Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naga yadda take satar Kallon mu a parlour jiya da dare sannan naganta da wani mutun da ban yarda dashi ba kuma yanzu naga tana record din maganar da muka kare da momi ” yana kaiwa nan ya saketa ya mikawa zulaiha hannu yace ” bani “? Ciki da tsana ta ciro waya da take gefen zaninta ta mika masa idonta a kafe babu ko alamun hawaye balle kuka

Cikin tsoro zara tace ” yaya to mieye anfanin yin haka wuka fa ka yanka mata “? ” Nasani zara inba haka na mata ba zata bani ba ”

Malik ya dafata yace ” plz zara bana son kowa yasan munyi wannan abun indai ba ita ta fadaba plz wannan between us ne kiyi min alkawarin babu wadda zaiji plz “?

Zara da kwala suka cika mata ido tace ” to idan ba gaskiya bane fa yaya kafa yanka mata hannun kayi rashin tausayi da yawa fa “? Ajiyar zuciya ya sauke yace ” gaskiya ne zara ni Barrister nasan abubuwan dake baki saniba tunani da naku ba dai yakeba kuma wannan da kika gani inba haka nayi mataba bazata bamuba sai kowa yajimu karshen tama ta gudu plz juz promise me bazaki fadaba “?

Kai ta daga mishi ” ok yay babu wadda zaiji a promise u ” ” thank you little sister ” ya juya da sauri ya bar kitchen din

Zara ta matso kusa da zulaiha tana ya mutse fuska tace ” srry zulaiha bari na dauko kyale na daure miki kinji “?

Sai a lokacin hawaye suka fara bin fuskar zulaiha ta kalli zara tace ” na gode but plz karki bari momi taji maganar nan plz zara “? Shiru zara tayi tana kallonta sannan tace ” da gaske ne duk abunda yaya ya fada kin aikata “?

Da sauri ta dafata ” no ba gaskiya bane kawai dai inason sai ya gama binciken shi dan yanzu in momi taji zata iya hanashi kinga shi kuma sai ya dauka da gaske ne plz zara ki yarda dani ya za aiyi nayi haka “?

Zara tace ” shikenan mubar wannan maganar babu wanda zaiji bari na dauko miki abu ki daure hannun kinji “?

Kai ta daga mata zara ta juya da sauri tabar kitchen din

Runtse ido  zulaiha tayi tana sauke ajiyar zuciya,

Takai hannunta daidai inda wukar ra yanke ta a baki,!!!

Zara bata fi minti goma da fita ba ta dawo rike da kyale ta kama hannun zulaiha cike da tausayi ta daure mata tace ” wlh dakin momi rufe yake balle nayi treatment dinki kuma taje da keys dinta “.

Zulaiha tace ” no karki damu zanje Pharmacy ” bata jira mie zara za tace ba ta tashi ta nufi kofar fita

Zara bata bar Kitchen din ba saida ta gyra komai,

sannan ta nufi dakinta sai da dare bayan isha malik ya shigo gidan , duk suna zaune parlour har momi,

Fuskarsa a hade ya shigo parlor duk suka juyo suka kalleshi gannin ya shigo babu sallama kuma fuskarsa babu annuri ya samu gurin kusa da nafeesa ya zauna ,

Momi ta kalleshi tace ” lafiya dai malik mie damunka “?

Ajiyar zuciya ya sauke yace ” babu komai momi “

Ya kalli zara ” ina zulaiha “? ” ta fita bata nan ” ya sake kallon Momi yace ” plz momi daga yau a kori zulaiha aiki a gidan nan plz mom “?

Momi ta juyo ta kalleshi tana gyaran murya tace ” excuse me “? Kawarda fuskarsa yayi yace ” u hear me momi plz juz a koreta plz mom ki sallameta daga aiki “? Momi tace ” i cmpltly dn’t udrstnd wht ar u tlk abt akoreta as hw “?

Nafisa ta gyara zama tace ” hlp me ask him mom nima dai abunda ban fahimta ba kenan “? Da angry face malik ya kalleta yace ” kar in sake jin bakinki cikin magana ta am nt tlkng 2 u ” ya kalli momi data saki baki tana kallonshi yace ” momi ya za ace kamar zulaiha mai diploma tana aikin abinci da sauran aiyukan gida momi lafiyarta ta fa kalau tsaye da kyau zaune da kyau amman ta tare karkashin mu “? Momi tace ” feel free mie kake nufi “? ” momi ban yarda da zulaiha ba momi ki koreta karta haifarda abunda ba shikenan ba ” momi tace ” kamar yaya “?




   VOTING COMMENTING PLEASE
[11/16, 10:18 AM] Khadeeja Candy: Malik Yace ” momi hw macce kamar zulaiha zata zo tayi aikatau a nan gidan momi diploma ne da itaba fa amman ace ta tare nan tana wanke wanke da sauran aiyukan gida haba momi kiyi tunani mana tun ba yau ba na sha nuna miki ni ban yarda da aikin da zulaiha take acikin gidan nan ba but kinki fahimta ruwa a cokali ya ishi mai hankali wanka fa ” momi tace ” to ai ta bada Reason dinta tace kudi takeson ta tara ta cigaba da university ko ” malik yace ” yanzu momi kin yarda da wannan dalilin nata wannan fa ba dalili bane yanzu in cutar damu tazo yifa momi fa makashinka yana tare dakai “? 

Tashi zara tayi tsaye tana girgixa kai zatayi magana malik ya daga mata hannu ” no banson kice komai zara get lost ” 

Momi ta kallesu  fuska a hade tace ” ku tashi kuje dakinku wannan between us ne ” 

Duk suka tashi suka nufi stairs, 

Akabar momi da malik kadai cikin parlour 

Malik ya kalli momi yace ” momi akwai yan aiki cikin gidan nan zasu isa inma kina da bukara wasu zan karo but momi ki kori zulaiha dan zaman ta a nan ba alkhari bane zata iya cutar dani da dinah da ke da duk ma wadda yake cikin gidanan ” murmushi momi tayi tace ” bazan kore taba dan banga hujar korarta ba kwatan ta 5 cikin gidan nan a tanada niyar cutar damu da tayi ” yace ” momi damisa ki sabo ce ba a ganewa tanan momi kuma in yanzu na fada miki dalili na bazaki yarda ba ” 

Momi bata ce dashi komaiba ta daga kai tana kallon Zainab dake saukowa downstairs shima juyawa yayi yana watsa mata wani mugun kallon dan yasan gulma ce ta dawo da ita, 

bata karasa saukowa ba ta tsaya a stairs tace ” momi wayarki na ringing ” tsawa malik ya katsa mata ” bakiga magana muke ba go bck 2 ur room “

Jkinta na rawa ta juya ta koma inda ta fito, momi ta kalleshi tace ” karka cire haushinka akan yara na malik dan naga wani gurin aka tabo ka ” tashi tayi ta nufi stairs tana fadin ” zamuyi magana gobe dan yanzu naga baka cikin natsuwa somting is wrng wth u “!!!

Ya dade zaune parlour yana tunani sannan naga ya tashi ya nufi stairs, 

Dakin dinah naga ya nufa da karfi ya tura kofar dakin,

Dinah dake kwance da sauri ta tashi ta kura masa ido, 

Da hannu ya nuna ta yace ” karki sake bari zulaiha ta shigo dakin nan ki fada zainab ita karta barta tashiga mata daki kuma gobe zanzo kar wadda ya fita akwai maganar da zamuyi “

bai jira mai zatace ba ya juya yafice, 

Tashi dinah tayi ta koma bakin kofa tana lekonsa, 

Saida taga ya sauka downstairs sannan ta nufi dakin zainab, 

Tana kwace rike da littafin anty fauziya d Suleiman (abun-duhu)

Tashi tayi zaune tana kalli dinah, 

Kusa da ita ta zauna tana fadin ” yaya yace na fada miki karki kuskura ki bari zulaiha ta shigo dakinki kuma gobe yana da meeting damu kar wadda ya fita “

Zainab tace ” hmm ke wai yau yaya lafiya yake kuwa “? 

” yau ni ina zan sani amman akwai abunda ya faru tunda kikaga haka dan duk abunda zaisa yaya yayi haka ba karami bane “

Zainab tace ” nima haka na gani but mie yasa yake son akori zulaiha “?

Dinah tace ” wlh ban saniba but nima zulaiha bata kwanta min arai ba momi ce take sonta “

” a a nima ina sonta gaskiya tanada mutunci da kyautatawa “

Tabe baki dinah tayi tace ” tohm Allah barku tare nidai bari naje na isar masa da sokonsa gurin nafisa da zara “

” okay gud night “

Dinah ta tashi tana fadin ” aha night “

Washe gari karfe 10:00am momi ta shigo part dinta, 

Tana shigowa ta tararda zulaiha na gyaran parlor,

Tana ganin momi ta dur kusa har kasa ta gaisheta, 

Momi ta amsa tana murmushi ” lafiya kalau zulaiha an nan anata aiki ko “? 

” ae momi ” momi tace ” tohm yayi kyau yarana sunyi break ko “?    ” Ae momi tun daxu suka karya “

 ok kawai momi tace ta nufi stairs 

Ita kuma zulaiha ta cigaba da aikinta, 

Saida ta gyara parlor tsab ta turare shi sannan ta nufi kitchen tayi wanke2 ta gyarshi ta nufo dakin momi, 

Abakin kofa ta tsaya tayi sallama,

Bayan momi ta amsa mata tace ” shigo “

Cikin ladabi ta shigo kanta a kasa, 

Ta shiga gyara dakin saida ta kammala sannan ta nufo  momi dake zaune saman kujera tana dannar laptop, 

ta risina tace ” momi yau dakin zara da nafisa kawai na gyara dan dinah da zainab sunce basa so “

Momi ta tsayar da abunda take ta kalleta ” mie yasa “? ” wlh nima ban saniba haka dai suka ce “

Momi tace ” je ki kira min su har nafisa da zara “

Cikin girmamawa ta tashi ” tohm momi ” ta fice 

Zara ta fara shigowa dakin ta nufi kusa da momi ta zauna tana fadin ” morning momi ashe kin shigo “

Momi ta kalleta tana murmushi tace ” na shigo auta hw ws ur nigt “?

” so good mom ” momi tace ” gud ” ta cigaba da danne2 

Har su zainab da dinah da nafisa suka shigo 

Duk suka mata morning ta masa tana dannar laptop, 

Kusa da ita dinah ta zauna, 

Nafisa da zainab da zulaiha suka zauna kasan carpet, 

Momi ba tare da ta kallesu ba tace ” zainab da dinah mie yasa kuka hana zulaiha ta gyara muku daki “?

Dinah ta kwanto jikin momi tace ” yaya Malik ne yace kar mubari ta shiga mana daki “

Shiru momi tayi har na wani lokaci sai danne2 ta take,

Ganin haka yasa zainab tace ” srry momi bazamu karaba “

Ba tare da ta kallesu ba tace ” no need daga yau dai kowa shi zai rika gyara dakinsa da kansa kuma anjima kuje BQ gurin maman maryam zata fada muku aiyukan da zaku rikayi cikin gidan nan every day “

Da sauri nafisa tace ” momi ” 

Momi ta kalleta ” any correction “?

Kasa tayi da kanta tace ” no ” 

Zara ta leki fuskarsa momi tace ” har da ni momi “?

Momi tace ” ban cire kowa ba har ke oya every body get lost “

Suna tashi tsaye. Momi ta kalli zulaiha tace ” tsaya ina son magana dake zulaiha “

Koma tayi ta zauna su kuma suka fice kamar su fasa kuka, 

Momi ta aje laptop din dake jikinta saman Table din take gefenta, 

Ta kalli zulaiha tace ” mie ya hada ki da malik “?

Zulaiha ta dago ta kalli momi tace ” a a babu abunda ya hadani dashi wani abun yace ne “?

Momi tace ” no kawai na tambaya ne “

” a a babu abunda ya shiga tsakanina dashi sai in cikin kuskure ne ” momi tace ” ok tashi ki cigaba da aikinki daman shine kawai “

Saida tayi ma momi sallama sannan ta fice

Gugaren sha biu gali maigadi ya shigo parlor da sallama, 

Bayan Zainab ta amsa masa yace ” .idan dinah tana nan kice tana da bako a waje ” zainab tace ” wanene “? ”  Bai fada min koshi wayeba amman dai yana nan waje ” 

” Ok bari na fada mata ” to kawai yace ya fice

Yana fita Zainab ta tashi ta nufi stairs tana yan wake2 ta, 

Dakin dinah ta shiga a bakin kofa ta tsaya tace ” ana sallama dake awaje “,

Dinah dake kwance tana online game ta dago ta kalleta ” wanene “? 

” in kikaje kya gani ” tana kaiwa nan ta juya ta rufo kofar dakin 

Sai da zainab tayi 20 da fita sannan ta tashi ta nufi wadrope ta dauko hijab milk color tasa 

Ta nufi dakin momi tana taba kofar dakin taji ta kulle, 

Juyowa tayi ta nufo downstairs, 

Tana karsa sauko parlor ta kalli zainab da nafisa tace ” ni ana sallama dani awaje kar momi tazo kuma kuce baku san inda nayiba ” 

Nafisa tace ” munji kidai je ki dawo muje gurin maman maryam kar momi ta dawo bamu jeba “

Zainab tace ” lailaikan dan Allah karki dade dinah dan yanzu momi ta chaja ba kamar daba in taga bamu jeba komai zai iya faruwa ” 

Kai kawai dinah ta daga mata ta fice!!! 


Tana fitowa ta shiga duba harabar gidan inda yasan baki na tsaya wa, 

Ganin bata ga kowaba bayasa ta nufi gate 

Tana fita taga abdul-rashid jingine jikin mota yana kallon t-t 

Da fuskar zolaya ta kasa kusa dashi tace ” shine ka wani tsaya bakin t-t kamar bako dan kasa ni inyi wahalar fitowa har nan ” saida yayi dariya sannan yace ” to ai gidan ne naku sai a hankali kar mutun ya shiga aiyi mai wulakanci ” 

” Wulakanci kuma kamar ya gidan wukanci ne dasu “?

Murmushi yayi yace ” no mubar zancen ykk kwana biu naga kinbar shiga makaranta shine nace bari na biyo naji ko lafiya kinsan san hankalina ba kwanciya yake ba in bana tare dake ” 

Girgixa kai tayi tana murmushi tace ” abdul 2 bazaka bari ba ko nidai ya friends dina “? Da sauri ya rufe baki ” oh sorry na manta kar yayanki yajini ko dan akwai shi da zafin kishi ” kamar ya yayana zaiyi kishi na haba dai “

Tabe baki abdul-rashid yayi yace ” Allah zafin kishi ne dashi kinga yadda yayi min ranar da nazo dubaki hmm ai ahiyasa nace bazan ma shiga ciki ba karya hadeyeni ” 

Da dan mamaki dinah tace ” nifa ban gane makaba ka fito fili ka fadamin yayana zaiyi haka “? 

” ya mayi but yana da gaskiya ai kinsan abinda akeso ake kishi ” dinah tace ” dan Allah kabar wannan zancen wlh babu soyayya tsani na dashi kawai yayana ” daga kafadunsa yayi yace ” anyway nidai nazo na ganiki ne kawai dan nayi miss dinki sosai ” murmushi tayi ” i miss u too my sweet friend ” da fusakar zolaya yace ” juz “? 

Fari tayi da ido sannan tace ” Nop sweet boyfriend ” wink ya mata yace ” yauwa my Precious ” murmushi tayi tana hade hannayenta tace ” nidai muje ciki mun tsaya a t-t ” 

” no ni wucewa zanyi daman nayi miss naki ne nace bari nazo na ganki ” 

Dinah tace ” gaskiya ka kyauta kuma naji dadi sosai ” 

Bude motarsa yayi yana fadin ” nidai n tafi plz come back soon we all miss u a lot “

Daga masa hannu tayi tana murmushi tace ” i wll insha Allah take good care of yourself “

Yana sama motar key yace ” oh yeah my heart ” 

Murmushi kawai tayi ta daga masa hannu shima ya shiga daga mata,

Saida ya hau t-t sannan ta juyo ta shigo cikin gida,

Karfe 3 da yan mintina malik ya shigo gidan, saida yaje part din abbah ya gaishe shi sannan ya nufo part din momi, 

Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shigo parlour cikin kananan kaya,

Abul-khair kawai ya tarar cikin parlor zaune gaban tv yana kallon mbc 2,

Kusa dashi malik ya karasa ya bugi kafadar yace ” big man kallon American film akeyi ne ” dagowa yayi cike da dariya yace ” yesss men momi tace na kalla kamin lokacin islamiya ” 

Malik yace ” gud ” ya juya ya nufi stairs abul-khair yace ” yaya muyi game mana kamin momi tazo “? ” no banida time ” ” yaya dan Allah “?

” Kabuga da zara ko zainab “

” ai duk basa nan sun tafi BQ ” juyowa malik yayi ya kalleshi ” gurin mie “? 

Abul-khair yace ” nima ban saniba “? Dawowa malik yayi ya zauna yana fadin ” je ka kirasu “

To kawai yace ya tashi da sauri ya fice
Da dare2 suka shigo parlor saida suka zauna sannan suka shiga gaishe shi,

Maida hankalinsa yayi gurin tv yayi kamar bai san dasu cikin parlor ba 

Can kuma ya kallesu yace ” mie kuka je yi BQ “? 

Tasowa zara tayi ta kusa dashi ta zauna cikin fuskar shagwaba tace ” gurin maman maryam mukaje wai momi ce tace araba mana aikin da zamu rikayi a gidannan ” 

” aiki kamar ya “? 

nafisa tace ” wai yanzu in nayi abinci rana zara tayi na dare gobe zainab tayi na dare ko rana kuma wai mu zamu rika gyara dakin mu da kanmu “

dinah tayi ” malik yace ” hala an kori zulaiha ne “? 

dinah tace ” a a tana nan ” 

Shiru yayi har na wani lokaci sannan ya kallsu fuskarsa babu alamun wasa yace ” dinah ta fada muku za muyi magana ko “? 

Duk suka daga masa kai tare da “ae ta fada mana “

Yace ” gud ” ya kalli dinah ” zaki iya komawa makarantanki duk lokacin da kika tashi munyi magana da momi ” murmushi dinah tayi tace ” thank u yaya naji dadi ” 

Malik yace ” gobe zamu wuce muda abbah sati mai zuwa zan dawo inason kamin na dawo ko wace cikinku ya fitarda mijin aure banda zara “

wani irin kallo suka masa suka sakar masa baki, 

Sannan suka shiga kallon junansu 

Nafisa ce tayi karfin hali tace ” yaya wasa kake yi dai ko “?

 kallonta yayi fuska a hade yace ” ae wasa nake mana sai mie kuma “?

Dinah da gumi ya shiga karyo mata ta kalleshi tace ” yaya da gaske kakeyi kenan “?

Tashi yayi tsaye yasa hannayensa aljihu yace ” babu wasa dinah da gaske nake yi in kuma har bakuda mijin ne inna dawo zan muku “

Yana kaiwa nan ya fice duk suka bishi da ido baki sake,

Zainab tace ” inna’lillahi wa’inna ilaihi raji’un mun shiga uku mie yake shirin faruwa damu a gidan nan ne ” dinah bata ce komai ta tashi kamar marar lakka ta nufi stairs,

Da Dare guraren 9 momi ta shigo part dinta cike da far’ah, 

Saman kujera ta zauna tana karewa su zainab da nafisa da dinah dake kwance kamar masarasa lafiya kallo, 

Tace ” lafiyarku kuwa ” ?  Dagowa sukayi a firgice suka kalleta dan basu sannan da shigowar taba,

Nafisa tace ” momi sannu da zuwa ” 

momi tace ” yauwa nafisa ya maga fuskarku haka gashi na zo muku da good news “

Zara dake saukowa downstairs 

tace ” wai dan yaya yace su fitarda miji shine suka wani bata rai kamar an musu mutuwa “

Girgirza kai momi tayi tace ” haba dan Allah wani irin abu ne haka dan ance ku fitar da miji kukayi haka 

aure sunar Manzon Allah (S. A. W) abunda musulunci yace ce ayi kuke adawa dashi to wlh ku gyara tun Allah baiyi fushi da kuba

 dan Manzon Allah (S. A. W)  yace aure sunna tace kuma duk wadda baya son sunna ta to baya tare dani 

da lafiyarku da jinku da ganinku son kowa da maneman ku kuce baza kuyi aure ba to mie zakuyi ?

 in yanzu kuka mutu kucewa Allah mie kuce kun tsaya karatu boko bakuyi aure ba ina ma karatun addini ne kukayi haka bana zamani ba to bari kuji na fada muku Manzon Allah (S. A. W) yace yana tausayawa macce da ta mutu bada aure ba

Karatu dai baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu 

Kuma duniya ba matabbataba ce arone aka bamu dan aga wane irin result zamu fito dashi

kuma Allah cewa yayi bai halice muba face dan mu bauta masa kuma aure bautar UBANGIJI ne

Lafira dai lafin wani baya shafowar wani kuma kowa yayi dakyau zai gani ya nan a qur’ane Allah ya fada ranar da baki baya karya ranar tonon asiri sai ku tanadi abunda zaku fadawa Allah 

 in kuma kunyi auren kunbi mazajen ku ku samu Aljanna 

In kuma ba kuyi ba kanku 

mudai munyi Allah ya karbi ibadar mu “!

Tana kaiwa nan ta tashi rai a bace ta nufi stairs!!!

Wani sanyi jikinsu yayi sukayi sukuku suna tunani

 dan suma sun san basuyi daidai ba kuma duk abunda momi ta fda musu babu karya aciki, 

Har momi ta kare abunda zatayi ta nufo downstairs sunanan yadda ta barsu, 

Tana karasa saukowa dinah ta tashi ta karasa inda take ta rika hannunta tace ” srry momi insha Allah bazaki kara jin haka daga gare muba zamuyi aure insha Allah ” ajiyar zuciya momi ta sauke tace ” aiko da naji dadi dinah duk da nasan bani za kuyiwa ba “

Nafisa tace ” insha Allah momi zamuyi aure dan mu cika ibadar mu wa azin ki ya tsara mu ” 

Momi tayi murmushi tace ” to Allah yayi muku albarka ya zaba muku mazaje na gari da duk diyan musulmi ” 

Duk suka ce amin dinah ta dora kanta kafadar momi tace ” amin my sweetest mother “

Zara tayi dariya tace ” yauwa momi minene good news din da kika zo mana dashi dazu “?

Murmushi momi tayi tace ” dazu da magariba mukayi waya da yayanki yace a gaishe ku kuma a muku albishir yananan zuwa cikin satin nan dan ya karbi takardu sa  kuma ya samu good result, 

Yanzu babu abunda ya rage masa, sai dawowa “

Cika parlor sukayi da ihu dan murna 

Dinah ta rungume momi tana fadin ” wayyo dadi i miss my best yaya Allah kawoshi lafiya ” 

Zainab tace ” amin shi kenan ma na huta ” 

Momi ta harareta ” kin huta da mie “?

Rufe ido tayi ta tashi da gudu ta nufi stairs tana kalkatar dariya

Momi ta tabe baki tace ” oh yayan zamani babu kunya Allah ya shirya ” 

Ta kalli dinah ” nidai sake ni na baro abbah ku shi kadai ” dinah ta saketa tace ” gud night sweet mom “

Momi ta nufi kofar fita tana fadin ” night kudai kula da kanku “,

Washe gari da wuri dinah tayi shirin shiga makaranta 

Cikin bakar abaya da jan gyale ta fito kamar yar larabawa 

Tana daukar handbag dinta wata farar takarda ta fado,

Cike da tsoro ta dauke ta saida tayi bissmillah sannan ta bude ta shiga karantawa, 

           ” MORNING LOV

HOP U SLEEP WELL 

NASAN KINYI MISS DIN NA DAN KIN DAINA GANI NA KO SAKONA BUT KARKI DAMU INA TARE DAKE NASAN MALIK YACE KI FITAR DA MIJI KO HMMM NAN MA KARKI DAMU 

DALILIN RUBUTU MIKI WANNAN SAKON SHINE 

KISA IDO AKAN DUK ABUNDA YAYANKI ZAICI KO SHA IDAN YA DAWO 

KI TABBATAR A HANNUNKI YA FITO BA A HANNUN KOWA BA HAR A WATSE MURNAR DAWOWARSA 

DAN AKWAI WADDA ZAI SAMA YAYANKI     POISON YA MUTU SABODA SHI NASHI KARATUN BAIYI KYAU BA

 NA YAYANKI KUMA YAYI KYAU KUMA AKWAI GABA TSAKANINSU KUMA KODA KI YIWA YAYANKI BAYANI BAZAI GANEBA DAN HAKA INDAI KI SON RAYUWAR YAYANKI TO KI KULA DA ABUNDA NACE MIKI 

PERHAPS KINADA TAMBAYOYIN DA NIKADAI ZAN IYA AMSA MAKI SU 

SO KI BUDA BEDSIDE DRAWER ZAKIGA ADDRESS DINA 

       TAKE CARE MY DEAR WIFE ”

                      #KISS
[11/16, 10:18 AM] Khadeeja Candy: Da sauri dinah ta nufi bedside drower din ta buda, 

Wani dan karan card green aduke da address da number waya, 

Da sauri ta saki card din tayi baya2 tana maiyarda numfashi da karfi, 

Har ta jingina jikin wardrobe sai kallon takardar take kamar wadda bata gane abunda aka rubuto ba, 

Can kuma naga ta sulala xaune kasa tana sauke ajiyar zuciya,

Ta hada kanta da guiwa, ta lumshe ido 

Tayi kusan minti 30 a haka sannan. Ta tashi jikinta a sanyaye ta bude wardrobe din tasa takarda, 

Ta rataya handbag dinta ta nufo downstairs

Zulaiha ta parlour sai faman aiki take yi.

 tana ganin dinah ta sarkar mata murmushi tun kamin ta karasa saukowa tace ” morning dinah ” 

Ciki2 dinah ta amsa mata ” morning sannun da aiki “

Ta nufi kofar fita har ta saka kafarta daya awaje sai kuma ta tsaya chak jin zulaiha ta amsa da dariya 

Juyowa tayi ta tsurawa zulaiha ido 

Ita kuma kanta a kasa tana goge Center Table

Kamar ba ita tayi dariyarba 

Dinah fuska a hade tace ” mie kike yiwa dariya zulaiha “?

Da sauri ta dago tayi murmushin yake tace ” yanayin yadda kika amsa ne yaban dariya “

Wani mugun kallo dinah ta watsa mata tace ” mie abun dariya

Please Login or Register in order to submit comment