Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma kan kujeran ya zauna,
Captain Sani dake bakin qofar ganin yadda yake a murtuqe yasa ya shigo cikin sanyi,
can gefen Meenal ya dire Trolley da ya shigo dashi tare da qatuwar jaka sannan ya zauna gaban ta kad'an,
ita kuwa Meenal ganin shi yasa ta d'an sake tare da share hawayen ta,
shiko General ko inda suke bai kuma kollo ba.

A hankali ya bud'e trolleyn cikin sanyi yace.
"Meenal ga kayan ki."

Shiru tayi tare da tsurawa kayan ido.
D'inku nane masu kyau na zamani na gani na fad'a sannan ga dogayen riguna zubin larabawa sai kuma riguna da siket yar kanti sabbin zubi sannan ga hijabai manya masu kyau sai su onthis nata masu laushi da tashi sannan d'aya jakar kuma takal mane a ciki masu kyau sai mayuka da turaruka su shampoo dai kala-kala sai man gashi da dai sauran kayan buqata na matan zamani,
ido ta kuma tsurawa yan d'inku nan da aka mata masu kyau lokaci d'aya taji sanyi a ranta zata cire wannan riga mai dogon hannu,
a hankali ta bud'e baki tace.
"Na gode."

Ido ya qifta mata cikin rad'a da alama da ido yace.
"Oga ne ya saya miki shi zakiyi wa godiya."

Kai ta juya ta kalleshi ganin baya ko kallon inda suke yasa ta juya cikin sanyi ta kad'a kai a hankali tace.
"Zaiyi fad'a."

Kai ya girgiza mata tare da cewa.
"Kije kimai godiya."

Yana fad'in haka ya miqe tare da cewa.
"Oga bari naje na watsa ruwa."
Baiyi magana ba kuma bai bud'e ko idon shiba.

Shi dai Sani yayi gaba abin shi,
Ita kuwa cikin sanyi ta matso gunshi a hankali tace.
"( mi yetti masin) na (gode sosai,)
Allah ya saka."

Bai kula taba sai miqewa da yayi ya shige cikin bedroom d'in kai tsaye ya wuce toilet ruwa ya d'an watsa da sauri-sauri sannan yayi al'walah yana fita ya kimtsa sannan ya fesa turare mai sanyi da qamshi sannan ya fito,
a parlour ya same ta zaune tana ta ninke kayan fita yayi ya nufi masallah ci,
a qofar fitan ya had'u da Nafeesat dake shirin shiga part d'in nasu tana ganin shi tai sauri ta matsa baki na rawa tace.
"Hamma Aliyu zanje gun Meenal ne."
tsaki ya d'an ja cikin tsuke fuska yace.
"Na tabba yeki ne da zaki tsaya min surutu kamar parrot."

Kai kawai take juya mashi tare da rab'awa gefen shi ta wuce cikin parlour tana murmushi a ranta tace .
"Nagode dai da baka hanani shiga ba."

Shiko fita yayi ba tare daya kuma sauraron taba.

Tana shiga cikin sanyi ta isa kusa da ita gefenta,
ta zauna a hankali tace.
"Meenal kina da kyau."

Murmushi tayi tace.
"Na gode."

Kallon ta ta kuma yi tace.
"Wallahi naji ina sonki kinmin kyau gaki da gashi,
dama nazo ne inbaki haquri da abinda Mama tayi miki kiyi haquri insha Allah bazata sake ba."

Murmushi ta kumayi tana mai tattara kayan tace.
"Ba komai ya wuce me sunan ki kekuma?."

dariya tayi sannan tace.
" Ni sunana Nafeesat kinga daga yau mun zama qawaye ko ga Anty Aysha ma tace tana sonki kin zama qanwar ta wai zaki na zuwa kina taya ta hira ko."

"Ehh mana zanje nima ina sonta ."

ganin tana tattara kayan ne yasa itama ta miqe tana tayata tana ta mata hira suna shiga cikin d'akin ita ta shirya mata kayan sannan suka fara tattara daga ciki har parlour har zuwa cikin kitchen duk suka gyara ko ina suna gama moping aka kira sallah,
al'walah sukayi sannan sukayi sallah suna idarwa Meenal ta shiga wonka riqe da gorar shampoo ita kuwa Nafeesat sai ta zab'a mata kayan sawa ,
tana fita ta shirya tsab abinta sannan sukayi ihsha parlour suka koma Nafeesat taje cikin gida ta karbi sitirecan Anty Aysha tana zuwa ta zauna kan kujera cikin fara'a tace ,
"Allah ko in na ja miki gashin kin nan zaizo har gadon bayan ki gashi mai sulb'i."

Ita dai Meenal sai murmushi lokaci d'aya ta gyara gashin nan yayi tsab ya miqe sai sheqi yakeyi da qamshi daga nan kuma tace.
"Meenal muje cikin gida ."

Kai ta jinjina a hankali tace.
"a a bacci nake ji."
murmushi tare da cewa .
"Hmm toh bari in tafi sai da safe."

"Na gode BANDIRAWO am
Na gode y'ar uwa ta."

Tace mata lokacin da take fita .

Toh kawai tace ta fita,
tana fita shiko General ya shigo Captain Sani na biye dashi a baya riqe da leda a hannun shi .

a parlour suka zauna suka d'an ci abin ci itako tana cikin bedroom d'in tayi konci yarta tana jinsu can kuma bacci ya fara d'ibarta kafin woni lokacin tayi bacci dan sanyin AC dake ratsata .

Su kuwa suna gamawa Sani ya miqe tare da cewa .
"Sai da safe oga."

Kai ya d'an dago cikin sanyi yace.
"Gobe fa zamuje katsina ka shirya dan da wurin zamuje mu dawo."

Toh yace tare da fita a ranshi yana jin dadi dan harga Allah yana son yaga Ogan nashi na zuwa gun mahaifin nashi.

Abba mahaifin Aliyu tunda ya rabu da mahaifiyar Aliyu Ammi bai sake zaman Kaduna na tsawon wata d'aya ba sai dai ya kan d'an zo yaga halin da Aliyun ke ciki kuma har yau bai kuma Aure ba ya koma can yana rayuwa shi d'aya kamar wandda akayiwa sihiri da zaman kadunan,
shiko Aliyu yakan dan je kad'an-kadan in Daddy ya nace mai da yaje d'in.

Captain Sani na fita ya miqe ya nufi bedroom en bai kalli ko ta inda take ba ya bud'e durowar ya zaro blanket sannan ya matso bakin gadon kanshi a gefen yasa hannu da nufin ya d'auki pillow,
da sauri ya d'an juyo jin hannun shi ya sauqa kan ququnta ido ya zura mata ganin gaba d'aya ta mirgino sauran kad'an ta rikito qasa.

Pillow ya zare tare da Jan tsaki ya juya a fili yace.
"In kin rikito ai zaki tashi."

juyowan da zai yaga tayi luuu....

*kuyi haquri In na samu time zuwa dare zan qara 1 page*

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣3⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers

*Dedicated 2 Zahra Muhammad Mahmoud (Surbajo) godiya mai tarin yawa hak'ik'a bazan manta k'aunar da kike min ba😍😍😘*

*My dear Khadija candy Allah ya baki lafiya rabbi yasa zakkan jikina Allah ya baki lfy*


``` Masu karatu kuyi haquri a pages na biyu da suka gabata akwai inda na d'anyi typing error duk da dai nasan kun gane```



Ta mirgino tayi k'asa,
Shi kuwa,
tsayuwa yayi ya tsura mata ido yana mai yin murmushi mugun ta a cikin ranshi yayin da ya murtuqe fuska kuma.

Ita ko Mirgino war da tayi yasa tayi k'a ba tare da sani ba,
kanta ya bugi jikin tayis d'in lokaci d'aya azaban ya ratsata a firgice,
ta bud'e ido cikin gigin bacci da tsaro ta mik'e tsaye tana dafe da goshin ta,
tana ta yarfa hannu da za gaye tsakiyar d'akin tare da sakin kuka cikin sanyi murya tana.
"Shiihhh wayyo goshi na k'afata wayyo k'eyana,
wayyo Bappa na".

Harara ya cillah mata cikin tab'e baki ya ja dogon tsaki tare da juyawa ya koma parlour.

Tsakin da yaja ne ya tuna mata ina take kuma dawa take tare.

Tsoro ne ya rufeta ita a ganin ta turota akayi ga zogi da goshin ta keyi mata tausa yin kanta da kanta ne ya kamata sai ta koma jikin k'ofar fitan ta rakub'e tare da sakin marayan kuka mai sanyin sauti .

Yana parlour dai Amman yana jinta bacci yake sonyi ta addabi rayuwar sa da kuka gashi dama rayuwar takura yakeyi a kan 3str d'in da yake kwana sannan tazo ta toshe mai kunne da kuka,
a k'ufule ya mik'e ya nufi d'akin,
yana shiga ya tsaya kanta cikin tsuke fuska da murtuqe fuska voice a dak'ile ya nunata da yatsa cikin fad'a yace.
" Wallahi ki fita idona in rumtsa kin isheni wallahi kin isheni iya isa,
yarinya kina nan kamar mayya dan tsabar fitina yenzu tsakiyar daren nanne zaki tashi ki tasoni da kukan banza."

Kai tayi ta girgiza mai cikin fidda ido woje dan tsoron masifar da yake mata jikinta har yana b'ari cikin tsoro ta kalleshi baki na rawa tace.

"a a fahh, fahh turoni akayi na fad'o daga kan gado gashi goshi na sai ciwo yake k'uguna ma ciwo yake."

Matso ta yayi cikin fad'a tare da nuna mata yatsa yace.
"Ciro idonki a kaina wallahi inba hakaba sai na k'wak'ule k'attin idanun nan naki ki rink'a zaro minsu kamar y'ay'an boris mayya fiti nenniya,
wazai tureki da kike cewa turo ki akayi kina nan kamar mage sai shegen son jikin tsiya da yawan birgima kina ta faman mirgine-mirgine kina shiga cikin blanket,
ba dole ki rikito ba,
gobe ma karki nitsu kiyi ta shure-shure a cikin bacci ke da fad'uwa kuma kun k'ullah,
wallahi kuma kika kuma bud'e baki da sunan kuka ,
Hmmmm tam kinsan sauran."

Tunda ya fara surfa mata masifa ta koma jikin ginin tana zubda k'ollah sai numfashi da takeyi sama-sama cikin tsoro.

Tsawa ya kuma buga mata .
"Maza kauce jeki konta."

Nur- nur ta juya kan gadon ta konta cikin sanyi ta rumtse idon ta,
shi kuma blanket ya zaro cikin durowar ya cillah mata a kanta yace.
"Mage kawai ga blanket an k'ara miki sai kiyi ta nad'ewa a ciki sauran kuma kar kiyi Addu'a,
sai kin samu abinda zai turokin da hasken wallahi ni ba ruwana ."

yana kaiwa nan ya juya ya kashe wutan d'akin sannan ya koma parlour yayi konci yarsa,
Ita ko kukan take sonyi kuma tana tsoro ga duhun da ya barta a ciki,
a haka dai har bacci ya tsure ta......


Washe gari tun 7:00 Am suka gama shirin tafiyar su,
ita kuwa lokacin ta gama kimtsa cikin d'akin ta fito parlour da nufin ta d'auki tsintsiya zata sharo d'akin har zuwa parlour,
tana fita ta same su Sani na tsaye rik'e da laptop en ogan nashi shiko yana zaune kan kujera ya sunkuyo kanshi yana d'aura igiyar takal manshi,
cikin sanyi ta kalli Sani fuska a d'an sake tace.
"Bandirawo ina kwana?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"lfy lau Meenal,
kin fito ke nan,
dama yanzu zamu tafi kuma gashi bamu sallah meki ba."

"Allah ya kiyaye hanya ."
tace dashi tare da juyawa gun General murya can ciki tace.
"Jam b'an d'una,
Ina kwana?."
Bai kula taba bare ya amsa sai mik'ewa da yayi cikin bada umurni yace.
"Captain mu tafi ."
"Toh" yace tare da bin bayan shi ,
itako ido kawai ta tsura musu ,
har sunje bakin k'ofar fita ya juyo fuska a had'e yace.
"me kike zura min ido?
wallahi ki kula ko k'ofar nan bance ki takoba."

Kai kawai ta gyada mai,
sannan taci gaba da aikin ta..

*Katsina*
10:00Am sun isa Katsina,wani gida ne d'an ma daidaici suka shiga bayan mai gad'i ya bud'e musu gate,
Sani nayin parking ya fito ya bud'e mai mota sannan ya fito cikin gidan suka nufa kai tsaye,
wani parlour suka shiga tare da yin sallama suna shiga General ya zauna kan chains carpert din dake tsaki yar parlour shiko Sani cikin d'akin ya
wuce,
Jim kad'an sai ga Sani ya fito shida wani mutun mai d'an girman shekaru Wanda da ka ganshi zaka San shine mahaifin General dan kamar halitta dake saka ninsu farine tas mutu min mai kyawun fuska gashin kanshi mai yelwa da shek'i.

Kan kujeren dake bayan Aliyu ya zauna .
Murmushi yayi cikin kafe d'an nashi da ido yace.
"Haiydar sai yaushe zanga happy a fuskar ka?."

Kai ya sunku yar cikin sanyi yace.
"Abba Ina kwana? ya jikin ka? kana shan magani ko?."

Murmushi yayi tare da nunawa Captain Sani General d'in da ido sannan yace.
"Alhamdulillah da sauk'i."
Captain ne ya zauna gefen Abban a k'asa cikin sanyi yace.
" Abba Yau kam ai zamu tafi tare da kai dan gwara ka koma kusa da oga yafi."

Shiru yayi yayin da shiko Aliyu yake jiran amsar sa shima Captain ido ya zuba mai.
A hankali ya sauk'e ajiyar zuciya sannan yace .
"Me ya rege min da zaman Kaduna? me zanje inyi a can?."

Wani irin nannau yan numfashi General ya sauk'e cikin sanyi yace .
"Sani aini na saba da rashin iyaye a kusa dukda son kasan cewa dasu dana keyi Abba baya k'auna zama dani bansan laifin da nayi mishi ba."

Shiru Abban yayi tare da shafa kansa shi kuwa Captain Sani Abban ya kallah cikin sanyi yace .
"Abba General fa yayi Aure yanzu matar sa na gidan kuma Abdul da Mama sun matsa mata."

Tunda Captain ya yace Aure Abba ya zura mai ido cikin mamaki yace.
"Sani Aure kuma? Haiydar yayi Aure? waya aura ? y'ar waye? yaushe akayi auren banda labari?."

Haka ya jero mai tabbayoyin cikin kad'uwa shiko General fuska ya had'e yana kallon Sani cikin yana yin.
"Wayace ka fad'a."
Shiko Sani ya kalli irin kallon da ake mai amman sai yayi kamar bai gani ba,
ya maida hankalin shi gun Abba cikin nitsuwa ya mai bayani yadda akayi auren.

Hamdala Abba ya rink'ayi cikin happy yace.
"Insha Allah Yau tare zamu tafi."


Ita kuwa Meenal suna fita ta gama sharan nata ta goge komai sannan tayi wonka ta fito tana tunanin me zataci ta shiga kitchen gas ta kuna sannan ta d'aura ruwan tea ta dawo parlour,
can jimawa kad'an taji k'amshin tafasan tea din da yake tasa citta da kanamfari, ruwan
tea din ta d'ebo amti sai sugar sannan tazo tana d'an kurb'a cikin kewan gida,
Sallamar Nafeesat ce tasa ta juyo cikin jin dad'i dan tasan zata d'ebe mata kewa,
gefenta ta zauna cikin fara'a tace.
"Meenal mu je gun Anty Aysha tace naje na tayata girki niko in ason muje tare."

Shiru tayi tana tuni gargad'in wannan mugun ita kuma ta gaji da zaman kad'aici dan haka kawai sai ta mik'e cikin sanyi tace.
"Muje."

Suna fita.....


By
garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣7⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Pure moment of life writers


Yasa hannu ta bayanta ya tallabe k'eyan ta,
sannan yasa d'aya hannu kan goshin nata ,
ita kuwa ido ta tsura mai cikin tsoron ganin yadda yake murtuk'e da fuska gashi yasa hannu kan goshin ta dake suntume tib,
tafin hannu shi yasa ya danna k'ulun tare da fara murzashi da k'arfi,
cikin azaban da yake ratsa ta tasa hannu ta kamo hanna yenshi duka biyu tana tsalle cikin azaban da zubda k'ollah tsalle take sosai tare da tirjr-tirje tana kuka da magiya.
"Wayyohhhh Allah na wayyoh kaina wayyo goshina zan mutu kaina zai fashe wayyo Bappa na."

Bai kulata ba sai k'ara murza wurin da yakeyi cikin tsura mata ido yana kallon fuskarta da yadda take tsalle kamar yar tsana,
ita kam Meenal zuwa yanzu tuni ta sake mai hannu taci gaba da tsallen da yarfa hanna yenta hawayen ma ya k'afe sai juya kai take cikin fara ganin duhu.


A haka yaci gaba da murza k'ulun har ya b'ace bat,
a hankali ya d'an sake ta tare da tsura mata ido ganin sai wani irin lumshe ido takeyi can sai kuma wasu siraran hawaye dake bin fuskar ta.

cikin tsurawa fuskar tata ido yaga tana wani irin layi kamar mai maye,
tayi wani luuu zata fad'i,
ganin haka yasa cikin sauri ya rik'o hannun ta,
ta fad'o jikin shi sannan tasa hannu biyu ta zagaye k'ugunshi sai kuma tayi lib kamar maiyin bacci.

Haka tasa dole yaja jiki a hankali ya zauna bakin gado da ita,
ita kuwa sai k'ara mik'ewa tayi ta narke a jikin shi,
a hankali ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya tare da lumshe ido,
cikin nitsuwa ya kuma bud'e idon ya tsura su kan fuskar ta,

Baki ya tab'e tare da jan dogon tsaki sannan ya mirgina ya matsa gefe,
ita kuwa sai ajiyar zuciya ta sauk'e tare da gyara konci yar ta,
taci gaba da baccin cikin sauk'e ajiyar zuciya.


Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki a hankali ya shiga cikin toilet d'in,
jiki a mace ya samu ya watsa ruwa sannan ya fito,
gefen gadon ya zauna hannushi rik'e da towel yana goge suman kan shi,
tare da kafeta da ido har zuwa wani lokaci kollon da yake mata ne yake k'ara kashe mai jiki,
da k'yer ya samu ya d'an shafa mai sannan ya shirya cikin galila mai matuk'an kyau kalan sararin sama niya sai farin takalmi da farar hula,
wani irin kyau shigar tayi mai kalan kayan da takalmin da hular sai ya fita tamkar adon sararin samaniya,
kyawun surarsa da cikar haibarsa ya k'ara fitowa ba abin da yakeyi sai k'amshi da shek'i farar fatar sa ta k'ara fito da cikar haibar sa.


Yana gamawa ya dawo gaban gadon ya tsaya yana kallon yadda take rawan sanyin,
a hankali yasa hannushi kan wuyan ta,
jikin zafi kamar wuta,
shiru yayi yana tunanin ko me zayi mata? gashi ko ruwan tea d'in ta na jaraba bata shaba yau.

Kai ya kad'a tare da fitowa parlour,
a tsaye ya samu Captain Sani na jiran shi,
yana ganin shi yayi gaba har ya fita sai ya kuma juyowa jin ba alamun ogan nashi na bayan shi,
yana juyowa ya ganshi ya fito kitchen rik'e da filas da cup ya nufi bedroom d'in,
shi kam Sani murmushi yayi tare da juyawa ya fita yana jiran shi cikin mota.

Shi kuma General kan durowar gefen gadon ya ajiye mata sannan ya juya ya fita,
a babban parlour ya samu Abba da Daddy sunyi shirin su na tafiya masallaci da yake yau jumma'a ane in sun tafi tun safe sai dare suke dawowa tare suka fito ,
a hara bar gidan suka samu ya Amir ma da Anuty Aysha tare da Nafeesat zasuje anguwa,
a haka suka shiga motocin suka fita suna fita motar Abdul kuma tana shiga,
wani irin murmushi mugun ta Abdul yayi tare da cije lips d'in shi sannan ya kuma lasar lips d'in binsu da ido yayi cikin happy ganin duk sun fita mutanen gidan gashi ita kuwa Meenal tana cikin gidan,
cikin sauri yayi parking jikin shi har yana rawa ya nufi cikin gidan..


Su Abba suna fita masallaci suka wuce,
Su ya Amir ko Zaria suka tafi.

Suko su General kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim mai dala suka wuce,
suna isa kai tsaye cikin gidan suka wuce da jagoran Captain Sani,
gidan Alhaji Ibrahim gidane mai girma cike da alfarma da kayan k'awa na rayuwa.

Wani Babban parlour suka shiga bayan sunyi slm an basu izinin shiga,
suna shiga Captain da General Sani suka wuce gaban Alhaji Ibrahim wanda ke konce kan wani tattausan carpet suka zauna,
cikin girmamawa General ya gaida shi tare da cewa.
"Uncle ka rege tunani dan gudun kar ya cutar da kai."

Cikin rawan jiki irin na mara lafiya ya yunk'ura ya zauna tare da rik'o hannun wani mata shi mai cikar zati Dr Jabeer Muhammad wanda d'an uwan captain Sani ne uwa d'aya uba d'aya,
kuma shine wanda Alhaji Ibrahim yayi niya da alk'awarin aurawa yarshi Amina kuma ko yanzu da ta bace bai fasa niyar saba acewar sa tunda bata rayuwa cikin birniba burinshi ya aurawa Jabeer ita dan Jabeer yaro ne mai mutunci da sanin ya kamata ga tausayi kuma dama tun Amina tana k'arama in sunje Membila sai yace itace matar sa shiko Alhaji Ibrahim yayi alk'awari kuma shi Alhaji Ibrahim irin mutanen nanne musu kaifi d'aya fad'a da cikawa ne.

Yana tashi zaune ya kalli General cikin sanyi da rawan murya yace.
"Aliyu na kasa mantawa na gaza daurewa kuka na ina Amina take? ko a wanne halin take ciki? ko ya lafiyar ta?."

Sai ya kuma yi shiru cikin sanyi ya rik'o hannun Dr Jabeer sannan ya kalli su General da sauran mutanen dake parlour yace.
"Ita min kena d'aya tak gashi azzalu mai sun d'auke min ita gashi mahaifiyar tama kullum sai kuka."

Cikin tausayi General yace.
"Insha Allah Uncle zamu maida hankali kan ne mota kuma zamu d'auki mataki."

Shi kam Jabeer sai hannu ya mik'awa General tare da share k'ollan dake bin fuska shi murya na rawa cikin sanyi yace.
"General kuyi duk abinda ya dace ko nawa ne wallahi zamu kashe dan samun dawo war farin cikin mu,
Amina itace burin rayuwa ta itace sanyin idanniya ta bazan iya rayuwa inba itaba ban tab'ayin 2 weeks ban ganta ba duk rintsi a sati sai naje Taraba na ganta Amman gashi yanzu har tsawon wata d'aya ban san halin da take ciki ba."

Sai kuma ya juya gun Alhaji Ibrahim cikin kukan yace .
"Uncle dan Allah gobe a d'aura mana Aure da Amina ni ko bata nan na yarda a d'aura mana aure kuma duk halin da zata dawo a ciki na amince da ita a matsayi mata."

Kuka yake yana magana lokaci d'aya kukan nashi yasa Uncle d'inma kuka Captain Sani shima sai kuka Hajia Amina ma sai kuka yayin da Aysha ko mahaifiyar Amina take cikin gidan bata wurin,
sai wata yarin y'ar budurwa wacce itama take ta kukan wui-wui harda majina a hanci kuma sai kallon General take cikin zubda k'ollah,
da kyer Uncle ya kama hannun Dr Jabeer yace.
"Insha Allah gobe za a d'aura muku auren."

Cikin kukan ya kalli General da Captain Sani numfashi ya furzar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.
"Aliyu na tsani duk wanda ya nesan tani da y'ata ji nake inama ace gani gashi wallahi ban ma sannan wanne irin abu zan mishi ba,
rok'ona a gareku in Allah yasa kuka kamashi kar ku barshi da hankalin shi a mai dashi yadda bazai taba gane banbanci tsakanin mace da namiji ba bare ranshi ya tuna mai ya sace wata."

Kai yake gyad'a mai cikin k'arfin guiwa yace.
"Insha Allah ."

A haka sukayi ta bawa Uncle hak'uri da bashi baki Dr Jabeer kam kamar wanda aka yiwa mutuwa.

Sai lokacin sallah suka tafi masallaci daga nan kuma suka wuce cikin Jaji.


*Abdul*
kuwa cikin farin ciki da mugun ta jikin shi har yana rawa ya kutsa kai cikin ......

By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣4⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers


*Dedicated to Anty Sis*


Kitchen suka nufa,
Anty Aysha na ganin su ta kalli Meenal cikin murmushi tace.
"Meenal ya gida?."
"Alhamdulillah Anty Aysha ya aiki?."
"aiki kam na kam mala ma yanzu zan je in shirya kan dainin ne."

Kula ta d'auka cikin sanyi tace.
"Nafeesat d'ebo sauran mu tafi."

Tare suka shirya komai tsab sannan suka koma parlour Anyt Aysha suka zauna suna d'an hira yayin da Nafeesat da Anty Aysha ke ta janta a jiki,
har zuwa azahar ganin lokacin sallah yayi ta mik'e tare da cewa.
"Anty Aysha zan tafi lokacin sallah yayi."

Cikin kula tace.
"Toh muyi sallan a nan mana sai muci abinci in yaso sai ki tafi ,
wota k'il ko zakiyi bacci ne."

Murmushi tayi sannan Anty Aysha ta ce mata .
"Muje ciki kiyi al'wala."
Murmushi kawai tayi tare da binta a baya.

Bayan sunyi sallah ne suka zauna suka d'anci abinci suna d'an hira,
kafin su ankara har 3:13 pm tayi ganin haka ta mik'e cikin sauri tana cewa .

"Kai bari in tafi ."

Nafeesat ce ta kuma tsaida ta a dole tayi sallah bayan sun idar suka kuma shiga kitchen tare suna shiga kitchen d'in itama ta zage suna ta aiki tare dan tana son gane kan kayayya kin aikin ba laifi kuwa ta fara ganewa gashi Anty Aysha na janta a jiki Nafeesat kuwa duk abinda zasuyi sai tayi mata bayanin yadda ake sarra fashi,
dad'i sosai takeji a wannan d'an taraiyar da sukayi dan ta d'auki darusa da yawa ta fara gane komai bugu da k'ari dama ta iya girki kam tsab.

Suna cikin kitchen d'in har zuwa 5 dai-dai zuwa lokacin kuwa sun kammala komai.

*Mutan Katsina kuwa*

har sun iso cikin gida
A gajiye Abba ya zauna a parlour part d'in nasu,
yayin da suka wuce babban parlour gidan kuwa ba kowa dan Mama da Abdul sun fita yawon mugun tarsu ya Amir kuwa da Daddy basu dawo gida ba tukun.


Captain Sani ne yaje ya kawo musu ruwan sanyi tare da zama gefen Abba yana .
"Abba sannu."

"Yau wa Sani sannu kai ma dan ai kaine mai tuk'in ka fimu gajiya."

Shi kuwa General wucewa yayi cikin bedroom yana shiga yayi shiru a nufin shi ya saurara ko tana cikin toilet d'in,
shiru ba motsi hakan yasa ya matso jikin k'ofar a hankali ya dan buga k'ofar ,
shiru ba motsi tsaki ya d'an ja sanna ya murd'a marfin tare da d'an lek'awa,
wayam ba kowa ganin haka yasashi juyawa cikin tsuke fuska kitchen ya shiga nan ma bata ciki ganin hakan yasa ya fito a fusace kai tsaye tsakiyar babban parlour yaje ya tsaya tare da tsurawa tsakiyar parlour ido cikin d'aga murya tare da tsuke fuska ya fara aika mata kira.

*"MEENAL"*
sai kuma ya d'anyi shiru tare da k'ara had'e fuska dan yasan yanzu Mama zata zo tayi rashin mutuncin nata.

Jin shiru bata amsa ba yasa ya fara antaya mata kira

Please Login or Register in order to submit comment