Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ciki “?

Sukuku zulaiha tayi murya kamar wata marainiya tace ” yi hakuri dinah in na bata miki rai banyi dan ranki ya bace ba “

Lumshe ido dinah tayi tana hade yawu,

Ta juya ta fice, 

Bata bar gidan ba saida ta biya part din abbah ta gashe shi da momi ta kuma yi masa sallama sannan ta dauki hanyar skul,

4 saura dinah ta shigo gidan tana yi parking ta nufi parlour kwaran2 ,

Tana shigowa ta zube saman kujera kusa da zara 

Kallonta zara tayi tace ” wai yau kan kinsha rana sannu “

Dinah zatayi magana taga Zainab ta fito kitchen tana rawa tana dage2 

Wani kallo Dinah ta mata tace ” lafiyarki “?

Zainab ta karaso kusa da ita cike da far’ah tana girgixa kai tace ” dinah na samu aiki “,

Ihu dinah tayi ta tashi ta rungume ta tana fadin ” u Fulfills your dreams ” 

Zainab ta saketa tana tace ” yes sis yes i SOKOTO rima rediyo ” dinah ta dafa gefen kumatunta tace ” ohh congratulations sweet sis we are really proud of u “

Zainab ta hada kafardarta da kanta ta saka hannun dinah tsaka tana fadin ” tnks my twins sis ” 

Zara ta tabe baki tace ” a a Artery sis karewar twins ” 

Duk suka fashe da dariya har nafisa dake saukowa downstairs 

Kusa dasu ta tsaya ta kalli dinah tana dariya tace ” dinah yau naga kinyi kwaran ko duk karantun ne “?

Saida dinah ta saci kallon zara sannan tace ” tun tea da nasha da safe ban karacin komai ba shiyasa “

Zainab ta dan bata fuska tace ” wani abun ya sake faruwa ko “?

Da sauri dinah ta zare mata ido ta dan yi murmushi ” a a wane abu kuma “?

Dinah ta sake satar kallon zara ta rika hannun zainab tace ” let go inside kiji labarin makaranta “

Nafisa ta nufi corridor tana dariya tace ” an samo wata gulma kenan “

Murmurshi kawai dinah tayi taja hannun zainab suka nufi stairs, 

Zara ta isu da ido tana girgixa kai 

Dinah bata saketa ba saida suka shiga dakinta taj kofa ta rufe 
Ta zauna saman gado tana fadin ” Zainab ta karaso kusa da ita ta zauna tace ” mie ya faru wani abun ne ko “?

Da kafa dinah ta turo mata card din dazu 

Sannan ta tashi ta bude wardrobe ta dauko takardar ta mika mata 

Cike da tsoro zainab ta amsa ta shiga karantawa 

Tana karasa karanta wa tajo waje da ido ta kalli dinah da sauri tace ” da gaske ne dinah gaskiya be wannan “?

”  ga zahiri kina gani ni abun nan yana rikita mun kwakwalwa ” 

Zainab ta jefarda takarda tace ” waya fada mishi yaya zai dawo wannan karya ne ” dinah tace ” jikinna yana bani kamar gaskiya ne saidai zuciya ta taki ta gasgata abunda aka fada ” 

Zainab tace ” karki gasgata komai dinah wannan ba aljani bane tunda kikaga ya baki address dinshi saidai kuma ya akayi yasan yaya zai dawo “?

Dinah tace ” ba shine abun tambaya abun tambaya ya akayi yasan wani zai yawa yaya guba “?

Zainab tace ” abunda na fahimta dinah akwai wadda yake playing games with us kuma ko wanene yana tare da mu ” 

Dinah tace ” haka nake gani duk da jikina ya mutu dazu fa zulaiha haka kawai naji tayi dariya dana tambaye ta tace babu komai “

Zainab ta gyara zama tace ” kardai maganar yaya ta tabbata akan zulaiha dan gaskiya ni ina kwankwanton wannan lamari “?

Dinah tace ” nima haka nake gani but kinsan abun yi “?!!!

      

Sorry,

 In an kawo wuta zaku jini… 

Zainab ta girgixa jai tace ” a a saikin fada ” dinah tace ” musa mata ido da duk wani motsi nata inhar da ita ne to zamu gano “

Zainab ta daga mata kai ” hakane kan zamu gano koma wanene dan haka daga yau mubar ma wani motso ” dinah ta zauna kusa da ita ” ni har yanzu inajin soro zainab mie yasa yace za asawa yaya guba kuma ya kari ya sani “?

Zainab ta sauke ajiyar zuciya ” hmmm ai zai iya sanin komai tunda yana tare damu “

” nifa abun yana bani tsoro dan ina gudun kar ace wadda yake son kashe yaya ne yake. Mana haka ” Zainab tace ” ke dan Allah ki manta dan so yake mu tsorata kawai mu zama mahaukata babu wani guba da za samishi kawai yana son mu kasa sukuni ne dan haka kibar  wannan tunanin “

Kai kawai dinah ta daga mata ta dauki takarda da card dinta ta tura karkashin gado 

Washe gari  ma haka akayi sai kusan La’asar dinah ta shigo gida a balcony ta tararda momi tana shan kankana 

Kusa da ita ta zauna tana fadin ” momi huwa yau ake awaje ” momi tayi murmushi tace ” kinsan nan faruk yake zama duk lokacin da yake gida to yau ina miss dinshi ne kuma ina murna da kammala karatunsa da yayi gashi kuma ya samu good result, “

Dinah ta kwanta jikin momi tace ” haka ne nima naji dadi momi sosai wai wace rana zai dawo “

” ranar Saturday yace zai dawo yace tuwa yake so na masa da miyar ganye ” 

Dinah tayi murmushi ” Allah sarki yaya shekara nawa ai dole ya yayi marmarin tuwo ” momi tace ” ba tuwo ba ai har fura sai an masa Allah dai ya nuna mana dawowarsa “

Dinah ta tashi tana fadin ” amin momi nidai nayi ciki sai kin shigo “

Da dare dinah tana kwance tana tunane2 zara ta turo kofar dakin ta shigo ” Assalamu alaikum “

” Amin Wa alaikissalam ” dinah wai yaya malik yace ki hau Skype yanzu zakuyi magana ” dinah ta dan harareta “wani abu kika ce masa ne”?

Mayar mata tayi da harara ” to mie zance masa da bakin matsifar ki mie kikasan kinyi ” Mtswww taja tsaki ta fice

Koda 9:30 tayi dinah na Skype ita da malik sai fira suke tana kwasar dariya 

Kofi dake hannunsa naga ya aje cikin natsuwa ya kalleta fuskar sa babu alamar wasa yace ” bani hankalin ki sis inason muyi magana ” kai ta daga masa ” ina jinka yaya ” 

” dinah ina son muyi magana ne akan maganar da mukayi daku baya ta fitar da miji “

Yanayinta ya dan sauya ciki saran kiuzari tace ” okey wani abunne “?

” ae kinsan satin nan zan dawo kuma kinga shine satin da na deba muku ko “?

Ta daga mishi kai ” yauwa faruk na nan zuwa cikin satin da zanzo nasan ko yana zuwa zainab shi zata tsaida tunda daman son junansu suke kinga ke da nafisa kawai kuka rage shine nake son naji in kin samu wadda zaki tsaida din ke”?

” a a yaya ni vansan wadda zan tsada ba kuma kaga ni ce ma kadai na rage tunda nafisa ma nasan kai zata tsaida kaga………”

Da karfi malik yace ” wht!!!? Dinah ni zata tsaida kamar ya “?

” haba yaya kafa san nafisa tana sonka tun ba yauba kuma kasan bata sauraren kowa kuma fa har momi ta sani kawai dai batayi magana bane dan baku fito kuka nunawa junanku ba “

” no karki min wannan Fasarar ni babu wannan tsakani na da ita nida na aureta ba kara na aurekiba “

Dariya dinah tayi harda rufe baki tace “haba yaya ya za ayi hakw ta faru kana yayana ni basai ka wani ji kunya tava dan bazan hana kaba “

Murmurshi yayi yace ” yanzu sis in nace ina sonki bazaki so niba”?

” hakan bazai faruba yaya nifa dakai yaya da kanwa ne kuma matar ka yaya tace kaga ko a mafarki ai bazai yiwu ba “

Hade fuska yayi yace ” haushe matata ta zama yayarki “?

” kafi kowa sani yaya haka ya dade da waka dan Allah yaya mubar maganar nan kaji plz”

Kai kawai ya daga mata ya rufe computer sa.

Dafe kanta dinah tayi ta lumshe ido ta dade a haka

 sannan ta tashi ta nufi dakin nafisa koda ta shiga ta tararda ita kwance tana waya kusa da ita ta zauna ta shiga duba wani English novel dake gabanta 

Bayan ta kare wayar ta juyo ta kalli dinah tace ” baki kwanta ba “?

“ae nafisa ni gaskiya abun nan ya dame ni ” nafisa ta tashi zaune ” na mie ba “? 

Cikin fusakar damuwa dinah tace ” maganar yaya mana ta aure “

” nima abunda yake damuna kenan but ba mafita ai tunda yace kamin ya dawo kuma mun yiga muncewa momi zamuyi “

Dinah tace ” to ke yanzu wa zaki fitar zainab dai nasan ya Faruk ne nata “?

Ajiyar zuciya Nafisa ta sauke tace ” to ni ina nasani ni banda wadda zan fitar “

” to ya zakiyi kindai san yaya bazai kalekiba bare momi “?

” ni momi zance ta fitar min mana ba shikenan ba nidai na hutaba “

Dinah tace ” to in ta fitar miki da wadda bakya so fa “?

” hmm zan ma so kidai Allah ya kaimu kawai koma wanene zanso”

Murmurshi dinah tayi ” hmm dan kinsan yaya malik zata fitar miki ko ” dariya nafisa tayi tace 

“nidai babu ruwan duk wadda ta fitar zanso ni jin kikayi nace shi banda abunki “

Dinah tace ” ba wani nan dan dai kinsan shi zata fitar miki ne kawai tunda tasan kina sonsa” 

” ohh yau naji dinah dama dan ki cimin fuska kikaxo dan Allah tashi ki fice ni bachi ma nakeji “

Dinah tayi murmushi tace ” dan Allah nafisa mubar zancen wasa kinason yaya saosai “?

” mie yasa kika tambaya”?

“Kawai ina son sanine ” nafisa ta hade fuska ” to ban saniba tashi ki fita dan Allah kinga karatu nake “

Ta karasa maganar tana turata 

Dinah ta tashi tana fadin ” basai kin koreni ba zan fita kuma nima kar ki tambaye “

Murmurshi tayi ” naji jeki”

Dinah ta juya ta fice tana murmushi 

Dinah tana fita ta dawo dakinta saman gado ta zauna fuskarta cike da damuwa ta shiga magana da kanta ” ni gaskiya bazan iyaba ni gaskiya saidai kaga laifina ya za aiyi nayiwa nafisa haka da anty murja kuma momi na kalleta da wane fuskar nifa ban taba sonka son soyayya ba ya za aiyi muyi haka ni gaskiya banzan iyaba…………” haka tayi ta maganganu har bachi ya dauketa 

        WANENE MALIK???

Alhaji Muhammad salisu tsohon alkali ne  kuma kanene ga Alhaji umar salisu tanko wato mahifin dinah, su uku mahaifansu suka haifa mahaifiyar nafisa ce ta farko sannan mahaifin dinah sai kuma mahaifin malik wadda shine auta mahaifin dinah mutun ne mai son zumunta da yan uwa haka yasa ya dauko zainab da nafisa tun suna kanana ya rikasu har suka girma a kaduna mahaifin malik yayi aiki shiyasa da yayi ritaya  ya tare a kaduna ganin haka yasa mahifin dinah ya sake dauko abul-khair ya dawo dashi gurin shi,

Barrister malik Muhammad salisu shine kikanke sunansa matarsa daya da yaransa biu mas’ud da khadija, 

Anty murja kamar yadda dinah take kiranta Yar kaduna ce sunyi aure da malik tun yana karatunsa a England,

Yana karewa ya samu aiki a abuja federal high court, 

Hakan yasa ya koma abuja ya tare tare da matarsa murja sai dai duk ya samu hutu to SOKOTO yake yinshi saboda dinah,

Duk abunda take so yana mata duk kuma abunda zai bata mata rai baya sonshi,

Shiyasa dinah koda yaushe yayanta dai ko minene shine shima kuma komai ya samo na sis dinshi

Hakan yasa suka shaqu sosai da dinah har murja matarsa son dinah take sosai dan in kaga abunda take mata sai ka rantse ciki daya suka fito 

duk da yake halinta ne na son jama ah da far ah da iya zama da mutane, 

Duk irin rawar kan da malik yake yi inga dinah ko in suna tare bai taba sa tayi kishinta ba,

Hakan yasa Dinah ta tasake jiki da ita sosai ta ta kuma dauke ta tamkar yayarta.

Ba itaba ko momi tana jindadin yadda take yiwa dinah dan abunda take mata ko ciki daya suka fito iyaka kenan, 

Shiyasa ko kadan dinah bata son bachin ran murja ko kadan 

Hankalinta yama fi kwanta in akace ran malik ne ya bace bana murja ba,

             WANNAN KENAN

          Back to labari 

Washe gari 8:44am momi ta shigo dakin dinah 

Kwance ta tararda da ita ruf da ciki tana wasa da k'afafunta 

Tana ganin momi ta tashi zaune tana murmushi ” morning mom “

Kusa da ita momi ta zauna tana fadin ” morning yau banga kin fito kinyi break ba yan uwanki ma duk sun wuce ke kadai kika rage “

” ae momi yau sai 10 zan shiga makaranta shiyasa ” momi ta taba jikinta ” lafiyarki dai kalau ko “?

Kalau momi kawai dai ina tunani ne “

Momi tayi fuskar rashin fahimta tace ” tunani kuma mai akayi “

“kawai ina kunani ne wai yanzu in nafisa tace ki fitar mata da miji wa zaki fitar mata “? ” cewa tayi na fitar mata da mijin ne ko mie nifa ban gane mikiba “

Dinah ta gyara zamanta tace ” a a haka dai nake tunani zatace tunda kinsan ba sauraren kowa take ba kuma yaya da yazo shi ba ruwanshi da haka”

Momi tace ” to bari har tace ” 

Fuskar shagwaba dinah tayi ” haba momi dan Allah ki fada min mana “

Momi ta kalleta ” to saboda mie “?

” momi inason inji wazaki fitar mana dan gani nake kamar yaya malik “?

” shine ma to wazan fitar mata wadda ya wuce shi kuma itama in tace na fitar mata ai kinsan shi take nufi sbd baza iya fitowa fili tace tana sonshiba “

Dinah tace “but momi baki ganin anty murja zataga ba a mata adalci ba”?

” mie abun rashin adalci a ciki? Inda kamar ace yarda na haifa da cikina ce ko kuma ke da kuka shaku da ita ne to zata ga an mata rashin adalci 

Amman nafisa ai baza tace wani abuba tun da yar uwar babanku ne banawa bale tace nina hada dan wani abun kuma nasan bazata rasa sanin nafisa tana son malik ba ko malik yana son taba dan haka ni banga rashin adalci cikiba “

” hakane momi kinyi gaskiya barina na tashi nayi wanka “

Momi ta kalli window ta tace ” lalai kan ga hadari nan ya rufe gari kuma dinah na rabaki da bude window da in zaki kwanta bakyaji ko “?

Tashi tayi tana fadin ” a a momi da safen nan na bude ta ai ni yanzu ko yar kusurwa bana bari bari wannan window da mutun zai iya haurowa “

Momi ta tashi ta nufi kofar fita tana fadin ” lalai kan wannan window ai sai a hankali in kika kare ki sameni downstairs muyi break dan nima ban karya ba ” kai ta daga mata tana kokarin shiga bathroom tace ” owk my sweet mom “

Murmurshi momi tayi ta fice

Da wuri yau Dinah ta dawo gida kasan cewar jumma ah ce kuma momi ta fada mata ta dawo da wuri dan akwai aiki,

Tana shigowa cikin gidan ta wuce dakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfa light green ta nufo downstairs 

Parlour ta tararda momi da zainab da wani inyamuri

Suna duba hotunanan cakes 

Kusa da ita dinah ta zauna ta shiga duba hotunanan itama tana fadin ” momi wanne kika zaba “?

Momi ta mika mata pic din wani cake tace “wannan na zaba masa ” 

Dinah tayi fusakar shagwaba “haba momi wannan da akabar yayi gaskiya bai sonshi ” 

Zainab ta tamata “ae gaskiya bai yi kyau ba ga masu kyau nan “

Kwasar potunan momi tayi ta zubasu jikin dinah ” gasu nan in kuka zaba ku bashi ni inada abunyi “

Tana kaiwai nan ta tashi ta nufi stairs 

Sunyi kusan 30 minutes suna zabe2 sannan suka fitar da pic din wani mai kyau suka mikawa masa,

Washe gari suna kare break suka fara aiki babu kama hannun yaro 

Ranar dinah tafi kowa tasha wahala dan kitchen suka tare da momi komai tare suke yi su kuma sauran ta raba musu ayukan da zasuyi ta turasu BQ 

Haka suka wuni suna aiki sai biyar saura suka kammala komai kowa ya nufi dakisa danyi wanka,

Shiri sukayi na musamman cikin atamfa red and yellow ko wannnensu kwanin sha awa dan atamfa kamar dasu akayi, 

Duk dasu suka dawo parlor suka zauna.
[11/16, 10:19 AM] Khadeeja Candy: Suka cikin cin cin2 da drinks sukaji anyi horn da gudu dinah ta tashi ta nufi kofar fita 

Wasu samari ne su hudu naga sun fito a motar

Dinah na ganin su ta rufe ido tana dariya dayan dake kokarin fitowa a driver seat ya kalleta yana murmushi yace ” ashe kina jin kunya to mie ya fito dake “?

Bude idon tayi ta kalleshi ” daman na dauka yayana ne ai “

Daya da ya fito a front seat ya kalleta yace ” lalai ma wannan yarinyar kajin min ita bashir watou muda ba yayanki ba bazaki tarbe muba ko”? 

Kai ta daga mishi tana murmushi ta juya zata shige parlor

 da sauri wani daga cikin samarin ya mika hannun ya riko hannunta ya fusgota da karfi ta juyo

Wani shu’unmin kallo ya watsa mata yace ” kina son yayanki ko”?

Kai ta daga mishi tana ya mutsar fuska

” ae mana ina sonshi”.

Murmurshi naga yayi ya matse mata hannu saida tayi kara sannan ya saketa, 

Na kusa dashi naga ya kalleshi ” haba siraj miye haka “? 

Wani kallo naga yama siraj din yace ” nothing ” ya kunna kai cikin gidan 

Wadda naji ankira da bashir dazu ya matso kusa da ita yace ” siraj mugune srry plz yanzu zakiga yayanki in the next 30-40 minutes owk ” 

Kai ta daga shi tana murza hannun dayan ya kalleta yana murmushi yace ” bashir nifa naga ruwan da zasu min wanka “

Duk suka fashe da dariya suka nufi parlor 



Basu dade da shigowa ba wasu kawayen hajiya da Neighbors da wasu abokanin faruk suka shigo, 

Biyar saura kwata motar faruk ta kunno kai cikin gidan malik ne ke driving faruk kuma yana front seat sauran abokaninshi 3 suna baya

Tun kamin malik yayi parking su zara da dinah da Zainab suka fito 

yana fitowa suka rumgume shi suna ihu abokaninshi suka shiga mishi dariya malik ma murmushi yayi yana Girgirza kai yace ” Allah ya sauwake “

 suka nufi parlour shida abokan faruk suna dariya ,

Suna kokarin shiga momi ta fito sanye da wani material maikyau maroon color fuskarta dauke da murmushi ta kalli malik “sannunku da zuwa” 

“yauwa momi sannu” abokanin faruk suka shiga gaisheta a gajarce ta amsa ta nufi gurin faruk 

Yana ganinta ya saki su dinah ya yo gurinta ya rumgume ta yana fadin “ohhh my dear mother i miss a lot “

” miss u too son alhamdulillah na jidadi da Allah ya nuna min wannan ranar da rayuwata da lafiyata Allah ya maka albarka faruk” 

Dagowa yayi ya kalleta “amin my mom Allah ya bar mana ke”

Matsowa dinah tayi ta kama hannunshi tana daga mishi gira” yes yes bro’s congratulations “

duk suka tinsire da dariya momi ta rika hannunshi suka nufi parlour 

Suna shiga wani ihun ya sake tashi aka shiga rungumashi ana mishi sannu da zuwa daker ya samu ya wuce dakinsa

Yana shiga ya fada bathroom ya sakarwa kanshi shower tare da alwala ya fito,

 bayan ya shirya cikin kananan kaya ya shiga sallar magariba,

bayan ya kare ya nufo downstairs 


Ciye2 ake tayi ana fira kowa ka gani fuskarsa dauke da fa ah

Dinah na zaune kusa da faruk duk abunda zaici ita take mika masa sai rabon ido take kana ganinta kasan hankali ba aguri daya yake ba,. 

So uku faruk na mara magana bata jiba saida ya tabo ta sannan ta juyo da sauri “naam yaya “? 

Fuskarsa dauke da murmushi yace ” drinks na keso “

kai kawai ta daga mishi ta tashi taje ta dauko tare da cup ta zuba masa ta bashi

A hankali naga fuskar faruk na chanjawa kamar wadda kesha abu mai daci

Sai firara karfin hali yakeyi da abokaninsa 

Can kuma naga ya tashi yana cizon lips ya nufi stairs 

Daya daga cikin abokaninsa ya kalleshi yace “ya dai faruk”? 

Juyowa yayi fuskarsa dauke da murmushi yace ” ba komai ina zuwa ” bai jira mie zaice ba ya juya 

Yana dora kafarsa stairs naga ya rike karfen da karfi yana wani irin numfashinsa kamar wdda zai a mayarda wani abu

Da sauri sukayo kansa suna tambayar lafiya faduwa yayi zaune yana ya mutsar fuska yace” cikina ne yake ciwo” 

“momi momi fito yi sauri kizo ” cikin tashin hankali dinah take kiran momi 

Da dan gudu momi ta fito jin irin kiran da dinah take mata tana ganin an zagaye faruk ta shiga salati tana tambayar ba asi 

Kwan towa faruk yayi jikinta yana fadin ” cikina ne momi ji nake kamar ana yan kamin hanji plz ki taimaka min da madara”


Ciye2 ake tayi ana fira kowa ka gani fuskarsa dauke da fa ah

Dinah na zaune kusa da faruk duk abunda zaici ita take mika masa sai rabon ido take kana ganinta kasan hankali ba aguri daya yake ba,. 

So uku faruk na mara magana bata jiba saida ya tabo ta sannan ta juyo da sauri “naam yaya “? 

Fuskarsa dauke da murmushi yace ” drinks na keso “

kai kawai ta daga mishi ta tashi taje ta dauko tare da cup ta zuba masa ta bashi

A hankali naga fuskar faruk na chanjawa kamar wadda kesha abu mai daci

Sai firara karfin hali yakeyi da abokaninsa 

Can kuma naga ya tashi yana cizon lips ya nufi stairs 

Daya daga cikin abokaninsa ya kalleshi yace “ya dai faruk”? 

Juyowa yayi fuskarsa dauke da murmushi yace ” ba komai ina zuwa ” bai jira mie zaice ba ya juya 

Yana dora kafarsa stairs naga ya rike karfen da karfi yana wani irin numfashinsa kamar wdda zai a mayarda wani abu

Da sauri sukayo kansa suna tambayar lafiya faduwa yayi zaune yana ya mutsar fuska yace” cikina ne yake ciwo” 

“momi momi fito yi sauri kizo ” cikin tashin hankali dinah take kiran momi 

Da dan gudu momi ta fito jin irin kiran da dinah take mata tana ganin an zagaye faruk ta shiga salati tana tambayar ba asi 

Kwan towa faruk yayi jikinta yana ya mutsar fuska yace ” cikina ne momi ji nake kamar ana yan kamin hanji plz ki taimaka min da madara”

Riko shi malik yayi tare da fadin “no asibiti xamuje” ya karasa maganar yana kokarin ta dashi bashir ya kama masa suka nufi kofar fita!!!



Usman danfodiyo University teaching hospital, (uduth)

Suka kaishi suna isa aka wuce dashi emergency

Dan har kunfa ya fara fita bakinshi,

Koda su momi suka iso sun tararda malik da bashir da siraj tsaye bakin kofar,

Tun kamin ta karso malik yadan saki fuska dan yaga hankalinta a tashe yake 

Muryar ta na rawa ta shiga tambayarsa “ina faruk yake mie ya sameshi”?

Rikata. Malik yayi ya zaunar saman wata kujera dake gefen dakin yace ” ki kwantar da hankalinki momi dan dr yacd ba wata matsala bace kar mu tashi hankalinmu” 

Kai kawai ta daga mishi badan ta gansu ba,

Sai kusan 11 dr ya fito dakin su momi na ganinshi suka tashi tsaye cike da natsuwa ya kallesu yace “ina mahaifinsa ko mahifiya” ?

Momi na kokarin hade yawu tace”gani nice mahaifiyarsa ya mutu ne”?

Kai ya girgiza mata yana shirin tafiya yace “ku sameni office” 

Cike da sanyin jiki momi da malik suka rufa masa baya

Kabar dinah da bashir dan siraj ya dade da tafiyarsa,

Sunyi awa daya dakin sannan suka fito cike da damuwa musamman fusakar malik dan ita momi sharar kwanla kawai take, 

Da sauri dinah ta nufi gurinsu “momi lafiya”?

Momi bata ce da ita komai ba ta nufi kujera ta zauna kamar marara lafiya, 

Malik ne ya dafata yace “yayanki yana nan da ransa saidai dr yace mana yaci guba amman ki kwantarda hankalinki ya samu sauki”

” subhanallahi inna’lillahi wa’inna ilaihi’raji ” 

shine abunda dinah ta furta ta dafe kanta da sauri malik ya zaunar da ita kusa da momi, 

Ya shiga kwantar mata da hankali

Washe gari

A hankali faruk ya fara motsi har ya bude idonsa, 

Silin ya fara kallo sannan ya sauke idonsa kan mahaifiyarsa suna hada ido ya sakar mata murmushi da sauri ta taso ta shafa kansa “son mie ke damunka yanzu ina ke maka ciyo kanajin wani abu cikin ya daina ciyo ko har yanzu”?

Tamvayoyi momi ta shiga masa har yasa wace zai amsa mata malik yayi murmushi yace “momi ya fa samu sauki kuma gashi kina gani” 

cikin fuskar damuwa momi tace ” Alhamdulillah bari na kira dr dan yace in ka tashi a kirashi” ta karasa maganar tana kokrin tashi

Da katar da ita malik yayi ” momi

Please Login or Register in order to submit comment