Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamin ka dauki yar aiki lailai nayi wauta inda yanzu na rasa ki shikenan ” malik yace ” kuma fa kamata yayi a rika daukar wadda aka sani bawai kowa yaxo ka daukeshi aikiba koda bakasan inda nutun ya fito ba ” nafisa tace kuma ai ba aiki kadai ba harda komai ma tunda ga driver nan shima haka yake “

Momi tace ” lailai kan kinga daya samu asara biu ga faruk ga ki ” faruk yace ” to ai babu komai koda mun tafi tare kunsan jininmu yafi haduwa dama kunga duk cikin zumunci ne yaya da qanwa sun tafi tare ” duk suka kwashe da dariya har abbah 

Sun dan jima suna fira sannan abba ya tashi ya nufi part dinsa tare da momi, 

Bayan sallar a’zahar malik da faruk suna parlor suna buga game da abul-khair da zara momi ta shigo, 

Kai momi ta girgixa tace ” to Malik taso ga wani aiki kuyi zaune kuna buga game kamar yara ” tasowa yayi yana murmushi ya nufo momi yana fadin ” momi can yeni za suyi ” momi na kokarin mika masa kopin dake hannunta tace ” ai kara su canye ka dinah nake son kabawa wannan rubutu ne kasan kuma basonshi take ba dan Allah karka bari ta ragashi ” ok kawai yace ya nufi stairs momi kuma ta nufi hanyar kitchen, 

Tana zaune saman carpet dafe da kai danjin take wasu kwari na mata yaro aka, 

Tana ganin malik ta saki kanta da sauri tana murmushi ” yaya ” ” naam sweet sis ” ya karasa magana tare da zaunawa 

Baice da ita komiba yajanyo kanta ya hada bakinta da kopin ya shiga dura mata, 

Ba musu ta bashi hadin kai 

Bai dire kofinba saida ta shanye sannan yayi murmushi yace ” yauwa  kanwata Allah ya kara tsarewa ” ” amin yayana ” janta yayi ta kwanto jikinsa yace ” wai na tambaye ki sis “?

 ” ae yayana mienene “? Shiru yayi har saita tace ” inajinka yaya ” sannan yace ” wai kanwata da kika je gurin bayan abunda kika fada min sunyi miki wani abu “? ” a a yaya basu min komaiba ” ” dan Allah sis ki fadamin “? ” wlh yaya maimin komaiba bakaji na rantse ba wlh ko kissing dina baiyiba ” ajiyar zuciya ya sauke ” Alhamdulillah ” can kuma ya riko fuskarata yace ” sis da ba agankiba bansan yadda rayuwata zata kasanceba wlh dinah ina sonki sosai fiye da tunaninki shiyasa nake son muyi rayuwa ta har abadam dake,,,,

Tashi tayi zauna idonta kamar mai jin  bachi tace ” haba yaya mie yasa zaka sake fadin haka na fada maka babu soyayya tsakanin mu shin wai kai yaya ko kunyar matarka bakaji ne kuma nafisa fa kace mata mie dan Allah kabar wannan zancen”

Ido ya tsura mata sannan yace matata tasan ina sonki dinah tun ba yauba. Dinah tun kina karama nake sonki sosai bana ganin ko wace mace sai ke. Kuma dan Allah kibar maganar nafisa bana sonta ban taba jin sonta a raina bamu dace da juna ba, ke nake so dinah mie yasa kika kasa ganewa “? Zatayi magana sukaji faduwar abu mai kamar glass, wani kallo dina ta masa ta tashi da sauri ta nufi kofa, 

Tana fita bata ga kowaba sai glass cup guda 2 har biu sun fashe da drinks, 

Da sauri ta nufo hanyar downstairs 

Bata karasa kawowaba taji an rufe kofar dakin nafisa da karfi, 

Dafe gabanta tayi yana kallon malik dake tsaye bakin kofar dakinta, 

Kamar zata fasa kuka ta nufo dakinta, tana shiga ya rufa mata baya kallonsa tayi tana ware hannaye tace ” kagani ko taji taji komai ” 

A fusace yace ” to taji mana sai mie ana so dole ne miye laifina dan nace bana sonta ke nake so haramun ne “? Fadawa tayi saman bed tana turo baki tace ” nidai i need to rest ” 

          ” ok na fita na baki guri kenan “? 


Washe gari suna zaune parlor har nafisa banda dinah dake daki tun safe, 

Momi ta shigo kusa da nafisa ta zauna ta kalleta tace ” nafisa mie yake damun tun jiya naga yanayinki ya chaja kodai irin na dinah ne kema “? Murmushi tayi ” a a momi kaina ne yaketa ciyo shiyasa ” ” to Allah ya sauwake yashi kisha magani yana dakina ” to kawai tace ta tashi ta nufi  stairs

              ***  ***  ***  ***

Wasa2 yau wata 2 kenan da kwana uku da dawowar dinah gida kullum cikin addu’ah take da shan rubutu tun tana jin wasu abubuwa da mafarkai barkatai har ta daina yanzu,

Suna zaune garden ita dasu zara da zainab suka fira.

nafisa ta shigo tare wani handsome guy cikin shigar kamala sai murmushi yake.

Suna ganinshi suka tashi tsaye suna kallonshi.

a hankali ta shiga nuna mishi su, daya bayan daya suna gaisawa 

Saida suka kare sannan dinah ta kalleta tana murmushi tace ” nafisa friend dinki ne “?

Kai tsaye nafisa tace ” mijin da zan aurane ” wani sanyi jikin dinah yayi ya ratsa gefensu ta wuce. 

Parlor ta nufo tana shiga ta tararda manyan ledodi gaban momi. 

Kusa da ita ta zauna tana kallon kayan momi tayi murmushi  tace ” yanzu nafisa ta kawo wadda zata aura shi yazo min da wannan kayan “

 dinah tace ” momi yaya malik fa “? ” to gashi dai kina gani ai bata sonshi kuma shima baya sonta ” 

Dinah tace ” a a wlh tana sonshi ”  ” tana sonshi zata kawo wani to koma tana sonshi shi baya sonta ai ” momi shine yace baya sonta “? 

Momi tace ” ae da bakinsa ya fada min baya sonta ” shiru tayi ta tashi momi tace ” wuce min da kayan nan ” bata ce komai ba ta dauki kayan ta nufi stairs, 

Kwana hudu da faruwar hakan dinah tana zaune dakin ta wayarta tayi ringing tana dubawa taga number malik 

Kamar karta dauka dan saida ta kusa katsewa sannan tayi picking 

Saida yayi sallama ta amsa ta gaisheshi bai amsa gaisuwarba 

Yace ” dinah duk abunda momi da abbah suka tambayeki kice musu ae kawai kinji ” ” kamar ya mie zasu tambayeni “? 

” zasu tambayeki ko kina sona pls karki amsa musu karki ce kina sona plz kiyi min alkawari dinah dan Allah karki min butulci “

 ” mie yasa kake son nace haka “? ” saboda zasu tambayeki plz komai suka tambayeki kice yes kijin promise me sis “? 

Shiru tayi sannan tace ” ok i promise “
[11/16, 10:20 AM] Khadeeja Candy: Ranar wata laraba da dare Dinah na kwance dakinta zara ta shigo ” momi na kiranki tana part din abbah ” kai ta daga mata ta taso suka fito tare, 

Nan zara ta tsaya parlor ita kuma ta nufi part din abbah. 

Da sallama ta shiga parlor tana ganin malik gabanta ya fadi dan batasan yaxo ba.

Momi ta amsa mata fuskarta babu yabo babu fallasa abbah kadai ke murmushi. 

Guri ta samu kusa da malik ta zauna sana gasheshi. 

Gyaran murya abbah yayi ya kalleta fuskarsa babu alamar wasa yace ” dinah wace magana kukayi da malik “?

 Shiru tayi gabanta sai faduwa yake  tana satar kallon malik da kansa yake kasa,

Can kuma ta dago tace ” wace magana abbah ban ganeba “? 

“momi ta hade hannayenta tace ” malik yace kunyi magana aure tsakaninku kuma kun amicewa junanku dan kuna son junanku hak ne “?

Wani majiyar taji kanta yayi sai kallon malik take can kuma ta kalli abbah kamar rudaddiya. 

Abbah yace ” dinah bakuyi wannan maganarba ne “?daker ta iya cewa ” ae……. munyi ” ba abbah da momi da dinah ba koni da nake dauko muku rahoto saida naji saukar ajiyar zuciyar malik.

Murmushi abbah yayi yace ” nafi kowa farin ciki da wannan abun dama inada wannan niyar araina ta hada aurenku saidai ina tsoron ko bakwa son junanku ne na tirsasaku Alhamdulillah nasan kowa sai yaji dadin wannan maganar ” shikenan zaku iya tafiya in munyi magana zakuji mu 

idon dinah cike da hawaye ta taso ta fito malik ya rufa mata baya, 

Baice da ita komai ba dan yasan ranta a bace yake kallonta kawai yake har ta shige part din momi, 

Sannan ya shiga motarsa ya fice. 

Karfe 10 malik ya kira dinah tana yin ringing guda ta dauka ” haba yaya mie yasa zakamin haka mie kakeson matarka tace mie kake zatun nafisa zata zarga “? ” cool down sis matata nasan ina sonki dinah kuma nafisa ai ta kawo wadda zata aura har ana batun saka musu rana ga zainab nan itama da zata auri faruk ke yanxu wa zaki fitar a matsayin miji da yawuce ni kuma fa ko abbah yaji dadin abunnan kuma nasan dik family mu zasuji dadi mie abun bakin ciki aciki dinah yanzu kina ganin na zauna da bakin cikin ban aurekiba akan wani dalilin banza yafi miki”?

Shiru tayi sannan ta kashe wayar


Duk family su babu wadda baiyi farin ciki dajin maganar ba bama kamar abbah malik kamar ya xuba ruwa a kasa yasha, 

Kowa cewa yake sun dace da juna,

Tare aka sa musu rana da zainab da nafisa, 

Malik dayan ATM dinsa ya bawa momi yace duk wani abu da akeda bukata tayi, 

Saboda ba shida time yanzu dan suna wani case kuma daman gidan ya isheshi dan ko ya zauna ba dadi yake jiba dan tun ranar da abun ya faru dinah ko kallonsa bata sake yiba balle ta masa magana kwata2 ya kasa gane kanta gashi yana jin  sonta balle ya rabu da ita 

Kwanakin aurensu sai kara matsowa suke amman babu jituwa tsakaninsu. 

Duk wani shirye2 da akeyi saida yayi shi da momi dan bai isa yace abashi dinah yayi magana da itaba. 

Kana gani kasan bata farinciki da auren dan duk wasu shirye2 zainab ne da nafisa sukeyi.

Ita bata da wani sakewa sukuku take kamar marar lafiya 

Tana zaune dakinta guraren 3 na ranatana duna iv dinsu 

 momi ta shigo rike da wani iv tana murmushi ta zauna kusa da dinah ta dafata tace ” dinah kinga iv ko sun miki kyau “? Shiru dinah tayi tana son kuka momi tace ” dinah ki kwantarda hakalinki wlh koni na jidadin da malik zai aureki dan nasan yana sonki sosai kuma zai rikeki amana kuma kibar tunanin matarsa tunda kinga itama ta nuna farinciki ta duk da nasan ana kishi amman ita bata nuna mikiba kuma matukar bake kika chanja mata ba nasan vazata taba chanja mikiba dan haka ki sake ranki nima kinga sai naji dadi ” 

Haka momi tayita sanyaya mata zuciya da maganganu har ranta yayi fari

Sannan momi ta tashi ta fita

 FIRST AUGUST

Ka dauran auren

 dinah da malik

Zainab da faruk 

Nafisa da haruna 

Bayan anyi bukukuwan da al ada ta tanada anyi kashin kudi kamar ba asan zafin neman suba musamman ranar fulani day da dina da arrab day dangi babu wadda bai halarta ba kowa sai yaba bukin yake abun gwanin ban sha’awa


⭐8:30pm⭐

Yan daukar amare suka zo 

nasiha sosai momi da abbah sukayi musu da sauran dangi duk wani jan kunne da yakama iyaye suyiwa yayansu am musu kuka sukayi sosai bama kamar dinah dan kuka takeyi sosai  kamar wadda kace za a raba da ranta har wasu daga cikin abokan malik suka fara zargin kodai bata sonshi,

Dakar ta shiga motar suka kama hanya dan su zainab da nafisa tuni aka wuce dasu.

Gidane maikyau da tsari ko ina flowers ne 3 bedroom and 2 parlor babu abunda ba zuba ba ciki kamar diyar govt 

Dakin da yafi kowane kyau da tsaruwa shi aka kaita, 

Ba a jimaba malik ya shigo tare da tawagarsa suka shigo yar nasifa kadan suka musu ganin dare ya somayi suka fice bayan anyi siyen baki  akabar ango da amarya,..

Suna ficewa dinah ta kara fashewa da sabon kuka..

Babbar rigarsa ya cire tare da hula ta aje gefe ya yaye mata mayafin data lulluba dashi yaja ta jikinshi ya rungume,,,,

A hankali ya shiga mata magana ” yi hakuri sis nasan nasaki abunda bakiyi niyaba ni kuma bazan iya jurewa bane saboda son da nake miki ” saukar hawayensa taji a goshinta da sauri ta kalleshi murmushi ya mata yasa hannu yana share mata hawaye. 

Ya rika hannunta ” tashi mu godewa Allah ” tare suka tashi yana rike da hannunta suka shiga bathroom 

Suna fitowa ya shinfida musu carpet, 

Raka’ah biu sukayi sukayi addu’o i sannan ya juyo ya rika kanta ya shiga mata addu’ah, 

Yan karewa ta tashi da sauri ta koma saman bed ta zauna tunowa da maganganu friends dinta 

Tashi yayi ya nufi wasu akwatuna ya ciro mata doguwar rigar bachi, 

Nufota yayi ya mika mata rigar ” jeki ki saka wannan dan kayan dake jikinki suna da nauyi ” bata fuska tayi kamar zatayi kuka daker ta karba ta tashi ta nufi kofar fita 

” ina zaki”? yace da ita ” parlor zan chanja kaya ne ” yana nuna bathroom yace ” nan fa “? Batace dashi komaiba ta nufi bathroom din 

Koda ta fito ta tararda shi sanye da kayan bachi riga da wando bakin kofa ta tsaya tana kallon madarar da yake zubawa a cup. 

Saida ya juye harda kazar dake cikin leda a plate sannan ya taso yazo ya rika hannunta kamar karamar yarinya ya zaunar da ita ya shiga bata kazar,

Ssaida taci ta koshi sannan ya mika mata cup din milk 

gurin karba hannuwansu sukayi taraiyya da sauri ta saki cup din ta tashi tsaye zuciyar sai bugawa take 

Tashi yayi ya dauko towel ya goge gurin ya sake zuba mata wata cikin tsoro ta karba ta sha gado ya nuna mata ” kwanta ki huta ” tsakiyar gadon ta kwanta ta dunkule da bargo murmushi kawai yayi ya hau gadon shima ya kwanta, 


Washe gari gurarin 11am yan tuwon amarya sukazo, 

Sai xolayarta suke suna mata shegantaka basu bar gidan ba sai kusan magariba 

9pm 

Malik ya shigo da sallama  tana zaune parlor ta wani turo baki, ta dan saki fuska ta amsa masa tare da masa sannu da zuwa 

Yana zaunawa kusa da ita ta tashi da sauri 

Ya Kalleta ” sis wani abun ne “? ” a a daman wanka zanyi ” tashi yayi tsaye 

” owk muje muyi ko “? ” dawa “? Tayo waje da ido ” dake mana ” Girgirza masa kai tayi ” a a wlh Allah ya kiyaye indai na gama kayi ko kuma kaje kayi sai nima nayi ” koma yayi ya zauna ” ba matsala jeki kiyi sai nayi ” 

Ok kawai tace ta nufi dki 

saida tayi minti 5 da shiga sannan ya tashi ya nufi dakin shima. 

Yana shiga ya duduba bai ganta ba

A kofar bathroom ya dora kunnesa saida yaji ta fara motsi da ruwa sannan ya tura kofar ya shiga yasa key

Uhu ta shiga masa tana masa magiyar ya fita amman yaki a dole sukayi wankan tare koda suka fito sai kwasar murmushi yake yana mata wani shu’unmin kallo 

Ita kuma duk ta wani hade rai sai hawaye take

Wasa2 yau dinah kwananta 6 gidan malik amman wani abu bai taba shiga tsakanin suba,

 Tana zaune sanye da riga da wando na sari malik ya shigo cike da far ah ta tarbeshi ta tashi ta dauko miki drinks 

Tana ajewa ya janyota ta fado kanshi ya rungume ta 

Nan ta shiga kokuwa dashi har ta samu ta kwace kanta ta nufi daki da gudu

 kwafa kawai yayi ya tashi ya nufi dakinshi 

Da dare suna zaune parlor kasan carpet suna cin abinci malik ya maida wayarsa gefe yadda bazata ganiba ya danna calling 

Nan da nan wayarta dake bedroom ta fara ringing 

Yi tayi kamar bataji ba kallonta yayi yace ” bakiji wayarki ba “? Saida takai loma sannan ta tashi ta nufi daki,,,

Tana shiga naga ya ciro wani wasu table da sauri ya zuba mata cikin cup din da drink dinta yake. Ya kara mata juice, 

Yana direwa tana fitowa harararshi ta danyi cikin shagwaba tace ” kaine ko “?

Murmushi kawai yayi ya cigaba da cin abincin shi daukar drink din rayi zata sha da sauri ya rike mata hannu ” haba babyna kina cin abinci kina shan ruwa bari ki kare mana ” ba musu ta aje cup din ta cigaba da cin abincinta 

Saida ya tabbatarda ya narke sannan ya dauka da kansa ya bata sai murmushi yake yana mata wink.. 

Kurare 10 dinah na kwance dakinta sanye da kayan bachi sai soshe2 take idanuwanta sun chanja malik ya shigo rike da vanilla yogurt

Ta data yayi zaune sai wani laggabe2 take kafa mata cup din yayi a baki yana murmushi saida tasha rabin cup din sannan ya ajeshi ya kalleta ” babyna “? Da sleep eyes ta kalleshi bata iya amsawa ba 

Dukowa yayi a hankali yasa bakinshi cikin nata ya fara kissing 

Wani jarrrrr taji gashin jikinta ya tashi ta shiga mayar masa da martani 

sunyi 20 minutes a haka sannan ya kwantarda ita ya fara kissing din wuyanta hannunshi na dama makale da gashinta sai wani mayarda numfashi suke daga ita har shi 

Sun dade a haka sai romance dinta yake  sannan ya shiga rabata da kayan jikinta 

              Nidai nan na kashe musu wuta na fito dakin da gudu 😉


Da asuba shiya taimaka mata tayi wanka ta gasa jikinta sai kuka take msa sannan tayi alwala

Daukota yayi suka fito yasa mata doguwar riga tare da hijab ya shinfida musu carpet suka kabbarta sallar asuba., 

Suna karewa ko addu’ah bata tsaya yiba ta fada saman bed nan da nan bachi yayi gaba da ita 

Shikan saida ya kare addu’o insa sannan ya gyara mata kwanciyarta ya kwanta gefenta 

Sai 11 dinah ta farka tana bude ido taga malik zaune ya tsare ta da ido sai murmushi yake turo masa baki tayi tashiga masa kuka dariya yayi yace ” Allah yayi miki albarka babyna ” ya manna mata kiss saman goshi ” da ban aureki ba da bansan yadda rayuwa zata kasan ceba ina sonki sis fiye da tunaninki Allah ya barmu tare ” harararsa tayi yayi dariya ya dauketa suka nufi toilet brush yayi mata shima yayi ya sannan ya dauketa ya nufi parlor can sukayi break sai shagwaba take zuba masa 


***    ***     ***   ***  ****

11 YEARS LATER

dinah ta fito daga court sanye da kayan lauya abokan aikinta sai congratulations suke mata. Akan case din datayi winning,

Saida ta gama gaisawa dasu sannan ta nufo parking space inda malik yayi parking tun kamin ta karaso Al-amin da Amir suka fito mata da gudu sukayo kanta ” congratulations mom ” shafa kansu tayi tana murmushi ” thank you my dear sons ” suka rika hannunta suna murna suka nufi mota, 

A front seat ta shiga bayan ta dauki ummu-salma dake boxing da gwalanniya, su kuma suka shiga baya

 Kallonta malik yayi ” i lov u so very much my dear wife ina alfahari dake “

 dinah saida ta saci kallon yaranta dake bayan mota taga hankalinsu na wani gurin sannan tayiwa Malik wani hot kiss cikin muryar kissa tace ” i lov u more my dear soul ” murmushi yayi mata itama ta mayar masa sannan yayi ribas cike da so da kauna suka nufi gida.!!! 

     !!!  TAMMAT  !!!

Ni KHADEEJA CANDY Anan na kawo karshen wannan littafi nawa mai suna DEENAH korakuran dake ciki Allah ya yafemin no body is prefect O! Allah i hp 4 ur mrcy do nt leave m 4 myslf crrct ol of my affrs 4 me.

    ni KHADEEJA ABUBAKAR ALKALI ke ce muku 

L❤U~~~OLL 😘

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment