Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta mika mata hannu “karkimin wata jayayyah bani ” Zainab ta watsa mata harara ” ai na rigaki dauka dan haka sa plz ki rungume srry ” dinah ta kalli momi tace ” momi ce tabani tafa san ni nake daukar irinsu ” momi tace ” waya riga dauka “? Zara tace ” Zainab ta riga kuma ita dinah kullum in aka kawo Talkami kalar take take dauka ba gaskiya ta barma Zainab ” momi ta kalleta tace ” to kibar mata tunda ta rigaki dauka kuma kinada irinsu dayawa gawasu nan ki dauka ” dinah ta bata fuska kamar tayi kuka tace ” ni su kawai sukamin su nakeso ” Zainab tace ” bazan ko baki suba saidai ki mutu ” momi ta dafe kanta tace ” waiku bakuda aiki sai fada kamar kananan yara “! 

Zara tace ” ai duk dinah ce ke jan magana ” dinah ta watsa mata harara cikin tsara tace ” wlh zara zanyi ball dake dake ake magana dazaki sawa mutane baki ni warinki ce ” ta kalli momi ” wlh momi ki mata magana kona daketa “!

Momi ta tashi tana fadin ” chan ku karata ni bazan iya da rigimarku ba ” ta kalli nafisa ” in kuka kare nafisa ki kawo min sauran daki ” tana kaiwa nan ta nufi stairs  Zainab sai gwalo take yiwa dinah ta shiga gwada takalmin! 

Wani kwalin takalmin dinah ta dauka ta jefi Zainab dashi tayi kwafa,,

sannan ta tashi ta nufi dakinta!


Tana shiga ta fada saman bed tana jan tsaki ta dauki wayarta ta shiga game tana zagin zainab,

Tana haka mai aikinsu zulaiha ta shigo tace ” dinah wai momi tace kije kici abinci su sunci nasu tun dazu ” dinah kai ta daga mata batare da ta kalleta ba zulaiha ta juya ta bar dakin,

Saida tayi minti ashiri da fita sannan dinah ta tashi tana game ta nufi downstairs,

Babu kowa parlor sai zulaiha dake daning side,

Saman 3 seater dinah ta zauna stll hankalinta yna kan game!

Saida zulaiha tace mata ” dinah gaba abincin na zuba miki kuma fa na amta in gaya miki momi tace karki yarda ta fito bakici abinci ba “! 

Da sauri dinah ta tashi ta nufi daning dan tasan halin momi zulaiha taja mata kujera ta zauna ta mika mata wayar sannan ta fara cin abincin,!

Tana cikin abincin wayarta dake hannun zulaiha tayi kara alamar sako da sauri ta dinah ta mika mata hannu ” bani an turo min sako ” da sauri zulaiha ta mika mata!

Dinah na kokarin aika loma abakinta naji tace  ” wake da wannan number kuma “? Saida ta sha ruwa sannan ta buda sakon ta shiga karantawa,!

         ” HI LOV 

KARKI DAMU TAKALMIN KI ZASU DAWO GARE KUMA DAN ALLAH BABY NA KARDA KIJI TSORO KICI GABA DA CIN ABINCIN KI,! 

                  #KISS “

ihu dinah tayi ta saki wayar tana haki ta kalli zulaiha ciki da tsoro!

Da sauri zulaiha ta dafata tana fadin ” lafiya dinah miya faru “? Dinah bata tsaya bata amsaba ta nufi stairs da gudu,

Tana kaiwa kofar dakin momi sukayi karo da Zainab data fito dakinta da gudu,

Duk suka zube saman tile suna maida numfashi,

Dinah ta hade yawu tace ” Zainab yanzu aka aikomin da sako wai karna damu Talkami nan nawane kuma wai kar naji kicin abincina kuma abinci fa nake ci lokaci da aka aiko sakon ” zainab tace ” mun shiga uku wlh nima yanzu aka aikomin da sako wai takalmin nan ba nawa bane nakine kuma lokaci ina chatting akace wai na aje chatting din nan nazo na fada miki “!

Dinah tayi waje da ido tace ” to ya akayi yasan ni ina cin abinci ke kina chatting “? Zainab tace ” bana fada mikiba wlh aljani ne “! 

Dinah zatayi magana sukaji muryar zulaiha ta nufo stairs tana fadin ” dinah wayar ki na ringing an kiraki ” 

       Da gudu ita da Zainab suka fada dakin momi suna ihu,

Da sauri momi ta kallesu tace ” lafiya miye haka “? Zainab tace ” wlh momi yanxu ne aka…………!shiru tayi sakamakon buge mata baki da dinah tayi,

Momi ta watsama dinah harara tace ” sbd mie zaki buge mata baki “? Dinah tayi kasa da idonta, momi ta kalli Zainab ” ina jinki cigaba “!

Soshe2 Zainab ta shigayi sannan tace ” dama zuwa nayi in fada miki na barwa dinah takalmin na yafe mata “! Da sauri Dinah ta kalleta tace ” a a wlh ni banaso bazan karba ba “! Kafin momi tace wani abu sukaji sallamar zulaiha, 

Momi ta amsa tare da cewa shigo zulaiha cikin ladabi ta shigo tace ” daman wayar dinah ce keta ringing naje dakinta ban gantaba shine nace bari na kawo miki “! Momi ta kalli dinah tace ” karbi wayarki ” dinah kamar tayi kuka tace ” tohm momi ” 

ta mika hannu ta karba aka kara kira!
[11/16, 10:15 AM] Khadeeja Candy: Janye hannunta Dinah tayi da sauri taja da baya, momi tace ” ki karba mana karta katse “, jikinta na bari tace” ni gaskiya momi saidai ke ki karbi wayar “! Momi batace komaiba ganin zulaiha na dakin karsu tsaya jayayya ta mika hannu ta karba,

Zulaiha ta juya tabar dakin daman momi ita take jita ta juyo ta kalli dinah fuska a hade tace ” ki cigaba dayi min irin haka karki fasa in kina ganin abun kwaraine ” ta kalli Zainab ” ke kuma kici gaba da biye mata kuna min rainin hankali ” Zainab ta dan risina ” srry momi ” momi taja tsaki ta cigaba da dannar laptop dinta, Zainab ta sussuda ta fice,

A hankali dinah ta zauna kusa da momi ta kamo hannunta zatayi ” momi I’m really sorry banyi haka dan na bata miki raiba kawai inajin tsoro ne shiyasa “, momi dai bata cemata komaiba ta cigaba da abunda yake da dayan hannunta,! Ganin haka yasa Dinah ta kwantarda da kanta a kafadar momi tace ” I’m srry plz momi ” nan ma momi kyaleta tayi dinah ta shiga kukan shagwaba ” momi say somting plz ” sai a lokacin momi ta kalleta tace ” gt ot ” dinah ta bata fuska ” momi plx ” momi tace ” wuce dakinki “! Tashi tayi kamar munafuka ta fice,

garden ta nufa tana samu bushi yar lemo ta jingina , ta tsurawa cages din parrots idon tana kunburo fuska kamar kwado,

Tayi 1 hour a garden din.sai tunane2 take tana haka zara ta shigo garden din tace ” dinah jidda ta kirani tace na fada miki wai tayi ta kiranki baki dauka ba tace wai bukin da zaku gobene karfe 3 dan haka ki shirya zata zo ta dauke ki “, dinah tace ” laaah Ashe ma itace taketa kirana banko tsaya na dubaba kai nikan akwaini da wauta mtssss ” nafisa ta kalleta ” to miya hanaki ki duba ” harararta tayi tace ” ina ruwanki dake nake magana “?

Dariya nafisa tayi ” tohm Allah ya sauwake ” dinah bata sake cewa komaiba ta shige dakinta…

Da dare dinah kasa kwana tayi dakinta sai tsoro ta keji gashi babu damar zuwa dakin momi tunda sunyi fada haka yasa dole ta daure ta kwana daki daya da zara,

Washe gari dinah sai 8:am ta fito dakin bayan sun kare fada da zara,

Ta nufo dakinta tana tura kofar dakin wata rakarda yellow ta fado,! Baya2 tayi tana rabon ido, sai kuma naga ta matso ta dauki takarda jikinta na rawa ta bude,


          ”     MNG LOV

HOP KINYI BACHI MAI KYAU JIYA DAN NASAN TSORONE YA HANAKI KWANA DAKINKI

            NA AJE MIKI KUDI BAYAN PILLOW KIN DAN KISAMU NA KARI AKAN BUKIN DA ZAKIJE YAU PLX KI GAIDAMIN DA KAWARKI JIDDAH “

                          #KISS


Tana kare karanta takarda ta nufi gurin pillow tana dagawa daga yan 500 sabbi hul guda 4,,!

Wani irin ihu ta saki ta nufi dakin momi da gudu ,

Daga bakin kofa ta tsaya tana tana matse kukan dake son fito mata,

na ganinta ta taso da sauri ta dafa ta ” lafiya dinah miya faru “? Rungume momi dinah tayi kukanta ya fito fili babu kankwau tawa..

Dagota momi tayi ta Karasa shigowa da ita cikin dakin ta

Zaunarda ita saman bed dinta, tace “fadin dinah wani ne ya mutu fadamin mana “?

Kai kawai Dinah ta girgixa alamar a a dan kukan kawai take bata iya magana,

Hankalin Momi ya tashi sosai dan tasan duk abunda zai sa dinah kuka haka ba karami bane,

Idonta suka ciki da kwala tace ” dinah ki fada ko mahaifinku ne wani abun ya sameshi “?         Sai a lokacin dinah tayi kokarin tsayarda kukanta tace ” a a momi kawai nayi munmunan mafarki ne kuma inajin tsoro shiyasa “!

momi ta kwanto da ita jikinta tace ” mafarki ba gaskiya bane dinah dan haka kibar irin haka dan kinyi mafarki kinji annabawa kawai suke mafarki ya zama gaskiya “,

Momi ta dagota ta riko fuskarta tace ” in mutun yayi irin wannan rokon Allah ake kar abunya tabbata kuma wani abunne yake damun kiroki Allah ya yaye miki koya bayyana miki”

   VOTE
[11/16, 10:15 AM] Khadeeja Candy: Kai dinah ta daga mata momi tace ” amman ba ason kuka kinji kuka baida kyau ”

Momi ta kara riko fuskarta da kyau tace ” kuma in wani abu na damunki u cn fel free n tak 2 ur momi rght “?

Dinah tace ” yes momi  ” ,       momi tace ” gud hau gado ki kwanta kamin akare hada muku  break “,

kai kawai Dinah ta daga ta koma tsakiyar gadon momi ta kwanta tare da jan bargo ta rufa,

Momi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shiga bathroom,

 

Karfe 3:25 jidda ta shigo gidan,

saida ta fara shiga dakin momi ta gaisheta sannan ta wuce dakin dinah,

Tan tsaye jikin window dakinta tana rike curtains,

A hankali jidda ta dafata ” bestyyy “! Dinah ta juyo fuskarta dauke da murmushi ta rungume ta tace ” besty har kin iso “!

Jidda ta saketa tace ” aeh kin gama 4 ta kusa  muje kawai kar muyi African time “, ta karasa maganar tana duba agogon hannunta!

   Dinah tace ” owk bari na chanja kaya dan wannan tun dazu nasasu “!

Tana kaiwa nan ta nufi wadrope ta dauko wata atamfa brown mai ratsin fari, da farin gyale ta dora saman bed,

Jidda tace ” bari naje gurinsu nafisa kamin ki shirya ” kai kawai Dinah ta daga mata,

Ta tashi ta fice,

Dinah ta shiga saka kayan tana karewa ta shafa power da Lips gloss ta daura dan kwalinta ta dora gyalen saman kafadarta tana cikin sa takalmi jidda ta shigo,

Wani kallo ta mata tace ” gaskiya bestyy mijinki ya huta dube ki ba wani makeup kikayiba amman ki kin fito Mrs world duk kayan da kikasa sai sun miki kyau “,

Dariya dinah tayi tace ” nidai muje inkin tashi “!

Suka fito suna dariya ,                saida suka shiga dakin momi suka mata sallama sannan suka fice

Koda suka isa 4 ta dan gota, jidda nayin parking suka nufi wani cikin hotel din,

Suna tafe suna hira har suka karaso, wani katon hall ne da shikura hotel suka ware dan masu dina ko kamu,

Gurin ya kawato sosai sai kida ke tashi, tun daga kofar hall din jidda ta fara rawa har suka karasa gurin da amarya da ango suke,

        Sukayi magana da ita suka dauki photo sannan jidda ta riko hannun dinah suka samu guri suka zauna,

Kida ke tashi kalakala,

     Jidda sai rawa take da kai, chan kuma taji bazata iya jureba taja hannun dinah suka shiga tsakiyar hall din inda ake rawa,

Da sauri dinah ta fito tana dariya ta koma chan gefe inda babu mutane sosai ta tsaya tana kallon jidda take faman rawa, murmushi kawai take tana girgixa kai,

Tana haka kanshi wani turare mai taushi ya daki hancinta, a hankali taji ana mata rada,

     ” hmm 2 day dis lady lukin frsh prtty n cute juz lik  a queen ”

     Da sauri ta yunkura zata juyo aka rufe mata ido yana murmushi yace ” no no u hav 2 ges ”

Kyalkyace wa tayi da dariya tace ” yaya malik ne ”

dariya yayi ya janye hannunshi, ta juyo tana dariya tace ” I’m genius ” lakatar mata hacci yayi yana murmushi ” prtty sis ykk “? Tace ” yaya yaushe kazo “? ” yau din nan 12 na shigo sokoto kuma karfe 7 na safen goben zan wuce “! ” to yaya ya akayi kaxon gurin nan “? ” ke nabiyo “! Bata fuska tayi ” nidai dan Allah yaya fada min gaskiya karka kara tsorata ni ” gira ya daga mata yace ” wasa nake miki angon ne abokina ” tabe baki tayi ” shine yaya ko ka biyo gidanmu ko kirana ma kabar yin “!

Yace ” hutu ne banda sis wani case ne muke marar dadi but dis Monday zamu kare kuma abbah yace zaizo ranar Friday tare zamu zo “!

Tace ” to miyasa yanzu kazo “? ” ango ne yace in ban zoba fada zamuyi shiyasa kawai but plz sis karki fadawa kowa kin ganin kiji ” ” to yaya kayi kyau fa ” murmushi yayi yace ” tnc ” tace ” i miss u ” to xo muje musha ice cream nima nayi miss din shan ice cream tare dake “,

Dariya tayi tace ” kana son na bata kayana kenan ” shima dariyar yayi ” to ai nima kinga sabon kaya nasa basai mu bata su tare ba ” tace ” tohm Bari na kira jidda sai muje ” ya riko hannunta ” no plz kinsan zata iya fa tace ta ganin, ” ok to bari nayi mata sallama sai muje ” ” ok karki dade ”

  Kai kawai ta daga masa ta nufi gurin jidda,

        bata dade ba ta dawo ta rika hannunsa suka fice,

Suna shiga mota yasa wakar p-square_game is over,

hannun dinah ta kai ta chanja tasa wakar banky_w_yes_or_no murmushi yayi yace ” banson ta ” ya dannan prev wakar dazu ta dawo

Dinah ta sake danna next ya sake danna prev haka sukayi ta har saida ya gaji yace ” owk yanzu bari in rufe ido in dauko wani plate insa kinga ai ban ganiba ko “? ” dariya tayi tace ” ban yarda ba saidai ni in dauko ” hannu ya daga mata yace ” fine dauko ” hannun takai ta dauko wani plate fari baida rubutun komai tasa,

    Wakar Lionel_Richie ce i_call_it_love

   Duk sukayi dariya suka shiga koyon mawakin suna bin wakar,

Dinah sai rawar kai take kamar wata karamar yarinya har suka kawo gurin traffic

         Daidai nan massage ya shigo wayar dinah da dan tsoro ta buda,


        ” HI LOV

KICE YA AJEKI GIDA YANZU SRRY NA KATSE MIKI JINDADI DAN NASAN KINA JINDADI IN KINA TARE DASHI BUT I FEEL VERY SAD IN KINA TARE DA WANI BANIBA IN KUMA KIKA KI TO DUK ABUNDA YA FARU DASHI DON’T BLAME ANYBODY ”

                          #KISS


Mugun tashi  hankalinta yayi ta rasa yadda zatayi yanayinta duk ya chanja,

Malik na lure da ita saidai baice mata komaiba saida motoci dake gaban su suka wuce ya cigaba da driving ba tare daya kalleta ba yace ” sis miya faru naga yanayinki ya chanja “? Murmushi tayi tace ” ba komai yi sauri dai muje inda zamu ” baice mata komaiba yaci gaba da driving dinsa ,

      Basuyi nisa sosaiba motarsu ta fara rawa tana kokarin kwacema t-t da sauri dinah ta kalli malik tace ” yaya miya faru “?

Malik nata kokarin saita motar amman abun yaci tura sai gaba sukeyi sunayin baya nan da nan motar ta fara hayaki,

Dinah ta fashe da kuka tace ” yaya sauke ni plz yi parking “

Dinah na rufe baki motar ta kara gudu. motoci sai basu hanya suke ganin irin gudun da motar take mutane sai kallonsu suke,

Wani mugun bugu motarsu ta kaiwa wata mota dake gabansu.! Ihu dinah tayi ta fashe da kuka ta Kalli malik ” dan girman annabi ka tsayarda motar nan kar mu mutu ko mu kashe wasu plz yaya ” cikin tashin hankali malik yace ” bazan iya ba motar ita take controlling din kanta ban san miyasa ba “,   dinah tace ” wayyo Allah na na shiga uku ” malik dai bai kara cewa komaiba sai ko kokarin saita motar yake amman ina sai abunda ya cigaba

haka sukayi ta tafiya har suka bugi wani icce dogon yaro sannan motar ta tsaya !!!           da sauri suka fito motar, malik ya zagayo side din da dinah take sai kuka take kamar ranta zai fita. ya rumgume yana  fadin ” srry2 sis kukan ya isa haka mun tsira yanzu plz ki kwantarda hankalinki ” bata ko saurare shiba kukan kawai take

mutane sukayo kansu sai tambayar ba asi akeyi, malik ya shiga musu bayani

    Suka shiga masu Allah ya tsare gaba wani ya kalli dinah yace ” taso in rage miki hanya tunda motarku ta lalace ” malik yace ” no need yanzu zan kira wani abokina ya kaimu barshi kawai mun gode ” ya ciro kudi masu dan dama ya bawa murumin da suka bugewa mota tare da bashi hakuri,!

Malik ya ciro wayarsa ya shiga kiran abokin nashi tare da masa kwatancin inda suke.,

Yana karewa ya kalli dinah yace “srry sis gashi nan zuwa yanzu xamu wuce gida kinji “? Cikin yanayin tsoro ta kalleshi tace ” a a yaya bari naje gida in yaso inyazo sai ya dauke ka ” kai ya girgixa mata “a a ban yarda ba kiyi hakuri yanzu zaizo plz kinki ” ?

Kai ta girgixa masa ” a a yaya bana son wani abun ya sake. Faruwa ” murmushi yayi yace ” bazai sake faruwa ba ko wanchan ai kinsan halin karfe wani lokacin haka yake ” tace ” yaya babu laifin karfe ciki nice naja komai yaya ka barni na tafi kar abunda yafi haka ya sake faruwa ” !

  Malik ya kalleta yace ” u scared calms babu abunda zai sake faruwa owk ” ;

tace ” babu tambas yaya yace fa baya son ganina da kai to kaga komai ai zai iya sake faruwa ” fuskarsa ta nuna alamun rashin fahimta yace ” wanene haka waye shi “?

Da karfi ta hade yayu ta shiga rabon ido can kuma ta kalleshi tace ” yaya ……uhm… Naam… Uhm…..” sai kuma tayi shiru ta bata fuska kamar zatayi kuka tana soshe2.

Tsare ta yayi da ido fuskarsa babu alamun wasa yace ” ehem fadi ina jinki ” hannu tasa cikin baki tana bantalar haurenta sai kalle2 take.chan ta kalleshi tace ” yaya inajin kishin ruwa bari nasha ruwa ga shago chan bani kudi na karbo “?

Yayi minti 2 yana kallonta ita kuma idonta na kasa,

sannan ya waiga a hankali ya kalli shago ya tashi yana fadin ” bari na karbo miki “; tace ” yauwa harda maltina plz ” kai kawai ya daga mata ya nufi shagon.!


Tana ganin yakai gurin shagon. ta tashi ta watsa da gudu mutane sai Kallonta suke,

Ita batama kula suba gudunta kawai take saida ta kusa karya kwana,

sannan malik ya juyo yana kallonta tana karya kwana,

Sai haki take da sauri ta tare wani dan achaba dazai wuce, saida ta hau sannan ta masa kwatancin inda zai kaita tana ” fadin yi sauri dan Allah kaji ” ? Aiko tana rufe baki ya fara gudu kamar an aikoshi ”

Cikin kankanen lokaci suka shigo unguwar tun kamin ya karsa kaiwa gate din gidan tace “tsaya nan ya isa bari na karbo maka kudi ” ta sauka ta nufi cikin gida da sauri kamar zata tashi sama.

Duk suna zaune parlour har momi suna kallon Z- world ana wani drama,

Da dan gudu2 ta shigo parlor duk saida sukaji tsoro.

Nafisa tace ” haba dinah miye na shigowa gida ko sallama babu ” ? Dinah bata ko kula taba ta nufi stairs cikin sauri, bata dade ba ta fito rike da #1000,

Zata fita momi ta kwala mata kira ” dinah zo nan “.. Ta fita tana fadin ” tohm momi gani nan ” da gudu ta karasa gate din tana fita ta nufi gurin da tabar mai achaban sai rabon ido take dan bataga mai achaban ba., horn taji anyi da sauri ta kalli gefen t-t inda taji horn din.

Wata sabuwar motace baka mai kyau. A hankali aka sauke glass din motar,… Da hannu taga yayi mata well done yana murmushi ..,,

Baya2 tayi tana numfashi mai karfi ta watsa da gudu kamar wadda kare ya biyo., da karfi ta banki kofar gate din ta karasa parlor kamar zata fadi.

Ta zube Jikin momi ta fashe da kuka., ba karamin tsoro sukaji ba duk  suka taso suna tambayarta miya faru,

Momi hankalinta a tashe tace ” dinah kalleni fada min miya sameki “?

tashi tayi ta nufi stairs da gudu jin anyi parking din mota., momi ta bita da kallo tana ”  fadin inna’lillahi wa’inna-ilaihi raji’un ”

Momi na rufe baki malik ya shigo da sallama shida abokinsa momi ta kalleshi tare da amsawa ” amin alaikassalam ” ta dan saki fuska tana murmushi tace ” Malik ne haka yau kuma aka mana zuwan ba zata “,, murmushi yayi yana karewa su zainab da zara kallo yace ” ae wlh momi ina dinah “?

Nafisa tace ” gata chan dakinta yanzu ta shigo tana kuka ” malik ya kalli abokinsa yace ” nasir zauna ina zuwa ” nasir din ya zauna sukaci gaba da gaisawa da momi,

Shi kuma malik ya nufi stairs.,!!

Kofar dakinta malik ya nufa yana yana tabawa yaji ansa key kwankwasa ya shiga yi yana fadin ” sis bude min kofa inason nayin magana dake ” shiru baiji ta amsa masa ba ya sake cewa ” sis nine fa malik bude mana ” cikin muryar kuka tace ” yay xamuyi magana Lttr kaina yana ciyo yanzu “, ” ok sis Allah ya sauwake ” ya dade gurin tsaye sannan ya nufo downstairs,

A sanyaye ya karaso parlor,

Kusa da abonkinsa nasir ya zauna,

Suka dan taba fira da momi sannan ya dubi  agogon hannunsa,

yace ” momi mu zamu wuce ” momi tace ” tun yanzu malik to duk yaushe kazo “?

Yace ” momi akwai abunda zan danyi yanzu dan gobe 7am zan wuce shiyasa ” momi tace ” tohm shikenan Allah ya kiyaye hanya ” ,

ya amsa da amin nasir yayi mata sallama suka fice.

Bayan sallar magariba momi ta nufo dakin dinah tana taba kofar ta jita rufe. Ita kwankwasar tayi daga can ciki dinah tace ” waye “? Momi tace ” nice bude ” tasowa tayi ta bude kofar. Ta kalli momi  tace ” momi yay malik ya wuce “? Tace ” ae tun daxu ya tafi ” tace ” owk momi wani abu zanyi “?

Momi tace ” magana na keson muyi ”

dinah cikin tsoro tace ” momi yay malik ne yace miki wani abu “? Momi ta girgixa mata kai dinah kamar marar lafiya ta juyo ta dawo saman bed dinta ta zauna. Momi ma kusa da ita ta zauna ta tsare ta da ido sannan tace ” dinah ni mahaifiyarki ce nice kadai zan iya zama dake komai tsanani komai dadi kuma uwa abokiyar shawara. Ba zanyi cilas takiba akan ki fadamin but inason kisan koda yaushe kofata abude take kuma inason kisan tun za aje ake shawara basai an dawo ba “.,

Dinah tayi murmushin karfin hali tace ” momi ni babu abunda yake damuna na ” Momi ta shafi fuskarta tace ” karki koyewa mahaifiyarki komai dinah tun ba yauba naga yanayin ki ya chanja dan haka basai kin min karya ba dan ni bazan saki dole ki fada ba ” dinah tayi kasa da idonta bata ce komaiba sai wasa takeyi da hannayenta ganin haka yasa momi ta tashi ta fice

Please Login or Register in order to submit comment