Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DEENAH

BY

KHADEEJA CANDY


PAGE ONE TO END .....



Da sauri sauri take tafiyar ganin unguwar babu mutane sosai ta tada kai ta kalli sama sai ta kara bata fuska ganin hadarin daya lullube garin!

Bata ankarava taji an sako da ruwa mai karfi nan da nan ya fara jikata da gudu ta nufi wata bishiya dogon yaro tafake aiko ruwan kamar ita suke jira suka kara karfi!

Kankame jikinta tayi ta bata fuska kamar zatayi kuka

Ruwan suka cigaba da zuba harda kankara duk sun jka mata kaya

Wata kafirar mota ta wuce ta gabanta sai kuma naga tayi reverse ta dawo daidai inda take tsaye ta tsaya!

Ahankali naga ana sauke glass din motar ni khadeeja candy nace”Allah gwanin iya halitta”

wani kyayyawan saurayi ne na gaban kwatance da bazai wuce 33 yrs ba na gani a driver seat!

Fari fes mai manyan ido da dogon hanci akasan hancin an yanka masa madaidaicin bak’i!

Cikin sanyayyar murya mai taushi naji yace”my dear deenah shigo” kallonsa da yaga ta tsaya masa ne yasa yace” plz shigo mana kar ruwan ya kare a kanki”

Tattaro rigarta tayi mai kamada ta indiyawa ta shiga tare da rufe ganbun motar!

Handkerchief ya ciro ya mika mata,sannan ya ja motar! 

Ya dauki hanyar da zata fitar dasu unguwar baice da ita komai ba itama batace mishiba har suka bar unguwar sannan ya samu gefen t-t yayi parking! Ya kalleta a karo na biu yana murmushin da ya fitarda beauty point dinsa ya bude baki kamar zaiyi magana!

   Sai kuma naga ya ciro wayarsa ya ya shiga dane dane,,

Suna haka aka watso wata irin walkiya da saida dinah ta razana ba shiri ta rufe idonta!

 ya a hankali naga ya kalleta yayi. Murmushi mai sauti,

Ta dago suka hada ido wani yarrrr taji lokacin da idonta suka shiga cikin nashi,da sauri ta kawarda fuskarta,

Shima ya Mai yarda dubansa gurin wayar ya cigaba da dane dane sa! Sunyi minti 5 ahaka sannan ta dago ba tare da ta kalleshi ba tace” waye kai” yayi kamar bai jitaba, ta kalleshi tace” kai wanene” yayi banza da ita yana buga game

   Wannan karon kallon tsaf ta masa sannan tace akaro na uku ” ina nufin ya sunan ka ina kake kuma ina kasan ni” ko dagowa baiyiba balle ya bata amsa shirun da taji yayi har na wani lokaci baice mata komaiba yasa ta sake Kallonsa a fusace tace ” wai kai wani irin miskiline ina maka magana zakayi min shiru kamar kurma ” 

nan ma shiru, 

Bude motar tayi zata fita da sauri ya riko hannunta yace” haka zaki fita ruwan fa bai dauke ba ” tana harararsa tace ” aeh din to ina ruwanka dan rainin hankali ina magana zakayi banza dani” “I’m srry my dear rufe motar zan baki amsa ” saida tayi kwafa sannan ta rufe motar, dora hannunsa yayi saman sitari yana Kallon t t yace ” ni mutum ne irinki kuma musulmi kuma yanzu haka ina garin SOKOTO tare dake ” ba tare da ya kalleta ba yace” nabaki amsarki sai mie kuma”? Mtswww taja tsaki ” ni bazan kara tambayarka ba balle kamin yanga”!

Ya kalleta yana murmushi yace ” ni namijine ba mace ba dan haka bamu hada hanya da yanga ba” harara ta watsa masa ya dauke kansa ya kunna motar suka hau t t,

ahankali yake tafiyar kamar mai L batare da ta kalleshi ba tace ” ni ka sauke ni a nan dan sauri nakeyi” 

Hannu naga yakai ya dauko wati plate din DVD yasa, ya kure volume nan da nan wakar ‘kirrish’ ta fara tashi,,

Dagowa dinah tayi ta kalleshi taga ya kafeta da ido tace ” ni guiwa locos zaka kaini ” kai kawai ya daga mata ya fisgi motar kamar zai tashi sama!

Ganin yanda yake gudun ya tsora tata Kuwa ta shiga masa harda kukanta kamar ma haukaciya ” na shiga uku wai ina zaka kaini da wannan mugun gudun haka ai mun kusa kawo fa ka rage gudun haka dan Allah “!

Bai kula taba har suka shigo cikin unguwar sannan ya tsagaita gudun dayake … Gaban wani katafaren gida mai katon gate naga yayi parking,, 

Takai hannu ya rage volume sannan ya kalleta yace ” my queen nan ya isa ko mu shiga ciki dan naga akwai sauran yayyafi ” kallonshi tayi cike da tsoro tace” ya isa na gode “,

 ta bude motar ta fita ta nufi cikin gidan  sauke glass din motar naga yayi yana kallonta har shige sannan yaja motarsa yayi gaba

Da gudu dinah ta karasa cikin parlor,, bata tararda kowaba! Kai tsaye ta nufi stairs dakinta ta shiga ta fada bathroom saida tayi wanka sannan ta fito daure da towel,

Gefen gado ta sauna tana yarfarda gashin kanta,, 

Sannan ta nifi wadrope ta dauko gown din sari mai stones maroon color tasa tare da red ribbons ta daure gashinta,,

Sannan ta nufo dakin mahaifiyarta! 

Tana ganinta ta daki kirgi tace” yanzu cikin ruwan nan kika tafo hajiya ” Saman jikinta ta fada tana fadin” tun kamin a fara ruwa na fito kuma wani ne ya rage min hanya ruwa bai jika niba ” murmushi mama tayi tace” toh alhamdulillah yar albarka tashi kije kici abinci sai na baki tsara bar da babanki ya aiko miki” kai kawai ta daga mata ta tashi ta nufi kofar fita! 

  WACE CE DEENAH?? 

   
[11/16, 10:13 AM] Khadeeja Candy: WACE CE DEENAH??? 


Alhaji. Umar salisu tanko shine mahaifin Deenah tsohon ambassador Nigerian ne to Japan dan majalisa ne a yanzu kuma babban dan kasuwa dan yana daya daga cikin manyan yan kasuwan dake shigowa da nigeria kayan masarufi matansa 2 aisha ce uwar gida wanda suke kira da hajiya bata taba haihuwaba haka yasa ya auro halima wanda itace mahaifiyar su Deenah ta haifa masa yara biyar !

Abdullah ne na farko abuja yake saune da matarsa yaransa biu yana aiki a central bank of Nigeria,sai samira dake aure a kaduna da yaranta 4 sai mai bimata faruk dake shirin kammala karatun likitan cinsa a india sai DEENAH dake karatun low a usman dan fodiyo university sai auta zara dake iman international school,

Mahaifin Deenah haifafen ba sakkwace ne amman yanayin aiki bai barshi ya zauna haka yasa ya tare da uwar gidansa aisha a abuja,

A kabar halima wanda ita ta zabawa kanta zama a nan dan mace ce maison zaman lfy ganin basa shiri da aisha yasa taki binsa a chan, kuma gashi duk wasu harkokin kasuwancinta ana SOKOTO take guda nardasu

Deenah farace faes tana da kyau saida ba sosai ba dan ta biyo mahaifinta ta dauko farin fulanin mahaifiyarta, bata cika tsayiba kuma ita ba gajeruwa ba coca cola ce dan tana da shaf ga gashinta har gadon baya ta dauko halin mahaifanta na son addini da jama ah da far ah ga kuma farin jini agurin kowa dan ko iyayenta tafi soyuwa a ransu sama da sauran yayansu shiyasa mahaifiyarta ta hana akaita ko ina karatu dan tafison tana kusa da ita a koda yaushe suna nuna mata gata musamman mahaifinta shiyasa ta sagarce,,, in tana abu kamar ba yar shekara 22,

Su biyar suke zaune a gidan yanzu ita da zara sai cousins dinta  Zainab da nafisa da abul-khair dan shekara 13  dukansu yayan kanne mahaifinta ne in aka cire zara

Gidan sama suke zaune mai rai da lafiya mai hawa 2 kowa da dakinsa,

 part din mahafinsu daban babu abunda ba a zuba a cikin gidan ba ga yan aiki kalakala basa aikin komai daga ci sai wanka,

Duk abunda take so shi ake mata ba tada matsala da ko ina,!

Rayuwar india ta zabawa kanta kamar wanda ta taba zama cikinsu,

Koda yaushe cikin kayan india take da sauraren wakokin su shiyasa ta iya rawar india kalakala gashi in tayi dress ba zaka banbanta ta da indiyawa ba,

        !! Wannan kenan!!

Back to labari!!!

Deenah tana fita dakin mahaifiyarta ta nufi daning room,

Kujera taja ta zauna sannan ta zuba white rice da sauce din kaji ta zuba juice din pineapple and coconut hadin gida,ko spoon bata saba ta shiga aika lomomi, 

bata tsaya ba saida taji ta koshi sannan tayi hamdallah ta tashi ta nufi kitchen ta wnke hannuta, sannan ta nufo dakin momi sai gyatsa take.

Da sallanar ta shigo momi na zaune gaban laptop sanye da glass tana nazarin harko kinta na kasuwanci ta saman jikinta deenah ta kwanta tana fadin ” momi na kare ina tsarabar take” dagowa momi tayi ta kalleta tana murmushi ta nuna mata bedside drawer, ta sauri ta tashi ta nufi gurin,

wani dan cute box ne pick colour ta dauko ta dawo gefen gadon momi ta zauna tana hadi yawu jikinta sai zazzan yake duk taga nawar ta bude,

Da karfi da balle lid din wata kyakkyawar sarkal gol ta fado!

Wata kara da saki ta chafki sarkar tana rawa..

 da sauri momi ta rufe kunnuwanta tana kallonta tace” dinah ar u out of ur mnd zaki cika mana daki da ihu haka gt ot”!!! Ta karasa maganar tana nuna mata kofa, dinah sai dariya take kamar wata tababba tace” momi ina cikin murna bakiga abunda abbah ya aiko min ba” momi na nuna mata kofa tace ” nariga ki gani ai je chan downstairs kiyi murnar ki karki rikita min lissafi ” da gudu dinah ta fita tana ihu!

Dakin Zainab ta shiga ba tararda ita ta nufo dakin nafisa nan ma ba kowa, da sauri ta nufi dakin zara nan ma wayam.. 

Tsaki taja ta banki kofar dakin ta nufi downstairs

BQ ta nufa da gudu gurin yan aikunsu, tana isa ta shiga kwala musu kira” maman Maryam hindatu kowa da kowa ya fito ” da gudu suka fito suna fadin lafiya dinah miya faru? Sarka ta shiga nuna musu tana rawar kai tace ” sarkan dana fada muku abbah zai siyo min dazun ya aiko min da ita ” duk suka kwashe da dariya suka karbi sarka suna yabawa dan daga ganinta kasan mai tsada ce,

Tayi kusan awa 1 chan sannan da dawo main house,dakinta ta nufa

     tana shiga ta tsaya gaban madubi tana gwada sarkar sai kwasar dariya take ta dauko wayarta ta shig daukar pic..,

 haka dinah ta wuni cikin far ah da jindadi sai bayan i’sha zazzabi ya taso mata hakan yasa ta bachi da wuri,

       Washe gari 

 kowa yana daning danyi break dan al’adar gidance tare ake cin abinci musamman ran weekend,

Momi na fito ta duba kujerar dinah bata ganta ba ya kalli nafisa tace” ina dinah”?  Tace” banga ta fito ba tun jiya” momi ta hade fuska tace” shine kuma Bazaku iya zuwa ku dubata wai ku miyasa ba kuda kula” duk suka shiga ce mata srry momi,
taja tsaki ta tashi ta nufi upstairs.

Dun kule cikin bargo momi ta tararda ita, takarasa kusa da ita ta yaye bargon tana tafa jikinta a hankali ta bude ido ta kalli momi tace” momi ” momi ta zauna kusa da ita tace” I jiya kinsha ruwan sama shine kika boye min ko kuma kinsan jin kisha ruwa zazzabi kikeyi” murmushi kawai dinah tayi momi tace ” to ai yanzu jikinki ya gaya miki ” momi na kaiwa nan ta kwalawa zara kira, da gudu ta shigo tana fadin ” momi gani ” momi tace ” je ki dauko mi wayata ta nan saman gado yi sauri ” ta fita da gudu cikin yan mintuna ta dawo dauke da wayar ta mika mata,

Momi ta karba ta shiga neman number diyar abokiyar ta sannan ta kara akunne,

Sallama naji ta fara amsawa sannan tace ” lafiya kalau sa adatu kizo dan Allah kanwarki ce ba lafiya ki zo dan Allah yanzu ki mata alurai ko magana ” chan kuma naji tace” ok shikenan ” ta aje wayar tana fadin ” dinah tashi kici abinci yanzu za azo aiyi miki alura” kai ta girgixawa momi taja bargo ta rufa momi ta kalli zara tace” zara je ki hada mata tea mai kauri ” 

  Zara ta sauka downstairs ta hada mata ta kawo wa momi ta bata saida ta tabbatarda ta shanye sannan suka bar dakin ita da zara,

Bayan fitar su da awa daya sa adatu ta shigo bayan sun gaisa ta bata magani tayi mata alura sannan tabar dakin nan da nan bachi yayi gaba da dinah

Karfe 2:00pm nayi application dinta na kiran sallah ya fara aikinsa,

A hankali ta fara motsi tana juye2 jin takarda cikinta yasa ta bude ido,

sillin ta kurawa ido har na wani lokaci sannan ta kai duban ta gurin hannunta inda ta kardar take jikinta ba kwari ta tashi zaune tana kallon takarda mai zagayen heart red color an daureta da wani zare yallow, takai hannu da sauri ta dauki takardar tana dubawa sannan ta shiga warware zaren,

   wata yar karamar takarda ta fado,,. A hankali takai hannu ta dauketa ta shiga karantawa

      ” HI LOV HOPE U                                          FEELING MUCH BETTER NOW OHH I REALLY MISS U DEAR #KISS ” 

mamaki ta shigayi tana duba takarda har ta juya bayanta taga an rubuta 

        ” IN KINA SON      GANI NA GANINAN BAYAN WINDOW KI “

Da sauri ta nufi window tana lekawa ta ganshi jin gine jikin mota cikin black suit yana kallon tagar dakin fuskarsa babu yabo ba fallasa,

Da sauri ta juya masa baya ta dafe zuciyar ta tana tunano jiya har saida ta tabbatarda lallai shine ta sake juyowa ta ganshi a yadda ta barshi ta juyo da gudu ta nufo downstairs,

Tana kawowa parlor su zainab suka Tambayar lfy bata kula suba ta cigaba da gudun har tabar gidan.
[11/16, 10:14 AM] Khadeeja Candy: Bayan gidan ta nufa tana karyo kwana ta fara hangensa still yanda ta ganshi dazu saidai wannan karon kwanar da ta fito yake kallo kamar wanda yasan da zuwanta,

Da gudu ta karaso inda yake sai hak`i take,

Ido ta kuro masa kamar mai tunanin abunda zatace ta kalli tagar dakinta sannan ta kalleshi cikin fuskar tausayi tace “dan Allah kai wanene ya kayi kasanni may kake nema a gareni” juyarda fuskarsa yayi ya maidata right side yana duba agogon hannunsa kamar mai jiran wani, ta dawo side din da fuskarsa take ta hade hannayenta tace” plz n plz ka fadamin abunda na tambayeka koda kai aljani ne wlh zan raurareka” sai alokacin ya dago ya kalleta yana murmushi yace ” ni ba aljani bane ni muttun ne irinki saidai kuma kince bazaki sake tambayata ba ko kin manta ” ” kabar zancen baya kawai ka bani amsoshi na karka rikitamin kwakwalwa “, wayarsa tayi kara alamar sako ya ciro ya duba sannan ya bude motarsa ya dauko wata leda ya mika mata murza yatsunta ta shigayi tana kwankwanton karba yace ” duk amsoshinki suna nan gurin dan haka karbi kawai”!!

Kamar wata karamar yarinya ta zama tana shafa hannayenta a rigarta kamar mai goge abu tace ” inna karba bazan bata ba “? yana kallon saman kanta yace” yan gidanku na kallon ki zaki bata! ” tunani ta dan shigayi sannan tace ” kamar ya ban ganeba ” ? Ratsewa yayi gefe ta hango su zainab da zara tafe da saurinsu ” cike da tsoro ta kalleshi tace ” ya aikayi kasan zasu zo “?

Baice da ita komaiba ya duka ya aje mata ledar gabanta ya shiga motarsa!!

Yana shirin rufe ganbu tace ” tace magana fa nake maka ” ya karasa rufe motar tare da cewa ” wish u quick recovery my queen ” yana kaiwa nan yaja motarsa ya hau t-t ido ya bishi dasu,

Har su zainab suka kawo kusa da ita! Zainab ta dafata tana murmushi tace ” wow sis amman gaskiya wannan ya hadu waye shi”? Juyowa tayi tana karyo dan soshe soshe tace” am wani friend dina ne a skul “!

Tace ” gaskiya ya hadu handsome guy ” ” uhmm ” kawai tace ta matsa nesa dasu sannan ta kalli zara tace ” za daukar min ledar nan ” dukawa zara tayi ta dauki ledar, dinah tayi waje da ido tace ” zara bki ji komaiba “? Kai ta girgixa mata tace” minene hala”?

Murmushi tayi ” a a babu komai nidai kaimin ita dakina “

Kai zara ta daga tace ” to amman mie yasa kika fito gida da gudu “? ” dama wannan mutumen ne yace zai bani abu kuma in banyi sauriba zai tafiyarsa shiyasa nayi gudu “

Zainab ta dafata tace ” to muje gida kar kuma wani yacewa momi ya ganemu waje bayan gid kinsan kuma fada zatayi ” dinah ta rike baki tace ” to ma inta ganmu mie zamu ce mata"?

Zara ” ai ta fita tun dazu “

Dinah ” yauwa dan Allah karku fada mata komai “

 duk suka daga mata kai sannan ta rika hannun zara suka nufi gida!

Tare suka shiga dakin ita da zara gefen gado ta aje mata ledar sannan ta fice 

Kusa da ledar dinah ta zauna ta tsur mata ido tana tunani, 

Sai kuma ta zabura da sauri ta tashi ta nufi bathroom!

Wanka tayi tare da alwala sannan ta fito,

Wadrop ta nufa ta fido da golden abayah mai hula tasa.

Ta dauko carpet ta shinfida tasa hijab, sannan ta kabbarta sallah azahar!

Bayan ta kare ta dawo gaban ledar ta zauna,

Har takai hannu zata taba sai kuma ta fasa.so uku tanayin haka sai ciron lips dinta take,

sannan naga ta tashi ta fita… dakin Zainab ta nufa tana kwance tana faman chatting,

A bakin kofa dinah ta tsaya tace ” dan Allah Zainab dan zo kiga wani abu ” 

Saida ta kashe datarta ta aje wayar sannan ta taso suka nufo dakin dinah tare,

Guri dinah ta nuna mata tace ” zauna a nan ” bayan ta zauna dinah ta zauna kusa da ita tace ” rike min rigata komai kikaji karki saki koda kinga na zama yar kankannuwa ” da dan mamaki Zainab tace ” ban ganeba ” murmushi karfin hali dinah tayi tace ” ba komai wasa nake miki nidai rike ni “!

Zainab ta kama rigar dinah ta rike iya karfinta,

Ayyatul-kursiyu dinah ta shiga karantawa sannan ta mika hannu jikinta na barri ta jayo ledar! Da karfi ta barke 

Zainab tace ” wai minene haka nifa ban gane mikiba ” dinah tace ” ke dan Allah sarkin tsoron banza kayane gasu nan dama kiranki nayi ki gani ” 

Zainab tasa hannu ta dauki ledar ta kara fito da kwani dake ciki mai hoton sarry, 

Ita dai dinah bata taba ba tace ” buda mugani ” tana budawa sukaga do sarry mai bakin Les blue color da katon ribbon shima d same color,

Zainab na warwarewa dinah taga daidai size dinta…

Da dan tsoro dinah tayi murmushi tana satar kallon Zainab tace ” amman gaskiya guy nan ya iya dinki ” Zainab dai batace komaiba ta mika hannu zata dauki wata yar takarda data fado,

Dinah tayi saurin riganta dauka ta matsa nesa da ita ta bude takarda tana krantawa

       

        ” OOOPS SRRY 

LOV U MY BABY ”                 #KISS

bata fuska tayi ta langwashe ta kardar cikin hannunta..,

Zainab ta nufo ta tana fadin ” minene bani in gani ” ta mayarda hannunta baya tace ” ba komai jeki dakinki ” kokuwa Zainab ta shigayi da ita dakar ta kwace takardar, ta koma bakin kofa tana karantawa,

Dagowa tayi ta kalli dinah tace ” may hakan ke nufi dinah kimin bayani “? 

Dinah tace ” inna fada miki bazaki fadaba ” Zainab tace ” wlh bazan fada ba kinji kuma na rantse”!


Hannuta dinah ta kamo suka zauna

 sannan ta kwashe komai ta fada mata

Mamaki Zainab tacika dashi tana girgixa kai dinah tace ” bari ma kiga in nuna miki takardar dazun ” ta tashi ta nufi gurin da tasan tabar takarda ta shiga dubawa bata gantaba ta hankada zanen gado nan ma bata nan ta nufi window ta leka ta dawo gurin drower nan ma haka ta huyo da sauri ta kalli Zainab tace ” wlh nan nabarta kuma kinga yanzu ta bata ” Zainab tayi murmushi tace ” mudai hankada gado d wadrop mugani ” 

Duk sukabi dakin suka har gitse basuga komaiba .

Zainab ta kalleta tace ” dinah anya ba aljani bane kuwa wata kila kinyi gamo ne “!

Dinah tace ” haka nace masa ammam yace mun shi ba aljani bane “

Zainab ” ai bazai fada mikiba kece dai zaki gane da kanki in kikaga alamu yanzu ya aikayi wannan takardar ta bata fadamin “?

Dinah tace ” wlh ban saniba kuma fa ko ranar daya daukoni ban fada masa gidan da zai ajeni kawai parking yayi kofar gidannan kuma bansan yadda akayi yasan inason wakokin India da kayansu ba “

Zainab tace ” kingani ko wlh gwanda ki kyale shi tun wuri kar wani abu yazo ya faru nidai ba ruwana ” 

Dinah zatayi magana sukaji muryar momi downstairs tana kiran Zainab 

Da sauri dinah ta dauki sarin ta jefar ta window ta rufe window sai haki take saida ta shiga bathroom tasha ruwa sannan ta kama hannun Zainab suka nufi downstairs 

Momi na ganinta ta saki far ah tace ” masha Allah hajiyata taji sauki ko “

Kusa da ita dinah ta zauna tayi fuskar shagwaba tace ” naji sauki momi ” 

Momi ta shafa kanta tana fadin ” to allah kara sauki yar baba ” duk suka washe da dariya 

nafisa dake sauko wa downstairs tace ” momi har kin dawo “

Tace ” aeh na dawo ga takalmin yan dubai nan na zabo muku cikin wannan nayi odo kowa ya dauki size dinshi ” ta karasa maganar tana zazzage ledar!!

Momi na karasa zazzagawa ledar takalmin! dinah ta hango kwalin wasu takalmin silver da sauri takai hannu zata dauka Zainab ta rigata dauka,

Fuska dinah ta hade

Please Login or Register in order to submit comment