Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayin damuwa tace ” guys wannan fa ba abun dariya bane ku duba abun nan plz ” aliyu zaiyi magana suka ga dinah ta zube kasa!! 

Da gudu suka tashi suka karasa inda take ba suma tayiba jikin nata ne a zube kamar marar lakka.

suka dagata suka sata innuwa suna mata fita maryam da hindatu suka fashe da kuka ita kuma sai hawaye take kamin kace kwabo duk daliban makaranta sukayo kanta. 

Tare da wasu malamai kowa sai tambayar ba asi yake. Babu wanda ya iya cewa ga dalilin, malaman makaranta sukace akira yan gindansu a fada musu ko kuma a dauketa akaita gida. 

Girgixa kai tayi tace ” no plz mutum daya ya iya ya kaini gida ” A hankali ta kalli maryam tace ” plz maryam keda abdul-rashid ku kaini gida ” wani malamin yace ” zaki iya tafiya “? Kai ta daga masa ta shiga kokarin tashi tsaye maryam ta rikata suka tashi tare,

Abdul-rashid ya rika jikarta da takardu suka nufi motar abdul-rashid ganin ita zasu shiga yasa ta kalleshi tace ” plz abdul mu shiga motata ga ki nan hannun maryam plz ” kai ya daga mata ya karbi key din ya nufi motarta.

Baya suka shiga ita da maryam shi kuma ya shiga driver seat yasa ma motar key.

Malamai na musu Allah ya sauwake ya tsare suka fice!! 

Maryam na rungume da ita har suka isa abdul-rashid yayi horn mai gadi ya bude musu gate.

Yanayin parking ya zagayo suka fito da ita ta kalli maryam da abdul-rashid tace ” plz karku fadawa momi kawai kuce faduwa nayi karku cd mata komai plz ” abdul-rashid yace ” saboda mie “? Maryam tace ” nima shi na gani ai kara afada din ” ta dafata ” no plz friends kumin wannan favor plz nasan yadda zan fuskance ta ” abdul rashid ya daga kafada yace ” nidai ba za asamu matsala daga gareni ba saidai ko maryam “?

Maryann tace ” nima haka ” dinah tayi murmushi tace ” tnx u ol ” abdul-rashid yace ” nvr mnd dear ”

Suka nufi parlor. Maryam na rike da ita da sallama suka shiga momi na zaune ita da yan aiki suna hira. Suna amsa sallamar suka yo kanta suna fadin ” lafiya miya sameta “?

zaunar ita sukayi saman kujera momi ta taso tana fadin ” maryam miya sameta “? Maryam shiru tayi tana kallon abdul-rashid bakinta sai motsi yake .

abdul-rashid ne kalli momi yace ” kawai ganin mukayi ta fadi shine sai akace a kawota gida ” momi ta kalli dinah ” dama bakida lafiya ne “? Tayi murmushi tace ” a a banci abinco bane shiyasa sai naji jikina babu kwari ” momi girgixa kai tayi tace ” yayi kyau karki daina ” abdul-rashid ya kalli momi yace ” momi ayi hakuri mu zamu wuce dan munada lacca ” momi tace ” tohm na gode Allah ya saka. Muku da alkhari ”

Sukace ” amin” suka mata sallama suka fice yan aikin suka shiga mata fada wai tana son ta kashe kanta, !!!

Haka dinah ta ni yini momi na fushi da ita da dare dinah ta shiga dakin momi tayi ta ma momi magana momi ta kyaleta babu irin hankurin da bata bata ba amman momi taki ta hakura.

Haka yasa dole dinah ta hakura ta dawo dakinta

saman gado ta fada ta shiga shefarda pillow tana ya musar zanen gadon tana hawaye can kuma ta koma kasan carpet ta zauna tana ta sake sake cikin ranta har bachi ya dauke ta

Washe gari dinah sai da ta cika cikinta sannan tayi shirin makaranta ta nufo dakin momi

Ta dan dade bakin kofa tsaye sannan ta sauke ajiyar zuciya ta shiga.da sallama,

Ciki ciki momi ta amsa mata kanta a kasa tace ” morning momi ” ” morning hw ws ur night “? Dinah tace ” cool momi zanje makaranta ” ” no dinah kin daina zuwa makaranta daga yau ” waje tayi da ido ” but why momi “?

Momi tace ” haka kawai sai in nayi tunani ” dinah tace ” plz momi dn’t do dis to me wlh ba zan karaba momi plz “? Momi ta daga ta kalleta tace ” no na riga na yanke shawarane kuma bana son jin wata magana ki fice min daga daki ” dinah ta matso kusa da ita ta rika hannayenta tace ” momi plz karki min haka wlh bazan karaba ” momi babu alamun wasa a fuskarta tace ” naace miki ki fice ko “?

Kamar ta fasa kuka ta taso ta baro dakin,

Koda ta shigo dakinta har hawaye sun fara mata zuba tana shirin zaunawa ta ga farar takarda saman gadonta daukarta tayi da sauri ta jifar ta windo taja ta rufe.ta zauna gefen gado ta rafka uban tagumi.

Sai dare dinah ta fito dakinta kai tsaye dakin momi ta nufa tana shiga ta fada saman godon momi ta shiga murje2 tana kuka

Momi ta kalleta a fusace tace ” ke dinah ki tashi daga samn gadon nan dan ban daukar miki wannan abunda kike ko abul-khair ba yayinshi ke dai ba yarinyace ” ” wlh ni bazan tashi ba sai kince kin yafe min shikenan kin hanani zuwa makaranta kuma kina fushi dani dan kinga abbah baya nan ” momi taja tsaki ta cigaba da cin abincinta aiko dinah ta cigaba da kuka kamar karamar yarinya har momi ta kare cin abinci ta shiga bathroom ta fito.

Dinah bata dainaba  tun abun na bata haushi har ya fara bata dariya

Ta zauna kusa da ita tace ” tashi yi shiru na yafe miki amman fa bazaki makaranta ba sai abbah kin ya dawo ” dinah ta tashi tana share hawaye tace ” naji nidai ki daina fushi dani ” ta dora kanta saman cinyar momi

Momi tace ” shikenan na daina yar baba wadda bata san ta girma ba ” dariya tayi tace ” ai in ba haka na mikiba bazaki yafe min ba ” momi tace ” naji tashi kije kici abinci ” tashi tayi ta dauki kwanukan da momi taci abinci ta fice.

Tun daga lokacin dinah bata da matsala da momi saidai har yanxu ta hana ta shiga makranta shina kuma bai dame ta sosaiba dan tasan da abbah ta ya dawo zai barta ta koma.kuma gashi sauran kwana biu ya zo

Da dare dinah tana zauna parlor ita da nafisa da zara da zulaiha

suna kallon mbc 2 ana wani horror film

kamar wadda aka tsikara ta tashi ta nufi kitchen

Tea ta shiga hadawa tana yan wake wakenta har ta gama tana shirin fita taga farar takarda a kasa yi tayi kamar ta wuce sai kuma ta tsaya ta dauka ta bude

       ” HI LOV

NASAN ABBAH KI ZAI DAWO RAN FRIDAY KUMA TARE ZASU ZO DA MALIK KUMA U KNOW BANA SON KINA SHIGE MASA DAN HAKA KI KAMA KANKI KUMA KIBAR JEFAR MIN DA WASIKA SAI KIN KARNTA OK “

                     #KISS

sakin kofin tayi ta fito da gudu tana ihu ta shige jikin nafisa

Zulaiha tace ” lafiya “? Dinah tace ” aljani a kitchen “

Duk suka tashi suka wasa da gudu stairs har ita.

bata jiba but kwannan nan tana cikin damuwa ” malik ya kwala mata kira ta fito da sauri tana murmushi.

Ta nufo inda suke tana hada ido ta malik ta dan hade fuska ta rumgume abbah tana ” welcome home dad ” abbah ya shafa kanta yace ” dinah mie yake damunki “? 

Zatayi magana momi ta fito tana murmushi tace ” abbah zara an iso sannu da zuwa ” yana murmushi yace ” yauwa ya gida hajiya “? ” gida kalau muje ciki ka huta ” abbah ya kalli dinah yace ” zamuti magana anjima kinji “? Murmushi tayi ” ok dad haka yayi a huta gajiya ”  kai kawai ya dag mata yana murmushi ya saki hannunta ya nufi part dinsa shida momi

Zara ta rika hannun malik tace ” yaya muje ciki kaima ka huta ” yace ” ok kuje gani zuwa “,!!

Sakar masa hannu tayi suka nufi part din momi. 

Dinah na ganin haka ta saci kallon malik taga yana kallonta kara sanda kanta tayi kasa ta nufi part din momi da sauri

Rikota yayi da karfi yace ” ina zaki we ned to talk ” kwace kanta ta shigayi ” no yaya ba yanzu ba plz ” ” no yanzu zamuyi ” ” a a yaya plz ni na kyaleni ” ta shiga kwalawa momi kira janta yayi ta fada jikinsa yace ” ko abbah zaki kira ba zan sakeke kiba dan haka kara ma kiyi shiru ” ” Tohm shikenan sakeni zan fada maka ” saketa yayi yace ” ina jinki “? Zatayi magana sai kuma tayi shiru sakamakon ringing din da wayarsa tayi,

Kallonta yayi yace ” ina jinki ” ” to bakaji an kirakaba ” harara ya watsa mata yace ” ina ruwanki da wayata “?  ” to yaya in tanada muhimmanci fa ka daga mana plz ” 

Hannu yasa ya ciro wayar yasa a kunne ji nayi yace ” ae ka iso ne “? ” ok gani zuwa ” kashe wayar yayi ya rika hannunta suka nufi gate tace ” yay ina zamu “?  ” Sako zamu karbo ” 

Haka suka fita yana rike da hannuta kamar karamar yarinya. Har suka isa gaban wata mota mai motar ya fito suka gaisa da malik yana murmushi ya kalli dinah yace ” wannan fa “? Wani irin hade fuska malik yayi yace ” ina ruwanka da ita ” murmushi ya sake yi ya fido da wasu takardu cikin motar ya mika masa yace ” ni zan wuce ” malik yace ” ok tnz ” mutumen ya kalli dinah yace ” baby sai anjima ko ” ta dago ta masa murmushi tace ” ok sai anjima ” malik ya shiga fada dashi wai ina ruwansa da ita ita kuma sai kallon gefensa take inda ta cinkayi wata mota kara daga kanta tayi taga ya watso mata wata mugunyar harara fuskarsa a daure. 

Jikinta ya shiga rawa tana kokarin kwace hannunta.,, fisgo ta malik yayi bayan ya kare fada da abokin nashi suka nufo cikin gida 

Har suka shigo parlor jikinta rawa yake tana kuka su zainab da zara sai kallonta suke stairs ya nufa da yana rike da hannunta, 

Saman bed dinta ya zaunar da ita ya aje takardun hannunsa gefenta ya kalleta yace ” dinah mie yake damunki ” kukan kawai take taki tace komai

 zai sake mata magana wayarsa tayi ringing hannu yasa aljihu ya fiddo ta ya duba,

Sakinta naga yayi ya tashi ya fita saida ya rufo kofar dakin sannan ya danna receive ya kara a kunne          banji mie aka ce masa ba na dai ji yace ” gud aikinka yana kyau but tana da bukatar hutu yanzu mu barta har ajima “,!!!
Har yanzu kukan take dukawa yayi gaban ya kama hannayenta yace ” sis mie yake damunki mie kike yiwa kuka haka “?

Fisge Hannuwanta tayi ta juya masa fuska cikin muryar kuka tace ” plz yay ka tashi kabar dakin nan “

Da dan mamaki yace ” why sis mi nayi miki haka “?

” nadai fada maka plz indai kana son na daina kukan nan “

Yace ” but sis ina da bukatar muyi magana ki fada min abunda yake saki haka “?

” yay we cn tlk ltr amman yanzu plz juz ka fita kawai “

Ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya ce komaiba ya tashi ya fice,

Da sake2 ya karaso parlor saman kujera ya zauna ya jinginarda kansa jikin kujerar,

Zara ta kalleshi tace ” yay lafiya kuwa “?

Dagowa yayi ya kalleta ” wlh zara na rasa gane kan dinah bansan mie yake damunta ba “

Zara ta tabe baki tace ” ai dinah yanzu ta chanja wasu da bi’u take da muma mun kasa gane kanta “

” yanzu zara bakisan musabbabin wannan abunba “?

Zara tace ” wlh ni ban saniba yay kasan ba shiri muke da itaba saidai ko zainab “

Da sauri Zainab ta kalleta ” wht!!! Ya zakice ni ni wani shiri mukeyi da ita ne bana son iskancin nan fa ni warinki ce ? Wlh…… “

Tsawa malik yayi mata ” ke daga magana sai ki hau yiwa mutane masifa mie haka “?

” to yaya ya zatace ni nasan wani abu ya za ai nasani “

Hade fuska malik yayi yace “Ke dan Allah rufewa mutane baki tashi ki kawo min ruwa ” ta tashi ta nufi kitchen tana rabon ido tana shiga malik ya kalli zara yace ” kina ganin zainab nada masani akan abunda yake faruwa da dinah “?

Shiru tayi sannan matso kusa dashi tayi kasa da muryarta tace ” haka nake gani yaya dan kasan dinah tana fadawa zainab sirrinta kuma akwai wata rana ina kitchen Zainab da dinah naji suna tautauna irin wannan maganar ”

Da sauri tayi shiru ganin zainab tafe duk suka maida kallonsu gurinta,

Ita kuma sai rabon ido take jikinta na rawa ta aje masa juice da ruwa sai cup guda biu,

Ta taci kallonsa da sauri ta nufi stairs

Zara ta bita da ido malik ya kawarda fuskarsa yana murmushi,

Can kuma ya kalli zara yace ” tashi ki debo min abinci ”

Tashi tayi ta nufi dining room tana fadin ” wane zan zubo maka dan kasan yau ba abinci guda akayi gidan ba “?

Cire hularsa yayi ya dora saman kujera yace ” yace duk wadda kikasan yafi dadi shi zaki xubo min “

Batace komaiba saida ta kare zubawa sannan ta juyo ta kalleshi ” yay gashi na zuba “

” ok kawo min nan zanci “,

Faranti ta dauko ta saka plates din ta nufo inda yake ta dire masa gabansa,

Kuskus ne da farfeson kaza sai kuma white rice da taji vegetables da Sauce,

Zaunawa yayi kasan carpet ya lankwashe kafafunsa. Ya shiga ciki,

yanayi yana murmushi har ya kare sannan ya sha ruwa ya tashi yana hamdallah.

Ya kalli zara yace ” ni zanje gida na dawo “

” ok yay a dawo lafiya ” kai kawai ya daga mata ya nufi kofar fita ita kuma ta shiga kwashe plates din,!!!

Kai tsaye inda yayi parking din motar ya nufa,

Hannu yasa ya bude yana shirin zaunawa yaga farar takarda,

Dauka yayi ya rike saida ya zauna sannan ya bude takarda ya shiga karantawa,


         ” HMMM

KACIKA SHINSHIGI MALIK TUNDA KAGA DINAH BATA SON FADA MAKA KA RABU DA ITA MANA KUMA NASAN KAGA CHANJI YANZU TO TANA NUFI KA FITA HANYAR GABA DAYA KENAN DAN ZAI FI MATA KWANCIYAR HANKALI KAMAR YADDA KAIMA ZAI FI MAKA ZAI FI MAKA DAN HAKA KA FITA HANYAR TA KUMA ZANCI GABA DA SA IDO AKANKA DAN KO YANXU INA TARE DAKAI “

                      #HATE U


da sauri malik ya juya yana duba mazaunin bayan na mota,

Ya sake fita ya bude booth yaga babu komai

Waige2 ya shiga amman baiga wani abu da zai gansarda shi akwai wani tare dashiba,

Yana haka yaga mai gadi ya bude gate wata mota ta kunno kai cikin gidan,

Yanayin parking ko inda malik yake bai kallaba ya nufi kofar parlor

Da sauri malik yasha gaba fuska a hade yace ” waye kai ina zaka “? ” sunana abdul-rashid usman zanje gurin dinah ne ni friend dinta ne “

Malik yace ” to bata nan koma inda ka fito ” daga kafadu yayi yace ” ok inta dawo kace mata best friend dinta yazo “

malik yaja masa tsaki yace ” i sai gt ot “

Juya yayi yana wani irin murmushi dani kaina ban gane na minene ba

ya nufi motarsa

bayan ya shiga ya juyo yayiwa malik wani kallo yana murmushi

ya sawa motar key yayi Reverse mai gadi ya sake bude masa gate ya fice,!!!

Malik ya dade gurin tsaye yana nazari,

Sannan ya nufi motarsa har ya zauna yasa mata key sai kuma naga ya fito,

Ya nufi parlor yana shiga ya kwalawa zara kira daga kitchen ta amsa ” naam yaya gani zuwa ”

Da sauki ya nufi kitchen din yana fadin ” no yi zamanki gani na zo ” tsaye ya tararda ita tana yanka kankana jin gina yayi jikin Fridge yana kallonta yace ” zara wace irin magana kika ji zainab da Dinah sunyi “?

” gaskiya banji sosai mie suke magana kaiba dan kadan kadan sukeyi basu ma san ina cikin kitchen ba “

Rumgume hannayensa yayi yace ” fadamin mana dan nasan bazaki rasa jin bawani abu ba”?

Tsayarda yankan tayi ta tsurawa wukar ido tayi shiru alamar tunani,

sannan ta kalleshi tace ” naji tana cewa dinah wai an turo mata sako har dinah take fada mata wai ranar da kazo din nan zai ya turo mata sako wai dataki jin abunda ya fada mata motarku ta shiga rawa wai kamar zaku mutu ”

Gyara tsayuwarsa yayi yace ” inajinki cigaba “

Tace ” bakin nan naji yay banji sauranba kuma yaya da gaske hakan ya faru daku “?

Ajiyar zuciya ya sauke yace ” zamuyi magana Lttr ok but banason kowa yaji munyi maganar nan plz “

Daga mishi kai tayi ” wlh yay babu wanda wannan btwn us ne “

Murmurshi yayi yace  ” gud haka nake so saina dawo ”

” okay yay a dawo lafiya “

Kai kawai ya daga mata ya fice,!!!

Bai dawo gidan ba sai dare part din abbah ya fara zuwa dan yasan momi tana chan,

Saida yaci abinci suka dan taba fira har kusan 9, sannan yayi mata sallama ya nufo part dinta,

Duk suna zaune parlour suna kallo Dinah na ganinshi ta taso cike da far ah kamar ba ita ba zata tarbe shi, hannu ya daga mata fuskarsa babu yabo babu falasa yace ” no sweet sis zauna warki kawai nima zaman zanyi ” koma tayi ta zauna jikinta a sanyaye dan tasan fushi yake da ita ya samu guri kusa da nafisa ya zauna yana fadin ” dazu koda mukazo baki gida “? Nafisa ta kalleshi tana murmushi tace ” ae ina makaranta koda kuka dawo ya hanya ya kuma aiki “? ” lafiya kalau Nafisa ya yan makaranta an kusa zama dr ko “? Dariya tayi tace ” haka ne yaya kai ya naka aikin “? Ya amsa da ” Alhamdulillah ” suka dan taba fira da ita harsu zara da zainab suka sa baki banda dinah yanayi yana satar kallon dinah da Zainab har kusan 10 sannan ya tashi yana hamma yace ” gud night sisters ni zan wuce ” duk suka masa gud night suma banda dinah da tun dazu takure take kai kawai ya daga musu ya nufi kofar fita saida taga ya ficewa sannan ta tashi da sauri ta nufi inda yake tana fadin ” yaya “? Juyo yayi ya mata murmushin yake yace ” night sis ” ya fice

Bata fuska tayi kamar tayi kuka sai soshe2 take tana satar kallon su zara da nafisa dan tasan dariya zasu mata

Tayi kusan minti 3 a haka chan dai Nafisa taji baza iya jurewa ba tayi dariya tace ” yau naga yay kamar na fushi dake mie kika masa “? Kamar tana jira ta juyo ” ina ruwanki muna fuka kawai yar sa ido Mtswww ” ta watsa mata harara ta nufi stairs,!!!

Washe gari sai kusan la asar malik ya shigo gidan

Zara kawai ya tararda parlor rike da arba’una hadis tana karatu murmushi malik yayi yace ” yayi kyau zara haka nakeso ” ita mayar masa tayi da murmushi tace ” yay sai yanxu ka shigo “? ” ae nadan biya gurin abokina ne ina momi “? ” tana kitchen ” ok kawai yace ya nufi kitchen din

Cike da far ah ya shiga kitchen din yana fadin ” yau momi mie aka dafa “? Momi tayi murmushi tace ” yau dan gidanka nake hadawa ” yana lekawa yaga zobo wani kofin roba naga ya dauko ya tsunbula cikin robar da momi take hada zobon ya shiga dan danawa yana lumshe ido dan yana son zobo sosai musamman ma in momice ta hada shi saida ya shanye sannan ya kalli momi dake faman gyara abarba itada zulaiha Yace ” momi a dan kara suga kuma abarbar nan ta kama basai kin karaba ”

Murmushi momi tace ” to shugaban iya hada zobo “

wata irin dariya malik yayi kamar wadda akabawa rabin kano

Momi ta kalleshi tana girgixa kai tace ” Allah ya gyara ” cikin dariya yace ” amin momi amin ” ya sake cika kofin yasha yana fadin ” momi gora hudu za a ajemin kuma a barsu suyi kankara ”

Ajiyar zuciya momi ta sauke tace ” nidai ba wannan ba magana natsuwa nake son muyi dakai malik ” malik ya gyara tsayuwarsa yace ”  inajinki momi wance irin magana “?

Momi tana wanke hannunta a fanfo tace ” akan maganar Zainab da nafisa da dinah na ” malik yace ” mie sukayi momi “?!!!

Momi tace ” akan maganar aure ne malik kana gani yanxu nafisa ta kusa kamala karatunta amman babu batun aure ga zainab nan ana nema mata aiki ita babu batun auren balle dinah da ta dauki fanni low shiyasa ma kwanan kinnan na hanata zuwa makaranta danni duk yanzu haushi suke bani kowane ka taro kayi masa maganar aure sai ya rika yi maka yawo da hankali “

Malik ya kalli zulaiha yace ” momi wannan maganar bata fi dacewa a daki ba da kinbari munje daki sai muyi maganar “

” a a muyi ta a nan ai duk daya ne nidai so nake kayi musu magan dan kai kawai zaka iya sasu dole suyi abu tunda mahaifinsu ba iya yimusu magana zai yiba in zasu shekara dari sai ranar da su suka kawo maganar auren da kansu kuma ka duba fa ko zara gatan ta kusa girmansu su taru ni kuma bazan sa musu ido ba kai nake so kayi musu magana dan ni yawo suke min da hankali shiyasa ma ni naji dadin zuwanka ” malik yace ” za aiyi yadda kike so momi insha Allah dan nima ki fice soso min inda yake min kaikai naji dadin maganar nan sosai ” momi tace ” karya kake miyasa bakayi ba sai yanzu da kaji nayi “?

Murmushi yace ” to yanzu momi in nayi ai zaki goya min baya sa banin baya kinga in nayi magana za aiya cewa akan bukatar kainane kawai ” ” bukatar kanka kamar ya “? ” na’am…uhmm..ai…..ni. ….no…. nothing ina nufin zaiyi musu magana kawai ”

Momi tace ” haka kan yafi dan ni bakin karatun nan ya isheni basu da aiki sai karatu kamar dashi za asa su kabari na gaji wlh ” malik yayi murmushi yace karki damu momi insha Allah komai zai wuce kamar ba ayiba ” momi ta dauki keys din store ta nufi kofar fita tana fadin ” sai na jika ni na tafi part din babanka ” ” ok mami ” a dawo lafiya ” !!!

Momi na karasa fice kitchen malik ya dawo kofar kitchen din yayi tsaye

saida yaga tabar parlor gaba daya sannan ya juyo yanufo gurin zulaiha fuska a hade ya mika mata hannu ” bani wayarki “?

Zulaiha ta shiga rabon ido tayi kamar bata jishiba ta cigaba da zuba zobon a goro tsawa malik ya katsa mata ” bada ke nake magana yar rainin hankali ki bani wayarki nace ” jikinta na rawa tace ” mie wayata zata maka mie zakayi da wayata “? Wani wawan mari malik yakai mata saida ta saki ihu yace ” bana son gardama dan bana jimirin haka bani nace ” daidai nan zara ta shigo kitchen din tana fadin ” lafiya mie ya faru “? Zulaiha ta kalleshi a fusace tace ” bazan bayar ba zoka kwata ” malik yayi murmushi yana girgixa kai yace ” nice lady “,

Yana rufe baki ya dauko wukar da momi ta yanka abarba da ita ya rika hannun zulaiha ya yanka mata ita nan da nan sai jiki,

Wani irin ihu zara ta saki ta juya a firgice zata bar kitchen din da sauri malik ya jefarda wukar hannunshi ya fisgo ta,

Ya dora hannunshi saman lips dinshi yace ” shiiiiii karki min ihu zara plz inada rising din yi haka jiya naganta part din dad kuma

Please Login or Register in order to submit comment