Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu yalwar gashi suna da sura ta haqiqa.

10:00 Am
Suna cikin garin Membila daga nan
Aliyu ya tsaya tare da tara yaran shi cikin sanyi,
ya tsura musu ido d'aya bayan d'aya
da salon bada umurni yace.
"Sani daga nan su Garba zasu tsaya ni da kaine zamu qarisa cikin dajin domin saimun ga yanayin wurin sannan mu shigo baki d'aya".

Cikin bin umurnin suka sassara mai tare da qamewa daga nan,
ya jaqoran cesu zuwa tantin sojin dake kula da dajin Membila sabida yawan kashe fulanin wurin da akeyi.

Sai da ya tabbatar ya sama musu duk abin buqata,
sannan suka wuce shida Sani.

Tafiya ma budin ilimi taken Mahmoud Nagudu,
Tafe suke Sani na mishi hiran yanayin wurin tare da nuna mai tsirrai masu ban sha'awa,
shi kam Aliyu bin hanyar yake da ido cikin mamaki tabbas hanyar Membila abin kallone da bada mamaki,
tafiyar suke Sani tun yana surutu har yayi shiru.
Cikin sanyi ya kalli Aliyu tare da cewa "Oga inaga daga kan dutsen nan hanyar ta tsaya ba ci gaba sai waccar hanyar da muka wuce".

Kai ya d'an juya tare da cewa ka zagaya bayan dutsen nan ta gefen dama akwai y'ar qaramar hanya tabin shanu sai mubi ta wurin"

Haka suka kutsa cikin dajin yayinda suke ta ratsa tsaunuka wani wurin badan Hilux bane da bazai fitaba.

Wasa-wasa sukayi yawo cikin tsaunu kan duk ya zagaye rigar Fulani dake ta wurin baiga rigar Rumoh ba,
gashi da zaran sun tsaya a wasu rigan dan sunyi tabbaya sai su samu ba maza sai mata matan ma yara dan mazan sun tafi kiwo matan ko sun tafi tallar nono shiyasa sai yara suko da yaran sun gansu da yinifon din sojojin da bindiga a hannusu sai su gudu.

A hakan har d'imuwa ta fara dibarsu cikin jarumta Aliyu yacewa sani
" Muyi gaba gancan wani ma ki yayin".

suna zuwa gunshi daga d'an nesa dashi sukayi parking sannan suka fito tare da cire rugunan jikinsu suka bar best sannan suka qarisa gunshi cikin sanyi dan gudun kar ya tsorita Aliyu yai gyaran murya tare da cewa.

"Akuma *BANDIRAWO*, noi layde e dabbaji men"
Sannu dan uwa ya daji da dabbobin mu"
Cikin mamaki ya juya gunsa tare da yin magana cikin fillanci yace .
"Ra ga Allah Surbajo toi yiftu d'on Mi hetayi on"
Kai d'an Saurayi ina kuka fito ban ganeku ba"

Daga nan kuma sukaci gaba da magana cikin fillanci yayinda Sani ko ya bushe a tsaye mamaki yake wai ase dama General Aliyu ya iya fillanci ji yadda ya juye kamar cikin su yake rayuwa shi kam sai murmushi yake dan tabbas Aliyu ya burgeshi ase akwai masu adana yarensu dan irin wannan ranar.

Suko Aliyu zuwa yanzu d'an fullo har ya masoshi tare da rik'o hannushi ya miqa mai sanda cikin fillanci yace.
"Ko zakayi kiwo?"
Ba kin shi kawai ya d'an motsa alamar murmushi sannan yace .
"Yanzu dai tabbaya muke sai wani jiqon in na kuma zuwa sai muyi kiwon ko".

Ido ya tsurawa fuskar Aliyu tare da cewa.
" kai ko bakayi fillanci ba wlh zatinka ke muna kai asalin ba fulatanine gaba da baya,
dan haka ba matsala menene tabbayar?".

Ajiyar zuciya ya d'an sauqe tare da yamutsa fuska yace .
"Rigar Rumoh nake nema".

Cikin tsoron ya zare ido tare da ja baya gani da nunashi yana fad'in.
" kodai kune mutannen birnin nan da kuke zuwa kuna korar mutanen rigar Rumoh! kuna kashe su! kuna kama musu yan matan su! kuna tafiya dasu birnin! sannan Ku sace musu shanayensu! da raqumansu! kuna zalum tarsu?".

Sani ne ya buga mai tsawa cikin fad'a yace.
"Shi wannan mai gaskiya me baya aiki sai na gaskiya shi ba mugu bane shi mai taimakon wanda aka zalum tame".

Cikin tsoron yace "ya zanyi na yarda?".

Qara matsoshi yayi tare da cewa.
" Shin kana jin General Aliyu Muhammad Umar Rumoh?
shin kasan shine shuga ban kare haqqin makiyaya dake cikin fad'in wannan qasa tamu da suke cikin dazuzzuka da tsaunuka? shin ko kasan shine soja na forko d'aya rasa cikin dajin Sambisa ya kuwa ci nasara?".

Shiru yayi tare dayin murmushi ya matso kusa da Aliyu a hankali yace.

"BANDIRAWO ka makaran kana can kana baiwa wasu sashuka na qasarmu ranka dan ka karesu yayinda masu b'arnar sukazo tushenka suka tarwatsa mutanen ciki suka koresu suna kashe na kashewa suka qona na qonawa".

Cikin tafasan zuciya Aliyu ya rumtse idonshi tare da cewa.
" Muje ka kaimu Rigar Rumoh na gani".

Shiru yayi tare da siyayar da hawaye ya kamo hannun Aliyu cikin takaici yace.
*Bandirawo* a inda muke tsayennan cikin asalin rigar Rumoh ce ai an dad'e da watsa rigar Rumoh ta zama wurin kiwonmu yau kimanin shakaru 4 kenan da y'an ta adda suka hana rigar zaman lafiya sabida suka watsasu,
Kaga wadan can rigogin dake kusama
kullum cikin baraza na ake musu kan dole subar nan ".

Jikin jijiyar bishiyan da suke qasanta Aliyu ya zauna tare da dafe kanshi har zuwa d'an wani likaci sannan kuma ya miqe tare da cewa Sani.
" Shi kenan na rasa ma dafa na rasa ma dosa mu tafi Sani zan qare rayuwa ta ba farin ciki".

Cikin sanyi da tausaya mai Sani ya miqe tare da cewa"oga kaqa yamma tayi kuma ba zamu gane hanyar ba mu roqi Gainako ya rakamu".

Matsosu gainako yayi ganin suna tafiya dan Aliyu ya muna baya buqata.
da sauri yasha gaban sa cikin sanyi da jin son shi yace.
"Bandirawo kalli kan dutsen can da wancan qoraman".
Ido ya tsurawa dutsen da saman qoraman sai wani irin farin hayawi ke tashi tuni wurin ya fara rufewa da hayaqin sai duhu ya fara qaruwa".

Maganar Gainako ta kuma katseshi cikin fillanci dai har yanzu yace.

" kaga wannan yanayin shi muke kira da *Labbare* yanayin ne da yake sauqa da zaran yamma tayi dashi muke kwana sai kuma gari ya waye yake fara tafiya da zaran labbare ya sauqa ko dabbobinmu basu fiye gani sosaiba kuma sanyine ke ratsa ko ina sannan tanan baku da hanya fita sai ta bayan dutsen inko nan zakubi dole sai kun kwana a nan kafin ku samu fita sabida yanzu duk ta inda zakubi zaki hadu da hayaqin labbare da kuma makiyaya sun taso kiwo".

Ido Sani ya dan kuma warewa ganin a take wurin ya fara wani irin yanayin duhu da sanyi mai tsananin gaske.

Shi kam Aliyu duk bai ganiba don baijin komai
Amman gani tako ina dabobine ke faso dajin na fita yasa dole yabi hanyar zagayen yayin da Gainako ke binsu a baya tare da sakin wani irin ihu irin na makiyaye da dabobnsu,
aiko sai ga dabobin sun biyishi a baya.
Cikin d'aga sauti yace.
"BANDIRAWO Ku biyoni zan nuna muku hanya".
Jin haka yasa suka rinqa bin shi a baya da motar su.

Tafiya mai dan nisa sukayi
Sai gasu sun fito ta bayan wata rigar Fulani mai matuqar kyau da tsari rigace mai zagaye da ni'imomi da korayen tsirrei ta bayan rigar shukoki ne masu matuqar kyau daga gaban rigar kuma wata koramace mai ruwan garai-garai ke gudana sai dutsen dake gaban qoramar gaba d'aya wurin sai ya banda wani kalan qamshi da ni'imah.

Gainako tsayuwa yayi tare da ajiye sand'ar kiwonsa a wani fili mai farin yashi dake gaban qoramar sannan ya juya gunsu dai-dai lkcin wani farin dottijo ya fito cikin wani gida daga dukkan alamu gidane sai dai yanayin gidane mai zagaye da katanqar manyan duwatsu,
kai tsaye gunsu dottijon ya nufo cikin sanyi da tsura musu ido tare da murmushi
cikin sanyi yace.
(" Surbajo waru d'o")
"D'an saurayi zo nan"
Cikin sanyi suka matsoshi Sani ne ya gaida shi shiko Aliyu kawai bin shi da ido yake .
Cikin sanyi ya juya tare da cewa su biyo shi.
Shi kam Aliyu bin shi kawai yake cike da mamaki inane nan kuma Gainako ya kawosu.
Suna shiga tsakiyar gidan
dottijon yace
"Badd'i waru an e Inna waziri"
Badd'i kizo keda Inna waziri kuzo da madara da ruwa munyi baqi".
dai-dai lkcin wata Yar budurwa mai kimanin shekaru 16 ta fito daga cikin wata bukka riqe da gwaryya a hannuta kanta a qasa tafiya take cikin kula da qoryar karta subuce ta fad'o ta fashe,
tazo dai-dai kan Aliyu da yake sunkuye yana qoqarin kwance but din qafafunshi qoryar tai qasa......

*Wasa farin girki masu karu yanzu muka fara shiga cikin labarin muje zuwa*

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 4⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers
P.m.l.w


*Dedicated 2 Ummee pinky & Becky Tika tare da Hanan smart*


Ta fad'a gefen shi lokaci d'aya ya d'ago kanshi cikin sauri don jin d'umin madarar shanun da ya ratsashi gashi duk ya watsumar a jikinshi har izuwa fuskar sa.

Harara ya cillah mata cikin murtuqe fuska lokaci d'aya ya had'e gira sama da qasa yana mai binta da wani irin mugun kalloh,
duk jikin sa sai d'iga yake tal-tal da nono.

Ita kuma Bodd'i qasa tayi da kai sai kerma da jikinta keyi kar-kar hatta numfashin ta sai da ya sauya salon harbawan da yake,
cikin tsananin tsoro yana yin General Aliyu baki na rawa ta rinqa d'an ja da baya cikin sanyi tace.

*"Wad'u muyal BANDIRAWO* kayi haquri dan uwa".

Cikin murtuqe fuska ya kuma watsa mata wani mugun kallo da yanayin jin haushin abinda tai mai yaja wani irin ajiyar zuciya tare da jan d'an gajeren tsaki dan haqiqa kunyar dottijon nan yaji ba dan shiba da zai zuba mata mari kam ai ita ba makauniya bace.

Itako tuni ta jabaya gun dottijon cikin fillanci tace.

"Bappa bari na kawo musu wani nono"

To yace tare da cewa.
"Ki kula fa karki sake zubda Wanda zaki kawon."

Kai ta gyad'a mai tare da juyawa cikin sanyi ta komai cikin gidan.

Shiko General cikin sanyi da d'an rad'ad'in zafin madarar ya kalli dottijon cikin fillanci yace.
"Bappa ni yanzu zan d'an watsa ruwa a jikina don na cire wannan kayan".

Toh yace tare da miqewa yana fad'in .

" Toh bari naje na sa a kawoma ruwan d'umi dan sanyin zaima yawa gashi labbare ya fara sauqa ga sanyin magriba ga sanyin yanayin damina."

Kai ya jinjina tare da miqewa cikin sanyi yace.
"A a Bappa ba matsala zanyi ko da mai sanyin ."

Cikin fahimtarwa dottijon yace .
" kai Surbajo mufa sanyinmu ba irin naku bane bazaka iyaba don baka sababa."

Cikin dan murmushi yace.
"Toh ai jikina ba irin naka banne Bappa nifa jinina a tsinke yake ba kamar naka daya fara bacci ba."

Dariya yayi sosai tare da cewa.
"Toh asheko Yau zaka san sanyin Gembu da Membila ya banbanta da na wuraren da ka saba zuwa a dai cikin wannan qasa tamu kam."

A haka ya muna mai wasu randu nan tab'o guda 3 manya suna jere rabinsu duk an binnesu cikin qasa sai samansu kad'an gaba d'aya jikin su sai naso yake da fidda damshin sanyi,
wata qorya ya d'ago daga gefen randar cikin murmushi ya bud'e randar,
da sauri General ya matso cikin sha'awa
yakarb'i y'ar qaramar qoryar yana juya ruwan cikin,
ruwane fari tas har yana wani garai-garai daga tsaye mutun na iya ganin fuskar sa da zanen qasan randar,
d'iba yayi ya cika qoryar sannan ya d'aga cikin fillanci yace.
"(Bappa hato gad'a sudu mai woni)
Bappa ina toilet d'in yake?."

da hannu ya muna mai cikin murmushi da binshi da ido,
she ko shiga yayi cikin sauri don maqariba ta qarato.

Cikin sakin fuska Bappa ya kalli Captain Sani cikin hausar sa da take d'an fita yace .
"Surbajo tashi inkai ka d'akin ku."

Miqewa yayi tare da cewa.
"Toh Bappa bari na d'auko jakar kayan mu a mota."

Bayan ya dawo Bappa ya nufi wani d'an dakin bukka Wanda yake shatin kobo shi dai yana binshi a baya cikin bin tsohon da ido tsohone fari tas mai kyawun fata da gashi sannan da ka ganshi kaga mutun mai sanyin hankali da nitsuwa.

Suna shiga cikin d'akin Sani ya dire jakar General cikin mamaki ya sake baki tare da bin d'akin da ido,
Komai na d'akin tsaf yake sai qamshi yakeyi ba wani tarkace sosai
katifa ce bai girma wacce akayi mata shimfid'a da wani tattausan blanket sannan ga wani blanket d'in kuma har guda 2 a ninke a gefen pillows din da aka jera kan katifar sai d'aya gefen bangon wata y'ar ma daidaiciyar katifarce a jingine sai d'aya
gefen kuma y'an wata kanta ce na mutanen da gaba d'aya cike take da littafai na karatun addinin isilama suna shirye tsaf daga qasanshi kuma wani tattausan sallah yane a shimfid'e sai sauran tsakiyar d'akin dake d'auke da irin kujerun nan na rida sai kuma irin akwatunan nan na zamanin da .

Sani kam yayi nisa a kallon tsarin d'akin cikin shawa tuni ya fara jin sh'awar ya ganshi cikin blanket din nan don sanyin da yakeji yana ratsa mai jiki da jini,
yana cikin tunanin yaji wani irin d'umi mai dad'i wanda ke fidda qamshi mai sanyi.

Kai ya d'ago ganin Bappa da ke ajiye musu kasko mai d'an girma wanda ke cike da rushi jazur dashi,
(Wanda dama duk wacce tasan gembu membila toh kasan tabbas baqo na zuwa forko kaskon rushi suke kawo mai)
Cikin sanyi ya zauna gefen kaskon tare da cewa .
"Gaskiya Bappa sanyin garinku nada dad'i."
Murmushi yayi tare da cewa.
"shiyasa dole muke rayuwa da rushi a d'akin sannan muke shan madaran shanu mai zafi ko kuma ruwan Lipton mai zafi don muke rege sanyin."

Slmar General ne ta juyo dasu cikin mamaki Sani ya bishi da ido ganin yadda yake ta qaqqame jiki sai
d'an bari yake.

kai tsaye kan kujerar ridar ya zauna cikin jin sanyi yace.
"kai Bappa sanyi har cikin hanjina ruwan kamar ruwan qaqqara wlh."

Ido Bappa ya tsura mai tare da cewa.
"Habba dai Surbajo kaifa sabon jinine ."

Kai ya jinjina tare da hard'e Hanna yen shi a qirjinshi kafin ace kobo ya fara rawan sanyi tuquru gaba d'aya jikinshi sai kerma yake yana fidda sautin.
"Shihhhh hahhhhhhh hsshhhhahi."

Ganin sanyin yamai yawa cikin kula Bappa ya tura mai kaskon rushin kusa dashi sannan ya jawo akwatin qarfen dake gefenshi cikin sauri ya zaro wani borgo fari tas mai kauri da laushi
irin borgunan haramin nan ne,
kai tsaye ya,
yana mai borgon sannan ya jawo y'ar qoryar gaban shi ya miqa mai tare da cewa.
"Karb'i kasha madara ce mai d'umi insha Allah kana sha zaka bar jin sanyin ."

Hannu na rawa ya karba ya d'an kurba sai ya kuma cire kai
shiko Bappa ganin bazai sha da yawaba yasa da kanshi ya riqa basho yana kurba kad'an-kad'an har yasha mai d'an yawa a hankali sanyin ya fara raguwar mai,
sai ya tsurawa Bappa ido cikin mamaki a ranshi yake tunani .
iya tsanin shi tunda da Ammin shi ta gujeshi bai tab'a samun irin wannan kulawar ba ya lura cikin qauna Bappa ke mai komai ayyah ashe wanda ya haifeka zai gujeka,
ka rasa sonsu sai wani bare wanda baka saniba zai gwada ma qauna lokaci d'aya yaji qaunar tsohon na ratsashi cikin sanyi yace.
"Bappa maqqariba ta kawo kaifa."

Miqewa sukayi a tare Bappa na gaba suna binshi a baya shi kam General Aliyu da sannan mayafin na jikinshi suna fita a dai-dai qofar gidan suka riski masallaci daga d'an baya kad'an kuma makaran tar alloh ne babba sai qatuwar bishiyar maqqoro daga gabanta kuma wutsiyar dutsen membilan ne wanda daga samanshi ruwa ke kwaranyowa ruwan fari tas gefen dutsen ko garken shanayen Bappa ne bila'adadin da ka juyako tako wanne gefen shanaye ne konce an huhhura musu wuta a tsaka ninsu maganin sanyi da kaska can gefen kuwa lambune mai girma .

Cikin sha'awa Aliyu ya rinqa bin ko ina da kallo har suka shiga masallah cin,
suna idar da maqqariba suka zauna sukayi ta karatu har lokacin isha yayi sannan sukayi ishan bayan sun idar suka nufu cikin gidan
har yanzu dai Bappa ke musu jagora bayan sun shiga ne ya d'auki kaskon ya nufi cikin gida dashi.

D'akin Inna waziri ya nufa tare da yin slm ya shiga y'ar budurwan nan ya samu zaune a gefen gado cikin fillanci yace .
"Bodd'i ina Inna waziri?."

Cikin yanayin ta dayafi kama da sanyi da tsoron laifi tace .
"(Od'o kanderu)
tana kitchen."

Juyawa yayi tare da cewa
"toh zomuje mu kaiwa baqimu abinci."

Binshi tayi har zuwa cikin kitchen d'in nasu,
suka shiga Inna dake rufe akoshin dake gaban ta,
ta kallesu cikin farin cikin tace .
"Bodd'i zo ki d'auki wannan ki fara kaiwa ."

Miqa mata tayi sannan ta karb'i kaskon hannun bappan ta cikashi da rushi ta miqawa Bappa ya karba yana fita ya tarradda ita a bakin kitchen tana jiranshi.

A Jere suka shiga d'akin ajiye musu tayi sannan ta fita,
ta dauko wasu akoshin guda biyu shiko Bappa yana ajiye musu ya fita qofar gida gun d'alibanshi.


Tana dawowa a dai-dai bakin qofar tatsaya tare da yin slm
Sani ne ya amsa gami da cewa.
"ki shigo BANDIRAWO."

A hankali ta shiga ta duqa tare da ajiye musu har zata juya Sani yace.
"BANDIRAWO ke bakya magana ne? ko tsoron mu kikeji?."

Kai ta girgiza cikin sanyi tace.
"a a na gaidaku bakuji bane."

har ya bud'e baki zai kuma magana General ya d'aga mai hannu fuska a murtuqe .

Ganin haka yasa yaja bakinshi ya tsuke.

Itako cikin gida ta koma ta samu Innarta a dakinta tana cin abinci zama tai gefen ta cikin sanyi tace.
"Inna kinga baqinnane?."
Kai ta juya gamida cewa.
"a a Bappa yace yanzu sun gaji ga sanyin da basu saba ba ga dare yayi sai gobe zasu shigo mu gaisa."

Ajiyar zuciya ta sauqe gamida cewa.
"Ni dai tsoron su nakeji gwara ma d'ayan yana da fara'a shiga d'aya kamar mugune baya dariya sai murtuqe fuska."

Dariya tayi gani da cewa
" ke dai kin fiye tsoro."
Haka sukayi ta hira yayinda Bappa ko da yaran sa suke qofar gida .
Su Captain Sani kuwa tunda ya bud'e abinci yaga tuwon farar masane fari tas tare da miyar d'anyen kub'ewa da naman rago ga man shanu da kitse sai qamshi yake d'aya akoshin kuma gasheshshen naman zabbine da yake ta nason mai sai d'aya kuma mai damemmen kunun nono.
Cikin shaqar qamshin yace
"oga wlh abincin nan zaiyi dad'i kar kace bazaka ciba."

Fuska ya d'an tab'e sannan yace .
"Kai dai kaci ni kam banjin kamar zan iyaci."

Dai-dai lokacin Bappa kuma ya shigo cikin fillanci yace.
"Toh bari a kawo ma tea in shi kafi so ga naman nan sai kaci kafin zuwa safe ama abin da kake son."

A dole Bappa ya kawo mai tea din tare da tura mai akoshin naman gaban shi,
cikin sanyi ya d'an kurb'i tea d'in lokaci d'aya kuma ya lumshe ido dan yadda yaji wani irin d'and'ano ga qamshin citta da kanam fari,
naman ya d'an yaga yasa a baki ido ya lumshe tare da cewa.
"Toh Bappa muci tare mana."


Cikin lokaci d'aya Bappa ya sake dasu sukaci abinci suna hira dukda shi Aliyu sai dai ya d'an zuba musu ido ananne Sani yake bawa Bappa labirin wani aiki sukaxo yi kuma ance mutanen rigar da za suyi aikin duk sun qaura daga nan kuma basu mishi wani bayani ba shi kuwa bai musu shishshigin tabbayan su ba,
a nan d'akin suka kwana Aliyu na kan babbar katifar shiko Sani ya shimfid'a d'ayar,
sukayi baccin su cikin blankets masu taushi.

Washe gari bayan sun idar da sallah Asuba suka zauna suka karanta Azkar har gari ya d'anyi haske sannan suka fito cikin girmamawa suka gaida Bappa wanda shiko ya amsa tare da nufar garken shanu,
gamida ce musu.
"Muje ku tayani tatsar nono."

Shi dai Aliyu ya bashi ne kawai dan zumud'in da Sani keyi.

Suna shiga cikin taron shana yen da raquma da tumaki daga can bayan Aliyu kad'an yaji alamun ana tatsar nono cikin qoriya caar caar,
cikin sanyi ya d'an juyo dan ganin wake wannan aikin cikin mamaki ya d'an.......

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 5⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers


*dedicated 2 Ummu amhumy tare da Billy A A & baiwar Allah amnoor*


Ya d'an kalleta a fakaice ganin yadda take tatsar cikin iyawa da qorewa idonta a qasa kamar wacce ta lumshe su yayinda ta kauda kanta gefe kamar mai gudun kar ta shiqi qamshi nono kanshi ya kawar tare da matsowa gefen Bappa cikin yanayin shi na tsuke fuska ya dan shafa kanshi tare da cewa.
"Bappa yanzu nake son zamu wuce dan tafiyar dake gaban mu tana da nisa."

Matsoshi Bappan yayi tare da miqa mai madarar da ya tatso yanzu sai tururi take yace.
"Gashi kasha maganin sanyi."

Kai ya d'an juya a hankali yace.
"kai Bappa da sanyin safiyar nan mutun ya kama d'ura nono a cikinsa."

Murmushi yayi tare da miqa mai har bakinshi ganin shirin bashi yake a baki, yasa hannu ya karb'a tare da d'an sha,
lokaci d'aya ya d'anji sanyi ya sake sa,
sannan ya miqawa Sani sauran shima ya sha,

Haka sukai ta d'an zagawa cikin garken bayan d'an wani lokaci Bappan ya miqe tare da cewa.
"Bodd'i zomu je cikin rafi da aiki a ciki."
Sannan ya kalli Aliyu cikin kula yace.
" (Surbajo war en yaha) Saurayi zomuje."
Shi kam Aliyu ido ya zubawa Sani ganin azarb'ab'in shi tuni shi har yayi gaba ganin haka yasa ya bi bayan su ta gefen dutsen da suka ratsa
A hankali yarinyar da ake kira da Badd'i ta bi bayan shi suna tafe har suka isa cikin lambun.


A hankali General ya lumshe ido tare da hard'e hanna yenshi a qirjin shi sannan ya rinqa d'an zagawa cikin lambun yana mai mamaki ganin irin ni'imomin da Allah yayiwa ma zauna wannan wurin komai mai sanyi Allah ya basu ba abinda babu a cikin lambun na y'ay'an itatuwa hatta tupa da inabi akwai su kad'an a ciki bar pia kam ayaba lemu goiba abarba kakana maggoro dibino kashu,
gefe d'aya kuma rekene iya ganin mutun.

yana cikin shaqar qamshin da wurin ke fiddawa yaji Bappa na cewa .

"Bodd'i kicire wanda bai qarisa nunan ba sabida su Surbajo zasu tafi dashi kinga kar ya logob'e a hanya da zafin mota."

Gunta ya juyo d'an shi yarinyar Sam mamaki take bashi ita bata mgn sai iya barna da jiqa mutane da nono.

Itako bata ma san yanayi ba dan ko inda yake bata dubawa aikinta take cikin sanyinta banana take yanka manya-manya sai kuma ta koma gefen pia tai ta sinko manya sannan ta juya gun Inabi da tupa suma ta had'a saida ta cika kondon kabar guda biyu manya da fruits sannan tazo ta ratsa gefen shi cikin sanyi ta matso Bappa a hankali take magana shi dai ba jin me take fad'iba,
Amman dai ya lura cikin shogoba take magana abinda shiko ya tsana a rayuwar sa ko dan bai tashi da hakan bane.

Kai ya kawar ganin yadda Bappa ke mata magana cikin kulawa harda kama hannu ta yana hura mata iska ko tofi yake mata ne ma oho musu .

Daga nan kuma ita ta fara fita ta nufi gida shiko Bappa ya kira Sani dake ta cin banana kamar biri yace .
"Sani d'auki wannan kondon mu tafi" shiko ya d'auki d'ayan sannan ya kalli Aliyu yace kai kuma d'auki nonunan ayaban nan mu tafi gida."

Toh kawai yace sannan ya d'auka suka kama hanya.

Bayan sun fito ne yaga kab ba shanayen sai y'an qananan da aka bari dan bazasu iya nisan kiwo ba wurin yayi shal sai korayen tsirrei dake zagaye dasu.

Kai tsaye cikin gida suka shiga Bappa na gaba suna baya har qarqashin bishiyar ced'iya dake tsakar gidan,

Inna na ganin su ta shiga d'aki tare da d'auki taburma ta zo ta shimfi d'a musu sannan ta zauna kan kujerar tsuguno dake gefen wurin, Bappa ne zauna tare da kallon Aliyu da ke zaune gefenshi cikin murmushi yace.

" Inna Waziri ga jikanki mai irin halin Sayyadi naki!"

A hankali ta juyo ta tsura mai ido cikin sanyi tace .
"Surbajo me sunan ka?."

Kanshi a qasa yace.
"Aliyu "

Ajiyar zuciya ta sauqe tare da yin murmushi tace .

*"Aliyu Haiydar* babu rego ko gafalelle Haiydar Jan zaki gadanga kusar yaqi ."

Jin kala manta yasa ya d'ago kanshi ya kalleta lokaci d'aya kuma suka had'a ido da ita sai kuma yayi mamakin ganin hawaye na bin fuskar ta .

Sai kuma yaji abun bai mai dad'i ba sai ya rinqa juya mata kai a hankali tare da cewa.
"Kiyi haquri "

Duk da baisan damuwar taba yaji yana tausaya mata itako sanyi taji da ban haquri shi.
Bappa kam sai murmushi yake tare da binsu da ido a filiko yace.

"Inna Waziri baki kawowa jikokin naki abinci ba gashi sunce

Please Login or Register in order to submit comment