Join Our WhatsApp Group

BANDIRAWO Complete Hausa Novel Document by BANDIRAWO


BANDIRAWO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 72889



BANDIRAWO

Reading Time: 6 Hours

Added On: 09, Feb 2024

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : moment of life writer's

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 398.14 kb

File Type: txt

Views: 996+

Download: 892+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: *Muhammad kabir*
Documentation work shop
08160112181

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
بسم الله الر حمن الر حيم.

(30/06/2017./11:42 Am)

*BANDIRAWO* pg 1⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w



```Godiya ta tabbata ga Allahu (S.W.A) mai komi mai komai da ya yini musulma ya kuma cikamin zuciyata da imani ya kuma bani rai da lafiya sannan ya k'aramin da konciyar hankali nagode wa Allah da ya bani damar fara rubuta wannan littafi nawa lfy Allahu
rabbi ya nufeni da kammalashi lfy
Ameeen ya rabbil izzati```!..


```Dan Allah masu juya min novels na Ku bari bana so naga wata ko wani ta juyamin NAMIJI BAYA KADAN
har da cire sunana ko mene dalili ban sani ba zancen gsky a kiyaye bana so sam```

Wasu motacin Hilux ne kusan guda goma suka fita daga cikin harabar makarantar sojojin dake jihar Kaduna wato *Jaji* a jere suka danno anci nansu kan babban titin da zai kaisu su zuwa cikin k'oryar birnin kadunan
Hilux biyar ne a gaban wata kyakkyawar mota mai matukar d'aukar hankali k'irar
BMW 7series kalar color ta bak'i mai kyau da sheki hatta glass d'in mai duhuce,
sai Hilux biyar kuma dake binta a baya
tafiya suke cikin gudu da k'aran jiniya da suka karad'e kan titin dashi ,
Sojojin dake cike cikin Hilux d'in gaban BMW 7series da biyar da suke bayan shi duk fuskokin su a mirtuk'e suke ga hancin bindigogin su da suka watsa ta fuskar sauran ababen hawan da ke kaucewa gefen titi suna basu hanya dan jin wannan jiniyar ke shaidawa ma zauna cikin Kaduna cewa yaufa
Brigadier general Aliyu Muhammad Umar Rumoh,
ya shigo gari.

Cikin BMW 7series yake zaune a baya cikin shigar kakin su na sojojin mai cike da tabburan girma kala-kala da ganin kafad'arsa zai ganar da mai kallonshi tabbas wannan babbane ya taka mata kai da dama.

Cikin lumshe ido da yana yinsa na fuskar kad'aici a hakan yana kallon meke gudana a fad'in garin na kd.

Kai tsaye Ugguwar Sarki suka nufa cikin tafiyar su ta tsarin sojojin kwarai.

Ido ya tsurawa kan titin yayin da yake ganin wuce warsu ta dakatar da al'ummah
da dama da yawan cikin su masu kai yaransu makaran ta ne dan tun da a kayi sallah yaune makaran tu suka daddawo hutun sallah,
Phone d'inshi yazaro tare da kallon time cikin d'an jan gajeren tsaki ganin har (7:50 Am) tayi a ranshi, yake tuna wannan fitowar tasa yau yara nawa zata jawa makara zuwa makaran ta? waya san adadin yaran da za'a zane a sana dinshi? cikin jin abin bai mai dad'iba ya juya kanshi d'aya gefen titi nan ma motoci ya gani a jere a baking titin sun basu hanyar wucewa yayin da wasu kuma ma da k'afa suke tafiya wasuma matane suna rike da hannun yaran da nufin kaisu makaran ta wasu kuma yan matane.

Kai ya kuma juyawa cikin jin wani yanayi na sauk'ar mai ganin wata mace a gefen titi ta jawo d'anta da yake ta sa hannu yana tare fuskar sa dan idon rana yana kashe musu ido ganin haka ta cire tafin hannun ta a fuskar ta,
ta tare mai nashi tare da jawoshi jikin ta tana mai shafa kanshi.

Ajiyar zuciya ganeral Aliyu ya sauk'e tare da rumtse idon shi cikin ranshi yake jinjina soyeyya irin ta uwa a kan d'anta so da tausa yawa da k'auna da kulawar uwa abinda shiko tasa uwar ta kasa bashi.

Ido a lumahen ya bud'e baki cikin bada umurni yace.
"Kai Sani kauce bakin titi ka tsaida motar ban son tafiyata
ta tsare ta wasu."


Cikin bin umurni ya juya linzamin motar zuwa gefen titi yayi parking sannan Hilux 5da ke binsu suma suka tsaya,
suma guda biyar dake gaba jin k'arar tsayuwar motocin yasa suka tsaya tare da dirowa daga cikin motocin suka dawo suka zagaye
motar da Aliyu ke cikin suka tsaya cikin yanayin bada tsaro ga uban gidan nasu.
Sani dake gabanne yayi saurin fitowa ganin
Ogan nasu na shirin fita ,
cikin hamzari ya bud'emar marfin motar tare da sara mai.

Cikin zafin nama da jarum ta ya diro daga cikin motar yayin da duk sauran sojojin suka sara mai tare da k'amewa a wurin.

Kai tsaye kan titin ya nufa suko ganin haka yasa suka biyo bayanshi tare da d'ana kunamun bindigogun su .
Jin karan d'anawa wan kata-k'ak'at ya sashi d'aga musu hannu alamun su sauk'e !
ba tareda bata lkciba sukayi k'asa da bindigogin sannan suka tsaya suna masu mmkin me zaiyi kuma me ya fitar dashi yayin da d'aya bank'aren kuma suke tsoron kar wani abu ya sameshi domainko shi jigone ga wannan k'asa tamu ta Nigeria kuma shi Garkuwa ne ga al'ummar wannan k'asa tamu Aliyu shine soja d'aya da sauran rund'unar sojojin k'asa ke jin zasu iya bashi ransu da lfy yarsu dan tsaron lfyarsa domain ko shine daya tamkar da 1000.

yayin da jama'ar gari ko, ke mmkin ganin Wanda suke kaucewa suna bashi hanya sai kuma gashi ya fito yana basu hannu alamun suzo su wuce duk da fuskar sa ba walwala ko fara'a Amman hakan yasa al'ummah sun samu nitsuba dashi yayin da matasa ke bid'ar ganin shi ido a rude a man sai dai su ganshi a fuskar TV da jarida saiko suji jiniyarsa ko suga tawagar sojojin da ke tsaron lfyar sa haka yasa
matasan dake cikin ababen hawa suka rink'a sara mai da cilla mai Addu'ar,
"Allah ya tsare mana kai ya barka ekon bawa mutan kasarmu kariya".

Cikin minti 5 duk ababen hawan sun wuce sai sauran masu tafiyar k'afa sai kuma gashi ababen hawan sun yanke ganin haka ya juya gun matan nan da d'anta daya fara k'olloh yana cewa.
" Mami ni dai bazan jeba don ko naje nayi letti za'a dokeni",
cikin kula ta sunkuyo kan yaro tare da cewa "inkaje ka gaya musu uzurin ka na tabbata zasu barka"

k'arisawa yayi cikin sanyi tare da kauda kai ya mik'awa yaron hannushi,
shima yaro sai yasa nasa hannun cikin nasa yana mai tsoron lek'a fuskarsa shiko jan hannun yaron yayi tare da juyawa zai tafi dashi,
cikin sanyi matar ta bud'e baki da nufin gaya mai makaran da zata kaishi,
hannu ya d'aga mata tare da yin magana a dakile yace.
"ai nasan makaran ta zaki kaishi".

k'ara binsu tayi tare da cewa.
"toh ai bakasan sunan school din nasu ba kuma baka san inda makantar takeba."
cikin kauda kai yace .
"ai kinga ni makaho ne banga inifon d'in dake jikin shiba bare na game ina zan kaishi,
shi kuma yaron kurma ne bazai min bayanin inda zan kaishi ba ko?".

kai ta jinjina tare da juyawa tana mmkin wannan mutumi daga mgn sai fad'a.

Shiko kai tsaye ya d'auki yaron ya kaishi makarantar tasu da taima kon yaron ya kuma hanesu da tab'a yaron.


Kai tsaye suka sake d'iban hanya har cikin Ugguwar Sarki inda gaba d'aya suka cika ugguwar da sowar jiniyar tasu.
wani kata faren gida gidane nagani na fad'a suka dosa kafin su isoma an wangale musu gate cikin iyawa da k'orewa suka kutsa cikin gidan yayin da farfajitar gidan dauke motocin har yana neman k'ari cikin sauri Sani ya fito tare da bud'e mai motar ya fito,
suma sojojin suka rik'a d'iriwo tare da Sara ma,
kai a sunkuye ya d'aga musu hannun tare da yimusu alamar su sauran su tafi lkci d'aya hilux 5 na bayanshi suka juya suka tafi 5 biyar na gaban shi kuma ya wanda ko wanne da sojojin 5 a cikin suko sai suka firfito tare da tsare farfajiyar gidan.
cikin takun kad'aici ya nufi cikin gidan k'ofar ya bud'e tare da kutsa kai cikin wani babban parlour taku biyu yayi ana uku ya tsaya cak tare da d'ago kanshi cikin tsuke fuska.

Ido ta tsura mai cikin murmushin mugunta da salon isa ta watsa mai mugun kallo murya a gadaran ce tace.
"Kai dakata me kake shigo mana gida da gad'ara? da isa ka dai san nan ba cikin Jaji akekeba bare kai mana mulkin mallaka! ka kuwa san
nan ba hurumin ubanka bane bare kai!
bare ka shigo mana kai tsaye cikin gadara!".
Ido kawai ya tsura mata cikin jin zafin kala manta kai ya kawar tare da kaucewa gefen ya nufi wani babban corridor kanshi a k'asa,
cikin sauri ya rumtse idonshi jin furucin ta.
gabanshi ta kuma tahowa tare dayin murmushi cikin cusa bak'ar mgn race.

" Ba laifin ka bane tarbiya ce baka samu ba tun fari,
koda yake ina zaka samu tarbiyar tunda kai rain non gourone dama ina gouro zai iya bada tarbiya!,
ko daya take duk ba laifin Ku bane shi ya k'asa zaboma uwa ta garine tunda gashi ta watsar da kai,
ka zama tantirin d'an duniya! itama ta shiga tata duniyar ! ta watsar da kai ! wai a hakan kake ganin kai d'an sunnane?! waya ma san tsiyar da take shukawa? kai kuma a hakan kakejin uwace ta haifeka? ai duk uwa ta gari zama take ta kula da d'anta !".


Cikin jin zafi da d'aci,
ya k'ara rumtse Idonshi tare da damk'e hannushi zuciyar sa tamkar wutu cikin kwayar idanunshi yakeji kamar rushu aka cusa mai lkci d'aya kanshi ya ringa wani irin mugun sarawa.

Cikin azama ya rab'a gefen ta ya wuce da sauri kai tsaye cikin bedroom ya wuce bindigan shi ya cillah gefen tareda fad'awa kan gadon cikin karfi ya rarumi......


10:00 Am
03/07/2017
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* pg 2⃣ Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w

www.aishaaligarkuwa.blogspot.com

*Masoya na yadda baku manta dani ba hakalazali ka bazan manta da kuba har kullum kuna raina dan farin cikinku na fara wannan novel din kuyi hakurin rashin ganin Noor ala Noor kasuwace ta cinyeshi*


Kanshi ya raruma ya matse dan jin kanshi yake tamkar zai dare zuciyar sa tamkar tayi bindiga sai wani irin harbawa take,
a ranshi yake jin hak'ik'a Mama tana gasa zuciya ta da rayuwa ta da ruhina da mugayen kala manta inama ace zan samu hawaye ya zubo min da na samu sauk'i,
kai ya kuma turawa cikin pillows tare da matse kanshi lkci d'aya kuma tunanin shi ya tafi kan
lallai jirwaye ne mai kama da wanka Mama ta mai ai ba k'arya tayiba na rasa so da k'auna da gata da kowanne d'a yake buk'ata a gun mahaifan shi,
shin laifin me nayiwa iyaye na suka sani cikin rayuwar k'unci da kad'aici ase iyaye zasu haifa su guda, tun yarinta na rasa gatan uwa gashi har rayuwa ta juya dani ga zuwa mata kin girma rashin masoyi a duniya shi yasa na kasan ce Sojo zuwa yanzu na wayi gari a duniya duk wani motsina da numfashi na sun k'are kan kare kasata da al'ummah ta duk bayan minti d'aya mutuwa ke kara matsoni yayin da har yanzu ban samu mai sharemin hawaye naba shin ni Aliyu sai yaushe zan samu kula da k'auna.

Tunanin yake tunanin dake kara soya mai zuciya dasashi cikin kad'aici yana cikin azabar kunan zuciya yaji motsin mutun kusa dashi ba tare daya juyoba,
ya gane
Ya Amir ne dan yasan shi kad'ai ke damuwa da damuwar sa sai Nafeesat. Autar su.

Cikin kula Amir ya dafa kafad'ar sa murya a sanyayye yace.
"Aliyu kai hak'uri hak'ik'a nasan mahaifi yata bata kyauta maka tabbas nasan tana k'untuka maka bak'in ciki,
amman bamu da mafita a kullum zan baka haquri ne tunda ba yadda na iya da ita,
d'an uwana kai haquri insha Allah farin ciki zai cika rayuwar ka na tabbata yadda kake kula da qasarka kaima Allah zai kula da farin cikin ka!"

Shiru yayi ba tare da yayi mgn ba bare ya kulashi ko ya tanka mai,
shi kam Amir inda sabo ya saba da halin rayuwar Aliyu Amman shi ya dangana abin da rayuwar kad'aici d'aya tashi a ciki shi yasa baida yawan mgn ko fara'a ko shiga harkar wani sam shi baida shiga hurumin daba nashiba.

Ganin yayi shirun yasashi ya fice daga part en nashi kai tsaye part enshi ya nufa gun matar sa Aysha.

A d'akin Mama kuwa Nafeesat ce tabi bayan ta bayan ta gama yiwa. Aliyu rashin mutin ci cikin sanyi Nafeesat ta kalleta murya na rawa tare da zubda qollah tace .
"Ayyah Mama meya sa kike yiwa Hamma Aliyu haka meyasa kike banbanta shi damu da kika haifa Mama Hamma Aliyu bai cutar dake da komai ba,
kuma
ke kinfi kowa sanin da uwarsa da ubansa kina sane Babanmu da Abban Hamma Aliyu uwa d'aya uba d'aya suke .Amman Mama meyasa kike jifarsa da kalmar son shegan tashi,
Mama kin san ba abinda kewa Hamma Aliyu ciwo a ransa a duniya kamar rasa kula war iyayenshi ! Amman kullum yazo sai kin tuna mai ! ko kina bin iyayenshi da mugayen kalamai ! Mama kina qoqarin sawa Hamma Aliyu qiyeyyar iyayen shi ! Mama me ribar ki in kika haddasa qiyeyyar?".

Cikin fuskar tsana ta kalli 'yartata tare da cewa.
" Wlh Nafeesat ko ke da Amir da kuke rabar Aliyu yasa ina jinku kamar ba ni na haifeku ba,
Wlh ina dab dana yafewa Aliyu Ku sam baku da kishina.
Abdul ne kad'ai yasan kimata ,
Wlh daga Yau sai Yau ki kuma shiga batuna da Aliyu sai naci ubanki har zakizo kina cemin ban kyauta ba,
bai dace nai kaza da kaza ba wato ke ga uwata toh wlh bari kiji muddin ina raye Aliyu bazai yi farin cikiba kuma har a bada bazai samu kulawar uwarsa ba".

Cikin tsawa tace "kauce ki bani wuri "
Jiki a mace ta miqe tare da cewa.
"Mama kiyi haquri ki gafar ceni".

Shi kam Aliyu wunin wannan rana ya wuni cikin bak'in ciki da tunani ba abinda ke ta dashi sai sallah ko parlourn shi bai fito ba a haka yai ta saqe-saqe a ranshi haka ya wuni har zuwa dare ba abida ya iya ci sai dan ruwan tea da ya sha abu kamar wasa har zuwa 1 baiyi bacci ba yana konce kan d'an qaramin gado duk da kyauwun gidan da tsarinshi gadon konciyar sa kuma da durowan duk na dane cikin tunanin ya juya rufda da ciki,
a hankali ya bud'e baki murya na rawa yace.
" Abba na mai nai maka ka hukun tani da sakar min mahaifi yata ?
Abbana meya sa kaima ka gujeni ?
Ko kana ganin ka barni gidan d'an uwanka ne shi yasa?
shin Abba baka san Mama tafi karfin Baba ba ?!"

Sai ya kuma juyawa cikin sanyi yaja borgon jikin gadon tare da cewa.
"Ammi ashe mutun zai haifa ya gudu ya bari ! ashe mace bazata iya haqurin zaman gidan auren taba ko dan ta raini yaran ta,
ta basu tarbiya ta sasu farin ciki!
Ammin ashe uwa na qin d'anta?
kin tafi kin barni baki tuna ya zanyi yarin tata ba kin...


Read / Download BANDIRAWO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album