsayin ne kawai,kayar dani zakiyi fa!”
Dariya tayi idanunta cikie da hawaye tana kallonsa,ta turo masa d'an k'aramin bakinta gaba.

Ai kuwa basu bar airport d'in ba sai da jirginsu Shattima ya tafi, suka nufi gida, ita take tuqin yana nuna mata hanya.
Tinda suka dawo gida bai sake kallonta ba, haka itama bata damu da shi dan bata tab'a jin d'igon sonsa ba, biyayya take da hanka ta shige d'akinta tayi kwanciyarta.

*Nigeria*
Asokoro
Alhaji Hashim suna zaune a falo, umma Sa'idah gefensa suna magana.
“Abban Salim! Ya kamata fa ayi bikin yaran nan da wuri, inaga zaifi Aliyah ta zo tin safe tana ciki ashe bata San da had'in ba, inaga ba wanda ya mata mgnar agidan, ta lab'e d'aki wai kunya.”
Alhaji Hashim yayi murmushi yace.
“Au wai Yaya Basiru bai fad'amata ba? Kiramin ita mu gaisa.”
Umma Sa'idah ta miqe tana murmushi ta nufi d'akin da Aliyah ta sauka.
Farar matashiyace mai matsagaicin tsaya tanada k'iba ba laifi tanada kyanta na shiga gari zata kai shekaru 22.
Zaune Sa'idah ta isketa ta rabka tagumi.
Dafata tayi tayi firgigit tana kallonta.
Murmushi ta mata, ta kamata tace.
“Tunanin me kike Aliyah? Taso muje Babanku na kiranki.”
Bata iya magana ba ta miqe suka fito.
Atsakiyar falon sukaci karo da Salim zai shigo.
Kallonsu yay yana washe baki yace.
“Toh amarene? Shine ba ko D'an zuwa agaisa irin na da Aliyah?”
Aliyah batayi mgna ba kanta k'asa har suka shigo falon.
Aqasa ta zube ta gaishe da Hashim ta gaishe da Salim.
Salim ya rusuna yace.
“Father! Ina yini? Umma! Ina yini ya gida? Ina yaran kuwa?”
Hashim yace.
”Humm kana son wani abun ne?”
Salim yace.
“Ko d'aya albarka iyaye nake nema wlh, anjima zanje Taraba insha Allah jibi Zan dawo, sannan Father ayi bikin mana kaga mu baza'a sake tare jama'a ba kawai b'angaran my life ne zasuyi bikinsu can babban gida.”
Aliyah ta kalleshi tana mai farin cikin canzawarsa da amsarta da yayi.
Hashim yace.
“Masha Allah abu yayi dad'i Salim Allah yayi maka albarka, zanje muyi mgna da Yaya Basiru zuwa dare.”
Salim ya zube yana zuba godiya.
Sa'idah dai kallonsu take sam bata yarda da d'an nata ba.

*Katsina*
Malali
Inna tana kitchen tana had'a sanwar rana, sai sharce gumi take sabida bala'in zafin da ake musu yau, sosai abun ba'a magana.
Kukan Kabir taji yana kiranta, sai taji muryan Jamilan tana dukansa, tare da fad'in.
“Ni zaka zaga daga aikenka ka siyomin lemon kwalba?”
Inna ADAMA ta kwalama Jamilan kiran.
“Ke! Jamila! Wlh idan na iskoki zakici qaniyarki, sakarmin yaro, kafin na fito.”
Tana rufe baki Zainabu na fitowa daga band'aki, tayi jifa da sahanin ta nufi wajan Jamilan.
Amshe Kabir tayi tana mata fad'a irin na kurame.
Jamila tace.
Mamah! Aikensa nayi fa yaqi tafiya kuma ya zageni.”
Haquri ta bata ta kama hannunsu su biyun suka nufi d'akinta.
Raihana tace.
“Innah! Kinaji auntie ta kasar miki d'a wato taci bulus koh? Wlh sai na fad'a Abbu, ayi mata lilis kamar yadda akayi min ranan.”
Innah ta fito tana sharce zufa tace.
“Barni da ita Raihana, fito Jamila je ki qarasar girkin tinda dai bakisan abun arziqi ba,ke d'iyar baturen inace da sai kinsha lemon kwalba?”
Zainabu daga can d'akin ta murmusa tana girgiza kanta.
Ta amshi kud'in ta beqawa Kabir ta kwatanta masa da kurmanci yaje ya siyomata lemon.
Kabiru yace.
“Wlh Mamah danke zani wannan azalumar me dukana.”
Zainabu ta saka masa albarka ta shafi kansa tace yaje da hannu, Jamila kuwa tace taje ta qarasa girkin.
Rungumrta Jamila tayi tace.
“Ina sonki Mamarmu Allah ya kawo miki farin ciki mai d'orewa na har Abadan.”
Innah da ta leqo tace.
“Amin insha Allah yana tafe, atashi dai aje kitchen. ”
Jamila tace.
"Ai daman kece bakya son hakan bari naje toh.”
Tana fita innah ADAMA ta zauna kusan Zainabu tace.
“Don Allah Zainab ki ajiye hankalinki ki Kama jikinki ki saki ranki Allah ya kawomi miki miji kiyi aure, ko zakiga k'wanaki kema aduniya tinda wanda kika Haifa ko fuskarsa baki ganiba Allah ya amshi ransa, shekara biyar da sakin da aka miki bayan kin kwashe shekaru cikin huquba, shin Mustapah shi kad'aine autan maza? Zaki had'u da wanda ya fisa dududu nawa kike ko shekaru 40 bakiyi ba ki zauna kutun namiji ya kasheki.”
Zainabu ta share hawayen fuskarta ta jinjinawa ADAMA kai alamar ta gamsu zata gyara komai zata daina tunanin Mustapah insha Allah.
Sosai Innah ADAMA taji dad'in bayanin na Zainabu takuma san halinta bata magana biyu...

Cikin talatainin dare jirgin su Shattima ya sauka Nigeria Abuja.
Gidansa na can suka sauka daman yanada meeting washegarin.
Can jigawa kuwa Mamy Bilkisu ce zaune saman darduma tana kai kukanta wajan Allah sbd yawan mafarkan da take sun fara damunta.
Har ta rame kwana biyu.

Acan Asokoro kuwa adaidai lokacin, Aliyah ta baje tanata sharara bacci taji mutum samanta ana kissing d'in ta ko ina ana shafata, ana ta qoqarin cire mata rigar baccin jikinta...


_YI WA KAI...!_


_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 17&18*

Jin irin yadda ake kissing nata tare da qoqarin cire mata kayan jikinta, tsoro ya kamata, jikinta ya shiga b'ari ta riqe hannun mutumin tare da bud'e baki zatayi ihu, ya tura mata bakinsa cikin nata.
Kokowa suka fara tana yakushin sa ta ko ina, duka take kaimasa amman ina wanda ya yi nisa baya jin kira, ya turmusheta, da qarfin tsiya ya cira rigar jikinta, nan ya haukace mata kamar mayuwacin zaki, ko ina ajikinta bai bari ba, har ya yayi nasaran rabata da budurcinta ta k'arfin tsiya, tana kuka tana dukansa har k'arfinta ya k'are.
Sai da ya sauke jaraba da take tare da shi ya mirgina gefe, yana sauke numfashi, kafin cikin zafin nama yayi azamar miqewa ya sauka saman bed d'in, yana sanyan wandonsa cikin azama ya bud'e d'akin ya fice.
Aliyah kuwa ko 'yar yatsarta bata iya d'agawa tsabar azabar da take ciki, hawaye kawai yake silalowa saman kumatunta, tana jin rad'ad'i azuciyarta, shin meye da Salim sai ya mata fyade bazai iya haquri su tare ba? Ita d'in fa matarsa ce.
Har garin Allah ya waye bata motsa ba, ta kasa tashi, har sai da hantsi ya fito, har suka hallara akan dining area, za suyi breakfast, ganin bata fito ba umma ta shigo d'akin taga KO lafiya.
Halin da taga Aliyah aciki ya firgitata.
Agigice ta hau saman gadon tana dikira tare da salalami, ta kamo tana fad'in.
“Aliyah! Me zan gani? Yaushe Salim ya biyo dare ya aikata miki wannan mummunan aiki haka?”
Ta k'arashe mgnar tana sakin Aliyan ta shiga bathroom ta had'a ruwan d'umi cikin bathtub ta dawo ta kamata, dak'yar suka shiga bathroom.
Ita ta taimaka mata ta shiga ciki dauriya kawai tayi taqi kuka tana ciza baki, sai da ta canza mata ruwa ta barta tayi wankan tsarki, ta fito.
Zanin gadon ta cire.
D'akinta ta tafi ta Kira Salim sai da ta kusa katsewa ya d'aga.
Ashar ta k'unduma masa tare da cewa.
“Maza-maza karka sake ka rufe mintina biyu baka shigo ka d'auki Aliyah ka kaita hospital an duba lafiyarta ba! Mutumin banza da wofi, ashe tsabar munafurci ne yasa kace ka tafi Taraba.”
Salim daga can yace.
“Innalillahi ummatah! Ni kuma? Wlh bana garin tin daren jiya, me Aliya tace nayi mata sabida Allah? ”

Umma Sa'idah tace“Kaci qaniyarka ni zaka mayar 'yar iska Kai bari kaji ni tinda kaga Aliya naji kace zakayi tafiya nasan akwai mugun nufinka da kake shiryawa, sai dai banyi zaton haka kake nufi ba, wlh kazo yanzu duk Inda kake.”
Ta katse mgnar tana huci.
Salim kuwa ya kashe wayansa yace.
“Nifa wlh bansan abinda take nufi ba dan haka ba Inda zanje ah toh.”
Bayan Aliyah tayi wankan tayi alwala ta fito ta sanyan kaya tayi sallah, umma ta shigo mata da kayan breakfast dak'yar taci kad'an sai zazzab'i,ta sake kiran Salim amman wayansa akashe, dole ta fad'awa Alhj Hashim halin da ake ciki, ya kama fad'a kamar zai ari baki sun masa kiran duniya basu samesa ba, sun sami Abdurrazaq abokinsa yace rabonsa da shi tin jiya da zai tafi Jalingo.
Dole Umma takai Aliyah asibiti aka dubata aka mata allura aka rubuta mata maguguna, suka dawo gida dole ita ce take jinyarta dan tasan ba wani wanda zai shigo gidansu yama Aliyah fayd'e.

Washegari.
Shattima suna idar da meeting yay shirin tafiya gida,k'arfe 4 na yamma jirginsu ya d'aga zuwa dutse daga Abuja.

Maryam
POV
Zaune a bedroom d'inta saman lafiyayan bed d'inta, tayi tagumi da hannayanta biyu,babu abin da take tunani se Shattima.
Fuskar shi take mata gizo, ya kafeta da na narkakkun kaifafan idanunsa yana sakar mata sansanyan murmushin sa mai kashe mata sassan jiki.
Ta shagala da kallon kyakkyawar fuskarshi da yake mata gizo, ta lula duniyar tunani batasan lokacin da Ammi ta bude k'ofar d'akin shigo bakinta d'auke da sallama.
Har ta iso ta zauna gefan gadan bata saniba.
Ammai ta zauna gefenta cike da mamakin Maryam tunanin me take haka? Har tayi sallama ta zauna kusanta ba taji ta ba?
Kafad'arta ta dafa da hannayenta biyu ta girgizata ta ce maryam lafiyar ki kuwa”?
Firgigit tayi ta kalli mahaifiyar tata Se ta Saki mirmishi ta d'an langwab'ar da kanta gefe,tace “Wlh ammi ba komai me kika gani?”
Ammi ta kamo hannayenta duka biyu tace.
“Maryam! Ni mahaifiyar ki ce naga canji dayawa atare dake tinda kika dawo daga gidan Bilkisu,Shin me yake faruwa? Ko wani abu kikaji ga Ummulkhairi ba kyaso ki fad'a mana? Ni de nasan lokacin da muka baro ta lafiya lau take ita da Abdullahi,so akwai wata matsala ne da kikaji KO kuwa wani abune dai bakya so ki fad'amini?
Don Allah ki fad'amin idan baki fad'amin ba waza ki fad'ama?”
Maryam ta sauke ajiyar zuciya da k'arfi haka kawai taji zuciyar ta tayi rauni tana so ta fad'ama mahaifiyar ta duk duniya bawanda take so irin Shattima se de tasan baza ta tab'a samun goyan baya ba gurin mahaifiyarta, kuma ita kanta bazata iya fad'awa wani mahaluki da yake cikin duniyar nan ba , cewar tana Son minister Shattima a bokin mahaifinta.
Wanda matar shi ta d'auketa tamkar 'yar cikinta, kai wannan abun ai abun kunyane ma ace ya fito daga bakinta,zata bar abin aranta koda hakan yana nufin zata rasa ranta bazata tab'a furtama kowa aduniya tana son Shattima ba abokin mahaifinta, wanda yake mata kallon d'iyarsa kamar Khairynsa.
Maryam jin Ammi ta sake dafata tana fad'in.
“Wai menene Maryam yake damunki haka?”
Murmushi tayi ta rungume mahaifiyar ta sai kuma ta fashe da kuka tace.
Wlh Ammi wani irin mafarki nayi , ya firgitani wasu mutane ne guda biyu wai suke bina da wukak'e suna cewa se sun kasheni Allah bai basu iko ba, Zan fad'a wani rami se naga haske yazo,, wani mutum ya Kama hannuna ya fizgeni daga garesu. kawai sena zabura natashi firgigit shi ne yadameni wlh Ammi.”
Ammi kallan d'iyar tata tayi ita de bata gamsuba da bayanin sede kuma zata sanyama yar ta ta ido taga komine ne yake faruwa idan har bata sauyaba sai ta d'auki matakin matsa mata sai taji me ke damunta.
Ta shafi fuskarta tace.
“Maryam! idan mutum yayi mafarki ai addu'a yake , lokacin dakikayi mafarkin naki kuma kince da fararn kaya yake sanye kin gani koda sharri ne ake neman ki dashi,alkhairi ze zame miki tinda kince da fararen kaya kuma ya ceceki baki fad'a ramin ba so dan haka idan kinyi mafarki addu'a zakiyi kinji?

Maryam ta jinjina Kai tace.
“Nagode sosai Ammita I love u.”
Wai ammi tin ma da kuka zo daga Singapore na manta in ce miki yayana be baki komai kikawo min bah?” Zungurar ta tayi akai tace.
“Bakida kirki yayan naki yana cikin halin rishin lafiya me ze bada akawo miki kawai sakon gaisuwa ya bayar agaisheki. Tashi mutafi gasu Nafisa can suna falo suna sha'aninsu ke kina nan najiki shiru ne shiyasa na lek'o naga KO lafiyar ki”
Maryam ta mik'e tana kallan mahaifiyarta.
Langwab'ar da kanfa tayi gefe tace.
Wayyo ni Ammi wlh ina so yau na leqa Mamy nayi missing nata kibari naje na leqota.”
Ammin ta girgiza kai tace.
“A'a ki bari har akwana biyu dika yaushe kika dawo kuma kice zaki koma? Kinga yau mijinta yake dawowa daga Singapore kinga kiba su sarari suga juna OK?”
Se Maryam ta jinjina kai tace.
“Tom shikenan Ammi bakomai,idan an kwana biyu zanje.”
Ammi ta kamo hannunta suka fito falon.
Habib da Nafisa suna zaune se ta zauna acikin su suna fira cikin ikon Allah firan da suke cikin barkwnnci wasa da dariya se ta saki jikinta cikin 'yan uwanta se ta maida maganar Shattima gefe ta ajiye gefe, tabarwa zuciyarta tayi k'ok'arin sakin jikinta ai kuwa ta manta damuwarta sai hirasu suke da k'anninta

Can kuwa Dutse Mamy da masu aikinta su Laraba sun kama mata,ta shiryama Shattima girke-girke na tarba, ta masa duk launikan abincin da yake so da lamuka, an gayara ko ina k'aton falon mai cike ababan more rayuwa sai bala'in k'amshi yake tashi da sanyin A/C.
Tana fitowa daga wanka ta shirya cikin wata lace marar nauni mai taushi Riga da zani, tayi bala'in kyan d'inki ya masheta, tabi jikinta da humrah mai bala'in k'amshi ta shafe, ta fesa sansanyan turarenta mai shegen k'amshi, ta murza d'aurin d'ankwali Zahra buhari, wuyanta yasha sarqar gold haka hannayenta, tayi simple makeup tayi kyau sosai, ta sauko qasa ta zauna saman sofa ta kunna TV hankalinta baya kan Tv ma ta tafi wani dogon nazari, sam bataji qaran door ba, har Laraba ta bud'e masa aka shigo masa da kayansa yazo ya zauna kusanta yana kallonta cike da mamakin al'amarin.
Tattausan hannayensa ya sanya ya d'ago da fuskarta ya k'ura mata idanu cike da bala'in tausayinta, ya rasa me yake damunta kwana biyu, ta canza.
Firgigit tayi ta dawo hayyacinta jin tattausan hannunsa afuskarta tare da sansanye k'amshinsa.
Idanu ta kafa masa gabanta na sake tsanaita fad'uwa,wani irin kyau yayi, sanye yake da wata dakekiyar shaddah Green colour, tai saurin lumshe idanunta tare da saurin tura kanta tsakiyar k'irjinsa ta zagaye hannayenta bayansa ta sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya, tace.
“Mi amor! Yaushe ka shigo wallahi banji zuwanka ba, sannu da zuwa ya hanya I miss you mi amor.”
Shattima ya matseta sosai ajikinsa, yana shafa bayanta, yakai bakinsa dab da kunnenta, ya sauke mata hucinsa mai d'umi, ahankali cikin taushin muryasa ya furta.
“Yawwa sweetheart amman tunanin me kike. haka? Don Allah ki fad'amin me yake damunki? Farin cikin ki shine nawa, damuwarki ita ce tawa,Sam a 'yan kwanakin nan bakida nutsuwa meye fad'amin kodai nayi ajiyene?”
Ita kam tasan abubuwan nan na mafarkinta koda ace ba.... Bazata iya furta masa ba sbd gudun tsayawar numfashinsa, dan haka tasan bazata iya komai akan al'amarin sai addu'ar Allah ya zab'a musu abinda yafi alkhairi.
Murmushin k'arfin hali tayi ta d'ago kanta tana kallon baqar kyakkyawar fuskarshi, ta d'aga masa gira k'asa² tace.
“Wow! Da nafi kowa farin ciki ace yau baby zata samu qani ko k'anwa mi amor banda komai wlh yauma Ina cikin hutun sallah.”
Ta k'arashe mgnar acikin kunnensa tana cizon fatar kunnensa tace.
“Muje ka tub'e kayi wanka sai abinci ya biyo baya OK? Wai ya babyna? Hope tana lfy?”
Mitsinanta yay yana murmushi yace.
“Har ta fiki lafiya tace ki tura mata dambun zabo.”
Mamy Bilkisu ta kyalkyale da dariya tace.
“Ai kuwa dole nayi mata da kaina tsaf a tura mata.”
Ta k'arashe mgnar tana janye jikinta daga na Shattima ta nufi wajan fridge ta bud'e ta d'auke jug ta iso saman table ta d'auki cup d'aya cikin cups d'in da suke Jere saman tire ta tsiyaya masa masoyinsa ta rusuna ta kafa masa abaki ya fara sha.
Tass ya shanye ta ajiye cup ta Kama hannunsa ya miqe yana murmushi zai d'auketa taqi tana dariya tace.
“Please mi amor ni dai da k'afafuna zanje.”
K'ananun bom² d'inta ya riqo yana mata wani shu'umin kallo da ya sanya gabanta fad'u ya bushe da dariya yace.
“Toh ba ruwana duk ranan da kika ga Ina goyon amaryata kika tayar da hankalinki.”
Fuska ta had'e idanunta sun fara Tara ruwa ta ruqunqumeshi tana girgiza kanta..
“Lah! Su Mamyn sweet anji kunya kukan kishi, toh Allah bada haquri oya muje ni kimin wanka wasa nakeyi daga ke na rufe k'ofata.”
Ya k'arashe mgnar yana d'aukarta kamar wata baby ya nufi stairs.
Bilkisu dai jinsa take kawai amman ita tasan me takeji akansan idan ya mata zancan wata macan.


*Singapore*
Azizah sai da ta qara kwana biyu kafin ta tafi Nigeria.
Zaman Ummulkhairi da Abdoul kadaran kada han ne, baya shiga sabgarta itama hakan bata shiga sabgarsa, bayan gaisuwa.
Kullum zata gyara d'akinta da falo taje d'akinsa shima ta gayara masa ta masu girki safe Rana yamma ba kunya zai bud'e cikinsa yaci iya cinsa, ba godi bare na gode.
Yau kwanan Dadynta biyar da komawa Nigeria, hannaun Abdoul kullun samun sauqi yake 'yan makarantarsu koda yaushe kan hanyar zauwa suke gidan nasu, shiyasa Khairy bata zama falon tana d'akinta.
Abdoul zaune yana cin dambun kifin da ya saka Khairy tai masa yana kallon TV tashar MBC action.
Sanye yake da 3 quarter fari sai baqar T-shirt ta kamasa yayi kyau sosai, mulmula sai k'iba yake sabida dadd'an girkin khairy da yake kwasa.
Kamar gumi yakeji na kusantosa tare da k'auri kamar wani abu na qonewa sai ya waiga yana kallon hanyar kitchen tare da fad'in.
“Khairy! Ke! Baki bar wani abu a kitchen ba? Inajin k'auri karki jazamin masifa fa zo ki duba.”
Ya fad'a afusace yana miqewa zai nufi hanyar kitchen.
Wayansa ta d'auki ringing, ya juyo ya
Waiga yaga sunan mahaifinsa na yawo saman screen d'in wayan.
Da sauri ya dawo ya d'auki wayan yay picking call d'in, tare da zama cikin ladabi yay sallama tare da gaishe da mahaifin nasa.
Daga can commissioner Aminu ya amsa cikin kulawa tare da fad'in.
“Abdoul! Ya jikin hope kana jin sauqi sosai? Ina daughter?”
Abdoul ya amsa cike da ladabi yace.
“Alhamdulillah Abba jiki yana sauqi tana lafiya yanzu ta shiga d'aki.”
“Masha Allah don Allah ka riqe yarinyar nan amana ku zauna lfy har ka warke je ka Kai mata wayan ina son magana da ita.”
Abdoul ya amsa da.
“Toh Abba insha Allahu.”
Ya k'arashe mgnar yana miqewa tsaye ya nufi hanyar d'akin Khairy.

Can ciki kuwa khairy ta fito daga wanka kenan, tana goge jikinta da k'aramin towel, babban towel d'aure ajikinta.
K'aran bud'e qofar taji wanda yayi daidai da shigowar kiran Mamy awayanta,kunyar ganin da ya mata ahakane ya sakata saurin
zaunawa gefen bed tana kallonsa tare da had'e fuska,bata d'auki kiran ba har ya katse.
Abdoul ya had'e fuska yana fad'in.
“Abba gata.”
Ya k'araso ya beqa mata wayan,yana zama gefen bed d'in tare da zuba mata mayatattun idanunsa ganin kyawun surata,duk sai ya rud'e.
Sake had'e rai tai tana kallon screen d'in wayan, ganin me maganar yasa da sauri takai wayan kunnenta tare da sallama ta gaishe shi a ladabce, tana kakkare jikinta sbd kallon da Abdoul yake mata.
Abba Aminu ya amsa yana tambayar.
“Hope Khairy kina lfy ba wata matsala koh?”
Khairy ta amsa “Eh Abba ba komai ina ammi?dasu Maryam...?”
Daidai lokacin sukaji k'aran abu kamar tarwatsawar gas kamar kuma k'aran bindiga wani irin dararammm baki d'ayansu suka Saki ihu Khairy ta saki wayar tayi kan Abdoul wanda shima yayo kanta yana sakin ihu tare da rungumeta ya manta viwon da yake ma A hannunsa...

_YI WA KAI...!_


_Free Novel_

*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 19&20*


Ummulkhairi cikin matsanaicin tsoro da fargaban abinda ya fashe, ta sake qamqame Abdoul tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yaya Abdoul kamar fa gaz ne ya fashe,wayyo Allah mun shiga uku,wlh ni dai ban bar gaz akunne ba, se dai A mak'wabta.”
Ta k'arashe mgnar tana zazzaro idanu.
Abdoul ya zaro idanu waje yana fizge jikinsa daga na Ummulkhairi yana fad'in.
“Innalillahi toh maza je kitchen ki duba mana me yake faruwa wlh wutar nan agidan nan

Please Login or Register in order to submit comment