Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji kan abun.”
Yay maganar yana d'aukan wayansa ya danna number Shattima.
Alokacin Shattima yana zaune shima bayan ya gama sallar nafila yana addu'o'insa na yau da kullun, sai dai yau addu'arsa tafi raja'a akan nemawa 'yarsa zaman lfy, da bata dangana akan rashin masoyinta da tayi.
Hasken wayarsa da take kan bedside ya hango, kasancewar bai fiye barin wayoyinsa da sauti ba, mafi akasari silent suke, ko vibration.
Da mamaki ya miqe domin ganin wa yake kiranshi tsakiyar dare.
Ganin sunan mahaifinsa yana yawo saman screen yay saurin d'aukar wayan, yay picking call d'in, yakai wayan kunnensa tare da sallama yana zama gefen bed.
Baffa liman ya amsa yana fad'in.
“Abdullahi! Na kasa bacci inata jimamin shin ya akayi auren Khairy ya koma wajan mai sunanka d'an gidan Aminu? Wlh abun ya tsayamin arai, inata jiranka ko zaka zo kamin bayani haka inarka su da suka wuni acan ko zanji wani batu amman shiru.”
Shattima ya gyara zamansa ya ce.
“Baffa! Wlh alhaji Hashim ban tab'a zaton haka daga garesu ba....”
Tsaf ya zayyanewa Baffansa abinda ya faru da taimakon da Aminu ya masa suka fita kunya.
Liman ya ce.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ikon Allah! Kai duniya haka ta lalace? amman ba komai karka damu Kansu sukayi wa, wanda Allah ya rufa masa asiri ba mai tona masa, yanzu ya ita Ummulkhairi ba abinda ya sameta koh?”
Shattima ya shafi lallausar suman kansa ya ce.
“Toh Baffa da sauqi dai sai gobe ma Zan kaita gidan nata da kaina insha Allahu.”
Liman ya ce“Allah yasa haka yafi alkhairi, shi kuma Aminu Allah ya masa albarka, ya biya masa buqatunsa na duniya da lahira.”
Shattima ya amsa da.
“Amin Baffa.”
Sukayi sallama.

*Singapore*
Abdoul zaune cikin falo yana sanye da 3 quarter, da singlet fara yana dafe da kansa, ya rasa me yake masa dad'i aduniya.
Wayansa ta d'auki ringing, ya waiga ya kalli gefen da take ajiye saman table yaga sunan Aliyah wanda yay saving da.
_(My love)_
Dogon numfashi yaja yana murza goshinsa, ya beqa hannu ya d'auki wayan, tare da d'aukan kiran, ya kai wayan kunnensa ba tare da yayi magana ba.
Daga can wata farar matashiya ce ta fara magana cikin yauqi tana wani lumshe idanu kamar bataso take mganar.
Siririya mai fad'in hanci sam baida tsayi sai dai farinta mai kyaune, tanada ido ba laifi dogowa ce mai cikar gashin gira da ta idanu, sai dai batada wata k'ira mata sabida sirintakarta, amman ba laifi tana k:irji sai dai sun kwanta kad'an, amman akwai goshi ba laifi, shekarunta na haihu 24.
“Baby! Wai yau lafiyarka kuwa? Tin fa d'azu nake online ina jiranka.”
Abdoul ya sake sakin dogon numfashi ya ce.
“My love! Ina lfy akwai abinda nakeyi ne shiyasa kika jini shiru, hope kina lfy?”
Fari tayi da idanu ta ce.
“Ina lfy Baby fatan kaima haka?”
Sama-sama suka tab'a hira ya mata sallama akan zai kirata gobe, sabida baida nutsuwa sam ayau.
Yadda yaga rana haka yaga dare bai iya runtsawa ba,har gigin asubah wayoyinsa na kashewa yayi,sabida baya son magana da kowa,shiyasa bayan yayi sallar asubah bacci mai nauyi ya d'auke shi.

Washegari misalin 7 am, Ummulkhairi ta farka da kuka tana sambatu.
Bilkisu ta kamota ta rungume ta ce.
“Haba! Baby don Allah kiyi hkr tinda sun nuna basa k'aunarki sun so tozarta mu Allah ne baiyi ba, ko wannan kad'ai ai ya isa ya saka ki godema Allah, kiyi qoqarin cire Salim aranki kamar yadda shima ya cireki,na roqe ki karki kunyata mahaifinki Khairy dan Allah. ”
Ummulkhairi cikin kuka ta ce.
“Allah Mamy duk yadda akayi badaga nisful Hayat bane, ni nasan irin son da yake min bazai tab'a guduna ba...”
Bilkisu ta katse mata hanzari cikin b'acin rai ta ce.
“Ok Baby yayi kyau kiyi abinda kika ga dama tinda mu muke miki k'arya Salim bazai iya tozartaki ba, mune zamu iya tozartaki. ”
Ta k'arashe maganar tana janye jikinta daga na Ummulkhairi ta sauka daga bed d'in ta nufi qofar fita.
Ummulkhairi ta d'ora hannu akai tana rusa kuka tana fad'in.
“Innalullahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku na lalace, ya Allah ka kawomin d'auki, Mamy tayi fushi dani wa zai fahimci halin da nake ciki ayau?”

A qofar d'akin sukayi karo da Shattima zai shigo, ya riqo hannunta yana kallonta cikin kwantar da murya ya ce.
“Please kar kiyi fushi da ita, ahalin da take ciki ayanzu, dole zamu lallasheta Musa ta dawo normal, yi hkr muje kinsan duniya zaune ma bata k'aunar kiyi fushi da ita.”
Bilkisu hawaye suka silalo kan kumatunta, ta kwantar da kanta saman k'irjinshi ta zagaye hannayenta bayansa tana shasheqar kuka.
Shattima ya matseta jikinsa yana fad'in.
“Ya Salam! Kinga fa matsalata dake, toh ke kina kuka ita fa? Haba! Sweetheart yi shiru muje mu lallashi d'iyarmu.”
Abinda ya sake tayarma da Ummulkhairi hankali kenan agigice ta diro daga saman bed d'in aguje ta nufo wajan iyayan nata.
Hannunsa d'aya Shattima ya bud'e mata, ta shigo ya rungumesu su duka yana buga bayansu, yana murmushi tare da fad'in.
“Wallahi kun cika fitinar kuka Billy kece kika b'atamin Baby da kukan nan naki gaban nan zaneki ma zanyi Sam tinda bakya girma da kuka.”
Ya k'arashe mganar yana Jan kumatunta, tare da kwaikwayon kukan kowace a cikinsu.
Sai yaga dukansu suna dariya harda k'yak'yatawa, suna ruqunqumeshi.
Wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa tare da samun nutsuwa,arayuwarsa yana son ganin iyalinsa cikin farin ciki da annushuwa, yafi masa komai.
Hancin Ummulkhairi yaja ya ce.
“Sweetheart! Ya naga baby da kayan bacci ta kuwa yi sallah?”
Bilkisu ta ce.
“Yanzu fa ta farka tin jiyan.”
Sakinsu yay ya ce.
“Oya je kiyi wanka kiyi sallah sai kizo ina son magana dake OK sweet daughter? ”
Kai ta d'aga masa tana tafiya kamar k'wai ya fashe mata a cikinta.
Hannun Billy ya kama suka fita.
Khairy anan d'akin Mamynta tayi wanka ta shirya tana kaya anan ta saka doguwar riga ta atamfa, ta sanya hijab ta tayar da sallah.
Suna zaune afalonsa ta shigo bakinta d'auke da sallama.
Jikin Bilkisun ta shige tana turo baki gaba ta ce.
“Mamy! Kiyi hkr karki kuma fushi dani bazan sake mgnar Salim ba.”
Cikin farin ciki Mamyn ta rungumeta tana sanya mata albarka.
Shattima yay gyaran murya ya ce.
“Baby! Kinsan ina sonki bazan tab'a cutar dake ba koh?”
Kanta ta d'ora kan kafad'arsa ta ce.
“Yeah sweet Dady na sani.”
“Yawwa Baby Allah miki albarka dan haka inaso ki amshi Abdoul amatsayin mijinki da hannu biyu insha Allah bazaki tab'a kuka koda nasanin aurensa ba, dan Allah wannan taimakon zakimin bana son nasake ganin kukanki akan wannan auren.”
Ummulkhairi ita tasan me takeji acikin zuciyarta, amman azahiri sai ta murmusa ta ce.
“Na amshesa har abadan Dady ka kwantar da hankalinka, insha Allah bazan baku kunya ba, Zan masa biyayya daidai iyawata bazan tab'a k'in abinda ya fito daga hannun mahaifina ba, wanda banda kamarsa afad'in duniya.”
Sosai minister Shattima ya ji dad'in kalaman 'yarsa, rungumeta sukayi suna saka mata albarka.
Bilkisu ta ce.
“Sai muje muyi breakfast, Baby je ki taso Maryam tana d'akinki.”
Ummulkhairi cike da farin ciki ta miqe tana fad'in.
“Lah! Ai ban sanaiba Mamy.”
Shattima ya ce.
“Bata tafi ba kenan?”.
Kai ta d'aga masa ta ce“Kasan Maryam da k'aunar gidan nan, jiya tace bazata tafi ba nan zata kwana, na Kira hajiyata na fad'a mata na riqeta sai ta kwanan min biyu na fitar da kewar baby tinda ana hutun makaranta.”
Kai ya jinjina ya d'auki wayansa wadda Kira ya shigo...

Misalin k'arfe 9 na dare Bilkisu ta shirya Ummulkhairi tsaf cikin wata lafiyayyar lafaya, milk colour tayi kyau matuqa, nasiha mai ratsa jiki ta mata tana kuka haka ta kaita har mota, Shattima na zaune yana jiransu, ta zaunar da ita front seat tana hawaye ta juya zata tafi Ummulkhairi ta riqota gam tana kuka.
Shattima ya b'anb'are hannunta yace.
“Please sweetheart ku shiga ciki sai na dawo.”
Ya k'arashe mgnar yana rufe motar.
Mamy tana hawaye ta Kama hannun Maryam suka nufi ciki.
Key yama motar da kansa tare bada umarni kar kowa ya bisa.
Gate ya nufa anutse yake murza stiyarin motar ahankali yana horn.
Mai gadi ya danna remote k'aton gate ya fara yin sama har ya bud'e baki d'aya.
Ya silala hancin motar waje.

*Asokoro*
Salim zaune a cikin motarsa,a gate d'insu, sai gwada kiran number Abdoul yake tin jiyan da Abdulrazaq ya turo masa yake famar gwadawa amman bata shiga.
Ashar ya lailayo ya maka tare da fad'in.
“Munafukin banza ba dole ba ka rufe waya,tinda ka samu tsuntsu daga sama gasashe.”
Ya k'arashe maganar yana sake gwada kiran number.
Cikin sa'a ta shiga sai dai har ta katse ba'a d'auka ba, sai da ya Kira sau biyar aka d'aga ba tare da anyi mgna ba.
Salim cikin k'ufula ya ce.
“Munafukin banza ka auremin mata ko? Toh wallahi tallahi kwana d'aya na baka daga yau zuwa gobe ka saketa, idan ba haka ba zakaga abinda zai biyo baya kare ma sai ya fika daraja a k'asar Singapore d'in dan uban babanka...”
Daga can Singapore kuwa abinda yake faruwa shi ne.....

_YI WA KAI...!_



_Free Novel_


*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 7&8*


A gate d'in gidan commissioner Aminu minister Shattima ya tsaya yana horn.
Ya waigo yana kallon Khairy, ganin har lokacin kuka take, ta cusa kanta tsakanin guiwowinta.
A hankali ya furta.
“Ya Rabbi! Baby! Yi haquri mana please, ba fa rabuwa zamuyi ba, ta har abadan.”
Ya idar da maganar tare da sauke ajiyar zuciya, me qarfi lokacin aka bud'e masa gate d'in gidan ya danna hancin motarsa cikin gidan.
Murmushi ya sub'uce masa lokacin da ya ga commissioner Aminu, da iyalansa suna tsaye a compound d'in gidan, fuskokinsu asake cike da annushuwa.
Parking yay nan dab dasu, bai shiga parking space ba.
Ya kalli Ummulkhairi wacce ta k'ara sautin kukanta, tana d'ago kanta jin an kashe motar.
Hannayenta ya kamo wanda suka sha jan lalle cikin lallami ya ce.
“Sweet daughter! Kiyi haquri kukan ya isa haka, kin manta inda kikazo ne? Ai ko kullun kike son ganinmu da mamynki kiranmu kawai zakiya awaya muzo ji ganmu muA, ko kizo gobe idan Maryam zatazo zan bayar da wayanki akawo miki kinji baby?”
Kamar jira take ta qara sautin kukan, tare da qamqame shi tana kuka mai tsuma zuciya tare da fad'in.
“Dady! Ni ban saba da rashinku ba, yanzu haka zanyi rayuwa ba iyayena akusa dani? Wa zai dinga riritani da shagwab'ani, tare da sani ahanya idan nayi ba daidai ba?”
Murmushi me sauti ya yi tare da buga tsakiyar bayanta, ya ce.
“Mijin ki mana baby ga kuma Dadynki Aminu da Amminki Abida, kafin ku tare agidanku, don Allah ki daina kukan nan yi shiru kinji? Sannan kiyi aiki da dukkan nasihar da muka miki kullun zamu dinga zuwa tinda sassafe ganin ki, shi kenan koh?”
Kai ta d'aga tana share hawayen fuskarta da tafin hannunta.
Handkerchief ya zaro cikin aljihunsa ya goge mata fuskar da kyau, ya sumbaci goshinta, ya ce.
“Oya murmushi mugani.”
Ummulkhairi ta saki murmushi.
Yaja dogon hancinta ya ce.
“Good baby oya muje.”
Ya k'arashe maganar yana zura hannunsa ya bud'e mata motar.
Shima ya bud'e b'angaransa ya fito.
Abida ta rungumeta tana fad'in.
“Oyoyo sweet daughter, barka da shigowa families d'inmu.”
Ummulkhairi tai k'asa da kanta, tana neman zubewa k'asa ta gaishesu Abida ta hanata.
Shattima sukayi musabaha da Aminu, yana amsa gaisuwar yaran cikin sakin fuska, ya ce.
“Toh ga 'yarku nan na kawo muku amana, ni zan koma Allah ya bamu alkhairi, Maryam na gaisheku.”
Aminu ya ce.
“Wlh baka isa ba sai mun shiga kaga wajan zamanta. Wai kai kad'ai ka fito ne?”
Dariya ya yi yana fizge hannunsa ya shige mota yana fad'in.
“Nafi kowa sanin wajan da na kawo Khairi meye na ganin d'akin da zata zauna kuma? Toh meye dan na fito ni d'aya? Ai Allah yake tsare damu ba mutum ba, kaga na tafi seda safe bye.”

Ya k'arashe mgnar yana rufe qofar yama motar key yana ja da baya har ya juya ya nufi gate.
Aminu ya girgiza kansa yana d'aga masa hannu. Can falonsu sukaje da Khairy sukayi mata nasiha sosai,taji dad'in hakan, ta dan sake kad'an.
Abida ta kai Ummulkhairi har b'angaranta, tare da sake mata nasiha kamar yadda,zatama Maryam da Nafisa, ta ce Nafisa ta zauna wajanta su dinga kwana har Abdoul ya dawo.
Hakan ba qaramin jin dad'i ya saka Khairyn ba! Sai dai taqi nunawa azahiran ce.

_Abunda ya faru a Singapore kafin kiran da Salim yama Abdoul shi ne._

Abdoul tin bayan kwanciyar da ya yi bayan sallar asuba, wani irin zazzafan zazzab'i ya tashi da shi.
Da k'yar ya iya miqewa ya yi wanka ya had'a tea me kauri ya sha, ya sha magani ya koma ya kwata.
Bai sake tashi ba sai wajan 1 na rana, cikin ikon Allah bai tashi da zazzab'in ba, ya yi wanka yay sallar azuhur, ya shirya zuwa makaranta sunada lecture k'arfe 3.
Tsautsayi da bai wuce lokaci, bayan sun tashi daga makaranta 1 hour kawai sukayi, ya biya super market ya yi shopping, a ciki yana zagayawa yana zab'ar abinda yake so, wata yarinya da bata wuce 6 years ba, suna tafe da iyayanta, suna zab'ar abubuwan da suke buqata, tana shan ice cream, dai-dai lokacin da Abdoul ya biyo ta wajansu, suna dab da juna, idanun yarinyar ya sauka akan wani kwalin biscuit, ta saki roban ice cream, d'in, cike da shagwab'a take nunawa iyayan nata kwalin biscuit d'in.
Abdoul sam bai kula ba, hankalin shi agaba ya take robar ice cream d'in samtsi ya kwashesa, ikon Allah kamar ana jansa ya tafi shuuuuu, yana kiran sunan Allah, yana duba abinda zai riqe amman ina abunka da tayis mai shegen sulb'i, sai ga shi k'asa wanwar yayin da kwandon hannunsa ya fara kaiwa k'asa shi ya biyu baya, ya yi muguwar fad'uwa akan hannunsa na hagun, wanda atake hannun ya karya.
Idanunsa ya rumtse cike da jin azaba, lokacin da yaji qaran karayar qashin hannunsa, tabbas yasan karya ya yi.
Iyayan yarinyar sukayo kasan aguje hankalinsu atashe ganin robar ice cream d'in da Diana ne ta yar.
Kamasa sukayi suna masa sannu tare da ba shi haquri.
Kai ya girgiza musu.
Su suka kaishi hospital, mahaifin Diana shi ya tsaya akan komai, har kuka yayi jin Abdoul karaya ya yi.
Abinka da harakar manyan mutane kafin qarfe 6:30 pm, lokacin su na can har an d'ora hannun, an masa qarin ruwa tare da allurai, ya samu bacci.
Mahaifin Diana ya kasa ya tsare ya kasa tafiya gida, har sai da ya farka yaga jikin nasa da sauqi ya tafi, daman asibitin basa barin masu jinya su kwana, sunada masu kula da majinyaci, za'a amshi number mutum idan sun ga majinyaci na matse zasu kira.
A lokacin da josnny suka tafi gida da iyalansa ne, Abdoul ya ji yana sha'awar kiran mahaifinsa ya sanar da shi tsautsayin da ya sameshi.
Da hannunsa mai lafiya ya kunna sabuwar wayan da siya jiyan, yana kunnata ne kiran Salim ya shigo, daga d'agawa ne, ya ji irin zagin da yake masa, har yana basa umarnin ya saki Khairy wai matarsa ce.

Cike da mamaki Abdoul ya muskuta yana ciza lips d'insa, tsabar zafin d'orin hanunsa da yake ji.
Ahankali ya furta.
“Please ba wanda kake nema bane, karka sake kirana, kai kasanta ma wacce kake maganar kanta.”
Daga can Salim ya bud'e motarsa ya fito, yana zuba ruwan masifa.
“Wallahi k'arya kakeyi kace baka san Ummulkhairi ba, tsohon munafuki daman can sonta kakeyi, wallahi ko kaffara bazanyi ba, daman can sonta kakeyi, kaida iyayanka kuka shirya makirci dan ku rabani da ita, toh wallahi k'arya kukeyi sai naga bayanku Ku zuba ido ku gani...”
Abdoul yay murmushin k'arfin hali ya ce.
“Kai kasan suwaye iyayena, ba tsaffin ala gwangwan bane, basa b'atawa sai dai su gyara, dan haka anqi a saketa idan akwai inda zaka kaini a fad'in duniyar nan a sakani na saketa toh bismillah, sakarai k'idahumi wanda baisan Annabi ya k'aura ba! Mahaukacin gangan.”
Ya k'arashe mgnar yana kashe wayan baki d'ayanta, yana Jan tsaki tare dafe kansa, ya lumshe idanunsa, yana fad'in.
“Haka kawai ina zaman zamana an had'ani da masifa, Ina dalili daman hakan Salim d'in nata yake? Mstwwww!”
Daga can kuwa Salim ya kama masifa da bala'i sai ashar yake lailayawa Abdoul jin yace bazai saki Ummulkhairi ba.
Motarsa ya shiga yana zuba horn aka bud'e masa gate ya shiga ciki.
A farfajiyar gidan yay parking, koh rufe motar baiyi ba, y nufi b'angaran iyayan nasa.

Falon ya fad'o kamar ana koro shi yana famar masifa.
Cikin sa'a alhaji Hashim na zaune.
“Father! Umma! Nace kunga abinda kuka jazamin koh? Ga shinan na kirasa ya sakar min mata yace bazai Saki ba Toh wlh na rantse muku da Allah za kuga binda zai biyo baya, ba abu bane me kyau idan na fasa binda nayi niya akan Ummulkhairi ni ba dan halak bane, daga yau bazan sake maganarta ba sai abubuwan sun fara fitowa a aikace. Ita kuma Aliya ko zataci ubanta na rantse da Allah sai ta tsani me sunan Salim arayuwarta.”
Ya k'arashe maganar yana juyawa fuuuuu yabar falon ba wanda ya tanka masa.
Sa'idah ta ce.
“Kana jinsa yana mana rashin arziqi bazaka iya masa komai ba? Wlh da nasan iskancin Salim ya kai haka, daman munbarsa da annobar yarinya can...”
Alhj Hashim ya girgiza kansa yana fad'in.
“Kashhh! Sa'idah! Bakya ganewa, kin tab'a ganin mahaukaci ya warke ne? Barsa dan ubansa nasan maganinsa.”
Ya k'arashe maganar yana miqewa ya d'auki wayoyinsa ya nufi hanyar barin falon.
Hajiya Sa'idah tayi tagumi tana nadamar rabashi da Ummulkhairi da sukayi, tana tsoron abinda zai je yazo, tabbas ko kashewa Salim ya ce zaiyi to fah... . Dan ba zata tab'a manta abinda ya tab'a faruwaba, kud'ine da matsayi da cikkakun takardunsa kawai suka nuna komai ya wuce kamar ba'ayi ba, hakan sirrinsu ne sai likitoci duk duniya ba wanda ya Sani, ko acikin family d'insu mutum biyu kawai suka sani.


_Commissioners Quarters_
Shattima yana dawowo gida, bai shiga ciki ba, cikin mota yake, yana waya.
Can ciki kuwa Mamy wata irin matsanaiciyar kewar Ummulkhairi ta addabeta, ta kasa zaman falon tabar Maryam ta ce tayi kallo idan taji bacci ta kashe kayan kallon ta hau saman, kanta yake ciwo.
Maryam kuwa zamanta tayi tana kallon wani flim na larabawa tashar MBC 2.
11 pm. Minister Shattima ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama.
Duk irin nisan daga qofar zuwa falon bai hanawa da kayi sallama aji, sabida yanayin tsarin ginin.
Maryam jin daddad'ar sautin amon murya Shattima yana sallama taji wani irin bala'in sanyi acikin zuciyarta, tare da sa bud'e k'ofofin hancinta, ta fara shaqo daddad'an k'amshinsa mai sanyaya zuciya, ta bud'e bakinta tana rarraba idanunta ta idan zata hango shi, ai kuwa ta hangoshi hannayensa zube cikin aljihun wandon dakekiyar shaddarsa,ta amsa sallamar.
“Wa'alaika salam, welcome Dady.”
Tsakiyar falon ya shigo yana amsawa.
“Thank you daughter, ina mamynki?”
Ya mata tambayar yana janye idanunsa daga kallonta.
K'asa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, sbd wani bala'in sanyi da ya fara ratsa dukkan sassan jikinta, SBD kaifafan idanunsa masu wani iri sinadari da mata basa jure kallonsa na wani lokaci.
Can k'asa cikin sanyin da gab'ob'inta sukayi ta ce.
“Mamy tin da muka shigo bayan mun rakaku da auntie mota tace kanta na ciwo zata kwanta.”
“Subahanallahi.”
Shattima ya nufi seat d'in kujerun da suke b'angaran gabas ya zauna yana ajiye hular kansa tare da cusa hannunsa cikin yalwatacciyar sumar kansa yana shafawa, ya miqe qafafunsa zuwat saman kujeran, yana jingina bayansa da allon kujerar.
Wayarsa ya d'auka ya latsa number Bilkisu ya danna mata kira.
Kwance take saman makeken bed d'inta sai juyi take takasa bacci jiran Shattima take yazo ta kwanta cikin jikinsa ko ta rage kewar Khairy.
Sanye take cikin kayan bacci Riga da wando masu samtsi sun mata kyau sosai, duk da ramarta.
Jin ringing d'in wayanta, ya sanye ta bud'e idanunta ta mirgina ta iso dab da wayan da take kan pillow.
Ganin me kiran ya saka ta d'auki wayan tare da picking call d'in.
Asanyaye ta amsa.
“Hello Mi Amor! Ka shigo?”
Murmushi mai kyau ya saki tare da furta.
“Uhmm! Duk kewar babyn ne koh?”

Maryam asace ta d'ago da kanta ta kalli b'angaran da yake zaune, jin yadda yake magana cikin kamewarsa tare da nutsuwa, sautin amon daddad'ar murya shi tana zagaya falon ahankali.

Maryam bata san lokacin da a zuciyarta ta furta.
“Wow! Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci Dady Shattima, Allah ya masa tsari me kyau, ga shi kamar sauriya Sam baya tsufa ko alamar tsufa basu fara bayyana ba atare da shi, Sam bazaka ce shi ya haifi auntie Khairy ba wayyo Dady I love you so much, son so domin Allah, my dad, inama Mamy Billy ba mutuniyar kirki bace wallahi da bazan iya b'iye son da nake maka ba, sai na bayyana amman ina ba hali ana barin halak dan kunya.”
Ta furta duk wannan bayanan acikin zuciyarta, ta masa k'ura da idanu tanajin ruwa sun fara taruwa acikin idanunta, tana son salon yadda yake tafiyar da rayuwarsa, shi d'in gwanine wajan nunawa iyalinsa soyayya ga nutsuwa ga tsaf ga kyau,duk da yana baqi amman yanada wani irin bala'in kyau mai d'aukan hankali, ga shi bayada wulaqanci ko girman kan shi wani ne.
“Yanzu dai sweetheart oya sauko ki dafamin black tea.”
Ya k'arashe mgnar yana katse kiran.
Bisa tsautsayi ya waigo b'angaran da Maryam take zaune.
Karaf ya kamata tana kallonsa idanunta akwai kwancin k'walla acikin su.
Muguwan kuyan taji lokacin da ta tsinci muryasa mai rud'ar mata da k'wak'waluwa yana fad'in.
“Subahanallahi daughter! Me ya sameki kamar hawaye kike? Ko bacci kikeji?”

Daburcewa tayi ta rasa me zata ce sabida bata iya wani katab'us idan yana kusanta.
Cikin inda-inda kamar zatayi kuka ta ce.
“Wallahi Dady cikina yake ciwo tin yamma, yanzune nakeji kamar yana qaruwa.”
Ta k'arashe mgnar kanta aqasa.
Shattima cikin kulawa ya ce.
“Subahanallahi sannu daughter, bari mamynki ta sauko yanzu sai ta dubaki ta baki magani kisha, ko muje hospital.”

Maryam gabanta ya fad'i ta shiga raba idanu dan ta tsani maganar hospital ko shan magani sbd tsanar da mata allura da magani.
Cikin inda-inda ta ce.
“Dady! Zai bari wallahi ba sai nasha komai ba!”
Bai kalleta ba ya ce.
“No! Dole fa sai anyi d'aya cikin kota baki magani ta miki allura agida ko muje hospital. ”
Shasheqar kukanta yaji kamar wasa na tashi a falon.
Manyan kaifafan idanunsa ya zaro waje cike da mamaki zaiyi magana yaji takun saukowar Bilkisu daga stairs.
“Innalillahi! Mi amor! Me ya samu daughter?”
Kai ya girgiza yana murmushi ya mata bayanin abinda yake faruwa.
Bilkisu ta ce.
“Dan mafi akasari idan tazo gidan nan har ta tafi baka k'asar Baku fiye had'uwa anan ba, sai idan wunine tazo baka San k'iyayyar Maryam da magani ba, ko allura ai bata k'auna.”
Ta k'arashe maganar tana isowa wajan Maryam ta kamota ta rungume tana buga bayanta ta ce.
“Yi shiru k'yale dady, ya kikejin ciwon cikin?”
Maryam ta ce.
“Na rantse da Allah Mamy naji sauqi komai banaji yanzu Allah Mamy.”
Dariya sosai ta k'wacema Shattima ya fara yana k'yak'yatawa, cikin sauti me fita a sannu.
Mamy ta girgiza kanta ta kamata ta ce.
“Ok muje ki kwanta.”
Hayewa sukayi sama da dubara Mamy taba Maryam maganin ciwon ciki harda su sweet dan ta manta maganin, ta sakata ta shirya cikin kayan bacci sai da ta kwanta ta lullub'eta ta sakata tayi addu'ar bacci kafin ta rufo mata k'ofar ta sauko wajan Shattima.
Black tea ta dafa masa ta saka kayan k'amshi da citta ta kawo masa.
Saman cinyarshi ta hau tana basa abaki yana Sha, suna magana k'asa-k'asa cike da soyayyar junansu, daga k'arshe suka haye stairs, can suka k'arasa soyewar.

Washegari Ummulkhairi sai ta shi wasai batajin wannan k'uncin da takeji abaya na rashin Salim,sai da sonsa da k'aunarsa na nan daram zaune acikin zuciyarta.
Tin bayan sallar asuba da tayi sallah ta gyara falon da bedroom d'inta tsaf, ta sanya turaren wuta, ta ce da Nafisa tafi part d'insu Ammi su d'ora girki.
Nafisa ta ce.
“Lah! Auntie Khairy ai mu bama komai masu aiki sukeyi, girki Abba ne kawai Ammi take yi.”
Khairy ta ce.
“Eh muje na tayata nifa na saba bana iya bacci bayan asubah har na tafi school, ba ruwana da masu aiki komai yi nakeyi muje don Allah.”
Ba yadda Nafisa ta iya suka fito suka nufi part d'insu Ammi.
Lokacin da suka shigo Lantana na shara Lami tana mopping ko ina sai k'ylli yake, kai tsaye kitchen Nafisa ta jata suka shige.
Ammi tsaye tana juye ruwan tea a flask, taji sallamar su Khairy.
Cikin sakin fuska ta amsa, tana fad'in.
“Ah Khairy! An tashi?"
Rusunawa tayi aladabce ta gaisheta.
Ammi ta amsa tana tambayarta baqunta.
Ummulkhairi ta amsa tana juye ruwan tea d'in Ammi ta ce.
“Ki bari mana Khairy kuje ku kwanta ku huta.”
“A'a Ammi bari mutaya ki aiki.”
Haka kuwa akayi tsaf da Khairy da ita akayi komai na breakfast ta shiya a kan dining area, taje ta gyara kitchen tsaf, Ammi sai albarka take sanya mata.

*Singapore*
Abdoul

Please Login or Register in order to submit comment