Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in.
“Ya Allah!”
Shine abinda ta furta tana saka wayan A silent.

Baffa ya koma ya zauna yana fad'in.
“Allah ya miki albarka Maryama Ngd sosai, alfarmar da nake nema ita ce yanzu zamuji yadda akayi Ummulkhairi ta zama ba 'yar Shattima ba, har ta halatta ya aureta, koma yaya akayi nasan wacece Bilkisu bazata tab'a abinda ba sanin Abdallah aciki ba, dan haka inaso kiji komai ta fad'a agabanki sabida ki cire zargi kuma rufamana asiri ki binne maganar anan inda kika jita, duk wanda ya rufawa wani asiri shima ubangiji zai rufa masa duniya da lahira, wannan ita Ce alfarmar da nake nema wajanki.”
Baffa Liman ya fad'a yana kallon Mamy tare da cewa.
“Bilkisu! Kibar kukan muna jinki ki gayama me ya faru shekarun baya, har Ummulkhairi ta zama ba jinimu ba? Toh ya akayi take jininmu? Sosai take kamata.”
Inno ta share hawayen fuskarta tana fad'in.
Liman! Wlh bazanyi kaffara ba duk abinda ya farun nan yanada nasaba da lokacin da wannan yarinya marar jin maganar mu ta uzurama Bilkisu akan bata haihuwa, har sukayi rikici da Shattima, dudu aure shekara biyu bai gama rufewa ba, amman sun takurata hakan kuma ai nice ya kamata ace nayi amman banyi sabida nasan Allah ne mai bayarwa.”

Mamy ta b'arke da kuka tana fad'in.
“Tabbas Inno haka abun yake, wlh duk auntie Aisha Ce ta janyomana har mukayi abinda ga shi yanzu dole duniya sai ta Sani, daman komai nisan dare dole gari zai waye...”

Shin meye asalin labarinsu??

Abdallah (Shattima) Umar fulanine na asali, mahaifinsu Umar malami ne babba mai tsoron Allah.
Su shidda ne wajan mahaifinsu, shine d'a na 3 wajan liman Umar, kuma shi d'ayane wajan mahaifiyarsa randa ta haifesa ranan ta rasu ta barma Inno amanarsa.

Liman Umar Fulanin GARIN MALAM ne, nan ne asalinsu Amman tin zamnin kakansu suke garin jigawa.
Liman tsayayyan namijine agidansa, yanada rufin asiri tin can asali sunada dukiyar dabobi da suka gada wajan iyayansa, su biyune wajan iyayansu shi da Rabi'atu, matansa na aure biyu, Inno ita Ce uwar gida 'yayanta biyar sai Bahijja, wacce ta kasance mahaifiyar Shattima, bayan aurensu da shekara biyar ta samu cikin Shattima, Tasha wuya kafin cikin ya girma, har yakai ga haihuwa, randa yazo duniya kuwa tace ga garinku nan cikin ciwon mutuwa ta dinga saka masa albarka da yafe masa akan naqudarsa da ta bata wahala, ta barma inno amanarsa ta kuwa riqe.
Dan Shattima bai san wata uwaba bayan inno yadda ta raini 'yayanta haka ta renaisa, ta tarbiyantar da shi.
Munnir shine Babban su sai Aisha shi yake bima Aisha, shi kuma Nuraddin yake bimasa, sai Balaraba da autarsu Bahijja wacce taci sunan mahaifiyar Shattiman, dukkansu sunada aure da yara.
Sun samu ilimi na addini da boko sosai, Shattima tin yana yaro mutum ne mai barkwanci da wasa da dariya, haka baida qin jama'a, kyakkyawane sosai baqin bafulatani, talaulayi bayada jiki Amman akwai kyawun jiki, ga farin jinin al'umma,haka yanada wani irin kwarjini, Allah ya had'ashi da 'yan uban nagari masu k'aunarsa kamar yadda Liman yafi sonsa sai dai bazaka tab'a ganewa ba.
Duka karatunsa har jama'i anan Nigeria yayi sabida shi mutum ne wanda bayada girman Kai ko kad'an duk da kuwa mahaifinsa nada hanyar fitar da shi. Tin yana secondary school Allah ya had'asu aminci da Aminu and Hashim duk da sun girmemasa amma jininsu ya had'u suka zama amini kirki, Aminu d'an kazaure ne, yayin da Hashim d'an Ringim ne.
Koda Shattima ya fara aikinsa bai Fara da qaramin aiki ba da babban muqami ya fara, sabida qwazonsa alokacin ne ya fara fita qasasashen waje tsawon shekaru 4 yayi a Australia, kafin ya dawo yana dawowane Allah ya had'ashi da Bilkisu Bilal wato (Mamy).
Lokacin bata ko gama secondary school ba, Allah ya d'ora masa masifar sonta, itama lokacin ta kamu da matsanaiciyar k'auanrsa.
Bilkisu Bilal su hud'une wajan iyayansu Adamu shine babba Bilkisu na binsa sai Abdurrahman, and Fauziyya, itace qarama kowanensu ayanzu yanada aurensa da yaransa Fauziyya ce d'a d'aya, da Mamy sbd basunsa Khairy ba yarta bace .
Masha Allah sunada kyau zuri'arsu mahaifiyarsu Ce bafulatana, mahaifinsu bahaushene,fararene tass masha Allah, sunada rufin asirinsu daidai gwargwado.
Soyayya mai tsafta Shattima da Mamy sukayi, har ta idar da secondary school akayi maganar aurensu, akan bayan biki zataci gaba da jami'a agidanta.
Auren Mamy da Shattima aurene na soyayya da qaunar juna sukayi, suna bala'in son junansu kamar zaci juna kowa yana gudun b'acin ran d'an uwansa.
Wata biyu sukayi suna gurzar amarci kafin ta masa mgnar komawa makaranta, bai musaba sabida yana son mace mai ilimi bare ita da zatayi karatu akan likitanci ta taimaki al'ummah.
Tin bata rufe shekara ba Auntie Aisha ta saka mata idanu akan wai ya shiru ba labarin ciki, Bilkisu bata damuba karatunta take anutse tinda mijinta yana sonta.
Lokacin da ta shiga zango na biyune akaratunta Aisha ta tisata gaba da maganganu har wasu daga cikin dangi na kama mata, har Aisha ta matsawa Shattima sai ya qara aure suka hau sama suka hau k'asa yace bazai qaraba ita ba uwarsa inno bace, haka haihuwa ta Allah ce, ba auren bane zai basu haihuwar.
Shattima ganin Mamy ta tashi hankalinta tana neman haihuwa idanu rufe, sunata zuwa gwaji asibiti ana fad'a musu lafiyarsu lau lokacine baiyi ba.
Shattima da kansa yaba Mamy shawara ta fara laulayin qarya alamar ciki gareta, da yaje wata uku sai suce ya zube haka haka har Allah yasa su sami cikin gasken, dan baya son ya mata kishiya haka baya son a tsaneta adanginsa.
Ai kuwa haka sukayi ta fara laulayin k'arya har tsawon wata uku kafin ace tayi b'ari, aikuwa Auntie Aisha ta sarara mata sai murna harda tattalinta take, ita dai burinta taga d'an Shattima, Allah yajarabeta da son k'anin nata.
Sunyi hakan har sau uku ana hud'un ne Shattima yace su jinkirta karta ce ya zube su dinga rainon cikin qarya gwara suje gidan marayu su samo jariri kafin su samu nasu d'an, koda daga baya asiri ya tonu idan sunyi nasun shi kenan.
Ai kuwa haka sukayi, suka dinga rainon cikin k'arya har ya shiga wata bakwai, lokacin sukaje gidan marayu suka bada cigiya idan an samu jariri sabon haihuwa amusu magana, yabar lambar wayansa da za'a kirasa.

Ranan wata weekend Bilkisu ta matsa sai sunje yawon shaqatawa bakin ruwa, babynta nason ganin ruwa, ya kuwa biye mata suka tafi.
Suna yawon shaqatawarsu, suka yada zango can bakin gari wajan k'orama me gudana kawai suka shimfid'a dardumarsu suka zauna suna hira cike da nishad'i Shattima yana shafa cikin k'arya yana dariya, yace.
“Sweetheart me ciki.”
Dariya tayi tace.
“Ni fa kamar ma yaune zan haifi yaranmu dan twins zan haifo mi Amor.”
Shattima zaiyi mgna sai ya hango abu saman ruwa kamar kwali.
“Sweetheart d'agani naje naga meye akwalincan.”
Bilkisu ta riqeshi gam tace.
“Wlh bazan barka ba haka kawai aje mutanan ruwa su janye min Kai.”
Please ba komai insha Allah bari na duba.”
Ya fad'a yana janyeta daga jikinsa ya Kama hanunta yace.
“Muje ki tsaya na d'auko kwalin nagani, kinsan fa wlh ana saka yara kwali ayar.”
Mamy tace.
“Yayan shegu koh?”
Shattima bai mata mgna ba yajata suka isa bakin kogin.
Wandonsa ya tattare yay bismillah ya shiga ruwan ya d'auki kwalin, ya fito.
Zama yayi aqasa ya bud'e kwalin.
Zabura mamy tayi gani jaririya baqa kyakkyawa qatuwa da ita cibinta na fitar da jini ba kaya ajikinta yatsunta biyu a bakinta tana tsotsa tana harba qafafunta, kana ganinta kasan haihuwar yauce.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mi amor! Mun shiga uku! jaririya Anya mutum Ce?”
Shattima ba tare da tsoron wani abu ba ko d'arrr yay bismillah ya cirota daga kwalin yana kallonta ya kai bakinsa saitin kunnenta, yay mata kiran sallah tare da Kalmar shahada yayi mata addu'a, ya d'ago ya zare hannunta da take tsotsa ta fashe da wani irin kuka, yay saurin tura mata lips d'insa na k'asa.
Ai kuwa ta fara tsotsa tana harba qafa, ta damqe yatsarsa ta tsakiya cikin hannunta.
Mamy tace.
“Wai mi amor kasan me kake? Daga ganin jaririya abakin ruwa baka tantance mutum ko aljana ba sai ka d'auketa ka rungume kana bata leb'anka tana tsotsa, idan kuma ba mutum bace ba fa!”
Tayi maganar cikin qufula ta haye saman cinyarsa, tana shirin janye yarinyar ya girgiza mata Kai ya zare lips d'insa ya saka mata yatsarsa qarama abakinta taci gaba da tsotsa, shi kuma ya shiga tofa mata addu'a tsawon 10 minutes, kafin ya d'agota yana fad'in.
“Masha Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan kyakkyawar babyn tawa Ummulkhairi Abdallah Umar Shattima.”
Mamy ta kalleshi cikin mamaki tana miqewa kamar mahaukaciya tana masa kallon tuhuma.
Azafafe tace.
“Mi Amor! Me kake nufi? Daman d'iyarka ce? Kana nufin wata kayiwa ciki a waje ka kawo nan kaje ka kawoni dan...”
Tattausan hannunsa yasa ya rufe mata baki, yace.
“Haba! Kar b'acin rai ya saka kiyi maganar da zata dameke daga baya, har kin manta waye Shattima sabida kishi koh? Idan har inason kusantar wata matar bayan ke inada rufin asirin da ajiye mata sama da biyu ko uku toh meyasa zanyi zina?”
Shiru Mamy tayi tana kallonsa, sai taji jikinta yayi sanyi,ta rungumeshi ta fashe da kuka tana basa haquri.
Shattima ya buga bayanta cikin kwantar da murya yace.
“Allah ne ya bamu wannan yarinya kuma mun amsa yanzu abinda za'ayi muje gida acikin kayan haihuwar da auntie Aisha ta siyo kima Khairy wanka agasa cibiyarta asaka mata kayan sanyi sai muje hospital adubata sai an tabbatarmana tana lfy sai na saka abaki gado kamar bakyajin dad'i nayi Kira gidanku da namu nace kin haihu sai na nemo muki maganin Saka ruwan nono, shi kenan Allah yaji qanmu ya bamu haihuwa OK?”
Mamy cikin murna ta rungume Shattima da Baby wacce har yanzu yatsar Shattima take tsotsa.
“Ngd ngd ngd Mi Amor haqiqa Kai masoyina ne na gaskiya duk dan kar asakaka kayi aure kamin kishiya ka taimakeni hakan I love you so much na maka alqaealin Zan kasance mace mai biyayya da haqurin zama dakai duk runtsi Allah ya bani ikon faranta maka.”
Shattima ya amsa da.
“Ameen sweetheart ya kuma raya mana Khairy ya kawo twins k'annen Khairy koh?”
Dariya suka sanya yana rungume da Khairy suka nufi mota, suna waige-waige cikin ikon Allah babu wani d'an Adam da ya gansu.
Aikuwa suna zuwa gida sukama baby wanka aka gasa mata cibiyarta aka sanya mata kayan sanyi tayi wani irin kyau,Mamy ta bata nono taqi kamawa sai kuka dole suka nufi asibiti yatsar Shattima abakinta tana famar tsotsa.
Suna zuwa asibitin Dr Sambo aka duba baby batada wata matsala Mamy tayi qaryar ciwon ciki taqi yarda aduba ta can bare su gane ba ita ta haife ta ba, tace batada matsala sai ciwon ciki.
Shattima yana kiran 'yan gidansu da 'yan gidansu Mamy kafin kace me asibitin ya cika.
Auntie Aisha murna har kunne.
Zuwa dare aka sallamesu can gidan ma ya cika da jama'a Amman har lokacin babyn bata shan nonon Mamy kuma ruwan nono yazo.
Dole Shattima ya siyo Madara Ana kad'a mata ai kuwa ta fara Sha kamar ba gobe.
Gudun kar jama'a su ankare Shattima yayi takardar qarya akan nonon Mamy bashida kyau ne baby zatasha Madara tsawon wata uku kafin maganin da akaba Mamy ta gama shanyewa ta warke.
Ahaka aka zauna har akayi suna, suna na 'yar gata Shattima yayi bajinta sosai. Haka suka dinga kula da babynsu cikin so da k'auna cikin wata shidda ta zama wata qatuwar baby mai shiga zuciya. Khairy yarinya ce mai wayo da fara'a sai dai ta fiye sanyin hali, shekarunta 9 a haife amman har yanzu Shattima da Mamy goyonta suke, mugun son yarinyar suka dan tin satin da suka sameta qofofin arziqi suka qara bud'ema Shattima, har Mamyn da yanzu take cikakkiyar doctor, tanada babbar asibitinta wadda Shatyima ya bud'e mata, mai sunan.
*(Khairy clinic and maternity)*.

*YI WA KAI*

Free Novel

*33&34*

Khairy ranan da ta cika shekara 12 ranan Shattima ya zama minister d'in ilimi, ranan karkaso kaga murna wajan Khairy.
Ta gayyato k'awayenta na makaranta, suka had'a party, haka Mamy ma, Amman bakin su uku mijinta da 'yarta ta nuna farin cikinta.
Ba yadda ba'ayi ba Shattima ya koma Abuja da iyalinsa yaqi, yana zuwa yana zauwa, haka yakeyi.
Yau ta kama weekend Shattima and Mamy suna gida haka Khairy ma.

Goye ya fito da Khairy daga bedroom d'inta, tana sanye da kayan bacci pinky colour riga da wando, masu kauri kanta sanye da hula itama pink jelar gashinta wadda aka raba gida hud'u, aka d'aure da ribbons, ta ziro daga cikin hular sai reto takeyi.
Dariya take kyalkylawa ta saqala hannayenta wuyansa, tana fad'in.
“Please sweet Dady ka kaini garden ni ba zanyi breakfast ba.”
Mintsininta yayi aqafa yana fad'in.
“Baki isaba sweet daughter, dole kici abinci kafin ma kiyi wanka, haka kawai ulcer ta Kama min babytah.”
Dariya tayi ta ziro kanta ta sumbaci gefen kumatunsa, tace.
“I love you sweet Dady Monday Zan bika Abuja bazanje school ba...”
Mamy da take falon zaune tana sanye da farin glass manne a fuskarta, laptop akan cinyarta tana dannawa ta kallesu ta girgiza kanta tace.
“Baby Allah shirye ki fisabilillahi kin fara zama 'yan mata Amman sai Dady yayi goyo, ya kaiki ya baki breakfast shekara 12 amman abin 'yan 6 kikeyi, dubi lokaci 11 am, amman bakiyi breakfast ba! Fitowa da wasu jibgin kayan baccinki koh?”
Khairy ta turo baki gaba tana ma Shattima rad'a akunnensa.
“Sweet Dady please karka tanka Mamynah kawai neman magana take, dan ka fasa goyona bayan ita tana goyona idan baka nan.”
Shattima ya kyalkyale da dariya yana zarcewa kan dining area da ita abayansa, yana fad'in.
“Sweetheart adaina sakawa uba da 'yarsa idanu ehen.”
Mamy tace“Ku kuka sani sai ta ramar dakai, daman ba wata tsokace da Kai ba.”
Ta fad'a tana dariya.
Shattima yace.
“Oho dai naga Zan iyane.”
Khairy ta kyalkyale da dariya tana zama kan dining.
Shattima da kansa ya had'a mata tea mai kauri ya bata tana Sha da hnnunsa, ya zuba mata fankasun alkama da miyar kayan cikin rago, ai kuwa taci sosai tana zuba santi.
Tana gamawa tace.
“Sweet Dady! Bara naje na sake wanka yau gidan Abba Aminu zan wuni gibe kuma gidan Father Hashim.”
Kiss ya mata kumatu yace.
“Oya je kiyi wanka ni da kaina zan kai Baby gidan iyayanta.”
Rungume shi tayi tana murna kafin ta sake shi ta tafi dan shirin tafiya.
Khairy k'awarta d'aya Suhailat tin primary.
Tsakanin Aminu da Shattima da Hashim akwai aminci mai qarfi haka 'ya'yansu ma suka taso, Aminu yanada 'yaya 6 Hisham nada 'yaya 4 sai Dady me 'ya 1 Khairy, idan kaga amincinsu dole su burgeka kowa na kula da d'an wancan idan yazo gidansa, abin gwanin ban sha'awa, Abdoul jininsu ya had'u da Khairy tin tana qarama, sun shaqu sosai amman bada soyayya ba, ta d'aukesa yayanta ya d'auketa k'anwarsa.
Salim shine d'a na farko wajan Hashim, ya samu gata da kulawa wacce ta sanya shi ya zama sangartacce shagwab'abb'e.
Amman da ya fara girma sai ya fara nutsuwa, ya rage wasu abubuwan abayyane sai a b'oye, Salim mugun d'an wiwi ne da k'waya, Amman ab'oye.
Salim kuwa yana bala'in son Khairy tin tana zanin goyo, hakan yasa ya b'oye mummunan halayansa sabida bala'in son da Shattima yake mata yasan idan yasan ko shi waye idanta girma ta isa aure bazai tab'a bashi ba.
Haka ya saka Salim ya qara kusanci da Khairy yana janta jiki yana kyautata mata, hakan ya saka ta shaqu da shi matuqa, kominta yaya Salim ko yaya Abdoul.
Lokacin da Khairy ta shiga secondary school, alokacin Salim ya kashe wani saurayi bayarabe shima yaje karatu A Canada, wanda aranan hauka ya tabbata wanda akaba mahaifinsa tabbacin shaye-shaye ne ya saka shi hakan.
Hashim ya shiga tashin hankali sbd bai tab'a sanin Salim yanada mummunar d'abi ba, ta shaye²,harda kashe mutum.
Kafin ya samu case d'in ya mutu yaci azabar wuya dan kusan rabin dukiyarsa ta tafi, akama Salim cikakkun takardun hauka, aka d'orashi akan magani, Hashim ya shiga malamai birni da qauye ya raba kud'ad'e ana masa roqon Allah, akan shaye-shaye ya fita aransa.
Cikin ikon Allah kuwa addu'a ta amsu Salim ya daina shan komai idan yaji warin wiwi har amai yake, sigari Ce kawai bai daina sha ba haka haukansa bai kuma tashi ba, sai abinda ba'a rasaba dan daman wiwi da k'wayoyin da yake shane suka juye masa k'wak'waluwa...
Bayan shekara 4 lokacin Salim ya gama kame zuciyar Ummulkhairi da zazzafar soyayyarsa, wata irin k'auna sukema junansu, har iyayansa suka shiga lamarin Hashim na nemawa Salim auren Khairy Shattima ya basa dan yasan 'yarsa tayi dace, sbd yadda yake nuna shi na Allah ne azahirance.
A lokacin da aka sanya ranan aurensu wata 6 lokacin aka fara ma Shattima tamfatsetsan gininsa tamkar aqasar larabawa, gidan da ya had'a komai na jin dad'in rayuwa, cikin wata biyar an gama komai an zuba komai agidan sun tare.
Sunaci gaba da soyayyarsu har biki yazo Salim yama Khairy akwatina na kece raina, haka mahaifinta ya zuba mata uwar dukiya an mata kaya na 'yar gata, wanda tin saura kwana biyar d'aurin aure akaje aka shiryama Khairy d'akinta.
A lokacin ne tsautsayi yafi kala biyar da ya afku akan Salim, ida an gama da tin na farkon, wanda wajan bin malaman Hashim aka sanar dashi Salim ya rabu da Khairyn, shine sabida son kai ya hau Kai ya zauna akan Khairyn Ce ta saka Salim yake yawan asara, bai duba aminci ba yabi son zuciya da canfin, shine dalilin da yasa suka fasa auren, suka aura masa Aliyah, wacce agsky bata dace da shi ba, sbd tarbiyarta, amma ba yadda bawa ya iya da k'addarasa.
Wannan dalilin ne ya saka Aminu yayi jihadi yabada d'ansa aka d'aura da Abdoul wanda shi kuma yake soyayya da Azizah Ya'u, kusan shekarunsu uku atare sun ajiye mgnar aure, amman mgnar gsky Azizah batada tarbiya kusan duk 'yan gidansu ma hakane sbd basuyi dacan uwa tagari ba, sabida muguwar 'yar tashi tsaya ce, shiyasa yaranta baki d'aya sai gyaran Allah, amman cikin ikon Allah, Allah ya dubi mahaifinsu ba mai aikata zina sai dai yawon biki ko club da sauran abinda ba'a rasaba, irin mallake mazan aurensu.
B'angaran Maryam tin bata kai haka ba take masifar son Shattima, amma tasan ba halin ta fad'amasa, ko nunawa shiyasa koda yaushe tana hanyar gidan Mamy, Maryam kyakkyawace tanada hankali da nutsu shekarunta na haihuwa 18.
*Dawowan labari.*

Mamy tana duqe gaban Liman tana kuka bayan ta fad'a musu yadda suka samu Khairy.
Baffa liman da inno atare suka fad'i.
“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!”
Liman ya gyara zamansa yana gyaran murya yace.
“Aisha! Aisha!! Aisha!!! Wlh bata kyauta mana ba,ita ce ummal aba'isan komai da ya faru, sai laifi na biyu ke mahaifiyarta kinppp0san da maganar sun ta kurama Bilkisu tin farko,me yasa baki fad'amin ba? Ita ce ta haifa min Abdallah nan da zata matsawa matarsa bata haihuwa ya qara aure kawai dan yana mata biyayya? Ina ce itama 'ya'ya mata gareta duk suna gidajansu, idan haka ta faru dasu ya zatayi?
Bilkisu! Haqiqa kin cika mace tagari kuma 'yar halak, kunyi jihadin taimakon Kahiry da kuka yi, sai dai kuma kunyi wauta, duk da Allah ya taimake ku ya dubi kyawun niyarku sannan shi kad'ai yasan dalilin da ya hanaku haihuwar, kuma shi kad'ai yasan manufarsa akan tirsasaki ki bayyana cewa Khairy ba 'yarku bace, kinason Shattiman ya aureta.
Amman kuma abun dubawar anan shine Bilkisu! Duk fa duniya da zuri'armu suna kallon Khairy matsayin d'iyar Abadallah, ya zamuzo rana d'aya muce ta zama matarsa? Sannan ya Khairy zata amshi abun ya zata iya rayuwa da wanda take kallon ubantane amtsayin mijinta? Anya zuciyarta zata d'auki hakan? Wanda ka sani fa matsayin iyayanka rana d'aya ace baka had'a komai dasu ba, ba iyayanka bane dole zaka shiga tashin hankali. Bilkisu! Don Allah kibar mgnar nan iya mu, Maryam don Allah dan Annabi ki riqe mna amana karki fitar da zancan nan ki taimakemu ki binne mgnar nan ki tausayama Khairy.”
Ya k'arashe mgnar yana sauke numfashi tare da sadda kansa qasa, yanajin matsanaiciyar damuwa.
Maryam tace“Insha Allahu nayi alqawali Baffa nima ku yafemin lab'en da nayi haqiqa nayi kuskure babba.”

Liman yace“An yafe miki mungode.”

Inno tsakaninta da Allah take kuka tana fad'in.
“Wallahi Malam bansan komai akai ba ta ya Zan bar 'ya'yana su takurawa Bilkisu? Ai haihuwa Allah ne yake bayarwa ba mutum ba, idan kunji tawa shawaran don Allah arufe mgnar nan iya mu Sam wannan abinda Bilkisu take buqata ba mai yuwa bane ba.”
Mamy ta riqe qafafun inno tana wani irin kuka tace.
“Don Allah inno kuyi haquri ku tirsasa Shattima ya auri Khairy, wlh ji nake idan basu auri juna ayanzu ba,nan gaba kad'an Zan Iya mutuwa kuma su kasance ataren sabida irin mafarkan da nakeyi akansu, wlh ni gani nake duk duniya ba wanda zai kula da Khairy amatsayinsa na mijinta kamar Shattimaa shi zai zame mata miji uba ni kuma uwarta kishiyarta abokiyar shawaranta, wlh iya gaskiyata nake fad'a muku, Baffa don Allah Ku taimaka had'a babban taro families d'inku da namu zanyi bayani gaban kowa kamar yadda na muku ni dai burina Ku saka Shattima ya yarda.”
Ta k'are maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
Liman abun ya girmi tunaninsa kallonta kawai yake.
Maryam takaicin Mamy ya isheta kamar ta fallasa komai uban kowa yasani takeji.
Liman yay gyaran murya yace.
“Ok naji kukan ya isa haka kiban kwana uku zanyi istihara naga abinda ya bada zan nemeki keda mijin naki, yanzu dai ki rufe mgnar ki kwantar da hankalinki kinji?”
Kai Mamy ta d'aga hankalinta ya kwanta kad'an.
Sai bayan Maghreb suka bar gidan liman, zuciyar Maryam babu dad'i Sam ta dake ne tabi Mamy gidansu can basu jima ba,suka nufi gidanta.

Mamy sosai tayi qoqarin b'oye damuwarta ganin Maryam ta nuna ba komai har ta biyota gidanta dan zatonta suna fita zata tafi gidansu, sai taga akasin hakan.

Washegari kuwa ta kama weekend, suka shirya Mamy da Maryam direba ya d'aukesu sai Abuja wajan Khairy.

*5 pm.*
Khairy zaune falon Auntie Aisha tana karatun Qur'ani, Ilham kusanta, tana game. Suhal yana aikinsa a system, yayin da Auntie Aisha na falon baqi suna ganawa da 'yan business d'inta.
Qaraman Wayar Auntie Aishan ta d'auki ringing.
Ilham ta d'auki wayan tana fad'in.
“Auntie Khairy! Lambar waje Ce ba suna, amshi ki d'aga kinji, ni Mummy ta Hana ni d'aukar mata kiran lambar da ba suna.”
Daidai Khairy takai k'arshenta suratul Rahman, ta rufe Qur'anin, tana miqewa tsaye tana kallon Ilham ta harareta tana fad'in.
“Aha ke an hanaki ni kuma na d'aga koh? Toh barmata wayanta har ta sallami baqinta ba ruwana ni dai.”
Ta fad'a tana amsar wayan, tana gyara hab'ar hijabinta, daidai lokacin kiran ya katse, zata ajiye wayan ta wuce kiran ya qara shigowa.
Khairy tana kallon lambar tace.
“Sweet Dady yana Tunisia maybe shine.”
Ta fad'a tana picking call d'in, takai wayan kunnenta, tare da sallama.
Daga can Tunis Shattima wanda yake zaune a falon d'akin da ya sauka a wata babbar hotel.
Sanye da fararen kaya na sanyi masu bala'in taushi ya rufe kansa da hular rigar,dogayen baqaqen qafafunsa masu gargasa ya meqesu akan glass table d'in da yake gabansa.
Akame ya amsa sallamar yana fad'in.
“Baby! Kece? Ina Auntie?”
Khairy ta saki siririn ihu cike da shagwab'a take fad'in.
“Wayyo sweet Dady! I miss you kana Tunisia abunka, shine kaqi kazo ka gannin ko? Dady ina wuni?”
Shattima ya shafi sajansa yana murmushi marar sauti har dimples d'insa suna lob'awa, cikin sigar lallashi yace.
“Lfy lau sweet daughter ya hqr zanzo da zaran na dawo qasar OK? Hope kina lfy?”
Khairy ta turo baki tana gyaran runguman Qur'anin k'irjinta, tace.
“Yawwa sweet Dady wlh jiya nayi mafarkin ka Kai da sweet Mamy, kuna sanye da shaddah fara qal getzner, sai wani irin qamshi kuke, ni kuma ina wani jeji me yawan ciyayi tsanwaye shar, sai famar gudu nake wasu irin halittu masu bala'in muni haqoransu kamar zasu karci qasa kowane da wuqa ahannunsa suna bina suna saramin, Amman basu sameni ba ina kuka ina ihu, har n shiga wani baqin jeji mai duhun gaske, bana ganin ko gabana sai kalmar kukasheta karku bari ta tsira da ranta nakeji.
Na samu wata uwar bishiya na haye saman ko motsi banayi sbd tsoro lokacin da naji suna fad'in.
“Gata can sama Ku harbota da kibiya, atake fitsari ya ku'buce min ina qoqarin sake b'oyewa wani wajan,kawai sai na hango wani irin haske doki ne fari tass da mutum biyu asama,Ashe Dady kai da Mamy ne,atake kuka yaqi wannan halittun da wani irin takobi mai haske d'auke da sunan Allah b'ata suka b'ata, ka hau itaciyar ka saukoni, ka hau min fad'a akan Karna sake barinku, na rugumeka ina baka haquri, ka d'orani akan dokin kuka sakani tsakiya Mamy tanata

Please Login or Register in order to submit comment