Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*Muhammad kabir*
Documentation work shop
08160112181

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
بسم الله الر حمن الر حيم.

(30/06/2017./11:42 Am)

*BANDIRAWO* pg 1⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w



```Godiya ta tabbata ga Allahu (S.W.A) mai komi mai komai da ya yini musulma ya kuma cikamin zuciyata da imani ya kuma bani rai da lafiya sannan ya k'aramin da konciyar hankali nagode wa Allah da ya bani damar fara rubuta wannan littafi nawa lfy Allahu
rabbi ya nufeni da kammalashi lfy
Ameeen ya rabbil izzati```!..


```Dan Allah masu juya min novels na Ku bari bana so naga wata ko wani ta juyamin NAMIJI BAYA KADAN
har da cire sunana ko mene dalili ban sani ba zancen gsky a kiyaye bana so sam```

Wasu motacin Hilux ne kusan guda goma suka fita daga cikin harabar makarantar sojojin dake jihar Kaduna wato *Jaji* a jere suka danno anci nansu kan babban titin da zai kaisu su zuwa cikin k'oryar birnin kadunan
Hilux biyar ne a gaban wata kyakkyawar mota mai matukar d'aukar hankali k'irar
BMW 7series kalar color ta bak'i mai kyau da sheki hatta glass d'in mai duhuce,
sai Hilux biyar kuma dake binta a baya
tafiya suke cikin gudu da k'aran jiniya da suka karad'e kan titin dashi ,
Sojojin dake cike cikin Hilux d'in gaban BMW 7series da biyar da suke bayan shi duk fuskokin su a mirtuk'e suke ga hancin bindigogin su da suka watsa ta fuskar sauran ababen hawan da ke kaucewa gefen titi suna basu hanya dan jin wannan jiniyar ke shaidawa ma zauna cikin Kaduna cewa yaufa
Brigadier general Aliyu Muhammad Umar Rumoh,
ya shigo gari.

Cikin BMW 7series yake zaune a baya cikin shigar kakin su na sojojin mai cike da tabburan girma kala-kala da ganin kafad'arsa zai ganar da mai kallonshi tabbas wannan babbane ya taka mata kai da dama.

Cikin lumshe ido da yana yinsa na fuskar kad'aici a hakan yana kallon meke gudana a fad'in garin na kd.

Kai tsaye Ugguwar Sarki suka nufa cikin tafiyar su ta tsarin sojojin kwarai.

Ido ya tsurawa kan titin yayin da yake ganin wuce warsu ta dakatar da al'ummah
da dama da yawan cikin su masu kai yaransu makaran ta ne dan tun da a kayi sallah yaune makaran tu suka daddawo hutun sallah,
Phone d'inshi yazaro tare da kallon time cikin d'an jan gajeren tsaki ganin har (7:50 Am) tayi a ranshi, yake tuna wannan fitowar tasa yau yara nawa zata jawa makara zuwa makaran ta? waya san adadin yaran da za'a zane a sana dinshi? cikin jin abin bai mai dad'iba ya juya kanshi d'aya gefen titi nan ma motoci ya gani a jere a baking titin sun basu hanyar wucewa yayin da wasu kuma ma da k'afa suke tafiya wasuma matane suna rike da hannun yaran da nufin kaisu makaran ta wasu kuma yan matane.

Kai ya kuma juyawa cikin jin wani yanayi na sauk'ar mai ganin wata mace a gefen titi ta jawo d'anta da yake ta sa hannu yana tare fuskar sa dan idon rana yana kashe musu ido ganin haka ta cire tafin hannun ta a fuskar ta,
ta tare mai nashi tare da jawoshi jikin ta tana mai shafa kanshi.

Ajiyar zuciya ganeral Aliyu ya sauk'e tare da rumtse idon shi cikin ranshi yake jinjina soyeyya irin ta uwa a kan d'anta so da tausa yawa da k'auna da kulawar uwa abinda shiko tasa uwar ta kasa bashi.

Ido a lumahen ya bud'e baki cikin bada umurni yace.
"Kai Sani kauce bakin titi ka tsaida motar ban son tafiyata
ta tsare ta wasu."


Cikin bin umurni ya juya linzamin motar zuwa gefen titi yayi parking sannan Hilux 5da ke binsu suma suka tsaya,
suma guda biyar dake gaba jin k'arar tsayuwar motocin yasa suka tsaya tare da dirowa daga cikin motocin suka dawo suka zagaye
motar da Aliyu ke cikin suka tsaya cikin yanayin bada tsaro ga uban gidan nasu.
Sani dake gabanne yayi saurin fitowa ganin
Ogan nasu na shirin fita ,
cikin hamzari ya bud'emar marfin motar tare da sara mai.

Cikin zafin nama da jarum ta ya diro daga cikin motar yayin da duk sauran sojojin suka sara mai tare da k'amewa a wurin.

Kai tsaye kan titin ya nufa suko ganin haka yasa suka biyo bayanshi tare da d'ana kunamun bindigogun su .
Jin karan d'anawa wan kata-k'ak'at ya sashi d'aga musu hannu alamun su sauk'e !
ba tareda bata lkciba sukayi k'asa da bindigogin sannan suka tsaya suna masu mmkin me zaiyi kuma me ya fitar dashi yayin da d'aya bank'aren kuma suke tsoron kar wani abu ya sameshi domainko shi jigone ga wannan k'asa tamu ta Nigeria kuma shi Garkuwa ne ga al'ummar wannan k'asa tamu Aliyu shine soja d'aya da sauran rund'unar sojojin k'asa ke jin zasu iya bashi ransu da lfy yarsu dan tsaron lfyarsa domain ko shine daya tamkar da 1000.

yayin da jama'ar gari ko, ke mmkin ganin Wanda suke kaucewa suna bashi hanya sai kuma gashi ya fito yana basu hannu alamun suzo su wuce duk da fuskar sa ba walwala ko fara'a Amman hakan yasa al'ummah sun samu nitsuba dashi yayin da matasa ke bid'ar ganin shi ido a rude a man sai dai su ganshi a fuskar TV da jarida saiko suji jiniyarsa ko suga tawagar sojojin da ke tsaron lfyar sa haka yasa
matasan dake cikin ababen hawa suka rink'a sara mai da cilla mai Addu'ar,
"Allah ya tsare mana kai ya barka ekon bawa mutan kasarmu kariya".

Cikin minti 5 duk ababen hawan sun wuce sai sauran masu tafiyar k'afa sai kuma gashi ababen hawan sun yanke ganin haka ya juya gun matan nan da d'anta daya fara k'olloh yana cewa.
" Mami ni dai bazan jeba don ko naje nayi letti za'a dokeni",
cikin kula ta sunkuyo kan yaro tare da cewa "inkaje ka gaya musu uzurin ka na tabbata zasu barka"

k'arisawa yayi cikin sanyi tare da kauda kai ya mik'awa yaron hannushi,
shima yaro sai yasa nasa hannun cikin nasa yana mai tsoron lek'a fuskarsa shiko jan hannun yaron yayi tare da juyawa zai tafi dashi,
cikin sanyi matar ta bud'e baki da nufin gaya mai makaran da zata kaishi,
hannu ya d'aga mata tare da yin magana a dakile yace.
"ai nasan makaran ta zaki kaishi".

k'ara binsu tayi tare da cewa.
"toh ai bakasan sunan school din nasu ba kuma baka san inda makantar takeba."
cikin kauda kai yace .
"ai kinga ni makaho ne banga inifon d'in dake jikin shiba bare na game ina zan kaishi,
shi kuma yaron kurma ne bazai min bayanin inda zan kaishi ba ko?".

kai ta jinjina tare da juyawa tana mmkin wannan mutumi daga mgn sai fad'a.

Shiko kai tsaye ya d'auki yaron ya kaishi makarantar tasu da taima kon yaron ya kuma hanesu da tab'a yaron.


Kai tsaye suka sake d'iban hanya har cikin Ugguwar Sarki inda gaba d'aya suka cika ugguwar da sowar jiniyar tasu.
wani kata faren gida gidane nagani na fad'a suka dosa kafin su isoma an wangale musu gate cikin iyawa da k'orewa suka kutsa cikin gidan yayin da farfajitar gidan dauke motocin har yana neman k'ari cikin sauri Sani ya fito tare da bud'e mai motar ya fito,
suma sojojin suka rik'a d'iriwo tare da Sara ma,
kai a sunkuye ya d'aga musu hannun tare da yimusu alamar su sauran su tafi lkci d'aya hilux 5 na bayanshi suka juya suka tafi 5 biyar na gaban shi kuma ya wanda ko wanne da sojojin 5 a cikin suko sai suka firfito tare da tsare farfajiyar gidan.
cikin takun kad'aici ya nufi cikin gidan k'ofar ya bud'e tare da kutsa kai cikin wani babban parlour taku biyu yayi ana uku ya tsaya cak tare da d'ago kanshi cikin tsuke fuska.

Ido ta tsura mai cikin murmushin mugunta da salon isa ta watsa mai mugun kallo murya a gadaran ce tace.
"Kai dakata me kake shigo mana gida da gad'ara? da isa ka dai san nan ba cikin Jaji akekeba bare kai mana mulkin mallaka! ka kuwa san
nan ba hurumin ubanka bane bare kai!
bare ka shigo mana kai tsaye cikin gadara!".
Ido kawai ya tsura mata cikin jin zafin kala manta kai ya kawar tare da kaucewa gefen ya nufi wani babban corridor kanshi a k'asa,
cikin sauri ya rumtse idonshi jin furucin ta.
gabanshi ta kuma tahowa tare dayin murmushi cikin cusa bak'ar mgn race.

" Ba laifin ka bane tarbiya ce baka samu ba tun fari,
koda yake ina zaka samu tarbiyar tunda kai rain non gourone dama ina gouro zai iya bada tarbiya!,
ko daya take duk ba laifin Ku bane shi ya k'asa zaboma uwa ta garine tunda gashi ta watsar da kai,
ka zama tantirin d'an duniya! itama ta shiga tata duniyar ! ta watsar da kai ! wai a hakan kake ganin kai d'an sunnane?! waya ma san tsiyar da take shukawa? kai kuma a hakan kakejin uwace ta haifeka? ai duk uwa ta gari zama take ta kula da d'anta !".


Cikin jin zafi da d'aci,
ya k'ara rumtse Idonshi tare da damk'e hannushi zuciyar sa tamkar wutu cikin kwayar idanunshi yakeji kamar rushu aka cusa mai lkci d'aya kanshi ya ringa wani irin mugun sarawa.

Cikin azama ya rab'a gefen ta ya wuce da sauri kai tsaye cikin bedroom ya wuce bindigan shi ya cillah gefen tareda fad'awa kan gadon cikin karfi ya rarumi......


10:00 Am
03/07/2017
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* pg 2⃣ Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w

www.aishaaligarkuwa.blogspot.com

*Masoya na yadda baku manta dani ba hakalazali ka bazan manta da kuba har kullum kuna raina dan farin cikinku na fara wannan novel din kuyi hakurin rashin ganin Noor ala Noor kasuwace ta cinyeshi*


Kanshi ya raruma ya matse dan jin kanshi yake tamkar zai dare zuciyar sa tamkar tayi bindiga sai wani irin harbawa take,
a ranshi yake jin hak'ik'a Mama tana gasa zuciya ta da rayuwa ta da ruhina da mugayen kala manta inama ace zan samu hawaye ya zubo min da na samu sauk'i,
kai ya kuma turawa cikin pillows tare da matse kanshi lkci d'aya kuma tunanin shi ya tafi kan
lallai jirwaye ne mai kama da wanka Mama ta mai ai ba k'arya tayiba na rasa so da k'auna da gata da kowanne d'a yake buk'ata a gun mahaifan shi,
shin laifin me nayiwa iyaye na suka sani cikin rayuwar k'unci da kad'aici ase iyaye zasu haifa su guda, tun yarinta na rasa gatan uwa gashi har rayuwa ta juya dani ga zuwa mata kin girma rashin masoyi a duniya shi yasa na kasan ce Sojo zuwa yanzu na wayi gari a duniya duk wani motsina da numfashi na sun k'are kan kare kasata da al'ummah ta duk bayan minti d'aya mutuwa ke kara matsoni yayin da har yanzu ban samu mai sharemin hawaye naba shin ni Aliyu sai yaushe zan samu kula da k'auna.

Tunanin yake tunanin dake kara soya mai zuciya dasashi cikin kad'aici yana cikin azabar kunan zuciya yaji motsin mutun kusa dashi ba tare daya juyoba,
ya gane
Ya Amir ne dan yasan shi kad'ai ke damuwa da damuwar sa sai Nafeesat. Autar su.

Cikin kula Amir ya dafa kafad'ar sa murya a sanyayye yace.
"Aliyu kai hak'uri hak'ik'a nasan mahaifi yata bata kyauta maka tabbas nasan tana k'untuka maka bak'in ciki,
amman bamu da mafita a kullum zan baka haquri ne tunda ba yadda na iya da ita,
d'an uwana kai haquri insha Allah farin ciki zai cika rayuwar ka na tabbata yadda kake kula da qasarka kaima Allah zai kula da farin cikin ka!"

Shiru yayi ba tare da yayi mgn ba bare ya kulashi ko ya tanka mai,
shi kam Amir inda sabo ya saba da halin rayuwar Aliyu Amman shi ya dangana abin da rayuwar kad'aici d'aya tashi a ciki shi yasa baida yawan mgn ko fara'a ko shiga harkar wani sam shi baida shiga hurumin daba nashiba.

Ganin yayi shirun yasashi ya fice daga part en nashi kai tsaye part enshi ya nufa gun matar sa Aysha.

A d'akin Mama kuwa Nafeesat ce tabi bayan ta bayan ta gama yiwa. Aliyu rashin mutin ci cikin sanyi Nafeesat ta kalleta murya na rawa tare da zubda qollah tace .
"Ayyah Mama meya sa kike yiwa Hamma Aliyu haka meyasa kike banbanta shi damu da kika haifa Mama Hamma Aliyu bai cutar dake da komai ba,
kuma
ke kinfi kowa sanin da uwarsa da ubansa kina sane Babanmu da Abban Hamma Aliyu uwa d'aya uba d'aya suke .Amman Mama meyasa kike jifarsa da kalmar son shegan tashi,
Mama kin san ba abinda kewa Hamma Aliyu ciwo a ransa a duniya kamar rasa kula war iyayenshi ! Amman kullum yazo sai kin tuna mai ! ko kina bin iyayenshi da mugayen kalamai ! Mama kina qoqarin sawa Hamma Aliyu qiyeyyar iyayen shi ! Mama me ribar ki in kika haddasa qiyeyyar?".

Cikin fuskar tsana ta kalli 'yartata tare da cewa.
" Wlh Nafeesat ko ke da Amir da kuke rabar Aliyu yasa ina jinku kamar ba ni na haifeku ba,
Wlh ina dab dana yafewa Aliyu Ku sam baku da kishina.
Abdul ne kad'ai yasan kimata ,
Wlh daga Yau sai Yau ki kuma shiga batuna da Aliyu sai naci ubanki har zakizo kina cemin ban kyauta ba,
bai dace nai kaza da kaza ba wato ke ga uwata toh wlh bari kiji muddin ina raye Aliyu bazai yi farin cikiba kuma har a bada bazai samu kulawar uwarsa ba".

Cikin tsawa tace "kauce ki bani wuri "
Jiki a mace ta miqe tare da cewa.
"Mama kiyi haquri ki gafar ceni".

Shi kam Aliyu wunin wannan rana ya wuni cikin bak'in ciki da tunani ba abinda ke ta dashi sai sallah ko parlourn shi bai fito ba a haka yai ta saqe-saqe a ranshi haka ya wuni har zuwa dare ba abida ya iya ci sai dan ruwan tea da ya sha abu kamar wasa har zuwa 1 baiyi bacci ba yana konce kan d'an qaramin gado duk da kyauwun gidan da tsarinshi gadon konciyar sa kuma da durowan duk na dane cikin tunanin ya juya rufda da ciki,
a hankali ya bud'e baki murya na rawa yace.
" Abba na mai nai maka ka hukun tani da sakar min mahaifi yata ?
Abbana meya sa kaima ka gujeni ?
Ko kana ganin ka barni gidan d'an uwanka ne shi yasa?
shin Abba baka san Mama tafi karfin Baba ba ?!"

Sai ya kuma juyawa cikin sanyi yaja borgon jikin gadon tare da cewa.
"Ammi ashe mutun zai haifa ya gudu ya bari ! ashe mace bazata iya haqurin zaman gidan auren taba ko dan ta raini yaran ta,
ta basu tarbiya ta sasu farin ciki!
Ammin ashe uwa na qin d'anta?
kin tafi kin barni baki tuna ya zanyi yarin tata ba kin barni baki tuna ilimi naba baki tuna tarbiya taba Ashe laifin uba zai shafi d'an da kika haifa !
Ayyah Abba ai duk laifin da Ammi tama yaci kama ta uzuri ko dan ni,
sam kun k'asa tuna makomata".

Haka yai ta suru tai cikin kad'aici inda sabo ya saba zaman kad'aici tunda tun yana d'an shekara 4 yake kwana shi kad'ai.

Gajiya da damuwar ya,
ya miqe ya shiga toilet alwala yayi sannan yazo yayi ta nafilfilin da karatu qura'ani har ya fara jin bacci na d'ibarsa cikin sanyi ya ninke shimfid'ar ya bud'e 'yar durowar zai ajiye a hankali idonshi ya sauk'a kan yinifon din shi dai dai kan saman qirjin rigar sa ya duba sunan shi ya karance
*Aliyu Muhammad Umar Rumoh*
*Rumoh* ya kuma maimata karshen sunan nashi
a hankali ya dawo kan gadon ya zauna cikin tunanin ya jawo na'urar yanar gizo-gizo gizonsa laptop enshi,
kamar yadda yake binci ken masu laifin a cikin daji haka ya fara binci ke kan wannan suna na Rumoh forko cikin jihar kd ya fara laluba yayi har ya gaji babu anguwa ko qauye mai wannan suna daga kd ! katsina ya tsallaka domai tabbas yasan su fulani ne'
katsinanma ba nasara !
daga nan sai Kano ta dabo sam ba nasara a nan ma !
sai kuma ya diro jihar Gombe nan ma ba canji sai ya kuma tsallah kawa bauchi canma babu,
haka yayi ta laluben jihonin Nageria har zuwa jihohin kudu a hankali daga Abbah ya dawo da hasashen shi cikin jihar Adamawa Yola ya gama binciken sa sam babu gaba d'aya zuwa yanzu idonshi ya fara rufewa a fili
yace.
"Rumoh canne asali na tunda ya zama inkiyar iyayena toh amman ya zanyi na ganesu har na gano Zuriya ta,
jawo laptop din yayi har zai rude idonshi ya dira kan Taraba Jaligo a hankali yace,
"Canma garin fulanine "
forko babban lokal gmt esu ya kafawa ido *Gembu* ya fad'i
tare da sake cusa kai cikin babban lardinsu can qasa gefen yaga *Membila*
daga qasan shi kuwa sai sunayen rigar fulanine dake zagaye da dutsen membilan cikin sa'a yayi tozali da *Rumoh* garin mai cike da Fulani makiyaya ga dutsen membila daya zagaye su yayi musu qawanya daga bayan su kad'an kuma kokin membila ne zagaye dasu,
sai babbar gadar da akayi daga saman garin nasu gadar babban sai dai ta kata koce yayin da rigar Rumoh ta kasan ce a bakin gaba bayan garin kuwa dutsen membila ne d'aya kasan ce farin ciki ga d'aukacin al'ummar wurin ya kuma kasan ce abin ziyartar turawa da baqaqen mu ta yadda ya zama lardin wurin ya zama babbar hanyace konce kan dutsen hanya mai salon tafiyar maciji yayin da qasan kuma kogine gefen kuma tabki ne mai girma gaske can daga saman su kuma forres iya ganin mai kallo,
garin Rumoh kenan da Aliyu ya gama binci ke a cikin Sa,
dukda bai gamsuba Amman ya gudurta tafiya cikin kwana nan biyu masu zuwa yashirya tafiya tun kan hutun shi ya qare!..

Haka Aliyu yayi ta shiryer-shiryen shi shi kad'ai ba tare da neman shawaran kowa ba sai Baba da yacewa an turashi taraba wani bincike.

Daga manya shi biyu kuma a wurin aiki an bashi pars na tsawon 2 weeks.


Yau jummah tun safe Sani ya had'a kan sojojin da zasuwa Aliyu rakiyi Wanda an hadasu da sabbin Hilux dan sanin hanyar da zasu dosa hilux 6 da sojojin 27 aka had'a sukayi sammako tun sanyin safiya suka nufi hanyar Adamawa Yola,
yayin da shiko Aliyu da Sani jirgi zasubi zuwa cikin Adamawa dan babu na Taraba,
sai na Kaduna 2 Yola suka samu hakan yasa sai dai su diro jihar Adamawa daganan su ma tawagar sojojin dake ta howa a motocin sun iso daga Yolo sai su kama hanyar Taraba da mota.

Su sun tashi tun safe,
suko sai 4 na yamma jirgisu ya tashi zuwa Yola.

4:25 pm jirginsu yayi diran mikiya cikin..!!!!!!


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* pg 3⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*pure moment of life writers*
P.m.l.w


jirginsu ya dira cikin International
Airport na Yola,
bayan d'an wani lkcin matafiyan suka rinqa fitowa d'aya bayan d'aya,
cikin sanyi General Aliyu ya zuro qafarsa tare da shaqar iskar garin Adamawa Yola ,
Sani na biye dashi a bayan shi cikin salon shi na murtuqe fuska suka sauqo yayin da
Airport din ya ke cike da sojoji maqil,
domin ko ya samu tarba daqa shugaban sojoji na jihar Adamawa tare da tarban fadawan masarautar Sarki Muhammad barkind'o,
don karramawa ga jarumin dake sadaukar da ransa domin baiwa qasarsa kariya.

Kai tsaye daga Airport din cikin Yola suka nufa domin kai gaisuwa ga Sarki Muhammad,
daga nan kuwa barrack suka dawo inda nanma suka gaisa sama-sama daga nan suka fito suka kama hanyar Taraba.

Tafiya suke cikin gudu dan su samu su isa da wuri
tunda Yola 2 Taraba tafiyar awa 3 ne
bare su suna tsula gudu,
uwa uba kuma su duk inda suka biya basu hanya ake,
shi yasa 9:00 pm suna cikin birnin Taraba jaligo ja gari na baba Abasu.

Barrack din suka wuce tare da tarbar mutanen jihar
a barrack din ya diro sauran sojojin yayinda ya fita shida captain Sani suka wuce jummu hotel dakin Sani na qasan nashi ,
shi kad'ai ya tare a dakinshi daga shi sai tunanin shi da ya cika mar rayuwa wonka ya samu danyi sannan yazo ya kwanta tare da jawo laptop enshi ya fara aiyukan shi tare da banda umurni ga sojojin da suke qarqashin sa,
haka dai baiyi bacci ba har zuwa 12:30: Am sannan ya d'an rumtsa.

Kashe gari suna idar da sallah suka kammala shirin su suka kama hanyar Gembu,

Tafiya mai dad'i hanya mai cike da abin al'ajibi hanya mai tarin abin sha'awa hanyar da duk fad'in qasarmu ta Nigeria bamu da irinta
hanya mai cike da tsirrei da qoramu da koguna da lambuna tare da sanyi mai dad'in ji yanayi mai sanya sanyi a zuciyar bani Adama
hanyar Gembu 2 Membila kenan.


Shi kam Aliyu zaune yake a bayan yayinda yake tsurawa dajin ido mamaki
yake ganin yadda fulani sukawa dajin qawanya duk inda ya cillah idonshi dabbobi yake gani bila adadin sai mata masu fasa cikin dajin da qoren nono da ka shigo sashin wurin zakaga banbanci matan wurin da sauran matan sauran jihohinmu wannan ba shati fadi bane
matan Gembu sunyi zarrar da tasa sunka doke matan kamaru ma
Kyawun halitta haiba cikar zati uwa uba tsafta duk wanda yasan matan Gembu ya sansu tamkar larabawa suke
fararene tas

Please Login or Register in order to submit comment