Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace wallahi tun bamu bada ƴan kallo ba, muka raba hali a titi me haɗin ka da Zainabu? Zindiƙin ƙato kazo kana taɓa ta, sauketa..."
Liman da Shattima suka haɗa baki wajan roƙonsa akan ya matsa ya shiga ko soron ƙofar da ita.
Abbu ya girgiza kai yana faɗin.
"Duk da ban sanku ba, kallo ɗaya za'a gane kuna da mutunci, amman kuyi haƙuri bazan yafe Wannan bawan Allah ba."
Ya faɗa yana isowa wajan Mustapha ya sanya hannunsa ya amshi Zainabu ya juya ya nufi ciki yana faɗin.
"Na rantse da Allah idan ka shigo min gida sai na ɗaureka..."
Liman yace.
"Bawan Allah mu ka bamu izinin mu shigo?"
Abbu yace.
"Eh ku shigo banda shi."
Ya faɗa yana shigewa cikin soron kai tsaye ya wuce cikin gidan yana banbamin faɗa.
Usman yana riƙe da hannun Karima yace.
"Wai Mom me yake faruwane haka? Kalli jama'ar da kika tara mana."
Kuka take tana sosa jikinta tace.
"Wallahi ban saniba ku tambayi babanku."
Shattima ya nufi soron ƙofar yana sakin tsaki, takaicin Karima ta ishesa da mutuncinsu da darajar su tana nema ta tara musu jama'a.

Liman ya kalli Usman da Nadiya yace.
"Ku mu shiga, kai Mustapha kayi haƙuri ka koma mota ka zauna har na shawo kansan karkaga laifinsa fa!"
Mustapha ya goge gumin fuskarsa ya jinjina kansa yana nufar mota.
Liman yaja su Usman suka shiga ciki.

Karima da Gudu tabi Dad Mustapha tana kuka tana faɗin.
Dadyn Usman wai me na maka kake wulaƙantani?"
Wanke fuskarta yay da mari yana hankaɗata, sai da ta faɗi ya shaƙo
wuyanta cikin ɗacin zuciya yace.

"Me ma yasa na aureki? Ke ba irin macan da nake so bane, wlh bansan yadda akayi na aureki ba shekaru kusan talatin da wani abu Ni ban taba jin daɗin zaman aure dakeba, kece kika rabani da Zainabu koh? Wlh idan haka ta tabbata sai na sakeki saki uku..."
Ya faɗa yana hankaɗata ta sake faɗuwa ƙasa.
Wani irin ihu tayi tana birgima a ƙasa tana faɗin.
"Allah ya tsinema Zainabu tinda ta shigo rayuwarmu na kasa gane kanka..."

Can cikin gidan bayan su Mamy sun shiga, da sallama.
Inna ADAMA ta amsa musu fuska sake tana kallonsu hankalinta wajan Khairy ganin tana yanayin Zainabu. Sai dai wannan da ganinsu ba ƙananun wayayyu bane, koda yanayin suttura jikinsu ta nanu wasune barin yadda fatarsu take sheƙi.
Tabarma ta shimfiɗa musu tana faɗin.
"Bismillah ku zauna."
Ta faɗa tana shiga kitchen ta ɗauko kwanon silver sabo taje randa ta kwalho musu ruwa me sanyi ta kawo ta ajiye musu ta koma saman ɗayar tabarmar ta zauna.
Abin mamaki taga Mamy ta ɗauki kwanon tasha ruwan sosai, haka Khairy ma, sosai taji daɗin hakan, sai murmushi take.
Tana shirin tambayar su ne Abbu ya shigo da Zainabu yana sababi.
Inna ADAMA ta miƙe tana faɗin.
"Subanallahi malam me zan gani? Ina ka tsintota? Yanzu fa ta fita siyan kifi tace muyi jalof."
Ta faɗa tana ɗaukan sauran ruwan dasu Mamy suka sha, ta sheƙama Zainabu ajikinta.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana buɗe idanunta, tana fashewa da kuka tana girgiza kanta.
Inna ADAMA, tace.
"Sannu Zainabu me ya faru a wajan?"

Abbu ya riƙe hannunta yana faɗin.
"Kwantar da hankiinki, ƙara zamu shigar kotu wlh, barima kuka kina ɓata ranki."
Kai Zainabu ta jinjina kanta tana lumshe idanunta.
Shasheƙar kukan Khairy ne yasa Zainabu ta ɗago tana sauke idanunta akan kyakkyawar fuskarta.
Sai lokacin Abu ya waigo yaga Mamy da Khairy.
Mamy tace.
"Dan Allah kayi haƙuri insha ALLAHU komai yazo ƙarshe Zainabu zata samu ƴancinta fiye da yadda bakuyi zato ba."
Abbu yace.
"Ok wato keda wannan me fuskar Mustapha kune ya turo ku yaudari ƙanwata ko me kuke nufi?"

Zainabu dai ta ƙura ma Khairy idanu, tana kallon ta kamar zata cinyeta.
Khairy ta sadda kanta tana kuka ta rungume Mamy.
Mamy tace.
"Don Allah Baby kiyi haƙuri bari kukan.
"A'a Baba ba haka bane mu alkhairi ya kawo mu kayi haƙuri..."
Sallamar da liman yake ne ta katse ma Mamy magana.
Abbu ya miƙe yana amsawa ya nufi soron ƙofar.
"Bismillah ai nace ku shigo."
Ya faɗa yana musu jagora zuwa cikin gidan.
"ADAMA kawo babbar tabarma."
Ta miƙe cikin sauri ta shiga ɗaki.
Babbar tabarma ta ɗauko ta shimfiɗa musu, ta kawo musu ruwan randa me sanyi ta gaishesu ta koma wajansu Mamy.

Shattima ya kalli gefensu Mamy yaga sai kuka Khairy take harda shasheƙa, Mamy na aikin lallashi.
Kansa ya ɗauke tunda baida daman lallashinta, dole zai daure.
Liman yace.
"Ummulkhairi! Me ya faru kuma kike kuka?"
Rage kukan tayi ta ɗago kanta tana kallon Zainabu.
Idanu suka haɗa tana mata nuni da hannunta tayi shiru.
Khairy cikin kuka tace.
"Bakya magana ne?"
Zainabu ta ɗaga kanta da kurmanci tana nuna mata da hannu tun tana ƙarama daga ciwon dussa ta rasa bakinta.
Khairy ta share hawayen fuskarta tace.
"Bansan me kika ceba."
Inna ADAMA tace.
"Ce miki tayi tun tana ƙarama da tayi ciwon ƙanda ta kurumce tanaji amman bata iya maidawa."
Khairy tace.
"Allah Sarki sannun Umma."
Khairy ta faɗa tana kwantar da kanta cinyar Mamy tana lumshe idanunta.
Zainabu taji wani irin bala'in sanyin daɗi da nutsuwa wacce rabon da taji irinta tun tana tare da Mustapha.
Mamy ta shafi fuskar Khairy tace.
"Baby akwai gajiya koh?"
Khairy ta ɗaga kanta tana

kallon ɓangaren dasu Shattima suke, zaune Liman nayima Abbu magana.
Idanusu ya manne waje ɗaya, ta janye idanunta tana cinno baki gaba, tare da lumshe idanun nata.
Shattima ya shafi sumar kansa yana sakin sihirtaccan murmushi.
Mamy ta murmusa tana kauda kanta kamar bataga abinda yake faruwaba.

Liman ya gyara zamansa yana faɗin.
"Don Allah kayi haƙuri Mustapha ya shigo magana zamuyi ta fahimta dole sai da shi hakan zata kasance, kayi haƙuri nine na nemi alfarma."
Abbu ya numfasa yace.
"Shi kenan yaci darajar ka ya shigo."
Liman yace.
"Na gode sosai, Usman kira Mahaifinka."
Usman ya amsa da.
"Toh ya miƙe ya fice.

Can kuwa waje Mustapha cikin mota ya shige yabar Karima nan kamar kamun mahaukaciya, tana sambatu yara na mata dariya, ta kuma gagara shiga gidan.
Usman ransa aɓace ya shiga kore yaran, ya sunkuya ya kama hannunta yana faɗin.
"Haba! Mom wannan wani irin abun kunya ne kika jaza mana haka? Don Allah ki shiga ciki."
Ya faɗa yana jan hannunta.
"Usman ka rabu dani bakaga cin fuskar da mahaifinku ya yi min ba cikin mutane?"
"Ni bansan me ya haɗaku ba, amman shiga ciki ki jira komai zaiyi daidai duk da bansan me ke faruwaba."
Ya faɗa yana sanya har cikin gidan.
Da kallo suke abinsu.
Zainabu ta ƙura ma Karima idanu, tana murmushi ta yafi tota da hannu, tunda Ita dai bata san Karima ta cutar da ita a a zamansu, tunda zaƙon ƙasa ne ta mata.
Karima ta nufi Zainabu tana kuka sai sosa wuyanta take tace.
"Zainabu! Tunda Mustapha ya sakeki sai kika raba zumunci da Ni? Haba! Zainabu."
Zainabu ta mike zata wajan Karima, Khairy da wani irin sauri ta miƙe ta kamo hannunta tana zaunar da ita.
Kallon tayi tana son jin dalili.
Khairy ta koma jikin Mamy tana lafewa tace.
"Umma karki je yi zamanki keda bakida lafiya..."
Karima idanu ta zubawa Khairy tana takowa gabanta na matsanancin faɗuwa jin ta kira Zainabu umma.
Inna ADAMA tace.
"Hajiya Karima kina nan ashe? Daga ina kike haka busu-busu kamar kinyi kwance a ƙasa?"
Zama tayi kusan Zainabu tana fashewa da kuka tace.
"Zainabu kin huta yanzu Ni Mustapha yake azabtarwa dukana ya yi awaje daga cewa kar ya taɓa Zainabu tunda ba muharamarsa bace saki uku a tsakanin..."
Nadiya cikin kuka tace.
"Wai Mom meke damunki hakane?"
Karima tace.
"Ubanki yake damuna."
Sai lokacin Zainabu ta ankare da Nadiya ta kalleta tana ɗaga mata hannu, Nadiya tazo aguje ta afka jikinta tana sakin kuka tare da cewa.
"I miss You Momy."

Usman da Mustapha ne suka shigo da sallama.
Amsawa sukayi suna kallonsa.
Dad Mustapha ya zauna yana haɗe hannayensa idanunsa sunyi jajir yace.
"Don Allah dan darajar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam, Abbu karka rabani da Zainabu wallahi tallahi ban saketa ba..."
Karima tayi caraf tace.
"Wallahi ka saketa saki uku gabana gaban kowa..."
"Toh kije ke na sakeki saki ɗaya saki biyu kina sake magana zan cike sakin ɗayan gaban kowa..."
Wani irin ihu Karima ta saki tana faɗin.
"Wlh ban sakuba..."
Da sauri ta koma ta zauna tana rufe bakinta tana kuka jin kashedin da ya mata zai ƙarasa sakinta.
Liman yace.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, La Haula wala Quwata illah billah.
Mustapha ya isa haka karka ƙarasa gudun, muyi abunda ya kawomu.
Ke Karima zo nan zamuyi magana idan kin faɗi gaskiya idan har kin cancanci Mustapha ya maidaki zan saka ya maidaki burinmu ki fadi gaskiya."
Jikinta na rawa tana kuka ta miƙe tazo nesa dasu ta zauna.
Liman yace.
"Zainabu! Taso zo nan ki zauna akwai tambayoyin da zan miki.
Ummulkhairi zo nan. Bilkisu kema zo nan." Zainabu ta miƙe anutse ta nufi wajansu, ta zauna kusan Abbu kanta a ƙasa.
Liman yace.
"Nadiya kema zo."

Mamy ta janye Khairy miƙe tana kama hannunta suka isa wajan, duk wajan ba wajan zama sai kusan Shattima ta zaunar da Khairy ita ta zauna kusan Khairy'n, kanta ƙasa.
Khairy ta goge hawayen fuskarta tana haɗiye yawu marar daɗi.
Hannunsa ya zura ta ƙasan hijabinta ya kamo tattausan tafin hannunta, ya ɗan murza, yana kallon mutane, ba wanda ya lura da su, can ƙasa ya ɗuƙo cikin kamular muryansa yace.
"Bana son kukan ya isa haka. Kina jin yunwa koh?"

Kallonsa tayi, taga sam hankalinsa baya wajanta.
Wani irin abu taji jikinta yanayi, ga taushin hannunsu da ya haɗe cikin nasa.
Ahankali tace.
"Banaji Dady."
Ta faɗa tana ɗora hannunta saman nashi tana sauke ajiyar zuciya, wanda ya saka Mamy saurin waigowa ta kalleta, tace.
"Baby ki nutsu komai zai kare yau Ok?"
Khairy ta gyaɗa kanta, tana maida hawayen idanunta.
Ta fara ƙoƙarin janye hannunta da ta ɗora saman na Shattima.
Gam taji ya riƙe, tai saurin kallon Mamy taga hankalinta wajan tambayoyin da Liman yake wa Karima.
Ji tayi da kansa ya zame hannunsa ya ɗan matsa baya kaɗan, jikinsu ya bar goguwa da juna.
Wata irin wawar ajiyar zuciya ta sauke amman a ɓoye, tana maida kallonta wajan Zainabu suka haɗa idanu tana kallonta.
Tsintar kanta tayi da sakar mata murmushi, itama ta maida mata.
Liman yace.
"Tsakaninki da ALLAH zaki fad'a Karimatu, kinada saka hannun a raba Zainabu da Mustapha...? Idan baki faɗi gaskiya ba zanyi addu'a dukkan wanda yake hannu ayanzu abinda duk ya faru dasu ya dawo kan wanda ya rabasu..."
Karima a rikice tace.
"Wlh zan faɗi komai da nasani..."🤣Kai jama'aaaa! Wai daman haka duniya take??🤔
Real Ladingo Omu Farisah


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*

*MTN* . *Airtel*
1GB = N300. 1GB = N300
2GB = N600. 2GB = N600
3GB = N900. 3GB = N900
4GB = N1200. 4GB = N1200
5GB = N1500. 5GB = N1500

*GLO* . *9MOBILE*
1.5GB = N500.
2.9GB = N1200. 1.5GB = N1100
4.1GB = N1600. 2.9GB = N1400
5.8GB = N2100. 3GB = N1650
7.7GB = N2700. 4GB = N2100

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
For more information call or whatsapp me
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

🪀08066268951


*YI WA KAI!*


*Free Novel*

_#MatarɗanAlhaji🫣_
_December 7/12/2022_



*Bismillahir Rahmanir Rahim*


*81&82*


"Maganar gaskiya tun randa na fara ganin Mustapha, sonsa ya yimin mummunan kamu, na kasa bacci komai nake shi nake gani, abu kamar wasa naji duk duniya banida mijin aure sai shi. Ji nake idan ban aure shi ba zan iya rasa raina.
Ahankali na fara ƙoƙarin cusa kaina gare shi, kasancewar Company'n abokinsa na samu aiki, kuma yana yawan zuwa wajansa.
Kusan wata shidda ina bin kansa, da duk wata hanya da nasan zanbi ta kwarkwasa da kissa da kisisina, da kyautata masa, amman ina abanza.
Ganin wankin hula zai kaini dare ranan wata Alhamis da yamma bayan la'asar yazo wajan Alhaji Mubarak, bayan ya gama abinda ya kawosa ya tafi dan shiga mota, nabisa na naimi alfarma akan zamuyi magana, uhmm! Bayan na zayyane masa ta cikina me zai biyo baya.
Kash! Akayi rashin Sa'a bana cikin irin sahun matan da yake ƙauna, sabida anan yacimin mutunci tass akan bazai taɓa sonaba, banida abubuwan macan da yakeso, idan nayi wasa zai saka alhj Mubarak ya koreni aiki daga kamfanin sa.
Abun yamun ciwo sosai yadda ya aibatani, koda baya sona yanada kyau yabini asannu sai mu rabu lafiya.
Hakan ya saka ina dawowa gida na faɗawa mahaifiyata ina kuka.
Ita kuma dama ta saba mana ƴan neme neme sai tace duniya ba'a zama hakanan...aranan ba'a kwanaba sai da muka kai sunansa gida Malam mai LANƘWASA Allah ya jiƙansa shine yayimana asirin da Mustapha ya kawo kasan gidanmu, ya nunamin ƙauna muraran amman naƙi nace shi yace ni ba kalarsa bace...
Da ƙyar ya shawo kaina harda kukansa kafin nan yarda na auresa da sharadin zanyi business kuma shine zai bani jari, ya amince.
Bayan wata uku aka sha biki muka tare agidanmu, muna zuba soyayya wadda maganin Malam mai LANƘWASA ne yake zaune dani agidan.
Munada shekara ɗaya da aure na haifi Usman, wanda yake kama da Mustapha sak.
Bazan mantaba Usman yanada shekara 8 cif Malam mai LANƘWASA ya rasu, kuma ban sake samun ciki ba, kawai abubuwa suka fara sauyawa, kwatsam ko wata biyu bai rufeba Mustapha yace min aure zaiyi ya samu yarinya ƴar shila ɗanya shatak akatsina, wallahi alokacin ji nayi gwara na mutu na huta, amman na dake ganin ya fara canzamin idan na tayar masa hankali zai iya sakina saboda idan zakayi aure ana lallashin mace, toh Ni wulaƙanci na haɗu da shi abinda yasa na nuna masa komai ba komai ba, shine zanyima amaryar zangon ƙasa ne, idan ta shigo, haka yasa na saki jikina nayimasa fatan alkhairi, tunani bai ban na sake zuwa wajan wani malamin ba.
Bayan auren Zainabu da Mustapha, da aka kawota sai naga yarinya ce ƙarama ko banza zan bata shekaru goma, kuma abin farin cikin ma kurmace bata magana, shi kenan sai na sakata ajikina kamar gaske, kafin nasan abun yi.
Amman ganin irin mahaukacin son da Mustapha yake mata ya tashi hankalina na kasa haƙura na shiga bin bokaye da ƴan tsubbu.
Abun takaicin duk maganin da nake akan ya saketa sai ma ƙara soyayya sukeyi sai da abin mamaki na samu Mustapha a hannuna sai dai ina masa maganar Zainabu sai naga yana naiman dawowa hayyacinsa,sai na fasa.
Watanta biyar tayi ɓarin ƴan biyu sabida maganin da na saka mata taci cikin abinci.
Sai dai ko wata uku bata rufe ba wani cikin ya ƙara bayyana sanadin laulayi na sake ɓara dashi.
Ana uku ne ba yanda banyi cikin ya zube ba yaƙi zubewa, Boka YANKAN WUƘA shine yacemin bazai zubeba na haƙura idan cikin yakai haihu na amshi haihuwar da hannuna dan na kashe abinda ta haifa da hannuna Zaidu.
Da wannan shawaran na haƙura.
Cikin Zainabu yanda wata 8 tafiya ta kama Mustapha zuwa London, yanada kwana biyu da tafiya akamana rasuwa can gidan kawuna da yake Jigawa, na tattara ta muka tafi, randa muka cika kwana shidda ranan acan naƙuda ta kama Zainabu, sosai nayi farin ciki da yake ɗakinmu mu biyu ne na kamata muka tafi asibiti, ta haihu lafiya ƴarta mace kyakkyawa kamar Mustapha baƙa ce, sai dai Zainabu batama san inda kanta yake ba.
Bayan a gayara baby kamar abun arziƙi na amsa na siyi wata tsohuwa muka gama baki da ita ta tsare min Zainabu nace kan dan ta farka kafin na dawo tace ta haihu lafiya amman ɗan da ta haifa ya koma.
Ni kuma sai da na sanɗi jama'a na fice da jaririyar, cikin ikon ALLAH batayi kuka ba, har na hau adaidaita sahu.
Can bayan gari na sauka na samu katin na siyi kwali na nufi bakin ruwa.
Zaune nayi saida na ƙarema yarinyar kallo tana lasar baki, tana harɓa ƙafafunta, na sanya hannu na shaƙe mata wuyinta saida naga bata numfashi na sanyata akwali na jefa ruwa..."

Daidai nan Zainabu
Tayi wani irin ihu tana cakumar wuyan Karima tana kuka ta shiga dukanta ta ko ina duka take kaimata harda cizo da yakushinta, tana gunguni ba bakin magana, sai kuka take.
Abbu da Inna ADAMA suka miƙe dan rabawa.
Mustapha yace.
"Mai wa kushewar iyayansa kar ya rabasu, ku bari ta rage zafi, wallahi Karimatu kin cutar damu, ɗiyata gudan jinina nida Zainabu kika kashe mana?
Allah ya tsinemiki Karima na ƙara sa miki saki ɗayan jeki ya zama saki uku ban yafe miki ba, nida ƴaƴana da Zainabu bazamu yafe miki ba tsinanniya macuciya azzaluma munafukar ALLAH, dan Allah kar wanda ya raba ku bari ta kasheta mu huta da irin annnoba."

Hajiya Karima ba Dukan da Zainabu take mata ya dameta ba,sai sakin da taji Mustapha yace yamata shine ya sakata take kururuwa tana faɗin.
"Wlh ban sakuba nida kai mutu ka raba, takalmin kaza..."

Khairy ta girgiza kanta ta fashe da kuka tana faɗin.
"Umma ki rabu da ita."
Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa, wani irin jiri ya ɗauke ta tayi luuu baya zata faɗa saman Mamy.
Shattima yay wani irin saurin sanya hannunsa ya kamota baki ɗayanta ya zaunar kusansa yana ɗago da fuskarta kaifafan idanunsa ya kafa mata yana share mata hawayen da tafin hannunsa, cikin nagartacciyar muryansa mai taushi anutse yace.
"Shiiit! Bana son jin wani kuka anan, bari wasan yazo ƙarshe ta ɗan mata duka kaɗan zata rage jin raɗaɗin zuciyarta, yi shiru, Zaki zauna nan na kwana biyu da ita ki lallasheta zataji sanyi Ok?"

Kukan ta haɗiye da wani kalar shagwaɓa ta gyaɗa kanta, tana kallonsa.
Anutse ya furta.
"Very good Baby karki sake kukan."
Ahankali ta damƙe hannunsa tana faɗin.
"Dady Usman da Nadiya suna kallo kalli kuka sukeyi dan ALLAH abarta dan ƴaƴanta nagari..."
Ta faɗa kamar zata shige jikinsa, sai tai saurin nutsuwa tana matsawa baya tana waigowa ta kama hannun Mamy tana faɗin.
"Mamynah abarta dan ƴaƴanta komai mutum yay kansa, kanta tayi wa ba kowaba, kunji Please iyayena ku yarda?"
Mamy tace.
"Baby munji hawayen ya isa haka toh bari naje naga ko zata haƙura..."
Mamy ta faɗa tana zame hannunta ta miƙe ta nufi wajan Zainabu wacce ta zauna kan rushe shan cikin Karima tana duka, Nadiya kuka take tana ba Zainab haƙuri.
Shattima ganin ba me kallonsu hankalin kowa wajan Zainabu tana jibgar Karima, ya sunkuyo da kansa dab da fuskarta, cikin tsadaddiyar muryansa mai fitar amon sauti me daɗi yace.
"Kinajin yunwa koh baby? Bana son ƙarya faɗamim gaskiya cikinki ba komai ko?"
Idanunta ta janye anasa sabida wasu irin maganaɗisu da suke fitowa idanunsa suna shiga a idaunta.
Ahankali ta buɗe baki tace.
"Dady inajin yunwa amman bazan iya cin wani abu ba wallahi..."
Yatsarsa taji akan lips ɗinta, yana wasa da lips ɗin yace.
"Shiiit! sai kinci oya Anjima ana gama komai ki sameni a mota idan baki zoba babu ruwana dake Ok?"

Kai ta jinjina tana sadda kanta ƙasa kallonsa kasala yake saukar mata.
Hannunsa ya zare anata
Can gefe ya matsa yace.
"Je kema kiyi rabon bada kashin, banda kuka."

Cikin murna ta miƙe tabi bayan Mamy.
Amma tana ganin Nadiya da Usman suka bata wani irin tausayi ta nufesu ta rungumesu tana sakin kuka mai ciwo tace.
"Kuyi haƙuri dan ALLAH kunji?"
Usman ya fara ƙoƙarin janyeta daga jikinsa, ganinsa bai daceba ba muharamarsa bace ba.
Amman Khairy taƙi ta riƙe su da Nadiya tana kuka.
Shattima ya miƙe yana furzar da ya iska me zafi ya nufi hanyar ficewa sabida kiransa da ake waya, anutse ya furta.
"Usman wannan muharamarkace ku lallashi juna, Nadiya rungumi ƴar uwaki."
Ya fad'a yana wucewa abinsa anutse ya zuba hannayensa cikin aljihunsa, baima ciro wayan ba, bare yaga me kiran.

Liman kam takaicin abubuwan da Karima tayi ya hanasa dakatar komai ya zura idanu kawai yana kallon yadda Abbu da Inna ADAMA da Mamy suka kasa ƙwatar Karima hannun Zainabu ashe dagaske kurame basuda daɗi wajan faɗa?
Kallon Usman da Khairy da Nadiya ya yi, sai suka basa tausayi.
Yay gyaran murya yace.
"Zainabu! Ki nutsu ga ƴarki halak malak bata mutu ba bari dukan haka ya isa, ayanzu tasan ALLAH ɗaya ne, barta ko zamuji sauran bayanin."
Cak Zainabu ta tsaya da abinda take tana sakin Karima ta kalli Liman dan neman ƙarin bayani.
Liman yace.
"Eh zo ki zauna ki nutsu Karima ta ƙarasa mana bayani sai na faɗa miki inda ƴarki take mu muka tsinceta. Karima ki daure ki ƙara sa mana bayani, kiyi haƙuri ki ƙarasa mana sai a sulhunta."

Karima ta rarrafo wajan liman tana wani irin kuka, cikin fitar hayyaci sabida ta daku ga ƙaiƙayin da gabanta yake da wuyanta, bayanta kanta, ko ina ƙaiƙayi yake mata, cikin sauran hayyacinta kafin ya gama fita tace.

"Dan Allah kacema Mustapha karya sakeni ina sonsa dalilin sonsa nayi komai, tun farko da bai wulaƙantani ba, da haka bata faru ba.
Ina dawowa asibiti bayan na jefa gawar jaririyar aruwa, bata farka ba na tashe ta muka gudo dan kar likitoci su ankare ba ɗiyar, sai acikin adaidaita nida tsohuwar da na siya muke bata labarin ta haifi ɗa ya rasu, an binne shi nan asibiti.
Taci kuka sosai har ta haƙura bayan haihuwar da kwana uku muka dawo Gumel, sai lokacin na kira Mustapha na faɗa masa, shi kansa yasha kuka yace na bata wayan suyi magana, ta amsa tana kuka ya lallasheta har ta sosai jikinta, taci gaba da sabgoginta.
Bayan shekara guda da haihuwar Zainabu na haifi Nadiya, Nadiya tanada wata shidda Zainabu ta sake ɓari, wanda daga shi na saka YANKAN WUƘA ya hanata samun ciki, shekaru masu yawa suka shuɗe har yara suka girma, suna karatunsu.
Ganin irin son da yake mata bata haihuwan ma na saka Boko YANKAN WUƘA ya turo masa aljani ya shiga jikinsa, aljanin da kansa ya saketa saki uku akan zaman Mustapha, aka sauya masa tunani ya mantata baki ɗaya tun randa tabar gidan, ya zamana sai Ni da ƴaƴana muke sha'aninmu hankali kwance bana bukatar wani ya raɓar min mijina koda ƴan uwansa ne..."
Liman yace.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Zainabu toh kunga ƴarki nan ummulkhairi, da ranta yarana suka tsinceta, kuma da suka tsinceta babu alamar wani tabo ajikinta ko anso kasheta..."
Tsaf ya basu dukkan labarin abinda ya faru tun tsintar Khairy har zuwa aurenta na farko da mutuwar Abdoul da aurenta da Shattima har zuwa lokacin da Shattima ya gano Usman ɗan uwan Khairy ne...
Ya ƙara sa basu labarin yana faɗin.
"Khairy! taso ta ganki."
Baki ɗayan wajan ba wanda baya kuka abun ya rikitasu matuƙa.

Zainabu ta waro idanunta tana kallo Mamy da Shattima, wanda batada kamarsu a duniya, hannayenta ta ɗaga tana musu godiya tana kuka.
Inna ADAMA tace.
"Wlh banga irinku a duniya ba, wannan bayin ALLAH.
Mamy ta share hawayenta tace ma Khairy.
"Baby je ki rungume ƴan uwanki."

Khairy ta rungume Mamy cikin kuka tace.
"Wallahi Sweet Mamy kece komai nawa bazan taɓa ƙamarki ba aduniya."
Wani irin kuka suke sun maƙale junansu kamar ance za'a rabasu.

Shattima ya furzar da iska mai zafi ya iso wajansu ya kamo Mamy anutse ya mannata ƙirjinsa yana buga bayanta yana kallon Khairy anutse ya furta.
"Babu jeki abada kina tare da Mamynki."

Kai ta jinjina ta nufi Zainabu, ta rungumeta.
Wata irin runguma Zainabu tama Khairy, tana sunsunata tare da tattaɓa fuskarta.
Abbu da inna ADAMA kansu kuka suke suka haɗu suka rungume Khairy.
Usman da Nadiya suma suka zube gaban Khairy suna kuka.
Shattima kuwa ya nufi zaure da Mamy dan lallashinta.
Tsakiyar ƙirjinsa ya sakata ya zagaye hannayensa bayanta, ya duƙo da kansa yana manna bakinsa kunnenta, anutse yace.
"Ya isa haka Sweetheart kar kanki yayi ciwo, kina jin yunwa koh?"
Kai ta girgiza tana lafewa cikin jikinsa sosai tana sauke ajiyar zuciya.
Wani irin fitinannan tausayinta yakeji yana bukatar ya bata farin ciki ayanzu mai wuyar mantawa, hakan ya saka ya kama hannunta suka fice ya nufi mota.
Maleek na ganinsa ya nufi motar ya buɗe musu baya.
Guard ɗinsa na Shirin shiga front seat yana gyara bindigarsa.

Shattima yay gyaran murya yace.

"No! Maleek Ban key, zan ɗan fita ni ɗaya, anjima za'a kaiku hotel ku huta zuwa gobe."
Ya faɗa yana amsar key ɗin.

Mamy ya saka ta zauna front seat, ya rufe ya zagaya
Ya shiga mazaunin direba, yama motar key ya jaya yabar wajan, su biyu kawai suka tafi abinsu, yana driving da hannu ɗaya hannun ɗaya cikin na Mamy yana murzawa, anutse yace.
My sweetheart please kukan ya isa haka bari muje ki nutsu ki kwanta ki huta."
Da sauri ta kalle shi, ya kashe mata ido ɗaya yana maida hanakalinsa akan driving.
Idanunta ta lumshe tana ɗora kanta ƙirjinsa tayi shiru, abunta kamar yadda ya maida hankalinsa wajan tuƙi sabida gudun samun matsala.

Mustapha idanu kawai ya zubama Khairy da mahaifiyarta dasu Usman.
Ya

Please Login or Register in order to submit comment