Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qara tunzura shi cikin tsawa yace.
"Ke kina jina ina magana kin wani share ni ko ke kurma ce?."

A tsora ce ta d'an d'aga mai kai cikin zare ido da tsoro ta gyada mai kai alamar ehh tana jinshi .

Qara murtuke fuska yayi tare da zare mata ido cikin muryar fad'a yace.

"Kina jina ko wlh doka ce zan kafa ya miki ! kuma umarni ne ! Wlh kika kuskura kika sab'a abinda zance miki Wlh zaki gane kurenki ."

Sai ya kuma d'anyi shiru sannan ya qara tamke fuska yace.
"Kina jina ko?."
Kai ta gyad'a cikin sauri da tsoro .

Cikin bada umurni yace.
"Kinga wannan d'aki toh kada ki yadda kada ki kuskura inga qafarki ko a parlon nanne bare kuma ta kai ga kin fita cikin gidan nan,
Wlh in kuwa kika yarda kika sab'a umarni nina wlh sai kin gommace kid'a da karatu,
sannan kada ki kuskura kice zakiyi wani abu da zai nuna akwai mutun a d'akin nan in kuwa kinqi zaki gane kuren ki."

Kai kawai take ta gyad'a mai tana numfashi sama-sama dan tsoro.

Shi kuwa ido kawai ya tsura mata sannan ya juya cikin rashin kula,
jikin Windows yaje ya rinqa zuge glass d'in yana rufewa sannan ya sassauqe labulayen ya juya ya kunna mata wuta sannan ya fice ba tare da ya kalli inda take ba.


A cikin gidan kuwa su Mama duk sun fito parlorn jin shiru qaran bindigar ya tsaya gaba d'aya sukayi cirko-cirko suna kallon Captain Sani da ya tsaya kamar dolo.

Mama ce ta kalleshi a yatsine cikin had'e fuska tace.
"Kai Sani wato uban gidan nakane yazo yana mana harbe-harbe a cikin gida kamar wani mahaukaci,
koda yake ba laifin shi bane mashayi kuma menene bazai aikata ba yaje ya gama d'ura giya yazo yana qoqarin hallkamu banza asararre ."

Nafeesat ce ta karya fuska cikin sanyi tace.
"Ya Sani ina Hamma Aliyu da gaske tare kuke?."

Abdul ne ya watsa mata harara cikin yatsin fuska yace.
"Can da Allah kauce banza kawai ji yadda kike wani damuwa dashi sai kace qanin ubanki ne shi."

A fad'ace Mama tace.
"Banza mashayi kawai yazo ya cika mana gida da yan iskan sojojin su mashaya ."

Cikin zage-zagen Abdul ya nufi part en nashi yana.
"Bari inje in sameshi wlh ya shiga hankalin shi."

Yana juyowa Aliyu dake tahowa ya d'aga mai hannu cikin tsawa yace.
"Kai dakata tsaya a wurin kar ka qara ko taku d'aya,
dan wlh duk maison kanshi da lfy kar ya kuskura yace zai zo iya kar part d'ina ko wacce ta tsaya matsa yinta daga yau kar wanda ya shiga hurumi na inba hakaba wlh zan iya yin komai ."

Baki Mama kam ta saki cikin qanqantar da ido irin na bala'i tace.
"Iyeh lallai ka isa yanzu kai ko ubanka ya isa yamin iyaka da wani wurin a gidan nan?."

Kai ya kad'a tare da cewa.
"Hmmmmm mutun ya goda mana ya gani Wlh"
Sannan ya juya gun cikin tsuke fuska yace,
Sani je ka kwaso kayan dake cikin motar ka kawo ."


Captain Sani kam juyawa yayi cikin bin umurni ya fara kwaso tsarabar da Bappa ya had'o musu yana shigar dasu har cikin part d'in Aliyun na sawa a fridge duk ya lodasu sannan wasu ko ya shiryasu a cikin kitchen d'in dake jikin parlour.

Shi kuwa Aliyu a babban parlon nasu ya zauna kan kujera tare da d'ora qafarsa d'aya kan d'aya yana d'an buga qafan ya kuma manna glass a fuskar sa ya murtuqe fuska tamau.

Mama ko sai kanne ido take tana juya kai da cije lebenta tana ta huci,
shi kuwa Abdul dama duk iskan cinsa yana shayin Aliyu dan baya mai wasa,
Ya Amir kuwa da Nafeesat murmushi sukeyi dan dama susan Aliyu sarai tarawa Mama yakeyi inya tashi baya sha yinta,
ita kuwa Aysha sai zame jiki tayi ta koma d'akin ta Daddy ko wanda shine mijin Mama kuma Baban ya Amir da Abdul sai Nafeesat kuma Yaya ne ga mahaifin Aliyu,
shima yana gefe yana hoggo yadda Aliyu ya tsare yau yana juyawa Matar tasa ido har ranshi yaji dad'i dan dama yana jin zafin abinda matar tasa take yiwa d'an,
d'an uwanshi sai dai ba yadda ya iya da masifar ta.

Shiko General Aliyu Captain Sani na fitowa yace ya gama shigar da kayan ya miqe yaje ya rufe qofar parlour sannan ya zura key d'in a haljihu suka fice tare.

Ita kam Mama bala'i ta rinqa yi bayan ya fita ya Amir da Nafeesat ko kowa ya kama gaban sa,
itako da Abdul zama sukayi suna ta tubka da warwara ta yadda shima zasu cusguna mishi.

Shiko suna fita kai tsaye Jaji suka nufa suna zuwa ya wuce gidan shi ruwa ya watsa sannan yasa Esther yarin yar dake mai girki su shara da dai sauran su ta kawo mai abinci yad'an ci sannan ya shiga ya konta dan yin baccin gajiya.

Esther aiki takewa General Amman ita har ga Allah take sonshi a burin tako koda bai aureta ba sunyi zaman daduro shiyasa take bin duk hanyar da zata iya kasan tuwa dashi,
Shiko Aliyu ya rigada Allah ya tsare mai imanin shi da sauran jikin shi duk da kasan cewar sa soja kuma mata shi mai cikar zati.


A Gida kuwa
Tunda Aliyu yayiwa Mama kashedi da karta shigar mai part enshi har yana "a goda agani mana " gaba d'aya ta rasa yadda zatayi dan tsanar yaron ga Daddy kuma ko da ta kaimai qorafi mijin Hajia sai cewa yayin "in yazo weekend ki mai fad'a ."

Yau kwana 3 da dawo warsu Gembu Membila Bodd'i kam tunda Aliyu ya qinda ya mata doka ko bakin qofar parlour bata jeba duk da irin rayuwar kad'aici da takeji ga azabebbiyar yunwar da takeji gashi bata san yadda zatayi komai ba dan ko bayan gida sai a hankali da tab'e-tab'e ta gane har ta samu tayi wonka komai dana Aliyu tayi amfanin kama daga soson wanka da brunch har zuwa towel a haka sai dai tayi wankan ta d'aura towel en ta fito ta d'an goge jikin ta sannan ta meda kayan jikina tun Wanda tazo dashi,
tunda shi kad'ai ne kayanta gashi irin kayan nanne na Fulani farine wanda yasha aikin Zane da ulu red da light green sai yellow rigar y'ar qara mace ko cibiyar ta bata gama rufewa ba sai in ta d'aura zanin sama kad'an kanta ko a tsefe yake sai dai ta d'an tub keshi.

A haka tai ta rayuwa inda taji yau d'in yunwa na shirin hallakata gaba d'aya jikin ta sai bari yake ko tsayuwa gagararta takeyi kawai sai ta kama kuka.

Shi kuwa Aliyu a office enshi Captain Sani da yake kamar shine do garin sa ya shiga bayan ya sara mai cikin sanyi yace.
"Oga ya Meenal kwana biyu bamu leqata bafa."

A fili kauda kai yayi kamar bai ji ba a bad'iri kuwa
ido ya rumtse cikin mamaki ya akayi ya manta da ita shi wlh sam ya manta da itama.

Cikin sanyi Sanin ya kuma cewa .
"Oga tun da Yau ba wani aikin yi ya kamata mu leqa cikin Kaduna."

Kai ya jinjina mai sannan ya miqe tare da cewa.
" ba yanzu ba."

Shiru yayi shi kam Captain dan yasan Aliyu kaifi d'aya ne .

Da yamma liris goshin maggariba ya Amir da Sauran mutanen gidan suna tare a babban parlourn sun zuba ido suna ganin yadda Mama da Abdul suke ta kicini Yar b'allah qofar parlon Aliyu Mama ta dage sai cewa Abdul take.
"Wlh yau sai mun b'alla qofar mun shiga har cikin muga tsiyar da ya ajiye a cikin d'akin."

Shiko Abdul ya dage sai buga qofar yake ganin bazai bud'u a hakan ba yasa ya fito farfajiyar gidan ya d'auki qaton dutse yazo yanata bugawa wai shi zai ballah qofar bugu 2 ana 3 ya d'aga hannu zai buga kenan yaji .......


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 9⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers


*Dedication 2 Anty Fauzah & Neena Cool and Maryama Abdool & Momyn sultan*


Toilet ya shiga tare da maida qofar ya datse har ya fara zare rigar jikin sa sai ya lura towel nashi baya cikin toilet en ganin haka yasa ya mai da rigar sannan ya fito.

Kanshi a sun kuye ya tsaya tsakiyar d'akin shiru ya d'anyi na wani d'an lokaci sannan ya d'ago kai ya dudduba cikin d'akin bai gani ba .

Ita kuwa tunda ya ajiye mata ledan a gaban ta tana zaune ko motsi ba tayi ba sai wasa da yatsun ta da take yi tana ta nad'e hannun rigar da yamata yawan .

Murtuqe fuska yayi tare da daqile voice yace.
"Ke ."

Kai ta d'ago cikin tsoro ganin yadda ya had'e fuska, kuma yasa tai saurin yin qasa da kai.

Shiko cika tunxura shi tayi da takaici yana mata magana tana wani mai kallon hadarin kaji.

A kufule yace.
"Ba ke nakewa magana bako?."

Miqewa tayi cikin sanyi da tsoro tace.
"Me zanyi?."
Mitsss yaja tsaki tare da tsuke fuska yace.
"Can tafi ni me zan saki!
ina kika d'ura min towel na ? da kika samu a toilet?."

Sanin akwai abin da ta d'auka a toilet fine ne yasa ta gane me yake nema,
shi yasa cikin sand'a ta wuce gefen shi kan qofar bedroom d'in ta jawo towel d'in da ta shanya data fito wonka.

A hankali ta taka tazo gaban shi cikin sanyi ta miqa mai kanta a qasa.

Shi kuwa ganin yadda take tafiya da yadda ta wani tsaya kamar marigayin zakara,
shi yasa ya tsura mata ido ba tare daya karba ba,
jin shiru bai amshi towel d'in ba yasa ta d'ago kai ,
cikin sauri tai qasa da idon ta tana kallon enda yake kallon.

Wuyan rigar ta ya d'an kalla ganin wuyan ya mata yawa ga d'aya botur d'in ya bud'u ,
itako ganin inda yake kallo yasa ta matse towel d'in a qirjinta sannan ta cukui kuye wuyan rigar ta had'a tare da damqe shi da hannun ta d'aya sai ta kuma tsaya tana d'an zare ido irin na tsoro.

Shi ko General harara ya cilla mata tare da jan tsaki sannan ya komo towel d'in ya fizge ya juya ya shige toilet d'in yayi wonkan shi tsab.


Itako tunda ya shiga ta koma kan gadon ta zauna tare da yin tagumi fuska na zubda qollah sai numfashi take fizga cikin son yin kuka mai sauti sai dai kuma tsoron shi take ji.

Shiko yana fita ya bud'e durowar ya zaro blanket mai taushi da laushi sannan ya zare pillow ya juya ya koma parlour ya konta kan 3str ba tare da jimawa ba bacci yayi awon gaba dashi.

Itako ganin shiru-shuru ba motsin sa ga bacci data fara ji ga yunwa yasa ta zauna kan carpet d'in tsakiyar d'akin sannan ta jawo ledar ta samu ta d'an ci abin cin tana mai zubda qollah sannan ta d'an shan juice ta koma tayi konci yarta kan carpet d'in tana cike da kewan yan uwanta da ta kaicin a haka da ker tayi baccin.


Haka dai sukayi rayuwar kwana 2 tare a d'aki d'aya kuma tun randa ya tabba yeta towel bai kuma mata magana ba,
Sani ke musu hidi mar girki ko yaje Restaurant ya seyo musu in dere yayi Sani ya tafi d'akin Abdul mai targad'e ,
shiko General ya koma parlour itako tana daga ciki,
Mama kuwa da Abdul suna nan suna ta shirin shirya mai gadan zare.


Yau Sunday da yamma Sani da General sun gama shirin komawa cikin Jaji Sani kam har ya d'auki jakar laptop d'in ogan nashi zayi gaba,
ganin General na zaune dole Captain ya dawo ya zauna .

Sukayi gum har zuwa d'an woni lokacin sannan ya miqe cikin d'akin ya nufa a bakin qofa ya tsaya cikin murtuqe fuska da muryar miskilanci yace.

*"Meenal"*
Shiru bata amsa ba a kufule ya kuma cewa.
*"Meenahl* shiru bata amsa ba.

Cikin quluwa yace.
"Bororiya zaki zo ko na tafi?."

Jin haka yasa ta futo da sauri hannun ta na riqe da wuyan rigar ta jikin ta har rawa yake sai fidda numfashi tsoro take.

Juyawa yayi ya nufi kitchen,
itako sai ido ta zura mai,
jikin ta na d'an rawa, bayan ya shige cikin kitchen d'inne
Sani ne ya kalle ta cikin rad'a ganin Ogan a kufule yake yace mata.
"

"In kinji ya kiraki da Meenal ki amsa sannan kome kikeyi inya kiraki kizo yanzu maza bishi kitchen d'in."

Kai ta geda cikin sanyi tabi bayan shi.

A tseki yar kitchen d'in ta ganshi a tsaye sai ta rab'a gefen shi ta tsaya,

Murya a turnuqe yace.
"Kin iya girki ne?."
"ehh." ta bashi amsa a taqai ce

Tsaki ya d'an ja sannan yace.
"Ke ni sauri nake ki matso kiga yadda ake kunna gas d'in sanan ki san abinda zaki dafa kuma kiyi iya ciki ki."

Ido ya zaro mata tare da cewa.
" kina jina ko?."

Kai ta geda mai.

Harara ya watsa mata sannan yace.
"ai baki da bakin magana aikin banza cikin ki ko cikina."
A d'an firgice tace.
"Ina ji."
Tsaki yaja tare da nuna mata komai sannan ya qara da cewa.
"Wlh in kikayi garaje da barin gas a banzace,
zaki babbaka fuskar ki kuma wlh ni ko a jikina."

Toh kawai take ce mai a haka suka gama ya fito parlour tana biye dashi a baya suna zuwa ya cewa Captain Sani .
"Mu tafi."
suna fita yaja qofar ya rufe saurin da yake yasa ya manta bai murd'a key d'in ba

haka suka fita suka tafi.
A parlour suka tarar da Mama tare da Abdul tana d'uma mishi hannu qato dashi,
wucewa yayi kamar bai gansu ba a ranshi kuwa zafi yakeji shi bai tab'a samun irin wannan kulan ba shi ya rasa wannan gatan a rayuwar sa.

Suna fita daga cikin parlour General Aliyu yaji muryar....


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣1⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers


*Dedication 2 Haermeebraeh & One luv and Maryam S bello (MSB)*

*Masoyan BANDIRAWO kuyi haquri da wannan page d'in jiya da yau duk baqi nakeyi amman insha Allah gobe zan mana page 2*


Gaban Mama ya tsaya cikin murtuqe fuska da yamutsa fuska tare da tsura mata ido cikin tsantsar zafi,
Abdul kam a hankali ya rinqa ja da baya cikin tsoro yana kauda kai,
Ita ma kanta Mama tabbas Aliyu yana mata korjini tana jin wani iri in ta ganshi ya koma kamar zaki.

Ita kuwa Meenal sai kuka takeyi cikin sanyi da tsoro ga wani irin riqo da Aliyu ya mata gashi ganin yadda ya juyen ya qara firgitata sai numfashi take ja cikin tsoro da qamqame jikin ta.


Cikin muryar gargad'i da daqilewar voice yace.

"Wlh daga yau ko kallon banza aka kuma yi mata, Hmmmm."

Sai kuma ya cike lips enshi cikin murtuqe fuska.

Cikin qarfin hali Mama tace,
"Hmmm zaka had'iye mune ? ko me zakayi mana? aikin banza ka kwaso karuwa ka kawo mana gidan Aure gidan sunan wallahi ko yanzu sai in dakata inga me zakayi?."

Turata yayi gaban Mama cikin murtuqe fuska yace.
"Gata wallahi gata magoji ya goda aga abin da zanyi."

Shiru sukayi sai tsilli-tsilli suke da ido.

Hannun ta ya kuma ja tare da matso Abdul cikin watsa mai harara yace.
"Duk randa ka kuma tab'ata ko mugun kallo kayi mata wallahi sai na karya ka."

Ya Amir kam da Nafeesat sai murmushi suke ganin yadda Abdul ke zare ido cikin tsoro.

Daddy kam mamaki ne da dariya da kuma tabbayoyi ne a zuciyar sa,
shin ita wannan wacece? me had'inta da Aliyun ? ita y'ar waye?.

Haka ya sake ido da baki yana kallon yadda General yake jan hannun ta,
itako tana biye dashi parlour suka shiga yana shiga ya maida qofar ya rufe,
ita kuwa hannun ta ya yarfa tare da watsa mata harara ya kuma qara tsare fuska cikin fad'a yace.
"Waya baki damar bud'e qofar parlour nanma ? bare kuma har ki fita tsakiyar gida ?,
dan tsabar iskanci da raini nace karki fita shine kika fita ko!?"

Kai take juyawa cikin tsoro da zubda hawaye baki na rawa tace.
"a a tsuntsune fa naga zai mutu."

Ido ya zaro cikin zafi ya d'aga hannushi zai yarfa mata mari dan in ba bugeta yayiba bazata nitsuba,
dan tsabar raini wai ai tsuntsu zata tai maka mari mai zafi ya d'ago zai zuba mata,
sai kuma ya tsaya yatsura mata ido ganin yadda ta,
rumtse idon ta tare dasa hannu ta kama kanta 🙆🏻🙉gaba d'aya jikin ta sai rawa yake sai numfashi take fuzga da qarfi cikin azaban tsoro.

Tsaki yaja da qarfi sannan ya koma kan kujera ya zauna ya lumshe ido tare da damqe hanna yenshi yana kad'a qafa,
ita kuwa jin shiru bata ji sauqan marin ba yasa ta bud'e idon ta a hankali kan kujeran da yake ta tsurawa ido tana kallon yadda jikin shi ke bari kamar mazari sai ta qara takure wa jikin 2str tana mai zubda qollah,

Can dai ya bud'e idon a hankali sannan ya sunkuya yana kunce igiyar takalmin but d'inshi hatta hannushi sai rawa yake dan an tsoka noshi kuma bai samu ya huce ba yana zare takal man ya d'an kalle ta da gefen ido cikin tab'e baki ya miqe cikin fushi ya nufi bakin qofar da ake buga musu a hatsele ya bud'e,

A fusashe ya......


*kuyi haquri my lovely fans na wlh naso yau nayi typing 2 page so baqi nayi yanzu ko na dage zan mana ko 1 page ne mai Reed More 3 toh Wallahi tallahi banji shauqi shiko typing dole sai da nitsuwa da shauqi da kuzari toh yau jikina a mace kuyi haquri insha Allah gobe zan mana 2 pages Ngd*


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 🔟
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers

*Wannan shafi Sa daukar wane ga duk masoyan wannan littafi na BANDIRAWO Ngd da qaunarku gareni*




Daddy na ki ranshi
tsayuwa yayi ba tare da ya juyoba,
shiko Daddy da sauri ya qaraso inda yake yayin da Captain Sani kuma yayi gaba,
gefen General d'in Daddy ya tsaya tare da kallon shi cikin tausayi da sanyi yace.
"Aliyu anya ko a kwana kinnan kana zuwa gun Abban ka."

Shiru bai bashi amsa ba sai ci gaba da tafiya da yake yi a hankali a zahiri da bad'iri Daddy yake sauraro amman kuma bai bashi amsa ba sai tsuke fuska da ya qara yi,
shiko Daddy ba tare da ya damu da rashin amsar saba yaci gaba da magana dan inda sabo ya saba dama yasan bazai bashi amsa ba a hakan yaci gaba da cewa.
"Aliyu kayi qoqarin a satin nan kaje gun Abban ka,
sabida ko jiya naje gunsa bai da lafiya ciwon sugarnshi ya tashi sannan hawan jinin sa ya qara hawa ."

Shiru yayi kawai suna tafiya a hankali shiko Daddy ba tare da damuwa ba yaci gaba da cewa.
"Aliyu kayi qoqarin ka canza rayuwar ka mana ka samawa kanka farin ciki ka tayani roqar Abban ka ya dawo gidan nan kaji ko Aliyu inason d'an uwana ya kasan ce kusa dani."

Kai ya d'an d'ago dai-dai lokacin da suka isa gaban motar.
Ajiyar zuciya ya sauqe cikin yace .
"Hmmm ."

Daga nan kuma yace.
"Daddy aini Abba ke gudu zama da nine baiso ya barni tun yarin ta na rayu ni d'aya a part namu tamkar maye,
sai yanzu kuma ince ya dawo kuma ni d'in dai ina gidan ai ni d'inne da basa so."

Kafa d'anshi Daddy ya dafa cikin kula yace.
"Kaje ka duba Abban ka Aliyu!."

"Toh" kawai yace tare da shiga mota suka tafi.

Shiko Daddy ido ya rumtse yana mai jin zafin yadda d'an qanin nashi ya tashi cikin kad'aici da maraici tamkar maraya al'halin iyaye yenshi na raye,
shine ya kamata ya lura dashi shiko Allah bai bashi mata ta gariba,
gashi sana din rashin gata daya tashi a ciki yasa ya taso mai tsaurin ra'ayi gashi tun asali dama shi miskili ne ga rayuwar kad'aici ta qara sashi ganin rashin gatan da qaunar iyaye da yake ciki,
murmushi ya d'an yi tune yadda yake tsare fuska cikin qin yarda da kowa shi tunda iyayen shi suka bashi yake ganin kowa ma baya son shi,
sai dai kuma duk da haka yana mutun ta Daddy kuma muddin ya mishi magana kan abu toh yakan bi shawarar sa.


Shi ko Aliyu a Jaji yayi kwana 4 ranar jummah da yamma yake ta shirin komawa cikin Kaduna da zugar yan rakiyar sa.

Ita kuwa Meenal tun randa suka tafi batayi gigin yin girki ba sai fruits kawai take sha wanda aka loda mata a firic Yau tun da safe take tajin zaman d'akin ya isheta gani take an binne mata rayuwa ace mutun bazai ga ko idon rana ba.


Bayan Anyi sallan la'asar ne Abdul kuma ya shigo gida cikin takai ci ya kalli Mama dake zaune a parlour bayan ya zauna gefen ta cikin bacin rai yace .
"Wallahi Mama ni nama rasa me zanyi wa wannan Hamma Aliyu wallahi qofar zan balla kamar yadda ya balla min hannu mugun banza duk horonsu na sojoji yake zuwa ya sauqe a kaina."

Fuska Mama ta tsuke cikin takaici tace.
"Wallahi ko yanzu zaman da nake a nan mamaki nake dan naje gefen window bedroom d'in shi wallahi naji motsin mutun tsoro na Allah kar dai Aliyu ya fara tsafi ne da cire kan mutane".

Ido ya zaro cikin kad'uwa da d'an dariya yace.
" Haba dai Mama cire kai kuma? tsafi kuma? Hamma Aliyu d'in?,
a a kam Hajia sai dai in karuwar shi ya kawo ta zauna zaman daduro."

Ido ta tsura mai tare da cewa.
"Ehh haka nefa wallahi kai Abdul kanka na jaa kai kaga ka gane,
toh wallahi muje mu balla qofar."

Miqewa sukayi a nufin zasu je cikin d'akin sai sukaji motsin ana bud'e qofar hakan yasa suka tsaya.

Ita ko Meenal ta window bedroom taga irin qananan tsuntsayen nan wanda ake cewa caccangi so tana son tsuntsayen tun a Membila ganin yana d'an firewa da ker yasa ta fita don ta taima ka mai.


Tana fita shiko tsuntsun ya zagoyo ta qofar aiko yana firewa a hankali,
aiko tai ta binshi a baya tana ta son kama shi tana ta faman murmushi.


Mama kam da Abdul baki da ido duka suka sake suna mamaki lokaci d'aya kuma sai ga Ya Amir da Aysha Nafeesat na biye dasu a baya Daddy da yanzu ya shigo shima sai ido kawai yake binta dashi.

Itako ko a jikin ta don bata ma san akwai mutane a wurin ba,
ganin bata ko kula suba yasa cikin qufula Mama ta qarisa gunta cikin bala'i da zafi ta yarfa mata wani irin gigiceccen mari.

Cikin tsoro ta dafe fuska jiki na bari tuni hawaye ya fara zuba sai tsoro da ya bayyana a fuskar ta,
Abdul ne ya matso cikin tsura mata ido da kallon qirjin ta har yana lasan lips enshi murya a sokan ce yace.

"Ke qaramar karuwa yanzu ke ayanzun kinnan har kin iya biyo ingarman namiji kamar Hamma Aliyu har gida?
lallai ka ruwanci ya zama abin da ya zama."

Mama ce ta kuma ture ta cikin masifa tace.
"Yau zakici ubanki zaki gane kinzo ka ruwanci shima ai nandin ba gidan ubanshi bane kuma nan ba gidan karuwai bane."


Nafeesat ce ta matso cikin tausayin yarin yar da tagani wacce bazata wuce sa'arta ba,
murya na rawa tace.
"Ayyah Mama zaton fa zunubi ko daya ya kasan ce gaskiya,
daga ganin ta kawai Ku bita da qazafin zina Mama kunfa san hukuncin maiyi wa wasu qazafin zina a musulun ce kalle tafa mai kyau da ita".

Ture ta Mama ta kuma yi sannan ta yarfawa Meenal wani wawan mari har saida tayi tanggal-tanggal kamar zata fad'i.

Dai-dai lokacin General Aliyu yayiwa parlour diran mikiya ganin suna tsaye cirko-cirko gaba d'ayan su,
ga Meenal kuma a tsakiyar su sai kuka take yi cikin sheshsheqa.

Su duka basuma san ya shigo ba sai da Mamata d'aga hannu zata kuma yarfa mata wani marin,
ita kam ido ta rumtse cikin tsoro .
Shiko Aliyu cikin. daga burya da zafi yace.

*" Meenal* ."

Jin muryar shi yasa gaba d'aya suka juyo inda yaken,
ita kuwa cikin tsoro da gudu ta juya da gudu tayi kanshi tana zuwa ta tsaya bayan shi tana kuka me cin rai.

Hannun ta General Aliyu ya kamo cikin takun isa da fushi cikin yanayin gargad'i ya yawota har......


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣2⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writer


*Wannan shafi naku matan GARKO group GARKUWAR Fulani na gaida ku a duk inda kuke ina qaunar Ku ina al'fahari daku*



Ya juya ya

Please Login or Register in order to submit comment