Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuka tana girgiza kanta sabida tuna yadda Baffa Liman ya roqeta akan ta riqe musu amana yanzu yana nufin da ta fad'awa iyayanta taci Amana kenan? Ta kuma tona asirin da har yanzu a lullub'e yake, sabida yadda Abbanta yayi bayani ya nuna Shattima baisan an d'aura masa aure da Khairy. Commissioner ya d'ago kanta ya d'ora akan cinyarsa yana shafa fuskarta,cikin kwantar da murya yace. “Maryamatah! Menene ya faru da kikaji auren Khairy kika fita hayyacinka har suma fad'amin komeye namiki alqawalin bazan fad'awa kowaba.” Khairy ta kalli mahaifinta tana shasheqar kuka tanajin ina ma Allah bazai tambayeta girman karya alqawali da cin amana ba! Da tabbas sai ta bayyanawa iyayanta komai da ta Sani ta d'ora da fad'a musu tana son Minister fiye da ranta. Cikin tsara k'aryar da ta qirqiro yanzun ta bud'e bakinta da ya mata nauyi tace. “Abba! Wlh na firgita da jin Auntie Khairy ta sake aure yayana koh wata bakwai bai rufe ba da mutuwa shine abin ya tab'amin zuciya.” Ta k'arashe mgnar tana kuka. Aminu ya buga bayanta yana murmushi yace. “Haba! Maryamatah! Ai wlh wannan k'arshen so Khairy ta nunawa Abdullahi aure da tayi da wuri, kiyi haquri ki mata addu'ar zaman lafiya da mijinta.” Maryam ta runtse idanunta tanajin bugun zuciyarta na sauyawa. Ammi tace. “Ki cire wannan abun aranki Maryam toh meye dan tayi aure? Ai wlh haka shine daidai.” bata sake magana ba ta rufe idanunta ruf kamar mai jin bacci dan Sam batason maganar ma...

Galadacin Inno zaune tana kallon wa'azi a tashar sunnah Tv, d'iyar wajan Munnir me suna Amal zatayi shekaru 17 tana mita taje ta kwanta ta barta ta canza tasha zuwa Bollywood. Inno tace. "Wlh bazan tashi ba ina jiransu Abdallah ne, wai ke Amal! Ba naji Liman yace aciremana tashar nan ba baya sonta agidan nan? Munafuka idan munyi bacci ita kike kallo koh?” Sallamar Shattima cikin daddad'ar muryasa ta kard'e falon, ta Mamy nabin bayansa, yasa ta katse mgnar da take ta amsa tana fad'in. “Marabarku da zuwa, Abdullah! Bilkisu! Kune tafe da Daren nan?” Shattima ya cire takalminsa yana murmushi ya k'araso yana zama ya gaisheta cikin girmamawa, Amal na gishesa cikin girmamawa, ya amsa cikin sakin fuska yana tanbayarta yayan nasa. Mamy ta rusuna ta gishe da Inno. Inno na amsawa cikin sakin fuska tace. “Kunyi dare ko wani wajan kuka biya ne?” Shattima yace. “A'a Inno Baffan yana ciki koh?” Inno tace. “Eh yana can b'angaransa yana jiranku.” Shattima ya miqe yace. “Ok bari muleqa.” Amal tace. “Mamy! Gobe zanje muku weekend. ” Mamyt tayi murmushi tace. “Ok ina jiranki fa!”

Liman yana zaune Qur'ani A hannusa karatu yake. Da sallama suka shigo. Sai da ya k'arshen ayar ya d'ago yana amsa musu sallamar yana rufe Qur'an d'in, lokacin har sun zauna qasa saman tattausan carpet d'in falon. Cikin girmamawa suka gaishesa, ya amsa gaisuwar yana fad'in. “Sai yanzu kuka samu isowa? Madallah.” Sahttima yace. “Eh Baffah.” Liman yayi gyaran murya yace. “Abdallah! Inaso ka saurareni kaji bayanina, Amman kacin wannan kasan dai nine mahaifinka ko? Kuma kasan bazan tab'a cutar dakai ba bazan yi abunda bai daceba akanka, sannan dakai da duk wani abunda ka mallaka mallakina ne hakane koh ba haka bane?” Shattima cike da girmamawa yace. “Hakane Baffa.” Liman yace. “Yawwa naji dad'i Allah ya maka albarka, maganace akan Ummulkhairi. ” Shattima yace. “Toh Baffa Allah yasa lfy?” Liman yace. “Ita tayi yawa na d'aura mata aure da mijin da ya dace da rayuwarta.” Da wani irin sauri Shattima ya d'ago kansa yana kallon mahaifin nasa. “Baffa aure kuma? Da wa kenan? Ita ce tace tana so? Waye shi??” Liman yayi nurmushi yace. “Bata ma saniba nayi kawai dan na isa da kai da itan koh ban isaba?” Shattima yayi qasa da kansa yana had'iye yawu mai d'aci ya lumshe idanunsa zuciyarsa fal cike da tausayin 'yarsa yace. “Baffa ka isa ko ni da kaina kama wannan hukuncin yayi bare kuma 'yata ta cikina wacce bata tsallake maganata, hakan ya farune sabida nima banma iyayena musu ba, mungode Allah ya saka da alkahiri yabasu zaman lafiya ya bata juriya da amsar mijinta. Baffa Zan iya saninsa?” Liman ya b'oye dariyarsa ya had'e fuska yace. “A'a ba yanzu ba lokacin bayyanawa idan yayi zaku Sani Ku dukanku, bance ka fad'a mata ba.” Shattima yace. “amman Baffa idan ta Sani kamar zata kiyaye dokokin wasu abubuwan da ya kamata matar aure ta kiyaye koh?” Mamy tace. “Haba! Dadyn Khairy kawai kabar komai ahannun Baffan kamar yadda ya umarcemu, Baffa mungode Allah ya bada lada ya qara maka lfy da tsawon rai me anfani.” Liman yace. “Ameen Bilkisu na gode Allah ya muku albarka.” “Ameen.” Suka amsa Liman ya musu nasiha akan suyi hak'uri gaba kowa abun zai masa dad'i idan mijinta ya bayyana... ★ Tsakiyar dare tsaye yake akan darduma yana bautawa Allah. Mamy kwance tana kallonsa tana lumshe idanunta. Qarfe 3 cif ya hauro saman bed d'in. Lokacin Mamy tayi bacci, rungumeta yayi yana sumbatar lips d'inta. Ajiyar zuciya ta sauke tana qara shigewa jikinsa, idanunsa lumshe ya zagaye hannayensa bayanta duk idan yakai tunaninsa da hasashensa bai gano da wa Baffa ya had'a Khairy aure ba! “Ya Allah kasa wannan auren ya zamema Baby farin ciki da kwanciyar hankali na har abdan...” ★★★ Bayan sati biyu. Maryam ta murmure ta barwa Allah ikonsa tana addu'a idan Shattima alkahirine Allah yasa ta zama matarsa ta 3 dan ko 3 gareshi zata shiga ta zama ta 4 sai dai tasan da wuya sabida yaunin Mamy. Shattima ya haqura yana roqon Allah yaba Khairy haqurin d'aukan duk randa Liman ya fito ya fad'i mijinta amincewa ba tare da ta tayar da hankalinta ba. Har yau kuma baima commissioner mgnar ba, shima bai masa ba. Yau kwanansa biyar A Abuja Amman ya kasa zuwa yaga Khairy haka kawai take basa tausayi. ★

Gumel Hajiya Karima tana zaune Apple take ci kamar bataso tana latsa waya tana murmushi. Anci ubansu kwalliya ansha gold, wani uban lace ajikinta mai tsada. Nadiya Ce ta fito tana waya ta zauna kusan mahaifiyarta, tana dariya tace. “Wlh Ya Ayuba bansan me zance ba,tsakani da Allah fa! Ni kallon yaya nake maka banajin zanyi iya soyayya dakai bama wannan ba ni inada wanda mukayi magana da shi, kawai ayi zumunci Ya Ayuba bana son kaga na yaudareka...” Hajiya Karima ta maido hankalinta wajan d'iyar tata, kallonta take har ta gama wayan. Rungume Hajiya Karima tayi tana dariya. “Nadiyah? Wane Ayuban kuke waya?” Nadiya tace“Ya Ayubah d'an mama Shaheeda k'awarki.” “Au d'an nawa kikecewa bakya so?” Baki ta turo tace. “Mom Ai gaskiya ni Lamir nakeso yana dawowa fa zai turo tambaya bai fi wata 5 sauransa ba, ya dawo daga Madinah.” Hajiya karima ta washe baki tace. “Bana takura y'ay'ana wanda kukeso zaku aura daman banma uwarsa alqawaliba.” Nadiya sosai tayi murna tana rungumeta. Wayar Hajiya Karima ta d'auki ringing. Tana ganin sunan Usman ta d'aga kiran tana fad'in. “Mutan Kaduna ya aiki?” Daga Kaduna Usman zaune cikin tsararran office d'insa, yana danna laptop, yayi kyau cikin milk d'in suit yamata sallama yana gaisheta tare da cewa. “Ashe Dad baya gari da safe munyi waya? Ya Nadiyah?” Hajiya Karima tace. “Eh baya nan ai shi yawo kamar jirgin sama, kai kam baka suna d'aya jace Dad kace Baba kace abba? Toh ykk nace yaushe zamu shirya muje Jigawa yin godiya wajan Minister Abdallah Shattima? Wlh inaso na k'ulla alaqa da matarsa?” Usman yace“Alaqar me kuma Mom don Allah ki tsaya Inda Allah ya ajiyeki muma Allahya rufa mana asiri munada kud'i daidai misali, kije kicewa matarsa me? Akace miki idan yayi alkahiri sai matarsa ta sanine?” Hajiya Karima tana hura hanci tace. “Kaci ubanka kai zaka nunamin hanya ko gaskiya? Idan naso sanin Matar minister kai zaka hanani dan ubanka? Sam Usman baka biyo ni ba.” Usman dan kar suyi rabuwar rashin arziqi ya shiga bata haquri har ta sauko tabasa Nadiya sun jima suna hira kafin ya katse kiran yanana mahaifiyarsa addu'ar shiriya.

Abuja Misalin 5pm. Wani irin hadarine baqi ya taso lokaci d'aya jama'a dayawa basu ankare ba da hadarin da wuri ba. Cikin kuwa harda Ummulkhairi wacce ta biyo Marfu'ah d'iyar Auntie Aisha wajan bikin k'anwar mijinta, ba garin suke ba suna kudu can Oyo state mijinta yake aiki. Anata shirin zuwa dinner ne hadirin ya taso hakan bai sakasu fasawa ba. Khairy sanye da wani shegen dakeken lace maroon yayi mata masifar kyau, d'inki rigar da skirt, abinka da mai kauri kad'an ga d'an tsayi, sai tayi masifar kyau, mayafinta maroon takalmi maroon handbag maroon,Tasha gold wuya da hannu ga zobenta uku ajera A yatsunta, simple makeup aka mata dole fa ta burgeka, sai wani sahihin k'amshi take. Idanunta ta shiga rabawa daga mab'uyarta, sbd batason taje dinner Mummy ta mata kashedi, sbd tasan tana zuwa sai an mata caaaa samari ita kuwa matar aure ce. Tana tsaye sai da motocin suka tafi harsu Marfu'ah wacce anata tunanim Khairy na tare da Jaliah amarya dan tare ta had'osu sai tayi k'aryar zatayi fitsari. Ajiyar zuciya ta sauke tana fitowa daga malab'arta, cikin sauri take tafiya har ta five ba wanda ya lura da ita. Bakin titi ta tsaya tana jiran abin hawa ga iska an fara. Kusan wannan motar da ta tsaya gabanta itace ta biyar, ko kallo basu isheta ba. Horn yayi mata ta kauda kanta tayi gaba da sauri sabida ruwa da ya fara saukowa. Motar yasha gabanta yay parking ya janye glass wani matashine fari mai kyau ba laifi sanye da jeans da T-shirt. “Haba baiwar Allah bakiga anfara ruwa ba? zo na saukeki ko bakya ganin titin shiru ba jama'a wani zai iya cutar dake fa!” Kamar zatayi kuka tace. “Ni dai bazan hauba Dady ya hanani hawa abin hawan namiji idan ba na haya bane, kuma Mamy ma sannan Mummy idan taimakona zakayi ka nemomin abin hawa taxi ko keke napep.” Kansa ya dafe yace. “Wallahi baza'a samuba nan kusa muje muna dubawa idan an samu Zan saukeki nayi miki alqawali.” Matsagaitan fararen idanunta ta kafa masa sabida tabbatarwa maganarsa, ya d'ora hannunsa akai yace. “Na rantse miki Baby.” Kai ta jinjina Ahankali ta fara takowa jikin motar sabida ruwa ya fara jiqata sosai. Adaidai lokacin wata wulleliyar baqar mota mai shegen kyau, farare biyu na biye da ita suka tinkaro daidai wajansu Khairy. Shattima da yake kame cikin baqar motar ya hakimce jarida A hannunsa yana karantawa, kamar ance masa d'ago kanka, idanunsa bai sauka ako ina ba sai akan kyakkyawar fuskar Ummulkhairi da yayyafin ruwan yake tab'a fuskarta, tana qoqarin shiga motar, da yake glass d'in farine ana kallon direba tarr Shattima sam baisan yaron ba. Da wani irin sauri yace. “Maleek! Kayi saurin isa wajan can yimasa horn da k'arfi ko waye.” Take Maleek direba ya yayi abinda Shattima ya sakashi. Khairy da har ta rusuna zata shiga motar tsoro ya hanata ta d'ago da sauri jikinta na b'ari jin horn d'in kamar zata fasa dodon kunnenta. Da wani irin sauri Maleek yay parking. Shattima bai jiraba a bud'e me ya fito cikin shigar wasu irin suit farare qal masu D'an banzan kyau, yana zuba wani mayen k'amshi. Security na bin bayansa da Lema ya d'aga masa. Ummulkhairi ganin Shattima wani irin tsoro ya kamata jikinta ya d'auki rawa ta runtse idanunta ta fashe da kuka tana fad'in. “Dady! Wlh ban sanshi ba hanya zai ragemin sabida ruwa kuma wallahi sai da ya rantse min bazai cutar daniba...” Tattausan tafin hanunsa taji saman labb'anta, ya rufe mata baki tare da kamo hannunta ya fara janta anotse yake tafiya da ita, security ya rufa masu Lema. Daidai saitin Glass ya tsaya ya kalli yaron yace. “Ngd da taimakon da kaso yima 'yata.” Yana fad'in haka yaja yana manne da hannunta suka isa motar, kallon sojan da suke farar motar yay yace. “Wannan yaron duk Inda yayi kubisa har kuka Inda zaije kuyi qoqarin bincika min me had'insa da 'yata daga yau zuwa gobe kuje aikinku.” Ya k'arashe mgnar yana shigar da ita motar, kafin ya shiga arufo musu motar direba yaja yabar wajan. Khairy rawar sanyi ta fara sbd yadda ta fara jiqewa ga sanyin Ac. Kuka take k'asa² tana kallon Shattima da ko kallonta baiyi ba, ya d'auki jaridarsa yana qoqarin karantawa. Jikinsa ta shige ta qanqameshi tana rawar sanyi ta sakar masa kuka mai sauti harda shasheqa tana fad'in. “Dady don Allah kayi haquri, wlh ba yawo naje ba kaji?” Muryasa taji cikin kamewarsa yana fad'in. “Maleek! Kashe A/C.” Ya fad'a yana lullub'eta da jacket d'insa wace kowace motarsa akwaita. Luf tayi ajikinsa tana kukanta k'asa² sanyin sosai ya rage mata sabida d'umin jikinsa da yake shiga jikinta. Kamar amafarki taji sautin muryasa babu wasa yana tambayarta. “Ummulkhairi! Daga ina kike? Wallahi tallahi kika min k'arya na gano gaskiya kashinki ya bushe wajena....”

+22796515805

*YI WA KAI*

Free Novel

_October29/10/2022_


*43&44*


Khairy ta d'ago kanta da sauri daga jikin Shattima, jin tambayar da ya jefo mata ba alamaun wasa, ta kalleshi ta na toshe bakinta sabida kukan da take.
Wani kallo ya watsa mata, yace.
“D'agani ki zauna wajan zamanki muyi magana, tin ban zuba miki maruka ba.”
Khairy jikinta na rawa ta janye daga jikinsa ta rakub'e ajikin kujarata, har yanzu kallonsa take, ganin ya maida hankalinsa wajan jarida kamar ba shi yayi magana yanzu ba.
“Dady! Kayi haquri wlh ba yawo naje ba, Allah Dady.”
Shattima ya kalleta yana sake had'e fuska yace.
“Khairy! nace daga ina kike waye wannan da na gani zaki shiga motarsa? Daman fitowa kikeyi kina yawo a abujan shiyasa kike son zaman nan d'in?”
Ya k'arashe mata tambayar cikin tsawa marar sauti yadda ita d'aya zai razana.
Yadda yakai k'arshen mgnar ba qaramin tsoronsa taji ba, ta sake lafewa ajikin kujera cikin kuka tayi masa dukkan bayanin abinda da ya faru wajan bikin, tare da cewa.
“Wallahi Dady ban sansa ba ban tab'a ganinsa ba, taimakona zaiyi har saida ya rantse min na yarda zan shiga ya kaini gidan, kuma duk naqi zuwa wajan dinner d'in ne sabida kai da Mamy ban manta kashedinku ba, Mummy ma ta barni ne sbd auren k'anwar mijin auntie Marfu'ah ne, tare mukaje dasu Mummy sai auntie tace ni natsaya, Allah Dady gaskiya nake fad'a maka.”
Ta k'arashe mgnar cikin matsanaicin kuka tana kifa kanta saman cinyarta.
Shattima ya sauke ajiyar zuciya tare jan dogon numfashi, yana lumshe idanunsa na second 5 ya bud'e ya zuba mata idanu, ta kifa kanta saman cinyarta, tana kuka.
Ya yarda da maganarta,sabida yasanta yasan halayyarta tin tana 'yar qanqanuwarta, amman duk da haka bazai barta ba da ita zai wuce jigawa sbd idan ana irin haka watarana za'a iya samun matsala babba, ga shi da igiyar auren wani akanta.
Lips d'insa na qasa ya d'an ciza kad'an yana lumshe manyan kaifafan kyawawan idanunsa, na seconds 10 yanajin kukanta har cikin b'argonsa. Handkerchief ya zaro mai bala'in k'amshi ya bud'e idanunsa, ya gyara zamansa, yana sanya tattausan hannunsa ya d'agota yana riqe fuskarta, anutse yake kallonta yana goge mata hawayen fuskarta, cikin kamewarsa da nutsuwarsa muryasa na fitar da sauti mai taushi yace.
“Ya isa haka kukan Baby, kar ki kuma hakan fitowa ke d'aya Ok?”
Ya k'arashe mgnar yana shigar da kaifafan idanunsa cikin nata, tare da goge mata dukkan fuskarta da handkerchief.
Shiru tayi ta daina kukan tana d'aga masa kanta, tare da lumshe idanunta ta kwantar da kanta k'irjinsa, take taji wani bala'in sanyi yana ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya tana sake lafewa ajikinsa cikin sanyi murya had'e da shagwab'a tace.
“Sweet Dady kayi haquri bazan qaraba, ni mutafi ma dutse wajan Mamy amma karka fad'a mata please sweet Dadynah.”
Ta k'arashe mgnar cikin zallar shagwab'a kamar zatayi kuka, tana sake shigewa jikinsa, tana jin duk duniya ba Inda takejin sanyi da nutsuwa da dad'i tare kwanciyar hankali irin taji ta ajikin Dadynta kwance tana qamqame da shi.

Shattima ya zagaye hannayaensa bayanta yana bugawa, tare da sakin murmushi, dan shi Sam tinda yake bai tab'a jin Khairy ta gusa daga matsayin 'yarsa da ya Haifa ba da cikinsa, haka ko me zatayi ajikinsa bai taba'a jin feeling akan haka ba tsakaninsa da Allah 'yarsa yake kallonta kamar yadda duniya take kallo.
Dan haka ya sake shigar da ita jikinsa yana lullub'eta da jacket, ya mata magana dab da kunnenta yace.
“Kina son mu wuce dutse direct uhmm?”
Awani shagwab'e ta d'aga kanta tana sake qanqameshi, tare da cewa.
“Eh Dady please. ”
“Ok..OK! Baby zamu wuce amma idan na gama abubuwan da nake, baki d'aya wannan watan ina nan Abuja ki zauna wajan Auntie idan na gama zamu wuce OK?”
Kai ta d'aga tana sauke ajiyar zuciya.

Acan kuwa wajan dinner anata shagali, sai daga baya Marfu'ah taga Khairy bata wajan su Jalilah, ta tambayeta ina Khairy? Nan ta sanar da ita ai har sun fito zasu shiga mota tace zataje fitsari, sunyi tajiranta bata fito ba, suka tafi ta zata tana ita zata biyo.
Marfu'ah hankalinta ya tashi, nan ta shiga nemanta bata wajan taron, ta Kira mijinta ya dawo da ita nan gidan bikin an dubata bata nan, Marfu'ah ta Kira Mummyn hankalinta atashe taji ko tazo gida.
Auntie Ausha tana tsaye tsakiyar falonta, har wata zufa take tsattsafo mata cikin tashin hankali tace.
“Marfu'ah! Kinada hankali kuwa kinsan me kike cewa? Ummulkhairin Ce ba'a ganiba? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Sai da nace mutafi da ita kika matsa na barta ga irinta na,kawai fitowa zatayi ganin hadari tace ta tari abin hawa ta dawo gida, ga shi batada waya bare na kirata naji, ganina fitowa yanzu.”
Ta fad'a tana katse kiran ta Kira direba ya fito da mota.
Marfu'a kuwa daga can harda kukanta hankalinta atashe, mijinta ya jata suka fita sai yawo suke saman titi cikin mota suna dube-dube ana sheqa ruwa, duk me taxin da suka gani sai sun tsayar da me napep, sun duba shiru ba labarin Khairy hankalinsu yayi masifar ta shi
*Maitama*
Wani narkeken gidane mai bala'in kyau, gini tamkar aqasar Saudiya, mai bene hawa d'aya tak, gidan ya tsaru iya tsaruwa, ya had'a kayan jin dad'i da more rayuwa, Kai kana kallon gidan daman kasan sai minister's ko governors da sauransu.
Maleek yana parking ya fito, qaton sojan nan mai d'auke da bindiga ya bud'e ma Shattima qofa, ya matsa can gefe.
Shattima ya kalli Khairy wacce tayi luf ajikinsa tsakaninta da Allah bacci takeyi.
Murmushi yay marar sauti ya shafi fuskarta, yay qasa da kansa yana kiranta ahankali.
“Daughter! Baby! Oya tashi.”
Kanta ta sunne qirjinsa tana shaqo fitinannan k'amshisa ta saqo hannayenta wuyansa idanunta arufe kamar zatayi kuka tace.
“Sweet Dady! Wlh bacci inaji ni bazan iya tafiya da qafafuna ba, ka tuna da ka goyani kaji Dadynah?”
Ta k'arashe mgnar kamar zatayi kuka, tana bud'e matsagaitan fararen idanunta, ta saukesu akan kyakkyawar baqar fuskarshi.
Idanunsa ya shige waje d'aya suna kallon juna, Khairy tayi murmushi tana shafa sajansa ta cinno baki gaba tana son sakin kuka tace.
“Dadynah! Ka kulani kaji?”
Harara ya zuba mata yana fad'in.
“Oya sakeni ki sauka amotar nan tin ban hukuntaki ba! Keda bakya girma kin fini qiba kikeson na goyaki ki karyani? Yanzu ai kin wuce goyo kina yarinya ya halatta na goyeki ba yanzu ba, na kuma ganin kin sake cewa na goyaki sauka muje.”
Ai take ta dawo nutsuwarta ta zare jikinta anasa tana matsar k'walla ta bud'e qofar b'angaranta ta sauko tana sanya yatsarta abaki.
Yana saukowa ya zagayo ya zare mata yatsar abakinta, ya Kama hannunta suka nufi cikin gidan.
Kallon ko ina take na gidan anutse tana maqale da hannun dadynta.
Wani irin sanyi da qamshi ta shaqa a falon ta saki hannun Shattima tana hawa saman sofa tace.
“Sweet Dady gidan ya qara kyau wlh, Dady bari na mana girki me dad'i.”
Kallonta yayi yana nufar stairs yace.
“No! Akwai kuku yana kitchen yana yi ai, oya wuce kije ki cire kayan nan na jikinki, kiyi wanka lokacin sallar Maghreb ya gabato, kisha magani kar kiyi mura.”
Direwo tayi daga kan sofan aguje tabiyo bayan Shattiman tana fad'in.
“Dady! Toh wane kaya zan saka toh kaban jallabiyarka koh?”
Bai tankata ba ya haye stairs da sassarfa sabida kar ya makara zuwa masallaci al'adarsa Ce zuwa masallaci Kafin akira sallar Maghreb.

*Katsina*
Zinabu tana zaune kitso takema Jamilah, innah ADAMA tana surfen hatsi zatayi fura, gobe tinda safe takai wajan rasuwa d'an k'aninta da ya rasu shekaran jiya.
Raihana tace.
“Umma! Wlh na manta na fad'a miki jiya mafarki na miki, wai wata yarinya budurwa baqa mai kyau tana binki tana kuka tana kiran Umma! Dan Allah kizo ki Kama hannuna Ina sonki nice 'yarki ban mutu ba.”
Raihana ta fad'a tana dariya tare da cewa.
“da na fad'awa wata 'yar ajinmu tace banyi addu'a bane da nayi addu'a ba zanyi wannan shirmen mafarkin ba.”
Zainabu tayi murmushi tana kallon Raihana, ta tsayar da kitson ta shiga mata bebanci da hannu.
“Ni yaushe ma rabona da haihuwa bare na haifa har ta dinga bina ina gudu? Allah yasa inada rabon ganin d'ana ko d'iyata bayan Ku ameen.”
Duk suka amsa da “Ameen.”
Sabida suna gane firata.
Jamila tace.
“Ummah! K'ilan kin kusa aure shiyasa Raihana ta fara mafarkin k'anwarmu.”
Zainabu hawayen fuskarta ta goge tana cigaba da kitson, Inna ADAMA tace.
“Tau zaki fara koh?
Zainabu ta girgiza kanta.
Abbune yayi sallama ya shigo.
Khabir ya tarso da gudu yana masa sannu da zuwa.
Inna ta masa sannu da zuwa, Zainabu da yaran suna masa sannu da zuwa ya amsa, yana fad'in.
“ADAMA! Surfe kusan Maghreb? Abun ki bayar akai ingi a sirfo?”
Murmushi tayi batace komai ba.
Ya zauna ya amsar ruwan da Raihana ta kawo masa ruwa yasha ya miqe yana fad'in.
“Gobe idan Allah ya kaimu da asubah zamuje Abuja, d'aurin auren d'iyar oganmu me kamfanin, ai kinsan nace miki acan iyalansa suke, toh gobe motoci zamuyi muje daga kamfani jibine d'aurin auren amman yace gobe mu hallara dan mu huta tinda bayan d'aurin aure zamu juyo.”
Inna ADAMA da ta ajiye tab'arya tana juye hatsin da ya gama surfuwa tace.
“Allah ya kaimu goben ya Kai Ku lafiya ya maidoku lfy.”
Ta fad'a tana d'auko butarsa ta zuba masa ruwan alwala ta beqa masa.
Amsa yayi yana amsawa da.
“Ameen”
Zainabu ma addu'a tayi masa su Jamila ma, yana amsawa da Amin.
(😂Ni ko nace Allah yasa Abbu ya had'u da Shattima.💃)
*Dutse*

8pm Mamy zaune a cikin falonta, sanyi A.C na ratsata, tana sanye da doguwar riga 'yar Saudiya,marar kauri mai gajeran hannu Ash kala, ta mata kyau a siririn jikinta mai kyan fasali.
Laptop ne agabanta tana dannawa.
Qaran door bell taji ta d'ago kanta tana kiran.
“Laraba! Je ki bud'e k'ofar mana.”
Laraba da take kitchen suna aikin girkin dare da basu idar ba har yanzu sbd sunje kasuwa yau, dan Mamy idan Shattima baya gari bata girki da kanta.
Aguje ta fito ta tafi.
Mamy ta d'aga kanta taga 8:10pm.
Sallamar Madina cousin, d'inta da Fauziya k'anwarta taji, ta d'ago kanta.
Murmushi tayi tana fad'in.
“Oyoyo lallai inada baqi yau.”
Ta fad'a tana miqewa ta tarbesu.
Rungume juna sukayi su ukun.
Fauziyya tace.
“Wlh Aunt Billy kinyi 'yar k'iba tsaf sai wani sheqi kikeyi, Anya ba Khairy zata samu k'ani ko k'anwa ba?”
Mamy ta zauna tana kai mata dukan wasa,tare da harara tace.
“Ai ni kam na barwa Babyna haihuwa shekaru 41 fa gareni ai da kunya ace ni ina haihuwa Baby na haihuwa, na barmuku keda baby kam.”
Fauziyya tace.
“A'a wlh hamma Shattima yana so kawai ki bamu baby, ga auntie Madina ma na haihuwa wacce ta girmeki bare ke.”
Mamy tayi murmushi tana d'aukan cup glass da Laraba ta kawo musu ruwa da lemo ta tsiyayama Madina ta beqa mata,ta amsa tana godiya, ta kurb'a tana ajiye tace.
“Bilkisu gobe zamuje Abuja gyaran gidan Lailah d'iyar yayan Alhaji, ki bamu address d'in gidansu Khairy sai muje mu dubota.”
Fauziyya tana Kai kankana bakinta tace.
“Wlh da Abban Nawwara zai yarda sai na biku ni dan naga Khairynah.”
Mamyt tace.
“Masha Allah biki yazo Ashe? OK Zan kuwa baki saqo ki Kai mata.”
Ta fad'a tana d'aukar wayanta, tayi dialing lambar Auntie Aisha tana ringing ba'a d'auka.
Katsewa tayi, tana fad'in.
“Maybe tanada baqi ko wayan na chaji, bari na Kira Mi Amor sai ya turan address d'in kai tsaye.”
Ta fad'a tana dialing lambar Shattima.

Acan Abuja kuwa daidai lokacin Shattima yana zaune, A dining area suna dinner da Khairy tana kusansa sai santin girkin kukun sa take.
Kallonta yayi Tana sanye da Turkish gown, ta yane kanta da mayafin qafafunta sanye da flat shoes fari, tayi kyau sosai barin yadda rigar bata kamata ko kusa, komai nata lullub'e ruf banda k'irjinta wanda dole tasa cikarsu sun danno

Please Login or Register in order to submit comment